Kenza eBookz

Yarima suhail complete novel - Chapter 11

Yarima suhail complete novel - Chapter 11

Yarima suhail complete novel Chapter 11: Yarima suhail complete novel Chapter 11. mama ce tace haba zarah ya kamata kid'auki k'addara muma ba a son ranmu…

3,345 words

mama ce tace haba zarah ya kamata kid'auki k'addara muma ba a son ranmu hakan takasanceba dan dai babu yadda zamuyine kinga ba zamuk'i amincemataba tunda har tazo gida tanemi alfarmarmu.

Zarah mik'ewa tayi tsaye tana kallon iyayen nata tana girgiza kai, cikin kuka tace kawai dai kuce kun siyar da ni, yanzu kud'i zasusa kubayar da ni? bakwa tsoron suwulak'antani? wlh bana sonsa kuma ba zan ta6a sonsaba inma dan kud'insu yasa kukayi min haka toh wlh saidai kumaida musu kud'insu domin ban aminceba, ni malam bello zan aura.

Yaya Rauda tace zarah wai minene haka kikeyi?

zarah cikin d'aga murya tace kubarni yaya rauda ba zan ta6a amincewa ba.

Aysha tace yaya zarah su abbah fa kike d'aga ma murya.

Zarah dasauri tatoshe bakinta da hannuwanta tana girgiza kai tace kugafarce ba zan iyaba, tana gama fad'in haka tashek'a da gudu tashige d'aki tafad'a saman katifarsu tana wani irin kuka saikace wadda aka aikoma da sak'on mutuwa.

gaba d'ayansu jikinsu yayi sanyi musammanma su Abbah da mama da basu d'auka abun zaiyi zafi hakaba.

Rauda ce takalli iyayennasu tace Abbah kuyi hak'uri 6acin rai ne yasa zarah tayi haka ammah ai tana da sanyi natabbata zata sauko daga fushin da take.

mama tace kar kudamu nasan halin d'iyata ni zan shawo kanta da kaina.

Abbah dai girgiza kai yayi takaici duk ya cikasa

Aysha ce tace Abbah kayi hak'uri zata safko yanzu tad'auki zafine saisa, ammah fa naji dad'i da zata auri yarima wlh ya had'u sai ma da nagansa a wajen safkarsu.

Rauda tace wlh kau ni har nahango sunyi match sosai, cike da murya Aysha tace yayata zata zama *Gimbiya Zarah* matar *Yarima Suhail* dak'uwa mama tayi mata tace gidanku munaso murarrasheta tasafko sai kinja ta jiyoki.

Aysha cike da farin ciki tarik'e bakinta da hannu tace afwan na daina.

mama kallon Abbah tayi tace malam kar kadamu insha Allahu Zarah zata safko ni zanma je na lallasheta har tafahimcemu.

malam murmushi yayi yace toh Allah yasa tafahimta inma dai bata aminceba zan fasa basu domin ba zanyi mata doleba, duk yadda kukayi da ita sai kufad'amin yanzu dai bari intashi infita koma mekenan sai nadawo

gaba d'ayansu sukace adawo lafiya.

bayan Abbah ya fita Rauda kallon mama tayi tayamutsa fuska tace mama yau naman kaza nakeson ci, murmushi mama tayi tace Rauda kin cika kwad'ayi tashi ga 1,500k kuje wajen dauda mai kaji yayanka yafige sai kuzo kuyi mana pepper kowa yaci.

Rauda cike da jin dad'i tace toh mama yanzu ko zamuje muna godia.

Aysha ma cikin murna tace Allah yabarmana ke maman gimbiya.

Mama duka takaima Aysha tagoce suna dariya ita da rauda, mama tace sai naci gidanku inbakuyi wasaba.

mik'ewa mama tayi tace kuyi sauri kuje kudawo ni bari inshiga wajen d'iyata in rarrasheta.

mama ko da tashiga lokacin zarah ta ci kukanta, kwance take kanta yana kallon ceiling d'in d'akin hawaye kawai suke zuba ta gefen idonta, mama gefen inda zarah take kwance tazauna tana mai k'arema zarah kallo da duk idanuwanta sun kumbura.

A hankali mama tace zarah kuka kikeyi ko? shuru zarah tayi batace komaiba, mama cigaba tayi da cewa kiyi hak'uri zarah wlh muma ba'a son ranmu hakan takasanceba dan dai babu yadda zamuyi mubijire ma buk'atarta domin yadda tazo ta aje girma da matsayinta tana rok'onmu mu amince mata muba d'ansu aurenki, hmm zarah munsan zakiyi tunanin ko k'wad'ayine yasa mukayi miki haka ammah wlh ba haka bane *k'addara ce* kawai, domin kowane iyaye suna burin ganin farin cikin 'ya'yansu koya suke suna son ganin farin cikin yaransu ko da ace zai tauye nasu farin cikin, canzawar yanayinki yasa abbanki ya ji ba dad'i domin har ya fara tunanin yaje da kansa yafad'a musu ya fasa badake, domin kowane iyaye suna burin ganin 'ya'yansu sun auri mijin da yacancanta mutumin da zai kular masu da 'ya, wanda yake sonta kuma danginsa suma suna sonta.

zarah lumshe idanuwanta tayi hawaye suna zuba tana jin wani iri a ranta, mama cigaba tayi da cewa saidai mu kuskuren da mukayi a baya har yanzu akwai sauran tabonsa bai warkeba a zuciyan zarah, zarah har yanzu kallonmu take a matsayin kwad'ayayyun iyaye, idan barinki ki auri wanda kikeso zaisa kigane cewa ba dukiyarsu muke k'wad'ayiba toh mun amince kije ki auri bello domin shima mutumin kirkine saboda farin cikinki shine namu fatanmu kigane cewa tuni iyayenki sunbar wacchan rayuwar da sukayi a baya, ko da ace za'a kallemu a matsayin k'ananun mutane masu magana biyu toh bazamu damuba saboda munfi buk'atar naku farin cikin.

zarah dasauri tatashi tarungume mama tare da fashewa da sabon kuka tace mama kuyafemin wlh ba haka nake nufiba, na amince da za6inku bana fatan ayi ma iyayena kallon marassa cika alk'awali koda ace zan mutu toh nagwammace inmutu ta dalilin faranta ma iyayena rai, tabbas nasan bazaku ta6a yimin za6in da zai cutar da ni ba wlh na hak'ura da malam bello wanda kuka za6amin shine zan aura, tana kaiwa nan tasake fashewa da kuka tace mama kuyafemin.

mama ma hawaye takeyi cike da tausayin d'iyartasu tace zarah bakiyi mana komai ba saima mu da mukayi miki.

zarah girgiza kai tayi tace mama kidaina cewa haka duk abinda kuka yanke akaina daidaine kuma cancanta da matsayine sukaja hakan.

mama rungume d'iyarta tayi tana hawaye tausayin zarah duk ya kamata, lallashin zarah tashiga yi har saida taga tayi shuru.

zarah mik'ewa tayi tace bari inje inba baba hak'uri nasan fushi yake da ni, mama tace ai baya nan ya fita.

zarah komawa tayi tazauna tace toh idan ya dawo zan je.

Mama murmushi tayi tace Allah yayi miki albarka zarah wlh kin cika d'iyar kirki, Allah yayi muku albarka gaba d'ayanku.

Zarah murmushi tayi tace Ameen mama.

Mama mik'ewa tayi tace bari inje nasan yanzu su Rauda zasu dawo

zarah batace komai ba, tana ganin mama ta fita yasa tatashi tashige toilet tare maida k'ofa tarufe anan tafashe da sabon kuka mai tsuma zuciya duk tausayin kanta da na malam bello yakamata domin tasan so d'ayane yakeyi mata batasan yadda zai fahimci maganarba idan taje masa da ita, saida taci kuka mai isarta sannan tawanke fuskarta tare da tad'auro alwallar magrib tashinfid'a darduma tad'auko alk'ur'ani tana karantawa domin samun sauk'in abinda takeji a ranta.

Bayan sallar isha'i zarah zaune tayi a d'akinsu har lokacin fuskarta babu walwala duk yadda su Rauda sukaso tasaki jiki ammah ta k'i, abincima dakyar tad'anci kad'an.

wajen k'arfe takwas tanajin dawowar Abbah saida tadaidaici daidai lokacin da yagama cin abinci sannan tataso tanufi d'akinsa jikinta a sanyaye tayi sallama.

Abbah da yake zaune hannunsa rik'e da redio yana sauraren labarai amsa mata sallamar yayi tare da rage k'arar redion.

Zarah shigowa tayi taduk'a k'asa muryarta tana rawa tace Abbah dan Allah kayafe min abinda nayi maka wlh na amince zan auri za6inku domin nasan ba zaku ta6a cutar da rayuwataba duk hukuncin da zaku zartas akanmu daidai ne burinku a koda yaushe kuga farin cikinmu, wlh akoda yaushe ashirye nake da incika umurninku domin 6acin ranku daidai yake da rugujewar farin cikina.

Abbah murmushi yayi cike da jin dad'in maganar zarah yace wlh zarah bakiyimin komai ba, indai baki sonsa kifad'a min wlh bazanyi miki doleba zan aura miki wanda kikeso domin farin cikinki nafi buk'ata.

zarah girgiza kai tayi tace Abbah wlh wanda kaza6amin shi nakeso ashirye nake a koda yaushe in amshi za6inka.

Abbah kasa 6oye farin cikinsa yayi yace nagode sosai zarah Allah yayi miki albarka kema Allah yabaki wad'anda zasuso farin cikinki, insha Allahu wannan auren zakiji dad'insa, Allah yayi muku Albarka gaba d'ayanku, zarah cike da jin dad'in addu'an da abbah yayi musu tace Ameen Abbana nagode sosai.

Zarah tunda takwanta kasa bacci tayi juyi kawai take abin duniya duk ya isheta tana tunanin yadda za'ayi ta auri wanda bata so, tunowa tayi da yarima suhail lokacin da yazo walimarsu yadda yake shan k'amshi, ba ya ma kallon kowa, tsaki taja tace wannan d'an jin kan zan aura, hawaye ne suka zubo mata tunawa da tayi da malam bello ta yaya zata fuskancesa da maganar zata auri wani ba shiba batasan yadda zai fahimci maganarba, tana ta sak'e-sak'e a ranta a haka bacci yayi awon gaba da ita batare da tashirya yinsaba........

_Comments_ *nd* _Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_ ?👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Yau page d'in nakune k'annena nakaina *JANAF nd SAFIYYA ALIYU* inaso kusani ina sonku irin totally d'innan Allah yabarmu tare😘_

Page 1⃣6⃣

Sultana Bilkisu ko da takoma gida cike da farin ciki tasamu Sultan Ahmad take bayyana masa yadda sukayi da iyayen zarah, shima farin cikinsa yanuna a fili yace gaskiya naji dad'i ammah kuma ba'a nan takeba,

murmushi sultana tayi tace nasan kana tunanin matsalar da zamu fuskantane wajensu memartaba da yarima?

Sultan Ahmad shima murmushi yayi yace tabbas hakane ammah Insha Alkahu komai zaizo da sauk'i kibani lokaci nima inyi tunanin yadda zamu 6ulloma lamarin domin maganar nan tana buk'atar tunani mai zurfi a cikinta.

Sultana Bilkisu Cike da damuwa tajinjina kai tace hakane nima zanje inyi tunani domin musamo mafita.

Sultan Ahmad tausayin matarsa yakamasa domin yasan yadda take son d'an nata, yace kidaina damuwa indai Allah ya k'addara akwai aure tsakaninsu toh za'ayi inkuma babu toh hak'uri zamuyi domin wani baya auren matar wani fatanmu dai Allah yashige mana gaba.

Sultana Bilkisu cike da gamsuwa da maganar mijin nata tace Ameen.

Gimbiya sumayya duk yadda taso tadaure kar tabada kanta ga yarima ammah kasawa tayi a daddafe tayi kwana biyu.

bayan sallar la'asar shiryawa tayi sosai tafito tanufi 6angaren yarima tana shirin shiga sai gashi ya fito da alamu fita zaiyi, kallo d'aya yayi mata yad'auke kai yana shirin ra6awa ta gefenta yawuce dasauri Gimbiya Sumayya tasha gabansa tace haba yarima wajenka fa nazo.

fuskar yarima babu alamun fara'a yace me zanyi miki?

Gimbiya kallonta takai ga dogarawansa da guards d'insa da duk kansu yake sunkuye suna jiran ogan nasu, ga kuyanginta da suke bayanta tsaye, kallonta tamaida ga yarima tace am daman, nan tafara kame-kame tace ko dai zamu shiga...... Yarima hannu yad'aga mata yace whatever ma dai you should meet me later, bai jira jin abinda zataceba yawuce dogarawan da guards d'insa suka take masa baya.

Gimbiya sumayya takaici duk yacikata ganin yadda yarima yadisgata gaban guards d'insa hararar kuyanginta tayi da kansu yake sadde a k'asa tacemunafukai kun zuba min na mujiya duk sai nad'au mataki a kanku.

dasauri duk suka zube k'asa suna cewa Allah yahuci zuciyar gimbiya, Allah yaja da ran gimbiya.

wucewa tayi fuu dasauri suka tashi suka take mata baya sunayi mata kirari.

ko da takoma part d'inta saman gadonta tafad'a tare da dafe kanta tsaki taja tace wannan mutumin bansan irinsaba anya yarima bai fara bin mataba? ya za'ayi yad'auki tsawon wannan lokacin batare da maceba? gabantane yashiga fad'uwa cikin d'aga murya tace No! i dont think yarimana akwai macen da zai iya kulawa wlh ba halinsa bane, chan takaima katifa bugu da hannunta tace inma akwai zan bincika domin nasan yarima baya iya kai tsawon wannan lokacin without ya yi making sex da niba ko da ace bana so, inma har naga akwai wadda yake tare da ita toh wlh ba zan bartaba sai na kasheta!!!

wayarta tajawo takira zinat bugu biyu tad'auka, muryar sumayya tana rawa tace wai ke zinat yaushe zaki dawo k'asarnan?

dariya zinat tayi tace kinyi missing d'ina ko? tsaki sumayya tayi tace ke ni tambayarki nake.

zinat murmushi tayi tace Allah yahuci ran gimbiyar yarima very soon zan dawo nima ai nayi missing d'in k'asata.

Sumayya tace hmm Allah yasa dagaske kike, nidai in kindawo kifara biyowa ta wajena.

'yar dariya zinat tayi tace sai kin ganni, sumayya dai badan ta yadda da maganar zinat ba takashe wayanta tare da komawa takwanta tana sak'e-sak'e cikin ranta.

Da daddare ganin ta kasa bacci yasa tamik'e tajawo alk'yabbarta tad'aura saman kayan baccinta tafito batare da ta nemi rakiyar kowaba tanufi 6angaren yarima addu'a take Allah yasa kar yadisgata domin ita tasan yau duk wulak'ancin da zaiyi mata ba zata damuba Indai zai biya mata buk'atarta inyaso daga baya sai tarama.

lokacin da tashiga ganin yarima baya parlour yasa direct tanufi bedroom d'insa, tsakiyan gadon tahangosa kwance idanuwansa a lumshe, cikin ranta tace lallai ma bacci yake

ahankali tataka tanufi gadon tahau takwanta a saman jikin yarima, muryarsa taji yace me kike buk'ata?

dasauri tad'ago kai takalli fuskarsa har a lokacin idanuwansa a lumshe suke ita tayi azan bacci yake, komawa tayi takwanta tace zuwa nayi intayaka bacci.

yarima dakyar yabud'e idonsa yasafkesu akan fuskarta yace sumayya kitafi kawai daman ai bake ketayani baccin ba saidai idan akwai abinda kike buk'ata.

Sumayya tallabo fuskar yarima tayi tace dear ni bacci kawai nazo muyi.

yarima janyeta yayi daga jikinsa yace ohk muyi baccin.

takaici yakama sumayya ganin yadda yake faujewa kamar bai fahimci abinda take nufiba, komawa tayi jikinsa tace wai yarima meyasa kakemin haka?

yarima kallonta yayi yace me nayi miki?

Shagwa6e fuska tayi tace naga yanzu kamar ka daina buk'atata, ka ma fita harkata, baka kula da ni bakasan yadda nake kwana nake tashiba baka tsoron hak'in aure?

yarima wata muguwar harara yawurga mata yace sumayya ashe kinsan hak'in aure? murmushin takaici yayi yace ammah ni kike tauyemin hak'ina.

sumayya haushine yakamata ganin yadda yarima yake neman wulak'antata cikin ranta tace kayi kagama ba zan damuba tunda ni nakawo kaina.

shafa sajensa tayi tace sweetheart yanzu dai shikenan na amshi laifina, yanzu kafad'i abinda kakeso zanyi maka.

yarima shuru yayi yakyaleta, marairaicewa sumayya tayi tace kayi magana mana.

Yarima murmushi yayi yace da zaki taimaka kibarni inyi bacci da nafi buk'atar hakan.

haushine yakama sumayya domin bata d'auka haka zaice mataba, ganin yadda tayi kicinkicin da fuska abun yaso yabashi dariya ammah yadake yace ya dai?

Sumayya d'auke kai tayi daga kallonsa tace suhail yanzu naga kamar ka daina buk'atata ko kasamu watane?

murmushi yarima yayi domin ya gano inda gimbiya tanufa yace Sumayya akanme zanta bibiyarki aini yanzu jikinki bai dameniba please kikyaleni ina buk'atar hutawa yanzu kinsan bana son yawan magana.

Sumayya fashewa tayi da kuka tace Suhail kaji tsoron Allah hak'ina fa? idan kai baka buk'atata nifa?

yarima d'aure fuska yayi yace ai banga alamun kina buk'ataba ni hak'ina nawa kika tauye?

gimbiya cikin kuka tace toh wlh ba zan yaddaba nidai nace kayi hak'uri.

Yarima cike da rashin damuwa yace shikenan naji zan taimaka miki, idan kin shirya toh bismillah.

Sumayya dai haka tabiyema yarima wulak'anci iri-iri yayi mata ammah lalla6asa tayi itadai burinta ya yabiya mata buk'atarta.

bayan komai ya lafa yarima tashi yayi yaje yayi wanka yazo yakwanta Sumayya mirginawa tayi jikinsa zata kwanta dasauri yarima yatureta yace kar kisaki kira6eni batare da kin tsarkake jikinkiba.

takaici yakama sumayya takoma gefe takwanta domin ita batayi shirin wanka yanzuba sai da asuba, cikin ranta tace yanzu ko zan fara rama wulak'ancin da kayi min.

da asuba saida yayo alwallah sannan yatadata dakyar tatashi saida yaga ta mik'e sannan yawuce masallaci.

tun daga ranar da sumayya taga tasamu biyan buk'atarta sai tadaina zuwa wajen yarima shi abunma dariya yake basa ganin sai tana buk'atar wani abu take zuwa wajensa, yarima bai wani damuba yace shi hakan ya fiyemasa da tazo tadameshi da surutu da haukanta.

*BAYAN KWANA BIYU*

yarima suhail ne a gidan gona tare da shaheed cikin wani k'ayataccen lambu, suna zaune bisa wani lallausan carpet da aka shimfid'a musu suna shan iska, daga chan nesa da su kad'an k'osassun guards d'insane tsaye, hannun yarima suhail rik'e yake da cup mai d'auke da ruwan inibi ammah ba sha yakeba, shaheed da yake zaune yana cin tufa kallonsa yakai ga wata 'yar tsuntsuwa da tad'auke hankalin yarima.

murmushi shaheed yayi cike da zaulaya yace ranka yadad'e tsuntsuwannan ta burgekane asa guards d'inka sukamo maka ita?

yarima suhail shima murmushi yayi tare da kai cup d'in bakinsa yad'an sha ruwan inibin batare da ya kalli shaheed ba yace kawai ina kallonta ne ammah...

shaheed jira yayi yaji abinda yarima zai ce ammah yayi shuru, ganin haka yasa yace ammah ta burgeka ko?

yarima suhail aje cup d'in hannunsa yayi tare da juyowa yad'an kalli shaheed sannan yamaida kallonsa ga tsuntsuwar yace eh kusan haka.

shaheed ma kallonsa yamaida ga tsuntsuwar yana shirin yin magana nan wayan yarima suhail tafara ringing dasauri d'aya daga cikin guards d'insa yazo yad'auko tare da russunawa yamik'a masa.

Suhail kar6a yayi ganin Daddynsane yasa cikin sauri yayi picking tare da yin sallama.

daga chan 6angaren daddy amsa masa yayi tare da tambayarsa yana ina?

yarima cike da ladabi yace daddy ina gidan gona.

daddy yace toh kazo gida kasameni domin akwai maganar da nakeso muyi me muhimmanci.

Suhail baikawo komai a ransaba yace toh daddy ganinan zuwa.

bayan ya gama waya da daddy kallon shaheed yayi yace muje gida daddy nason ganina.

ko da yadawo direct turakar iyayensa yaje a parlour yasamu daddy da ummi zaune da alama jiransa suke, dasallama yashigo tare da samun waje k'asa gefen daddy yazauna nan yak'ara gaishe da iyayen nasa suka amsa masa.

daddy ne yayi gyaran murya yace suhail wani taimako ne mukeso kayi mana ammah bamu san ko zaka iyaba.

yarima suhail d'ago kansa yayi yakalli daddy yace daddy kunfi kar6in haka a wajena ni mai cika umurninku ne.

daddy jinjina kai yayi yace nasan haka, sannan yace suhail aure mukeson muk'ara maka.

A firgice yarima suhail yad'ago kai yakalli iyayen nasa yace aure kuma daddy? Ina fa da aure.

ummi tace munsan haka wannan ma za6inmu ce mukeso ka aura, halinta da tarbiyarta sunyi mana, sumayya 'yar uwarkace kasan muna sonta, kawai alkhairine muka hango a tattare da k'arin aurenka, wannan alfarma ce muka nema a wajenka.

yarima suhail cike da tashin hankali yace kugafarce ni ummi ba wai nak'i bane kuduba kuga sumayya had'ani akayi da ita ba za6ina bace za6in memartaba ce, kuma a yanzu kuna neman kuhad'ani da wata, indai auren kukeso inyi toh na amince zanyi ammah kubari insamo za6in zuciyata.

Sultan Ahmad da ummi kallon juna sukayi sai chan sultan yace yarima ba wai munk'i ta takaba wannan auren za6inmu ne kaima kana da ikon auren za6inka a nan gaba ammah mudai muna buk'atar ka amince ma za6inmu insha Allahu akwai alkhairi a cikinsa.

Yarima shuru yayi na d'an lokaci yana tunani cikin ransa ko haushi yakamasa ammah baya ji zai iyayi ma iyayensa musu sai da yayi kusan minti biyu a haka sannan yad'ago kai yakalli iyayen nasa da suka zuba masa ido suna sauraren jin amsar da zai basu ahankali yabud'e baki yace daddy na amince zan aureta.

ummi da daddy farin ciki yakamasu kasa 6oye murnarsu sukayi sukace gaskiya munji dad'i sosai suhail yadda kafaranta mana kaima Allah yafaranta maka insha Allahu ba zakayi da nasaniba a cikin auren da zakayi.

yarima suhail murmushi kawai yayi batare da yace komai ba domin shi kad'ai yasan abinda yakeji a ransa na bakin ciki.

Daddy ne yanisa yace saidai wani hanzari ba guduba wannan auren bamusan kowa yasan mu muka had'asa munaso kanuna kaine kakeson yin auren, matsalar ma yanzu bamusan yadda yakamata a tunkari su memartaba da maganar ba.

gyad'a kai yarima yayi yace shikenan daddy ni zanje insamesa nasan abinda zance masa.

ummi tace a'a suhail kabari dai musamo mafita domin amincewarsu a lokaci guda kamar zatayi wahala.

d'an guntun murmushi yayi yace kar kidamu ummi kubarmin komai a hannuna.

ummi tace to yaushe zakaje kagano matar taka? na tabbata kaima zaka sota

haushi yak'ara kama yarima jin wai ummi ta ce zaiso wata, girgiza kai yayi yace no ummi ba sai najeba. nan yayi musu sallama yataso yafito ransa duk a 6ace duk gaisuwar da mutane suke duk'ewa suna k'wasa bai amsama ko mutum d'ayaba yawuce yakoma part d'insu yana shiga 6angarensa guards d'insa yayi ma warning kar subari kowa yashigo ko da kuwa gimbiya sumayya ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull