Yarima suhail complete novel - Chapter 26
Yarima suhail complete novel Chapter 26: Yarima suhail complete novel Chapter 26. Yarima ko da suka shiga cikin gidan yana rik'e da zarah har part d'insa…
3,331 words
Yarima ko da suka shiga cikin gidan yana rik'e da zarah har part d'insa umurni yaba guards d'insa yace kar subar kowa yashigo koda ace sumayya ce, gaba d'ayansu sukace to ranka yadad'e angama.
Suna shiga zarah cikin sauri taduk'e k'asa saboda wani irin juwa (jiri) da yake kwasarta. Tsaye yarima yayi yana kallonta sai chan yace kitashi mushiga ciki sai kikwanta. Zarah kasa magana tayi dak'yar tamik'a mai hannun. Ganin haka yasa yarima yatayar da it's tsaye ganin bata iya tafiya yasa yad'auketa yanufi bedroom da ita.
Maida idanuwanta tayi tarufe ahaka yakwantar da ita Saman gadon daga gefenta yazauna tare da shafa fuskarta cike da tausayinta yace bari insa ahad'a miki breakfast kiyi.
Girgiza kai zarah tayi alamun a'a tare d's rik'o hannunsa. Yarima ido yazuba mata ahaka har tayi bacci,
Ahankali yazare hannunsa daga cikin nata sannan yakoma gefenta yakwanta dan rama baccin da ake binsa.
Wajen 11am yafarka har lokacin zarah bacci take, wanka yashiga yayi lokacin da yafito ganin zarah yayi ta farka, Ganinsa d'aure da towel yasa tamaida idanunsa tarufe, yarima kallonta yayi yace kin tashi? Batare da ta bud'e idontaba tace uhm.
Cigaba yayi da shirinsa saida yagama sannan yashiga bathroom yahad'a mata ruwan wanka, bayan ya had'a dawowa yayi kusa da ita yazauna sannan yace taso muje kiyi wanka ko kin samu k'arfin jikinki,
Zarah bud'e idonta tayi ahankali sannan tace toh, Yunk'urin mik'ewa tashiga yi amma takasa, ganin haka yasa yarima yataimaka mata tatashi zaune sannan yamik'a mata towel, juyawa tayi alamun yazage mata zip d'in rigar,
Hannu yakai yazage mata, ganin tana ta kare-karen jikinta yasa yarima yata6e baki sannan yajuya mata baya. Ganin haka yasa zarah tacire rigar sannan tafara yunk'urin mik'ewa, juyowa yarima yayi yarik'ota tasafko daga saman gadon tana fara takawa nan tayi baya zata fad'i cikin sauri yarima yatarota, cak yad'auketa yanufi toilet da ita, zare towel d'in yayi daga jikinta sannan yasakata cikin ruwan, Zarah dasauri takai hannu takare k'irjinta ahankali tace kafita zanyi.
Kallonta yarima yayi yace kina ganin zaki iya? Gyad'amasa kai zarah tayi, baice komai ba yajuya yafita yabar toilet d'in.
Zarah kwance tayi cikin ruwan tana jin dad'in ruwan, kasa yin wankan tayi nan tamaida idanuwanta talumshe.
Yarima tura guard d'insa yayi part d'in zarah wajen kiyanginta aka kar6o mata kayan da zatasa, Ya dad'e Zaune ammah zarah bata fitoba, ganin haka yasa yarima yamik'e yanufi toilet d'in.
Tsaye yayi bakin k'ofar toilet d'in yana kallonta, zarah idanuwanta a lumshe batamasan da shigowarsaba, wucewa yarima yayi ya ida isa wajen k'irjinta yazuba ma ido sai daga baya yad'ibi ruwan ya watsa mata a jiki, firgit tayi tabud'e idonta, sponge yad'auka yafara wanke mata jikinta zarah kasa hanasa tayi dan tasan indai tace zata hanasa toh ita bazata iya yiba, ganin yadda yazuba ma k'irjinta narkakkun idanuwansa yasa ta maida idanuwanta tarufe cike da jin kunya ahaka yarima yawanketa tas, bayan ya gama nad'ota yayi a towel yana rik'e da ita suka fito.
Bakin bed d'insa yazaunar da ita sannan yad'auko mai yashafa mata, shi yataimaka mata tasaka kaya sannan rik'ota suka koma parlour yazaunar da ita, dining yaje yakwaso musu breakfast, a saman lallausar carpet d'in da yake shimfid'e a tsakiyar parlourn, kallon zarah yayi yace kisafko muyi breakfast d'in.
Zarah kallonsa tayi tace na k'oshi, kallon da yayi matane yasa tasafko tazauna, dakansa yahad'a musu breakfast yatura mata nata gabanta, da k'in shan tea tayi sai juya spoon d'in take ganin yarima ya kalleta yasa tad'aga cup d'in tafara sha kad'an-kad'an batasha wani na kirkiba ta aje sannan tad'an ci chips d'in.
Yarima ma bawani nakirki yaciba yamik'e, nan yabada umurni akazo aka kwashe komai, bedroom yashiga yad'auko mata drugs yazo yabata dak'yar takar6a tasha kasancewarta batason shan drug's, Nan yahad'a injection yayi mata. Zarah har da 'yar k'wallarta takoma saman 3 seater takwanta.
Yarima bedroom d'insa yashiga, bayan 'yan mintuna yafito da key d'in mota, kallonta yayi da itama tazuba mai ido, saida yajanye idonsa daga gareta sannan yace akwai abinda kike buk'ata? Ahankali tace a'a. Ohk, ni na wuce hospital, cewar yarima. Ahankali Zarah tace adawo lafiya. Chan k'asan mak'oshinsa ya amsa yace Allah yasa.
Ko da yafita k'ara gargad'in guards d'insa yayi kar subar sumayya tashigar mai part, sannan yawuce yatafi.
Zarah taso tatashi takoma part d'inta ammah takasa, a dudduk'e tatashi tagyara mai bedroom d'insa tasa aka gyara parlour sannan takunna kallo tana yi.
Wajen k'arfe biyu wanka tayi tashirya sannan tayi sallar azuhur, Ko da aka kawo lunch k'inyi tayi dan ji take gabad'aya abinci ya fita ranta yanzu dan haka tayi zamanta.
Around 3 o'clock yarima yadawo, har lokacin Zarah tana zaune tana kallo, kallonsa tayi tace sannu da zuwa. Yauwa, cewar yarima da yazuba mata ido, sai Chan yace ya k'arfin jikin? Saida tad'an ciji le6enta sannan tace Alhmdllh yai sauk'i. Wucewa yayi yashiga bedroom d'insa dan yakimtsa.
Bayan ya gama yafito kallon zarah yayi yace kinyi lunch? Uhm kawai zarah tace. Kallonta yarima yayi alamun rashin yadda sannan yace muje kik'ara.
Zarah turo baki tayi tamik'e tana tafiya dak'yar har suka isa dining, ko da suka zauna yarima ne yayi serving d'inta sannan shima yazuba nasa, ahankali yakeci idonsa yana kan zarah da take turo baki har lokacin batayi ko loma d'ayaba.
'Dago kai tayi takalli yarima ganin yana kallonta yasa tad'ibi abincin takai bakinta, dak'yar take taunawa saida tayi kusan minti biyar tana tauna sannan tahad'e, ganin haka yasa yarima yajanyo plate d'in gabansa yad'ebo batare da ya yi magana ba yakai wajen bakinta, kallonsa zarah tayi cike da mamaki, ganin fuskarsa ba alamun wasa yasa tabud'e bakin yasaka mata, zarah tana yatsine fuska take taunawa, yanayin yadda take taunar ya burge yarima dan haka yaita bin bakinta da kallo, ahankali yacigaba da feeding d'inta idanuwanta sukayi rau-rau kamar zatayi kuka, d'ura mata yacigaba da yi har saida yaga alamun ta k'oshi sannan yabata drugs yamik'e yabar wajen.
Zarah goge k'wallar da tazubo mata tayi sannan takalli plate d'insa da ko rabin abincin bai ciba, ahankali tace to shi kuma wa yabarma nashi yacinye?.
Mik'ewa tayi tadawo parlour nan tatarar da yarima kwance saman 3 seater yana kallon wrestling, chan saman 2 seater taje tazauna ganin wrestling yake kallo yasa haushi yakamata ahankali tace mutum yana kallonsa an canza mai channel, batasan maganar ta fitoba saidai jin yarima tayi ya ce d'akinki ko d'akina? Kallonsa zarah tayi taga hankalinsa yana ga T.V kamar ba shi yayi maganan ba, mamaki yakamata shuru tayi batace komai ba.
Kiran wayan yarima da akayine yasa yamik'e yafita batare da ya ce mata komai ba. Mik'ewa tayi taje tad'auko remote tacanza channel tacigaba da kallonta.
Har akayi sallar isha'i yarima bai dawoba wanka tashiga tayi tashirya, dinner kad'an tayi tasha drugs d'inta sannan tabi lafiyar gadon yarima tayi kwanciyarta.
Wajen 9pm yarima yadawo ganin tana bacci yasa shima yayi shirin kwanciya yakwanta, zuba ma fuskarta ido yayi yana kallo cike da tausayinta daga k'arshe yarungumota jikinsa tare da jan dogon numfashi, yanayin yadda yamatseta har saida tamotsa sannan yad'an safsafta mata rik'on, zage mata zip d'in rigarta yayi sannan yatura hannuwansa cikin rigar tare da lumshe ido yana jin wani sanyi a ransa, ahaka bacci yad'aukesa.
Cikin dare juyin da zarah zatayi jinta matse yasa tafarka, mamakine yakamata ganinta jikin yarima, jin hannunsa tayi a k'irjinta murmushi tayi tare da zuba ma fuskarsa ido tana kallo cike da sonsa k'wallah ce tacika mata ido cike da tausayin kanta tace ina ma ace kana sona muka kasance haka, jin k'irjinta ya fara bugawa yasa takoma takwanta tare da gyara kwanciyarta.
Da asuba ko da yafarka ahankali yajanyeta daga jikinsa sannan yatashi yashiga toilet saida yayi wanka sannan yad'auro alwallah, yana fitowa zarah tafarka zage zip d'in rigarta tayi sannan tamik'e tashiga toilet.
Lokacin da tafito har ya fita masallaci dan haka tayi sallarta ko da tagama saman gadon takoma takwanta, ba ita tafarka ba sai wajen 11 lokacin yarima har ya fita.
Gyara masa part d'insa tayi sannan takwashi kayanta takoma part d'inta, bayan sun gaisa da kuyanginta bedroom d'inta tashige wanka tayi tashirya sannan tafito tayi breakfast.
Bayan ta gama saman 3 seater takwanta wayarta tad'auko tahau chart daga k'arshe da tagaji tabud'o novel *(K'ADDARA CE)* cikin wayar tana karantawa gaba d'aya tamaida hankalinta ga karatun, sallah ce kawai takesawa tana ajewa ahaka har tagama.
Da dare kwanciyarta tayi part d'inta duk sai taji babu dad'i, tana kwance wayarta tafara ringing janyowa tayi tana ganin yarima ne batasan lokacin da murmushi yakubce mataba, zuba ma wayar ido tayi har saida taga ta kusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama cikin 'yar siririyar muryarta, daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi daganan shuru yabiyo baya sai chan yarima yace ya jikin naki? Zarah kwantar da murya tayi sannan tace Alhmdllh ya yi sauk'i. Ohk, kinsha drugs d'in? Cikin shagwa6a tace uhm, Daga chan 6angaren yarima saida yalumshe idonsa sannan yace kin tabbata. Zarah kamar zatayi kuka tace dagaske fa na sha. Daga nan duk sukayi shuru saida sukayi kusan minti ukku sannan yarima yace sai dasafe. ahankali tace Allah yakaimu ko inzo intayaka bacci? Yarima baisan lokacin da murmushi yaku6uce masaba sannan yace no kiyi kwanciyarki, yana fad'in haka yakashe wayarsa.
Zarah ma murmushi tayi sannan ta aje wayar saman bedside tare da kashe gloves.
Sumayya tsaye take bakin k'ofar yarima ta cika tai fam dan duk wayar da yayi da zarah a gaban idontane, cikin fushi tatako ta iso bakin gadon tace haba yarima wannan wane irin zaluncine? Yarima kallonta yayi cike da mamaki yace zalunci kuma? Cikin d'aga murya tace eh zalunci, akan me zaka kira waccan jakkar yarin.... 'Daga mata hannu yayi fuskarsa ba alamun wasa yace kar kikuskura kik'ara min shouting koda ran girkin kine sai akace banda ikon yin waya da matata? Toh bari kiji wlh kikiyayeni ko in sassa6a miki.
Sumayya ta6e baki tayi tace eh d'in adai dunga jin tsoron Allah.
Wani irin kallo da yayi matane yasa tasha jinin jikinta, cikin 6acin rai yace indai kinsan abinda yakawoki kenan toh kifita kiban waje kar kimin hauka yana fad'in haka yajuya mata baya.
Sumayya ta ji haushin abinda yayi mata cikin ranta tace babu inda zanje, infita waccan gajar tashigo, ahankali tahau gadon takwanta tare da rungumo yarima ta baya tace toh kayi hak'uri na daina.
Yarima lumshe idonsa yayi sannan ahankali yace shikenan sumayya.
_Comments_ *nd* _Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_*Wannan page d'in tukuicine agareki mummyna chubad'o muhammad, hak'ik'a kin wuce duk yadda kike tunani a zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare mummy😘*_
*PAGE* 4⃣5⃣
Ahankali yake warwarewa har yagama sannan yabud'e yafara karantawa gabansane yafad'i ganin sunansa aka rubuta da larabci, sai wasu rubutu da shi kansa baisan menene aka rubutaba saboda mitsi-mitsine daga chan k'asa kuma sunan zarah yaga anrubuta sannan daga gefe akasa d'aya ansa _ni zarah zan mallaki yarima_ gabansane yacigaba da fad'uwa cike da mamaki yace zarah ce tasamin laya dan tamallakeni? Me take nufi da hakan? cikin sauri yaje yad'auko na toilet d'in yawarware sunansa da na zarah kawai ne jikin takardar, tsaye yayi cike da mamaki yana k'ara bin takardun da kallo,
Zarah kwance take d'akinta duk kasala ta rufeta tanaso taje part d'in yarima ammah ta kasa saboda batajin dad'in jikinta, daga k'arshe dai daurewa tayi tamik'e tad'auko alkyabbarta tasaka sannan tafito tanufi part d'insa.
Ahankali tabud'e bedroom d'insa tashiga tsaye tagansa rik'e da layar, juyowa yayi yaimata wani irin kallo, cak zarah taja tatsaya cikin ranta tace shikuma wannan mutumin me yake nufi da hakan? Muryarsa taji ya ce abinda kikayi shirin yi toh bai yuwuba dan haka sai kicanza sabon shiri ammah ni nafi k'arfin duk wani sihiri.
Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cikin rashin fahimtar abinda yake magana a kai, ahankali tace ban fahimci akan abinda kake nufiba.
Yarima wurga mata harara yayi yace kar kimaidani wanda baisan abinda yakeba ko kin d'auka banga layun da kika ajeminba cikin toilet da k'arshin pillow na ba, zarah zaro ido tayi tace ni kuma?
Mik'amata yarima yayi yace toh ai sai kiduba kigani idan k'arya akayi miki, cikin sauri takar6a tashiga dubawa, tsoro da fargaba duk suka cikata, cikin sauri tad'ago kai takalli yarima da shima yake kallonta, muryarta tana rawa tace wlh ban aikataba bansan wanene yake neman jamin sharri ba, innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, dasauri taje wajen yarima tarik'o hannunsa k'wallah duk ta cika mata ido tace kayarda dani wlh bani bace nakawo maka laya, Fizge hannunsa yayi cikin d'aga murya yace idan bake bace toh wanene? Kuma sunan wanene a jiki? Zarah kallonsa take cike da mamaki tace yanzu ka yarda zan iya yi maka asiri? Cike da rashin damuwa yace toh idan ban yardaba me kikeso inyi? Murmushi Zarah tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace da ace ni mushrikace da ba akanka zan faraba kuma ba zan ta6a amincewa in aurekaba da tun farko zan san yadda zanyi inga ban aurekaba saboda nima inada wanda nake so, kuma da ace ina asiri da tun farko zanyi maka ba sai munkai wannan lokacinba, wlh nagaji da wannan sharrin da ake ja min komawane yaje dan kansa, tak'arashe maganar cikin kuka,
Yarima kallonta yake har takai aya sannan yace idan kin gama zaki iya tafiya dan magangununki bazasu ta6a tasiriba agareni, Zarah d'ago kai tayi takallesa tace bakomai insha Allahu gaskiya zatayi halinta komawanene asirinsa zai tonu, tana fad'in haka tawuce tafita tabar d'akin.
Tafiya take zata koma part d'inta hawaye suna zuba daga idanunta ita kanta batasan inda take jefa k'afartaba, hawaye d'aya na bin d'aya, ahankali take furta ya ubangiji kakawo min mafita a cikin wannan al'amari, ya ubangiji katona asirin duk wani mai nufin sharri agareni, me nayi musu? Meyasa sukeson ganin sun 6atamin rayuwa, wanene yake nufina da sharri haka? Tuntu6e ne tayi batasaniba nan tatafi zata fad'i, cikin sauri taji an rik'ota tafad'a jikin mutum, d'ago kai tayi cike da mamaki dan ganin kowanene? Ido tazuba ma jakadiya da itama take kallonta, ahankali jakadiya tace ranki yadad'e meyake faruwa dake ne haka? Zarah runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawayen suka shiga gangarowa, jakadiya cikin sauri tawaiga gaba da bayanta ganin bakowa yasa tarik'e Zarah suka ida isa part d'in Zarah.
Jakadiya kallon kuyangin Zarah tayi tace kubamu waje, cikin sauri duk suka ficce sukabar d'akin.
Zaunar da Zarah tayi saman d'aya daga cikin cushin sannan tazauna k'asa gaban Zarah, kallon Zarah tayi da tajingine kanta a jikin cushin d'in hawaye suna zarra daga idanunta, tace ranki yadad'e meyake faruwa da ke ne? Zarah ahankali tabud'e idonta takalli jakadiya, nan tayi murmushi wanda yayi kuka ciwo sannan tadafe kanta.
Jakadiya gyara zamanta tayi tace gimbiya kifad'a min matsalarki ni nayi alk'awali zan taimaka miki kid'aukeni a matsayin uwa, Zarah d'ago kai tayi takalli jakadiya har a lokacin hawaye suna zuba daga idonta cikin muryar kuka tace ya akeso inyi da rayuwata? Narasa wanene yake k'ullamin sharri da angama wanchan sai afad'a ma wannan shin ya akeso inyi? Ni zan iya hak'ura da auran inkoma gidanmu, Cikin sauri jakadiya tagirgiza kai tace a'a ranki yadad'e kar kice haka dan Allah kifad'amin abinda yake faruwa nayi alk'awali zan taimaka miki.
Zarah kallonta tayi cike da gamsuwa da maganar jakadiya sannan takwashe duk makircin da akeyi mata tafad'a ma jakadiya,
Jakadiya jinjina kai tayi tace wannan ba aikin kowa bane sai na gimbiya sumayya, Zarah cike da mamaki tace yanzu kina ganin itace zata yi min haka? Jinjina kai jakadiya tayi tace tabbas itace dan nasan wacece gimbiya sumayya da mahaifiyarta fiye ma da haka zasu iya yi.
Zarah share hawayen fuskarta tayi tace toh wlh zan iya hak'ura da auren inkoma gidanmu.
A'a gimbiya kar kice haka bai dace kikaraya ba, mu munsan halinsu, kuma sumayya da kikaga yarima ya aura toh auren had'ine ba auren soyayya bane sukayi.
hatta shi kansa yarima da kike gani akwai abinda mahaifiyar sumayya take k'ullawa akansa wanda ita kanta sumayya bata saniba.
Zarah ido tazuba mata cike da mamaki.
Jakadiya tacigaba da cewa akwai wani lokaci da dada ta aikeni wajen sultana sadiya, lokacin da nashiga parlour bakowa har na juyo zan baro d'akin najuyo magana k'asa-k'asa a bedroom d'in sultana sadiya tsaye nayi lokacin da najuyo tana cewa so take gimbiya sumayya tahaihu idan yaron yafara wayau tanaso tabi kowace hanya dan ganin ta kawar da yarima inyaso mijinta abashi rik'on k'warya kafin jikan nata yagirma daga baya yazama shine sarkin gari, ta san idan yahau toh sai yadda taso mulkin gidan zai tafi, dan ta tsani mahaifiyar yarima taso ace itace tahaifi d'a namiji Wanda zai gaji garin ba mahaifiyar yarima ba, ina jin haka cikin sauri nafito nabaro part d'in gudun kar taganni dan nasan idan taganni toh bazata ta6a barinaba.
Zarah cike da rud'ewa tace daman haka matarnan take? Toh shi yarima baisan halintaba ya amince ya auri d'iyarta.
Murmushi Jakadiya tayi tace tabbas yarima yasan kad'an daga cikin halayyarta dan tun yana k'arami idan yaje part d'inta wahalar dashi take dan akwai lokacin da tata6a watsa mai ruwan zafi, tagargad'e ni da idan nafad'a ma wani sai tayi sanadiyar barina aiki, kasancewar nikad'aice lokacin da abun yafaru.
Toh ba'a gane taba? Cewar zarah. Eh toh, yarima yana da wani irin hali wanda ba komai bane yake iya bud'e cikinsa yafad'aba wannan halinsane tun yana k'arami, kuma na tabbata shi kansa yana sane da abubuwan da tayi masa kawai dai ya sharene, indai wajen makircine toh kala-kala matarnan ta iya dan ina tunanin dasa hannunta sumayya takeyi miki wad'annan abubuwan.
Zarah jingine kanta tayi cike da jin tausayin mijin nata, Jakadiya tace ranki yadad'e kigode ma Allah da basubi ta wata hanyarba dan ganin sun kawar da ke, koda basubin boka ammah sun san makirci kala-kala.
Jinjina kai zarah tayi cike da mamakin halin su sumayya, ahankali tace duk makircinsu basu isa suyi abinda Allah bai nufa ba, kuma ina neman kariya daga ubangijina, saidai bansan yadda zanyi inshawo kan yarima yafahimceniba.
Jakadiya tace kar kice haka ranki yadad'e kuma baidace kiga laifin yarima ba tunda duk baya makircinsu da suke miki baiyi tasiriba a garesa ammah a yanzu kiduba kiga har da sunansa da naki aka had'a kinga ai bakowa bane zai iya k'in yarda, yanzu dai abu d'aya zakiyi shine nake tunani kamar zai taimaka wajen ganin kin ku6utar da kanki, zarah kallon Jakadiya tayi tace wane abune please kifad'a min.
nan Jakadiya tace kice yatambayi guards d'insa sufad'i Wanda yashiga da baya nan tunda ke kince baki shigaba, Zarah tace anya kina tunanin zai amince? Eh insha Allahu ai ya aminta da su yasan bazasu ta6a yi masa k'aryaba,
Zarah jinjina kai tayi tace nagode sosai jakadiya, hak'ik'a kin taimakeni a lokacin da nake buk'atar taimako nakekai kukana ga ubangijina,
Jakadiya tace kar kidamu gimbiya har cikin raina nake jinki dan kece kikafi dacewa da yarima ba sumayya ba kuma ina fatan yakasance kece zaki fara aje mana magajin yarima.
Zarah saida gabanta yafad'i dasauri tagirgiza kai tace kar kice haka, sumayya ita tafi dacewa tahaihuwa da yarima.
'Yar dariya jakadiya tayi tace tuni tayi watsi da damanta koda haka mahaifiyarta taci buri itama ammah a yanzu k'addara ta riga fata,
Zarah cike da mamaki take kallonta tace ban fahimci abinda kike nufiba? Murmushi jakadiya tayi tace kar kidamu dasannu zaki fahimta nan ba da dad'ewaba, jakadiya tana fad'in haka tamik'e tare da d'an rissinawa tace nabarki lafiya ranki yadad'e.
Zarah d'aga kai tayi tace nagode sosai jakadiya saidai ince Allah yabaki ladar abinda kikayi min.
Jakadiya murmushi tayi tace kar kidamu ai yi ma kaine, nidai fatana kirik'e sirrin maganar da nafad'a miki.
Zarah murmushi itama tayi tace insha Allahu babu wanda zai san maganar nan bayan mahaliccinmu sai ni da ke.