Yarima suhail complete Novel - Chapter 12
Yarima suhail complete Novel Chapter 12: Yarima suhail complete Novel Chapter 12. koda yashiga saman gadonsa yazauna tare da dafe kansa yana jin wani iri a…
3,372 words
koda yashiga saman gadonsa yazauna tare da dafe kansa yana jin wani iri a ransa ganin duk an watse masa budget domin kwata-kwata bai shirya k'ara aure yanzuba yafiso sai yasamu macen da yakeso sai ya aureta, tsaki yaja tare da kaima katifa naushi cikin d'aga murya yace wacece wannan wadda iyayena sukeson had'ani da ita me ke gareta da har tarud'esu taja duk wani plan d'ina ya watse tashi yayi yashige toilet tare da sakarma kansa shower.
_Comments_ *nd* _Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Wannan page d'in nakune my *Blood Sis Aufana nd Mummy Sainah Ummun Meenal* hak'ik'a kunfi k'arfin page a wajena, fatana Allah yabarmu tare 'yan uwa nagari😘_
*PAGE* 1⃣7⃣
Bayan ya fito shiryawa yayi sannan yahau saman bed d'insa yakwanta tare da jawo wayoyinsa yakashesu gudun kar adamesa da kira, nan yayi ta tunanin yadda zai 6ulloma lamarin, domin kwata-kwata bayaso yasa dada cikin maganar gudun kar tatarwatsa komai.
kiran sallar magrib ne yafarkar da shi daga tunanin da yakeyi, jiki babu k'wari yaje yad'auro alwallah yaficce masallaci.
Bayan sallar isha'i yarima fada yaje domin yagana da memartaba, lokacin memartaba da wazirine kawai cikinta suna tattaunawa akan wasu kud'i da za'a ware akai gidan marayu da gajiyayyu, yarima gaishesu yayi, nan suka amsa masa cike da sakin fuska da fara'a, sannan yasamu gefe d'aya yazauna yajanyo wayansa yana dannawa yana jiran sugama.
ganin yarima a wannan lokacin ya tabbatar ma da memartaba fa akwai magana dan haka cikin sauri ya sallami waziri.
Bayan waziri ya fita memartaba kallonsa yamaida ga yarima yace suhail na tabbatar akwai magana me muhimmanci da take tafe da kai domin kwata-kwata ban saba ganinka a wannan lokacinba.
yarima murmushi yayi yace ranka yadad'e tabbas hakane akwai maganar da take tafe da ni.
memartaba murmushi yayi yace ina saurarenka ka sanar da ni.
yarima kunyace takamasa yafara kame-kame yace am dama ranka yadad'e..... sai kuma yayi shuru.
memartaba murmushi yayi a karo na biyu yace suhail kayi min bayani mana.
ahankali suhail yad'ago kai yakalli memartaba cike da nutsuwa yace ranka yadad'e kagafarceni daman aure nakeson k'arawa ammah idan ka amince.
memartaba cike da mamaki yace aure kuma suhail? yarima gyad'a kai yayi yace ammah amincewarka nafi buk'ata ranka yadad'e domin ba zan iya zartas da hukunci batare da amincewarkaba.
memartaba shuru yayi nad'an lokaci yana nazari sai kuma chan yace suhail ba zan hanaka raya sunnar ma'aikiba, idan nace zan hanaka aure to natauye maka hak'inka kuma bazanyi jayayya da maganar ubangijiba domin shine yayi umurni da muyi aure, saidai bansan ko kuna samun matsalaba da matarka domin baku ta6a kawo k'arar junaba, inma akwai wata matsakar ba zance dole sai nasantaba domin wannan sirrinkune, ko da aure nufine na ubangiji, yanzu dai katashi katafi gida zanyi shawara in Allah yakaimu gobe zan nemeka.
yarima rissinawa yayi yace Allah yak'ara maka tsawon rai nagode sosai atashi lafiya,
memartaba gyad'a kai kawai yayi, ahankali yarima yamik'e yabar wajen yana sak'e-sak'e cikin ransa yadda za'a kwashe da su dada domin shi k'wata-k'wata baya jin ta gimbiya sumayya dan ashirye yake da yafad'a mata.
ko d's yakoma shirin bacci yayi yakwanta duk yadda yaso yayi baccin ammah ya kasa juyi kawai yake saman gado takaici duk ya cikasa ganin kamarsa ammah ace sai anza6a masa matan da zai aura, takaicinsa ma ba'a ma basa za6in kansa saidai aza6a masa saikace wani k'aramin yaro, tsaki yaja. haka yayita tunane tunane da sak'e-sak'e cikin ransa a zaciyansa sai yaji yana burin ace memartaba bai aminceba, wani irin dad'i yaji nan yasaki murmushi mai sauti ahankali yace Allah ma yasa memartaba yace a'a, ahaka bacci yayi awon gaba da shi.
*WANSHE KARE*
Yarima suhail cikin sauri yagama shirinsa kasancewar yayi late a gurguje yad'anyi breakfast sannan yaficce yanufi wajen aikinsa.
Bayan sallar la'asar zaune yake a parlour d'insa yana kallon wrestling cike da nishad'i kasancewarsa yanason kallon irin boxing da wrestling, wayarsa ce fara neman agaji, tsayar da kallon yayi tare da d'auko wayansa ganin memartaba ne yasa yayi picking dasauri tare da yin sallama.
amsa masa memartaba yayi sannan yace kazo turakata kasameni, cike da ladabi Yarima yace toh ranka yadad'e.
mik'ewa Yarima suhail yayi yaje yad'auko alk'yabbarsa yasaka sannan yafito nan guards d'insa suka take masa baya har turakar memartaba da sallamarsa yashiga.
mamakine yakamasa ganin iyayensa da na sumayya sai dada, cikin ransa yana mamakin dalilin da yasa aka tarasu. a k'asa yazauna tare da gaishesu.
memartaba ne yayi gyaran murya yace toh Alhmdllh nasan zakuyi mamakin tarakun da nayi, toh ba wata babbar magana bace dan kufad'i ra'ayinku domin wannan taron duk akan suhail akayisa saboda yazomin da wani babban zance.
shuru memartaba yayi nad'an lokaci sannan yace suhail yana da burin k'ara yin aure .
gaba d'ayansu suka rikice a firgice dada tace aure kuma? wane irin aure? duka-duka yaushe akayi aurensa da sumayya?
Sultana Sadiya tanaso tayi magana ammah bata iyawa saboda memartaba yana wajen, wani k'ululun bak'in cikine yatsaya mata harara tashiga wurga ma yarima suhail.
Memartaba murmushi yayi yace dan baidad'e da yin aureba wannan ba matsala bane domin yana da ikon auren sama da mata d'aya kuma baidace atauye masa hak'insaba inda matsalar take shine yasafke ma kowace mace hak'inta da yarataya a wuyansa, kallonsa yamaida ga sultan Ahmad da Abban sumayya yace toh ku iyayensa kuyi magana ya kuke ganin ya dace.
Abban sumayyane yayi karaf yace ranka ya dad'e abarsa yayi aurensa tunda yana da iko kar a tauye masa hak'insa.
Daddyn suhail yace ammah...... dasauri Abban Sumayya yakatsesa yace yaya dan Allah kar kace wani abu abarsa kawai yayi aurensa Bayan wannan ma yana da ikon k'aro wasu matan biyu.
Sultana bilkisu da Sultana Sadiya sudai basuce komai ba saidai binsu da suke da ido, sultana sadiya haushin mijinta taji ganin za'ayi ma d'iyarsa kishiya ammah bai damuba sai ma turawa da yakeyi.
dada ce cikin 6acin rai tace suhail inbanda abunka miye na gaugawa shi fa aure lokacine, kaduba kaga mutuncin matarka 'yar uwarka.
memartaba murmushi yayi yace dada kubarsa yayi aurensa tunda yana da burin yi.
dada tace ranka ya dad'e gaskiya ni ban aminceba ban yarda yawulak'anta min jikaba daman nasan yanayin zamansu kuma kaduba kaga..... memartaba d'aga mata hannu yayi yace ya isa haka k'ara auren da zaiyi ba shine yake nufin zai wulak'anta sumayya ba kuma na yarda da suhail nasan ko fiye da mata biyu aka basa zai iya kula dasu domin yana da hankali.
dada shuru tayi batace komai ba.
memartaba yace ko akwai me magana acikinku?
gaba d'ayansu sukace a'a ranka ya dad'e.
memartaba kallonsa yamaida ga Yarima suhail da yake zaune k'asa kansa sadde a k'asa yana sauraransu domin shima kansa baiso amincewarnan da akayiba dan dai ba yarda zaiyi ne kuma yanason cika umurnin iyayensa, muryar memartaba ce yaji yace suhail ka fad'ama iyayen yarinyar zamu tura a neman maka aurenta, dafatan dai ka fad'a ma matarka zaka k'ara aure?
Yarima Suhail girgiza kai yayi yace a'a ranka yadad'e bata saniba, memartaba yace toh shikenan kaje kasanar da ita nasan sumayya batada matsala zata amince.
Yarima Suhail yace toh ranka yadad'e.
memartaba yace zaku iya tafiya idan ba mai magana.
gaba d'ayansu duk'awa sukayi suka kwashi gaisuwa sannan suka tashi suka ficce.
Yarima bai koma 6angarensuba motarsa yashiga yaficce yatafi asibiti saboda akwai theater d'in da zai yi ma wasu.
Sultana Sadiya cike da tashin hankali takoma 6angarensu a parlour tayada zango tare da korar duk ma'aikatan da suke ciki nan tafara saffa da marwa tana jiran Sultan Abbas da yatsaya suna magana da Daddyn yarima.
Bayan kamar minti biyar sai gashi ya shigo, da mamaki yatsaya yana kallonta yace lafiya Sadiya naganki haka?
Cike da 6acin rai tace haba Abban sumayya wannan wane irin cin mutuncine yaron nan yakeson yi mana, kaduba kaga duka yaushe akayi bikkinsu dukaba shekara d'aya da rabi kenan ammah wai aure zai k'ara.
Murmushi Sultan Abbas yayi yace toh menene dan zai k'ara aure?
Sultana Sadiya tace kai wai naga kamar baka damuba d'iyarka fa ce za'ayi ma kishiya saikace bakasan ciwontaba?
Murmushin takaici Sultan Abbas yayi yace sadiya nine bansan ciwon Sumayya ba? nine mahaifinta kuma ita da suhail basuda banbanci dukansu 'ya'yanane kuma bari kiji dakaina ma zan iya zuwa inneman masa aurenta dan haka idan zaki sa d'iyarki tanutsu tabi mijinta toh inkuma taje garin haukanta takashe aurenta toh baruwana dan haka shawara tarage taku, yana kaiwa nan yaficce yabarta nan tsaye.
da harara sultana sadiya tarakasa tace ai zamu gani, wayarta tad'auko takira sumayya.
Lokacin Sumayya tana kishingid'e tsakiyar kuyanginta nan aka mik'o mata wayar tayi picking tace ummah ya dai?
ummah cikin fad'a tace ke jakkar inace mijinki yana nan yana shirin k'ara aure.
'yar dariya sumayya tayi tare da mik'ewa tanufi bedroom d'inta tana cewa haba dai yariman nawa? taya zaiyi aure?
Sultana Sadiya ta k'ule sosai cikin tsawa tace ke wace irin bahuwace? ina fad'a miki ammah baki ma damuba.
Sumayya zama tayi saman bed d'inta tace ummah ai nad'auka tsokanata kike.
Sultana Sadiya tace wace irin tsokana yanzu muka zauna da iyayenku akayi maganar har da memartaba kece kawai baki saniba.
Sultana Sumayya a firgice tamik'e tsaye tace ummah yariman nawa zaiyi aure batare da na saniba?
Ummah tace k'warai kuwa sumayya abun bak'in cikinma har da mahaifinki cikin masu goya masa baya.
sumayya k'asa tazauna tare da fashewa da kuka tace ummah yanzu yarima ne zai yaudareni yak'ara aure?
ummah tace ai saisa naso kihaihu ammah kika k'i d'aukar shawarata daman abinda nake guje miki kenan domin nasan halin yaudarar maza saboda basuda tabbas.
Sumayya cikin kuka tace wlh bazan yaddaba babu macen da zata auri yarima duk ma wadda tayi gigin shigowa wlh sai na kasheta domin bazan zauna da kishiyaba.
ummah tace kisa kuma sumayya? kibari mubi komai a hankali nima kinsan ba zan ta6a amincewa ayi miki kishiyaba domin farin cikinki shine nawa.
Sumayya cikin kuka tace kuma dada tasan da maganar? Ummah tace babu fa Wanda bai saniba.
K'ara fashewa tayi da sabon kuka cikin d'aga murya tace wlh k'aryane babu macen da ta isa ta auri mijina wlh ko ma wacece sai na kasheta, tana fad'in haka tayi wurgi da wayarta tare da duk'ewa tana wani irin kuka me tsuma zuciyan mesaurare dasauri tatashi tafito tanufi 6angaren yarima ammah tana shiga taga baya nan.
dan haka tafito tadawo d'akinta tana wani sabon kukan nan tafara watsi da kayan d'akinta dan dressing mirror d'inta batabar komai ba duk ta watsesu k'asa masu fashewa sunayi masu zubewa sunayi sumbatu tafarayi wlh sai nakashe ko wacece ba zan ta6a yadda a auremin mijiba saman gado tafad'a tana me cigaba da risgar kuka,
ma'aikatanta tsaye sukayi daga wajen d'akin sukayi cirko-cirko suna jinta ammah ba mai iya shiga d'akin gudun kar suma 6acin ran yashefesu.....
_Comments_ *nd* _Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_*Wannan page d'in na sadaukar da shi agareku Mamansadiq, Mummyn khadija nd Mrs Dawud ina alfahari da ku a kodayaushe, godia ta agareku bazata ta6a gushewaba wlh ko da page ko ba page nariga na ajeku waje guda acikin zuciyata😘*_
*PAGE* 1⃣8⃣
Jin abun gimbiya ya k'i k'arewa yasa haule tafita dagudu tanufi turakar yarima tana zuwa nan guards suke shaidamata baya nan, juyowar da tayi zata koma taji tsayuwar motar yarima dagudu tafita tanufi inda yake.
yarima yana fitowa daga mota daidai lokacin haule ta iso dasauri tazube gaban yarima yarima kallonta yake cike da mamaki, tace ranka yadad'e kagafarceni daman gimbiyace tana cikin d'aki.
yarima shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace me yasameta?
Haule duk'ar da kanta tak'ara yi tace ranka yadad'e gaskiya bamu saniba mun dai jiyota a d'aki kamar tana kuka.
yarima baice komai ba domin yagane dalilin da yasa sumayya yin hakan, wucewa yayi yabar wajen, da har zai shige part d'insa domin baiyi niyar zuwa wajentaba, chan kuma sai yafasa yanufi 6angarenta har a lokacin kuyanginta suna tsaye cirko-cirko anrasa mai iya ta6uka wani abu.
ganin yarima yasa suka zube suna k'wasar gaisuwa sannan suka tashi sumi-sumi suka fita sukabar d'akin.
ahankali yabud'e bedroom d'in yashiga mamakine yakamasa ganin yadda tawatse komai na d'akin, sannan yasafke kallonsa kan sumayya da take raku6e k'asa saikace wadda tayi rashin iyayenta tana ruzgar kuka, jin anshigo yasa tad'ago kai ganin yarima yasa tamik'e dasauri tanufi wajensa tare da rungumesa tana shashek'ar kuka tace yarima kafad'a min cewar abinda naji ana fad'a akanka k'aryane.
yarima da yake tsaye yace sumayya me kikaji akaina?
sumayya d'ago kai tayi takallesa tace aure wai zaka k'ara.
janye idonsa yayi daga kallonta yace hakane aure zanyi.
gimbiya turesa tayi a firgice tare da matsawa tace suhail aure? ni zakayi ma kishiya?
Yarima Suhail murmushin mugunta yayi yace tabbas aure zanyi sumayya domin ke tuni kikayi wasa da damarki.
cikin d'aga murya sumayya tace enough suhail! enough!!! nan tafashe da sabon kuka tace dan Allah kafasa auren nan wlh zan kula da kai.
ta6e baki yarima yayi yace kin rin rasa damarki dan haka k'ara kawai kiyi hak'uri koma wacece tashigo kikar6eta hannu biyu kuyi zaman lafiya.
sumayya cikin k'araji tace ank'i d'in, wlh babu wadda ta isa ta auremin miji domin gidan nan ba za'a ta6a samun zaman lafiya ba.
yarima suhail fuskarsa babu alamun wasa yace kidinga tace maganar da kike a gaban yarima suhail domin kinsan wanene ni bana son raini, sannan indai kinason zaman gidana dole kiso abinda nakeso kuma kuyi zaman lafiya.
gimbiya sumayya a fusace tace Idan ank'i fa? murmushin mugunta yarima yayi yace igiyar aurenki zata fara rawa, yana kaiwa nan yajuya yaficce yabar sumayya tsaye sake da baki tana binsa da kallon mamaki, yana fita tasake rushewa da kuka tace nashiga ukku yanzu ni suhail zai yaudara? kamata ace zaiyi ma kishiya har yana ik'irarin sakina.
saida taci kuka me isarta sannan tajawo wayarta da tawullar taga har screen d'in yatsage dan haka tad'auko d'ayar takira zinat har tatsinke ammah zinat bata d'agaba.
A fusace gimbiya tamik'e tad'auko alk'yabbarta tasaka tafito nan duk kuyanginta suka take mata baya duk wanda zai ganta a lokacin yasan tana cikin 6acin rai, tana fitowa bata zarce ko'inaba sai sai turakar iyayenta, a parlour ana ta kwasar gaisuwa bata kalli kowaba ganin ummanta bata parlour yasa tashige bedroom.
lokacin sultana sadiya tana zaune saman bed d'inta tana waya, ganin yadda sumayya tashigo yasa arikice tamik'e tsaye tace sumayya lafiya?
dagudu sumayya tazo tafad'a jikinta tare da fashewa da sabon kuka tace ummah nashiga ukku yanzu ni suhail zaiyi ma kishiya.
Sultana Sadiya rarrashinta tashiga yi tace haba sumayya kiyi hak'uri man kinsan dai tunda memartaba ya amince toh babu wanda ya isa yace a'a dan haka kibarsa kawai yayi auren munga ta yadda amaryar zata zauna lafiya, sai tasan tashiga rayuwarki dakanta zata fita tabar miki gidan.
sumayya kallon sultana sadiya take cikin rashin gamsuwa, ta bud'e baki zatayi magana kenan nan wayarta tafara ringing ganin zinat ce yasa takalli sultana sadiya tace ummah ina zuwa.
mik'ewa tayi tafito tashiga d'ayan bedroom d'in sannan tayi picking d'in wayar ko sallama batayiba tafashe da kuka tace zinat nashiga ukku.
zinat a firgice tace sumayya me yake faruwane?
sumayya kasa magana tayi sai ma kuka da takeyi, zinat cewa take sumayya kiyi min magana mana please nima inbaso kike inyi kukanba.
sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace zinat yarimana kasheni yakeson yi wai aure zai k'ara.
'yar dariya zinat tayi tace yoh d'an wannan zaisa hankalinki yatashi?
sumayya daina kukan tayi tace zinat kin ko ji abinda nace?
zinat tace na ji man ba aureba? yaje yayi kema ai wani sauk'in ne zaki samu domin yanzu zaki samu right d'in zuwa inda kikeso kinga business d'inmu zaya ha66aka, koma wacece kibarta tashigo wlh dakanta zata bar miki gidan.
sumayya tace haba zinat kamar ya inbari yayi aure ya za'ayi kamata ace anmini kishiya
zinat tace haba sumayya matsalata da ke kiyita abu kamar baki wayeba, kinsan ni kaina ba zan amince ayi miki kishiyaba dakanmu zamu fitar da ita gidan.
Sumayya jinjina kai tayi tace yanzu nafahimceki baby, zinat tace yauwa dear ai nasan zaki fahimceni nan zinat taita k'unsa mata makirci saida taga sumayya tad'auka sannan sukayi sallama takashe wayarta.
sumayya dawowa tayi wajen sultana sadiya tace ummah shikenan nad'auki shawararki ammah wlh bazan ta6a bari amaryar tasamu zaman lafiya a gidanaba.
cike da jin dad'i sultana sadiya tace gaskiya naji dad'i da kika fahimceni ai inma kin bari tazauna lafiya toh baki haihuba kibarshi kawai daga shi har amaryar tasa sai sun san sun ta6o tsuliyar dodo.
dariyar jin dad'i sumayya tayi tace za'a fara babban wasa dominba mai ta6a gimbiya sumayya azauna lafiya, muje zuwa.
__________________
Zarah duk yadda taso tacire damuwa a ranta ammah ta kasa kawai dai tana 6oyewane dan kar iyayenta sukaranto halin da take ciki, ga malam bello da kusan kullum sai ya kirata ammah takasa fad'a masa matsalar da ake ciki.
shi kansa ya sha tambayarta abinda yake faruwa domin jin yadda duk tacanza masa saidai tace bakomai.
Yau Zarah ita kad'aice gidan kasancewar mama taje asibiti raka yaya Rauda awo, Aysha kuma taje bikkin k'awarta da akeyi.
ji tayi bata iya barin malam bello batare da yasan halin da ake cikiba dan haka wayarta tad'auko tanaso takirasa ammah ta kasa sai juya wayar take a hannunta ta rasa yadda zatayi daga k'arshe dai tadaure takirasa.
malam bello baiyi picking ba har saida tatsinke tana shirin tak'ara kiransa sai gashi ya kira, zuba ma wayar ido tayi ta rasa yadda zatayi tad"auka domin batasan abinda zatace ba, saida taga takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama.
malam bello ya amsa mata nan suka gaisa sannan Zarah tace malam idan kana kusa dan Allah kazo akwai maganar da nakeso muyi.
Cike da jin dad'i malam bello yace ganinan ko zuwa kinsan dama nakwana biyu bansaki a idonaba fatana dai ba laifi nayiba.
Zarah duk yadda taso tamaida kukanta kasawa tayi muryarta tana rawa tace babu komai sai kazo, dasauri takashe wayar batare da taji abinda zai ceba takife kanta saman katifarsu tashiga rera kuka cike da tausayin malam bello da kanta domin batasan yadda shima zai fahimci maganarba
bayan kamar minti biyar wayarta tashiga ruri ganin malam bellone yasa dasauri tamik'e taje toilet tawanke fuskarta sannan tafito tasaka hijab d'inta tafita jikinta duk a sanyaye.
A k'ofar gidansu tasamesa tsaye yana jiranta kanta yana sadde k'asa gudun kar yagano yanayin da take nan tayi masa sallama
malam bello fuskarsa a sake ya amsa mata tare da tambayarta mutanen gida tace duk suna lafiya, daganan shuru yabiyo baya sai chan malam bello ya nisa yace Zarah Allah yasa ba laifi nayiba dan fitama zanyi nafasa nace bari infara amsa kiran gimbiyata sannan sai inwuce
Zarah runtse idonta tayi tana jin wani iri a ranta jin kanta yafara sarawa yasa tajingina da bango.
malam bello rikicewa yayi yace Zarah lafiya? meyake faruwane? wani abu yasamu su abbah? Please kifad'amin matsalarki.
Zarah batare da ta bud'e idontaba tashiga girgiza masa kai hawaye suna zuba cikin muryar kuka tace ko d'aya malam bello babu abinda yafaru, inaso ne kayafe min wlh ba a son raina hakan takasanceba saidai dan ba yarda zanyi kuma banaso ink'i bin umirnin iyayena kayi hak'uri da..... sai kuma tayi shuru tare da fashewa da kuka.
malam bello jikinsa ya yi sanyi sosai yace Zarah da me zan hak'ura? kiyi min bayani, su Abbah basu amince da ni inkasance surukinsuba ko?
Zarah dakyar tabud'e idanuwanta da suka kumbura saboda kuka tace su abbah sunyi min miji muhak'ura da juna haka Allah yak'addara kai ba mijina bane.