Kenza eBookz

Yarima suhail complete Novel - Chapter 17

Yarima suhail complete Novel - Chapter 17

Yarima suhail complete Novel Chapter 17: Yarima suhail complete Novel Chapter 17. gyalenta tad'auko white tayafa tafito lokacin yarima yana zaune saman…

3,354 words

gyalenta tad'auko white tayafa tafito lokacin yarima yana zaune saman cushin, kallonta yayi yace babu alkyabbane cikin kayanki?

zarah tace akwai.

shuru yarima yayi baik'ara cewa komai ba, ganin haka yasa zarah takoma bedroom, red d'in alkyabba tad'auko tasaka sannan tafito tasamu yarima a zaune,

kallonta yarima yayi har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, mik'ewa yayi yace muje.

zarah bayansa tabi suka fito a jere nan guards d'insa da kuyanginta suka take musu baya yanayin yadda suke tafiyar kawai zaka kallah sai sun burgeka ko da ad'ankwai 'yar tazara a tsakaninsu anutse suke tafiya har suka isa fada itadai zarah duk fargaba da tsoro duk sun cikata kanta sadde yake k'asa har suka shiga fada da take cike mak'il da jama'a nan mutane suka fara gaishesu, yarima ne kawai yake amsawa ahaka suka isa gaban memartaba,

lallausan carpet ne aka shimfid'a musu nan dogarawa sukayi musu zobe har saida suka zauna bisa sannan suka janye manyan rigunansu gaba d'ayansu suka duk'a suka gaishe da su yarima, yarima gyad'amusu kai yayi nan suka mik'e sannan yamaida kallonsa ga memartaba da yake kallonsu yana murmushi.

Zarah ce tafara gaishesa sannan yarima suhail, gyad'a musu kai sarki yayi alamun amsawa, nan fadawa suka d'auka sarki ya amsa gaisuwarku yarima da gimbiya ku ma angaisheku, Allah yaja da ranku,

memartaba kallon zarah yayi yace Alhmdllh ina tayaki murnar shigowa wannan masarauta tamu muna fatan Allah yasa alkhairi a cikin aurennan naku.

nan fada tad'auka da Ameen.

wata 'yar jakka sarki yasa aka mik'o masa yaba zarah yace ga kyautata gareki.

zarah hannu biyu tasa takar6a tare da duk'ar da kai tace nagode ranka yadad'e Allah yak'ara girma da d'aukaka, nan kuyanga takar6a

nan fadawa suka d'auka sarki ya amsa godiarki gimbiya angaisheku.

memartaba kallon yarima yayi yace Allah yatayaka safke wannan nauyin da yahau kanka fatana Allah yasa ka kwatanta adalci atsakaninsu.

yarima kansa na sadde k'asa yace Ameen ranka yadad'e.

memartaba murmushi yayi yace zaku iya tafiya.

godia sukayi, dasauri dogarawa sukazo suka baje rigunansu suna ranka yadad'e atashi lafiya, takawarka lafiya jarumin jarumai saida suka tabbatar da sun mik'e sannan su kuma suka duk'e k'asa nan zarah da yarima suka fito sukabar fadar, kan zarah ya d'aure sosai ahaka suka shiga cikin gida turakar dada.

duk inda suka gifta duk'awa ake ana gaishesu, yarima d'aga musu hannu kawai yake itakuma zarah saidai tabisu da ido,

masu tsaron k'ofar dada ganinsu yasa sukayi saurin bud'e k'ofa tare da duk'awa sukace ranku yadad'e Allah yaja da ran yarima me jiran gado.

yarima bai tankasuba yana gaba zarah na biye da shi ahaka suka shiga nan kuyangin dada suka zube suka Kwashi gaisuwa sannan cikin sauri suka tashi sukabar d'akin.

yarima takawa yayi yaje saman cushin yazauna, zarah ko k'asa tazauna cike da ladabi tagaishe da dada.

dada nan ta amsa mata, fuskar yarima d'auke da murmushi yace 'yar tsohuwa ina kwana?

dada tace au yau kuma da tsokana kazo? toh bazan amsaba, yarima yace ayya yi hak'uri, murmushi dada tayi tace dafatan kun tashi lafiya?

yarima yace lafiya lou, dada kallon zarah tayi da har lokacin bata d'ago kai ba tace amarya ya bak'unta? zarah murmushi tayi tace Alhmdllh.

dada kallonta tamaida ga yarima tace akwai matsala fa yarima yace tame fa?

dada gyara zamanta tayi tace babu wata sheda da kuka nuna mana, mutane suna nan sun kasa kunne suna saurare ammah shuru wai meyake faruwa ne naga bedsheet d'in babu komai a jikinsa, ta k'arashe maganarta tare da kallon zarah.

murmushi yarima yayi yace ranki yadad'e saboda Allah komai ace sai mutane sun shaida, wannan ai tonon asirine.

dada tace a'a yarima wannan kasan shine zai d'aga darajar mace a idon kowa dake masarautarnan sannan kuma gada mukayi tun kaka da kakanni, rashin ganin jini zai iya sa ad'auka mace tazubar da mutuncinta a waje.

zarah da take saurarensu saida gabanta yafad'i dan ta fahimci akan abinda dada take magana.

yarima cike da rashin damuwa yace haba dada inbanda abinki yanzu ai anbar wannan.

dada tace injiwa? abinda muka gada tun kaka da kakanni? kai ni banyarda da kaiba anya kakwanta da yarinyarnan? inkuma ka kwanta da ita toh ya akayi babu wani alama da yanuna budurwace?

murmushi yarima yayi tare da kallon zarah da duk tabi tatsure cikin ranta mamakin maganganun dada take tace gidan sarauta akwai tonon asiri, ahankali yarima yace dada period takene saisa hakan takasance, zarah dasauri tad'ago kai takalli yarima da yake dannar wayarsa saikace bashine yayi maganar ba, yarima ya fad'i hakane gudun kar su ummi suji labari dan yasan sai dada ta fad'a musu kuma sai sun fahimci wani abu.

dada ce tace ayyah Allah sarki 'yar nan ai bamu saniba, kinsan haka abun yake, kinsan daren farko munaso muga alamar da zata nuna mana mace cikakkar budurwace dan hakan ne yake d'aga daraja da k'imarta.

zarah cike da kunya tak'ara sadda kanta k'asa, dada tace kikwantar da hankalinki zanyi ma kowa bayani yadda zasu fahimta.

yarima ne yace haba dada wannan ai tonon asirine. . dada tace gidanku, kaima ai kasan dokokinmu na wannan masarautar, yanzu dai yaushe ne zakiyi tsarki?

zarah kallon yarima tayi da shima yazuba mata ido, muryar dada taji tace ina saurarenki.

zarah batasan lokacin da tayi su6ul da baka tace jibi ba.

murmushi dada tayi tace Allah yakaimu, nan dada tamik'o mata alkyabba maikyau da turare tace ga tukuici na,

kar6a zarah tayi tare da godia ammah har lokacin jikinta rawa yakeyi.

nan yarima yayi ma dada sallama suka mik'e suka fito, daganan suka nufi part d'in sultana sadiya,

lokacin da suka shiga tana tsakiyan kuyanginta, da sallama suka shiga nan kuyanginta suka gaishesu sannan sukabar d'akin, ganinsu yasa gimbiya sadiya tad'aure fuska tare da wurgamasu harara, yarima baidamu da yanayin kallon da take musuba yaje saman kujera yazauna, inda zarah kuma tazauna k'asa tare da gaisheta, .

sultana sadiya shuru tayi bata amsaba, yarima suhail ne yace ranki yadad'e ana gaisheki fa, yamutsa fuska sultana tayi tace oh banjiba amarya kin tashi lafiya?

zarah k'ara duk'ar da kanta tayi tace lafiya lou, yarima suhail yace ranki yadad'e barka da safiya dafatan kin tashi lafiya.

lafiya, cewar sultana.

murmushi yarima yayi tare da kallon zarah yace wannan itace ummah sadiya mahaifiyar matata sumayya,

gyad'a kai kawai zarah tayi, ummah tace hmm mu ai muna nan muna jira muji anyi gud'a ammah har yanzu shuru babu abinda mukaji hakan yana nufin ba budurwa bace kenan kayayo mana cikin masarauta.

murmushi yarima yayi yace ranki yadad'e ai gud'a bashine ba kar kimance sumayya ma ba'ayi gud'aba lokacin da na aureta,

cike da 6acin rai sultana sadiya tace kar fa kayi min rashin kunya, yarima cikin kwantar da murya yace haba ummah ni na isa inyi miki rashin kunya? kawai dai tuna miki nayi saboda laifi tudune katake naka kahango na wani.

zarah abun ya d'aure mata kai ganin yadda yarima yakeyi ma surukarsa,

sultana sadiya har ta bud'e baki zatayi magana sai ga sultan Abbas ya fito daga d'aki fuskarsa d'auke da fara'a yace a'a wai amarene?

murmushi kawai suhail yayi tare da d'an zamowa daga kujerar da yake yace abbah ina kwana?

sultan Abbas zama yayi yace lafiya lou yarima dafatan kuna lafiya?

murmushi suhail yayi yace lafiya lou Abbah, zarah k'ara sadda kanta tayi cike da ladabi tagaishesa.

cikin sakin fuska sultan abbas ya amsa mata tare da cewa amaryarmu ya kike ya bak'unta? zarah tace Alhmdllh Abbah.

sultan Abbas yace masha Allah, dafatan zakiyi hak'urin zama da mu kinsan yanayin gidan sarauta sai andinga hak'urin zama da juna fatanmu kizauna da kowa lafiya, ko da yanayin ya nuna bazakiyi fitinaba.

Zarah cike da ladabi tace insha Allahu Abbah, mik'ewa sultan Abbas yayi yashiga bedroom bai dad'eba sai gashi yafito da wata leda nan yamik'a ma zarah yace ga kyautata,

zarah hannu biyu tasa takar6a tare da yin godia.

yarima suhail ne yamik'e yace abbah bari muwuce, sultan abbas yace to yarima mungode sosai a dai cigaba da hak'uri da juna. yarima yace insha Allahu abbah mungode, nan zarah tak'ara yin godia sannan tataso suka fito.

ko da suka shiga turakar ummi duk inda suka gifta nan ma zubewa ake ana gaishesu, a parlour suka sameta kishingid'e ita kad'ai, ganinsu yasa tatashi zaune fuskarta d'auke da fara'a hannu tamik'a ma zarah tace zo nan kusa da ni d'iyata.

zarah cike da jin kunya tataka taje kusa da ummi tazauna, inda yarima yazauna saman cushin.

zarah cike da girmamawa tace ummi ina kwana? ummi tace lafiya lou daughter ya bak'unta? zarah murmushi tayi tace Alhmdllh. yarima ma cikin girmama yagaishe da ummi, itama ta amsa masa fuska a sake tace ya sumayya?

murmushi suhail yayi yace tana lafiya ummi, daddy fa yafita? ummi mik'ewa tayi tace yana ciki bari inkirasa kugaisa nan tawuce tashiga bedroom d'insa bata dad'eba saigata sun fito tare da daddy,

bayan dady ya zauna nan suka gaishesa, daddy ya amsa musu daganan yad'anyi musu nasiha sannan yad'auko cheque yamik'a mata yace ga kyautata gareki.

zarah hannu biyu tasa takar6a tare da yin godia, daddy yace bakomai adaiyi hak'uri da zaman aure, sannan yatashi yafita.

ummi kallon yarima tayi tace inason magana da kai, saida tamik'e sannan tamaida kallonta ga zarah tace daughter yi hak'uri bari inzo, zarah murmushi tayi tace toh ummi bakomai.

yarima tashi yayi yabi bayan ummi, bayan sun shiga bedroom ummi kallonsa tayi tace suhail menene haka kayi ban fahimcekaba daman nasan bakason auren nan yanzu saboda Allah kakyauta gashinan anata surutu akan baiwar Allahn nan?

yarima shuru yayi saida sultana bilkisu takai aya sannan yace ummi please kifad'amin menayi?

harararsa ummi tayi tace au kana nufin bakasan abinda kayiba kenan, yanzu saboda Allah an aura maka yarinya ammah babu abinda yashiga tsakaninku.

yarima sosa k'eyarsa yayi cikin jin kunya yace ummi am ba daman,

ummi tace daman me? murmushi suhail yayi yace daman tana period ne.

dogon numfashi ummi taja tace toh ai shikenan na d'auka wulak'ancin nakane yamotsa nidai fatana karik'e min ita tsakani ga Allah kar kabani kunya.

murmushi suhail yayi yace ummi kenan saikace baki yarda da niba, kina tsoron inzalunceta ko?

murmushi itama ummi tayi tace ai nayarda da d'ana 100% Allah yayi maka albarka, murmushi yayi yace ameen ummina,

atare suka fito inda suka tarar da zarah inda suka barta, ummi murmushi tayi tace daughter munbarki kekad'ai ko?

itama zarah murmushin tayi tace bakomai ummi, wata leda ummi tamik'a mata tace ga wannan, sannan ummi tace rahama batanan da kun gaisa ammah insha Allahu idan tadawo zan turota kugaisa.

zarah tace toh ummi tare da yi mata godia, nan sukayi mata bankwana suka fito suka koma 6angarensu.

ahanyarsu ta komawa yarima suhail yakira sumayya

lokacin sumayya tana breakfast fuskarta babu walwala jin haushinta taje part d'in yarima ammah bata samesaba, dasauri wata baiwarta tamik'o mata wayar tace ranki yadad'e ana kiranki, kar6a gimbiya tayi a wulak'ance ganin mai kiranta yasa taja tsaki kamar bazata d'aukaba saida takusan tsinkewa sannan tad'auka babu ko sallama tace haba yarima yanzu saboda Allah ka.... yarima baijira tak'arashe maganarba yakatseya yace kisameni a part d'ina yanzu, bai jira jin abinda zataceba yakashe wayarsa.

_Comments_ *nd* _Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 2⃣4⃣

Yarima ganin zarah tana shirin wucewa part d'inta yasa yace suje part d'insa yanason ganinta, zarah bata musaba tabi bayansa dan bata iya musama yarima saboda girmansa da take gani.

ko da suka shiga saman cushin yarima yazauna, zarah har zata zauna k'asa yace tazauna saman cushin tunda suka zauna d'akin yad'au shuru.

yarima kiran sumayya yayi tana d'auka cike da jin haushi yace kinsan dai bana jira kuma baki isa inzauna ina jirankiba.

tsaki sumayya taja tace ai ganinan a hanya.

bayan minti biyu saiga sumayya tashigo fuskarta babu alamun fara'a ganin zarah yasa taja bakin k'ofa tatsaya, dasauri zarah tamik'e tad'an russuna tace Aunty barka,

wata uwar harara gimbiya sumayya tawurga mata tare da jan tsoki, tace Auntyn munafunci? kece kika auran min miji ko? lallai natayaki murna tak'arashe maganar tare da yin k'wafa

jikin zarah duk sai yayi sanyi.

yarima da yake dannar waya yana saurarensu batare da yakallesuba yace ma gimbiya sumayya ai saikizo kizauna kin wani yi ma mutane tsaye,

sumayya tana hararar zarah tatako cike da isa tazauna saman kujerar da yarima yake zaune, zarah ma jiki ba k'wari tazauna inda take tare da saddar da kanta k'asa.

yarima shuru yayi yana dannar wayarsa baice komaiba saida akayi kusan minti ukku,

sumayya ta k'ule kallonsa tayi tace haba yarima ya zakayi shuru kabarni a zaune.

banza yarima yayi da ita saida yagama abinda yake sannan yad'ago kai yakallesu d'aya bayan d'aya tare da gyaran murya kamar bayason yin magana yace toh Alhmdllh ba akan komai natarakuba sai dan infad'a muku dokokina domin duk wadda takeson zama da ni dole tabisu, kallon sumayya yayi da taci face yace ke sumayya kece babba dan haka kija girmanki banason fitina ko tashin hankali, sumayya cike da masifa tabud'e baki zatayi magana, yarima hannu yad'aga mata yace kar kikuskura, kin san wanene ni idan ina magana ba'a tsinkemin.

sannan yamaida kallonsa ga zarah da take wasa da yatsun hannunta yace ke kuma kece k'arama dan haka dole kibata girmanta sannan kizauna da ita lafiya kar kikuskura inji kinyi mata rashin kunya, zarah shuru tayi batace komai ba.

yarima yacigaba da cewa kar wanda yasaki yakawomin tashin hankali a gidana, sannan maganar kwana bayan sati guda zaku koma kowace kwana bibbiyu, jinjina kai yayi yace na fad'amuku kar inji kar ingani banason tashin hankali wlh duk wadda tanemi takawo min raini zan d'au k'wak'waran mataki a kanta, yana kaiwa nan yayi shuru na d'an lokaci sai chan yace idan akwai mai magana zata iya yi.

ba sumayya hatta ita kanta zarah taji haushin maganganunsa, sumayya ce tace yanzu dai wad'annan maganganun naka ban ganeba kafito fili kace da ni kake wannan shine adoki mutum sannan ahanasa kuka, ka gama yimin kishiya sannan ka...... hararar da yarima yawurga matane yasa tayi shuru, d'an guntun murmushi yayi yace ban miki alk'awalin bazan k'ara aureba kai koda ace a nan gaba naga wadda tayimin nakeso toh sai na aureta saidai duk wadda taji bata iya zama toh k'ofa a bud'e take dan haka kutashi kuban waje.

zarah ce tafara tashi dasauri tafita sannan sumayya.

zarah tana cikin tafiya taji muryar sumayya tace ke! zarah batare da ta juyoba tatsaya nan sumayya tatako cike da isa tazo inda zarah take, kallonta sumayya tayi daga sama har k'asa sannan tace gimbiya zarah ko? l dariya sumayya tayi tace gaskiya natayaki murna gaki d'iyar talakkawa ammah zaki had'a miji da gimbiya kamata, chan kuma sai gimbiya sumayya tad'aure fuska tace wlh baki isa inyi kishi da keba dan haka yazama dole kirabu da mijina, inkuma ba hakaba bakeba hatta talakkawan iyayenki sai sunsan kwad'ayi yakaisu ya baro, dan suma sai sun gane kurensu dan haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya.

tana gama fad'in haka tazagaye zarah tawuce tabarta nan tsaye.

zarah dai binta take da kallo cike da mamaki kasa cewa komai tayi tawuce tanufi part d'inta zuciyanta cike da k'unci

zarah ko da takoma part d'inta sama-sama tatsaya suka gaisa da kuyanginta sannan tashige bedroom d'inta, saman gado takwanta tana tunanin maganganun da sumayya ta yada mata, sai tatuno da yarima suhail, tsaki taja tace wlh darajar alk'awalin da nad'aukar ma malam bello da kuma darajar aure wlh da bazan yadda a wulak'antaniba.

hawayene suka fara zarra daga idanunta chan tafashe da kuka cike da tausayin kanta.

wajen azuhur kuyangarta tashigo tahad'a mata ruwan wanka.

bayan zarah ta fito wanka tad'and'ara kwalliyarta gown d'in atamfa tasaka, bayan tayi Sallah tafito parlour, ganinta yasa kuyanginta suka zube suna kwasar gaisuwa, zarah bata ce komai ba saida taje saman cushin tazauna sannan tace banason irin wannan gaisuwar da kukeyimin kudaina duk'amin.

zabba'u shugaban kuyangince cike da girmamawa tace ranki yadad'e kigafarceni matsayinkine da k'imarki da cancantarki sukaja haka, murmushi zarah tayi tace nagode ammah kudaina, yanzu dai inason asani nishad'i wazai ban labari mai dad'i?

nan zabba'u takalli d'aya daga cikinsu tace daso aikinkine, wadda aka kira da daso nan tafara ba zarah labari suna dariya, cike da nishad'i suke hirarrakinsu.

chan wajen k'arfe ukku zarah tace yanzu lokacin cin abincinane, nan suka duk'a sukace toh ranki yadad'e atashi lafiya sannan suka mik'e suka fita.

masu kula da abincinta har sun tsaya nan zarah tace sutafi kawai.

zarah dakanta taje tayi serving d'in kanta taci abinci, bayan ta gama nan takira tace suzo sukwashe abincin suje suci.

bayan sallar la'asar zarah kallo takunna tana yi duk kad'aicin 'yan gidansu ya dameta, saida aka kira magrib sannan taje tayi sallah dakanta tashiga kitchen tadafa 'yar indomie, duk yadda kuyanginta sukaso tabari suyimata ammah tak"i tace musu zaman ne ya isheta saisa takeso tad'an motsa jikinta, kan dole suka hak'ura suka barta.

bayan sallar isha'i zarah 'yan gidansu takira sukasha hira tare da tambayarsu yaushe zasuzo, Aysha tace saidai kin ganmu kawai abbah ne yahanani dan naso inzo yau yace a'a sai kinkwana biyu.

zarah cikin rashin jin dad'i tace toh Allah yasa ya amince kuzo kuyi min kwanah ni wlh kad'aici yana damuna.

dariya Aysha tayi tace haba yaya zarah wane kad'aici bayan gidan akwai mutane kuma ga kallo, ni wlh ji nake daman nice.

tsaki zarah taja tare da kashe wayanta tace Aysha kenan, shirin bacci tayi ta sallami kuyanginta tayi kwanciyarta.

*wanshe kare* bayan zarah ta yi sallar asuba bacci takoma sai wajen k'arfe goma tafarka, nan aka had'a mata ruwan wanka tayi tashirya cikin material coffee colour kayan sun kar6eta sosai, nan tafito suka gaisa da kuyanginta tayi breakfast, bayan ta gama breakfast kallo takunna tanayi kasancewarta mai son kallo, kuyanginta suna zaune k'asa, sallamar da taji anyine yasa tad'ago kai, Rahma ce tashigo cikin shigarta ta alfarma sanye da alkyabba, ganinta yasa kuyangi suka duk'e k'asa suna kwasar gaisuwa, zarah tunda taganta tasan jinin yarima ce saboda taga kamansu dasauri tamik'e tare da d'an rissinawa cike da girmamawa tace sannu da zuwa, kuyangi bayan ta amsa musu tashi sukayi suka fita daga d'akin, nan Rahma tatako taje tazauna saman d'aya daga cikin kujerun d'akin saida tazauna sannan zarah ma tazauna tare da gaisheta.

Rahma da take k'arema d'akin kallo amsawa tayi ciki-ciki, zarah fuskarta d'auke da fara'a tamik'e tace bari inkawo miki ruwa,

sumayya yamutsa fuska tayi tace no kibarsa kawai am ohk, daman nazone mugaisa ina fatan kinji labarina wajen mijin naki, nice k'anwarsa.

murmushi zarah tayi tace eh ummi ta fad'amin jiya tace bakyanan ne saisa bamu had'uba, Rahma mik'ewa tayi tsaye tace zan wuce Allah yabada zaman lafiya, zarah ma mik'ewa tayi tare da rissinawa tace mungode Allah yakiyaye, Gimbiya Rahma batace komai ba tawuce tafita.

zarah komawa tayi tazauna tare da dafe kanta cikin ranta tace wannan indai halin yarima ne takwaso daga gani zatayi wulak'anci _(Ni kuma nace haba zarah gani d'aya kawai ammah har kin fassarata)_

bayan sallar azuhur wanka tashiga tayi.

zarah bayan ta fito daga wanka kwalliya tazauna tayi sosai sannan tashirya cikin boyel less d'inta blue nd orange colour d'inkin riga da skirt ne kayan sun kar6eta sosai sannan tad'aura alkyabba orange colour daga saman kayan tayi kyau sosai saida tafeshe jikinta da performs sannan tafito parlour lokacin kuyanginta na zaune k'asa suna jiran fitowarta ganinta yasa gaba d'ayansu suka rissina sukace barka da fitowa sarauniya tsarki ya tabbata ga ubangiji da yahalicci wannan kyakkyawar kuma mata ga sarki mai jiran gado angaisheki gimbiya.

gimbiya zarah takowa tayi tana murmushi kamar ba zatayi maganaba ammah ganin basuda niyar d'agowa yasa tace nafad'a muku banason hakan da kukemin ammah kunk'i dainawa ko?

kuyanga d'aya batare da ta d'ago kaiba tace ranki yadad'e kigafarcemu ke shugabace agaremu kuma mai mutunci dan haka girmamawa yazama dole muyi maki, murmushi zarah tayi a karo nabiyu sannan tace wasu sutaso surakani 6angaren gimbiya sadiya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull