Yarima suhail complete Novel - Chapter 25
Yarima suhail complete Novel Chapter 25: Yarima suhail complete Novel Chapter 25. Bayan ta gama knocking d'in k'ofar tayi nan yarima yabud'e yana rik'e da…
3,352 words
Bayan ta gama knocking d'in k'ofar tayi nan yarima yabud'e yana rik'e da ita yazo da ita wajen darduma, saida yazaunar da ita saman darduma sannan yaje yad'auko mata hijab tasaka sannan yakoma saman gadon yazauna yana kallonta, daga zaune tayi sallar,
Bayan ta gama ganin tanaso tatashi yasa yarima yaje yad'auketa cak yamaidata saman gado yakwantar da ita sannan shima yakwanta gefenta, Zarah shigewa tayi jikinsa nan yarima yarungumeta ahaka suka koma baccinsu.
Wajen k'arfe goma yafarka ahankali yazareta daga jikinsa sannan yamik'e yafita yabar d'akin yakoma part d'insa. Nan yarubuta drugs yaba guard d'insa yace yasiyo masa sannan yashiga bathroom yayi wanka.
Bayan ya fito shiryawa yayi bai ko tsaya breakfast ba yafito saida yakar6i drugs d'in sannan yawuce part d'in zarah.
ko da yashiga bedroom d'in zaune take saman gadonta tana ta fama zata zage zip d'in rigarta amman ta kasa, shigowar yarima yasa tabisa da kallo, suna had'a ido nan tajanye idonta garesa tare da gaishesa, Yarima saida yazauna gefenta sannan ya amsa mata tare da tambayarta ya jiki, zarah tace Alhmdllh sannan tacigaba da kai hannu zata zage zip d'in rigar, Ganin takasa yasa yarima yakai hannunsa zai zage mata, zarah kallonsa take shima yazuba mata ido suna kallon juna bata san lokacin da yazage zip d'inba saidai ji tayi ya salu6e mata hannuwan rigar ta safka k'asa, zaro ido tayi cikin sauri tafad'a jikinsa tarungumesa tareda kare k'irjinta, sun dad'e a haka sannan yarima yajanyeta daga jikinsa tare da d'auko towel d'in da yaga an aje gefe yamik'a mata, cikin sauri zarah takar6a tad'aura tare da duk'ar da kanta k'asa cike da jin kunya,
Cike da rashin damuwa yarima yamik'e sannan yace muje inrakaki toilet d'in, zarah bata musaba tamik'a mai hannunta yatasheta tsaye yana rik'e da ita har suka shiga toilet sannan yafito tare da jawo mata k'ofar yakoma saman gado yazauna yana jira tafito.
Bayan kamar minti goma sai gata tabud'e k'ofar, cikin sauri yarima yaje yarik'ota yazo yazaunar da ita bakin gado sannan yad'auko mata lotion tashafa, Bayan ta shafa magani yad'auka yashafa mata a k'afar yana d'an murzawa zarah saboda zafi har da 'yar k'wallarta, dakansa yaje yabud'e wardrobe yad'auko mata kaya yamik'a mata sannan yaduba agogon hannunsa yace bari insa akawo miki breakfast kiyi sannan ga tabs nan kisha guda biyu ni nawuce hospital,
Zarah binsa tayi da kallo har ya juya ya fara tafiya tace am bakajiba, tsayawa yayi cak batare da ya juyoba, ahankali tace nagode sosai da taimakon da kayi min. Yarima murmushi yayi sannan yabud'e k'ofar yafita. Zarah ma murmushin tayi nan tafara saka kayanta.
Bayan tagama nan aka kawo mata breakfast tayi sannan tasha magani takoma takwanta, tunda takwanta tunanin yarima kawai take musamman ma idan tatuna hidimar da yayi mata daga jiya zuwa yau dan batayi tunanin samun hakan daga garesaba ta dalilin haka har yakwana part d'inta, murmushine yasu6uce mata, wani irin sonsane taji yana fizgarta.
A chan 6angaren gimbiya sumayya koda kuyangarta tazo mata da labarin abinda yafaru da zarah tayi murna sosai har d'aga hannuwanta tayi tai ddu'a Allah yasa ta sanadiyar haka zarah tagurgunce a ranar baccinta tayi cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.
Wajen k'arfe 12pm zarah ce a parlour zaune saman cushion ta mik'e k'afafuwanta, gefenta plate ne mai d'auke da tufa tana ci, sumayya ce tashigo da sallamarta fuskarta d'auke da murmushi.
Ba zarah ba hatta kuyanginta sunyi mamakin ganinta cikin wannan yanayin, gaba d'ayan kuyangin zarah suka duk'a suka gaisheta Sumayya nuni tayi musu alamun subar d'akin. Cikin sauri suka tashi suka fita, saman d'aya daga cikin cushin d'in tazauna har a lokacin fuskarta d'auke da murmushi takalli zarah da tazuba mata ido tace gimbiya zarah ashe tsautsayi yafad'a miki, gaskiya banji miki dad'iba toh waima garin ya hakan takasance da ke? Ke bama hakaba Ina fatan dai baki gurgunceba.
Zarah tunda sumayya tafara maganar tazuba mata ido cike da mamaki, chan sai tayi murmushi tace kar kidamu tsautsayi ne da k'addara, kuma da kike maganar gurgwancewa ko da ace na gurgunce ai ba abun damuwa bane tunda Allah ne daman yabani k'afar dan ya kar6a alokacin da yakeso shine zan damu bayan naci moriyarta? Inaso kisani ni nayarda da k'addara nasan duk abinda zai sameni daga ubangijine.
Ta6e baki sumayya tayi tace hakan ya yi kyau saidai fa natayaki murna da baki nakasaba dan kinsan babu yadda za'ayi yarima yazauna da gurguwa.
'Daga mata hannu zarah tayi tace please ya isa haka idan kin gama abinda yakawoki zaki iya fita dan a yanzu banda lokacinki.
Dariyar mugunta sumayya tayi sannan tamik'e tsaye tace dakyau zarah am naga kamar kina jin jikin buguwar da kikayi bari dai inbarki kid'an samu kihuta saidai ince sai mun had'e a karo nagaba.
Murmushi zarah tayi tace kar kidamu nagode sosai, saduwar alkhairi.
nan sumayya tawuce tafita daga d'akin zarah binta tayi da kallo sannan daga baya tajinge kanta a jikin cushin d'in da take tare da maida numfashi
_Comments_ *nd* _Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_*Sak'on gaisuwa mai tarin yawa agareka Dr S Fulani😍👍*_
_Yau page d'in nakine *Sadiya Sidi Sa'id*, ko da ace sau goma zan mallaka miki page toh bazan ta6a gajiya ba saboda cancatarkice tasa haka, nagode sosai da soyayyar da kike nunamin_
*PAGE* 4⃣1⃣
Wajen k'arfe biyu da taimakon wata kuyangarta zarah tasamu tayi wanka tai sallah ko da tayi lunch maganin tak'ara shafa ma k'afar sannan takwanta saman 3 seater nan bacci yayi awon gaba da ita.
Wajen k'arfe ukku yarima yadawo daga wajen aikinsa, bayan yayi wanka ya shirya yai lunch sannan yafito yanufi part d'in zarah dan yak'ara dubata, ko da yashiga ganinta yayi tana bacci ahankali yataka yaje wajen kujerar da take kwance a kanta, daga gefen k'afarta yatsaya nan yakai hannu yad'an tatta6a k'afar gani yayi kumburin ya sa6e kad'an yarage nan yad'auki maganin yak'ara shafa mata sannan yafita yabar d'akin.
Zarah ko da tafarka k'amshin turaren yarima ne da taji yashaida mata yazo d'akin murmushi tayi sannan tatashi tana bin bango tasamu har taje toilet tad'auro alwallar sallar la'asar, bayan ta fito shimfid'a darduma tayi daga zaune tayi sallah bayan ta gama ahankali tamik'e tana d'an k'engesawa har taje parlour tazauna.
Wajen 8 yarima yashiga part d'inta lokacin tana zaune saman gadonta cikin shirin baccinta tana tufke gashin kanta, ido tazuba mai har yazo gefenta yazauna, kallonta yayi sannan yad'auke kai ahankali yace ya k'afar ina fata dai tayi sauk'i? Zarah marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace da dai sauk'i, yarima ido yazuba mata sai chan yad'auko k'afar yad'aura jikinsa yana dubawa batare da ya kalletaba yace ammah ai kumburin ya sa6e kuma zaki iya d'an takawa, jin shuru batayi maganaba yasa yad'ago kai yaga ta tsaresa da manyan idanuwanta, janye k'afar yayi daga jikinsa sannan yace kinsha magani? Gyad'a mai kai tayi alamun eh, Yarima mik'ewa yayi yace akwai abinda kike buk'ata ne? Zarah k'wallah ce tacika mata ido tayi shuru, Yarima har zai shareta yatafi sai kuma yaji baya iyawa, komawa yayi yazauna tare da rik'o hannunta yace ya akayi ne? Zarah jikinsa tafad'a tare da rungumesa tana jin wani irin sonsa a cikin zuciyanta. Lumshe idonsa yayi tare da kai hannu yana shafa gashin kanta, nan ta ida lafewa a jikinsa, ahankali yajanyeta idanuwanta suna a rufe yakwantar da ita ya d'an jima yana kallon fuskarta chan kuma ko me yatuno cikin sauri yamik'e har ya juya zai tafi kawai sai ji yayi ta ruk'o masa hannu.
Cikin sauri yajuyo yakalleta wani irin tattausan murmushi zarah tasakar mai wanda yakusan zautasa sannan tasaki hannunsa tace sai dasafe. Yarima kasa magana yayi dak'yar yaja k'afafunsa yafita yabar d'akin cike da kasala,
ahaka yakoma part d'insa yakwanta cike da kewarta dan duk jikinsa ya mutu jiyake kamar yakoma d'akinta yakwanta ko bakomai zai rungumeta yad'anji sauk'in abinda yakeji tare da ita ammah yasan jin kansa bazai barsa yayi hakanba, chan kuma sai yatashi zaune tare da dafe kansa yace me yake faruwa da nine? kar dai ace... dasauri yamik'e tsaye yafara zagaye d'akin yace hakan bazai ta6a kasancewa ba, ni dai nasan tausayinta nakeji, inba hakaba ya za'ayi inso yarinyar chan, me takeda shi da kamata *yarima suhail* zaiso? Nasan dai abu d'aya yasa nake zaune da ita saboda za6in iyayena ce ammah babu soyayyarta a tare da ni. Nan sarautar tamotsa masa cikin rashin damuwa yakoma yakwantar tare da kashe gloves d'in d'akin, zarah ce kawai yake gani a duk juyin da zai yi saidai yaja tsaki ahaka yasamu bacci yad'aukesa.
A chan 6angaren zarah ma bayan yarima ya fita daga d'akin jawo pillow tayi tarungume a jikinta tare da lumshe idonta tana jinta cikin wani irin yanayi, chan kuma sai ga k'wallah tana fita daga idonta ahankali tafurta Allah kasa ma wannan bawan sona koda da k'wayar zarrane tausayin kantane yakamata dan ita kanta tasan yadda takeson yarima suhail batayi ma malam bello rabin sonba, tana acikin yanayin baccin yad'auketa.
Da asuba taji sauk'in k'afan sosai dan dakanta taje tayo alwallah batare da antaimaka mataba dan jitayi ta daina yi matazafi, Bayan tayi sallah komawa tayi takwanta dan jiya ta dad'e bacci bai d'auketaba.
Wajen k'arfe goma yarima yagama shirinsa saida yayi breakfast sannan yafito yanufi part d'in zarah, yana shiga lokacin zarah ta fito daga wanka tana zaune tana shafa kallo d'aya yayi mata yajanye kai,
Zarah saida gabanta yafad'i dan ya yi mata wani irin kyau, ahankali tagaishesa, Amsa mata yayi batare da ya kalletaba sannan yace ya k'afar dafatan yanzu tayi sauk'i? Zarah shuru tayi, Ahankali yarima yatako yazo saman gadon yazauna, Zarah kamar jira take nan tad'auko k'afar tad'aura a jikinsa, Kallonta yayi nan tad'aga mai gira tare da yin fari da ido tace duba kagani,
Yarima zuba mata ido yayi yana kallonta dan gaba d'aya ta rikitasa, Zarah turo baki tayi tace kaduba min, yarima baisan ma tana yiba dan gaba d'aya hankalinsa ya tafi wani wajen daban, ganin haka yasa zarah tata6osa, Firgit yayi, murmushi tayi tace ya dai tunanin me kake? Yarima janye idonsa yayi, cikin borin kunya tare da duba agogon hannunsa yace ina tunanin wani theater ne da zanyi a hospital yanzu, janye k'afar zarah yayi daga jikinsa tare da mik'ewa, Zarah binsa tayi da kallo sannan tace am baka dubamin k'afarba, Juyowa yayi yakalleta yace naga ai alamun tayi sauk'i, yana fad'in haka yajuya yayi tafiyarsa.
Zarah murmushi tayi sannan tatashi tad'auko kayanta tasaka sannan takoma parlour tayi breakfast.
Bayan tagama kallo takunna tana yi cike da jin dad'in da ita kanta tarasa namenene.
Yarima baibaro hospital ba sai dare saboda ranar suna clinic ga kuma meeting sunyi, Bayan ya dawo yayi shirin bacci yakwanta sai kuma yaji yanaso yaje yaga zarah dan rabonsa da ita tun safe, Shigowar sumayya ne yasa yad'ago kai cikin sauri yakalleta ganin itace yasa yajanye idonsa daga kallonta,
Gefensa tazo takwanta tare da shafa sajen da yake a fuskarsa tace yarimana ya kake? Batare da ya bud'e idonsaba yace klau, kefa? Rungumesa tayi sannan tace nima haka dear, Murmushi kawai yayi.
Sumayya d'ago kai tayi takallesa cike da so tace ina sonka sosai masoyina, Murmushi Yarima yayi tare da bud'e ido yakalleta har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa. Sumayya zuba masa ido tayi ahankali tace toh kaima kace kana sona dan tunda mukayi aure baka ta6a furtamin hakaba a k'arshema sai kayi min rashin adalci.
Fuskar Yarima cike da mamaki yace sumayya rashin adalcin me nayi miki? Maida kanta tayi takwantar a k'irjinsa sannan tace na auren da kak'ara man. Murmushi yayi yace k'arin aure shine rashin adalci sumayya? Ta6e baki tayi sannan tace ammah ai baidace kayi min kishiyaba kuma karasa wadda zaka aura sai 'yar talakkawa, Cikin d'aga murya Yarima yace ya isa haka sumayya!! Sumayya cike da mamaki tad'ago kai takallesa har ta bud'e baki zatayi magana wata uwar harara da yawurga mata yasa takoma takwanta cike da tsanar zarah dan tasan duk saboda itane yacanza mata har yake yi mata tsawa, cikin zuciyanta tace dasannu zan kawo k'arshen wannan matsalar, ahaka tayita sak'e-sak'e cikin ranta har Yarima yayi bacci yabarta sai daga baya itama baccin yad'auketa.
A 6angaren zarah tun tanasa ran Yarima zaizo dubata ammah har dare baizoba nan takaici yacikata tace daman nasan bai damu daniba nan k'wallah tashuga zuba a idonta cike da tausayin kanta.
_Comments_ *nd* _Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_~Masha Allah my dear *Sadiya Sidi Sa'id* ina tayaki murnar kammala novel d'inki mai suna *MAHAIFIYA* hak'ik'a kin baje mana basirarki a cikinsa mun ilmantu, mun nishad'antu sannan kuma mun wa'azantu, gaskiya na jinjina miki sosai da namijin k'ok'arin da kikayi, Abinda kika fad'a daidai Allah yabaki ladan kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, nagode sosai da soyayyarki agareni inaso kisani ina ji da ke har cikin zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare~_
_*I dedicated this page to you Admin of Admins*_
_On your birthday, today I wish u a year with loads of fun, excitement nd beautiful memories. Happy Birthday Admin of Admins *Hayatu Baba Zubairu (Yaya Hayat)*_
*PAGE* 4⃣3⃣
Da asuba saida yayi sallah sannan yatada zarah saida yataimaka mata tayo alwalla sannan tazo tayi sallah.
tana gamawa k'wallah ce cike da idonta takalli yarima da yake zaune ahankali tagaishesa.
Gyad'amata kai kawai yayi alamar ya amsa, janye idonta tayi daga kallonsa sannan tace nasan bazaka ta6a yadda cewa bani nazuba poison d'inba ko? Wlh ko da sau d'aya ban ta6a kawo ma raina incutar da kai ba, juyowa tayi takallesa da shima ita yake kallo sannan tace nasan bazaka ta6a yadda daniba a yanzu ka tsaneni ko?
Har a lokacin kallonta yake baice komai ba, zarah mik'ewa tayi dak'yar taje inda yake zaune tatsugunna tace koda ace zaka yanke min hukunci inaso kataimaka kayi min wanda iyayena bazasuji labariba, ammah dan Allah kataimaka kayi bincike kafin kazartas min da hukuncin,
Sai a lokacin yarima yajanye idonsa agareta sannan yace zarah kinji na ce miki wani abu?
Girgiza kanta tayi cikin sauri har a lokacin k'wallah tana fita daga idonta.
Toh indai banceba kikyaleni kije kikwanta kihuta.
Zarah girgiza kai tayi cikin kuka tace taya kake tunani zan iya kwanciya alhali ina cikin wannan matsalar? Tausayi tabashi yanayin yadda tayi maganar, d'aura hannunsa yayi a kumatunta sannan yace kar kidamu, yana fad'in haka yatashi yafita daga d'akin, Zarah kife kanta tayi da gadon tana mai ci gaba da kukan.
Koda yaje magana sukayi da doctor sannan yashigo yace ma zarah tataso sutafi har a lokacin kuka take jikinta ba k'wari dakyar take takawa, har bakin mota doctor yarakasu sannan sukayi sallama.
lokacin da sumayya tatafi d'akinta takaicine yacikata ganin burinta bai cikaba domin taso ace poison d'in yafara aiki agabansu dada saboda tasan da anga haka k'arshen rabuwar yarima da zarah tazo.
tsaki taitayi daga k'arshe dabara tafad'o mata nan takira kuyangarta zabba'u tace taje tasa mata ido akan duk wani motion d'in zarah
nan zabba'u takwashi gaisuwa sannan tafito tasamu inda ba za'a gantaba tala6e, tun daga fitowar zarah har tafiyar da sukayi da yarima asibiti duk akan idontane,
nan tazo taba sumayya labari dariyar mugunta sumayya tayi tare jinjina kai ahankali tace lallai zarah kinyi jarumta.
tunda asuba tazuba ido domin taga dawowarsu,
lokacin da yarima yayi horn suka shigo gate da mamaki yake kallon dada da umman sumayya da ita kanta sumayya da suke tsaye cikin ransa yace tabbas wannan aikin sumayya ne.
zarah kau rikicewa tayi takalli yarima tace shikenan yarima sun gano ni nashiga ukku.
yarima batare da ya kalletaba yace kar kisaki kinuna akwai wani abu indai kika nuna suka gane babu ruwana sai kisan yadda zaki Kare kanki,
daidai lokacin yagama parking d'in motar yabud'a yafita batare da ya kalletaba.
zarah tana ganin haka itama tabud'e tafito cikin zuciyanta tana ta addu'a
bayan yarima tabi a tsorace shidai tafiyarsa yake hankali kwance gab da zai isa wajen da su dada suke nan wayarsa tafara ruri tsayawa yayi yad'auko wayar yana dubawa murmushin nasara yayi sannan yayi picking d'in wayan batare da yayi magana ba,
daga chan 6angaren akace ranka yadad'e Dr, Ahmad ne yake magana daman wannan patient d'inne da kayi ma theater toh ya farka.
yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace idan kun tabbatar da babu abinda yake damunsa toh sai kuyi masa wannan injection d'in da na aje inyaso da anjima idan nashigo sai in rubuta masa drugs.
daga chan 6angaren akace toh ranka yadad'e sai ka shigo, yarima baice komai ba yakashe wayarsa, sannan yamaida kallonsa ga dada da tatsaresa da ido ammah ko inda su umman sumayya suke bai kallaba.
murmushi yasakar ma dada yace ranki yadad'e ya akayi naganki nan a tsaye a wannan lokacin?
fuskar dada a d'aure tace daga ina kuke?
shuru yarima yayi yana murmushi,
dada tace ashe yarinyar nan dagaske guba tazuba maka tunda da taci abincin saida kukaje asibiti, kai wlh bansan samna bane sai yanzu matar da tayi shirin kasheka itace kataimaka mawa toh wlh dole memartaba yaji maganar nan.
har a lokacin yarima murmushi yake sai chan yace dada bai dace kice hakaba tunda baki gani da idonki ba, kirana fa akayi daga hospital akan wani emergency case cikin dare shine zarah tace zata bini mukaje tare kuma ma yanzu ai gabanki aka kirani waya.
sumayya tayi karaf tace wlh bahaka bane poison d'in da tacine a cikin abinci kiduba kiga yadda duk tazure, ummanta tace ai wannan dama daga ganinta poison taci.
yarima murmushi yayi sannan yace sumayya gabanki tazuba min poison d'in? gabanki tayi girkin? Lokaci guda yajero mata wad'annan tambayoyin.
sumayya tace toh ai lokacin da takeyi naga ta zuba wani abu.
yarima wani mugun kallo yawurga mata yace toh kina dai nufin la6e kikayi mata.
sumayya hararar zarah tayi da take raku6e bayan yarima tace wannan gajar zan yi ma la6e? tak'aryata mana idan batayiba, kuma naga lokacin da katafi kakaita asibiti.
murmushin mugunta yarima yayi yace toh in ko ta zuba min poison toh tare da ke aka zuba kokuma ke d'in kika Zuba.
zaro ido sumayya tayi tace ni ya za'ayi inzuba maka poison?
yarima kallon dada yayi yace ranki yadad'e kiduba kiga inda ace yarinyar nan ta zuba poison kina tunanin zata amince taci abincin alhali tasan zata iya mutuwa?
dada jinjina kai tayi batare da tace komai ba.
yarima suhail rik'o hannun zarah yayi yace bari mushiga daga ciki.
kallon ummah yayi da tacika tayi fam yayi murmushi yace ummah gaskiya ya kamata kija ma d'iyarki kunne tadaina la6e, na barku lafiya. jan zarah yayi suka shige sukabar su dada a tsaye, sultana sadiya da harara tabi yarima ji take kamar tashak'esa yamutu kowa yahuta,
dada kallon sumayya tayi tace sumayya yakamata ki iya bakinki yanzu gashinan kinja naji kunya, tana gama fad'in haka tawuce tanufi turakarta.
sultana sadiya kallon sumayya tayi da duk tasusuce tace ai ga irinta nan gashinan kinja yaro k'arami yana nema yarainani,
sumayya turo baki tayi tace ammah ai ummah bak'arya nayiba.
ummah tace ko da ace ba gaskiya bane ai bakida k'wak'warar hujja, wlh matsalata da ke bakida isashen wayau, duk yadda zakiyi abu bakisan yadda zaki fitar da kankiba.
sumayya cikin fushi tace haba ummah dame zan ji? da rashin cin nasara ko da surutun da kikeyi min?
sultana sadiya ganin d'iyartata tayi fushi yasa tafara lallashinta har saida taga ta hak'ura sannan tace tafi kiyi baccinki kicire komai a ranki ina tare da ke kinji ko d'iyata.
Toh ummana kema kije kihuta, murmushi sultana sadiya tayi sannan tatafi cike da tausayin 'yartata.