Yarima suhail complete Novel - Chapter 36
Yarima suhail complete Novel Chapter 36: Yarima suhail complete Novel Chapter 36. Zarah cikin 6acin rai tace kamar yadda kika isa toh nima haka na isa,…
3,359 words
Zarah cikin 6acin rai tace kamar yadda kika isa toh nima haka na isa, yadda bana shiga harkarki toh nima kidaina shiga tawa, juyowa tayi tanuna zinat tace kekuma inke babbar marar kunyace toh kik'ara ta6ani. wlh duk wadda tak'ara ta6ani sai tagane batada wayau, ni kubani hanya inwuce.
Turata sumayya tayi tafad'a saman kujera sannan tace wlh yau nice silar zubewar cikinki,,,tana fad'in haka nan suka rufe zarah da duka, ta ko'ina bugunta suke.
Zarah duk'ewa tayi gudun kar subugar mata ciki, kuka kawai take, daga k'arshe sumayya tajawota daga saman kujerar tafad'o k'asa, nan suka cigaba da bugunta suna takata zarah kuka take tana neman agaji,
Wata baiwartace tajiyo ihunta cikin sauri tanufo d'akin tana zuwa taga su sumayya akan zarah janta suke suna nema subugi cikinta ammah ta duk'e, k'ara baiwar tasaki cikin sauri tanufo wajen tare da rungume zarah jikinta tana kuka tace dan Allah kuk'yaleta,
Sumayya cikin 6acin rai takaima baiwar mari tace ke har kin isa ina waje kitako kizo har ma kinemi kishiga harkar da ba takiba tashi kiban waje ko yanzu in kasheki.
Baiwar ture sumayya tayi tace wlh saidai kukasheni ammah bazan bari kucigaba da dukantaba.
Kan baiwar suka koma suka fara dukanta dak'yar ta k'waci kanta tatashi taruga dagudu tabar d'akin.
Zarah amai tafarayi tana maida numfashi sama-sama, ganin haka yasa suka kwashe da dariya sannan sumayya tace a haka kawai idan muka barki mungama da ke matsiyaciyar banza.
Zinat kallonta tayi tace anya sumayya cikin nan ya zube?
Sumayya k'afa takai zata harbi cikin zarah cikin rashin sa'a sai k'afar tatsaya a k'irjinta sannan sumayya tace ai dolema yazube muje kawai baby, nan tajawo Zinat suka fita daga d'akin suna dariya.
Zarah kwance tayi wajen tana maida numfashi sama-sama dan ko hannunta bata iya d'agawa.
Ko da baiwar tafita dagudu tayi part d'in yarima cikin rashin sa'a guards d'insa sukace bayanan dan haka tanufi hanyar waje.
Yarima koda yashiga part d'in ummi bayan sun gaisa zama yayi suka d'an ta6a hira da su Aunty husna saida aka kira sallar la'asar sannan yatashi yatafi masallaci.
Bayan ya gama sallah a hanyarsa ta dawowa tsayawa yayi suka gaisa da jama'a sai wajen biyar sannan yasamu yanufo gida, part d'in su ummi yai shirin komawa sai ga wannan baiwar da gudu tana zuwa gabansa tazube k'asa tana haki.
da mamaki yarima yake kallonta yace ke lafiya? Cikin rawar murya tace kagafarceni ranka yadad'e ga su gimbiya sumayya chan d'akin gimbiya zarah suna dukanta wai zasu zubar mata da ciki.
A firgice yarima yace duka kuma!, kuna aikin mi kukuma?
Girgiza kai tashiga yi tace kagafarceni wlh na shiga intaimaka mata shine suka had'a da ni har suka fashemin baki dak'yar nasamu nagudo.
Yarima bai ida saurarentaba yayi gaba cikin sauri yanufi 6angarensu, bai damu da gaisuwar da akeyi masaba dan baima san anayiba cike da tashin hankali yawuce part d'in Zarah, yana shiga yaganta kwance k'asa tana maida numfashi, cikin sauri yanufi inda take tare da janyota jikinsa a rud'e yace Zarah sannu garin ya haka yafaru, hannu yakai saman cikinta yana shafa.
Zarah fashewa tayi da sabon kuka muryarta tana fita ahankali cikin wahala tace me natsare ma sumayya takeson ganin bayana? Me yasa tatsaneni haka? Wannan wane irin tsanace tayimin har take ik'irarin kasheni.
Yarima runtse idanunsa yayi dak'arfi yana jin wani irin tsanar sumayya a ransa,,,ahankali yabud'e idanunsa yasafke akan fuskar zarah sahun hannuwansu sumayya ne kwance a fuskarta, bakinta kuma jini ne yake fita, handchief d'insa yajanyo yagoge mata jinin, ahankali yakai bakinsa cikin nata yayi kissing d'inta, sannan yad'auketa chak yanufi toilet da ita,
Ruwan d'umi yahad'a yasakata ciki dakansa yaimata wanka sannan yad'aukota yafito da ita, zaunar da ita yayi bakin gado, cikin sauri zarah taruk'osa, kallonta yayi cike da tausayinta yace bari ind'auko miki kaya.
Zarah sakinsa tayi nan yawuce yanufi wardrobe d'inta yabud'e yad'auko kaya yataimaka mata tasaka sannan yad'auko magani yabata tasha saboda jikinta da yaji alamun zazza6i, zama yayi gefenta nan zarah tafad'a jikinsa tare da fashewa da sabon kuka.
Yarima shafa kanta yayi yace please kukan ya isa haka, zarah rage sautin kukan tayi sannan tace please kamaida ni gidanmu inba hakaba sumayya sai ta ida nufinta a kaina,
Yarima k'ara rungumeta yayi jikinsa sannan yace kar kidamu babu abinda zata iya yi miki wannan ma a bisa kuskure ta aikatasa ammah....sai kuma yayi shuru batare da ya ida fad'in maganar da take bakinsaba.
Janye zarah yayi daga jikinsa yamik'e, cikin sauri zarah taruk'o hannunsa, kallon fuskarsa tayi da gaba d'aya ta canza saboda 6acin rai,,,muryarta tana rawa tace ina zakaje? Please kar kayi mata komai.
wani irin kallo da yayi matane yasa cikin sauri tasakesa dan gaba d'aya ya gama tsoratata. Batare da yayi maganaba yajuya yafita.
a 6angaren su sumayya koda suka koma part d'inta dariya suka cigaba da yi, sumayya cikin jin dad'i tace yanzu nasan burina ya cika, zinat tsagaitawa tayi da dariyarta tace baby toh yanzu idan mijinki ya dawofa ya zakiyi.
Ta6e baki sumayya tayi tace bazan damu da abinda zai min ba tunda nasan duk abinsa bai isa yasakeniba, dariya zinat tayi tace angaisheki gimbiyar yarima aikinki yana yin kyau, yanzu dai muje kiji da ni tunda hankali ya kwanta.
Kallonta sumayya tayi tace ina zuwa, nan sumayya tafito tasamu kuyanginta da suke tsaye waje tana yamutsa fuska tace kar kubari kowa yashigo min nan duk wanda kuka saki kukabari yashigo toh a bakin aikiku. gabad'ayansu suka duk'a sukace angama ranki yadad'e. juyawa sumayya tayi takoma ciki. Suna rik'e da junansu suka wuce suka shiga bedroom tun a hanya suka fara cire ma junansu kaya, jikin sumayya har rawa yake tajanyo zinat suka fad'a saman gado.
Cike da 6acin rai yarima yake tafiya yanufi part d'in sumayya, duk bawan da yatunkaresa zai masa magana da yaga yanayinsa zaiyi sauri yaja baya.
Kuyangin sumayya da suke gadin k'ofa ganin yarima yasa sukayi saurin ja baya tare da duk'awa suna kwasar gaisuwa, yarima baibi ta kansuba yawuce,
koda yashiga a parlour yatarar babu kowa dan haka cikin sauri yawuce yanufi bedroom d'inta.
_Toh fa koya za'a k'are idan yarima yashiga yaga sumayya tare da zeenat?_
_ko wane irin mataki zai d'auka akanta?_
_*duk amsar tana cikin next page dan haka Muje zuwa*_
_Comment_ *nd* _Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔
_Masha Allah, sak'on gaisuwa agareku masoya a duk inda kuka kasance, gaskiya ina jin dad'in yadda kuke comments a groups akan novel d'in *YARIMA SUHAIL* da yadda nake samun sak'on gaisuwa daga gareku nagode sosai saidai ince Allah yabar k'auna, Sis Nerja'art tana yinku over_
*PAGE* 5⃣6⃣
Cikin zafin nama yarima yatura k'ofan, abinda yaganine yafirgitasa a kid'ime yafara furta innalillahi wa'inna ilaihiraji'un.
Sumayya da zinat da suke manne da juna basu ma san shigowarsaba dan gabad'aya basu cikin hayyacinsu saida sukaji yana salati sannan sukayi saurin rabuwa da Juna, cikin sauri zinat tajanyo bedsheet tarufe jikinta.
Sumayya wata irin razanannar k'ara tasaki tare da furta na shiga ukku na bani na lalace dan Allah yarima kayi hak'uri ba laifina bane sharrin shaid'anne.
Yarima da yake tsaye jikin k'ofa ya runtse idonsa innalillahi kawai yake nanatawa dan samun sauk'in abinda yakeji a ransa inba hakaba ya san zai iya abinda za'azo ana da na sani.
Cikin sauri zinat tajanyo zanenta tad'aura tana zare ido saboda a tsorace take, Sumayya ko bedsheet d'in tayaye tarufe jikinta da shi har a lokacin kuka take tana jin abun kamar a mafarki.
Ahankali yarima yabud'e idanuwansa da suka koma launin ja saboda tsananin 6acin rai, murmushin takaici yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace Sumayya ban ta6a sanin ke dabba bace sai a yau, ke ko dabba ma ta fiki k'wak'walwa mai kyau, ace a matsayinki na mace kina aiwatar da wannan mummunan halayyar, wlh a yau na tsaneki Sumayya bana fatan k'ara sakaki a idona, na yi da nasanin amincewa da nayi na aureki.
kallon zinat yayi yace kekuma har da tako min gida kika daki matata sannan kuka aikata masha'a a cikin gidana!
Sumayya cikin kuka tace dan Allah yarima kayi hak'uri wlh nabi ka nai maka alk'awali bazan k'araba dan Allah kar katona min asiri.
Zinay had'e hannuwanta tayi waje guda tana kuka tace dan Allah ranka yadad'e kayi hak'uri wlh tsautsayine yakawoni.
Yarima maida d'akin yayi yarufe sannan yace da fari zan fara rama ma matata dukan da kukayi mata,,,wucewa yayi yajanyo adaptor irin mai kaurin nan yatsige kan yad'auki wire d'in, wajen da suke yanufa daga bakin gadon yatsaya yafara shaud'a musu, ihu suke suna kuka nan tacigaba da had'awa da mari daga k'arshe k'asa yajanyosu yacigaba da duka da harbi da k'afa, ihu suke suna kuka ammah yarima bai k'yalesuba saida yaga ya had'a musu jini da majina basu iya kotsin kirki sannan yabarsu,
Jikinsu duk sahun bulala ya kwanta duk saida sukayi da sun sani akan ta6a zarah da sukayi.
Yarima kallon Sumayya yayi da take kuka yace wannan ramama matata nayi, sannan kuma ada nazo da niyar inyi miki saki d'aya ammah ganin abinda kike aikatawa ya sa zan miki....cikin sauri Sumayya tace dan Allah yarima kar kasakeni please kacigaba da dukana kar kafurta kalmar.
Wani irin kallo yarima yai mata mai tattare da tsana sannan yace kije na sakeki saki ukku dan bana buk'atarki a cikin rayuwata.
Wata razanannar k'ara Sumayya tasaki tare da rarrafowa ta iso inda yarima yake cikin kuka tace dan Allah kabarmin saki d'ayan wlh shi kad'ai ma ya isheni please ka janye biyun tafad'i haka tare da ruk'o rigarsa.
Yarima fizge rigarsa yayi yace kar kik'ara ta6ani da wannan hannun naki mai najasa, wucewa yayi yabud'e bedside d'inta yad'auko paper da biro nan yarubuta mata saki ukku ya cilla mata sannan yace na baki nan da awa d'aya kitattara komatsenki kifita kibarmin gida inko ba hakaba zan sa6a miki.
Sumayya dafe kanta tayi tare da k'ara sautin kukanta tace na bani na lalace yau ni ya zanyi da rayuwata,,,,kallon zinat tayi da take raku6e waje guda fuskarta duk ta kumbura tace shikenan zinat kinja min yau nima aurena ya mutu yau ni nashiga ukku ina zansa rayuwata.
Yarima a fusace yace na dai fad'a miki kar kibari indawo in tarar da ke,,, yana fad'in haka yajuya yabud'e d'akin yafita.
Sumayya tana ta k'wala mai kira yai mata banza, nan tacigaba da kukanta.
Zinat na ganin ya fita ta rarrafa tajanyo rigarta da veil d'inta tasaka, dakyar tamik'e tsaye, sumayya ganin zata fita yasa cikin kuka tace zinat ina kuma zaki tafi kibarni kina ganin matsalar da kika jefani.
Zinat jakkarta tad'auka batare da ta kalli sumayya ba tace tafiya zanyi tun kan yarima yadawo ya6allani koma me kenan nidai sai munyi waya dan haka kinga ma tafiyata kisan yadda zakiyi kikare kanki,,,zinat na gama fad'in haka tabud'e k'ofan taficce cikin sauri, gudu-gudu haka tasamu tafita daga masarautar bata tsaya jiran abun hawaba tacigaba da sauri sai da tayi nisa sannan tasamu tahau abuabun hawa.
Sumayya na ganin zinat ta fita nan ma k'ara fashewa da sabon kuka tayi tace na bani ni yanzu ya zanyi da kaina wai nice yarima yasaka wlh ba zan yardaba sai anmaida aurenmu,,,,rarrafawa tayi tajanyo wayarta tana kuka tai dialing d'in number d'in ummanta.
Ummah tana yin picking taji kukan sumayya yana tashi, ahankali tace ya salam sumayya me kuma kike ma kuka kedai inba kukaba ba abinda kika iya.
Cikin kuka sumayya tace ummah ya sakeni.
Ummah da take kishingid'e zumbur tamik'e tsaye tace me kikace sumayya saki?
Eh ummah. Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un garin ya haka yakasance sumayya? Nashiga ukku ni halima, dan ubanki kifad'amin me kikayi yasakeki.
Sumayya cikin sheshek'ar kuka tace ummah daga na daki matarsa shine yasakeni. Dan Allah asashi yamaida ni
Sultana sadiya ajiyar zuciya tayi tace sumayya kin tabbata abinda kika fad'amin gaskiya ne? Eh ummah. Toh shikenan yanzu yi maza kije wajen su dada kisanar da su, nima ganinan zuwa ai dole kikoma d'akinki. Sumayya cikin kuka tace Toh ummah,,,nan takashe wayar tare da mik'ewa tajanyo kayanta tasaka.
A firgice tafito cikin sauri tanufi turakar su memartaba, tana shiga parlour dada ce kawai nan sumayya taduk'e k'asa tare da fashewa da sabon kuka.
Dada rud'ewa tayi tace lafiya sumayya me yake faruwane? Bakida lafiya ne?
Sumayya girgiza mata kai tayi tace kod'aya dada, yarima ne yasakeki.
Dada dafe k'irji tayi tace Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, saki fa kikace?
Memartaba da yake ciki yana shirin fita jin hayaniya yasa yafito yana cewa hayaniyar me nakeji haka?
Sumayya duk'awa tayi tagaishesa cikin girmamawa, Saida memartaba yazauna sannan ya amsa mata tare da cewa lafiya sumayya kike kuka?
Dada girgiza kai tashiga yi tace ranka yadad'e wlh yarima baya da mutunci yanzu saboda Allah ace ya saki 'yar uwarsa?
Memartaba cikin d'aga murya yace saki kuma? Anya kuwa sakinta yayi dan bana tunanin yarima zai zartas da wannan hukuncin batare da na saniba.
Dada tallabe ha6a tayi tace wlh indai yarima ne zai aika.
Memartaba kallon sumayya yayi yace ke kallanni nan fad'amin me kikayi masa yasakeki?
Sumayya rage sautin kukanta tayi sannan tace banyi masa komai ba daga matarsa ta ja ni fad'a har da cemin juya marar haihuwa, shine nikuma nabiye mata nan mukayi fad'a shine yakamani yai min duka,tafad'i hakan tare da d'age hijab d'inta su memartaba salati suka shiga yi da suka ga kwanciyar bulala a jikinta. Cikin sheshek'ar kuka tace bayan ya gama dukana shine yasakeni.
haushine yacika memartaba yace banyi tunanin hakan daga wajen yarima ba banta6a tunanin zai iya min cin mutunci irin hakaba ammah bari inkira iyayenku suzo asan yadda za'a 6ullo ma lamarin.
Memartaba wayarsa yad'auka yakira mahaifin yarima da na sumayya yace duk suzo da iyalansu susamesa.
Bayan kamar minti goma sai gasu su duka sunzo harda Aunty husna da rahma da suke gidan basu koma gidajensuba,
Lokacin su memartaba suna zaune suna tattauna al'amarin gabad'ayansu suka duk'a suka gaishesu, kowa da mamaki yake kallon sumayya.
Bayan su memartaba sun amsa gaisuwa, gyaran murya yayi yace wani ya aika akira min yarima dan na kira wayansa a kashe.
Abban sumayya ne yace toh ranka yadad'e nan yamik'e yaje ya aiki wani dogari yace yaje yakirasa.
Yarima bayan ya baro part d'in sumayya nan yakoma 6angaren zarah yanayinsa kawai zaka kallah kasan ba k'aramin tashin hankali yake cikinsaba, kallon zarah yayi da take kwance ta zuba ma waje d'aya ido tana kallo, daga gefen gadon yazauna tare da dafe kansa yana tunanin lamarin sumayya dan gabad'aya ta gama ficce masa a rai, wayoyinsa yakashe gabad'aya dan ya san dole sai memartaba ya nemesa dan dama gudun kar amaido masa aurenta yasa yaimata saki ukkun.
Zarah ruk'o hannunsa tayi cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace tunanin me kakeyi?
Kallonta yarima yayi cike da tausayi yace in kaiki asibiti adubaki ko?
Girgiza kai zarah tayi tace babynka lafiyarsa lau dan basu samu sun ta6asa ba nikuma ciwon jikine kuma nasan zan warke insha Allahu.
Yarima d'aura hannunsa yayi saman fuskarta sannan yace ammah kina buk'atar asa miki drip kuma jikinki akwai zazza6i.
Zarah maida idonta tayi talumshe, yarima zuba mata ido yayi yana kallonta.
Knocking d'in k'ofan da akayine yasa yamik'e yaje yabud'e kuyangar zarah ce cikin sauri taduk'a tagaishesa, yarima batare da ya amsa mataba yace ya dai.
Jikinta yana rawa tace ranka yadad'e daman dogari ne aka aiko daga turakar sarki yace yana son ganinka.
Yarima baiyi mamakin hakaba, dawowa yayi yakalli zarah da take kwance ta ji duk maganarsu, janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace bari indawo sai muje hospital.
'Daga mai kai kawai zarah tayi, nan yarima yajuya yafita yanufi turakar memartaba.
Lokacin da ya isa baiyi mamakin ganin family d'insa da suka hallaraba, bayan ya yi sallama, waje yasamu k'asa chan gefen Aunty husna yazauna, cikin rashin damuwa yagaishe da su memartaba.
Ciki-ciki memartaba ya amsa masa nan d'akin yad'au shuru kowa saurare yake yaji memartaba ya fara magana.
Gyaran murya memartaba yayi sannan yakalli yarima da kansa yake sunkuye k'asa yace wannan taron ba dan kowa nayisaba sai dan kai yarima. suhail ka bani kunya ban ta6a tunanin hakan daga garekaba koma menene ai ana son sasacin a cikin aure, wace irin zuciyace ta d'ibeka har kasaki matarka.
Gabad'aya 'yan d'akin sukace saki!! Nan aka fara kallon kallo.
Memartaba nuna sumayya yayi da take kuka har Lokacin Sannan yace toh gatanan dai ya saketa, ke kifad'a musu dalilin sakin suma suji.
Sumayya saida takalli yarima da kansa yake sunkuye sannan tamaimaita abinda tafad'a ma su memartaba.
Da mamaki yarima yad'ago yakalleta jin k'aryar da tadage tana shararawa, wata uwar harara yawurga mata nan Sumayya tafara dabarbarcewa.
Yana hararanta karaf a idon dada cikin fushi tace kikwantar da hankalinki kiyi bayaninki dan babu abinda ya isa yayi miki tunda kina a gabanku, Nan Sumayya tacigaba da bayani.
Bayan ta gama d'akin yad'au shuru kowa yana jimami a cikin ransa, dadyn yarima ko kunyace takamasa ganin abinda d'ansa ya aikata ma d'iyar d'an uwansa, ummi ma jin abun take wani iri dan bata ta6a tunanin hakan daga garesaba.
Gyaran murya memartaba yayi yace kunji jawabinta, kunga abin kunyar da yarima ya aikata kan bare yarabu da 'yar uwarsa, toh yanzu ba sai anja maganar da nisaba na umurceka kamayar da ita d'akinta.
Sai a Lokacin yarima yad'ago yakalli memartaba cike da girmamawa yace ranka yadad'e kagafarceni, bata fad'a muku saki nawa nayi mataba? Ko daman idan anyi saki ukku ana komawa.
Nan d'akin yarikice da salati memartaba yace da hankalinka zakayi ma matarka saki ukku yarima? Sakin da ubangiji bayaso ana yi, ina iliminka da tuninka suke.
Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.
Memartaba yace inji a lokaci guda kayi sakin?
Sumayya tayi karaf tace eh ranka yadad'e gabad'aya yayimin.
Toh Alhmdllh tunda gabad'ayane kuma cikin fushine zamu iya d'aukansa a matsayin saki d'aya kaga sai kamaidata d'akinta yanzu....cewar memartaba
Yarima k'ara duk'ar da kansa yayi sannan yace kagafarceni ranka yadad'e na riga da na haramta ma kaina k'ara auren Sumayya,
A firgice kowa na d'akin yakalli yarima, nan Sumayya tafashe da kuka tace na shiga ukku dan Allah kutaimaka min yamaidani d'akina.
Memartaba kallon yarima yayi yana jinjina kai dan ya ma rasa abinda zai ce masa,
Dada ce tashare kwallar da tazubo mata saboda tausayin Sumayya sannan tace ranka yadad'e ka gani ko? Lokacin da nake fad'a maka wulak'ancin da yarima yake ma Sumayya ba ka yarda, duk wulak'anci da cin mutuncin da matarsa takeyi mata bai ta6a tankawaba sai ita da suka d'an samu sa6ani shine yadank'ara mata har saki ukku.
Ummi kallon yarima tayi kallon mamaki, yarima cike da jin kunyar ummi yaduk'ar da kansa k'asa.
abban Sumayya ne yai k'arfin halin cewa kuyi hak'uri yanzu haka wani haukan ne Sumayya tayi masa kuma ba a ji daga garesaba.
Memartaba murmushin takaici yayi sannan yace bana buk'atar jin komai daga garesa, nagode sosai suhail ni kawulak'anta tunda ni na aura maka Sumayya yanzu ka maido min abuna ka ce ban isa inyi maka abinda bakasoba, Saboda ganin kamar ban kyauta makaba yasa nabarka kaje ka auro za6inka bayan shekara d'aya da aurenku da Sumayya, duk labarin da ake bani akan abinda kake ma Sumayya ban ta6a yardaba sai gashi yau na gane ma idona abinda zai d'aga min hankali abinda d'ana nacikina bai aikataba sai gashi jikana namiji tilo d'aya ya aikata ma 'yar uwarsa.
Yarima d'ago kai yayi yakalli memartaba yace kagafarceni ranka yadad'e nima ba a son raina na aikata hakanba, wlh Sumayya ba gaskiya tafad'a mukuba.
Memartaba d'aga masa hannu yayi yace dakata bana buk'atar jin komai daga wajenka abinda idona yagane min ya isheni.
Daddyn yarima kallon yarima yayi cike da takaici yace suhail ka ban kunya kana gani yadda nake zaune da d'an uwana lafiya ammah karintse ido kakarta min rashin mutunci har haka, yanzu da wane ido kakeso ink'ara kallonsa.
Girgiza kai yarima yashiga yayi yace kayi hak'uri daddy wlh nima ba a son raina hakan takasanceba.