Kenza eBookz

Yarima suhail complete Novel - Chapter 40

Yarima suhail complete Novel - Chapter 40

Yarima suhail complete Novel Chapter 40: Yarima suhail complete Novel Chapter 40. A 6angaren su sumayya koda suka isa 6angaren iyayenta tusa sultana sadiya…

3,338 words

A 6angaren su sumayya koda suka isa 6angaren iyayenta tusa sultana sadiya tayi a gaba tana kuka har da mirgina lallashinta sultana sadiya take ammah kamar k'ara tunzurata take, sumayya kuka take sosai tana cewa dole sai ta koma d'akinta wlh bazata ta6a yadda ba zarah asiri tayi tarabasu da yarima.

Daga k'arshe jugum sultana sadiya tayi tana sauraren d'iyartata, suna cikin haka sai ga sultan abbas ya shigo ganin sumayya kwance k'asa tana mirgina yasa yadaka mata tsawa yace ke menene haka kikeyi?

Sumayya tashi tayi a zaune tana cigaba da kukanta. Sultana sadiya ce tayi k'arfin halin cewa yauwa gama kanan dan Allah kazo kataimaka asan yadda za'ayi sumayya takoma d'akinta wlh tana son mijinta sosai.

Murmushi sultan abbas yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace sadiya kenan ai ban d'auka zaki mance da saki nawa bane suhail yayi mata,

Ke kuma,,yanuna sumayya da yatsa yace garin haukanki kinje kin kashe aurenki na tabbata suhail ba zai ta6a yimiki saki ukku ba batare da wani k'wak'waran daliliba, toh yanzu wa gari yawaya? Sai kizo kujera da mahaifiyartaki kiyi ta zaman gida, babban bak'in cikina ma da kikayi silar raba yarima da family d'insa.

Cikin 6acin rai sultana sadiya tace haba Alhaji wannan wane irin cin mutuncine tun a gaban memartaba kake ta kware ma d'iyarka baya toh inaso kasani hannunka baya ru6ewa kacire kayar kuma ni nasan sumayya ba abinda zatayi ma yarima wanda zaisa yaimata wannan saki haka saidai idan wacchan munafukar matsiyaciyar yarinyarce tashiga tsakaninsu.

Dakata ke banson shashanci nalura kamar ke kike goya ma yarinyar nan baya tana yadda takeso dan haka kukiyayeni ko gabad'ayanku insa6a muku, wlh kikiyayi lokacin da zakiji kunya dan naga kina d'orema k'arya gindi, ni a wajena da yarima da sumayya duk d'ayane dan dukansu 'ya'yanane bana goyon bayan kowa sai gaskiya dan haka gatanan tayi ta zaman gidan zata gane ai idan iyaye da miji d'ayane, duk dai inda mace takasance komai gatanta toh gidan miji shine kwanciyar hankalinta, Sannan ke sumayya ina k'ara tunatar da ke saki ukku ne yarima yaimiki bakida ko sauran igiya d'aya dan haka dole yanzu kicire tunanin komawa gidansa dan yariga da yayi miki nisa,,,,sultan abbas yana kaiwa nan a zancensa yawuce yashige part d'insa cike da 6acin rai.

Sultana sadiya da kallo tabisa dan gabad'aya ya kashe mata baki ga takaici da yacikata, cikin kuka sumayya tace ummah yanzu shikenan na rasa yarima ya zanyi da rayuwata.

Cikin 6acin rai sultana sadiya tace ai ga irintanan ke kibar ganin ina goyon bayanki kema ai kina da naki laifin a ciki yanzu gashinan kinja mijina nima yad'au fushi da ni yadda kika kaso aurenki toh nima bazakiyi silar mutuwar nawaba dan haka dole kihak'ura kicire suhail a ranki tunda bashikad'ai bane namiji a duniyar mutumin ma da baya k'aunarki baisan darajarkiba toh miye amfanin zama da shi hak'urin dai zakiyi Allah yamusanya miki da mafi alkhairi.

Sumayya ganin mahaifiyarta kamar itama tana nema takware mata baya dan haka tamik'e tawuce tashige room d'inta tana kuka.

________________

Yarima koda yafarka baccin da suka koma bayan sallar asuba kallon agogo yayi ganin har 11 ta yi yasa yajanye zarah daga jikinsa, zaune yayi yana k'arema fuskarta kallo cike da sonta dan yanzu ya tabbatar ma kansa yana son zarah, janye gashin da yasafko wajen idonta yayi nan yaduk'a yakai mata peck a goshi, ahankali zarah take bud'e idanunta nan tasafkesu akan fuskar yarima, murmushi tasakar masa tare da rik'o hannunsa d'aya.

Shima murmushin yamaida mata yace baby kin tashi? Mik'a zarah tayi tace jikina ciwo yakemin, jan d'an k'aramin bakinta yarima yayi yace toh muje inmiki wanka.

Turo baki zarah tayi tace saidai kad'aukeni dan ban iya tashi.

Hmm shikenan yadda kikeso haka za'ayi ai nasan nine nagajiyar da ke d'in,,yafad'i hakan tare da d'aura hannunsa saman cikinta yana shafa.

Ido zarah tazuba ma kyakkyawar fuskarsa bata ko kyaftawa, hura mata ido yarima yayi nan talumshe idanunta cike da jin kunya.

Murmushi yayi tare da d'aura kansa saman k'irjinta yace baby kallon fa?

Zarah batare da ta bud'e idanuntaba tace ni ba kai nake kallo ba,

Bakinsa yakai yad'an ciji le6enta har saida tad'anyi k'ara sannan yace toh wa kike kallo.

Rik'e le6enta tayi kamar zatayi kuka Sannan tace ni mijina na kallah ko laifine dan na kallesa?

Batare da ya bata amsaba yad'auketa yanufi toilet da ita atare sukayi wanka sannan suka fito suna rungume da juna, tana tsaye gaban dreesing mirror tana kwalliya nan yarima yai mata tsaye yana kallon kwalliyarta kashe mashi ido tayi tace nayi kyau? Ta6e baki yarima yayi yace ko d'aya bakiyi kyauba, Haushine yakama zarah nan ta6ata fuska tace Allah a'a K'unshe dariyarsa yayi yace ammah ai kinsan nafiki kyau ko? Harararsa tayi cikin wasa sannan tace saidai muzo d'aya ammah bakafiniba.

Murmushi yarima yayi tare da rungumota jikinsa yace ban yardaba nan yajanyo wayarsa yai musu selfie.

Zarah zame jikinta tayi tanufi wajen wardrobe nan tad'auko wata gown cikin kayan da yarima yasiyo mata tasaka nan tanad'e gashinta kamar gammo sannan tayi rolling d'in d'an k'aramin veil d'in kayan nan tayi gwanin kyau, juyowa tayi takalli yarima da yatsareta da ido tace toh yanzu ya kaganni?

Murmushi yayi yace har yanzu dai ina akan bakana, dariya tayi nan tamatso yacigaba da yi musu pic's saida sukayi kusan kala ashirin ganin baida niyar dainawa yasa tajasa suka fito main parlour nan suka tarar da mu'az da matarsa nan suka zauna suka gaisa daganan suka wuce dining gabad'ayansu suna breakfast. Zarah da yarima saidai kallon love suke aika ma junansu mu'az da jamila suna lura da su saidai suyi murmushi ahaka har suka gama breakfast d'in nan suka hau yin hira, yarima kallon mu'az yayi yace abokina inaso insamu gida insiya dan gaskiya ba zan iya cigaba da zama a nan ba saboda da takura muzauna muku nan zamu d'aura muku nauyi nikuma banason hakan indai kana ganin ba matsala toh kasanya min cigiyar gida.

Cike da damuwa Dr mu'az yace ranka yadad'e banta6a tunanin jin haka daga garekaba da kai da kaya ai duk mallakar wuyane, idan har kai ka mance abinda kayimin toh ni ban manceba kuma bana iya mancewa, wlh yarima zan iya sadaukar da duk abinda namallaka a gareka dan ka fiye min komai dan Allah kataimaka kucigaba da zama da mu Indai akwai abinda mukeyi muku wanda bakuso kusanar da mu insha Allahu zamu daina, gyad'a kai jamila tayi tace eh wlh zamu daina dan muna jin dad'in zamanku a tare da mu.

Yarima murmushi yayi yace kar kudamu ba wai saboda wani abu nakeson barin gidanba kawai dai dan kar mushiga hak'inku ne.

Girgiza kai mu'az yayi yace kar Allah yakawo ranar da zanji wani abu game da zamanmu tare nidai ka amince mucigaba da zama wlh munajin dad'in zama tare da ku.

Yarima kallon zarah yayi nan tasakar mashi murmushi, kallonsa yamaida ga mu'az yace shikenan na amince ammah ban d'aukar maka alk'awaliba. Murmushin jin dad'i mu'az da matarsa sukayi nan sukaima yarima godia daganan suka cigaba da hira koda rabin hirar mu'az da matarsa sai zarah ne sukeyi dan shi yarima da ido yake binsu saidai yayi murmushinsa mai tsada.

Sun dad'e suna hirar sannan Dr mu'az da yarima suka tashi suka fita inda zarah da jamila suka shiga kitchen dan suhad'a musu lunch, a tare sukayi komai duk yadda jamila taso zarah tabarta tayi ita kad'ai ammah zarah k'iyawa tayi saida aka gama komai tare da ita sannan suka kai saman dining suka jera daga nan kowa yawuce part d'insa dan yashirya jikinsa.

Koda yarima yadawo Zarah taimaka masa tayi yai wanka yashirya bayan sungama cin abinci part d'insu suka dawo nan tayi d'aid'aya saman cinyarsa tana zuba masa shagwa6a yana biye mata a ranar haka suka kasance takasa tatsare indai ba masallaci yarima zaijeba toh suna manne har dare yayi, taje tahad'o musu coffee a one cup a tare sukasha sannan sukaje sukayi wanka suka kwanta saida sukayi 'yan wasanni batare da sunyi making sex ba sannan sukayi bacci kowa yana jin d'an uwansa sosai a cikin ransa.

*BAYAN SATI 'DAYA*

Dr mu'az ne da yarima zaune a parlour suna hira, kallon yarima yayi yace yauwa prince ina zuwa, d'aga masa kai kawai yarima yayi batare da yayi magana ba nan Dr mu'az yamik'e yanufi part d'insu,

Bayan minti biyu yafito rik'e da wasu files, kujerar da yarima yake zaune yaje yazauna, kallon yarima yayi suka fuskanci juna sannan yace prince dan Allah wani taimako ne nakeso kayi min.

Kallonsa yarima yayi yace ina jinka Indai baifi k'arfinaba toh insha Allahu zanyi maka.

Murmushi Dr mu'az yayi yace tabbas baifi k'arfinkaba, nan yafiddo files d'in yamik'a ma yarima yace gashi ammah kayi hak'uri da karambanin da nayi maka muna buk'atarkane a hospital d'inmu.

Yarima dubawa yayi yaga upper ce ta aiki aka basa har da babban matsayi an nad'asa head of department d'in surgeon.

Girgiza kai yarima yayi yace gaskiya kayi hak'uri ba zan iyaba kaima sanin kankane ina da hospital d'ina.

Marairaicewa Dr mu'az yayi yace nasan da haka ammah dan Allah kataimaka ka amince ko yayane kasa albarka a cikin aikin nan kar kak'i amincewa dan muna buk'atar babban surgeon kamarka.

yarima shuru yayi kamar yana nazari sannan yace shikenan zanyi tunani akai.

Cikin jin dad'i Dr mu'az yace Allah yasa inji alkhairi.

Bayan yarima yadawo part d'insu kwance yake saman 3 seater ya yi matashin kai da hannuwansa kansa yana kallon ceiling,

Fitowar zarah kenan daga bedroom rik'e da apple tana ci, tsaye tayi tana kallon yarima da kwata-kwata batama san lokacin da yashigoba dan duk atunaninta bai dawoba.

Takowa tayi ta iso inda yake janye kansa tayi tazauna sannan tamaida kan nasa saman cinyarta, yarima lumshe idanunsa yayi.

shafa sumar kansa tayi tace ashe ka dawo ban saniba.

Murmushi yarima yayi yace uhm ban dad'e da dawowaba, duk'o da kanta tayi takaimashi peck a saman idonsa da yake lumshe, ahankali yabud'e idanunsa nan suka sakar ma juna murmushi, d'age rigarta yayi yayi kissing d'in cikinta sannan yace ina fatana kuna lafiya keda babyna.

Cike da tsokana zarah tace lafiya lou muke prince saidai missing d'inka da mukeyi.

Shafa cikinta yashiga yi yace nima nayi missing d'inku sosai yanzu muje ciki inga in dagaske kunyi missing d'ina.

Dariya zarah tayi tace nak'i wayon naka babu inda zanje.

Mik'ewa yarima yayi yad'auketa yanufi bedroom da ita tana wuntsila k'afa bai direta a ko'inaba sai saman gado, zarah shirin safka take nan yarima yarik'ota yace toh sarkin tsoro ni ba abinda zanyi miki magana ce nakeso muyi.

gyara zamanta tayi tafuskacesa tana jira taji abinda zaice mata.

Yarima janye idanunsa yayi daga kallonta yayi shuru har na kusan minti ukku sannan yakwashe yadda sukayi da Dr mu'az yafad'a mata.

Zarah kasa 6oye farin cikinta tayi nan tashiga washe baki, kallonta yarima yayi yace toh ya kike gani?

Cikin jin dad'i tace wlh nima na goyi bayan hakan kaga kaima zaka ji dad'i kuma taimakone Allah zai baka lada dan irin wannan aikin naku duk abinda za'a ba mutum baza'a ta6a biyansaba ladarku tana wajen Allah.

Murmushi yarima yayi yace hakane shikenan tunda kin amince toh nima na amince.

cikin jin dad'i tarungumesa tace nagode sosai my soulmate Allah yabarmin kai ni kad'ai.

Dariya yarima yayi yace toh Allah yasa,

'Dago kai zarah tayi takallesa tace ashe ka iya dariya haka gaskiya tana yi maka kyau saidai kai bakacika yin dariyaba murmushinma kafin kayi sai ansha wuya.

Jan hancinta yarima yayi yace yau kuma tsokanata akeji?

Murmushi zarah tayi tace ba tsokana bace gaskiya ce nafad'a dan ranar da nafara ganinka lokacin da kukazo islamiyarmu ranar da muke walima saida nakusan rikicewa dan ka burgeni sosai saidai a lokacin fuskarka a d'aure take.

Murmushi yarima yayi yace kedai kin cika tsokana nidai yanzu tashi muje muyi wanka mukwanta dan ni yau agajiye nake ga bacci da nakeji.

Mik'ewa zarah tayi tace angama ranka yadad'e, nan suka cire kayansu sukaje sukayi wanka bayan sun fito shiryawa sukayi cikin kayan baccinsu sannan sukabi lafiyar gado suka kwanta.

Wanshe kare koda yarima yaje ma mu'az da batun amincewarsa sosai mu'az yai murna,

bayan kwana biyu yarima motarsa yasiya maikyau da tsada sannan yafara zuwa wajen aikin.

Sosai ma'aikatan asibitin suke girmamasa musamman ma da sukasan matsayinsa da kuma matakin karatunsa, kamar dai yadda yake baya shiga harkar kowa toh nan ma haka hidimar gabansa kawai yakeyi.

Sosai sukejin dad'in aiki da shi musamman ma da sukaga k'wararrene sosai a 6angaren theatre.

Bayan kwana biyu Zarah kwance take saman gadonsu tunanin 'yan gidansu kawai take dan tasan dole sai sun nemi wayarta, tana cikin tunanin batasan lokacin da yarima yashigoba saidai jin mutum tayi gefenta, murmushi tasakar masa tare da cewa sannu da zuwa ashe ka dawo.

Shima murmushin yayi sannan yace ai daman bazakiji dawowataba tunda kin tsunduma kogon tunani wai ma tunanin me kikeyi haka?

Ajiyar zuciya Zarah tasafke sannan tace tunanin su mama nake nasan zasuyita neman layina bazasu samuba,,,tak'arashe maganar kamar zatayi kuka,

Yarima kallonta yayi yace kar kidamu ai sunsan dai kina cikin k'oshin lafiya zan kira miki su wani lokacin kugaisa.

'Daga kai Zarah tayi cike da gamsuwa da maganar yarima, jikinta yarima yakwanta tare da tura hannuwansa cikin rigarta yana cakud'ata Ganin yana shirin nemanta yasa tazame jikinta takoma parlour dan yanzu gabad'aya ji take batason yarima yana kusantarta saboda sai takwana jikinta yana ciwo ga yawan amai da tashin zuciya musamman yanzu da cikinta yafara yi mata nauyi, ammah indai wassani zaiyi da ita bata damuwa saidai tasan halin gogan nata dawuya ya iya tsayawa iya romancing. Ganin ta gudu yasa yarima yashareta yai kwanciyarsa dan ya lura kwana biyu haka take masa Indai zai nemeta toh sai tasan hanyar da tabi takubce masa.

_Comment_ *nd* _Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_[5/3, 9:51 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Aunty Aliyah Sharif bazan iya mancewa da ke ba akodayaushe kina raina dan haka kimatso kusa yau page nakine big Aunty, sai wanda kikaso zai karanta, jinjinar bangirma agareki 😍_

6⃣1⃣

Sumayya tunda takwana biyu ganin dagaske aurenta ya mutu gashi bata ganin yarima yasa tahak'ura tasaki ranta, ahaka akaje aka kwashe kayanta a part d'inta sannan aka rufe gabad'aya 6angaren yarima aka kaima memartaba key d'in.

Sumayya kwance take saman gadonta sai a ranar tajanyo wayarta takunna dan rabonta da ita tun ranar da aurenta yamutu, number d'in yarima tayi dialing da mamakinta taji bata shiga, dan haka talalubo ta zinat nan tafara ringing har ta tsinke ammah batayi picking ba, nan ma sumayya tak'ara kira saida tayi mata 3 missed call ammah bata d'aukaba dan haka tatura mata message dan daman tasan mawuyacine zinat tayi picking d'in wayar.

Bayan kamar minti biyar sai sumayya tak'ara kira da mamakinta saiga zinat tayi picking, cike da jin dad'i sumayya tagyara kwanciyarta tare da cewa Hi baby.

Daga chan 6angaren zinat a tsorace tace sumayya ya dai?

Murmushi sumayya tayi tace ke fa tsiyata da ke kin cika tsoro toh kisaki jikinki komai ya wuce.

Uhm sumayya kenan taya zan saki jikina bayan d'an banzan dukan da wannan mugun yayimin ke yanzu dai ya maganar aurenki?

Murmushi sumayya tayi tace hmm kibarsa kawai ai yanzu aurena da yarima ya k'are wlh ban ta6a tunanin zaimin wannan cin mutuncinba haka koda nasan inason yarima ammah babu yadda zanyi dole inciresa a raina tunda ko giyar wake nasha aurenmu bazai ta6a komawaba.

Zinat cikin ranta murna fal ji take kamar tazuba ruwa k'asa tasha saboda murnar auren sumayya ya mutu, a fili 6oye murnarta tayi tace Allah sarki baby ba haka nasoba toh yanzu ya su memartaba sukayi da sukaji labarin rabuwarku Allah dai yasa basuji abinda mukayi ba.

Dariya sumayya tayi tace kefa tsiyata da ke kin iya tsoro, daman fa nasan miskilancin yarima bazai ta6a barinsa yafad'aba kuma koma ba hakaba nasan yarima bazai iya tonamin asiriba saboda bayason tashin hankali, nikuma gudun kar ma yatona min yasa nayi sauri narigashi kai k'ara......nan takwashe duk abinda yawakana talabarta ma zinat.

Ajiyar zuciya zinat tayi tace gaskiya kinyi namijin k'ok'ari toh yanzu yarima shikenan ya bar gida bazai dawoba?

Hmm ba zai ta6a dawowaba, ni wlh kin ban mamaki da kika iya tafiya kikabarni ban ta6a tunanin hakaba daga gareki zinat.

Kwantar da murya zinat tayi tace kiyi hak'uri baby wlh gabad'aya rikicewa nayi ammah insha Allahu wani lokacin zan shigo.

Cikin jin dad'i sumayya tace gaskiya da naji dad'i dan gabad'aya kad'aici ya isheni Allah yakawo min ke lafiya.

Ameen baby zankiraki anjima. Ohk, sai kin kira,,nan sukayi sallama.

Tun daga ranar sumayya da zinat suka koma suka d'inke kullum suna manne da juna ta waya inba wayaba toh ta chart da video call, yanzu sumayya kusan kullum tana d'akinta suna waya da zinat.

Sultana sadiya ganin yanzu hankalin d'iyarta ya kwanta yasa itama tad'an kwantar da hankalinta ammah magana bata had'asu da ummin yarima dan da taga ummi zata fara d'aure fuska koda ummi tayi mata magana indai sukad'aine shareta takeyi inkuma gaban su dadane toh shine take amsa mata ciki-ciki. Ummi tun abin yana bata mamaki ganin ba ita tayimataba ammah da ita take gaba, daga k'arshe abun yadaina damunta.

Dada da memartaba ma danne damuwarsu kawai suke akan tafiyar yarima ammah su ma suna jin abun yana damunsu cikin rai, daga inda suka tuna da abinda yayi ma 'yar jikarsu sai kuma suji ba dad'i, dan haka ne suke nuna ma sumayya kulawa sosai ga tausayinta da sukeji saboda akanta akafara sakin aure a masarautarsu.

_________________

Zarah ganin yarima kwana biyu bai nemetaba dan yanzu har romance ya dainayi mata saidai kawai yarungumeta suyi bacci, nan abun yad'an fara damunta.

Yau ma tana fitowa daga wanka ganinsa tayi a kwance yana duba wata newspaper dan haka taje tafad'a jikinsa, kallonta yarima yayi yace Zarah sai kin ji ma babyna ciwo?

Turo baki tayi cikin shagwa6a tace au ba ma ni zanji ciwon ba babynka zanji mawa ko? babyn da yanzu andaina kulamu.

Aje newspaper d'in da take hannunsa yayi yace wajen me nadaina kulaki?

Kwantar da kanta tayi a k'irjinsa tace toh ba kai bane kadaina min komai?

Yarima ya fahimci inda tadosa ammah yanuna bai fahimtaba yace magana nadaina yi miki ko kulawa?

Girgiza kai Zarah tayi cikin jin kunya tace ka daina making sex da ni.

Murmushi yarima yayi yace toh ai naga kamar bakiso saisa nabarki kihuta.

Zaro ido Zarah tayi tace karufa min asiri taya zan k'i son lada, kawai dai babynka ne yake wahalar da ni, dan dadyn nasa jarumi ne,,,tak'arashe maganar tare da kashe masa ido d'aya.

Murmushi yarima yayi yace kar kidamu nima banason babyna yana wahalar min da ke kihuta warki kawai nayi miki uzuri.

Da mamakinsa sai yaga Zarah ta fashe masa da kuka. Cike da mamaki yace lafiya zarah? Me kikeyi ma kuka? Cikin kuka tace toh bakai bane.

Murmushi yayi yace toh kinaso inyi?

Cikin sauri tad'aga kai.

Toh shikenan kidaina kuka, nan yakwantar da ita yashiga lashe mata hawayen fuskarta daga nan yalalubo bakinta yacigaba da tsotsa kamar wanda yasamu lolli pop, gabad'ayansu jikinsu rawa yake dan sunyi missing d'in juna sosai, daga nan yarima yazare towel d'in da yake jikinta yagangaro da kansa a k'irjinta, ahankali yacigaba da lalla6ata har saida yaga sun samu nutsuwa sannan yabarta.

Duk da lalla6ata da yayi ammah saida jikin zarah yai ciwo dan daurewa kawai take, ko shi kansa yana lura da yadda take cize le6e.

Cike da tausayinta yashiga yi mata sannu daga k'arshe yad'auketa sukaje yaimata wanka shima yayi nasa sannan suka fito hatta kaya shi yasaka mata, jin jikinta ya d'au zafi yasa yad'auko drugs yabata sannan yad'auketa suka dawo parlour nan yakwantar da ita saman cinyarsa yana wasa da gashin kanta ahaka bacci yai awon gaba da ita.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull