Kenza eBookz

Yarima suhail complete Novel - Chapter 42

Yarima suhail complete Novel - Chapter 42

Yarima suhail complete Novel Chapter 42: Yarima suhail complete Novel Chapter 42. Girgiza kai Zarah tashiga yi cikin sheshek'ar kuka tace ummi kidaina cewa…

3,366 words

Girgiza kai Zarah tashiga yi cikin sheshek'ar kuka tace ummi kidaina cewa haka *K'ADDARA CE* kawai taja hakan kuma har ga Allah ban ta6a tunanin kun cutar da ni ba koda sau d'aya, saidai abu d'aya nake tunanin kunyi min shine kun sama ma rayuwata farin ciki, baku k'yamaceniba a matsayina na talakka kun had'ani aure da d'anku, taya zan yi wani tunani nadaban akanku? Wlh ummi ku masoyanane nagaskiya ku iyayene agareni dan dani da 'ya'yanku duk d'aya kukad'aukeni, K'ara fashewa da kuka Zarah tayi tace ummi wlh kun gama min komai a rayuwata tsakanina da ku saidai addu'a dan banda abinda zan biyaku.

Ummi Murmushin jin dad'i tayi tare da goge hawayen fuskarta sannan tace Allah yaimuku albarka Zarah, Allah yasafkeki lafiya mucigaba da addu'a insha Allahu memartaba zai safko daga fushin da yake kudawo gida.

Murmushi zarah tayi tace Allah yasa ummi, Yarima zare wayar yayi daga kunnenta tare da switching off d'inta gabad'aya.

Zarah da mamaki take kallonsa da ya aje wayar tare da komawa yakwanta yamaida idanunsa yalumshe, saman k'irjinsa takwanta ahankali cikin muryar lallashi tace kayi hak'uri insha Allahu komai zaizo k'arshe.

'Dan guntun murmushi yarima yayi sannan yace niko zama na nan ya fi min dad'i koda sau d'aya bana tunanin komawa gidanmu, nidai burina iyayena susami kwanciyar hankali.

Da ido take binsa har yakai aya sannan tace kadaina cewa haka yarima koma me akayi maka yakamata ace ka hak'ura domin 'yan uwa dabansuke ba a iya canzasu, cikin dangine zakashiga kai rayuwarka kaji dad'i.

Murmushi yarima yayi yace naji yanzu dai aji da ni sarkin surutu.

Zaro ido zarah tayi tace anya zan iya? Kaga fa yanzu nayi nauyi.

Kar kidamu baby zaki iya nima ai ahankali zan miki dan banason wannan rakin naki.

shagwa6e fuska tayi kamar zatayi kuka tace au nice ma sarkin raki?

Dariya yayi sannan yace toh ai haka kike,

Uhm naji ai kaine baka tausayina.

Yarima yace au haka kikace? Toh shikenan bari kigani.

Zaro ido zarah tayi tace dan Allah kayi hak'uri da wasa fa nake.

Shareta yarima yayi nan yakwantar da ita, ganin tayi rau-rau da ido yasa yai murmushi tare da komawa gefenta yakwanta, kansa yana kallon ceiling.

Kallonsa zarah tayi ganin baida niyar yi mata komai yasa tace toh ka fasa?

Juyowa yayi yakalleta yana murmushi yace sarkin tsoro ni ba abinda zan miki daman.

Dukan wasa zarah takaimasa tace kai ko? Dariya yayi yace ya na iya tunda Allah ya had'ani da matsoraciyar mata.

Uhm kaima kasan ni jaruma ce.

Nidai bansan komai ba ammah bari inyi just na 5 hours tanan zan d'an gane jarumtarki.

Zaro ido zarah tayi tace karufamin asiri ai sai inmutu.

Kumatunta yaja yace ba zaki mutuba dear, maida kanta tayi saman k'irjinsa tace Allah yasa ina da rabon rayuwar, Yanzu in namutu shikenan aurenka zaka sake kamance da ni,,,tak'arashe maganar kamar zatayi kuka.

Rungumeta yayi yana ji kamar ta soka masa mashi a mak'oshi da ta ambaci mutuwar, ahankali yace zarah kidaina cewa haka dan ni bana tunanin zan iya son wata bayan ki, ban ta6a son wataba sai ke.

'Dago kai tayi takallesa tace har sumayya?

Yarima ji yayi wani irin takaici da tsanar sumayya sun dabaibayesa musamman ma da yatuna halin da yasameta ita da k'awarta,,,cike da takaici yagirgiza kai yace sumayya auren had'ine akayi mana, Zuba mai ido zarah tayi tace toh kai bakada za6in kanka mu dukanmu baka akayi?

Cike da k'osawa da tambayoyinta yajanyeta daga jikinsa yamik'e yace baby kin cika tambaya har kinsa kaina ya fara ciwo yanzu dai bari inje ind'anyi wani research a system,,yana fad'in haka yaje yad'auki system d'insa yakoma parlour.

Zarah da kallo tabisa cike da so da k'auna har yaficce, sannan tayi murmushi tare da janyo pillow tarungume a k'irjinta.

______________ Ummi bayan yarima ya kashe wayar ajiyar zuciya tayi dan har cikin ranta taji dad'i da taji d'anta yana cikin k'oshin lafiya kuma ta ji hankalinta ya kwanta, a ranar saida kowa yasan tana cikin farin ciki dan rabon da aganta a yanayin tun ran da yarima yabar gidan.

A 6angaren sumayya ko hidimarta kawai take koda tanajin ba dad'i akan mutuwar aurenta ammah zinat tuni ta fara mantar da ita damuwarta dan basuyin ko 2 hours batare da sunyi wayaba nan wata shak'uwa tak'ara shiga tsakaninsu, da ace za"a duba wayarta a lokacin blue films da pic's ne kawai cikinta da ta zauna part d'inta batada aiki sai kallo sai waya, wulak'anci ko k'aruwa yayi dan ma'aikatansu har ji suke daman bata dawoba dan gabad'aya indai zata fito toh sai ta hanasu kwanciyar hankali.

Sultana sadiya ganin hankalin sumayya ya kwanta yasa itama taji dad'i a ranta, hatta shi kansa sultan abbas koda ya nuna fushi yake da ita saida taje tasamu tabasa hak'uri sannan tasamu sauk'in mahaifin nata.

Yau ma kamar kullum kwance take tayi d'aid'ai a saman gadonta tana waya da zinat, inkaganta sai karantse da namiji take waya dan shagwa6a kawai take zuba mata akan tazo taimata ko sati guda ne.

Zinat tace anya baby kina ganin ba matsala ni fa ina tsoron abinda yafaru da farko yak'ara faruwa dan kinga wanchan mijin naki har tabbai yabarmin a jiki.

Ta6e baki sumayya tayi tace ke kema tunawa da shi ai wlh tunda yasakeni toh sai nayi silar rabasa da wannan tsinannar matar tasa.

Dariya zinat tayi tace baby har yanzu dai kina akan bakanki, yanzu dai kisaurareni end of this week zaki ganni.

Wani irin k'ara sumayya tayi tace dagaske kike ko wasa?

Dariya zinat tacigaba da yi, sai chan tad'an tsagaita dariyar tace kai baby zaki ciremin kunne, zan shigo man ammah anya ba a hotel zan safkaba, saboda ni a yanzu gidanku yafi k'arfina.

Cike da Jin dad'i sumayya tace bawani fin k'arfi, dan Allah kizo kawai wlh babu matsala kinsan ba za'a barni indinga fitaba a yanzu.

Ajiyar zuciya tasafke tace toh shikenan baby sai na shigon.

Jibi kenan ko? Cewar sumayya.

Kai kedai kin cika hanzari zan dai gani idan jibin. Chab wlh baki isaba tunda dai kika furta toh dole kizo ranar dan ba kad'an nayi missing d'inkiba.

Toh shikenan dear yadda kikeso haka za'ayi. Nan sukacigaba da hirarsu sunfi 1 hour sannan daga baya sukayi sallama kowa yakashe wayarsa,

Memartaba tun bayan tafiyar yarima shi kansa ji yake duk ba dad'i, indai yana zaune fada kad'an kad'an ya kalli kujerar da yarima yake zama saidai yaga sultan Ahmad ne madadinsa, daurewa kawai yake yana danne zuciyansa dan shi kansa yasan yana kewar yarima ammah daga sa'ilin da yatuno abinda yarima ya aikata masa sai yaji wani irin haushinsa ya cikashi.

Dada ita kanta tana jin ba dad'i akan tafiyar yarima dan abu biyu yahad'e mata ga mutuwar auren sumayya ga tafiyar jikanta, Tausayin sumayya yasa kusan kodayaushe sai ta aika ankira mata ita taji abinda takeso, nan sumayya take ida komawa kalar tausayi tafad'i abinda takeso ko menene nan da nan Dada take sanyawa ayi mata, ciki kuwa harda canza mata mota tasa akayi mata, tana jin tausayinta sosai saboda akanta aka fara jawarci a masarautar tasu.

Shaheed ma ba k'aramin girgiza yayiba da yaji labarin tafiyar yarima, duk inda yake tunani yarima ya sani toh ya je babushi babu alamunsa.

_*Bayan Kwana Biyu*_ Sumayya ce zaune a parlour suna hira da ummanta cike da jin dad'i sunyi nisa da hirarsu sultana sadiya takalli d'iyartata cike da k'auna tace sumayya idan kika gama iddah kinga sai kisamu wanda kike gani yana da dama-dama ki aura.

6ata fuska sumayya tayi tace haba ummah wane irin aure yanzu ai ni nayi sallama da aure.

Zaro ido sultana sadiya tayi tace kirufa min asiri kinsan dai su memartaba da abbanki bazasu ta6a amincewaba, indai manemanki sukazo kawai kisamu kishige kicire wanchan matsiyacin a ranki.

Yamutsa fuska sumayya tayi tace ummah har kina tunanin zan iya zama da wani bayan yarima? Ni koda ma an matsamin sai nayi aure toh wlh saidai inyi auren kisan wuta inyaso daga baya infito inkoma wajen mijina dan ni Indai ba yarima ba babu wanda zan iya aure.

Jinjina kai sultana sadiya tayi cike da mamakin furucin d'iyartata tace sumayya anya yarima bai asirce min ke ba? Taya ana ga gabas kekuma kina ga yamma, ubanme suhail yakeda shi da zaki nace masa?

Dariya sumayya tayi tace kai ummah ni wlh kina ban dariya,,,,yauwa na ma mance infad'a miki gobe k'awata zinat zatazo.

Washe baki sultana sadiya tayi tace ayya na gane, wai ya business d'in naku yana dai tafiya daidai ko?

Yatsina fuska sumayya tayi tace eh toh dan tana turo min kud'i sosai, gobe ma zatazo min da wata sark'an gold da nasa tasiyo min cikin kud'in.

Cikin jin dad'i sultana sadiya tace angaisheki d'iyar albarka, kina jan kud'i, kai gaskiya naji dad'i Allah yakaimu goben, Allah yakawota lafiya.

Ameen ummana, nan sumayya tacigaba da bata labari akan business d'insu.

Wanshe kare sumayya shirye-shirye tayi sosai na tarbar zinat, girki ko anyi yakai kala goma, ummah dai binta take da kallo dan ko ba'a fad'a mataba tasan zinat tana da muhimmanci sosai a wajen sumayya, tun daga kan yanayin hirararta da take yawan yi mata sannan kuma batada k'awar da takema rawar kai kamar zinat dan haka take kallon shak'uwace sukayi sosai tunda tun a school suke tare.

Sumayya taso abarta taje da kanta tatarbo zinat ammah ummah tace ba ruwanta taje tasami abbanta tatambayesa, kan dole tahak'ura dan tasan bazai ta6a barintaba dan haka tatura driver d'insu yaje yad'aukota.

Koda ta iso sumayya tayi mamaki sosai ganin shigar da zinat tayi dan shigace ta mutunci ba kamar wadda takeyiba in zatazo, haka takaita wajen sultana sadiya cikin mutunci suka gaisa idan kaga yadda zinat tagaishe da sultana sadiya sai karantse ga Allah cewa d'iyar mutunci ce.

Bayan sungama gaisawa sumayya janta tayi zuwa part d'inta, suna shiga dariya sumayya tashiga yi tace kai baby wannan shiga da kikayi sai mutum yarantse cewa musulmace kamila, yau kece da babban veil.

Hmm kedai bari baby nima jina nake wata iri ke dakyar na iya tako gidannan dan gani nake kamar zamu had'u da wannan mugun.

Ta6e baki sumayya tayi tace wannan ai tuni yai nisan kiwo dan soyayya tarufe masa ido ya za6i matarsa yabar iyayensa, inma asiri waccan makirar tayi masa to sudai sukasani.

Ke ni naji dad'in tafiyarsa dan yanzu zamu wala zamuci karenmu babu babbaka.

Haka dai kikace baby ammah nifa banso aurena yamutuba dan inason mijina.

Ta6e baki zinat tayi tace ni da bakyaso ko?

Kirufan asiri kema ai shedace kinsan ina sonki sosai baby da ace ban sonki da bazan kulakiba,,,cewar sumayya.

Ammah ai kinfi sonsa,,, Dariya sumayya tayi tace zinat kenan ba bayaba wajen kishi, ni banfi sonsaba kowa da matsayinsa a wajena yanzu dai muje kiyi wanka kici abinci.

Ohk ma. nan suka sakarma juna murmushi sannan sukawuce sumayya tataimaka mata tayi wanka sannan suka je tayi lunch bayan tagama suka zauna hira daga nan suka haye saman network.

Haka zinat tacigaba da zama gidansu sumayya kullum suna manne da juna, sultana sadiya har mamaki take yadda yanzu sumayya ko firar da take fitowa suyi ta daina kullum suna k'unshe cikin bedroom,,,nan tai mata uzuri ta d'auka duk saboda jin dad'in zuwan k'awarne dan ankwana biyu ba a had'uba kuma ko bakomai yanzu taga d'iyarta tana cikin farin ciki dan rabonta da taganta cikin yanayin tun tana tare da mijinta.

_Comment_ *nd* _Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_ [5/3, 9:52 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 6⃣3⃣

Yarima tsaye yake gaban dressing mirror yana shiryawa inda zarah take zaune chan saman gado rungume da pillow ta zuba masa ido tana kallonsa.

Yana gama shirinsa juyowa yayi yakalleta tare da sakar mata murmushi yace ya dai baby?

Murmushin itama tayi tace ina kallon yadda handsome man yayi kyau nidai fatana kar aimin kwacensa.

Har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.

Ganin haka yasa itama taja bakinta tayi shuru, nan yazo yad'auki key d'in motarsa da waya.

Rik'o hannunsa zarah tayi tare da marairaicewa tace please kakulanmin da kanka.

Zuba mata ido yarima yayi chan sai yajanye kallonsa daga fuskarta zuwa kan cikinta d'an kuntun murmushi yayi sannan yace nima kikular min da babyna.

Zarah sakin hannunsa tayi tare da d'aga masa kai, kallon fuskarta yayi yace sai nadawo.

Ahankali tace adawo lafiya. Nan yajuya yafita yabarta nan zaune, shafa cikinta tayi sannan takoma takwanta tana mamakin halin yarima yadda cikin lokaci guda idan miskilancinsa yamotsa ko ita kanta bai saurara mata.

koda yaje hospital bayan ya gama round ya duba patients d'insa da suke ward, office d'insa yakoma nan yajanyo system d'insa yacigaba da research kasancewar kusan abinda yake kenan indai yazauna shikad'ai dan yasamu sauk'in yawan tunane-tunanen da yake.

Knocking d'in da akayine yasa yabada izini ashigo, ahankali taturo k'ofan tashigo tare da yin sallama.

Jin muryar mace yasa yarima yad'ago kai yasafkesu akan wata kyakkyawar yarinya wadda bazata gaza 25yrs ba sanye take cikin lace ta d'aura labcut daga sama sannan tayi rolling da veil kalan kayan, janye idanunsa yayi daga kallonta yamaida kan system d'in tare da d'aure fuska.

Bata damu da yadda yad'aureba tatako ahankali tazauna kujerar da take opposite d'insa, cikin kwantar da murya tace sannu da hutawa doctor.

Yarima batare da ya kalletaba yace meyakawoki office d'ina?

Batayi mamakin yadda yayi mataba dan daman tasan halinsane saidai ba yadda ta iya dole tafurta masa sirrin da yake cikin zuciyanta.

Murmushi tayi tace sorry doctor yanzu zan fad'amaka dalilin zuwana dafarko dai am Dr leemah ni staff ce a hospital d'innan dan nasan baka sanniba.

A gaskiya kana burgeni sosai yanayin yadda kake tafiyar da rayuwarka kuma naga kamar baka shiga harkar kowa komai naka da kakeyi me ajine saisa kake burgeni dan Allah idan ka amince inaso muk'ulla friendship.

'Dago kai yarima yayi yawurga mata wata irin harara har saida Dr leemah tatsorata ammah tadake dan a yadda takejinsa a ranta bata damu da duk abinda zaiyi mataba.

Ganin baida niyar yin magana yasa Dr leemah tacigaba da cewa kar kadamu indai zaka amincemin duk abinda kakeso zanyi maka koma menene,,,

Janye system d'in gabansa yayi tare da kallonta kamar ba zaiyi maganaba sai da yayi kusan 3 minutes sannan yace kin gama?.

Fari tayi masa da ido sannan tace eh my dear.

K'ara d'aure fuskarsa yayi tamau sannan yace ni anfad'a miki irin wad'annan banzayen mazan ne?

Ammah ai taimaka ma juna zamuyi ni kawai burina inga ka amince muna friendship koda ace bakasoniba nasan wata rana zaka soni.

Hanya yarima yagwada mata cikin tsawa yace get out of my office! kokuma yanzu in 6ata miki rai.

Ganin ba alamun wasa a tare da shi ga wani irin k'warjini da yayi mata, cikin sauri tamik'e tafita tabar office d'in tana mamakin halin yarima.

Bayan ta fita dafe kansa yayi saboda 'yar hayaniyar da yayi har yaji kansa ya fara ciwo, mamaki yake yadda daga fara aikinsa zuwa yanzu matan da sukazo daga different departments suka kawo masa kansu sunkai goma, tsaki yaja cike da jin haushi daga k'arshe tashi yayi yatattare komai yad'auki key d'insa yaficce, saida yafara zuwa masallaci yayi sallar azuhur sannan yawuce gida.

Lokacin da ya isa zarah tana zaune a parlournsu tana kallon wani indian series film, gabad'aya tamaida hankalinta a kallon dan tunda tayi wanka tayi sallah tazauna kallon hannunta apple ne take ci.

Sallamar da yarima yayine yasa tajuyo takallesa cike da mamakin ganin ya dawo ukku batayiba murmushi tasakar masa tare da cewa sannu da zuwa.

Yauwa kawai yace batare da ya bi ta kantaba yawuce yashige bedroom.

Mamakine ya ida kamata ganin yadda daga jiya zuwa yau duk ya canza mata, mik'ewa tayi dakyar tanufi bedroom d'in tana shiga lokacin yarima yana cire kayansa.

Takawa tayi ta isa inda yake, murmushi yarima yasakar mata yace ya dai?

Ajiyar zuciya zarah tasafke tace na d'auka laifi nayi maka.

Kallonta yarima yayi yace mekika gani? Langwa6e kai zarah tayi tace toh ai naga duk ka canzamin.

Murmushi yayi tare da shafa fuskarta yace kar kidamu baby babu abinda kikayi min ai ke bakya laifi, yanzu dai bari inje inyi wanka kije kijirani kinji?

'Daga kai zarah tayi tare da sakar masa murmushi.

Yauwa baby, yarima yace sannan yawuce yashiga toilet.

Zarah zuwa tayi tafiddo masa kayan da zaisa sannan tazauna tana jiransa yafito.

Koda yafito ita tataimaka masa yashirya sannan suka fito, ita taje tad'ebo musu abinci takawo musu nan yarima yana ci yana lalla6ata itama tana ci, Bayan sun gama zarah tagumi tazuba tana kallon yarima cike da son mijin nata.

Janye mata tagumin yayi yace kallon fa?

Duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya.

janyota yayi jikinsa yakwantar da ita saman cinyarsa tare da zame mata kallabinta yana shafar gashin kanta.

'Dago kai tayi takallesa tana murmushi tace my heartbeat akodayaushe naganmu a tare wani irin farin ciki nakeji a raina, ina k'ara godema Allah da ya mallakamin kai a matsayin miji abun sona.

Murmushi yayi sannan yace zarah banta6a tunanin zan iya son wataba a yanzu dan ko kusa bansa ma raina yin soyayya ba ammah a lokaci guda kinchanza min ra'ayina sai gashi Allah ya dasamin sonki a raina, a yanzu na gama yadda da cewa kece macen da nafara so a rayuwata ina fata Allah yabarmu tare dan kincika macen kirki tabbas su ummi gata sukayi min da suka za6amin ke a matsayin mata.

Tashi zarah tayi zaune tafuskancesa tana murmushi tace nafi kowa farin ciki dan gani nake kamar nafi kowace mace sa'ar miji dan komai na mijina daban yake.

jan hancinta yayi yace kedai kin iya tsokana na lura da ke.

shagwa6e fuska tayi kamar zatayi kuka tace ni fa gaskiya nafad'a dan mijin nawa komai nasa maitsada ne sauk'inma da yanzu nad'an samu sauk'in miskilancinsa,,,tak'arashe maganar tare da kashe masa ido d'aya.

Matsota yayi a jikinsa tare da tura hannuwansa cikin rigarta yace zarah nagama amincewa da ke a rayuwata sannan kuma d'an zaman da mukayi da ke a yanzu nima ina mamakin yadda gabad'aya nafara canzawa, girgiza kai yayi sannan yace bansaniba ko dan na baro gidanmu, murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace nima kaina ina mamakin hakan.

Zarah fad'awa tayi jikinsa cike da tausayinsa da k'aunarsa tace my heartbeat kakwantar da hankalinka insha Allahu zaka koma cikin family d'inka dan nima ina buk'atar inganka cikinsu.

Yarima batare da ya bata amsaba yalalubo bakinta yakaimata zazzafan kiss sannan yakwantar da kansa saman cinyarta tare da maida idanunsa yalumshe.

Zarah ajiyar zuciya tasafke nan tacigaba da wasa da gashin kansa batare da ta k'ara maganaba dan hakan kawai da yarima yayi ya sa tagane bayason maganar.

______________

Yau ma kamar kullum sumayya da zinat manne suke da juna suna hirarsu dan a 'yan kwanakin da zinat tayi saida tasan yadda tayi tasa sumayya tafara cire yarima a ranta, suna cikin hirar zinat kallon sumayya tayi tace baby inaso kirakani kasuwa daga chan muje gidan wannan friend d'in tawa khausar saboda jibi nakeso inwuce yola.

Shuru sumayya tayi kamar ba zatayi maganaba sai kuma chan tace baby kina ganin za'a barni infita? Kinsan halin abbana ba zai aminceba.

Ta6e baki zinat tayi tace ni fa tsiyata da ke kin cika tsoro fitar da zamu d'anyi kawai mudawo, kuma ai ko a 6oyene sai kifita batare da ya saniba kifad'ama ummah kawai dan gaskiya dole muyi tafiyarnan a tare inkuma ba hakaba ban k'ara zuwa gidannan idan natafi.

Zaro ido sumayya tayi tace baby meyayi zafi haka, indai hakane toh na amince muje ammah gaskiya sai zuwa gobe saboda su abbah yanzu suna nan fada, zansan yadda zanyi inlalla6i ummah ta amince, ammah kikace zaki daina zuwa wajena ai bansan yadda zanyi da rayuwataba da mi zanji da mutuwar aurena ko da rabuwarki da ni?

Rungumota zinat tayi tace kiyi hak'uri baby kema kinsan bana iya rabuwa da ke, Murmushin jin dad'i sumayya tayi tace nagode sosai baby Allah yabarmin ke.

Ameen babyna, cewar zinat.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull