Kenza eBookz

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 15

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 15

Zaki complete by khadeeja candy Chapter 15: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 15. Ya fadi hakan yana nuna ni sannan ya juya a fice cikin yanayin da…

4,425 words

Ya fadi hakan yana nuna ni sannan ya juya a fice cikin yanayin da ke nuna yayi fushi da ni. A ganina be kamata na fadi abunda zai iya zame min matsala, nasan idan har na fada masa dalilin kukan nawa wata kila zai iya tambayar mahaifiyarsa dalilin dukana da tai wanda hakan zai iya zama fada a tsakaninsu, idan kuma na fada masa abunda ke tsakanina da Aliyu abu ne da zai iya sakawa a koreni a gidan gaba daya ma, nai biyu babu. Tabarmar na daga na kabe saboda takawan da Aliyu yai sannan na sake shimfiďata na kwanta a kai ina saka hijabina na rufe kafafuna, sai ga Anty Maryam ta shigo garejin fuska a hade hannunta rike da wayar carja.

“Ke uban wa kike wa rashin kunya? Ya Aliyu sa'anki ne?”

Saurin tashi nai zaure a take jikina ya dauki rawa.

“Ban masa rashin kunya ba”

Ban gama rufe bakina ba ta watsar min wayar chajar a jiki iya karfinta, ban san lokacin da nai tsalle na dire ba, rabon da a saka wani abu a dake ni a jiki har na manta, amman yau saboda rashin gata na zo aiki gidan wasu yar gidan tana dukana akan abunda bata san gaskiyarsa ba. Haka ta bi ta bulale min jiki ko ina ta samu dukana take da wayar idan nai ihu ta ce na rufe mata baki. Ta fini girma da jiki sosai domin ita irin manyan yan matan nan ne masu kamar matan aure masu yaya shida, ba kamar Anty Rukaiya dake da karamin jiki ba.

“Kuma idan na ji muryarki a waje sai na ci ubanki”

Ta fada tana nuna ji da wayar da ke hannunta sannan ta fice ta barni a gurin ina ta murzar jiki ina hade kukana, duk inda ta bulalar ta same ni ya yi min ja kamar na jimu abun ka da mai farin fata, farin ma irin nawa mai ja sosai na jajayen buzaye. A gurin na kwanta ina ta hawaye, domin babu danar nai kuka sauti ya fita ta dawo ta kara min kamar yadda ta fada. Ana gaf da sallah magariba zazzabi ya rufe na rika jin sanyi na sauko min ga bulolin nata min zogi, kaina kuma yana ta ciwo har bana son daga idona. Ban iya fita karbar abinci a gurin Mama Fulani da Ammy ba, da yake kuma ba ni da gatan da wani zai da mu ban ci abinci ba babu wanda ya zo dubani ko a aiko min da abincin. Haka na kwana a gurin cikin rashin gata da galihu har gari ya waye, ina ta jin wuyar tashi amman ba ni da gatan da wani zai fanshe ni a aiki, na san ba ma za su yarda da uzurin cewar bana jindadi ba. A dan karamin madubin hoda ta na duba yadda idona da gefen kumatu na ya kumbura bulalar ta kwanta min har saman fatar ido. Wani ruwan hawayen ne ya sake cika min ido na fashe da kuka marar sauti ina ta jin kewar Nana da rayuwata da baya, na sani ba mu cikin jindadi amman a haka muke rayuwarmu babu wanda ya taba dukana, amman a nan ga duka ga wulakanci saboda kawai ina neman halalina. Ganin kamar zan bata lokaci ina kukan yasa dole na tsagaita kukan da ke kara min ciwon kai da damuwa na daura dankwalina na fito ina jin nauyin jikina saboda zazzabin da ke kara sauko min, na nufi part din Mama Fulani kamar yadda na saba, part din na fara gyarawa na ma komai tsaf sannan na nufi part din Ammy na gyara mata falonta, yanayi kawai ta lura da shi ta fahimci bana jindadi.

“Jiya Fulani ta aiko ta ce karna baki abincin dare da safe, wani laifin kika mata hala?”

Kaina kawai na daga na kalleta, ina bude baki nai magana sai kuka ya kubce min na saki tsintsiyar hannuna na durkushe a gurin ina ta kuka. Sai ta zauna a cushion tana ta kallona cike da tausayawa.

“Mamana ki yi hakuri, duk wanda ya ce zai nemi halal dole sai yayi hakuri, musamman aiki a gidajen wasu, dole za ki iya haduwa da abubuwa da dama, ban san dalilin na aiki a nan ba, amman dai ki yi hakuri wata rana sai labari zai zama kamar ba ayi ba kinji”

Na gyada mata kai ina share hawayena.

“Baki da lafiya ne naga kamar fuskanki ya kumbura”

“Kaina yana ciwo, kuma ina jin zazzabi”

“Me mikai wa Fulani hala?”

“Wallahi ban mata komai ba, kawai dai na fita ne bakin gate ina dawowa sai sai ta mare ni, kuma shine Anty Maryam ta dukeni da bulala”

Na karasa ina kara fashewa da kuka. Sai ta girgiza kai cike da tausayawa.

“Fulani bata da imani Wallahi, Allah ya kyauta”

Tashi tai ta nufi upstairs bata dade ba ta dawo rike da kwayoyin magani ta bani.

“Shiga kitchen ki debo ruwa ki sha”

“Na gode Allah ya saka da alheri”

Na fada ina saka hannu biyu na karba sannan na nufi kitchen kofi na dauka na debi ruwan na balle maganin sai na kasa sha, abun ka da wanda be saba ba, daman can magani da allura bana son su sai dole, daker na iya runtse ido na shanye maganin na fito ina ta bata baki, ko da na fito Anty Zee da Humaira, Inteesar da Batulu duk sun fito dakinsu, dan haka na shiga na gyara ko wane dakin da dakin Ammy sannan na fito.

“Idan kin gama ki zo ki karbi abinci, amman karki bari ta sani”

“To”

Na amsa sannan na fito daga part din na koma part din Mama Fulani dan gyara bedrooms idan yayanta sun fito. Ko da na shiga duka yayanta suna dinning har Ya Muhseen, da alama da gaske fushi yake da ni domin ko inda nake be kalla ba, ba kamar yadda ya saba kallona ya sakar min murmushi ba, har na dauko tsintsiyar da mopper na shiga dakunansu na gyara komai na fito cikin rashin dadin rai na ke na fushin da na lura da Ya Muhseen na yi da ni, domin har ga Allah na damu kuma na ji babu dadi. Sai da gama gyara bedrooms din sannan na fito na sauko kasa, a lokacin Ya Muhseen baya dinning din ba kamar yadda na saba ganinsa idan na gama gyara an barshi a gurin zaune ba, wani lokacin ma shi yake miko min abincin na safe. Inda na dauki tsintsiyar na nufa na aje sannan na juyo da zimmar komawa part din Ammy na karbi abincina domin na san wannan Mama Fulanin ba bani za tai ba, sai na ji ta kirani.

“Ke.... ”

Na dawo da sauri na durkusa a gabanta cikin ladabi na ce.

“Ga ni”

“Shiga dakin Rukaiya da Maryam da Baby ki kwaso kayan durowarsu ki je garden ki wanke, ko daya karki bari kuma ki wanke su tas”

Da to na amsa mata na taso ina tausayin kaina na nufi dakunnan na kwaso tulin wankin ko wanne zai kai kala goma sha biyar wani ma ashiri, sai da na kaisu garden din sannan na dawo na sake dukusawa a gabanta.

“Ina sabulu”

“Shiga store ki dauko”

“Abincina fa?”

“Sai kin gama wankin za ki ci ai tunda kika zabi rashin kunya sai na horaki a gidan nan”

Ban sake ce mata komai ba na tashi na ahifa store din na dauko sabulun na nufi garden din, dana isa kurawa kayan ido nai na rasa da wanne zan fara wankewa? Shikenan saboda ba ni da gata duk abunda aka ga dama sai ayi min. Ba ni da wani iko da karfin da zan iya cewa ba zan wanke ba, dan haka na saka tufafin a gaba ina ta wankewa ga rashin karfin jiki na zazzabin da na ke ji, ga yunwar jiya da dare gashi da safen nan ma ban saka komai a cikina ba. Haka na saka kayan a gaba ina ta wanki tun ina yi da dan kuzarina har na koma bana iya komai na gaji sosai amman a haka na tisa kayana a gaba na wanke su tas babu abunda na bari, sannan na bi na shanya su, sai na zuba ruwa robar na laba bayan itacen mangoro guda biyu da suka hade waje daya na boya a gurin nai wanka wai ko zan dan samu karfin jiki, sai dai abunda ban sani ba Ya Muhseen na daga dakin Mama Fulani yana hange ni, sai dai a lokacin da nake wanki ban ganshi ba, wata kila be zo gurin ba sai da na fara wankan, kuma ban lura da shi ba sai da na gama wanka. Kunya ce ta kamani duk sai na ji babu dadi ko ba komai yaga tsiraicina wanda shi kansa na san yasan haramun ne, ban tsaya saka rigata a gurin ba, na dauketa tare da dankwalina na fito daga garden din na nufi garejen, a cikin tufafin Inteesar da Ammy ta bani na dauki wani lace na saka na daura dankwalin sannan na nufo part din Mama Fulani dan bata ragowar rabulunta.

ALIYU POV.

A lokacin daya bar kamfani sai ya dauki hanyar gida, yana ta tunanin maganganun Nasir, tabbas shi kanshi ya san an cuci yarinyar kuma dole zara ji zafi saboda mahaifiyarta akai wa, but he like yadda take fada masa magana kai tsaye ba tare da tsoro ba, idan ya tuna ko wace kalma ta ta sai ya tsinci kansa a kogin tausayinta, yes she's right da ace yar masu hannu da shuni ce da Doc Asim be yarda ko yatsanta ya taba ba balle har ya cire kodar mahaifiyarta, and secondly na ji zafin hawayen da ta zubar da cewar da tai Mama Fulani ta mareta, yasan Halin Mama Fulani daman ba jutuwa take da yan aiki ba, shiyasa duk wacce aka kawo da taje ganin gida bata dawowa, a dayan bangaren kuma yana jin haushin yadda Muhseen yake masa. Iya kokarin da yai ta isa gida ba tare da Rahma ta gane yana cikin damuwa ba, ko da ya isa ya sameta a falo dinning mai dafa musu abinci namiji yana serving dinta, yana daya daga cikin dalilin daya saka take son zama a Abuja a nn ko kofi bata kawarwa mai musu aiki ne namijin dan kabilar igbo yake mata komai ciki kuwa har da dafa abincin da gyara duka dakunan. Juyowa tai ta kalleshi da far'a da alama tana cikin farinciki.

“Dear welcome”

Karasawa yai kusa da ita ya kai bakinsa ya sumbanci gefen kumatunta sannan yaja kujera a kusa da ita ya zauna.

“Na yi waya da Doc Perry gobe zan je na ganshi”

Shiru nai na wani dan lokaci sannan ha kalleta.

“Why ba zaki bari sai nan da kwana biyu ba idan kin huta”

“Ba wani zancen hutu, tunda yanzu na samu lafiya ai zan iya komai, kara kawai na maida hankali gurin neman haihuwar”

Ya gyada mata yana mikewa tsaye kamar be jidadin. A daren da tunani biyu ya kwana a ransa, na ganin Doc Perry da Rahma ta ce za tai da kuma na Ataa wanda be san dalilin na damuwar kansa da tunaninta ba. Ko da suka tashi da safe mai dafa musu abinci ya gabatar da komai a beburin karyawa, a tare ya karya da matarsa sannan na ya shiga dakinsa ya shirya cikin shiga ta manyan kaya ya fito yai mata sallama ya kama hanyar kamfaninsa. A kamfanin ya wuni duk wani abun da akai baya nan sai da aka gabatar masa da shi ya ganshi kuma ya duba yadda komai yake tafiya kowa ya san da cewar oga ya dawo sannan suka shiga meeting, bayan sun fito ne yake labartawa Nasir zancen ganin Doc Perry da Rahma zata je yi.

“Then why da ba zaka fada mata gaskiya ba? For how long za kai ta aje wannan sirrin ne Aliyu?”

“Ban sani ba, iyakar abunda na sani zan iya ajiyarsa har karshen rayuwata, kawai kasa a nemo min Doc Perry ina son magana da shi”

“Haka zaka daukarwa kanka a duk lokacin da zata je ganin wani likita sai ka samu kudi ka bashi a rufe maganar? Anya hakan zai haifar maka da da mai ido Aliyu? Idan ma kai baka son ganin iyalinka ai familynka suna so, muma kuma muna so”

“Matata tana da muhimmanci a gareni Nasir, idan ta san gaskiya ni ne zan fi shiga damuwa domin zata saka kanta a damuwa ne, kuma duk abunda nai mata zata ga na mata ba daidai ba, and kasan Mama Fulani ma zata fara damunta just like Momy daman can ba jutuwa suke da Momy ba”

“Amman wannan kawai ya isa ka kasa kanka a wannan matsalar? Kana ganin idan kai ne Rahma zata zauna da kai? No ina da Tabbacin duk yadda take son ka ba zata zauna da kai ba, shekarar ku takwas da aure Aliyu idan baka fara tunanin samun haihuwa a yanzu ba, zuwa yaushe zaka fara? Lokaci yana tafiya, a yanzu nan gaba kadan karfin ragowa zai yi ba karuwa ba, ya kamata kai tunani”

Aliyu ya tsaya cikawa bakinsa iska a lokacin daya riga Nasir shiga office din.

“Kamin na ga wasu yayan Rahma na fara gani, be kamata ace wani abun ya shiga tsakaninmu ba”

“Haihuwa ita ce shiga tsakani? Kai ba haihuwar ka akai ba?”

“Yes i mean kasan yanzu idan kowa ya gane gaskiyar Rahma zata shiga matsala ta shiga damuwa, kuma muna son junanmu ni da ita, be kamata abunda be riga ya zo ba ya saka mu damuwa”

“Ina da tabbacin da akanka ne Wallahu Rahma ba zata zauna da kai ba, zata fi son ganin gudan jininta fiye da kai, ballantana tana ganin cewar tana yar nai nera zata iya samun wani mai nera ta aura”

“Baka san yadda Rahma take so ba ne Nasir baka san so ba ne”

“Fine, idan kana son ka gane gaskiya ka daina cewa kai da ita ba ku da matsala, ka fada mata cewar kai ne mai matsalar wannan karon idan kunje tare ka biya Doc Perry ko nawa yake so ya fada mata haka, na tabbatar zaka ba ni wani labarin dabam”

Aliyu yai shiru yana nazarin kalaman Nasir. Ta wani bangaren yana ganin kamar be dace ya gwada Rahma kamar haka ba, wani bangaren na zuciyarsa kuma yana ta zugashi akan ya gwada din. Har ya bar office din be samu matsaya daya akan gwadarwa ko kin gwadarwa ba, ya sa dole zata kira shi tace mishi tana asibiti ya sameta a can a gwada lafiyarsu ta bangaren haihuwa kamar yadda ake musu a ko da yaushe, sai dai ba shi tabbaci ko Doc Perry zai yarda da hakan ba har ya aikata domin shi babban likita da kowa ya san da zamansa cikin garin Abuja, matukar kana amsa sunan mai nera to ka san Doc Perry, likita daya kware akan aikinsa kuma yake fadin gaakiya a ko da yaushe, ba iya nan kawai yake duba mutane ba har kasar waje an san da zamansa, sai dai Rahma bata taba damuwa da su je gurinsa ba, sai a yanzu da haihuwar ta fara damunta. A hanya yai sallah la'asar sannan ya isa family house gurin wato gidan Alhaji Hamza. A harabar gidan yai parking amman be fito cikin motarba ya tsaya dannen dannensa har ya hango Ataa ta fito daga Garden daga ita sai daura gaba, kirjinta a cike ga farin daya bayyana kansa a jikinta, gashin kanta a jike da alama wanka tai ko kuma ruwa ta fada, amman idan ruwa ta fada ai dole har tufafin jikinta zai jike, be taba kula da surar mace karamar yarinya kamar yadda ya kula da ta Ataa yau ba, karamar yarinya ce amman tana da abunda yake kauna a jikin mace wato breast ga yawan gashin kai, wanda ko Rahma da take babbar mace bata kaita breast ba, ga gashin kai kamar wacce akai wa dashe ya kwanta har gaban goshinta gwanin sha'awa, and every takunta jikinta motsawa yake fatarta na sheki kamar mai shafa wani kasaitaccen mai. Kasa dauke idonsa yai daga kanta har ta shige garejen ba tare da ta kula da shi ba.

“Miyasa tai wanka a Garden?”

Ya tambaya kansa cike da mamaki kamin ya tuna da cewar ai babu bandaki a garejin. Then miyasa ba a aje ta BQ ba? Ya sake tambayar kansa sai dai wannan karon a zuci yai tambayar kamin ya hade yawun bakinsa ya bude motar ya fito ya nufi part din Ammy sai da ya fara gaisawa da ita kamin ya shiga part din Mama Fulani. A falo ya samu kowa ban da Muhseen, Maryam da Rukaiya na ganinshi suka natsu sosai ko motsi kirki basa yi, cikin mutumci suka gaishe shi ya amsa musu kamar yadda ya ba fuska a daure sannan ya gaishe da Mama Fulani ita kan fuska a sake. Be yi zaman mintuna biyar ba Ataa ta shigo falon sanye da wani milk lace wanda ya kara fito da kyau sosai sam ba zaka ganta a hanya ka za ci yar talaka ce ba, lace din ya kara fito da kyauta da jan fatarta sosai ta yi mugun kyau duk da kasancewar bata shafa mai ba balle ma hoda haka ta fito naturally beautiful. Kasa dauke ido daga kanta Aliyu yai yana ta kallonta kamar yau ya fara ganin mace mai kyau, yanayin tausayin da ke fuskarsa yasa shi jin tausayinta ba tare da wani dalili ba, q nan ya lura da tabon bulalar da ke fuskarta da kuma kumburar da fuskar tai da idonta, tafiya take kamar zata fadi saboda rashin karfi na yunwar da take ji. Tana karasowa gaban Mama Fulani ta zube tana mika mata ragowar sabulun da ke hannunta.

“Gashi na gama wankin na wanke dika”

Ta fada cikin wata sautin murya daya saka tsigar Aliyu tashi.

“Je kitchen ki aje”

A nan Ataa ya hade hannayenta ta kama kafafun Mama Fulani ta rike ta fashe da kuka.

“Ki taimaka min dan girman Allah ki ba ni abinci yunwa na ke ji kamar na mutu....”

“Bata ci abinci ba?”

Aliyu ya tambaya yana kallon yadda hawaye suke sauko a idonta kamar ba gobe.

“Ai tun jiya da tai maka rashin kunyar nan ban bata abinci ba, kuma na fadawa Ammy karka bata, na sa Maryam ta zane mata jiki, kuma yau na hada ta wankinsu tun safe sai yanzu ta gama, haka zan rika mata tun da ta zabi yi ma mutane rashin kunya”

Wani irin abu yaji na rashin jindadi yana ratsa zuciyarsa a take tausayinta ya rufe shi, how old she's da za a ace tai wanki tun safe har la'asar and an a hana mata abinci kuma a saka Maryam ta dake ta duka saboda shi, a tunanin Mama Fulani rashin kunya tai masa shiyasa ta yanke mata wannan hukuncin.

“Ke zubo mata abinci”

Ya fada yana kallon Rukaiya, da sauri ta tashi ta nufi kitchen din ta zubo mata abincin a plate ta kawo sai ta tsaya gabanta.

“Tara dankwalinki a zuba miki ko kuma ki je ki dauko plate dinki”

“Bata da darajar da zata ci abinci a plate din ne? Give it to her....!”

Ya dakawa Rukaiya tsawa, da sauri ta mikawa Ataa plate din, cikin wani irin rawar jiki Ataa ta karbi plate din ta aje a gabanta ta saka hannu biyu tana cin abincin da su bata iya hakurin har ta cinye da dama ta sake debowa saboda azabar yunwar da take ji, sai dai idan ta ci da dama ta ci da hagu bata ma tsayawa tauna abincin sai dai kawai ta hade, jikinta na ta rawa sosai. Wani irin tausayinta ne ya rufe shi, ko ba komai saboda abunda akaiwa mahaifiyarta take aiki a gidan saboda ta sama mata magani kamar yadda ta fada masa, kuma sune silar ciwon mahaifiyar kusan shine silar komai ma, domin ko dukan da Mama Fulani ta saka Maryam tai mata ai saboda shi ne, iya kar abunda yake jin zai iya yi a yanzu na taimakonta ne ta samu saukin rayuwa a gidan kamin ya karkato da hankalinta har ta yarda ya taimaki mahaifiyarta ya nema mata magani.

“Mama pls karki sake horata da yunwa”

Ya fada cikin taushin murya kamin ya kalli Maryam yana mai jin haushi na rashin dalili cikin kakkausar muryar ya ce.

“Karki sake dukanta, tun da ba yar ki ba ce”

“To Ya Aliyu”

Ta amsa da sauri sannan ita da Mama Fulani sukai kallon kallo, mamaki ya gama cika su gaba dayansu. Wani bakin haushi da bacin ran abunda akai ma Ataa ya rufe shi, ga kuma tausayinta a bangare daya, yana ta kallon yadda take auna abincin a bakinta kamar wacce bata taba cinsa ba sai yau. Tsarkiwa tai ta fara tari tana ta wani abu kamar za tai amai saboda cikinta daya kulle.

“Kawo mata ruwa”

Ya fada yana kallon Maryam da mamaki ya kusa kashe a inda take zaune. Tashi tai taje ta debo mata ruwan na fonfo ta kawo mata Ataa ta saka hannu biyu ta karba.

“Na gode”

Ataa ta fada sai ta kafa bakinta ta shaye ruwan gaba daya. Tana dire kofin Sulaiman Mai ban ruwan fulawoyin gidan ya shigo da sallamarsa, aka rasa mai amsa sai Aliyu saboda kasaita kowa ganin yake ba zai iya amsa sallamar wanda yake kasa da su ba.

“Wai Kamal ya ce yana sallama da Aisha”

Aliyu ya kalleshi Mama Fulani da sai yanzu ta samu damar magana ta ce

“Aisha ko Maryam dai?”

“Aisha dai ya ce”

“Ba mu da Aisha a nan gidan”

“To”

Ya tashi da sauri ya fice, sai kuma ga shi ya dawo ya sake zubewa kasa kamar dazun.

“Ya ce wai Aisha mai aikin a nan gidan Ataa”

Mama Fulani ta kalli Ataa da bata san wainar da ake toyawa ba sai aikin aika abincin take a bakinta sannan ta kalli Sulaiman ta ce.

“Wane Kamal din wai?”

“Kamal dai soja wannan makocin mu”

“Ya ce yana kiran wannan yarinyar”

Mama Fulani ta fada tana nuna Ataa da tsananin mamaki.

“Haka dai ya ce”

“Tashi ka yi tafiyarka”

Aliyu ya fada masa sannan ya mike tsaye ya bi bayansa yana wani irin taku na kasaita da isa. Mama Fulani ta kalli Maryam.

“Wai ko dai manta sunanki yai?”

“Hmmm Wallahi ba wani mantawa kyau ne yake rudarsu, ba ki ganin wannan yarinyar kamar aljana”

Rukaiya ta fada tana kallonta, sai Mama Fulani ta kirata dan kara tantancewa.

“Ke”

Ataa ta dago ta kalleta.

“Na'am”

Mama Fulani ta kura mata ido tana ta kallonta kamin ta gyada kai.

“Eh lallai ko ba shakka”

Maryam taja tsaki.

“Shegiya mai kama da mayu, duk sai na yanke gashin kan nan”

Ataa dai bata ce musu komai ba, da ta gaji da yadda suke ta hantararta sai ta tashi ta fice daga falo dauke da plate din da cofin ruwan domin ta san Mama Fulani ba zata taba son kayan ba tun da ta yi amfani da su.

*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660* ZAKI

By Khadeeja Candy

22...

Ya Muhseen ya gyara tsayuwarsa yana kallon da mugun mamaki.

“Me kake nufi? Dan iska ne ni?”

“Ko ma dan ruwa ne kai ta shafa”

Aliyu ya fada mishi sannan yai min alama da na zo na wuce da ido, komawa nai cikin na dauko mopper da tsintsinyar na fito, duk irin rashin tsoron sa da nake yanzu kan na ji tsoron yadda na ganshi na san zai iya min wani abun ko kuma wani fadan ya shiga tsakaninsa da Ya Muhseen wanda a karshe ni ce aciki domin ni za a daka. Sai da na fice sannan ya biyo ni a baya ina ta sauri kar ya cin min har na shige part din Mama Fulani, sai gashi ya shigo cikin tsannanin bacin rai.

“Mama”

Ya kwala mata kira sai gata ta fito daga kitchen din da sauri.

“Mama kar yarinyar nan ta sake shiga part din Muhseen da sunan gyara masa daki, idan a cikin kanennsa ba zai saka wata tai masa ba ya hakura da gyaran kawai”

“Cewa kikai ya miki wani annmimiya?”

Mama Fulani ta fada, nikan tuna har na fara kuka domin na san ni za a dorawa laifi.

“Bata ce ba, ni dai na ke ganin rashin dacewar hakan tun da ba muharramarsa ba ce”

Da mamaki Mama Fulani ta kalleni ta kalli Aliyu sai kuma ta kalli Muhseen da ya shigo yanzu cikin bacin rai.

“Kai wani abun ka mata?”

“Ban mata komai ba, yadda yake dan iska haka yake tunanin kowa ya ke”

“Ni ba dan iska ba ne ka fi kowa sani”

“Then why ni zan zama dan iska? Ba uwa daya ta raine mu ba? Kai baka iya kyautatawa kowa zato? A yadda kaga dama haka kake son taka mutane? Ba zai yiyu ba Wallahi idan zaka taka kowa yadda kake so a gidan nan ni kan ba zaka iya da ni ba, sai dai bakincikina na kashe ka”

Aliyu be sake cewa Muhseen komai ya zauna a sofar da ke kusa da kofar yana ta huci kamar wani zaki.

“Zan baka mamaki Aliyu kuma fadan yanzu muka fara ni da kai”

Mama Fulani ta karasa fito daga kitchen din tana girgiza kai.

“Haba Muhseen? Haba Aliyu wannan wace irin rayuwa ce”

Aliyu ya dago ya kalleta.

“Mama miye laifina dan na ce kar a barshi ya kebe da wacce ba muharramarsa ba? Yarinya mai jini a jika kamar wannan za ki turara dakinsa ace ta share?”

“Kai muharramarka ce da ka kebe da ita jiya a Gareji? Waya san abunda kai mata take kuka?”

“Muhseen....!”

Mama Fulani ta daka matsa tsawa.

“Mama ba za mu taba shiryawa da wannan mutumen ba matukar ne dauke wannan girman kan da son milkin kowa ba, ba zai yiyi yace zai juya kowa yadda yake so ba, ba a karkashinsa na ke ba, dan haka ba zai yiyu ya ce zai juyani yadda ya ke so ba”

Mikewa Aliyu ya ya fice daga falon cikin wano irin zafin rai marar misaltuwa. Mama Fulani ta nufo inda na ke tsaye zata dake ni.

“Zo nan bakar munafuka ai duk ke kika hada komai”

Sai Ya Muhseen yai saurin tsakaninmu ya tare ni.

“Karki da ke ta Mama, za ki dauki alhakinta ne kawai, ba ki iya ganin laifin Aliyu sai dai wasu, bayan kuma shi ne mai laifin, kuma Wallahi sai na bashi mamaki”

Ya fada sannan ya juyo ya kalleni.

“Wuce daga nan”

Readers Also Read