Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 17
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 17: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 17. “Yes ni talaka ne kamin yanzu, a lokacin da muke yola mun sha…
4,207 words
“Yes ni talaka ne kamin yanzu, a lokacin da muke yola mun sha wahalar rayuwa, domin mahaifinmu ya rasu a lokacin da muke da bukatarsa, karatu ya so ya lalace sanadin hakan, amman talakawan nan da nake fada min na unguwarmu su suka hada kudi suka komai na makaranta domin suna ganin kimar mahaifina sosai, dattijon arziki haka suke kiranshi, da taimakon da suka min na kawo a inda na ke a yanzu, kin ga ko ai dole na san darajar su”
Yana fadar hakan ya faka motarsa gefen titi ya juyo ya kalleni.
“Fada min ke fa?”
“Ni ba yar kowa ba ce, babana ya rasu ina da kane Lukman shi ma ya rasu, daga ni sai Mamana muka rage”
“Ayyah sorry"
Ya fada cikin yanayin da ke nuna tsantsar tausayinsa a kaina.
“Kika ce ke kika kawo kanki aiki a nan miyasa?”Ban boye masa komai ba face zancen cire kodar mahaifiyata shi ma saboda ina tsoron kar Mama Fulani ta ji ne ta koreni dan sanan ba zata yarda cewar danta ya cirewa mahaifiyata koda ba, sai nai ma Kamal wata karyar da cewar ulcer ce take damun mahaifiyata na ke nema mata kudin magani, tsantsar tausayin da na gani a idon Kamal da fuskarsa ban taba ganinta a fuskar wani mai ganin tausayina kamar haka ba. Da kansa y ciro tissue paper ta gaban motarsa ya miko min.
“Share hawayenki”
Na karba na share hawayen da suka ki su tsaya min saboda tuna da irin rayuwar da na baro da kuma kalubalen da ke gabana.
“Kin yi kokari sosai Ataa kin zama jaruma, aiki a titi kula da mahaifiya ba abu ne mai sauki ba ko a gurin babba balle ke da ba zaki wuce 16 to 17 years ba, amman ina yan uwanki ba ki da kowa wanda zai iya kula da ku bayan rasuwar mahaifinku? Ya kamata ace sun kula da mulallinku ba su bar ku kuna ta bara ba”
“Ban san inda kowa nawa yake ba, mahaifina be taba firar kowa da ni ba, haka ma Mamana bata taba fada min wani abu daya shafi danginta ko dangin mahaifina ba, iyakar abunda na sani suna nijar”
Ajiyar zuciya ya sauke yana ta kallona sannan ya tashi motar ya hau titi muka cigaba da tafiyar, be sake ce min komai ba sai kallona yake har muka isa gida, a bakin gate din su Mama Fulani ya faka motarsa ya mika hannunsa baya ya dauko ledodin da aka saka masa a bayan mota ya miko min.
“Ungo wannan na ki ne”
Kin karba nai.
“Aa Mama Fulani zata iya min fada idan ta gani?”
“Ai ni na baki kuma yanzu da na aje motata a gida zan shigo cikin gidan a nan zan ci abinci rana”
Na saka hannu biyu na karba, sai ya saka hannunsa aljihu yan bandir din dari biyu ya miko min.
“Ungo wannan ki aje mana, za mu fara tarawa kudin maganin Mama”
Kallonsa nai baki a sake sai nai saurin girgiza masa kai.
“Aa ba zan karba kudi ba, idan Mama Fulani ta gani dukana za tai kuma aikin da nake saboda na tara kudin na ke za su iya idan na tara na wata uku”
“Ba za ki bari ta gani ba ai, boyewa za mu yi ki rika sakawa cikin kayanki, idan mun tara da yawa idan za ki je ganin gida sai a kaita asibitin ko?”
“Mama...”
“Ya isa, komai dai Mama Fulani zan mata magana ta daina takura miki”
“Aa dan Allah ka rufa min asiri wallahi zata iya dukana ma”
“To karba ki aje, karki bari ta gani sai ki boye abun ki ai”
Babu yadda na iya bayan karba domin ni ma kaina na san ina da bukatar kudin, dan haka na saka hannu biyu na karba cikin tsoro da firgice har na manta ban masa godiya ba, shi ya fara fita cikin motar ya zagaya ya bude min ya fito sannan ya rufe motar, wani abun da ban sani ba ashe Aliyu yana tsaye bakin gate din yana kallonmu amman ni ban lura da shi ba har sai da na ga Kamal yai murmushi ya daga masa hannu.
“Sannu dai Aliyu”
Sannan na koma cikin motar yaja abarsa zuwa gaban gate din gidansu ya danna horn aka bude masa ya shige ciki. Ina tsaye a inda ya aje ni ina kallon Aliyu da ke tsaye daf da gate din yana watso min wani kallo mai ban tsoro fuskarsa a hade kamar bakin hadari, tsakanin jiya da yau Allah ya saka min tsoronsa duk wani fitsara da nake jin zan iya masa sai na ji yai min kwarjini har na gagara karasa gurin gate din na shiga shi kuma yai tsaye a gurin yana ta kallona kamar daman can dan kallo kawai aka halliccesa. Ganin ba zan zo ba yasa ya juya ya koma cikin gidan, yana wani irin taku na masu karfi da kuzari. Sai na tabbatar ya shige ciki sannan na nufi gate din na tura kofar na shiga, sai na ganshi tsaye da alama ni yake jiran na shigo ni kuma nai tsaye a gurin dayan hannuna da kudin dayan kuma da ledodin.
ALIYU POV.
Tun ya bar gidan Mama Fulani ya saka samun sukuni da walwala a yadda yake, zuciyarsa na ta raya masa Muhseen zai iya cutar da Ataa, ya san Muhseen ba dan iska ba ne, amman ai ba a shaidun mutum a yanzu, kuma yadda Ataa take da kyau zai iya rudarsa ya jefata cikin wani halin, wanda yake da tabbacin shine silar komai tun da shi ne silar cire kodar mahaifiyarta har ta zo aiki a gidan, idan kuma wani abun ya same ta ai duk shine sila, dan haka ba zai bari rayuwarta ta lalace ba, ba zai taba yarda ta rika kebewa daga ita sai Muhseen ba, daman can tsakanin shi da Muhseen basu taba shan inuwa daya ba, saboda Muhseen yana jin haushin yadda yake da jin da nuna isa da dakama, shi kuma yana jin haushin yadda Muhseen yake da sakewa da mutane. Daga gidan Mama Fulani ya nufo gidansa cikin bacin rai, duk yadda yai kokarin ya kawar kar Rahma ta fahimci yana cikin damuwa sai ya kasa, in every minute sai ya ji kamar wani abun ne zai samu Ataa duk kuwa da yasan be barta mugun guri ba amman ya kasa natsuwa da zamanta a gidan tsakanin jiya zuwa yau. Rahma kallonsa take har ya shigo cikin falon ya karaso kusa da ita ya zauna yana matsa kansa alamar yana masa ciwo.
“Lafiya dai, na dauka sai nine zaka dawo gida idan mun ga Doc Perry?”
Kissing dinta yai sannan na kwantar da kansa jikin kujerar ya lumshe ido na wani lokacin sai kuma ya ciro wayarsa yai danne danne ya tura mata. A take sakon ya shigo wayarta da sauri ta dauki wayar dake gefenta ta duba.
“Za mu iya bari zancen Doc Perry for now? Bana son zuwa gurinsa”
Kallonsa tai bayan ta gama karanta sakon.
“But why? Wata kila ma mafita ce ta zo mana, waya sani ko waraka ce”
Dagowa yai ya zauna daidai yana kallonta.
“Rahma akwai abunda ban taba fada miki ba, ban so wannan maganar ta fito daga bakina ba, amman ban san iya lokacin da zan yi ta aje ta ba”
Kara matsawa tai kusa da shi da maida hankalinta gurinsa tana kallonsa kunnuwanta cike da kwadayin jin ko mienene daman yau ta fahimci yana cikin damuwa.
“Minene Aliyu akwai wata matsala ne? Fada min”
Wani dogon numfashi yaja ya sauke ya shafa fuskarsa cikin yanayin da ke nuna yana cikin damuwa, daman kuma a cikinta yake.
“Rahma ban sani ba ko zaki fahimta, ban san yadda za ki kalli abun ba, kuma ban san yadda za ki kalleni ba”
Saurin kama hannunsa tai.
“Fada min kawai Aliyu minene matsalar?”
“Rahma duka tsawon lokacin da muka dauka matsalar daga ni ne..”
Da sauri ta rufe bakinta sai kuma ta girgiza masa kai hawaye na cika idonta.
“Ba daga kai bane Aliyu sun ce ba mu da matsalar komai ba daga kowa ba ne, suna cewa za mu iya haihuwa a duk lokacin da Allah ya kaddara”
“Na boye miki ne saboda bana son ki damu, amman maganar gaskiya matsalar daga ni ne, a duk inda muka je ina sakawa likitocin su ce mu duka ne bama da matsala amman serious matsalar daga ni ne”
“Aliyu ba haka ba ne... ”
Ya rika fuskarta.
“Haka ne, kin san ba zan boye miki komai ba, ba zan miki karya ba, be kamata na kyale ki ki yi ta wahala akan abunda daga ni ne ba, na san idan muka je gurin Doc Perry dole zai fadi gaskiya domin shi baya karya”
“Duka shekarun nan da muka dauka da gaske matsalar daga kai ne? Ko kuma daga ni ne kake boye min?”
“Daga ni ne”
Hawaye ne ya sauko mata sai ta kwantar da kanta jikinsa.
“Miye amfanin fada min a yanzu Aliyu? Miyasa ba ka cigaba da boyen sirrin ba?”
“Saboda bana son ki yi ta wahalar da kanki akan abunda na san ni ne silarsa”
Rumgume shi tai ta fashe da kuka.
“Ba amfanin bayyanawa Aliyu, kai na ke so ba abunda ban gani ba, jin wannan kuma ba zai hana mu cigaba da neman haihuwar ba, wata kila gaba mu dace ba mu san inda rabo yake ba, da matsalar daga kai ne wata kila zan mu iya dacewa ka samu waraka”
Shafa kanta yai yana kara janta a kirjinsa ita kuma ta fashe da kuka mai tsanani har ya rasa ta ita zai fara rarrashinta. A haka suka kwana tana ta kuka, wanda yake tunanin wata kila da yace matsalar daga ita ne wata kila ma ba zata damu kamar yadda ta damu haka ba.“Kamal dai soja abokinka?”
Nasir ya fada cikin tsananin mamaki, Aliyu be ce masa komai ba, daman kuma ya san ba zai amsa basa ba, sai dai tunda yaji yai shiru ya san cewar Kamal din ne.
“Ina ya hadu da ita?”
Nasir ya sake tambaya, sai Aliyu ya fito daga gurin ya nufi kofa rai a bace, cikin sauri Nasir ya ce
“Aliyu ina za aka je?”
“Na zuba musu ido su lalata mata rayuwa?”
“Kana da tabbacin bata nata rayuwa za su yi? Daga Kamal har Muhseen ba irin samarin nan ba ne”
“Bana iya shaidar kowa sai kaina, idan ban taka musu burkiba lalata mata rayuwa za su yi, akan mi zai dauke ta ya fita da ita? Waya bashi izinin ma?”
“Ai ba yau aka saba ba, dan mace ta kebe da wanda ba muharraminta ba ba wani abun ba ne, naga gidanka ma namiji ne yake muku girki ya gyara gidan”
“Nasir baka da hankali kai ma, Rahma ai babba ce ta san ciwon kanta, ba zata bari wani ya yaudareta ba, wannan kuma karamar yarinya ce tunaninta be kai can ba”
Yana fadar hakan ya saka katinsa kofar ta bude masa ta fice. Nasir ya bishi da kallo yana murmushi.
“Aliyu kenan, at least dai yarinyar nan ta sa ka fara motsi kamar na miji, sai yanzu kasan da muharramin?”
Ya fada yana cigaba da murmushin tare da zaunawa saman kujera ya cigaba da aikinsa. Kai tsaye gida ya nufa gudu yake amman yana jin tafiyar ta masa nisa yau, a kada horn daya yake danna amman daya bisa bakin gate din sai da ya danna horn ya fi hudu a lokaci daya, har mai gadi sai da ya ji tsoro yai tunanin ko wani abun ne ya faru. Daf da kofar falon ya faka motarsa ya fito cikin zafin ran da be san ta ina yake fito masa ba ya shiga cikin falon ba ko sallama, Rukaiya ya samu kwance a kujerar tana lasar waya tana dariya da alama chat din ya mata dadi.
“Ke ina Ataa”
A firgice ta tashi zaune domin hankalinta yana kan wayar bata ma san da shigowarsa ba.
“Na'am tana, tare muka fita shopping shine sai Kamal ya ce na bashi aron ta ta taya shi shopping idan suka gama zai kawo ta gida”
“You're very stupid”
Ya fada yana kara matsawa kusa da ita cikin wani irin yanayin bacin rai marar misaltuwa, tana ganin hakan ta tashi da gudu ta nufi upstairs tana kiran sunan Mama Fulani, ta san baya dukansu ko ba su ba abu ne mai wahala ya saka hannunsa ya daki mace amman a yadda ta ga bacin rai a fuskarsa a yau ta san komai zai iya faruwa. Da sauri Mama Fulani ta fito daga dakinta dankwalinta a hannu yana tambayar ba'asi. Cikin kuka Rukaiya ke fada mata abunda ya faru sai ta nufi downstairs tana kallon Aliyu tare da fadin.
“Ta fada min ai, Kamal ne ya ce a ara masa ita”
“Ya za ara masa ita kamar wata sutura, idan wani abun ya same ta fa? And you.... ”
Ya fada yana nuna Rukaiya sai kuma ya juya ya fice sai huci yake kamar wanda yai gudun ceton rai. Mama Fulani ta saki baki tana kallon ikon Allah.
“Wannan yarinyar ta zama fitini ta zo ta koma garinsu ba zata zauna a gidan nan ba, gaba daya Aliyu ya canja ganin yarinyar nan, shi da babu ruwansa da kula da mace? Ji abunda yake?”
“Ba sai an koreta ba Mama, Wallahi kamaninta za mu canja, kyau ne yake rudarsu”
Maryam ta fada daga can upstairs din da take tsaye. Gate din Aliyu ya nufo ya tsaya yana ta jin kamar ya kira Kamal a waya sai kuma wata zuciyar ta hana shi, yana tsaye a gurin sai ga Motar Kamal ta karyo kwanar yana ta kallonsa har ya karaso kusa da su sai dai ba sosai ba, ya faka motar, sai kuma yaga yana magana da Ataa a cikin motar baya iya jin abunda yake cewa, amman wani irin abun yake ji yana masa yawo a cikin jinin, ji yake kamar ana tafasa hanjin cikinsa komai na jikinsa rawa yake har gumi ke karyo masa a take idonsa suka canja kala, bacin rai ya bayyana karara a fuskarsa, wani abu yaji yana masa yawo a zuciya wanda be taba jin irinsa a rayuwarsa, har numfashinsa na fita da karfi wani na tura wani, ji yake kamar yaje ya bude motar ya fito da Kamal ya shake shi a gurin, sai kuma wata zuciyar ta hana shi, lokacin da Kamal ya fito motar ya budewa Ataa ta fito ya daga masa hannu yana masa sannu ji yai kamar ua narke a gurin saboda zafin rai da wani bakim haushi daya kama shi. Bayan Kamal ya wuce Ataa ne ta gagara shigowa gidan sai ya juya ya koma ciki ya tsaya, sai gata ta shigo hannunta rike da kudi dayan hannunta da ledodi gashin kanta ya kwanta luf kana ganinsa kasan ya sha gyara gwanin sha'awa. Be san lokacin daya isa gabanta ya kware mata ido.
“Ina kika fito?”
Ya tambaya muryarsa har rawa take.
“Kamal ne ya are ni”
Ta fada tana turo baki. Hannu yasa ya fisge ledar hannunta da kudin ya bude gate din ya fice ita kuma ta fashe da kuka ta durkushe a gurin. Kai tsaye ya tsallaka titi ya tura gate din gidansu Kamal ya shiga, kadan suka kusa yim karo da juna domin Kamal din ma ya nufo gate, sai Aliyu ya jefa masa ledar da kudin.
“Kar ka sake daukar ta ku fita, har ka bata kudi, ba irin yan matan Abuja ba ne, ka je can ka nemi sa'ar ka wannan aiki ta zo ba shashanci ba”
Da mugun mamaki Kamal yake kallon Aliyu yana karantar abunda ke zuciyarsa da kuma mamakin bacin ransa akan ya fita da ita har yana fada masa abunda be taba ba ko da wasa.
“Fita kawai nai da ita”
Aliyu ya nuna shi da yatsa.
“Na fada maka ba irin yan matanka ba ne, wannan na zama na farko kuma na karshe”
Aliyu na fadar hakan ya juya, sai Kamal yai murmushi.
“Zai zama na farko amman ba na karshe ba, miye naka a cikin dan na fita da ita? Kaji haushi ne?”
Aliyu ya tsaya cak kamin ya juyo yana masa wani kallon wulakanci.
“Abun kunya ne ma ace ka fita da yar aikin gidanmu, har ka kaita saloon a gyara mata gashi what a shame”
Kamal yai murmushi ya matso kusa da shi.
“Abun kunya ne dai kai a ganka kana fada kan yar aikin gidanku! Ni daman ai nasan daraja talaka ba kamar kai ba, miyasa kake fada akan na fita da ita?”
“Ba zan taba barinka ka lalata mata rayuwa ba”
“Na lalata mata rayuwa? Like seriously?”
Kamal ya fada yana dariya. Harara kawai Aliyu ya watsa masa ba tare da ya sake cewa komai ba ya juya dan ya fahimci bata lokacinsa kawai zai yi a nan.
“A da bana son ta kawai burgeni take, amman wannan abun da kai sai ya saka min son ta Wallahi”
Kamal ya fada yana bin Aliyu da kallon haushi. Aliyu be juyo ba har ya fice daga gidan cikin zafin rai yana tauna hakoransa har suna kara.. ZAKI
By Khadeeja Candy
25...
A gurin tunda bachi yai gaba da ni ban sake sanin inda nake ba sai kusan magariba, domin na farka ne a lokacin da ake daf da gabatar da sallah magariba, da sauri na sauka saman katifar naje Garden da katuwar rigata da tai min yawa nai alwala na dawo nan sai na rasa hijab din da zan dauka na saka nai sallah domin komai nawa na cikin jakar ya jike shakaf sai kawai na zauna a gurin na rumgume hannayena ina kallon kasa, ji nai an jefo min abu wanda hakan tasa ni zabura na tashi tsaye da sauri, Aliyu ne ya jefo mij Hijab hannunsa a jike da alama alwala yai shi ma, ban ce masa komai ba na dauki katon Hijab din na zuba na soma rama sallah la'asar sannan na gabatar da magariba. Bayan sallah isha'i Muhseen ya bude kofar ya shigo daure da plate din abinci da ruwa a kofin ruwa ya dire min a gabana, tuwon shimkafa ne miyar ganye da tea mai zafi a kofin.
“tashi ki ci abinci”
Na tashi ina ta leken kofar daya fito.
“Idan Mama Fulani ta gani zata maka fada”
Murmushi kawai yai ya matsar min da plate din.
“Bana son tuwon”
“To ga Tea
Ya dauki kofin ya mika min, ni kuma na karba na kai a bakina, ina cikin sha Mama Fulani ta shigo ta kofar gaba sai nai saurin aje kofin na mike tsaye shi ma ya mike tsaye yana kallona da mamaki kamar be ga mahaifiyarsa.
“Muhseen ban ce karka sake shiga zabgar yarinyar nan ba? Ban isa da kai ba ne”
“Haba Mama wane irin ba ki isa da ni ba kuma? Amman zancen na fita hanyarta be taso ba, haba Mama ke ma ai ya kamata ki fahimci wani abu”
“Na gane me? Muhseen kana da hankali kuwa? Kasan abunda kake yi? Abun kunya kake son ka dauko mana? Yar aikin gidanku? Ai ko ganin ka akai kana mata magana abun kunya Wallahi a garemu kaskantacciyar yarinya kamar wannan?”
Shiru yai ba ce komai ba sai ta juya ta fice daga gurin, ni kuma na koma na zauna na kasa sanye tea din.
“Kar abunda Mama tace ya dame ki haka take wani lokacin idan ranta ya bace, shanye ki ba ni kofin”
Daga idona nai na kalleshi.
“Idan kana min abunda Mama Fulani bata so, zan ka iya samu matsala da ita, kuma ni ma zaka ja min wata matsalar, wata kila ta koreni ko ta dake ko wani abun dabam”
Lankwashe kafafunsa yai ya zauna gabana yana kallona tare da soma min magana a hankali.
“Ban taba zabar abokin rayuwa a wajen mu'amala ta abota ko ta aiki ko wani abun ba, ban taba gabatar da wata mace a matsayin wacce na ke so ba, duk da kasancewar akwai matan da zan gani na ji sun kwanta ko kuma su nuna ra'ayinsu a kaina, a talaka da mai kudi duka daya ne a gurina, domin duka mutane na dauke su, banbanci kawai su suna da kudi mu kuma bama da su, abota da talaka ko auren talaka ko zama da talaka ba zai taba damuna ba, matukar ni zuciyata ta kwanta da mutumen”
Shiru yai yana murmushi sannan ya cigaba
“Mama tana da wani hali da ni kaina bana son shi, ni kaina bana son irin rayuwar da take na kin jinin talaka, dana daya daga cikin dalilin daya saka ba mu jituwa da Aliyu, ita kanta Mama ta fin jin natsuwa da Aliyu fiye da ni, domin be rago komai a halinta da yanayin rayuwarta ba, har mamakin mu ke yadda ke yau ya sassauta miki ya doki Maryam saboda abunda tai miki, bayan be taba saka hannunsa ya dake kowa a gidan nan ba, sai da na fi alakanta hakan da zalincin da Maryan tai miki, domin baya son ya zalinci wani ko ya ga an zalince, sai dai fa ba shi da mutunci kuma hakan ba zai saka ya sake maka ba”
Hannunsa ya kai ya kama hannuna.
“Wata kila da ke zan iya canja musu rayuwa, wata kila da ke zai saka Mama ta fara daukar talaka da daraja, wata kila da ke Aliyu zai zubar da wannan halin nasa na nunanin talaka ba komai ba ne, kina da abubuwan da ke so a jikin mace, fari kyau gashi kurciya hankali ladabi da kuma kuzarin aiki, kin kwanta min sosai a raina Ataa tun ranar dana fara ganinki, dan talauci ba zai saka na kyamace ki ba, ko na kasa nuna kaunata a gareki ba, wata kila idan kika shigo cikinmu Rukaiya Baby Maryam Ahmad Aliyu Mama da duk wani wanda baya ganin darajar talaka zai daina ko ya rage, idan na samu sa'a kika so ni....”
Be karasa ba nai saurin fisge hannuna ina kallon cikin idonsa da mugun tsoro, ba tsoro na a dake ni ko amin wani abu ba, tsoro na kalamin daya fito daga bakinsa ji nai kamar kunnuwana ba za su iya dauka ba, kalmar ki so sai ta shiga a zuciyata tai min fadi sosai har ta sakar min nauyi a kirji.
“Kwantawa zan yi”
Na fada muryata na gargada a take na soma jin zazzabi na dawo min, be sae ce min komai ba, bayan yawun bakinsa daya hade ya dauki plate din da cup ya fice. Da sauri na kwanta saboda nauyi da naji kirjina yayi na kife ina ina fitar da numfashi daker, wani be taba fada min magana mai nauyi kamar wannan ba, a cikin talakawan yan'uwana babu wanda ya taba fada min haka, ban taba kawo wa raina wani zai so ni ba, shiyasa ni ma ban taba jin son kowa a cikin raina ba.
“Idan na samu sa'a ki ka so ni....”
Kalmar tana ta maimaita kanta ta cikin kunnuwana, a take na fashe da kuka ina jin wani sabon al-amari da ban taba ji ba, kuka na rika yi sosai kamar wacce aka daka ko aka fadawa wata bakar magana, sai na ji ina da bukatar mahaifiyata a kusa da ni ji nai kamar ace Nana tana kusa da ni na rumgumeta ta rarrashe ni amman ba dama.
ALIYU POV.
Sai da yai sallah magariba a unguwar sannan ya isa gida yana ta jin babu dadi a abunda Maryam tai ma Ataa and ganin Muhseen na bata magani ma it pain him domin yana ganin kamar cutar da ita kawai Muhseen zai yi, yana da tabbaci zai iya kare kansa daga duk wani abu da zai kusantar da shi daga Zina amman ba shi tabbaci wani zai iya kare kansa daga hadawa hallakar zina, ba kuma duk wannan yake damunsa ba, babban damuwarsa zuwan Ataa gidan saboda nemawa mahaifiyarta maganin kodar da aka cire mata wanda shi ne sanadi duk da ba da saninsa da amincewarsa aka cire ba, yanzu kuma idan wani abun ya same ta ai duk saboda shi ne. Babban plan din da ke gabansa na ya taimaki mahaifiyar Ataa ne ya nema mata magani ta samu lafiya sannan ya nemi yafiyarsu wata kila zasu yafe masa, amman ya kasa tunkarar Ataa kai tsaye da hakan, saboda tana fada masa magana son ransa a duk lokacin da yai maganar mahaifiyarta shi kuma girma kai da jin kai ba zai barshi ya iya tsayawa ya fahimtar da ita ba. Horn daya yai aka bude masa gate ya shiga cikin gidan ya faka motarsa a inda ya saba fakawa, sannan ya bude motar ya fito ya nufi kofar shiga falon, wutar falon a kunne take sai dai tv a kashe kamar yadda ya fita ya barshi amman ya an gyara komai na falon wanda hakan ke nufin mai gyara gidan ya zo ya gyara ya tafi, dakin Rahma ya fara nufa ya tura ya shiga, sai ya same ta kasa kwance ta dafe cikinta zuwa awanzunta tana wani irin daukar rai kamar zata mutu, wayarta na nesa da ita a kasa, da alama kubucewa tai a hannunta ta fadi kasa, hawaye na ta fita a idonta. A firgice ya karasa kusa da ita ya rikota yana taba fuskarta.
“Rahma minene?”