Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 20
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 20: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 20. “Zan maida ke amman ba yanzu ba, Aliyu be isa ya bani umarni na bi…
4,495 words
“Zan maida ke amman ba yanzu ba, Aliyu be isa ya bani umarni na bi ba, wani fadin rai nashi da hargaginsa na banza ba zai saka nai abunda zai dauka cewar tsoronsa na ke ba, ban san abunda kika yi daya saka Mama Fulani ta mareki ba, sai dai ina ganin kamar be dace tai miki hakan ba dan kawai kina aiki karkashinta”
Kasa nai da kaina na saka hannu na share hawayena, murya can kasa kasa na fara magana.
“Zan jure komai za a min a ko'ina matukar hakan na nufin silar farincikina, samun lafiyar mahaifiyata shine farinciki a yanzu shine abunda na ke bukata kuma shine dalilin zuwana aiki a nan, ka kyale na wulakanta ta dake ni idan tana ra'ayi ta yi min abunda duk ta ga dama, zan jure har na cimma cikar burina”
“Zan taimake ki Ataa zan taimake ki mahaifiyarki ta samu lafiya”
Kallonta nai idonta na zubar da ruwan hawaye na ce.
“Bana bukatar taimakon kowa a yanzu, bana son kowa ya taimake ni na fi yarda da nai komai da kaina, da sunan taimako wani ya yaudare yaudarar da ta jefa mahaifiyata da ni a cikin wannan halin, ba zan sake yarda da taimakon kowa ba, matukar ba talaka ne dan'uwan ba”“Sannu bakuwa ya sunanki hala?”
“Aisha”
“Kai kai sunan Mamanmu ne”
Ta nufi wata hanya da ke kamar corridor sai ta ga ta fito da gorar ruwa da kofi a hannu ta kawo gabana ta aje min.
“Ki fara shan ruwa kamin abinci ya zo”
“Na gode”
Na fada ba tare da na kalli ruwan ba, sai ta tashi ta fice daga falon ta bar ni nan zaune ina ta kallon yadda aka kawata ko'ina na falon. Wata budurwar ce ta shigo dauke da farantin nama da yaji a gafe ta aje mika min.
“Ga shi ki saka a baki bakuwar yaya”
Ta fada da kamar zolaya.
“Ina Kamal din yake?”
“Ya fita yanzu amman ya ce mu kula masa da ke”
A yanzu ma murmushi take tana maganar ni kuma na mike tsaye ina kallon kofa na ce.
“Bari na leka gidan Mama Fulani kamin ya dawo”
“Okay kin santa ne?”
“Eh na santa”
Shine kawai abunda na fada mata na nufi kofar ina ta sauri na fito daga falon.
“Aa har kin fito?”
“Eh nan zan je gidan Mama Fulani na dawo”
Na bawa matar dazun amsa sai ta amsa da.
“Okay sai kin dawo”
Kamin na isa gate din gabana nata faduwa ina ganin kamar haduwa zan yi da Kamal ya dawo ya hana ni fitar, ina samun nasarar ficewa daga gate din na tsallaka titi da sauri na buga gate din gidan Mama Fulani mai gadin ya bude min na shiga da sauri kamar wacce tai sata. Gadan gadan na doshi cikin gidan duk irin faduwar gaban da nake ji da tsoro arba da Mama Fulani sai na danne shi na tura kofar falon na shiga da sallama. Tana tsaye tana magana da suka yan matan nan na dazun da suka zo baki da kuma yayanta ta juyo ta kalleni.
“Me kika dawo ki yi?”
Durkusawa nai daga inda nake tsaye bakin kofar na hade hannayena ina rikonta.
“Dan Allah dan girman Allah ki yi wallahi ban san ya kai ni asibiti ba, kuma ban ce ya kai ni ba, dan Allah karki kore ni”
“Da ya kai ki asibiti da kar ya kai ni uwarsu daya ubansu daya a gurina, amman tabbas yau ba za ki kwana a gidan nan ba”
“Ki tausaya min dan Allah saboda Mama nake wannan aikin, bata da lafiya kudin maganinta nake nema”
“Ni nan da kika ganni ba ni da uwa da uba duka sun mutu marainiya ce ni, kara ke ma har da iyayenki a raye, wuce kije ki hada kayanki yanzu nan bana son ko minti talatin ki kara a gidan nan”
Ta fada cikin daga murya tana nuna min kofar fita. Siyama ta kalleta ta da tausayawa ta ce
“Mama ki yi mata hakuri idan ta sake sai ki koreta”
Sai Rukaiya tai karaf ta ce.
“Wallahi ni bana ma son minti biyar ta kara a gidan nan wacan yarinyar da kike gani tun da ta zo kullum sai wani mummunan abu ya faru”
“Za ki wuce ko ba zaki wuce ba”
Mama Fulani ta daka min tsawar da ta sakani mikewa tsaye a razane na fice da sauri. Garejin na dawo na zauna ina ta kuka mai karfi wai ko wani zai ji ya zo ya tambaya dalilin kukana yajd ya bata hakuri amman babu wanda ya zo har na ji muryarta tana kiran Zaharadden direba.
“Ki fito yanzu nan ko na shigo cikin na ci miki mutumci”
Da sauri na tashi na dauki jakar tawa na nufi garden na dauko ragowar tufafin dana shanya tun rana na saka a ciki na dawo garejin na saka sauran da musasshiyar farfesun kazar dana shanya na saka cikin jakar da siyayar da Kamal yai min, sannan na saka Hijab dina na fito ina hawaye na tsaya jikin garejin ina kallon kudin da take ba wa direban.
“Ka tabbatar ta shiga mota sannan na mika mata sauran kudi, idan an isa kaduna ta hau motar sokoto ai tasan gidan ubanta idan aka sauke ta a can”
“To Hajiya”
Ya fada yana karbar kudin tare da zagaya wa wajen motar ya bude ya shiga.
“Zo ki wuce mun rabu da kaya”
“Kudin aikina fa?”
“Aikin da ko wata ba ki yi ba? Je ki turo ubanki ya zo ya dibar miki”
“Ubana baya duniya Hajiya, ya tafi idan zan ki je zan je kowa zai je, amman Allah zai dibar min hakkina”
Shine kawai abunda na iya fada cikin kuka na nufi motar na bude na shiga, ina jinta tana ta zagina. Hawaye ne suke ta min zuba har muka isa tashar, a lokacin da direban yai farkin na bude zan fita sai na ji ya ce.
“Ki yi hakuri da rayuwa, haka take zuwa juyi juyi Allah ya sauwake mana talauci ni da ke mu daina zama karkashin kowa”
Da na kalleshi sai na ga hawaye a idonsa.
“Amin”
Na amsa sannan na sauka daga motar shi ma ya fito, sai da yaje gurin yan Union ya hannata musu ni ya basu kudin motar zuwa kaduna da kuma kudin motar Kaduna to sokoto sannan ya ciro dubu biyu ya mika min.
“Gashi ki rike wannan Allah ya kai ki lafiya sai wata rana”
“Na gode”
Na karba da hannu biyu ina ta hawaye kamar wacce akai wa ido dan hawayen kawai.
“Lafiya Mutuwa akai miki?”
Daya daga cikin mutanen ya tambaya. Sai na girgiza masa kai ina jan magina.
“Aa ba mutuwa akai min ba”
“To Allah ya sauwake”
“Amin”
Shi ya nuna min motar da zan shiga sannan ya bawa direban kudina da kuma kudin motar da zai saka ni ta Kaduna sannan na shiga na zauna muna jiran karin wasu mutum biyu. Ban dade da zaman ba aka kira sallah la'asar sai da aka kira sallar na tuna da cewar ban yi sallah azahar ba, sauri na fita daga motar na nufi gefen masallacin nai alwala da butar su sannan na nufi wani dan daki dana hango mata na shiga na shiga ciki nai sallah, na fadawa Allah bukakata kuma na kai masa kukana na kuma roki mafita akan dukan lamura na. Ba bar tashar ba sai biyar da kwata sannan direbamu ya kama hanya.ALIYU POV.
Da mugun bachin rai ya fita daga asibitin yana cikin motarsa Momy ta kira shi ta fada masa cewar an sallami Rahma kuma ya zo ya tafi da ita, jin wannan labarin yasa ki sakewa daga bachin ran da yake ciki sai ya dauki hanyar asibitin. Ko da y shiga ciki ya samu Momy da Mommy Rahma suna fita Rahma na zauna tare da kanenta guri daya fuskarta babu walwala, ganin Aliyu ya saka kanen nata suka tashi daga saman gadon suka dauki wasu kayan da za a tafi da su suka fice. Da murmushi Aliyu yake kallonta amman ita ka kasa sakewa kamar ba ita aka sallama ba.
“Amman na ce idan mun wuta yau zuwa gobe za mu tafi da ita can sokoto ta samu kula kuma idan tana kusa da mu ita kanta zata fi walwala”
Mommy Rahma ta fada har Aliyu ya bude ba ki zai yi magana sai Momy ta shiga kuma ta shanye duk wani abu da yake da niyar fada.
“Eh nima na yi wannan tunanin hakan zai fi, shi kanshi Dan wajen Fulani ai ba zai ki ba, Allah dai ya bata lafiya muma ai goben za mu koma”
Shiru yai be ce komai ba, saboda Momy ta saye bakinsa. Mommyn Rahma da Momy tare suka jera a gaba suna tafiya shi kuma ya jero shi da Rahma suka nufo gurin da ake aje motoci. Wata motar Mommyn Rahma da kanenta suka shiga Mommy kuma ta shiga gidan baya Aliyu da Rahma suka shiga gaba. Sai da ya fara shiga har cikin gidan Mama Fulani ya sauke Momy har sisters dinsa suka fito suka ga Rahma ban da Mama Fulani da take jin sai dai Rahma ta fita daga motar taje ta gaisheta. Bayan Momy ta fita ya wuce da Rahma gidansa, bata ce masa komai ba shi ma be ce mata ba har suka isa tana kao hannu ta bude motar sai ya rike dayan hannun wanda hakan yasa ta kalleshi.
“Rahma kamar ba ki murna da sallamar nan da aka miki?”
“Miye abun murna a gurin gawar da aka kai asibiti? Ai kasan daga asibitin sai kabari, ba warkewa nai gaba daya ba, to me zai saka ni murna?”
“Wani ya baki tabbacin cewa ba za ki warke ba? Ko kuwa kina da shaidar cewar mutuwa za ki yi saboda kina da wannan ciwon”
“Za ka iya bani tabbacin cewar zan warke na tashi kamar kai? Ko kuwa zaka ba ni tabbacin cewar wannan ciwon ba zai yi ajalina ba?”
Ta aika masa da tambaya cikin tambaya ba tare da ta bashi amsar tambayar da yai mata ba. Fita tai daga motar ya zagaya gefenta ya bude mata motar ya fito da ita ta rumgumeta sai ta karasa fashewa da kukan da take ta kankame shi sosai tana shakar turaren jikinsa.
“Bana son na rayu da wani namijin baya kai Aliyu, ina son ka sosai, ko da bana aurenka ba zan iya jurar ka kula da wata macen kamar yadda kake kula da ni ba, ba zan bari son wata mace ya shiga zuciyarka ba dan Allah ka min alkawari ko bayan raina ba zaka auri wata ba”
“Mi zai saka na auri wata bayan kina raye? Ko wace ta cancanci wani gurbi a zuciyata bayan ke Rahma? Be kamata kina irin wadannan tunanin ba”
Akwai abubuwa da yawa da ba su kamata na aikata su ba Aliyu amman dole na aikata, a zuci tai wannan maganar tana nasalta yadda zata rayu ba tare da Aliyu ba na dan lokaci kamin da dawo masa kuma ta dawo da farincikinta da cikar burinta na haihuwa. Rikata Aliyu yai suka shiga cikin falon zuciyarsa cike da tausayinta duk kuwa da irin maganganun da tai masa dazun suna cikin ransa. ZAKI
By Khadeeja Candy
28...
ATAA POV.
Misalin goma na dare muka isa Kaduna, a cikin tashar direban ya sama min guri na kwana bayan na yi sallah, washe gari ma sai da na siya pure water sannan nai sallah asuba, bayan ruwan naira goma ban sake saka komai a bakina domin jin nai bana bukatar komai kuma bana jin yunwa, da asuba muka kamo hanyar sokoto daga Kaduna, ina ta jin kamar zan yi amai a motar saboda kaurin mai da tafiya mai nisa wacce ban saba da ita ba. Ana gama sallah azahar muka shigo sokoto, ba dowowar dadi nai ba amman tuna cewar da mahaifiyata zan gana sai na ji sanyi, a wani bangaren kuma ina ta zullumi da tunanin abunda zan fada mata domin na san ba zata ji dadi idan na fada mata an korono ba, gashi kuma ban samu kudi ba. A babbar tasha muka sauka na dauko jakata da dubu daya da dari biyar da sauran canjin da na siya ruwa da su cikin kudin da direban Mama Fulani ya ba ni. Sai da na kawo bakin titi sannan na tari napep na shiga na fada masa inda zai kawo ni. Daga tashar zuwa Clapperto road dari da hansi ya kawo ni na bashi kudinsa na fita zuciyarta cike da zullumi da tunanin karyar da zanyi, har ina tunanin fara zuwa gidan Maman Salma sai kuma na wuce gidansu Farida kai tsaye. Wani dan karamin dakin kwano ne akai a gafen gidan wanda akai masa fuska daga can gabans ta yadda wanda yake cikin dakin baya ganin wanda zai zo wanda kuma zai zo baya iya ganin na ciki. Ina ta mamakin miye a gurin domin ban san da dakim kwanon ba kamin na tafi,. Da sallama na shiga cikin gidan sai Farida ta fito waje da sauri tana washe hakora.
“Oyoyo Ataa”
Rumgume ni tai duk da ina cikin bacin rai hakan be hana ni murna ba na rumgumeta muna murna da ganin juna.
“Ina jin muryar na ce ke ce”
“Ni ce fatar na same ku lafiya”
“Lafiya kalau”
Na sake ta na nufi dan kitchen din da nasan na bar Nana a cikin kamin na karasa ta ce.
“Ai am maida Nana dakin waje”
Cikin yanayin rashin jindadi ta fada fuskarta na nuna haka. Ban tambayi dalili ba sai dai naji faduwar gaba jin hakan, sai na juyo na fito daga gidan gaba daya na nufi inda kofar dakin kwanon take Farida na biye da ni a baya yanayinta kamar mai jin tsoro. Mutuwar tsaye a bakin kofar dakin kwanon na saki jakar da ke hannuna ina kallon Nana da ke kwance kamar kare domin babu tsoka a jikinta sai ƙassa, kanta ba dankwali gashin kanta ya tsire an rufa mata wani zane dakin gana daya wari yake warin kashi da fitsari, kallo take ba dan ta ganeni ba sai dan mutum take gani ban san lokacin da hawaye suka fara min zuba ba zuciyata ta rufe tai min wani irin mugun nauyi..
Daker na iya daga kafata na shiga cikin dakin hawaye na sauko min wasu na bin wasu. Kusa da ita na je na zauna ina kiran sunanta.
“Nana Nana Nana”
Shiru bata amsa min ba, sai kallona take kamar bata gane ba. Hijab dina na cire na na aje Farida na tsaye tana kallona har na janyota domin bana iya daukarta gaba daya bakin kofar dakin na kawo ta na aje, na fito da komai na dakin na nemi tsohuwar tsintsiyar mu da naga a cikin kaya na share dakin, na dauki roba na shiga ciki na debo ruwa kasancewar cikin gidansu Farida a akwai rijiya, na dawo dakin na zuba ruwan na wanke na masa tas, duk abunda na ke Farida na tsaye tana kallona ta kasa komai, Hijab din nawa na saka na je gawon nama na siyo omo da kudin hannu na siyo fura da nono da madara na dawo, ko da na dawo Farida ta shige cikin gida, ni kuma na sake sakawa dakin omo na wanke shi ya cire duk wani karni da warin da yake sannan na dauko turaren da Kamal ya siya min na saka duk da kasancewar na jiki ba hakan be hana dakin kamshi ba, zane da zane na hada na zagaye sannan na sake debo wasu ruwan na kai na jata a haka na kaita gurin na zuba mata ruwa nai mata wanka ko ina na jikinta sai da na wanke sannan na sake dawowa da ita a cikin tufafi na dauki wata riga da Aliyu ya bani na saka lokacin da nai rashin lafiya ta manya na saka mata na daura mata dankwalin sai na aje ta a waje saboda dakin be gama budewa ba. Wasu ruwan na sake debowa na saka kayan ci abincin mu a gaba na wanke su ma sannan na dama mata furar na saka ludayi ina ta bata tana sha a hankali har ta sha ya iashe sai na debo mata ruwa na bata ta ta sha da yawa, sai ta sauke wani irin ajiyar zuciya yana saka ni jin tausayinta fiye da da, sannan na dauke ta na maida ta dakin na fito na saka tufafinta a gaba na wanke su na shanya sannan na daw dakin kusa da ita na zauna ina ta kallonta kamar yadda ita ma take kallona irin kallo da ke nuna bata gane ni ba, ko kuma bata san inda kanta yake ba kawai dai tana gani ne.
“Nana”
Bata amsa ni bata kuma daina kallona ba, hakan yasa na fashe da kuka na kama hannunta na rike, na dawo amman babu kudin maganin kuma n tararda ciwonta ya fi na da, sai dai ina tunanin dawowar tawa tai amfani domin gashi yanzu ina zaune gabanta ina kula da ita. Farida ce ta shigo dakin ta tsaya daga jikin kofa tana kallona.
“Bayan tafiyarki abun yai tsamari bata iya tashi komai a inda take take yinsa, na iya kokarina na kula da ita, daga baya Mama ta hanani, wacan kitchen din da ke cikin gida ya lalace shiyasa Baba ya buga mata kwano ya dawo da ita”
Hannu na saka na share hawayen idonta.
“Kin san ba zaki iya kula min davita yadda ya kamata ba, miyasa kika ce za ki yi? Miyasa kika bari na tafi? Aminta ba ta ce haka ba Farida yanzu da mahaifiyarki ce kina tunanin zan iya barinta a haka? Wallahi ba zan iya ba”
“Na yi iya kokarina Ataa Wallahi dawainiya da Ataa ba abu ne mai sauki ba”
“Eh na sani ai, ba abu ne mai sauki kula da Nana ba, ba abu ne mai sauki kula da uwar da ba taka ba, amman kin san ba dan dole ba babu yadda za ayi na tafi na barta, idan kika duba dalilin tafiyata kadai ya isa ya saka ki tausaya min ki tausaya mata ki kula da ita”
Ta yi shiru bata ce komai ba, ni kuma na mike tsaye na fito waje nai alwala nai sallah na cire Hijab din na aje na rafka uban tagumi ina kallonta, ta ina zan samu mafita? Duniyar nan ta juya min ko ina na raba ba dadi, duk inda na saka gaba da zimmar cimma burina sai wani abun ya shiga gabana ya tare, sai yanzu na gane kwata kwata bana da sa'ar rayuwa kuma bana da nasara a rayuwata sai dai hakan ba zai saka na kyale rayuwar Nana a haka ba, ko da ko raina zan ransa. Ta ina zan fara baran zan koma? Ko kuwa sata zan yi? Wani zai kaiwa koke na ko kuwa mutuncina zan siyar? Duka ban gan mafita a wannan ba. Da tunanin inda zan samu taimako na kwana na a raina.
ALIYU POV.
Bayan sun shiga cikin gidan ne Rahma na dakinta na wuce dakinsa yai wanka ya fita masallacin unguwar yai sallah la'asar sannan ya dawo cikin gidan ya shiga dakin Rahma, zaune ya same ta saman sallaya da alama ita ta gama sallah ne a yanzu. Kasa ya zauna kusa da ita yana kallon fuskarta dake dauke da damuwa, har ya bude baki yai mata magana sai wayarsa dake aljihu tai vibration alamar kira, ciro wayar yai ganin number Mama Fulani be tsaya bata lokaci ba ya daga.
“Aliyu kana ina?”
“Gida”
“Zo ina son magana da kai?”
“Lafiya dai?”
“Lafiya akan matsalar haihuwarka ne, Rahma ta fada mana gaskiya ai”
“Gaskiya kuma? Wani abun ne?”
Mama Fulani bata sake ce masa komai ba ta kashe wayar. Sai ya kalli Rahma
“Wani abun kika fada wa Mama?”
“Ban yi magana da Mama ba, amman na yi da Momy shi ma kuma ban san cewa ba su sani ba”
Wani kallo ha aika mata irin kallon nan na me kika fada musu.
“Na fada mata cewar matsalar haihuwar daga kai ne”
“For what?”
“Na dauka sun sani”
“Ko sun sani be kamata ki yi wannan maganar da su Rahma”
“Abun ne ya fara damuna yanzu, kuma a da suna ta ganin laifina amman yanzu za su fahimci ba daga ni ba ne wata kila za su daga min kafa”
“Amman idan matsalar daga ni ne be zama damuwarki ba? Kina kokarin chanjawa daga yadda na sanki Rahma”
“Ba canja nake ba Aliyu, damuwar ka damuwa ta ce, sai dai a yanzu matsalar nan ni ta fi shafuwa fiye da kai, a baki rame na ke zan iya mutuwa a ko da yaushe, ba tare da na bar abunda za a tuna da ni ba, amman kai kana nan raye har na tsawon lokaci”
Be sake ce mata komai ba ya mike tsaye yana saka wayar ajihunsa ya fice daga dakin. Cikin bacin rai ya isa gidan sam be jidadin abunda Rahma tai masa ba, domin be fadawa kowa ba kuma be za ci zata iya fadawa wasu ba, wasun ma kuma iyayensa. Ko da ya shiga falon Kanensa na ciki suna ta fira da dariya, be kula su ba ya haye sama zuwa dakin Mama Fulani sai ya samu Momy da Abbah a ciki suna fira shiga dakin da murmushinsa ya zauna saman kujerar da Abbah yake zaune yana gaisawa da shi.
“Abbah dawowan rana kai?”
“Eh Wallahi Hajiya Fulani ta fada min na ce bari na samu na zo mu gaisa da ita”
“Gaskiya kam ko mu da muke cikin gida muna wahalar ganawa da kai balle ba ko”
“To ya za ayi aikin ne a haka sai hakuri”
Mama Fulani ce ta shigo dakin ta tsaya jikin kofa tana kiran Aliyu.
“Aliyu magana nake son yin da kai fa”
Tashi Aliyu yai ya bi bayanta suka nufi dakin Baby a ciki suka zauna. Ta kalle irin duban bana wasa ba ta ce.
“Rahma ta ce matsalar daga gareka ne?”
“Matsalar me ba?”
Yayi kamar be fahimci abunda take magana akai ba.
“Ba mu da matsayin da zaka fada mana matsalar ka ne Aliyu? Ko kuma ka boye mana gaskiya ne saboda ka kare matar ka?”
“Ba ko daya, na san idan na fada muku za ku damu, ni kuma ba haka na ke so ba, kuma ko da matsalar daga ni ne idan Allah ya rubuta zan haihu zan haihu”
“Da gaske ne kenan?”
“Gaskiya ne Mama”
Mama Fulani ta rufe baki idonta cike da kwalla.
“Aliyu da gaske fa ka ce”
Na gyada mata kai.
“Gaskiya ne Mama, sun ce kwayoyin halittafa ba su da karfin da za su rayu a mahaifar Rahma”
“Kuma babu wani abun da za a iya yi? Babu wata mafita”
Ta tambaya cikinnmuryar kuka domin har ga Allah bata son abunda ya taba Aliyu, balle kuma haihuwa da take babbar abu.
“Mafita kawai addu'a kuma zan cigaba da neman magani ko Allah zai saka a dace”
Dafe kai tai cike da tausayinsa. Tashi Aliyu yai ya koma kusa da ita ya zauna.
“Mama ki daina damuwa ba komai”
“Akwai komai Aliyu, haihuwa tana da muhimmanci sosai za mu so muga jikokinka, kuma ba zan so wata macen ta ki ka saboda rashin haihuwa ba”
“Miya kawo wannan maganar kuma?”
“Kana tunanin Rahma zata zauna da kai a haka? Gashi ta fara korafi tun yanzu, shiyasa na so ka kara auren tun tuni amman ka ki”
“Babu zance aure a gabana Mama, ni bana iya zama da mace sama da daya bana iya rayuwa da mata biyu”
“Ba ni kadai ba Aliyu Momynka ma ta damu kuma duk wanda yake kaunar ka idan yaji wannan maganar dole zai damu da matsalarka”
“Ko wane bawa da akwai abunda ake kaddara masa Mama wata kila ni irin jarrabata kenan”
“Haka ne”
Ta fada tana share hawayenta sannan ta ce.
“Kuma ina son na fada maka karka taba yarda ko tunanin daukar kodarka ka ce zaka bawa Rahma dan na san halinka”
Murmushi yai mai sauti.
“Mi ya kawo wannan maganar kuma Mama? Idan na na bata ai Rahma matata ce”
“Eh matarka ce amman mu iyayenka ba ku yarda ka bata ba, kar ma ka taba wannan tunanin a rayuwarka, sai dai a nema mata magani ko kuma a samu wata dabam a siya mata amman ba taka ba sam ba mu aminta ba...”
Mama Fulani bata kare gama rufe bakinta ba, Rukaiya ta shigo dakin da sallama tana fadin
“Mama Abbah na kiranki”
Mama Fulani ta mike tsaye ta fice tana nanatawa Aliyu zancenta, har Rukaiya ta juya zata fita Aliyu ya kirata ta juyo.
“Kamal ya kawo Ataa?”
“Eh amman be shigo ba ita kadai ta zo kuma Mama ta bata kudin mota ta maida ta gida”
Mikewa yai tsaye da sauri.
“What? Miyasa?”
“Daman ai Mama ta ce ba zata kwana a gidan nan ba”
Rukaiya ta bashi amsa tana kallon yadda hankalinsa ya tashi. Fita yai daga dakin ya nufi dakin Mama Fulani sai ya same ta ciki tana magana da Momy.
“Mama miyasa kika kori Ataa?”
Tsayawa tai kallonsa kamar yadda Momy ma take kallonsa.
“Why Mama why”
Ya tambaya kamar ya fasa kuka.
“Aliyu wai miye alakarka da yarinyar nan ne? Ina ce a nan gidan ka santa kuka aiki kawai ta zo amman kun bi ku fitini kanku da ita”
Cewar Mama Fulani Momy ta kalleta ta ce
“Yanzu Fulani sai da kika sallami yarinyar nan? Ba asibiti Kamal ya kai ta ba?”
“Ya dawo da ita ai na bawa Zaharadeen kudin motar ta na ce ya dora ta a mota, ni ba zan zauna da ita a gidan nan ba”
“Baki kyauta min ba Mama, ba ki san kudiri akan yarinyar nan ba”
Cewar Aliyu cikin rashin jindadi.
“Kudirinka kamar ya?”
Be bata amsa ba ya aika mata da wata tambayar.
“Wace tashar kika ce ya kai?”
“Ko kaje yanzu ba zaka same ta ba, and bari na fada maka indai na isa da kai karka bi bayan yarinyar nan”
Mama Fulani ta fada tana nuna shi da yatsa. Sa ya zauna a saman kujerar dakin ya dafe kansa, ji yai babu dadi gaba daya ranar ba tai masa dadi ba, an kori Ataa Mama Fulani ta hana ya bi bayanta and ga abunda Rahma tai masa.
“Daga zuwan yarinya ku dauki wani buri ku dora akanta yar talakawa? Abun kunya ma aiki take a gidan nan fa haba Aliyu ko kowa zai ce ya so ta ai ba da kai ba”
Dagowa yai ya kalli Mama Fulani.
“Ba son ta na ke ba Mama, taimakon zan yi saboda halin da muka saka ta”
“Wane hali? Halin me kuka saka ta? Ina ma kasanta idan ba nan gidan ba? Ko kuwa dan fadan da nai mata da be taka kara ya karya ba shine wani hali”
“Ba shi nake nufi ba, kodar mahaifiyar yarinyar nan aka cire aka sakawa Rahma ba da amincewar su ba, aikin da take a nan saboda ta samawa mahaifiyarta magani take”