Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 26
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 26: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 26. “To na gode”Na fada ina nufar bandakin, wanke bakin na fara yi…
4,448 words
“To na gode”Na fada ina nufar bandakin, wanke bakin na fara yi sannan nai wanka da ruwan data hada min da kuma sabulu mao tsada na dauki tawul din da na gani rataye na daura sai ya tsaya min iya jinyoyina. Haka na fito daga bandakin na samu gafen gado na zauna, bana son na taba wani abu ta zo ta ga na mata ba daidai ba, na fin son sai idan ta zo ta fada min man da zan shafa. Ina zaune ina kallon yatsun kafata masu tsawo kuma sirara na ji an bude kofar dakin na yi zaton Amina ce sai na ga Muhseen yana rike da wayarsa. daga can bakin kofar da yake ya tsaya yana kallona tun daga kaina har zuwa kafafuwana, daman rabin cinyata a waje suke. Ba zan iya fassara mana'anar kallonsa ba, domin a yadda na ke makaskanciya ban yi zaton wani mutum mai daraja dan masu daraja wato nera zai min kallon sha'awa ba, balle har yai tunanin yi min wani abu, sai dai yaba kyauwo na wannan na san wani abu ne da ba ko wane namiji ne zai iya rike bakinsa daga furtawa ba, sai miskilin mutum kamar Aliyu wanda nake ganin kamar ba shi be taba ganin kyau nawa ba domin be taba yaba wa ko nuna zai yaba din ba, kallon ma da yake min ina jin kamar na kurilla ne dan kawai nai magana ko kuma na tsargu. Ya dade yana kallona kamin ya karaso kusa da ni yana ta yawo da idonsa a kan surar jikina. Tsarguwa na soma yi irin tsarguwar nan ta jin haushi idan wani na kallonka tsabanin Aliyu da bana jin haka, ga kuma kallon da yai min lokacin da nake canja tufafi da lokacin da nake wanka, sai na soma jin ba dadi duk kuwa da kasancewar kallon mace ko tana jikinta a gurina ba wani abu bane, domin kuwa da wani babban abu ne da Nana ta zaunar da ni da fada min a matsayinta na mahaifiyata.
“Na rantse da Allah kina da matsifar kyau Ataa, look at you karamar yarinya da ke amman Allah ya miki sutura komai ya ji”
Ya fada yana kokarin zama kusa da ni sosai yana kallon kirjina da fuskata.Na sani kyau na daga cikin abunda yake burge Muhseen ba tun yau ba tun a lokacin da ya taba ganina a gidansu da sunan aiki ya umarce mahaifiyarsa cewar a zabe ni saboda kyau, sai da yadda yake koda kyau nawa har mamaki yake ba ni domin shi ma yana da na shi kyau daidai gwargwado.
“Ataa....”
Sunana kawai ya fira be fadi abunda yake da niya ba, sanadin shigowar da Aliyu yai dakin hannunsa rike da mug fuskarsa babu annuri yake kallona da kuma Muhseen.
“Wai kai baka jin kunyar kanka? Ka shigo cikin daki ka kebe da yarinya kamar wannan kuma da tawul kawai a jikinta? Ji yadda ka zauna jikinka na kusan taba nata”
Muhseen yayi murmushi yana mikewa tsaye.
“Ina ce yanzu nan Amina ta fada min cewar kai ka kawo ta, waya san inda ka fito da ita? Kai da ba a zarge ka ba? Kao kullum na zaka kyautatawa mutane za to ba? Ka dinga min abu kamar baka san inda na fito ba? Ko kuma mai mim fatar sheri? To yanzu muka fara tsakanina da kai Aliyu dan kana son ta be isa ya hana ni sonta ba, kai ma din ban san kalar son da kake mata ba”
Yana fadar hakan ya fice cikin bacin rai. Aliyu kuma ya nufo inda nake zaune ciki ba fada.
“Wai ke baki san haramun ne mutumen da ba muharramin ka ba ya kebe da kai?”
“Be min komai ba”
“Oh sai ya miki komai ne zai zama matsala? Kallon jikinki ko taba jikinki shi duk ba matsala ba ce? Ba ki tana sani ba?”Na gyada kai alamar ban sani ba din.
“Wace makarantar islamiya kika yi?”
“Bama zuwa makaranta saboda bara”
Na amsa masa ina dan turo baki kamar an min wani abu. Kallona ya rika yi irin kallon nan na mamaki jin furucina.
“To haramun kallon jikin mace da ba muharramar ka ba, kin san abunda ake nufi da muharrami ma?”
Na sake girgiza kai alamar ban sani ba.
“Kina cikin matsala”
Na fada yana juyawa sai kuma ya juyo ya ya nuna ni da tsaya.
“Kar na sake ganin kin zauna kusa da wani namiji, kar ki sake sakin jikinki har wani namijin ya gani ko da ni ne ko wani can dabam kuma ki kama kanki bana son yadda kike sakewa da kowa”
“To”
Na fada ina gyara daurin tawul din a kirjina sai ya matsa kusa da ni ya miko min mug din hannunsa.
“Ki shanye yanzu za ku tafi asibiti”
Hannu biyu na saka na karba garin karbar hannuna ya taba na shi.
“Kar hannunki ya sake taba nawa idan za ki karbi abu, kar kuma ya sake taba na kowa”
Yana fadar hakan ya juya ya fice daga dakin. Ni dai ban da binsa da kallon babu abunda nai yi.
ALIYU POV.
A fisace ya fito daga dakin ya rasa dalilin son shiga jikin Ataa da Muhseen ke yi, ya sani Muhseen ba dan iska ba ne amman ba shi da tabbacin zai iya rike kansa be fadawa Ataa ba, shi kansa a yadda ya ganta a yanzu haka ya ji wani abu dabam balle kuma Muhseen da kyau mace kadan kan iya jansa balle kuma Ataa ba zai iya misaltata da kowa ba.A falon ya samu Muhseen zaune yana lasa wayarsa Momy kuma tana kitchen ita da Amina da Siyama hada breakfast. Be cewa Momy ya tafi ba ya fice daga falon zuwa cikin motarsa. Sai da ya dauki hanyar gidansa sannan tunanin abunda zai fadawa Rahma ya fara fado masa a rai, be so yayi bachi a can ba, shi be san ma lokacin da bachin yai gaba da shi ba, and ko da ya farka tsakiyar dare ne gashi ta jera masa miss calls din da be san adadinsu ba, idan har ya daga be san amsar da zai bata ba, idan kuma yace ya dawo cikin dare a wannan lokacin be san irin kallon da zata masa ba, kuma be ji zai iya tafiya ya bar Ataa a nan ta kwana ita kadai, da ya barta a nan ba shi tabbaci shi din zai kwana a cikin natsuwa da kwanciyar hankali kamar yadda ya kasa samun sukuni har sai da ya jingina da kwanon dakin da take kwana, domin yana jin idan ma babu mutun wata kila wani abu mai cutar kamar kwari ko dabba za su iya zuwa su cutar da ita duk kuwa da ya san ba a daji take ba. Driving din yake yana juya kansa dan kwanan da yai cikin motar kamin ya fito juyansa ya yi ciwo ga sanyin dake sauka sai ya saka kansa yai masa nauyi. A harabar gidan yai parking ya fito yana saka wayarsa aljihu ya nufi kofar falon kai taaye ba tare da tsoro ko tunanin komai ba. Kamar yadda ya tsammata a tsaye ya samu Rahma cikin falon fuskarta futik futik alamar ta sha kuka har ya gode Allah.
“Ina ka kwana Aliyu?”
Ta tambaya tana doso inda yake idonta cike da hawaye. Tsaye yai yana kallonta har ta karaso kusa da shi.
“Ni ya kamata na tambaye ki ina kika je saboda ni na aje ki ba ke kika aje ni ba, na zo gidan nan da rana ban same ki ba”
“Ka sani kuma kai ka bani dama idan ma na fita ba ya wuce na je gida ko kuma gurin kawaye na, amman kai baka kwana a gida ba Aliyu, kuma na ta kiran wayarka baka daga ba, na kira Siyama ta fada min baka gida ina kaje?”“Fushi nai na bar gidan na kwana a gidan gona na dauka ko ba zaki dawo ba”
“Amman baka saba haka ba, kuma baka taba yi ba Aliyu”
Ya rika fuskarta da hannayensa biyu yana shafa kumatunta da babban yatsansa.
“Karya zan miki?”
“Amman.... ”
Be bari ta fadi abunda zata fada ba ya hade bakinsa da nata ya shiga aika mata da wani irin sako mai muhimmaci da girma, sakon daya sauko masa tun a lokacin da yai arba da surar Ataa wace rabin jikinta kw waje, cinyoyinta gashin kanta ta ya jike da ruwa ya kwanta a jikinta da goshinta ga fari da kuma gurin wuyanta da ke ta sheki. Tsayuwar ce ta gagaresu har ta kai ga yayi baya ya jingina da kofar falon, sai kuma juyar da ita ta zama ita ce jikin kofar shi kuma ya mata rumfa. Duk yadda Rahma ta zo ya hakura har su isa daki kasa hakura yai daman haka yake idan abun ya bijiro masa baya jira kuma baya iya yiwa mace uzuri matukar uzurin ba na musmmman ba ne, domin Aliyu ba shi da hakuri a wannan babin.A falo sukai komai daga bisani ya rumgume matarsa suka shiga bedroom dinsa a tare sukai wanka kamar yadda ya saba mata bayan sun fito ya saka wasu tufafi ita kuma ta daura tawul domin babu tufafinta a dakinsa, a kan gadonsa suka kwanta yana rumgume da ita har bachi yai gaba da shi.
Be farka ba sai da aka kara kiran sallah azahar, shi ya riga sauka saman gadon ya shiga bathroom ya dauko alwala fito sannan ya tashe ta, sai da ya tabbatar ta tashi zaune sannan ya sumbanci goshinta.
“Tashi ki yi sallah”
“Aliyu motar na ga ya fashe a gaba”
“Yeah accident muka samu amman da sauki Allah ya tsare babu abunda ya faru”
“Garin ya? Allah ya kare tsarewa”
“Amin”
Ya fada tare da daukar agogonsa ya daura a hannun sannan ya fice daga dakin yana fadin
“Na tafi masallaci”
Da kallo ta bishi har ya fice, sannan ta kawarda idonta ta dafe kanta ita dai har yanzu bata gamsu Aliyu ya kwanta gidan gona saboda ta fita ba, be taba haka ba be kuma tana haka ba.
MUHSEEN POV.
Ransa be taba baci kamar yau ba, ya rasa dalilin daya saka Aliyu yake shigar masa hanci, iyakar abunda ya sani yana son Ataa saboda tana kyau kuma ya san ba haramun bane son mace mai kyau and yes Ataa ta kai mace da za a kalleta a so ta, daman ya dade yana som aure mace mai kyau, bayan son na aure ba shi da wata manufa zuwa ga Ataa amman yadda Aliyu yake masa ya sashi jin haushi sosai,a yanzu ne ya shirya taba ta ko kebewa da ita da kuma neman aurenta domin ya lura kamar Aliyu yana kishi ne, ba taba ta ko kebewa da ita kawai ba ya dauki alwashin har kiss sai ya mata a gaban Aliyu sai dai idan mutuwa zan yi ya mutu idan kuma ya fusata shi sai ya yi mai gaba daya daman dai aurenta zai yi dan haka yana jin ko kaiwa yai a jikinta ba wani abun ba ne face samun damar da zai saka Mama Fulani da duk wani da zai masa karan tsaye ya amince ya aureta.
“Muhseen”
Momy ta kira shi da karfi jin tana ta kiransa kadan be amsa ba tana can wata duniyar yana tunani. Kallonta yai sai yai murmushi.
“Momy magana kike?”
“Ina ta magana baka ji ni ba, lafiya dai?”
“Wallahi Momy ba lafiya ba, abunda Aliyu yake min ne bana jindadins akan yarinyar nan”
Momy ta zauna a kujerar dake kusa da tashi.
“Mi yake maka? Daman Husna ta fada min jiya kun yi fada miya faru?”
“Momy bana da halin nai magana da yarinyar ko na kebe da ita sai ya saka zargi, kuma wallahi Allah ya sani bana da wani manufa akanta bace na aurenta”
Da mamaki Momy ta kalleshi.
“Aure kuma?”
“Eh na taba fada mata tun a lokacin da take Abuja cewar ina sonta, Mama ma ta san da maganar sai dai bata yarda da ni ba, kin san yadda take tsanar talaka tana ganin kamar kaskancine na auri mace kamat Ataa, amman ni har ga Allah ina son ya Momy dan Allah ki shige min gaba”
Ya fada yana wani marairaicewa kamar zai saka kuka.Maganar sam ba tai ma Momy dadi ba sai dai ba zata muna nuna masa ba.
“Amman Muhseen yarinyar nan yanzu ba soyayya ko aure ne a gabanta ba, ta mahaifiyarta take”
“Na sani Momy, ni ma ban yanzu nake nufi ba, sai hankali ya kwanta, amman Momy ke kadai zan iya rikewa domin ke nake da tabbacin za ki fahimtar da Mama kuma ki share min hawaye na”
“In-Sha-Allah ni mai maka komai ne Muhseen, bari na tashi na kira ta fito muje asibitin na gama abincin”
Momy ta fada tana mikewa tsaye cikin yanayin na rashin jindadi.
*Khadeeja Candy* ZAKI
By Khadeeja Candy
34...
Bayan fitar Aliyu Amina ta sake shigowa dakin ta dauko min man shafi na shafa sannan ta ba ni tufafi na saka ta fesa min turare da kanta.
“Gaskiya kina da kyau Aisha mashallah ga gashi, na ga har kin fi Mamanki kyau ma”
Na yi murmushi ina kallon kaina a madubi.
“Baba na biyo Babana yana da kyau sosai”
“Gaskiya ba laifi kina da kyau sosai Wallahi”
Kasa nai fa kaina ni kaina a yanzu sai na ga kamar na fi da kyau, domin jan yadi ne a jikina irin mai fitar da kyau farar mace.
“Bari na gyara miki gashinki”
Ta warware min gashin kaina ta ta dauko wani katon mataji ta shace min kaina ta saka min jan ribbon daga kasa kuma ta barbarza shi a bayana, sannan ta daura min dankwali ta shafa min kwalli a ido har zata shafa min jan baki sai Momy ta shigo. Murmushi na gani a fuskarka ita kanta da kalleni sai da ta yaba kyau na.
“Ai tayi kyau a haka Amina karki shafa mata jan baki sai kace wanda zai je gurin biki, ta so muje asibitin sai ki karya a can”
“Tau”
Na amsa ina mikewa tsaye sai amina ta dauko wani karamim mayafi ta dora min a kafada.
“Dan Allah Momy dan tsaya nai mata hoto”
Wayarta ta dauko tai min hoto ta sai kuma ta dauke mu tare sannan na bi bayan Momy daman ta dade da fita daga dakin.Ko da na fito babu kowa a dakin sai Muhseen yana zaune saman kujera yana cin dankali a plate ganina yasa shi mikewa tsaye yana kallona fuskarsa da murmushi. Kofa na nufa sai ya kira ni.
“Ataa...”
Tsayawa nai na kalleshi ba tare da na amsa ba har ya karaso kusa da ni ya kai hannunsa zai taba fuskata sai na kwace, fadada murmushinsa yai ya saka dayan hannunsa aljihu.
“Aliyu ya ce miki wani abu kaina ne? Ya ce miki ni dan iska ne ko?”
Na yi kasa da kaina ba tare da na ce masa komai ba.
“Ba dan iska ba ne ni, tun na ke a rayuwata ban taba aikata zina ba, dan kuma na ce ina son ki saboda kina da kyau ba laifi ba ne, shi kanshi da ba ki da kyau da ba zai kula ki ba”
Ya dan yi shiru kamin ya sake kallona ya ce.
“Ina miki fatar alheri ina fatar yanzu ma kije ki samu mahaifiyarki ta farka, kuma ina miki bankwana zan wuce Abuja yau, zan dawo satin sama amman lallai ne idan na dawo yin aikin na biyo ta nan ba, maybe ki ganni nan kusa maybe kuma sai nesa ina mik fatar alheri”
Dagowa nai na kalleshi sai ya sakar min murmushi ya nufi kofar fita daga falon ya bar ni tsaye ina juyo na kalleshi.
“Aisha”
Kiran Momy na yasa na fito daga falon na same ta gurin mota, a front seat na shiga ita kuma ta zauna a mazaunin direba tai ma motar key aka bude mana gate muka kama hanyar asibitin.Ban san dalilin rashin jindadin kalaman Muhseen ba, yanayinsa da yadda yake min maganar ba cikin farinciki ba ne, and i feel like kamar ba zai sake dawowa ba, wata kila wani abun Momy da Aliyu suka ce masa shiyasa ya yanke wannan hukuncin, wata kila kuma ra'ayin kansa ne ban sani ba amman sam kalamansa ba su min dadi ba. Bayan Momy ta yi parking motar ya na bude na fita ita ta bude ta fito sannan ta fito da kayan na rika wasu ta rika wasu muka nufi cikin asibitin, kusan mutane duk wadanda nake cin karo da su babu mai kallo ďaya mazan dai duk wanda ya kalleni sai ya sake kallona wasu har da sakar min murmushi suke. Ni dai in biye da Momy har muka isa cikin dakin da Nana take, Doc Bukar muka samu a ciki da Laraba Doc Bukar na duba Nana wacce ki kwance idonta bude tana kallon mutane, Momy ce ta karasa cikin yayinda ni na tsaya bakin kofa ina kallonta na kasa karasawa tsoro na ke kar na je kusa da ita tace min bata gane ni ba, Doc Bukar na ta sakar min murmushi ni kuma idona na kan Nana har na fara hawaye.
“Karaso mana Ataa”
Cewar Doc Bukar daker na iya daga kafana na fara takawa cikin dakin, karar sautin takalmin kafata ne yasa Nana ta kalli inda na ke wani abun mamaki sai na ga ta sakar min murmushi, dadi na ji da sauri na karasa kusa da ita ina ta kallonta kamar zan cinye ta.
“Nana”
“Na'am Ataa”
Mantawa nai da tiyata ce a jikinta ya rumgume ta ina kukan dadi, bata manta ni ba ko da ta manta komai ni bata manta ni ba, sai da Momy ta dago ni tana dariya ta ce.
“Karki ji mata mana yi a hankali”
Na kalli Doc Bukar ina hawayen farinciki na ce.
“Doc bata manta ni ba”
“Bata manta komai ba sai dai ki yi mata fatan samun lafiya”
“Al-hamdulillah Allah mun gode maka”
Na fada ina daga hannuna sama, dadin da make ji a yanzu ba zan iya misalta shi ba, duk wanda ya kalleni ya san ina cikin farinciki a wannan lokacin, ba ni da wani buri face samun lafiyar Nana da alama muka yanzu ta doro hanyar samun.Kasa cin abinci safen mai saboda murna sai an nemi yunwa na rasa, Ita kuma Momy ta hada mata tea ta bata da kanta a hankali tana sha har ta sha ya isheta.
“Na gode Momy Allah ya saka muku da alheri”
Murmushi tai ta aje kofin tana fadin.
“Ba komai ai yi wa kaine”
Ta dade a asibitin sannan ta fita ita da Laraba wai zata je gida tai wanka ta gyara ta dawo. Aka bar ni asibitin ni da Nana ina kula da ita, cikin muryarta na marasa lafiya take tambayata.
“ataa ina kika samo mutanen nan? Suna da kirki sosai”
“Wannan matar dan ta ne ya taimaka mana, daga gidan da nai aiki a abuja ya biyo ni zuwa nan na fada masa matsalata da kuma dalilin aikin da nake a can gidansu an Abuja shine ya fadawa Mahaifiyarsa sai suka taimaka mana suka kawo ki asibiti ya biya kudin aikinki kuma jinin da aka saka miki jiya ma ance shi ya bada jinin, kuma yanzu haka a gidansu nake zaune su suka ba ni wannan tufafin ma”
“Allah dai yana da kirki sosai Allah ya saka masa da alheri shi da babarsa, bayan Doc Asim mun sake haduwa da wani mutum mai taimako”
Na yi shiru ban ce komai ba, domin Doc Asim ko sunansa ba na son a ambata.
ALIYU POV.
Daga masallacin da yai sallah ya wuce gurin Momy, duka kanensa suna zaune tsakar falon suna cin abinci a plate daya, a tare suke gaishe shi ya amsa musu da dan sakin fuska sai dai ba Sosai ba ya nufi dakin mahaifiyarsa. Zaune ya same ta gaban madubi tana shafa mai a jikinta, juyo tai ta karba masa sallamar da yai tana kallonsa.“Wa'alaikassalam”
“Momy barka da rana”
“Yauwa, ka je asibitin kuwa?”
“No yanzu da na ke son na leka, ban sani ba ko wa a wuce da wani abu shiyasa na biyo”
“Yau Ataa tana cikin farinciki”
Ya kalli Momy da mamakin farincikin nata, Momy bata jira ya tambaye ta ba ta ce.
“Mamanta ta farka kuma bata manta komai ba”
“Wow”
Ya fada yana murmushi.
“Har tea na bata ta sha, yau Ataa har da min godiya”
Ya dada fadada murmushinsa shi kansa ya jidadin jin hakan balle kuma da aka ce masa Ataa tana farinciki, ya gyara zamansa yana kallon Momy ya ce.
“Ban sani ba ko idan na fada miki wani abu za ki yarda”
“Minene?”
“Jiya lokacin da kai abincin dare na samu Ataa bata nan har na kawo Husna na koma bata dawo ba, na tambayi Laraba tace min bata san inda take ba, sai na hankali ya tashi na zata ko Muhseen ya fita da ita ko kuma Doc Bukar domin shi ma kamar yana dan rawar kafa akanta, amman na fara zuwa gidan da na dauko ta na fara dubawa ko taje daukar wani abun kamin na kirasu, sai na same ta tana bachi bakin kofar dakin na kwano, na ji tsoron tashin ta saboda kar ta min masifa so i decided nai gadinta saboda ina jin kamar idan na barta a nan wani zai iya zuwa ya yaga mutuncinta, da daman na mota ya ishe ni sai na fito gurin kwanon na zauna a kasa na jingina....”
Yayi shiru na wani lokaci kaminnya cigaba.“For the first time Momy jiya na zauna akan turda, na ji wani yanayi na dabam da ban taba ji ba, gurin babu ac babu katifa, sai hasken farin wata, garin yayi tsif kamar ba bu mai rayuwa a duniyar nan, Momy abunda na fara tunawa da shi shine kabrina, wata rana zan kwanta kamar haka a cikin kabarina, babu shimfida mai kyau babu gado ko katifa, babu haske sai na aikina, duk wani abun dana tara na dukiya da kawa a nan zan bar shi, zan rayu ni kadai a cikin kabarina”
Ya fada idonsa da kwalla Momy ta yi murmushi cike da kaunar danta.
“Secondly Momy na ji yadda wandada basa da shi suke ji, na taba kasa na zauna a kai i feel it bata da dadi amman a haka wasu suke kwana a samanta a haka wasu suke rayuwa a cikinta, then i realise there are billions of her da abinci kawai suke nema da muhalli, not like thousands of us da idan muka ga dama ba a Nigeria kwana ba a wata kasar ne, i never thought akwai mutumen da zai iya rayuwa a irin wannan yanayin sai yanzu, i never thought there a alot of homeless people da zasu raba a gidan wani kamar haka sai yanzu, Momy na ji wani a cikina some thing differently, wani abun da ban tana tunanin jin sa ba”
Murmushi ne har yanzu a fuskar Momy.
“Shiyasa Musulunci ya koya mana taimakon marasa shi, ko abinci ka taimakawa wani da shi zaka samu lada kuma zai jidadi ya rika ganinka da kima, yatsun hannyen mu Allah yayi su dabam balle kuma.mutane, dole akwai mai arziki akwai mai talauci akwai mai tsakiyar shi ba mai arzikin ba kuma ba mai talaucin ba, sai dai abunda aka fi so, arzikin da tsarki zuciya, a lokacin da nake nuna maka kyamar talaka ba abu ne mai kyau ba, sai kake ganin kamar ban fahimta ba ne, saboda Fulani ta nuna maka wata tarbiyar ta dabam wacce ba ita na so na dora ka akai ba, talakawa mutane da ya kamata ace an rikesu an nuna musu kulawa da kauna ko da ko su din basa son ka, ka yi dan Allah shi zai baka lada, a lokacin da mutum yake cikin yunwa idan ka ka bashi abinci zai dauke babban masoyi, wanda yake kishi kuma ka shayar da shi, zai ga ba shi wani mai sonsa a duniya kamar kai, balle kuma wanda lafiya ta gagareshi ka tsaya nema masa ba zai taba mantawa da kai ba, kuma ragowar rabon yana gurin Ubangijinka, akwa su da yawa marasa mayafi lokacin sanyi marasa abincin lokacin yunwa marasa mafaka lokacin damina, abu kadam su ke son samun su yi farinciki, while kai Allah ya hada maka komai arziki ilmi lafiya hankali da komai, wani yana can shi hankali ma yake nema ya samu be samu ba, shikenan kai dan Allah ya hada maka komai sai ka ce ka fi kowa? Wata kila ma mutanen da kake rainawa sune a gaba ranar alkiyama kai kana baya a kaskance kuma shine babban talauci”
Ya kawar da fuskarsa yana sauke ajiyar zuciya maganganun Momy sun kara taba zuciyarsa ya karanta ya sani amman ya take saninsa saboda yana jin shi din wani ne, yana jin ya fi kowa kuma babu wanda ya isa da shi saboda yana kudi alhalin dukiyarsa ba komai ba ce a gurin Allah.Momy ta share hawayen da suka zubo mata tana dauko zancen Muhseen.
“Dazu Muhseen ya fada min cewar kana takura masa akan Ataa hya fada min sonta yake kuma yana son na shige masa gaba”
Aliyu ya kalleta da sauri mamaki a fuskarsa karara.
“Muhseen din ya fada miki?”
“Eh yace ya fada mata ma”
“Me kika ce masa?”
“Na fada masa ita yanzu ba soyayya ne a gabanta ba, domin mahaifiyarta babu lafiya, wata kila kalaman nawa ba su masa dadi ba, na tafi kai abincin asbibiti tare da ita ko da na dawo na tarar ya tafi, ni kuma ban jidadin hakan ba”
“Miye abun rashin jindadi a ciki Momy? Ai gaskiya kika fada masa mahaifiyar yarinya ba lafiya ban dan rashin tunani ba har ya dube ta ya fada mata yana son ta? Kuma yarinyar nan yanzu abunda take bukata ilmi, bata san komai akan addinta ba, yarinyar da bata iya banbance muharrami da ajnabi, ko mahaifiyarta ta samu lafiya ai ilmi ne first abunda take bukata a yanzu i never thought akwai jahilan mutane irinta Wallahi”
“Akwai sosai ma, bara fa take wai kaga ba lallai ne ace tana zuwa makaranta ba,ni kaina na fada masa hakan ne saboda na san be kamata yai mata maganar a yanzu ba, shi kuma be fahimci ni ba”
“Babu wani rashin fahimta, taya zai ce yana son yarinyar da be san familynta ba? Kuma yar talakawa kamar wannan ai yasan Mama Fulani ba zata taba Amincewa ba”
“Shiyasa yake son ma shige masa gaba, kuma ni mai masa komai ce idan hankali ya kwanta”
“Idan tana son sa ko?”
Ya fada yana mikewa tsaye domin shi sam baya son maganar ma.
“Mi zai sa ba zata so shi ba, miye Muhseen ya rasa?”
“Ina abincin yake?”
“Yana kitchen”