Kenza eBookz

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 29

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 29

Zaki complete by khadeeja candy Chapter 29: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 29. A haka muka tafi be sake tambayata cewar waya ba ni zoben ba, ni…

4,500 words

A haka muka tafi be sake tambayata cewar waya ba ni zoben ba, ni kuma ban damu sai na sanar da shi ba, wata kila ma idan ya san gaskiyar Muhseen me ya bani zai rika ganin laifina ne ko kuma wani fadan ya shiga tsakaninsu, domin na lura ko kadan Aliyu baya son ina kula kowa ciki kuwa har da Doc Bukar da nake ganinsa da kima da mutunci, idan ya tarar ina fira da shi ko wata gaisuwar ta hada mu sai ya hade rai ya bata fuska, ko kuma yai ta fushi da ni, ko da yake yanzu fushin nasa ya zame min jiki, ban zan iya fadar laifin da nai masa ba, amman tun daga lokacin da Momy tai masa fadan nan akan matarsa washen garin daya dawo ya tambaye waye ya bani zobe sai na lura da daina sake min kamar da, ni kuma ban damu ba daman ai matar da ta zo min fada ta fada min cewar na shiga hankalina domin be son talaka, daman kuma ni mi zai kai ni sakewa da mutum kamar Aliyu mai ji da kai da ganin kowa na kasa da shi.Satin Nana biyu a asibitim suka sallame ta a tsawon satin biyu da muka yi a asibiti babu ranar da ba ma gaisawa da Muhseen a laptop tun ina tsarguwa har na soma sabawa, a kullum kuma matar sai ta ba ni cake tace daga shi ne. Sau daya ya kawo mana ziyara a asibiti ba tare da sanin kowa ba, domin sai da ya gargade ni akan kar an fadawa Momy cewar ya zo garin nan wai aiki ya zo yi ba zai samu bi ta gidanta ba, ni kuwa a nawa tunanin ya ki sauka a gidanta ne ko yaje saboda Aliyu. Idan na kebe ni kadai bana tunanin komai sai Kamal dan nishadin da muka yi tare da labarin rayuwarsa da ya soma ba ni, tun bayan dana baro gidansu ban sake saka shi a idona ba, hakan kuma ba karamin haddasa min damuwa yai ba, ko yana ina yanzu? A wane hali yake oho? Wata kila ma ya manta da wata yarinya mai irin sunana. Daddy Siyama sau uku ya zo ganin Nana yana da son mutane sosai ya nuna mana kulawa har ya dauki kudi ya bawa Nana bayan irin dimar da Momy take da mu. Ranar da aka sallamo Nana asibiti da kafafunwanta take tafiya, Momy na tare da ita yayinda ni da Siyama muka yi gaba muna tafiya, motar Amina muka shiga ni da yan uwanta Momy da Nana kuma suka shiga motar Aliyu. Na yi zaton Clapperto road zasu nufa da mu domin sauke mu acan sai na ga an nufo gidan Momy da mu. Aliyu ne ya budewa Nana mota da kansa ta fito tana takawa a hankali tana bin bayan Momy wacce ta wuce gaba zuwa cikin falon. Ina lura da yadda Nana take karewa ko'ina gidan kallon, wata kila ita ma ya burge ta kamar yadda ni ma burge ni a farkon zuwana. A falon muka zauna Momy na ta murmushi ta ce

“To Nana kin ga gidanmu idan kin dan huta za ku koma bq na saka an gyara muku can za ku zauna ke da Ataa, kuma dan wajen Fulani yace zai nema mata makaranta nan kusa sai ta fara zuwa islamiya, ta bokon ma za a samu wanda zai fara koya mata a gida kamin a saka ta makaranta”

Ban san lokacin da idona ya cika da kwalla ba, na dade ina jiran zuwan wannan ranar da zan koma makaranta na samu ilimi, amman ban samu ba. Kallon Aliyu nai sai naga yanayi ma Nana murmushinsa kadan muna hada ido ya murtuke fuska kamar be taba dariya ba wai kar na ga damarsa.“Na gode”

Na fada murya kasa kasa. Be amsa ni ba sai ma dauke kansa da yai daga barin kallona ya kalli wani gurin dabam.

“Kana ta hidima da mu, bayan nema mana magani yanzu kuma kun kawo mu a muhallinku, kuma za ku nema wa Ataa karatu? Abunda na dade ina mata burin samu amman na kasa bata, ban tana haduwa da mutane masu karamanci da sanin darajar dan 'adam ba irinku, taimakon da kuke mana ya yi yawa da me za mu saka muku?”

Cewar Nana tana hawaye kamar yadda nima na ke yi. Momy ta yi murmushi

“Ba komai ai yi ma kaine, lokacin sakarwa zai zo lokacin da zan nemi wani abun daga gareki ina fatar ki amsa min da hannu biyu”

“Zan karba miki ko mienene a duniyar nan, matukar ina da iko da karfi akansa, ku ne mutanen da kuka mai mu mutum, ban tana mafarki haduwa da ku ba, kuma ba ku taimake ni dan ku samu wani abun daga gareni ba”

Har yanzu Nana hawaye take hawayen jindadi da farinciki. A nan muka ci abinci suka koshi sannan Amina ta raka mu zuwa bq din, wani bangare ne na gidan da aka kawata fulawoyi sam ba zaka dauka cewar bq bane sai idan an fada maka, dan madaidacin daki ne mai bandaki a ciki, haka aka jera dakunan har biyar kowa ne da bandaki a ciki, sai dai na mu shi aka sakawa katifa ta labule da zanen gado aka gyara ko'ina tas kamar ba bq ba.

ALIYU POV.

After Nana ta huta, Amina ta nuna musu bq ita da Ataa. Sai ya rage falon daga shi sai Momy.

“Momy Rahma bata gida har yanzu”

Kallon mamaki Momy tai masa.

“Ban gane ba?”

“Tun wacan lokacin da muka samu misunderstanding akan matsalar Ataa shikenan tai fushi ta tafi gida”

“Kana nufi duk tsawon lokacin nan bata gidanka?”

“Tana gidansu”

“Kuma iyayenta ba su kira sun bincike matsalar ta ba?”

“Da za su kira ai da sun kira ko kuma Abbah ta ya kira Daddy ya ji ko mienene matsalar”

“Hmmm Allah ya kyauta, abunda suke yi ma yarinyar suna ganin kamar so ne ko gata Wallahi suna lalata mata rayuwa ne kawai, abun kadan yarinya tace ta tafi gidansu sai kace wata mai shan nono”

“Ni dai Momy so na ke a shirya mu da ita na yi alkawarin ba zan je bikonta da kaina ba domin ni ne mai gaskiya”

“Ai da ka bi ta tawa ka barta can gidansu ta dandana zaman gidan ta ji idan da dadi kamar na gidan miji, kishi hauka ne ko cewa kai tana son Ataa laifi ne balle baka furta ba, haka ake rayuwa”

“Momy ni dai ayi hakuri a dawo min da matata dan Allah”

“Na ji sai Daddyn ka ya dawo ai ko?”

“Tau na gode”

Ya fada, ba dan komai yake son a dawo masa da Rahma ba, sai dan yasan ita kanta tana cikin damuwarsa a yanzu duk kuma abunda ta aikata saboda shi ne, domin tana son sa tana kishinsa ne, after that yana son matarsa a kusa da shi shi kanshi ya san yayi hakuri iya hakuri har na sati biyu ba tare da Rahma a kusa da shi ba, hakan na matukar damunsa domin ya san ita kadai ce a duniyar ke iya yaye masa wannan kishin da yake ji matukar ba alfasha zai aikata ba.

Husna ce ta fito manne da waya a kunne tana tambayar Momy ina Ataa.

“Wake nemanta?”

“Ya Muhseen ne ya ce a akai mata waya”

“Tana bq”

Momy ta bata amsa sai ta nufi hanyar fita daga falon, Aliyu ya bita da wani kallo kamar ita ce Ataa. ZAKI

By Khadeeja Candy

37...

“Momy idan ba ki takawa Muhseen burki tun yanzu ba, zai iya wuce guri fa”

Momy ta masa kallon rashin fashimta.

“Wuce guri kamar ya?”

“For god sake Momy taya zai rika nunawa yarinyar wata soyayya a yanzu? Allah kadai yasan irin kalaman da ya ke furta mata”

“Shi kiranta a waya har wani nuna soyayyah ne? Idan ma haka din ne ai sonta yake sai ya fara nuna mata yana sonta? Dan wajen Fulani ka rika kyautatawa Muhseen zato, ka fi kowa sanin cewar ba mugun mutum ba ne kuma ba dan iska ba ne”

“Na sani, amman ke kanki Momy kin san Mama Fulani ba zata bari Muhseen ya auri Ataa ba saboda tana ganin darajar Ataa da ita ba daya ba, shi kansa ya sani kawai yana son ya batawa yar mutane lokaci da rayuwa ne kawai, daga lokacin da ya samu damar kaiwa ga jikinta Wallahi ba zai sake cewa yana sonta ba, domin kyauta yake gani, kyaun da idan ya samu dama zai iya zaga mata rigar mutunci shikenan kuma ta daina burge shi, idan ba a taka masa burgi yanzu ba nan gaba karatun da ake son ta yi ma kasawa za ta yi domin soyayya kawai zata sakawa gaba”

Murmushi Momy tai tana ma danta wani kallon na fahimtar wani abun da shi Aliyu be san da shi ba.

“Idan ma haka ne, ai sai ta aureshi ta cigaba da karatunta a gidansa ja ga babu wani zancen daukar hankali, kai ka kanka mai nemawa Muhseen aurene fa, balle kuma ni da na ke uwarsa, hankali dai ya kwanta kawai”Mikewa Aliyu yai tsaye domin maganar Momy sam bata masa dadi ba, dinning ya nufa ya zauna ya zubawa kansa abincin rana da be samu ci ba ya maida hankalinsa yana ci ba dan abincin yana masa dadi ha duk kuwa da kasancewar abunda yake so ne aka girka, ba kuma zai iya fadar dalilin rashin jindadin abincin ba, ci yake hankalinsa na can gurin Ataa wacce Husna ta kai mata waya, kamin ta dawo duk ya takura, ji yai ba zai iya hakura ba ya tashi ya fice daga falon gaba daya zuwa bq, a gurin aje motoci ya samu Husna tsaye tana jiran Ataa dake can gefen fulawoyi ta gama wayar ta bata wayarta.

“Ke kar Muhseen ya sake kiran wayarki ya ce ki bawa Ataa ki kai mata, na hana daga yau”

“To ba zan sake ba”

Ta amsa da sauri tana gyada masa kai. Ya nufi inda Ataa take zaune wayar a kunnenta tana murmushi hannu kawai ya mika mata alamar ta bashi wayar, sai ta tsaya kallonsa ba dan ba ta fahimce shi ba sai dan jira take sai ya furta.

“Wani wayar”

Ya furta da karfi sai ta mika masa tana kallonsa da fararen idanuwanta masu kamar madara ta turo masa baki alamar ta ji haushi, katse kiran yai sannan ya nuna ta da wayar.

“Karki sake waya da Muhseen a cikin gidan nan”

Bata ce masa komai ba bayan idon da ta sakar masa shi kuma ya juya ya koma gurin Husna ya mika mata wayarta sannan ya bude motarsa ya shiga ya bar gidan. Duk abunda suke Momy na hangensu ta windows din kitchen murmushi tai tana ta kallon yadda Ataa ta turo baki, ta sani da ace wata ce a cikin kanensa wata ta turo masa baki yau sai ya fasa bakin nan amman da yake Ataa ce gashi ya tafi ya kyaleta, yadda Aliyu yake nuna kishinsa akan Ataa ta sani sarai son Ataa yake ba wai yana gudun shigarta wani halin ne kawai ba, sai dai shi din be san yana yi ba. Shigowar Husna a kitchen din yasa Momy barin jikin windows ta kalleta still tana murmushi.

“Momy kin ga Ya Aliyu da fusata wai kar na sake bawa Muhseen wayata su yi waya da Ataa, gashi Yanzu Ya Muhseen din kiran ma yake na ki dagawa ban san mi zan ce masa ba”

“Ina hangenku ai, idan ya sake kira kice ni ya kira a wayata zan bata su yi wayar”

“Okay tau”

Husna ta juya ta fice daga kitchen din, Momy ta dafa kitchen cabinets tana fadin.

“Lokaci da yana zuwa, zancena zai tabbata wata rana, zaka duka har kasa kana rokon yar talakawa ta so ka lokacin da ba zan iya maka komai ba, domin ba zan zabe ka na bar Muhseen ba ko kuwa ina son hakan, amman ko ba komai son yarinyar nan zai maida kai namiji na jidadin da kake kishi a yanzu, at least zata koya maka kishin matarka, zaka fahimce wayewar zamani da boko ba komai ba ce idan aka hada ta da addini”Ita kadai take magana da kanta cikin yanayin na rashin jindadi. Ba ta bar kitchen din ba sa da ta dora girki dare. Yau Daddy dawowar maraice yai domin ana daf da kiran sallah magariba ya shigo gidan, direbansa ne ya bude masa mota sannan ya fito ya dauki jakarsa ya shigar masa da ita part dinsa, Daddy kuma ya nufo part din Momy yana gyara zaman babbar rigarsa, tun kan ya kai hannu ya bude kofar ta bude masa fuskarsa da murmushi.

“Sannu da zuwa”

“Yauwa”

Ya amsa yana naso kafarsa cikin falon, kujerar da ke kusa da kofa ya zauna yana sauke agajiya, Momy ta nufi gurin freezer dake gefen dinning ta dauko masa gorar ruwa da kofi ta kawo masa.

“Yau dawowar wuri akai SSG?”

“To mun gama abunda za ayi, zama na me kuma?”

“Ai ko ka dawo a daidai, da na so ma na kira kuma ban samu dama ba”

Sai da ya sha ruwan da ta mika masa sannan ya kalleta ya ce.

“Wani abun ne?”

“Dazun ne Dan wajen Fulani yake fada min cewar wai Rahma bata gidansa tun sati biyu da suka wuce”

Daddy yayi fuska manya irin ta mamaki da son tantace magana.

“Tana ina?”

“Wai ta yi fushi”

“Fushi? Fada suka yi?”

“Ba fada suka yi ba, kawai dai akasan yarinyar nan da ke jinya asibiti, ita Rahma ta saka aka je aka daketa da zo na fada masa shi ne tai fushi”

Daddy ya kyalkyale dariya kamar ba wanin abun ba.

“To ko kishi take? Yaushe akai abun?”

“Tun sati biyu da suka wuce dazun ma aka sallamo Nana daga asibitin, ni ban ma sani ba sai dazun yake fada min wai a masa bikon matarsa”

“Kuma fa muna yawan haduwa da Alhaji Nasiru Gobir be taba min maganar ba”

“Wata kila yana maka kallon ka sani ne”

“To Allah kyauta mutanen ne basa da dattako sam, ace yarka ta dawo gida har na tsawon sati biyu ai ya kamata ya bincika ya ji miye dalili”

“Dalili ya wuce bin bayan yarsa, kasan duk abunda ta fada shine daidai, sam ba su mata tarbiya mai kyau ba, ace abun kadan ka debi kafafuwa zuwa gidanku, yarinya lafiya ma bata isheta ba duk dawainiyar da yake da ita basa gani, wani lokacin Wallahi har tausayi yake bani, kwata kwata dan wajen Fulani ba san dadin aure ba”

“To shi kuma a haka son abarsa yake, da dai ya samu wata ya kara ai ita ma zata bawa kanta lafiya, mace idan tana ita kadai kuma tana ganin gata ya mata yawa zata ta yi abubuwa da dama ai, ko da yake Aliyu dan boko ne ba son mata biyu yake ba”

“Ba wani gata rashin tarbiya dai ne tun a gida ba a koya musu tarbiya mai kyau ba, ni da gatan be saka na yi wani abun ba”

Daddy ya mike tsaye yana zolayar Momy

“To ke duk kika gwada yi ai sai a kawo miki kanwa, ga mata nan duk inda na shiga kallo na kawai suke”

Momy ta dan harare shi.

“Ai ba kai suke kallo ba mukamin ka da kudinka suke kallo, idan ba dan kudi ba waye zai so tsoho? Ko ma watan ka kawo ai na gama cin moriyarka kuma na zama uwargida mai yayan gida sai dai ta bi”

Dariya suka yi har ita da tai maganar domin ta kareshi maganar ne tana wani murmuda ido irin na su na manyan mata.

“Ina yarana? Ban ji motsinsu ba”

“Husna da Amina sun fita Siyama kuma tana can bangarensu Ataa”

“To Alhajin Fulani ya samu cigaba kamfanin nan da yake ikirarin za a siyar wani dan kasuwar kasar nijar ya siye shi, Kuma ya bar ragamar tafiyar da kamfanin a hannunsa, ya kamata ko ban samu zuwa ba ki shirya da yara ko kwana daya ne suke ku masa murna, samun cigaban dan'uwana kamar nawa ne, ba ni da wani wanda ya fi shi a yanzu”

“Gaskiya na masa murna sosai, Allah ya dafa ya taimaka, daman haka muke so ai, to wannan tafiyar fa?”

“Ki samu wata kuje daman biko ai na mata ne”

Yana fadar hakan ya fice daga falon ta biyo bayanshi tana ta taya shi murnar samun siyen kamfanin da akai har tana fadar ranar da ya dace suje.Bayan sallah magariba Momy ta kira kawarta Hajiya Ramatu ta fada mata cewar za su je bikon Rahma. After sallah isha'i idan tana da time, ana saukowa daga sallah isha'i sai ga Hajiya Ramatu ta zo gidan ita da danta wanda shi ya janyo motar ya kawo da ita a gidan, tana shiga falon Momy ta fito sanye da mayafi suka gaisa a tsaitsaye suka koma cikin motar Hajiya Ramatu, kamin su isa gidan Alhaji Nasiru Gobir wato mahaifin Rahma Momy take labartawa aminiyarta Hajiya Ramatu abunda ya faru tsakanin Rahma Aliyu. Tsaki Hajiya Ramatu taja cike da jin haushi ta ce

“Wai Hajiya Hadiza miyasa ba za ki saka Aliyu ya kara auren ba? Wannan iskacin da jin kan da yarinyar nan take masa ya yi yawa, wallahi idan yanzu ya kara aure duk wannan iskancin dainawa za ta yi kuma dole ta kama kanta idan ta ji ba zata iya zama ba ta fita”

“Kamar a gaban ki akai, Wallahi dazun mahaifinsa ma haka yace kin san ko maza ma basu cika kula da sha'anin aure kamar mu mata ba”

“Wallahi akwai haushi Hajiya Hadiza abunda ake masa ne ai yayi yawa, duk irin hidimar da yake musu basa gani? Bawa ne shi?”

“Ido ne nawa idan ya ji wuya shi zai nemi karin auren da kansa ai, amman na san da Fulani ta san da wannan Wallahi da sai tana zuwa bikon nan daman can ba son aurenta da Rahma take ba”

“Ke ma dai ai da ba ki je ba Wallahi da ya zuba musu ido ya barta tai ta zaman gidan har sai zaman gidan ya isheta”

“Kin san iyayen miji idan ba su yi ba, basa fita idan ma suka kai ba fitar suke ba, yanzu ma sai an dora laifin a kanmu”

Hajiya Ramatu ta tabe baki cike da jin haushi. Ba laifi yan'uwan Rahma yayanta da kannen sun tarbesu cikin girmamawa da mutunci, sai dai mahaifiyar Rahma na fitowa sai ta canja musu fuska kamar wacce bata son zuwansu. Ciki ciki ta gaisa da su Momy na ganin hakan ta dauke kai ta ki cewa komai sai Hajiya Ramatu ce tai bayanin abunda ke tafe da su.

“To ya gaji kenan? Yarinya ta zo gidansu sati biyu dan tsabar wulakanci be zo ba be aiko ba, sai yanzu idan ya gaji da ita ai ba sai ya wulakanta akan yar talakawa ba, wai har ya mari Muneera akan wata banza can sha sha sha, yarinyar da be san inda ta fito ba, idan ma gajiya yai da ita mu ai muna son ta ba mu gaji da ita ba”

Wani wawan kallo Momy tai mata har tana kashe ido tsabar bacin rai.

“Yar talakawa da ba a san inda ta fito aka dauki kodarta aka sakawa yarki, sai yanzu na gane ashe Rahma bata rage komai daga halinki ba, ke kika koya mata kyamar talaka talakar ma wacce ta taimake ke ku, ba mu damar zuwa bikon Rahma ba sai yanzu, shi kan shi mijin na ta ma be so mun zo ba, domin ba shi ya koreta daga gidan ba, yarinya kamar wata mai shan nono da an yi abu ta dauki kafa zuwa gida ko kunya babu, mi Rahma zata nuna mana? Gata ko kudi ko family? Ba ta nuna mata dukiya ke kanki kin sani zuri'a kuma duk sokoto an sani babu wanda ya fi torankawa asali da tarin yan'uwa, duk abunda take muke shanyewa muna shanyewa ne saboda muna son ta zauna lafiya da mijinta, domim Rahma bata san wani abu wai aure ba, dan abu kadan ta kwaso kafa zuwa gida haka ake yi?”

“Au daman ba shi ya aiko ku ba kuka zo? To ki koma Rahma ba zata koma yanzu ba sai ta huta, sai Aliyu tako da kansa ya dauki matarsa, dacan idan ba nan ba so kike ta koma gefen titi tana bara kamar yar da danki ke so? Abun kunya wai kamar SSG ace dansa yana son yar bara a titi, mutum mai daraja wanda ya rika mukamai masu girma ace an rasa wacce dansa mai kamfanin Sky global resources yar talakawa makaskanciya, ku kanku ai abun kunya ne a wajenku”Momy ta girgiza kai tana kiran sunan Aliyu baro baro.

“Sam ni nikam abun alfahari ne yau Aliyu ya auri Ataa ko babu komai zai inganta rayuwarta kuma sai san yayi aure, ya kuma gane banbancin tarbiya da rashinta”

“Daman ai saboda kin cusa nasa son wata ne kike wannan bobotan, indai yana son Rahma ta koma dakinta to ya janye neman aurensa da wannan kazamar yarinya, ya hada Rahma kishi da yar wani mai kudi ba amman ba wannan ba”

Momy ta yi yar dariyar takaici tana mikewa tsaye tare da Hajiya Ramatu wacce ta kasa cewa komai tun da aka fara fada.

“Hajiya Talatu kin yi tutu gonar mai munta, zaman gida dai ko? Rahma tai ta zama har Mahdi ya bayyana, idan kuma zaman ya isheta sai ki dauke ta ki kaita dakinta, amman wani daga ni ko Aliyu ba zai zo bikon wannan yar ta ki ba, kuma ki zuba ido indai ina raye Rahma sai ta kishi da yar talaka...!”

Momy na kawai nan ta nufi kofar fita a fusace, daf da zata fice Hajiya Talatu Mommyn Rahma ta ce.

“Ai dole ku nema masa yar talaka, domin kin san babu yar gata gabas da yamma da zata zauna da juya, dimmar da yai mata ai ya mata ne saboda ya san baya haihuwa su taru su mutu tare”

Momy ta juyo ta kalleta.

“Ke Hajiya Talatu idan ba ki gode ni'imar Allah ba za ki gode ma azabarsa, ruwan cikin lokali ya ishe mai hankali wanka kuma ki rubuta ki aje da ikon Allah sai Aliyu ya yi aure ya haihu....”

A fice Momy ta fice daga falon tana nadamar zuwan bikon da tai. Momy na fita Rahma ta fito idonta shakaf da hawaye ta fadi a kusa da Mommynta kamar zata narke.

“Na shiga uku Mommy mi yasa kikai fada da su? Na rantse da Allah Aliyu ba zai zo bikona ba, tun da kika taba masa uwa, Wallahi ba zai sake ganin kimata ba, Aliyu baya son a taba masa family”

“To sai mi? Aliyu shi kadai ya rage a duniya ne? Ko sakin ki yai sai kije ki auri mai haihuwa ki haihu, kar wannan abun ya daga miki hankali matukar yana son ki dole ya dawo, ai yasan gidan da ya dauke ki gidane mai daraja da kima”

Cikin kuka Rahma ta tashi ta koma dakinta, Muneera ta taso daga dayan bangaren na falon daman falon ya kasu biyu ne, ta nufo inda Mommynsu take tana dariya.Husna ta tashi ta nufi karamin firjin din dake dakin ta dauko mata ruwa da kofi ta kawo mata ta zuba mata, sai da Momy ta sha sannan ta labartawa Husna abunda ya faru.

“Mutanen nan suna ba ni mamaki, wai talauci hauka ne? Shikenan dan suna da arziki sai su taka mutane yadda suka ga dama”

“Su taka wanda yake neman abu gurinsu dai, arzikin da ba na shi ba, mai tinkaho da abun wani duk uwar dukiyar da yake kuri da ita idan aka kasa uku ko kashi daya ba zai dauka ba, dukiyar wani ce wanda idan yau ya kaushe abarsa sai dai tu koma rabe raben wani, shi har abun tinkaho ne? Wai wanda ya gaji arziki baya haka”

“Gaskiya abunda suke yayi yawa, haba jama'a wai Wallahi sun ja mata domin Ya Aliyu ba zai je bikon ta ba”

“Tai ta zama a can har sai zaman gidan ya isheta ta yi hankali aure dai sai Aliyu yayi kuma Ataa zai aura sai dai su mutu?”

“Momy da Ataa?”

Husna ta tambaya tana zare ido.

“Eh ba ni za su nuna isa ba? Sai ya aureta?”

“Ya Muhseen fa?”

“Amina zan bashi, daman ai Fulani ba zata yarda ya aureta ba, kuma ko aurenta yai ba dadin zaman zata ji ba, amman yanzu Aliyu nake son ya aureta ya maida mutum kamar yarsu in ya so sa su mutu”

“Amman Ya Aliyu zai yarda ya aureta ne? Kin san fa ba sonta yake ba?”

“Ba son ta yake ba yake kishinta? A banza ake kishin mace? Idan ma baya son ta sai ya fara daga yanzu”

Cewar Momy tana wani cika har yanzu zuciyarta ta ki ta sauka daga bacin ran dake tare da ita.

“Amman Momy Ya Muhseen zai ga kin masa rashin adalci”

“Na ce miki Amina zan ba shi ai yasan idan bana sonsa ba zan ba shi yar cikina ba, amman Ataa sai ta auri Aliyu In-Sha-Allahu”

“Idan kuma ita Ataa din bata son shi fa?”

Momy ta yi shiru alamar tunani kamin ta daki kan gadonta tana ta rawa da kafa.

“Ina bukatar sanin waye Ataa ina suka fito, shine kawai abunda na ke son sani a yanzu, amman bayan shi talauci ko wani abun ba zai hana wannan auren ba”

Husna dai ta kalli Momy ta janye fuskarta tana tunanin yadda za ayi wannan chakwakiya domin Muhseen ma ba kyalle ba ne, kuma yadda yake nuna yana son Ataa yana da wahala ya iya yarda ta auri Aliyu yana kallo.

Haka Momy ta kwana da bacin ran abunda ya faru ta tashi da shi, Daddy kan dariya kawai yake mata daman haka yake mata idan ta saka kanta a wani abun at the end kuma be yi kyau ba, sai dai bata fadawa Daddy kudirin na na aurawa Ataa Aliyu ba, domin ta san ba zai zabi Aliyu ya bar Muhseen ba, duk kuwa da kasancewar be san Muhseen na son Ataa ba, bayan maganar tafiya Abuja da suka aje jibi babu wata maganada ta sake masa.Lokacin data dawo part dinta bakwai da kwata ne na safe, sai da ta fara shiga kitchen ta kunna gas ta dora ruwan zafi sannan ya fito falon tana dauke da dankalin turawa ta shiga dakin Siyama, sai ta same ta zaune tana home work din da bata samu yi jiya da dare ba.

“Momy ina kwana?”

“Lafiya kalau rubutu kike?”

“Eh homework ne da ban yi ba jiya”

“Okay ba ri na kaiwa Husna ta gyara min dankalin”

Ta fada tana juyawa ta fice daga dakin Siyama zuwa na Husna, ita ma zaune ta sameta sai dai waya take tabawa, tana ganin Momy tai saurin saukowa daga saman gadon da kayan bachinta ta karbi robar hannun Momy.

“Momy ina kwana?”

“Lafiya kalau kin tashi lafiya”

“Lafiya kalau? Ya bacin rai?”

Readers Also Read