Kenza eBookz

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 31

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 31

Zaki complete by khadeeja candy Chapter 31: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 31. Tashi nai naje na saka hijab din na dawo, ko da na dawo yana cikin…

4,474 words

Tashi nai naje na saka hijab din na dawo, ko da na dawo yana cikin mota ya bude front seat da alama ni yake jira, shiga nai na zauna da gangan na ki rufe motar sai ta ya mika hannunsa ya janyo ganbun ya rufe sannan ya soka taka motar daman tuni aka bude masa gate.Ba mu yi wata lafiya mai nisa ba, muka iso gaban wata katuwar makarantar islamiya, wani irin dadi ne ya lullube na kalleshi da sauri.

“Saka ni za ka yi?”

Sai yai min banza kamar be san da zama a cikin motar ba, ya bude motar ya nufi wani bangare na makarantar ya bar a ciki, be dade ba ya dawo ya bude min murmushi motar da kansa na fito na tsaya a kusa da shi ya wani hade rai irin kar na ga damarsa din nan, wani malamin ne ya zo ta takardu ya ya tambayi sunana da sunan Baba lafiya ta da sauransu sai ya rubuta a form din hannunsa dabya bukaci number waya sai Aliyu ya bada tasa.

“Shikenan yanzu sai uniform za a siya mata da kuma hotonta da za a laka a jiki”

“Ana siyar da uniform din a nan”

“Akwai muma siyarwa dinkaken ma ne”

Be tambayi nawa ba yake ba kawai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin masu dan dama ya mikawa mutumen.

“A bata uniform din ka rike canjin ka cire kudin form din hoto kuma za muje ayi yanzu, dan Allah ka saka ido akanta bata iya komai ba, tun daga farkon fari za a fara koya mata komai”

“In-Sha-Allah ba ka da matsala, ba ri a dauko mata uniform din”

Komawa yai cikin makarantar ya dauko uniform din cikin wata farar leda ya miko min na karba ina wani irin murna kamar na zuba ruwa a kasa na sha. Sannan na koma cikin motar shi ma Aliyu ya zagayo ya shigo yayi mata key.

“Na gode na gode sosai Allah ya saka maka da alheri”

Be amsa ni ba ko inda na ke be kalla ba, ni kuma ban damu ba farincika ya gama cika zuciyata gaba daya, daga ilslamiyar ya wuce da ni gurin daukar hoto aka dauki hotona aka ba shi, fiye da kudin hoton ya bawa mutumen, abunda na lura da shi idan zai maka alheri ko ya baka hakkinka sai ya ninka maka ko kuma ya baka abunda ya fi yawan nawa, na yi zaton daga nan gidan za mu koma sai ya nufi AGG da ni, ban taba shiga shagon ba tun da nake ganinsa sai dai kawai na bi an wuce amman har bara na yi a gurin shagon lokacin da nake tsananin bukatar kudin nan. Yana gaba ina binsa a baya sai rabon ido nake ina kallon kayan shagon ina ta kalle kalle da kansa yake zabon kayan ciki, yawanci gowns ne na abaya da riga da skirt na kanti, sai takalmi masu kyau ta ki hudu, sai da ya biya kudin sannan suka saka masa a mota muka fito muka shiga motar ya dauki hanyar wata plaza da ni, wannan karon a motar ya barni ya shiga ciki domin be bude min dan na fito kamar yadda yai min dazun ba, ni kuma na zauna a cikin motar har yayi abunda zai yi ya fito wani na riko masa manyan ledodi.A bayan mota aka saka masa musu sannan ya shigo motar yana cin wani abu mai kamar chocolate kuma ba chocolate ba, ya ci kusan rabi sannan ya miko min sauran sai na karba na saka gefen hijab dina na goge kufan bakinsa sannan na ci, ido ya saka min yana ta min kallon rainin wayo sannan ya tashi motar muka kama hanyar gida ana kiran sallah magariba. A harabar gidan ya faka motarsa ya bude boot din ni kuma na bude na fito rike da uniform dina zan tafi bq sai na ji ya ce.

“Wa za ki bar wa wadannan kayan?”

Dawowa nai na dauki ledodin na yi zaton cikin falonsu za a shigar masa da su sai na ji ya ce.

“Leda ukun ne na ki biyu Mamanki ne”

Na zaro ido ina bude baki.

“Da gaske da gaske”

“Da karya”

Na fada ba tare da ya kalleni ba ya rufe boot din ya nufi sashen Momy, wani tsalle nai na dire rai na fes, a gaskiya yau Aliyu ya burge ni domin na kura shi ma yana da mutunci kamar Kamal sai dai Kamal ya fishi son mutane da far'a. Nana ma ta yawa sosai da ganin kayan da kuma halin Aliyu daman tun muna asibiti take ta yabonsa tana ganin kirkisa sosai, wannan karon har da cewat tana mamakin yadda hake ga hidima da ni haka. Bayan sallah isha'i Nana ta ce na je na masa godiya kuma na ce ita ma tana masa godiya. Rigar jikin na cire na saka daya daga cikin Egypt abaya da ya siya min na saka na yafa mayafinta sannan na nufi part din rigar sai kyalkyali take ko'ina na jikinta.

Da sallam na tura kofar falon na shiga, sai Momy ta amsa min da far'arta Aliyu yana zaune saman cushion ya hade rai sosai kamar an masa wani abu, ina juyowa sai na Muhseen tsaye yana sakar min murmushi.

“Laaa Ya Muhseen”

“Pretty na”

Ya fada yana kallon yadda rigar ta karbe abun ka da farin mutum ya saka babaken kaya.“Yaushe ka zo?”

“Yanzu nan, jiya na ban ji a waya ba kuma ina da bukatar ganinki shiyasa na zo, ya kike?”

“Lafiya kalau”

Na amsa ina dariya kamar an min wani abu, ni dai har ga Allah ina son mutum mai far'a da dariya kamar Kamal da Muhseen, sai dai Kamal ya fi kwanta min sama da Muhseen din kuwa da kasancewar shi ma yana min far'a sosai, kusan sai na ce duka suna burgeni kuma ina son su.

“Kin yi kyau pretty na rigar ya karbd ki”

Ya fada yana rika rigar nawa ya buda ta tai fadi.

“Eh dazun Aliyu ya siya min ita Nana tace na zo na masa godiya”

Yanayin fuskar Muhseen na ga ta canja sai ya dan wara ido yana zolayata.

“Hop kin daina sake jikinki dai domin na lura ana sake miki da yawa”

“Sake jiki kuma?”

Momy ta tambaya sai ya kalleta

“Yes, lokacin da take Abuja a garden take wanka, a gareji take canja tufafi sai da na mata magana”

Juyowa Aliyu yai ya kalli Muhseen yana lilo da kafarsa wacce dayar ki saman daya.

“Ka ganta kenan? Shiyasa ka ce kana son ta?”

“Idan ma haka din ne ai ban yi illa ba”

Tasowa Aliyu yai daga saman kujerar da yake zaune yana fadin.

“Ataa ba ki da hankali kuma kurciya na damunki, Momy kina ganin abunda na ke fada miki ko? Ya ganta tana wanka ta na canja tufafi kuma shi ne yanzu a tsaye a gabanki har kina amsa dariya? Wallahi baki san ciwon kanki sam”

Muhseen yayi murmushi har zai yi magana sai muka hi Aliyu ya kyalkyale da dariya mai karfi wacce ban taba zaton bakinsa na iya irin wannan dariyar ba.

“Magana ta fito Muhseen kana son Ataa saboda ka ganta a sirara, Wallahi wannan nuna mata rashin daraja ne da raina mata hankali, what a shame lallai kai yaro ne kuma wawan duniya tun da har tsiraicin yake maka sha'awar kallo what a sad”

Yana fadar hakan ya fice yana dariya dariya irin sosai din nan kamar ba ta hankali ba.ALIYU POV.

Duk wata dariya da yake na fuska ne kawai amman ransa cike ya ke da bacin rai da bakin cikin jin cewar Muhseen ya taba ganin Ataa tsirara wani abun yaji marar misaltuwa har yana jin kamar kirjinsa zai rabe biyu, sai kuma ya ji kamar ya danne Muhseen ya cire masa idanuwa. Be san abunda ya kawo shi yau ba ma, gashi yana cewa ba za a tafi da Ataa abuja ba saboda shi da Kamal shi kuma yazo yanzu. Yana faka motarsa harabar gidan sako na shigowa wayarsa, ganin sunan Rahma yasa shi budewa domin baya cikin mood din saurare kowa a yanzu.

_I'm sorry akan abunda ya faru, Mommy ta yi fushi ne sosai shiyasa amman dan Allah ka yi hakuri, kuma ina neman izininka zan tafi Dubai jibi_

“Really?”

Ya furta bayan ya gama karanta sakon.

“You will regret this Rahma ke da iyayenki”

Ya fada sannan ya bude motar ya fita zuwa cikin gidansa, haka ya kwana a gidan cikin wani irin yanayi na bacin rai tsakanin wanda Rahma tai masa da abunda Muhseen ya fada sai ya rasa wanne ya fi masa zafi. Ko da ya tashi da safe kansa kamar zai tsage sabar bacin ran daya kwana da shi jiya, he feel unsafe sai da yai wanka ya shirya cikin wasu tufafin ya dauki hanyar arkilla tun da farar safiya haske ma be gama bayyana ba. Ko da ya shiga falon babu kowa sai ac da wutar da aka kunna, but he got lucky yau Momy a part din ta tai sallah asuba after Daddy ya tafi masallaci ita kuma ta dawo part dinta tai sallah, daman ta kan yi haka wani lokaci wani lokacin kuma acan take yin sallah ta. Tura kofar dakinta yai ya shiga ba dan ya tabbatar tana ciki ba, idan ma bata ciki shi zai kwanta a nan ne for a while hankali zai fi kwanciya ace yana gidan fiye da yana can dabam. Zaune ya same ta saman carpet karbin a hannunta tana ja. Ita kanta ta yi mamakin ganinsa da safen nan.

“Lafiya dai?”

“Lafiya kalau Momy ina kwana”

“Lafiya Kalau, amman ba lafiya na ka zo da safen nan”

Ya yi shiru na wani lokaci sannan ya ce.

“Momy wai Rahma ta turo min sako zata je Dubai”

Da mugun mamaki Momy ta kalleshi.

“Dubai? Da izinin wa?”

“Wai izini take nema”

“Uhmm Wallahi Rahma nan ta maida wani sholobiyo, daman tun farko kai ka nuna mata fita ba da zininka ba ai, yanzu kuma ganshi ba nan, maganinta kamin ta dawo ka auri wata Wallahi”

“Yes nima abunda na kwana da shi a raina kenan”

“Haka ma za a mata, kuma idan zaka bi nawa Ataa na ke son ka aura wacce ta raina take ganin ba komai ba ce”

Kamar saukar Aradu haka Aliyu ya ji maganar Momy, Ataaa Ataaa Ataaa Ataaa sunanta na ta maimaita kansa a kunnensa, da sauri ya kalli Momy.

“Momy Ataa?”

“Yes”

“Amman..... ”

Sai kuma ya mike tsaye ya saka hannayensa aljihu ya daga kansa sama yana shakar iska kamin ya sauke ya juyo ya kalli Momy.

“Momy seriously?”

“Yes don't you like her?”

“I do, but.....”

Sai murmushi ya subuce masa ya shafa kansa.

“Momy ke kike fada min wannan da kanki? I can't believe this”

Murmushi Momy ta yi.

“Do you love her?”

Shiru yai na wani lokaci yana sauraren yadda zuciyarsa ke mugun bugawa with full farincikin da be daga ina yake sauko masa ba.

“Momy wasa dai kike min?”

“Indai tana son ka da gaske na ke yi”

“Zata so ni mana Momy ai ita bata san so ba, zan koya mata komai Momy trust me”

Ya fada yana dukawa ya kama hannayenta duka biyu ya rike, shi kanshi sai yanzu yake jin cewar son Ataa yake yi, duk wani abun da ya dade yana jinsa akanta sai yanzu kullin ya watse a jikinsa da zuciyarsa, domin tun da ta zo duniyarsa sai yake jin kullum kamar a takure yake. ZAKI

By Khadeeja Candy

39...

Kamar an diga man kuli a cikin ruwa mai mugun sanyi haka Aliyu yaji jinin zuciyarsa ya taso yayi tsama saboda kalaman Muhseen.

“Kai Pretty wai kin duba madubi yau ko? Gaskiya Allah ya iya hallita”

Cewar Muhseen yana kara kallon yadda uniform din yai mata mugun kyau kasancewarsa Maroon color, ga gashin kanta data sakawa ribbon ya sauko har bayanta gwanin sha'awa. Ko wace kalma ta Muhseen Aliyu hade ta yake da yawun bakinsa, ba kuma iya yawun ne kawai yake hadewa ba har da abunda yake ji yana taso masa yake dannewa, shi kanshi ya san yayi abunda ba zai iya ba, yana tsaye wani na yaba kyau matarsa.

“A a ba mu da madubi ai”

Ataa ta fada tana murmushi.

“Zo na nuna miki kanki a wayana”

Ya zauna a kujerar da ke kusa da shi yana ciro wayar daga aljihunsa na gaba, bata zauna din ba ta juyo ta kalli Aliyu wanda idonsa ke kan wayarsa tunawa da yace ta daina sakewa Muhseen.

“a a bari na je na duba a Mota”

Ya fada sannan ta fara takawa zata wuce Muhseen ya bi bayanta da kallo komai na jikinta motsi yake a cikin uniform din kasancewarta mai tubultubul kuma uniform din ya dan kama jikinta din jiki ga shi bata da komai a ciki, da gangan yai hanzarin kai hannunsa ya kama gashin kanta ya juyo da ita ta rika yatsun hannunta.

“Pretty ina zoben da na baki...?”

Bata amsa shi ba tai saurin fisge hannunta tana kallon Aliyu hankalinta a tashe kamar wacce za ayi ma wani abu.

“Muhseen....!”

Aliyu ya daka masa tsawa a cikin muryar da shi kan shi be san da zamanta ba.

“Karka sake kuskuren yabon kyau Ataa balle ka ce zaka kai dan iskan hannunta ka taba ta, wannan ya zama na karshe ina nufi na karshe....”

Magana Aliyu yake ma Muhseen cikin tsawa yana nuna Muhseen da yatsansa kwayar idonsa gaba daya ta canja ta rine kamar ba shi ne da farin ido ba, shi kan shi Muhseen sai da gabashi ya fadi domin ya razana sosai da yanayin da ya ga Aliyu. Kamar kyalftawar walkiya haka Ataa ta bace bat a cikin falon kamin ta isa Bq har da gudunta, ganin irin tsawar da yai ma Muhseen da yake kanensa kuma dan'uwansa to ita kan ta san nata dukanta zai yi. Da sauri Momy ta fito daga kitchen tana kallonsu, kannensa ma Amina, Siyama da Husna duk sai da suka fito daga dakunansu jin yadda falon gaba daya yake amsa muryar Aliyu. har be janye yatsansa daga nuna Muhseen da yake ba sai rawa yatsan yake kamar zai da ki Muhseen da hannunsa.Wani irin abu yake ji yana masa yawo cikin jini wanda be taba jin irinsa ba, duk wani kishin Ataa da yake a can baya na yanzu ya ninka shi ninkin ba ninkin, ya yaba kyauta ya janyo gashinta kanta ya rika yatsanta, tunawa da irin kallon da yai mata da kalamansa na jiya sai ya ji kamar an yanga tsagen jikinsa an zubar a kasa, har lokacin Muhseen be iya cewa komai ba banda kallon kallon da suke da juna shi da Aliyu.

“Wai miye haka ne? Shikenan idan kuma abuja hankalin Fulani ya tashi idan kuma kuna nan nawa ya tashi? Wannan wace irin rayuwarce?”

Aliyu ya juyo ya kalli Momy.

“Ki fada masa ya daina shiga gonata”

“In daina shiga gonarka ko ka daina shiga gonata? What kind of nonsense is this, idan ina yaba kyau Ataa ko magana da ita ko taba ta miye matsalar ka da wannan?”

“Babu har sai ka sake”

Aliyu ya fada yana daga masa gira sannan ya fice daga falon zuwa bq.

“It's because tana gidanku?”

Muhseen ya fada a fusace yana bin Aliyu da kallon haushi.

“Muhseen nan mu ba gidansu ba ne, gidanku ne”

“To idan ba shi ba Momy miye ruwansa da ni? Naga dai ba shi da alaka da ita kamar yadda ni ma ba ni da, kuma son Ataa na ke son ta na ke be isa ya hana hakan ba... ”

Amina ta kalli Momy Momy ma ta kalli Amina kamin ita Aminar ta juya ta koma cikin dakinta.

“Na rasa gane kan Aliyu”

Muhseen ya sake fada.

“Ka yi hakuri Muhseen zan masa magana, ka yi hakuri dan Allah”

Maganar da Momy ta masa ce ta saka ya zauna saman kujera yana ta huci da mamakin yadda Aliyu yake son masa fin karfi.

ALIYU POV.

Tafiya yake yana kamar ba kasa yake takawa ba shi kan shi be taba jin kanshi a cikin irim wannan yanayin ba kamar yau. Ji yake kamar ba zai jure wani ya kara yabon kyau Ataa ba, ko da mace ce balle namiji. Yana shiga bq din Ataa ta daka tsalle tana ihu ta yi bayan Nana da ke zaune ta boye gabanta sai faduwa yake ta yi zaton ko dukanta Aliyu ya zo ya yi, duk da bata tsoronsa a yanzu amman tana tsoron yanayin da ta ganshi a yanzu. Yayi kokarin sauke fushinsa ya dan saki fuska sannan ya taka balcony din yana isa bakin kofar dakin da Nana take ciki ya tsaya ya cire takalminsa sannan ya shiga, risinawa yai har kasa kamar jiya ya gaishe ta ya mata ya jiki ta amsa masa fuska a sake Ataa na bayan Nana zaune tana dan lekoshi ta kawar da kai.

“Dan Allah Mama kar a sake bari Ataa ta fita tsakar gidan nan babu mayafi a jikin, kin ga akwai aljannu masu shiga jikin mutum gidan be rufe jiki ba, ko ka rufe ma ya aka kwashe balle kuma ba a rufe din ba? Yana da ta rika rufe jikinta da gashin kanta”

“In-Sha-Allah zai rega sakawa, muna goziya jiya kaya sun zo masu kyau Allah ya biya”

“Amin”

Yana amsawa da amin ya mike tsaye yana watsawa Ataa wata uwar harara domin mugun haushinta yake ji kamar ita tace Muhseen din ya kama hannunta ya rike, ita kuma ta murguda masa baki ta buya bayan Nana.ATAA POV.

Yana fita na fito daga bayan Nana na zauna daidai ina turo karamin bakina.

“Wai shi baya son ya ga wani na min far'ah ko muna wasa ko magana, ya fi son ya gan ni cikin bacin rai, idan yaga wani ya sakar min fuska ji yake kamar an masa ruwan mutuwa a zuciya”

Da yaren buzanci na fada cikin mugun jin haushinsa. Dariya Nana ta yi tana kallona ta ce.

“Tunda ba ya so ai sai ki daina, namiji baya jindadi idan yana ra'ayin mace yaga wani namijin na kula ta”

“Wacan zai ra'ayina? Wallahi duk ya bi ya tsane ni ban san abu da nai masa ba, bayan ma ni na fi dacewa na natseshi”

“Ki tsane shi aka ce mi? Ai baki da wata hujja ta tsanarsa, domin ya gama mana komai a duniyar nan”

“Haushi na yake ji kila ma dan yaga na fi shi kyau ne, sai wani ji da kan banza, kuma sai na kula Muhseen din haka kawai sai na yi ta shiga kunci ina bakin rai kamar shi, haka jiya ya kori mai koya min karatun nan da ya zo, wai ya cika far'a ya fi son ya ga ina ta bakinciki, shi fa dariya ta bakinciki take saka shi mtchhhhhhh”

Na karasa ina jan tsake har ga Allah yau kan Aliyu ya ba ni haushi, ban san abunda na tsare masa ba yake bakincikin ganin dariyata, wani lokacin ma sai yai ta abu kamar ba shi ba, dazun da naje tambayarsa ai dariya yai min, jiya yai min siyayya har ina jindadi amman yau ya canja kamar ba shi ba. Murmushi kawai Nana take tana kallona kamin ta koma murza yatsun hannunta.

“Yanayin yaron nan yana tuna min da mahaifinki, haka yake kishi a lokacin da yake so na, ni kuma ina kishinsa saboda kyausa, idan yayan manyan sarakai suka zo nema na ranar ba zai yi bachi ba, saboda yana jin kamar zai rasa ni”

Ta fada da yaren buzanci hawaye na sauko mata, sai na kara matsawa kusa da ita na kwantar da kaina jikinta, sai ta shafa kan nawa hawayenta na sauka a kumatuna.

“Mutuwa ba tai kyau ba”

Ta fada da hausa tana son fashewa da kuka. Nima hawayen na soma yi tunawa da Baba na na san da yana raye duk wannan rayuwar ba mu shige ta ba, balle har Aliyu ya nemi takura domin Babana yana so na sosai. Ganin ina hawaye yasa tai saurin share nata kukan tana dariya kamar ba ita ba.

“Yana can cikin rahamar Allah In-Sha-Allah”

“Eh Nana yana cikin Rahama Allah ya jikanshi”

“Amin”Sanye da uniform Siyama ta kawo mana abun karyawar mu bayan ta gaisa da Nana ta fito daga bangaren mu ni kuma na biyota ina tambayarta ko nima zan iya zuwa makarantar.

“A a yau ba a zuwa sai da yamma, ai ita Islamiya sai assabar da lahadi kawai ake zuwa da safe”

“Na sani, amman na ga wata islamiyar idan mutum baya zuwa makarantar boko sai ya tafi islamiyar safe”

“Wannan ba a zuwa”

“Sai kin dawo Allah ya tsare”

Na fada ina kallonta gwanin sha'awa, sannan na juyo na dawo bq din na soma cire uniform din ina tunanin maganar Nana ta dazun wai idan yayan manyan sarakuna suka zo sai yai ta kishi, lallai Nana ta yi farin jini tunda har da yayan sarakuna sukai nemanta.

MUHSEEN POV.

Yana zaune a falon har Aliyu ya fito daga bq ya shiga motarsa ya dauki hanyar gida. Tunani yake ta yi yadda Aliyu ya zo rana tsaka yake son hana shi kula Ataa, idan ma wai wani sonta yake to shi mai gaba daya zai yi idan take takensa kenan shi zai fito kai tsaye ya aureta ya ga yadda zai yi. Har Momy ta gama hada breakfast din ta zubawa Siyama ta kuma zuba na su Nana ta bawa Siyama ta kai musu Muhseen na zaune a gurin be huce ba, a dinning ta jera sauran ta fada masa ya tashi ya karya sannan ta wuce bangare Daddy dan kai masa na shi su karya tare. Bayan ta gama da Daddy ta sallame shi ya wuce gurin aikinsa ta dawo part dinta sai ta samu Muhseen zaune a dinning shi kai yana cin plantain a hankali kana ganinsa kasan hankalinsa baya jikinsa, shi kai ne a dinning din hakan na nufi Amina da Husna sun gama karya sun tafi shi kuma ko rabi be yi ba. Sai da Momy ta kai kulolin data dauko part din Daddy kitchen sannan ta dawo dinning din ta ja kujerar da ke fuskantar ta Muhseen ta zauna.

“Ba ka ci abincin ba?”

“Momy ina tunanin ya kamata na fadawa Abbah da Daddy zancen Ataa kara su san da maganar, idan ma karatun za tai ko wani abu sai tai a gidana, ko waje ta kama sai a fitar da ita ai”

Momy ta dan yi shiru na waji lokaci tana sauke ajiyar zuciya. Kamin ta kalli Muhseen a natse ta fara magana.

“Shekaranjiya na tafi gidansu Rahma gurin bikonta, wai ta yi yaji ta tafi gida saboda mijinta na kula Ataa, nemawa mahaifiyarta magani da zuwa dubata da yake sai Rahma ta dauka son ta yake, shi ne tai fushi ranar da na je bikonta ni da kawata babu kalar maganar da mahaifiyarta bata fada min ba saboda Ataa, tana kiranta da yar talakawa yar bara a titi wai yar su ba za ta yi kishi da Ataa ba”

Tun da Momy ta soma maganar Muhseen yake kallonta dan shi be ga ta inda wannan abun ya shafe shi ba, domin ba matsalar wani ce yanzu a gabansa sai ta shi.“Gaskiya Rahma bata kyauta ba, kuma be dace tai haka ba, cewa akai Aliyun son ta yake ne?”

“Ni kaina ban jidadin abunda mahaifiyarta da ita Rahma kanta su kai na tun farko, kuma ina tunanin tana wannan abun ne saboda tana ganin it kadai ce a gurin mijinta, shiyasa na yanke shawarar...”

Sai ta kasa karasawa kamar mai jin nauyi. Muhseen ya kashe kunne sosai ya maida hankali yana saurarensa, main reason din yake son ya ji domin ya fara fahimtar inda zancen Momy na dosa.

“Shawarar me?”

“Wata kila Fulani ba zata bari ka auri Ataa ba, ko kuma idan ka aureta ta gallaza mata, ko wani abun ya samu kyauta wanda zai iya sakawa wata rana ka sabu da ita ko musguna mata, amman ina da tabbacin Aliyu ba zai iya juya mata baya ba ko da baya sonta saboda ya san hakkin aure, kuma mutumen da ya zauna da Rahma zai iya zama da ko wace irin mace a duniyar nan, duk wani guri da fada na Rahma da mahaifiyarta akan Ataa ne shiyasa na yanke shawarar Aliyu ya aureta ko dan gorin da suke mata na kuma nuna musu na isa da shi...!”

Wani irin abu ya ji ya daki kirjinsa sai yai murmushi yaja numfashi ya sauke.

“Ya fada miki cewar son iskanci nake wa Ataa ke nan? Kuma kin yarda duk da kin san ni bana neman matan banza, dan na ce ina son Ataa saboda tana da kyau ai ban yi laifi ba, kina tabbaci idan bata da kyau Aliyu ma zai so ta? Kina da tabbacin shi din Mama Fulani zata bar shi ya aureta? Kawai dai kin nuna ke kika haifi Aliyu da kanki kuma kin nuna masa son kai, kuma Ina masa farincikin samun uwa kamar ki wacce zata so abunda danta yake so har ta fishi son abun”

Yana fadar hakan yaja kujerarsa baya ya mike tsaye. Tuni idon Momy ya cika da kwalla zuciyarta kuma tana mata babu dadi.

“Allah shine shaidata, ban aikata hakan dan nuna son kai ba, sai dan ganin kamar Ataa zata fi samun kwanciyar hankali idan ta aureshi, kuma Rahma ta raina kanta gudun yar talaka sai ta ga ta aure mata miji ma gaba daya, idan har bana son ka ba zance Amina ta aureka ba, ba zan baka yar cikina ba Wallahi ban rike wani dabam ba, kai da Aliyu duka daya ne a gurina, na dauke dana wanda zan iya sakawa na hana, na zaba masa ko na canja masa zabi”

Juyowa Muhseen yai ya kalleta.

“Ashe kin dade da yanke hukunci kika barni ina da lalabe cikin duhu, ni da Aliyu ba daya ba ne a gurinki da ni ma kin dauke ni da da kin hana Aliyu son Ataa ko da zai mutu kin ba ni, domin na fishi sonta kuma na fi cancanta na aureta fiye da shi ita kanta idan kika tambaye ta zata fada miki ni take so, kin sani Momy na tun yau ba ina son Ataa amman yau ni za ki zauna a gabana ki fada min gaskiya cewar kin ba danki ita, good luck wish you all the best”

Yana fadar hakan ya fice daga falon a fusace, ya bar Momy tana aikin hawaye.Sai a yanzu take jin cewar bata kyauta, sai a yanzu take jin girman kuskuren da ta aikata, da tasan cewar Muhseen ba zai fahimce kamar haka ba da bata aikata ba tun farko. Fashewa tai da kuka a gurin ta tashi da sauri ta shige dakinta, Husna da Amina suka fito suka bi bayanta jin kukanta hankalinsu tashe.

“Momy lafiya?”

Husna ta tambaya tana zama kusa da ita.

Readers Also Read