Kenza eBookz

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 49

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 49

Zaki complete by khadeeja candy Chapter 49: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 49. “Allah ga Rahma nan, baiwar ka ce Allah yau ta dawo gareka aron ran…

4,415 words

“Allah ga Rahma nan, baiwar ka ce Allah yau ta dawo gareka aron ran da ka bata yau ka karbe abun ka ya Allah, Allah ina son matata ka sani, ita kuma tana so na, mun yi zaman aure da ita na shekaru tsabanin da muka samu atsakanina da ita na rashin jutuwa ko fada ko bacin rai da gangan ko cikin rashin sani Allah ka shaida na yafe mata, Allah kai ma ina rokon ka yafe mata, Allah jinyar da tai kasa ta zama sanadin tsira, Allah ka sadata mala'ikunka na Rahma ka sadata da Annabin Rahma, Allah ka hada ni da matata Aljanna”

Wannan karon be iya rike kansa ba ya fashe da kuka sosai kamar mace, har sai da aka shigo aka fita da shi, hankalin kowa be kara tashi ba sai da aka fito da ita akai mata sallah aka dauki gawarta zuwa makabarta inda gidanta na gaskiya yake kuma gidan kowa. Muhseen ne rike da Aliyu har aka kai makabarta aka saka ta cikin kabarinta, wa zai iya fadar yadda cikin kabari yake? Babu iyakar abunda ido ya gani ko ya ji a duniya ne kawai, the first thing da aka saka bayan gawar Rahma itace sannan aka saka tukane sai haki da ciyayi ya biyo baya, haka aka lullube kabarinta da kasa sai aka tabbatar babu wata kusurwa da wani abun zai iya shiga sannan aka kewaye kabarin ana mata addu'ar neman Rahma. Sannan aka taso aka baro ta can ita kadai daga ita sai aikinta. Gida aka kawo ana karbar gaisuwar, Momy kuma ta bukaci Aliyu ya koma gida su a can su yi na su karbar gaisuwar. Har lokacin Mama Fulani da Nasir ba su iso ba saboda mota suka biyo ba su samu jirgin da zai taso yau. Aliyu na kusan shiga motarsa Ikram ta zo ta miko masa wata wasika, idonta yayi ja sosai.

“Minene?”

“Ita ta rubuta ta, a lokacin da ka kirata bata iya magana ta miko min, na tambayeta ta waye tai min alamu da kai zan bawa”

Kallon takadar Aliyu ya rika yi na few minutes kamin ya kai hannu ya karba jikinsa na ta rawa. Sannan ya nufi motar ya shiga, Muhseen ne ke tukawa har suka isa gida sai taba takardar yake ya kasa budewa. A can gurin Momy ma an cika da mutane yan'uwan Daddyn da Momy, har Daddyn da kansa da wasu abokansa da suke kusa da kusa suna tare, har da yan'uwan Mama Fulani da suke yola wadanda suka zo ta jirgi. duk wanda ke gurin tausayin Aliyu yake, sai da magariba Mama Fulani ta iso ita da su Maryam da Ammy gaba daya gidan aka kwashe ba a baro kowa ba. After Sallah isha'i Aliyu ya shiga bangarensa da ke cikin gidan ya kulle kansa a cikin dakin ya bude takardar cike da fargaba ya fara karantawa.

_Zaka karanta wasikar nan ne wata kila, bayan ba raina domin na san ba sakan cewa ina asibiti ba, da farko zan fara taya ka murnar samun haihuwa da kai, kuma nai maka godiya na rufa min asiri da kai da hakurin zama da ni na tsawon lokaci, ina jin a jiki kamar ba zan rayu ba wani lokaci ba, amman ina rokon yafiyarka kuma ka nema min yafiyar Ataa da yafiyar Momy da duk wani wanda ka san na taba alaka da shi, ka nuna min soyayyar gaskiya Aliyu ta hanyar yi min addu'a bayan raina, Allah ya hada fuskokin mu a aljanna. I love you so much ina maka fatar alheri a sabuwar rayuwar da ka fara da Ataa, na san ka nuna min so, amman ni yanzu tawa ta kare, ka yafe min Aliyu kuma ka yafe wa mahaifiyata so na ne ya saka ta aikata maka komai, ka yi hakuri na san kana so na amman babu wanda ya iya kaucewa mutuwa, tarin dukiya ko lafiya bata amfani mai ita ba matukar mutuwa ta kusance shi, ka yafe min Aliyu_

Fuskarsa shakaf da hawaye ya gama karanta wasikar. Kansa kamar zai bare idonsa ya kumburo kamar ba na shi ba.

“Na yafe miki Rahma na yafe miki, Allah ma ya yafe miki”

Ya furta sannan ya mike tsaye ya shiga bandaki ya wanke fuskarsa ya fito harabar ya memi Abbah, can gefe ya koma da shi ya karbi number Mai Martaba saboda yana son kiran Ataa ya nema ma Rahma yafiyarta. Dakinsa ya dawo sai da ya fara gaisawa da Mai Martaba sannan ya gabatar masa da bukatarsa, sannan ya kashe wayar bayan Mai martaba ya tabbatar masa da za a fada mata, after like thirty minutes aka kira shi da line orange na can nijar wata bakuwar number wacce ba ta Mai Martaba ba.

Yana yin picking ya ji muryar Ataa kasa kasa kamar marar lafiya, sai da suka gaisa ya tambaye ta ko bata jindadi ne ta fada mishi lafiyarta kalau.

“Ya jikin Rahma?”

“Babyna jiki da sauki sosai ta ce a fada miki tana gaishe ki kuma na nema mata lafiyarki, tsabanin da kuka samu a baya”

Aliyu yayi kokari wajen ganin yayi magana da ita normal ba tare da muryarsa ta canja kuma ba tare da nuna akwai damuwa a tare da shi ba, sai dai kana jin muryar kasan baya cikin walwala. A maimakon Ataa ta tace ta yafe mata sai kawai ta fashe da wani kuka da cikin wayar har Aliyu ya kasa saurare ya kara wayar a kirjinsa yana hawaye.

Mutuwa....! 💔 Allah kai mana kyakkyawan karshe, Allah ka jikan Babana da Rahma😭😭😭😭💔

*AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta. Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.* Kuka na ke sosai jikina na raya min cewar Rahma ta rasu daman tun a lokacin da ya tafi na ke jin ba dadi, yanayin yadda na ji muryarsa ma na san ba lafiya ba, domin alamu ya nuna ba ya cikin walwala duk dai ban san ainahin abunda yake damunsa ba, sai dai jin cewar Rahma na neman yafiyata na san mutuwa ce kadai zata saka ta neman yafiyata, idan kuma ba haka ba, wata kila kuma Aliyun ne ya nema mata da kansa saboda ta mutu.

“Babyna kukan ya isa haka”

“Hamma ba a boyon mutuwa, idan ma ta mutu da gaske ba zan iya dawowa da ita ba, kuka ba ya dawo da wanda aka rasa, da yana dawowa da ya dawo min da Babana da Lukman, amman duka na rasa su kuma kuka da bakinciki be dawo da su ba, zan yi kuka saboda tausayinta ne da kuma kai”

“Bana son kukan ko tunanin ya janyo miki wata matsala, ke kadai kika rage min a yanzu sai abunda yake cikinki, idan na kara wani rashi ban san ya zan yi ba, rashi akwai ciwo sosai gashi ba zaka iya dawowa da wanda ka rasa din ba, akwai ciwo sosai ka rasa wani abun da kake so a lokacin da kake tsananin bukatarsa, akwai ciwo rabuwa da abokin rayuwa da ka shirya yin rayuwa da shi”

Hannu na kai na share hawayen fuskata, na san yadda Hamma yake ji saboda be taba rasa kowa ba a rayuwarsa sai yau, mahaifiyarsa mahaifinsa duka suna raye, wani karin gatan ma sai Allah ya kara masa da Mama Fulani da Abbah duk shi kadai, ni ko na san zafin rashi saboda na rasa mahaifina da dan'uwana kuma na san zafin babu saboda ana tashi a cikin babu din, shi ko be san babu ba sai akwai kuma be san zafin rasa komai ba a rayuwarsa sai yanzu.

“Fada min kina nan lafiya kalau”

“Lafiyata kalau, kuma na yafe mata abunda tai min wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah ya jikanta yai mata Rahma”

“Amin na gode, cikinji fa yana lafiya?”

“Komai lafiya kalau, zan fadawa Mama yanzu”

“Okay ki kula min da kanki pls”

Na gyada kai kamar yana gabana sannan na aje wayar akan gadon na zauna bakin gadon ina ta kuka, ban taba tsammanin jin labarin mutuwar Rahma zai sakani shiga damuwa ba balle har nai kuka, amman sai ga ni ina kuka kamar wacce na rayu da ita na tsawon lokaci na shaku da ita, a yau duk wata kiyayya da kishi da jin haushi ta kare, mai rabawa ta raba. Kaico mai rai ba abakin komai yake ba, lokaci daya idan Allah ya so kama ka sai ka raina kanka har makiyinka ya tausaya maka. Sai da na ci kuka na koshi sannan na fito falon Hajiya wato kakana idona a kumbure da kuma sauran hawaye na nufi inda Hajiyar take zaune na mika mata wayarta wacce ta ara min na kira Hamma da ita.

“Lafiya kike ko?”

“Rahma ce ta rasu”

“Wace Rahma?”

“Matar Hamma”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”

Shine abunda ya fito daga bakin Mama tana dafe da kirji, na san ta ji mutuwar kamar yadda na ji, abun kamar daga sama kuma babu dadi ko kadan. A nan suka shiga tambayar wacece ita, Mama ce ta fada musu ni kan sai wani sabon kukan ya kubuce min, har ga Allah ban jidadin mutuwarta ba, dan tsabanin da muka taba samu da ita sai ya dawo min sabo ina ta ganinta a fuskata. A cikin dare aka fadawa Mai Martaba halin da ake ciki na mutuwar Rahma, a waya ya kira Daddyn Rahma yai masa gaisuwa da kuma Abbah da sai aka sadashi da Daddyn Hamma shi ma yai masa gaisuwa sannan yai ma Hamma din, mu kuma aka ce mu shirya domin zuwa gaisuwa, a daren ban yi banchin kirki ba saboda tunanin Rahma ina ta ganin kamar ba da gaske ne ba, sosai na ji mutuwarta kamar wani ginshike nawa na rasa, har na soma jin ciwon kai na kama ni, da safe sai ga ni da mura, tun da nai sallah ban koma ba bachin ba, saboda tunani ashe Allah be yi zamu zauna a guri daya ba, balle ma na ga kishinta domin ni dai bana jin ina da kishin ma amman na san nata na musamman ne a yanayinta da yadda na karanci halinta. Ko da goma tai dukan mu muna airport, wani abu sai kudi, babu zancen siya mana tickets na zuwa Nigeria, da jirgin Mai Martaba muka tafi, ni, Mama sai kuma wasu cousins dinta mata biyu, maza biyu wadanda Mai Martaba ya turo su walkice shi su yi masa gaisuwar. Mun sauka sokoto cikin lokaci wani abun burgewa muna sauka motocin da za su dauke mu suka iso, a wani gidan suka so su kai mu mu huta kamin muje gaisuwar sai Mama da kanta ta ce a sauke gidan Momy su kuma Mazan sai su tafi can din su huta, haka kuwa akai ni da ita da wasu yayyunta mata aka sauke mu gurin Momy su kuma mazan aka wuce da su. Mun tarardar gidan da taro sai dai ba taro irin nan farinciki da walwala ba, domin kana kallon fuskarta duk wanda ke gurin kasan ba taron jindadi ne ya tara su ba. A cikin gidan kuma mata yan karbar gaisuwa, ganin taron ya karya min guiwa na san nima wata rana haka za'ayi nawa, ayi na kowa. Husna da Siyam su kai mana lale marhabun duk da kasancewar suma basa cikin walwala sosai sai dai sun yi murna da ganina suna ta dauki ba kuma murna na marmari na kawai ba har da murnar cikin da na ke da shi. Mama Fulani kan ba wani sakewa sumi sumi da ita kamar ta Allah, Ammy da duka yaranta suna nan, har ma da su Maryam da Rukaiya duka suna nan. Kar ka so ganin yadda Momy taks ta kokarin dawainiya da ni, sai kace wata mai tsoron ciki ko kuma wacce bata iya komai, abinci ma idan za a kawo min sai an tambayi wanne na ke so gudun kar a kawo min mai saka ni tashin zuciya. A ranar kawunai na da Mama suka koma da kuma cousins din da suka rako Mama, bayan sun yi gaisuwar a can bangarensu Iyayen Rahma, ban za ci Mama zata iya zuwa tai gaisuwar rasuwar Rahma ba, sai gashi ta maida komai ba komai ba, kana kallon mahaifiyarta zaka san a firgice take, irin figirtar nan na rasa wanda kake so a lokacin da ba kai tsammani ba, mahaifinta kan ya sha jinin jikinsa kamar ba shi ba, sai kallona suke ta yi daga shi har Mommyn Rahma. Bayan mun dawo daga gaisuwar ne su suka kama hanya, ni kuma aka bar ni nan a gurin Momy wai sai an gama karbar gaisuwa. Ina zaune saman carpet ni kadai a dakin ina salatin Annabina na ji shigowar mutum, ban waiga ba amman na san ko wanene tun daga kan kamshin turarensa, ta kuma yadda yake takowa zuwa inda na ke a hankali har ya iso. Ji nai an rumgume ni ta baya, sai na sauke ajiyar zuciya a hankali ni kaina na san na yi marmarin Hamma sosai tun a lokacin da na zo garin nan idona suke kai kayin ganinsa, amman ban saka shi a idona ba ko gaisuwar da su Mama da yan'uwanta suka masa ina kyautata zaton sai indai a can gidansa suka same shi ko kuma ya shigo ni ban ganshi ba ya fita domin tun shigowata gidan ban ji ko alamun motsinsa ba sai yanzu. Gafen kumatuna ya sumbata.

“Fada min kina nan lafiya?”

“Lafiya kalau, tun dazun muka zo amman ban ganka ba”

“Ina ta kokarin boye kaina dan kar na yi arba dake har sai idan ke kadai ce, saboda ina mararin na rumgume ki na jiki a jikina kuma ba zan iya haka abun a agaban mutane ba”

Ya fada ba tare da ya sake ni daga rumgumar da yai min ba.

“Mama ta tafi”

“Na sani na gode da ta bar min ke”

Mun dauki lokaci a haka yana rumgume da ni ta baya, sannan ya sake ni ya mike tsaye ya zauna bakin gadon Momy, juyowa nai na kalleshi sai wani irin kaunarsa da tausayinsa suka dirar min a zuciya lokaci daya, ya rame sosai kamar ba shi na har idonsa sun fada kamar marar lafiya.

“Hamma baka cin abinci?”

Kallona kawai yake ba tare da yace komai ba.

“Bari na saka Husna ko wata ta hada maka wani abu ko kuma idan akwai fura ka sha idan baka son abu mai nauyi”

Ina mikewa tsaye sai ya riko hannuna ya dawo da ni kusa da shi ya zaunar ya ja ni zuwa kirjinsa ya rungume ya lumshe ido, ina jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.

“Na gode Allah da be dauke min Rahma ba sai da ya ba ni ke, kuma yai min tukuici da wani dan ko ya, ni kada na san halin da na ke ciki kuma ni kadai na san iya abunda na ke ji a zuciyata”

Ya fada yana kara matseni a kirjinsa, rashi akwai ciwo sosai na san irin yadda Hamma yake ji a yanzu saboda ni ma na taba rasawa ba ma sau daya ba. Sai da ya ji kamar muryar wata a kusa da kofar dakin sannan yai saurin sakina ni kuma na mike tsaye cikin tsoron kar wacce ke maganar ta shigo ta gan mu a tare. Wata kanwar Momy ce ta shigo dakin da sallama ni na amsa mata sai ta miko min kofin fura.

“Ga shi inji Yaya ta ce ki sha”

“Na gode”

Na fada bayan na saka hannu biyu na karba, sannan ta juya ta fice. Zaunawa nai kusa da Hamma na mika masa furar wacce aka damata da kirdirmon nono.

“Ka sha”

Ba min musu ba, ya karba ya sha sai dai ba da yawa ba, ya mikon min sauran.

“Shanye”

Na sha rabin kofin sai na aje ina ta kallonsa, gaba daya ya koma kamar ba shi ba, so silent fuskarsa ma abun tausayi kallo daya zaka masa kasan cewar mutuwar Rahma ta taba shi ba kadan ba, ni ma da ban saba da ita ba ta taba na shiga damuwa kuma nai kuka balle kuma shi da yake mijinta kuma su kai rayuwa da ita.

“Ina auna yadda kika rasa babanki da dan'uwanki ne, kuma ki kaita dawainiya da mahaifiyarki, gaskiya Ayusher kin yi kokari kuma ke jajirtacciya ce, wani lokacin ana jarraba bawa saboda a gwada imaninsa da kuma irin hakurin da zai yi, ban yi tsammanin tunanin Rahma zai addabe ni kamar haka ba bayan rayuwarta, amman idan na tuna ki da abunda yake cikinki sai na jidadi kuma nai ma Allah godiya”

Ya fada a hankali yana ta kallona da murmushi a fuskarsa sai dai ba murmushin farinciki ciki ko na jindadi ba irin murmushin nan na godiya ga Allah da kuma jin zafin wani abun a lokaci daya. Shigowar Momy ce tasa na dan ja baya shi kuma ya mike tsaye yana saka hannayensa aljihu ya fice, ni da Momy da kallo muka bi shi har ya fice sannan Momy ta karaso cikin dakin ta dauki kofin furar da ta aiko min tana dubawa.

“Ba ki shanye ba?”

“Eh na sha rabi”

“Ki daina barin kanki da yunwa, na san ba za ki iya cin abu mai nauyi ba wata kila shiyasa na tanadar miki da furar”

“To Momy”

“Zauna”

Ta nuna min kujerar da ke facing din gandon, bayan na zauna sannan ita kuma ta zauna bakin gadon.

“Ataa ki matar aure ce a yanzu ina fatar kin san da haka?”

Na gyada masa kai ina maida idona kasa.

“Ke yarinya ce na sani, amman daga lokacin da kikai aure zancen yarinta ya kare sai dai a kira ki yarinya saboda shekaru ko kuma wani abun da za ki na shirme ko rashin tunani, ballantana yanzu da kike dauke da juna biyu”

Na kasa yin kasa da kaina saboda kunya.

“Mijinki na bukatar kulawarki a yanzu fiye da ko yaushe, na san ba ki san wata dawainiyar ba, amman kula da abincinsa ya ci ko be ci ba yana wuyanki a yanzu, karki zamana shi kadai zai dinga damuwa da ke, mijinko ya rasa daya abokiyar rayuwarsa hakan kuma ba karamin jefa shi yai a matsala ba, sai da taimakonki zai iya dawowa dai da ya manta komai kamar be faru ba, ki shimfida masa kalar rayuwar da kike son yai kuka ya bi saboda yana tsananin son ki ni na sani, na san ke ma kuma kin san da haka, ki rika yi masa abunda zai kwantar masa da hankali da saka shi natsuwa, hakan ba karamin kara mishi son ki zai yi, a yadda yake damuwa da ke kuma yake son ki idan kina nuna masa damuwarki akan rashin cin abincinsa zai ci saboda gudun damuwarki kuma zai sa ya rage damuwar, tun da akai mutuwar bana jin ya saka wani abu a cikinsa har yau sai ruwa, sannan ki rika yi ma mijinki addu'a a duk sallah musamman a sujadar karshe da kuma bayan tahiya kamin ki sallame, mace mai aure ma ba akarbar addu'arta har sai idan tana yi ma mijinta da kuma iyayenta”

“In-Sha-Allah Momy”

“Kuma ke ma ki kula da kanki, wani abun ba sai ance ki yi ba, ya kamata ace kin san aure kike a yanzu, kuma ke ce kadai a gurin mijinki, mijinki na bukatarki a yanzu fiye da ko yaushe, ina fada miki wannan ne saboda na san zaki iya kuma ke kadai na ke da tabbacin za ki saka shi cikin walwala a yanzu, mijinki be iya so ba, be iya ki ba, ba kuma iya sakawa rai abu ba, idan yana so gaba daya yake so baya ganin aibun abun har sai yayi zurfi a ciki, idan kuma ya tsane abu gaba daya yake tsanarsa baya iya ganin kyaun abu har sai yayi nisa a tsanarsa, idan kuma ya sakawa rai abu yana sakawa sosai ta yadda rashin abun nan zai yi ta damunsa yana cinsa a rai, daga ke har shi ni duk kallon yara na ke muku wani abu dole sai an nuna muku, saboda mun fi ku tunani da hangen nesa, na san ba ki yawance a komai ba, sai dai ke din jajirtacciya ce saboda gwargwarmayar rayuwa da kika sha, da kurciyarki kin fuskanci kalubale kala kala na rayuwa kamin yanzu, kuma da Allah ya tashi miki sakamako sai yai miki duka a lokacin da kike bukatar hakan, hakuri yana da kyau kuma yana da riba sosai duk wanda yai hakuri be ga riba ba to kadan yayi”

Sosai na jidadin magangannun Momy, a natse ta fada amin komai kuma na fahimci manufar da nufi, daga lokacin na sakawa kaina zan iya, kuma na fara jina a matsayin mace mai aure mai daraja wacce zata iya kula gidanta da mijinta da kuma yayanta duk kuwa da irin karancin shekaruna. Idan na waiwaya baya kadan na tuna abunda ya faru da ni irin halin rayuwar da muka shiga da fadi tashi da nai sai na ga wacan rayuwar kamar labari aka ba ni ba ni ce na wanzu a cikinta ba.

“Tashi ki bi mijinki ku kwana a can”

Maganar Momy ta katse min tunanin da nake.

“Ba ki bukatar komai dai ko?”

“Babu”

Na fada ina mikewa tsaye na dauki Hijabina na saka, sannan na fara takawa a hankali har na fito falo.

“Matar yaya ina za ki je?”

Siyama ta tambaya tana kallona da murmushi a fuskarta.

“Gida zamu je”

“Ba anan za ku kwana ba?”

“Eh”

Na amsa mata muryarta da kamar damuwa. Sannan na karasa kusa da Mama Fulani na dan risina na ce mata.

“Mama za mu tafi gida sai gobe”

“To Allah ya tsare”

Ya mayar min tana kallona, sannan na karasa gurin Ammy ita ma nai mata sallama da wasu kannen Momy da yan'uwan Daddy sannan ya fito harabar gidan. Na yi mamakin ganin Muhseen tsaye jikin motar Hamma yana magana da shi, ban san mi yake fada masa ba na ga dai Hamma ya gyada kai sannan ya bude min gaban motar tun kan na karaso.

“Ataa”

Kiran da Siyama tai min ne yasa na juyo sai ta nufo ni da yar karamar dogowar kular silba a hannunta.

“Ga shi wai Momy ta ce ku tafi da shi”

“Mun gode”

Na fada bayan na karba, ko da na juyo ban ga Muhseen ba balle mafarinsa sai Hamma tsaye yana ta kallona har na karasa, hannu ya kai ya karbi kular hannuna sannan ya matsa daga jikin motar wanda hakan ya bani damar shiga ciki na zauna shi kuma ya rufe motar, ya zagaya bangarensa ya shiga yai ma motar key. A hanya ya rika tambaya ko ina son wani abu, sai na ce masa bana bukatar komai, amman duk da haka sai da ya tsaya ya siya min gassashiyar kaza da yoghurt.

“Bana jin yunwa fa”

“Za ki iya bukata da dare ai, kuma ba dan ke kadai na siya ba”

“Dan wa?”

“Babyna”

Ya fada min fuskarsa babu walwala. Har muka isa gida ban sake ce masa komai ba shi ma kuma be ce min ba, har sai da ya faka motar na kai hannu zan bude.

“Tsaya ba ri na bude miki”

Fita yai ya zagayo gefena ya bude min motar na fito sannan ya rufe, ina gaba yana bayana har muka shiga cikin falon, sai ya zauna saman cushion yana ta kallona.

“Na hada maka ruwan wanka?”

“Zo nan”

Zuwa nai na zauna saman kafafuwansa kamar yadda na bukata sai ya rumgume yana sauke ajiyar zuciya a hankali sai dai hakan be hana ni jin saukarta. Mun dade a haka kamin ya barni na daga jikinsa mu shiga daki, rumguma a cikin abunda Hamma ya ke so kuma ni ma nake so domin ina jin natsuwa sosai idan ya rumgume ni hakan kuma yana kara min jin son kusanci da shi sosai. Cikin jikinsa na kwana kamar kullum sa'a daya nai ban farka cin abincin dare kamar yadda na saba ba. A lokacin da muka gama sallah asuba kuma sai na nufi kitchen na bar a dakin yana karatun qur'ane ni kuma na shiga na kunna gas din na sarrafa dan abunda na iya na ruwan zafin tea da suya wainar kwai da dankali sai kuma doya, sannan na bude kular da Momy ta ba mu jiya, farfesun kayan ciki ne a ciki, sai kawai na dora su akan wuta na dumama na juye a wata kular.

“Wow da kanki kike girki, na fada miki bana son wahalar nan da kike miyasa ba ki jin magana”

“Dan na yi aiki ba komai cikin zai yi ba, kuma ni bana son abincin waje”

“To amman sai ki bari idan na gama karatu Quranen na hada ko?”

“Bana son girki na namiji”

Wannan karon yayi kokarin fadada fuskarsa da abunda ya rasa daga lokacin da akai mutuwar nan zuwa yau wato murmushi shi ma kadan.

“Kin taba jin inda da zai ce baya son abincin babansa”

“Haka dai yace wai babansa be iya girki ba, idan ma yayi babu dadi shiyasa nake turo min shi nai amai”

Na fada ina yatsina fuska, sai ya kara matsowa kusa da ni ya rika hannayena.

“Karki masa karya, na san ba zai ce haka ba, ta ina ma kika ji ya ce haka? Yaushe kika iya karya”

“Yanzu”

Na fada da kamar kunya, sai yai murmushim gefen fuska yana aje numfashi. Shi ya taimaka min na karasa hada komai, sannan muka karya, be wani ci da yawa ba shi ma kuma dan na matsa masa ne, ni kan na ci abincin sosai kamar wacce ta kwana da yunwa, ni kaina har mamakin yadda na ke cin abinci sosai na ke kamar ba cin lafiya ba.

*** *** ***

Readers Also Read