Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 9
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 9: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 9. Na fada ina nuna shi da yatsana, mamaki ya cika Rahma, mijinta kuwa…
4,490 words
Na fada ina nuna shi da yatsana, mamaki ya cika Rahma, mijinta kuwa kallona kawai yake sai kuma ya kalli Doc Asim kamar mai son tantance abu. Doc Asim ya jinjina kai yana kallona yai kwafa.
“Ni kika mara? Sai kin yabawa aya zakinta, ni ban sanki ba ban san inda kika fito ba amman sai na nuna miki ko wanene ni”
“Babu abunda zaka nuna wanda ban san shi ba, na sanka na san zalincika tun har ka iya cire kodar mahaifiyata ba tare da saninta ba, saboda kawai ka maida ni zahila marar galihu, ka sa na saka hannu kai mata aiki ka cire mata koda, kuma kasa aka kulleni a gidan yan sanda saboda na nemi hakkin mahaifiyata, to wane zalinci zaka nuna min da ya wuce wannan? Idan kashe ni kaka son yi, to mutum baya mutuwa biyu, domin ni na dade da mutuwa tun daga lokacin da kasa mahaifiyata ta rasa lafiyarta, sanadin haka na rasa kanena, to me zaka min yanzu? Duk abunda kake jin zaka iya yi kaje kai, ba a duniya za a tabbata ba, akwai kiyamar Allah zata tsaya, kuma ni da kai za ku amsa ko wace tambaya daga Ubangiji...”
Na karasa ina fashewa da kuka tare da juyawa da zimmar zuwa na dauki tsintsiyar na cigaba da aikina, sai naji muryar mijin matar nan yana wata irin magana mai rikitarwa.
“Kardar kodar da aka dasawa Rahma take magana....?”
Juyowa nai idona na hawaye na nuna Rahma.
“Kodar Nana ka sakawa wannan matar? Matar da mahaifinta ya koremu a kangon gidansa saboda mun taba a gidan? Matar da mahaifinta be san daraja talaka ba? Matar da mahaifinta yasa a ka wulakanta mu? Ita ka sakawa kodar talaka? Talakar ma wacce ya wulakanta? Ka cuce ni ka cuci nana Allah ya isa tsakanina da kai, da kai da duk wanda yasa kuka aikata min wannan aikin ba za ku ga da kyau ba, Wallahi Allah ba zai barku ba”
Na fada cikin daga murya iya kar karfina, sam na manta da a gidan wani mai kudi nake, yau duk wani tsoro da fargabar gudun laifi ya fita a raina, daga Rahma har mijinta da Doc Asim yau kananan mutane na ke kallonsu kuma azzalumai.
“Uban waye yace ki siyar? Akan mi za ki rika fada mana magana son ranki cikin gida? Ubana sa'arki ne da zaki rika saka ko a maganar ki?”
Rahma ce ke wannan maganar tana matsowa kusa da ni, har ta ka hannu zata mare ni sai mijinta yai saurin rike duka hannayenta ya matsar da ita jikinsa yadda ba zata iya ko da kwakwaran motsi ba.
“Talauci ba hauka ba ne Rahma, kuma ba kaskanci ba ne, jarabawa ce daga Ubangiji, ba kuma zan sake yarda marar sanin darajar dan adam irinki wacce ta more da kodar mahaifiyata ta sake wulakanta ni ba, kin ci riba da ni tun da nayi aikin kwana biyu a karkashin ki, amman ba za a koma ba, ya zama na karshe, sai dai ki wulakanta wata amman ba ni ba, kuma tun da har kuka zalinmu lafiyar nan da bata yi amfani komai a jikinki ba”
Ina kawai nan na nufi kitchen din a fusacw na dauki Hijab dina na saka na fito fuuuu na fice daga gidan kamar iska. Kan kace kwabo har na kai gate na bude na fita raina na min mugun zafi zuciyata na ciwo sosai. A rayuwata ban taba ganin mutane masu son kai da tsantsan zalinci kamar likitan nan da mutanen nan ba, babban bakincikina sun ci riba da ni na aikin da nai a karkashinsu, wanda hakan ya fi komai yi min ciwo. Tun da na kama hanyar gida sai na nemi kukan zuciyata da na ido na rasa, wani karsashin da karfin zuciya dana ruhi suka rufe ni, na jaddawa kaina nemawa Nana lafiyata ta rayu ko dan bakincikin masu son ganin bayanta, a yau na gane ba kuka na ke bukata a yanzu ba, lokacin kuka da bakincikin abunda ya faru a baya ya kare, wannan lokacin na fuskartar gaba ne da inganta rayuwata da ta Nana, na yarda abunda ya tafi baya dawowa amman abunda be zai zo za a iya tarbarsa gabannin ya zo, zan jure ko wane kalar wulakanci da cin zafi daga duk wanda zai iya zama dalilin samun lafiyar Nana. A kullum idan zanje gida ina zuwa da kasala da jin gajiyar tafiyar, amman a yau na isa gida da karfi kamar daman can ban yi tafiyar ba, ban yarda Nana ta fahimci komai ba, na shiga dakinta na zauna ina ta kokarin yin far'ar da take ta zo min.
“Lafiya kika dawo da wuri haka Ataa?”
“Nana sun koreni daga aikin”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, sun kore ki kuma? Me kikai? Mun shiga uku”
“Ba mu shiga uku ba, kuma da yardar Allah ba za mu sake shiga uku ba, ina tunanin ma kamar wata hanyar zata sake bude mana?”
“Kamar ya? Yanzu ina za ki sake samun wani aikin”
“Farida ta fada min cewar Maman Samawa tana samawa mutane aiki a abuja, kuma a can ana biyan kusan 30k ko sama da haka, kin ga cikin wata biyu ko uku na hada kudin maganinki”
“Aa ni ba zan yarda kije can nesa ba, ban san iya abunda zai iya samunki ba, kuma nan wa zai kula da ni idan ki ka tafi?”
“Farida ta min alkwarin kula da ke, idan har za ki iya hakurin ciwon nan na ki zauna asibiti na tsawon wata biyu, zaki iya hankurin rashin ganina na wata daya, idan na samu lokaci sai na zo na ganki ni dai amincewar ki na ke bukataka kamin nai ma maman salma magana, ina son lafiyarki Nana, sai da lafiyarki zan iya neman dangina, hankalina kuma ya kwanta, dan Allah ki amince Nana”
Na fada ina kama hannayensa sai naga yanayinta da fuskarta sun canja.
“Ko daga nan zuwa wani gurin za ki je, ina jin tsoro Ataa sai naga kamar ba za ki dawo ba, bana son ki zo yi ta wahala da gawa waya sani ko ba zan kai wani lokacin ba”
“Da ba zaki kai wani lokacin ba, da baki rayuwa bayan wannan lokacin da akai miki tiyata ba, kuma babu wanda yasan rayuwa da mutuwar wani sai Allah, kina karya min guiya, ki rika nuna min cewar zamu rayu ni da ke ko da mu kai muka rage a duniya, dan Allah Nana ki barni nai wannan jihadin, ki bar ni na samun wannan faricikin da ladar”
Magangannun nai ta mata ina lurar da ita har na samu ta aminta duk da kasancewar ba ta so haka ba. Bayan sallah azahar na ja Farida muka kama hanyar gidan maman salma da shiga mu kai sallama muka gaisheta, sannan Farida ta koro mata da bayanin da ke tafe da mu, wani abun mamaki da jindadi sai tai murna da hakan har take labarta mana cewar daman ana neman mai aikin a wani babban gidan masu kudi da ke Abuja, sai dai tace ba zata yi komai ba har sai ta zo gurin Nana ta ji ta bakinta dan tabbatarwa, ni kuma na ce mata na yarda ta zo su yi magana, sallama muka mata muka kamo hanyar gida wani dadi ya lullube ni na soma yarda da cewar kukana ya kusa karewa...
ALIYU POV.
Zai iya rantsewa a rayuwarsa be taba haduwa da wata mace yar talakawa mai karfin zuciyar da ta iya tsaya gabansa ta fadawa Rahma magana son ransa ba sai yau, for the first time yau wata ta ciwa Rahma mutunci ya kasa yin komai, har yanzu fuskarta yake gani irin kyau da haiya ta yai arba da shi a fuskarta a yau ko a mafarki be ci karo da macen da kallonta ya saka shi faduwar gaba ba sai yau. Kalamanta da ďai-ďaiya suke masa yawo a kunne, kalma zalinci ita kalma ta biyu daya tsana bayan talauci, yes he's rich and he know be zama dole ya taimaki kowa da dukiyarsa ba, amman yai wa kansa alkwarin ba zai taba yarda dukiyarsa ta saka ya zalinci wani ba, ko da kuwa talakan daya kyama ne. Yasan yadda lafiyata take da muhimmanci tun daga lokacin daya fara neman ta matarsa yana jin tsoron rasa ta a ko wace dakika ita kadai da take a natsayin matarsa hakan yasa shi fahimtar Ataa wacce ita kuma take zancen mahaifiyarta. Haka sukai tsaye a falon bayan fitar Ataa har na tsawon mintuna talatin ba tare da kowa ya ce uffan ba, daga Aliyu har Rahma da Doc Asim dake ra sake saken yadda zai kare kansa. Rahma jiran take mai kare yace wani abu tun daga lokacin da Ataa ta fada mata ba daidai ba, amman bata ji yace komai ba, sai ma rike mata hannu da yai a lokacin da zata mareta. Aliyu kuma yana ta jiran abunda zai fito daga bakin Doc Asim amman ya kasa magana kamar an daure shi.
“Kodar mahaifiyata ka cire aka sakawa Rahma ba tare da sanin ba?”
Doc Asim yai saurin kallon Aliyu.
“No karya ta ke yi? Ita ta siyar da kodar da kanta, zan iya nuna maka shaida ma, ita ta siyar da kanta”
“Mi zai saka tai maka karya? You know what na yarda da komai amman ban yarda da zalinci ba, ban yarda na zalinci wani na kuma na kwanta nai bachi mai dadi ba, dan ina neman lafiyar Rahma ban ce ka zalinci wata ba, na fada maka ka nemo wacce zata saida zan biya ko dala dubu nawa ne, amman ban ce ka cire ba tare da sanin mai ita ba”
“Amman Dear ai yace siyarwa tai...”
“Silent”
Ya fada sai dai ba cikin daga murya ba, tare da dagawa Rahma hannun wacce ke kokarin kare Doc Asim da nuna abunda yai ba dai-dai ba ne.
“Ka bani amsa da saninta ka cire ko ba da saninta ba”
“Ni ban san wannan yarinyar ba”
Shine kawai abunda Doc Asim ya fada ya dauki akwatinsa ya fice a fusace har gumi na karyo masa idonsa su yi ja alamar ransa ya bace sosai. Yana fita Rahma ta kalli Aliyu sannan ta nufi upstairs cikin bacin rai da zazza6in da da ke kokarin rufeta. Zaunawa Aliyu yai saman cushion yana ta auna irin zalincin da akwai wa Ataa idan har ta tabbata Doc Asim ya cirewa mahaifiyarta koda ba tare da sani ba, mikewa yai tsaye ya bi bayan Rahma a bedroom dinta ya same ta zaune bakin gado tana waya be san me ta fada masa ba, kuma be san da wa take wayar ba, sai dai yana alamar kuka da hawaye a idonta, saurin fisge wayar yai ya kashe kiran sai ya kashe wayar gaba daya, ya zauna kusa da ita.
“Kin sani idan kina ciwo bana son kina wani dogon motsin, za ki yi street kanki ne kawai”
Kallonsa tai da duba mai mai ma'anoni da yawa idonta har ya fara ja.
“Miyasa zaka yarda da yarinyar nan ka karyata likitan da ya shekara biyar yana maka hidima?”
Be ce mata komai ba, ya kai hannunsa ya share mata hawayenta sannan ya rika fuskarta da hannayensa biyu yana mata magana a hankali yadda hankalinta zai kwanta.
“Za mu magana daga baya, for now ina son ki kwanta ki huta, and promise me za ki yi bachi?”
Ta dauke kai tana hadeye yawu. Sai ya jata zuwa kirjinsa ya rumgume, ya dan kishingida da gadon yana ta kallon sillin kamar mai tunani. Ya dauki awa daya a haka sannan ya soma jin sauka numfashinta mai zafi alamar bachi ya dauke, sai ya kwantar da kanta saman fillo ya lullube ta da blanket ya mike a hankali ya fita daga dakin dare da jan kofar dakin a hankali.
Fitowa yai daga cikin gidan gaba daya, tun kan ya karasa gurin motarsa ya danna key motar ta bude, yana shiga yai nata key tun kan ya kai gate mai gadin ya bude masa gate din yana daga masa hannu, ko kula shi be yi ba ya dauki hanyar gidansu wato gurin Momy, as usual idan babu Nasir ko Mama Fulani a kusa da shi Momy ce abokiyar shawararsa, ko da ma suna nan wani lokacin ya kan kirata a waya ya shaida mata, yau ma yana da bukatar fada mata abunda ya faru yaji nata tunani. He arrived in time a daidai lokacin da Momy ta kara Daddy ya shiga mota tana tsaye tana kallon yadda mai gadin gidan yake rufe gate, sai ta ya sake budewa da sauri jikin har bari yake, ashe Aliyu ya hango tafe. Murmushi tai domin ta san a duk duniya Aliyu kadai ya isa ayi masa haka a gidanta, baya danna horn sau biyu kuma bayana son jira saidai a jira shi, idan kana son kaganin bacin ransa ka kwada bata masa lokaci ko kuma saka shi jira na rashin dalili. Tana ta kallon dan na ta har ya faka motarsa a inda ya fi masa soyuwa a harabar gidan sannan ya fito fuskarsa ba yabo ba fallasa kamar kullum ya doshi inda mahaifiyarsa take, yadda yake takawa sai ka rantse da Allah takun kasaita ne da nuna isa, alhalin haka tafiyarsa take, kamshin turarensa na ta sanarda zuwansa tun kan ya karaso kusa da ita. Zai da ya rage sauran taku shida zuwa bakwai tsakaninsa da ita sannan ya dabbaka sunnar nan ta murmushi wacce ta kara mishi kyau da haifa.
“Na ga Daddy ya fita yanzu har mun gaisa da shi ma”
“Eh yana ta sauri za su je meeting”
Haka suka jero ita da danta suka shigo cikin falon suna wannan hirar. Saman cushion ta zauna tana nuna masa dinning.
“Ga ragowar breakfast can idan zaka ci kanenka suka raga”
Ya dan yamutsa fuska yana murmushi dan yasan zolayarsa kawai Momy take.
“Momy kin san ai bana cin ragowar kowa ni, ina Sisters”
“Duka suna school”
Ajiyar zuciya ya sauke wanda yasa Momy sake dubansa.
“Wani abun ne?”
Ya jimm na wani lokacin sannan sannan ya kalleta a natse ya ce.
“Momy kin san kwana ki ina ta neman mai aiki ko? Sai ga wata yarinya ta zo gidan neman aiki.... ”
Tun daga lokacin da Ataa ta zo gidan ya jera mata labarin har ya isa zangon da ya fi rikitar da shi. Da mugun mamaki Momy ta kalli.
“Kuma ba ka ji komai a ranka ba Dan wajen Fulani? Ba zuciya da jini ne a kirjinka ba? A zalinci wata ta dalilinku har ka tsaya neman hujja?”
“Amman ni ban ce a zalince ta ba?”
“Miyasa da aka kawo maka kodar baka bincika daga inda ta fito ba? Akan me zaka zuba kudi mai yawa ka ce a samo maka kodar? Ba kayi tunanin ganin kudin zai iya saka Doc Asim aikata komai dan ya samu kudin ba? Ai da tun farko ka samu mai kodar ka yi magana da ita da bakinka, yanzu ga shi ka raya matarta kana cikin farinciki, ita kuma ka jefata a damuwa da bakinciki? Ka ji tsoron addu'ar wanda aka zakinta, kuma ka ji tsoron Allah ya isa, domin idan bata bi jikinka ba, tana bin dukiya da kaddara”
Lumashe ido yai ya bude yana fusar iskar bakina a hankali.
“Ka tuna lokacin da aka ce maka Rahma zata iya rasa ranta idan ba mata wano dashen kodar ba? Ka tuna? Ka auna ka ji ya yarinyar nan ta ke ji? Ita da mahaifiyarta ce, kamar ni ce ko Fulani aka cirewa koda ba tare da saninka ba? Idan ka gano me zaka yi?”
“Zan yi duk abunda zan yi na kwato muku hakkinku”
“To sai aka samu akasi ita yar talakawa ce, bata da wannan ikon bata da wannan gatan, mahaifiyar tana raye ko ta mutu babu wanda ya sani, wane hali suka shiga bayan wannan babu wanda ya sani, ina jiye maku tsoron abunda ta zai biyo baya, amman gaskiya an zalinci yarinyar nan”
“Momy kin san inna sani ba zan zalince ta ba, na yarda bana kula kowa amman bana zalintar kowa?”
“Ka bude zuciyarka kai tunani... Na san kana son matar ka kuma zaka iya komai akan samun lafiyarta, amman ina son na fada maka wani abu, ka ji tsoron addu'ar wanda aka zalinta, kuma ka ji tsoro mutumen da zai ce ya barwa Allah Allah shine zai isar masa, hakan yana nufin babu komai tsakanin shi da kai Allah ne zai wakilce shi ya fidda masa hakkinsa akanka.....”
Kallon Momy yai zuciyarsa cike da tsoro da be taba jin irinsa ba, jikinsa yai mugun sanyi, tsoron abunda zai biyo baya kamar yadda Momy ta ce yasa zuciyarsa rauni...
_____________________
Page daya ya rage mana mu gama free pages In-Sha-Allah. if you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt Bank. sai ku turo shaidar biyan wato screenshot ta wannan number 08036126660, ko kuma katin mtn na 300 ga marasa account ta wannan number 08036126660. yan nijar za ku tura 500fc na line Orange ko Airtel ta number nan +22790165991 sai ku min magana ta wannan number 08036126660 Za'a saka ku Group.
Thanks 🙏🏻 Ku ziyarci YouTube channel dina, ku danna min subscribe kuma kui sharing. 👉https://www.youtube.com/channel/UCpAkml0pIh6MUnzt9nLh_qQ
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
1️⃣5️⃣
Ya dade a gidan Momy zaune gaba daya jikinsa ya gama yin sanyi, yana ta jin kamar akwai laifinsa a cire mata kodar da akai, and if da laifinsa ya akai laifinsa ya shiga ciki bayan shi idan ma ba yanzu ba be tana ganin yarinyar ba, idan yai duba ta wani bangaren yana ganin cewar ba shi da laifin komai, shi dai kawai matarsa yake nemawa lafiya and shi be ce a cire da karfi ba. A masallaci yai sallah magariba sannan na ya dawo cikin gidan, jikin ba kwari kusan sai ya rantse shi be taba jin jikinsa a wannan yanayin, wata kila saboda ba a taba cutar wani a gabansa ba, ko kuma shi din be taba cutar wani da dukiyarsa ko da ikonsa ko karfinsa ba, sai wannan karon, duk kuwa da kasancewar wani bangare na zuciyarsa na fada masa cewar ba shi da laifi. Yana shigowa falon Sisters dinsa sika make kyam kamar babu wani abu mai numfashi a falon, ko wacce ta shiga natsuwarta, tsayawa yai kallonsu kamar yadda ya saba idan ya shigo cikin gidan domin lura da yanayinsa da kuma halin da ko wace daga cikin kannen nasa guda hudu suke cikin.
“Ina Umar?”
Ya tambaya da irin fuskarka nan ta ba wasa.
“Be dawo ba”
Duka su hudu suka hada baki gurin bashi amsa dan sun sani sarai baya son kyaluwa, Momy zata iya tambayarsu abu su tsaya tunani ko wani sha'anin kamin su ba da amsa amman ban da Aliyu baya daukar wannan shashancin a time din da ya tambaye ka time din zaka ba shi amsa, idan kuma kai kuskure wani abun ya fito daga bakinka kuma kai ne a matsala. Juyawa yai ya shiga dakin Momy sai ya same ta zaune saman carpet tana jan carbi. Guri ya samu kusa da ita a kasan ya zauna yana fiddo wayarsa.
“Dan waje bata Fulani ina ta tunani anya likitan nan Asim zai kyale ta kuwa?”
Dagowa idonsa daga jikinkin screen din wayar yai ya kalleta.
“Ban gane ba?”
“Ina tunanin kamar ta jefa kanta a matsala ne, baka tunanin zai iya yi mata wani abun da nan gaba ba zata sake shaidarsa ba? Babban likita mai asibitin kansa kamar Asim ba zai dauki wannan matsalar ba, ba zai yarda ta karya masa aiki ba”
Aliyu yai shiru yana nazari.
“Wannan abu be min dadi ba sam Wallahi, saboda ban jidadi abunda ya faru da yarinyar nan ba, duk kuwa da ban santa ba, amman na san irin zafin da ake akwai ace an cuce ba gashi baka da hali jan hakkinka”
Mikewa yai tsaye yana fitarsa numfashi a hankali ya ce.
“Momy zan tafi gida, na san yanzu Rahma ta farka”
“To ka gaisheta”
“Za ta ji”
Ya juyo yana tafiyarsa kamar yadda ya saba har ya sauko kasa, ya nufi gurin motarsa yana shiga yai mata key ya dauki hanyar gidansa. Yana tafe yana tunanin abunda ya faru da kuma maganar Momy, he find himself in middle of tausayin Ataa da yarda cewa an zalince, every words of her yake tunawa da yadda take furta su, idan har ba zalince ta ba, ba zata iya daga hannunta ta mari babban mutun kamar Doc Asim ba, yadda ya lura da rashin tsoron da ke cikin idonta a lokacin da idanuwansa suke yawo a fuskarsa, ya tabbatar ko kashe Doc Asim zata iya yi a gaban kowa, and Momy was right ba lallai ne Doc Asim iya kyaleta ba.
‘Allah ya isa’
Haka maganarta ke ta dawo masa sabowa a kunne, ga wa zai isar mata, ga Doc Asim ko ga shi ko kuwa ga su dukansu? Haka yai ta saka tunani kala kala har ya isa gida, yai mamakin ganin Motar surikinsa a wannan lokacin, the first thing that come his mind is ko ciwon Rahma ya tashi ne, amman kuma idan ciwon ta ne ya tashi ai shi zata kira ba Daddynta ba. A bude ya samu kofar falon tun ka ya shiga yake jiyo muryar Alhaji Nasiru Gobir. Da sallama Aliyu ya shiga, surukinsa da wani yayan Rahma suka amsa masa, Rahma kan ko inda yake bata kalla ba. Gurin ya samu kusa da ita ya zauna yana kallon Alhaji Nasiru Gobir wanda fuskarsa ke dauke da damuwa.
“Rahma ta fada min abunda ya faru, daman ta fadawa mahaifiyarta tun a waya, wannan wace irin yar iskar yarinya ce marar tarbiya haka?”
Aliyu ya juyo gefensa ya kalli Rahma sai kuma ya sake kallon mahaifinta ya ce.
“Ba ta fada maka abunda akai wa yarinyar ba?”
“Ko ma mi akai mata ai ba mu muka ce ta siyar da kodarta ba, irin talakawan nan da kake gani Aliyu ba su da komai a ransu sai hassadar nai arziki, idan suka ganka da arziki ji suke kamar su kashe ka su kwashe dukiyar, shiyasa tsakaninmu da talaka aiki kawai mu biyashi, wata banza a banza bata isa ta shigo har cikin gidanki ta fada miki maganar banza ba, watan ma kuma talaka!”
“Daddy har da kai ta ciwa mutunci, wai a gidanka ta raba ka koreta ni da kai duk ba musan darajar talaka ba”
“Zan sa a binciko yarinyar da iyayenta sai na nuna mata ruwa ba sa'an kwando ba ne”
Duk abunda ake Aliyu ba ce uffan ba, har Daddy yai musu sallama ya fita, a lokacin ne Rahma ta tashi ta nufi dakinta, shi kan sai da yaji tashin motar surukinsa sannan shima ya mike tsaye ya bi bayan Rahma. Gaban madubi ya same ta zaune tana cire dankunnen da ke kunnenta, kusa da ita yaje yai mata kissing sannan ya zauna gefen gadon yana kallonta.
“Miyasa za ki kira Daddy ki fada masa maganar da bata kai ta kawo ba?”
Da mamaki ta kalleshi
“Wannan abun ne be kai ya kawo ba? Yarinya karamar yar talakawa kamar wannan ta fada min magana son ranta ka ce be kai ya kawo ba? Aliyu ka san me kake fadi kuwa?”
“Amman ai zalintar ta akai? Yanzu kuma sai ki fadawa Daddy bayan kin san zai iya daukar wani mataki?”
“Amman mu muka zalince ta? Daman can matakin na ke son ya dauka shiyasa na kira shi na fada masa, tun da kai ka kasa komai sai ma rike min hannu da kai dan kar na dake ta”
“Sanadinmu aka zalince ta, kodar mahaifiyarta aka cire Rahma aka dasa miki? Kuma kike tunanin ba zatai wani hargagi na huce haushinta ba?”
Juyo tai gaba daya ta kalleshi da kyau.
“Kana magana Aliyu kamar ba kai ba? Lafazin da ke fitowa daga bakinta yana karantar da ni cewar ba kai ne ba?”
Hannu ya kai ya kama hanyayenta ya cigaba da mata magana a hankali kamar yadda yake mata dazun.
“Dear, zan iya juye yi wa mutum komai amman ban da zalinci, an riga an cuci yarinyar nan, kuma kodar nan an dasa miki ita wannan kadai ya isa yasa jin tausayinta waya sani ma ko mahaifiyar ta mutu”
“Tausayi Aliyu? Tausayi? Tausayi fa ka ce? Mi mukai mata da har za mu ji tausayinta? Mu muka zalince ta ne? Akan mi zaka yarda da yarinyar daka soma gani cikin kwana biyu, saman da likitan daya saba yi maka aiki shekara da shekaru? Ban taba ganinka cikin wannan yanayin ba Aliyu, ba ka taba ce min na ji tausayin wani ba, baka taba ce min kana tausayin wani ba, wanin ma talaka irin wannan yar shekara a gidanka”
“Ba tausayinta nake ji ba, ina kallon abunda akai mata ne a matsayin zalinci, and be dace ki saka Daddy a wannan maganar ba, zai iya unkura yi mata wani abu sanadinki, ni fa na yarda da wulakanta kowa na ci mutunci kowa kuma na kyama ci kowa amman ban yarda karfin iko ko dukiya su saka na zalinci wani ba, ba zan iya da hakkin wani a kaina ba”
Kai ta girgiza masa tana murmushi irin mai ciwon nan idonta na cika da hawaye.
“Ban taba yin wani abu ka ce ban yi daidai ba sai yau, ban taba daga hannu da sunan dukan wani ba ka hana ni sai yau, wani be taba fada min mummunar magana a gabanka ka kyaleshi ba sai yau, na fahimcin inda ka dosa Aliyu, ta wanke fuskarta kaga tana da kyau tana da fari tana da gashi na fahimta...”
Mikewa tai tsaye zata fice daga dakin tana share hawayen da suka zubo mata, sai yai saurin rumgumeta ta bayan ya dora kansa saman wuyanta.
“Ba kyau ba ne matsalar, ina auna irin halin da na samu kaina ne a lokacin da aka fada min cewar za ki iya rasa ranki idan ba a canja miki koda ba, na ji tsoro sosai Rahma, kullum fargabata kar na rasa ki, na shiga damiwa sosai wanda hakan yasa na fadawa Doc Asim ya samu ko koda ta nawa ce zan siya, amman ban san cewa zalintar wata zai yi ya kawo min ba, ni kenan da nake tsoron rasa mata ina ga ita da take tsoro rasa mahaifiya tana da daraja ga yayanta Rahma ko da kuwa talaka ce”
“Babu ruwanmu da rayuwar wasu, abunda muke so shi muka samu, whither ya zalince ko mu muka zalince ba matsala ba ce, tun da mun samu abunda mu ke bukata, Aliyu bana son na sake jin maganar yarinyar pls”
Juyowa yai da ita ta yadda zata fuskance shi irin fuskartar da zata famince ko wace kalma da zata fito daga bakinshi.
“No ba haka ya dace ba, idan har ba mu bata hakurin zalincin da akai mata ba, be kamata ba, be kamata mu kara mata da wani abun ba, Daddy zai iya yi mata wani abu, and maybe Doc Asim ma ba zai kyaleta ba”