Kenza eBookz

A d u n i y a ta complt by huguma - Chapter 20

A d u n i y a ta complt by huguma - Chapter 20

A d u n i y a ta complt by huguma Chapter 20: A d u n i y a ta complt by huguma Chapter 20. "Na sani.....nafi kowa sanin wannan dan uwan nawa wanne iri…

4,498 words

"Na sani.....nafi kowa sanin wannan dan uwan nawa wanne iri ne......tun daga ranar da mukayi temple run dinnan na sake yadda da hakan..."

"A nan zaku gama hirar ne?,idan ku baku gaji ba ku tallafa ku kaini naga aminatu na" Muryar abba ta sauka kunnuwansu.

Fu'ad ne ya waiwaya don farouq yana fuskantar abban ne. Dan murmusawa kadan fu'ad yayi ya matsa yana yunqurin budewa abban qofa,amma farouq ya rigashi

"Dukkanku kai da abban yau qarqashin hidimata kuke....baqinmu ne ku daga South Korea".

"Sannu sarkin noma.....godiya muke" Shima abban ya fada cikin barkwanci bayan ya shiga motar.

Dashi da farouq din baya suka shiga bayan ya bawa shugaban security dinsa umarnin su bisu a baya.

Kusan duka a hanya ma dai tattaunawar ta kasuwanci ce. Farouq din yana bawa abban labarin yadda abubuwa suka kasance bayan tafiyarsu

"Amma tabbas sai ka sake sanya idanu akan mika'il.....ina suspecting wani abu tattare dashi,duk da bana ce gashi ba,amma nasan kai din zaka fini fahimtar komai" Farouq din ya furta.

Idonsa fu'ad ya dauke daga kan wayar hannunsa,wanda saqon mika'il dinne ya shigo,mutum na farko daya fara masa saqon barka da dawowa kafin kowa. Bai cewa farouq komai ba,amma kuma maganar tasa ta samu gurbi sosai a zuciyarsa ta zauna,sai ya gyada kansa a hankali yana sake maida dubansa ga wayar.

**"Anni an gama komai" Ta furta sanda take saukowa daga saman tsararren dining area din daya dauki kyakkyawan family dining table na wani mulmulallen tangaran kai kace an samar dashi ne daga burbushin diamond ko gold da kamfanin jadda ke wankewa su fiddashi. Fara ce tas,mai matsakaicin tsaho,saidai bata da qiba ko qanqani. Yanayin sumar gaban kanta kawai zai fada maka akwai suma me yawa a saman kanta wadda bata da duhu ta danyi brown kadan bame yawa ba. Yanayin yadda ta datsi daurin dankwalinta daga tsakiyar kanta shi zai baka daman ganin hakan sosai. Straight gown ce a jikinta ta atamfa me igiyoyi hagu da dama wadda ta daureta daga gefen qungunta guda daya.

"Ma sha Allah.....sannunku da qoqari....sun wuce ne?" Anni data daga kanta daga tab din hannunta da take duba wasu addu'o'i ta fada.

Fuska tadan yamutsa kadan tana zama kujerar gefan annin gami da ajiye qaramin towel din hannunta a side table sannan ta dauki wayarta dake ajiye akai tana qoqarin budeta

"Kowa ya wuce......yanxun abba da hamma kawai muke jira" Ta qarasa maganar murmurshi yana subuce mata.

"Umhummm......wato shi saddiq shine marainin wayonki da baki ta tasa ko?" Anni ta fada tana maida idanunta ga addu'o'inta . Fuska ta yamutsa,duk da bata kalli annin ba amma ta amsa

"Bar wannan anni,wa yake ta tasa,ba abinda ya iya sai takurawa mutum ba dalili......hamma takurawarsa me dalili ne idan bakayi abinda yace ba ko baka kiyaye dokarsa ba......amma yaa saddiq.....hmmmm....ko wayar nan yanzun ya shigo yana ina dannawa sai yayi challenging dina" Ta qarasa maganar tana zamewa ta kashingida saman kujerar tana maida hannunta kan shafinta na X.

Ita da annin kowa ci gaba yayi da uzurin gabansa,wannan ya bawa falon daman daukan shuru na wani lokaci kafin ta daga kanta. Haka kawai ta qarewa anni kallo sai ta saki dariya

"Anni.....kinsan tsadar kayannan?" Ta fada tana kallon kwantaccen lace din jikin annin dake wani yauqi da santsi duk kuwa da cotton ne. Peach color da ratsin green,bashi da nauyi ko kadan

"Saikin fada 'yar kasuwa......" Ta amsa mata ba tare data dubeta ba

"Anni Allah hamma yana shagwabaki......ki zauna da kaya me tsada haka a gida duk dogayen rigunanki?....amma dai....to,hala abba aka yiwa kwalliya?" Ta fada qasa qasa tana qunshe bakinta da hannu. Kadan ta dubeta ta harareta

"Akwai kayan da sukayi tsadar da zan kasa yiwa abban kwalliya dasu?" Kai ta girgiza tana qoqarin maida kanta ga wayarta tana qoqarin boye dariyarta

"Babu anni.....anni ta abbanmu".

"Amna.... Qoqarin maidani kakarki kike ko?"

"Aah anni wallahi" Ta fada da sauri tana duban anni still tana son shanye dariyarta

"Kici gaba.....inajin zan dauki shawarar farouqu ne,zaki komawa nanna ne kiyi zamanki a can". Kyabe fuska tayi da kyau tana aje wayarta gefe kaman zata saki kuka

"Dama haka yaa farouq din yace?,duk haqurin zama cikin mazan da nakeyi ban da sister?....."

"Oho koma.meye gwara ki koma can,tunda kinga can dinma akwai mata 'yan uwanki sai kinfi jin dadi". Sosai ta sake kwabe fuska tana duban anni

"Da gaske anni zaki iya bayar dani?" Daga kai tayi ta dubeta

"Ba mace bace ke?,wataran ba aure zakiyi ba?" Ta tambayeta,ai kuwa saira soma matsa hawaye tana juyawa annin baya

"Ai dama na sani......gidan nan babu wanda yake sona sai hamma da abba na......shi dama yaa farouq kaman ya bayar dani kyauta yakeji.....ni bazanyi aure ba.....dake zan yita zama". Yadda tayi maganar zata yita zaman da ita sai ya bawa anni dariya amma ta dake

"Sai kiyi kuma" Tace tana ci gaba da scrolling sama tana duba adduo'inta.

"Kinga.....ki daina biyewa ta BB farouq.......indai ina nan ba wanda zai matsa miki.......i swear" Muryar musaddiq ta biyo bayan sallamarshi. Tuni ta miqe ta zauna sosai tana qoqarin goge hawayenta.

"Kaima kana biye musu yaa musaddiq wani lokacin.....amma dai ka fisu" Ta fada tana daidaita zamanta saman kujerar.

Qaramar dariya ta qwacewa anni tana qoqarin ajiye tab dinta a gefe

"Uhumnnn..... Ai dama ba kasafai akewa amna abun arziqi ba.....wanda ke mata abun arziqi kai tsaye a gidannan Muhammadu ne......har kun dawo?" Ta tambayeshi tana duban musaddiq dake dariya qasa qasa.

"Eh anni.....su abban basu iso ba?"

"Sun sauka amma basu qaraso gidan nan ba.....amma na tabbata suna dab da isowa don tun dazu suka tafi daukosu". Ta amsa masa tana miqa hannu ta karbi purse din nata da yake miqa mata.

Tana yunqurin budewa su kuma suna magana tsakaninsu shi da amna. Ta zuge jakar cikin rashin tabbas da yaqini,ta bude ne kawai don taga meye yayi saura a cik,me ta samu?,amma ga mamakinta sai ta samu komai a muhallinsa ba tare da an canzawa komai waje ba bare a cire wani abu,sai wayarta data nuna low battery da alama ba'abi ta kanta bama bare a sakata a charge.

"Ikon Allah" Ta fada,abinda yaja hankalin amna da musaddiq kanta

"Ba abinda aka rasa a ciki musaddiq.....ba abinda ta taba kota dauka" Ta fada da mamaki idanunta cikin jakar

"Nima dana bude nayi mamaki,amma nace bari na kawo miki ki duba komai bansan ko akwai wani abun daban ba"

"Aiko yadda na zuba kudin a jere ba'a canza tsarinsu ba" Ta fada tana sake fiddosu

"Amma dai ka yiwa yarinyar godiya ka karbamin number wayarta ko?,ko mamarta na sake yiwa godiya?"

"She's not natural fa anni" Ya fada a taqaice

"Kamar yaya?" Ta tambaya cikin rashin fahimta.

"To nidai anni ko qyallinta ban gani ba,a bakin wani waje wani ya tareni ya bani,baicemin komai ba ya juya,nima haka na juya da kan motata na dawo gida"

"Ikon Allah......gashi bata bari ko sau daya na mata godiyar alkhairin data yimin ba.....na kasa manta damuwa da kulawar data nunamin" Annin ta fadi tana juya abun a ranta.

Bai samu ce mata komai ba saboda qarar bude gate da shigowar motocin da suke da tabbacin baqinsu sun iso

"Alhamdulillah" Anni ta fada tana murmurshi gami da ajiye wayar da jakar a gefe. *D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 53

Dukkansu da sallaman a bakunnasu suka shigo. Suka amsa musu suna miqewa tsaye tare da dakon qarasowarsu cikin falon,saidai amna ta kasa jurewa. Da sauri ta taka zuwa bakin qofa ta riqe abbannata da kyau tana dariya idanunta saman fuskar fu'ad

"Abba sannu da zuwa....hamma....hamma sannu da zuwa" Ta furta matsanancin murmushi yana subuce mata

"Sannu 'yar abba qanwar hamma.....hamman dai aka matso a tarba aka fake da abba". Abban ya fada yana lakuce mata kumatu. Dariya suka saki fu'ad yana tayasu da murmushinsa

"Amnee......barkammu" Ya amsa mata cikin kulawa. Sakin abba tayi ta matsa dab da fu'ad din tana karbar briefcase dinsa

"Su amna an iya munahirci" Muryar sadiq ta shiga kunnenta,sadiq din dake tsaye ta bayansu abban. Gotasu tayi kadan tana leqensa,sai ta bata fuska

"Duk abinka bazanyi welcoming naka ba.....abba me yasa baku samu wata bolar South Korea kun yar dashi kun gudo ba?" Ta qarasa tambayar tana kallon abba a shagwabe. Ba wanda maganar bata bawa dariya ba a cikinsu

"Idan muka yar dashi ke zaki fara qorafin muje mu dauko miki shi ai"

"Allah bazan nemi wannan ba....."

"......me qarya?" Saddiq ya datsi numfashinta yana fadi idanunsa a waje

"Dan aljanna" Ta fadi tana juya idanunta abinda zai sake tabbatar maka da sauran quruciya a tare da ita,hakanan kuma tana fama da sakalcin auta da gasken gaske.

Kasa jiran isowar abban tayi,sai ta taka ta ruskeshi a tsakiyar falon. Ta rusuna tana masa sannu da zuwa gami da gaidashi duka tare da qoqarin amsar qananun tarkacen dake hannunsa. Cikin nashi tsananin kulawar da kallon kewa yake amsa mata,fuskarsa ta wadatu sosai da fara'a yana tambayar lafiyarta dama ta jama'ar gidan gaba daya.

Hankalinsa yana kansu,qauna da kulawar dake tsakanin anni da abba sune abu guda daya tak da suka rage wadanda suke bashi hope din wataran qila zai iya aure. Soyayyar da sukema juna wani irin dasashen abu ne da har yanzu yake tasiri a tsakaninsu,babu alamun gushewa sam sam. Yanayin rayuwarsun yana burgeshi,wata irin mu'amala annin kewa abba,irin mu'amalar da bai taba ganinta ba tsakanin MAAMAHnsa da ABBEY dinsa ba. Mu'amalar da bai taba zaton akwaita tsakanin miji da mata ba sai a wajen annin.

Gabanta ya qarasa shima kaman ko yaushe,cike da ban girman nan da yake jinsa har cikin ruhinsa ya tsugunna yana gaidata. Bata iya tsaiwa saman kanshi ba saboda girman shima da take bashi sakamakon sunan MUHAMMADU da yake dashi......da wata ajiyayyar kima da martaba da take ganinsa dashi saboda dattakon halinsa data sani tun bai cika shekara sha takwas bama a duniya.......uwa uba yadda yake tattalin farincikinta kadai ya sanya kowanne lokaci takejin tamkar jikinta ya tsaga ya fito.

"Lafiya alhamdulillah me babban suna.....jiki na warware tun tuni......dama ta jima bata tashi ba,akasi kawai aka samu a ranar,nafi tunanin kuma matar da mukayi salla tare ne turarenta yayimin qarfi da yawa".

Dan qwarya qwaryar zama sukayi cikin falon na duba lafiyar juna,qananun zolaya tsakanin amna farouq da musaddiq abban yana shiga yana raba gardama kafin daga bisani anni tayi umarni

"Abinci ya zama ready.....zaku shiga ku watsa ruwa tukunna ko?" Ta fada tana duban abba me gayya me aiki

"Hakan yana da kyau ko me babban suna?" Ya maida tambayar ga fu'ad. Murmushi kadan ya saki,suna girmama ra'ayinsa qwarai,sunan da yake dauke dashi ya bashi wannan girman a iyalin da suka san girma da martabar sunan. Wani abu da sam sam bai gani ba ga maamah,tana iya kiransa a lokacin quruciya da sunan ta kuma zabga masa zagi fada da sauransu

"To abba" Ya amsawa Alhaji hamza yana miqewa. Farouq ne ya miqe ya dauki luggage din fu'ad din yana nufar qofa

"Muje na taka maka badon halinka ba......don wallahi ka shiga uku duk sanda mukayi aure muka barka kai kadai a gidan nan". Yayi maganar qasa qasa yadda su abba ba zasuji ba.

Harara fu'ad ya zabga masa yana jan qaramin tsaki

"Sannu tattabara sarkin aure?,yanzun ma idan kaga dama ka koma mana ka gani?......ni gwara fa ku qara gaba ku barni daga ni sai anni ko mayi kumari". Dariya ya fashe da ita harda buga qafa kadan

"Kayi asara wallahi.....kai ta qara qiba ma kake,kaci gaba da gandamewa a gaban annin?,idan bakayi wasa ba gaba gaba sadakarka za'a bayar Allah......"

"Munyi asara dai ni dakai mayen aure......idan kun tashi kuyi shelata a masallacin juma'a".

"Basai munkai ga nan ba......owner na diamondchore resources company guda.......ko a sirrance akayi shelarsa mugun ciniki zamuyi Allah,a zaba maka guda hudu qwarara......matsalar kawai har yanzun ni kaina bansan color na macen da kakeso ba.....". Shammatar farouq din yayi yakai masa wani wawan duka sai daya qame,don maganar ta fara isarsa,yasan kuma farouq baisan bari ba,baisan ya isa ba.

"Kaci bashi......sai na dauki fansa.....ka qarasa cikin da kanka na fasa rakiyar" Ya fada yana jingine masa luggage dinsa daidai qofofin sassansu

"Tafi nono fari" Fu'ad din ya fada yana zura key ma qofan sassansa yana budewa,saidai fuskarsa kwance take da murmushi yana juya halin farouq din. Shi daya farouq din yakewa haka.....kamar yadda shima farouq din kawai ke akwai 'yar hakan a tsakaninsu.

"Alhamdulillah" Ya furta a sarari murya can qasan bayan ya isa ainihin bedroom dinsa,yana jin ma'anar godiyar daga qasan zuciyarsa. Tarin godiya ce fal zuciyarsa game da ubangijinsa,godiyar da har wani lokacin ya dinga jin baisan ta yadda zaiyiti ba takai gurbin da akeso. Ubagijinsa ya gama masa komai.....ya kyautata rayuwarsa fiye da yadda yake tsammani.

Komai na sashen nasa a killace a kuma tsaftace akan tsari fiye ma da yadda yakeso. Wani irin qamshi ke tashi,abinda ya sanyashi sakin wata nannauyar ajiyar zuciya data sanya yaji wani nauyi ya ragu sosai daga saman zuciyarsa. Yana yiwa qamshi wani jarababben so,a duniya qamshin yana daya daga cikin jerin abubuwan da yafi qauna. Qamshi yana sanyashi maqalewa waje,kaman yadda akasinsa ke sanyashi rabuwa da waje.

Yana iya baiwa farouq dinsa komai amma indai ta fannin abinda ya shafi turare ne to zaka iya jin musunsa dashi. Bai yarda ba a taba masa turaruka,gwara ka zaba ko na nawa ne ya siya ya baka kyauta.

Kayan jikinsa ya dinga zarewa har sai daya rage saura fara qal din vest din jikinsa da gajeran wandon da bai qarasa gwiwarsa ba. Muradadde kuma ginannen jikinsan nan dake dauke da wasu lafiyayyun muscles dake alamta ainihin qarfi na siffa ta zahiri da badini ya bayyana,lullube da wadatattun gargasa ta ko ina. Wankan yakeson yayi amma shigowar kira ya hana masa hakan,tilas ya samu saman sofa bed ya zauna yana amsa kiran.

Amsa kiraye kirayen ya daukeshi lokuta masu tsahon da har musaddiq ya dinga zuwa dubashi zasuci abinci. Daga qarshe ya basu excuse akan suci din idan ya kammala zai fito.

Fitowar da bai samu daman yi ba kenan,don sanda ya fito a wankan gaba daya kasala da tsohuwar gajiya ce ta saukar masa,dole ya haye gadonsa bayan ya maida da dakin dark ta sakin dukka manya manyan curtains dinsa,ya kuma kashe kowacce fitila da zata iya bashi haske don baya son bacci a duhu sam sam. Koda baccin yakeyi kana kunnata ka tasheshi. Sunsha fafatawa da farouq akan hakan,don shi mutum ne da kwana cikin haske bai dameshi ba. Wannan dalilin yasa ko a yanzun yafi sha'awar kowa ya zauna a sassansa,ba kasafai ya fiya son takurawa mutum da salon tsarin rayuwarsa ba.

*****Su biyun dukansu suna zaune ne saman buzu na fatar dabbar da basusan wacce iri bace. Kaman yadda dukkaninsu jikinsu ke sanye da sutura ta alfarmar da zaka fahimci rayuwa ta basu sukuni yadda ya dace,saidai tasu salon miqa godiya wa mahaliccinsu da suka munana hanyarta.

Daga atamfar jikin hajja har lace din da maahma ke sanye dashi wanda ya darawa atamfar hajjan tsada isashen jari ne ga mutane masu yawan gaske. Kaman yadda jakar maahma din da takalman data sanyawa qafafunta suke wani jarin me zaman kansa ga wasu mutanen. Takalmin da fu'ad din yayi mata order dinsa da kanshi tun daga qasar Italy.

Kusan yadda ta bawa mutumin dan duqurqushi me zubin wada hankalinta hajja bata bashi nata haka ba.

Daya daga cikin qoqunan gabansa da suke kife ya daga,qoqon da babu komai amma saiga haske ya cikashi. Tafukan hannayensa ya saka yana rufe qwayar da hannunsa nasa. Idanunsa ya runtse,wasu irin maganganu ya dinga furtawa da ba'a gane abinda yake fadi,tun yana fada a hankali a hankali har ya fara furtawa da sauri da sauri da kuma qarfi har muryarsa tana amsa kuwwa. A hankali jikinsa ya fara wani irin kakkarwa tamkar wanda aka jonawa shocking. Da wani irin sauri yan fusge hannayensa daga saman qwaryar yana yarfar dasu kamar wanda wuta ta taba,sai kuma ya sake maidasun yana canza salon yaron da yakeji ba irin na dazu ba.

Ya kusa minti biyu a haka,wata irin zufa da basusan daga ina take ba ta gama jiqeshi sharkaf.....a hankali a hankali ya soma sassauta muryarsa sannan ya fara daidaita yanayinsa kafin ya bude idanunsa da suka ninka ja akan asalin jan da suke dashi.

"Matso!" Yace da maamah a tsawace. Tsoro ba kalma bace da ta santa ba kaf ray uwarta......qafafunta sun taka gurare da dama amma a yanzun saita samu kanta cikin shakka da d'ar d'ar har ta matso zuwa inda yake mata nuni

"Ba shine wannan ba?" Ya fada da qarfi yana nuna mata qoqon.

Fu'ad ne kwance saman gadonshi yana baccinsa hankali kwance kaman yadda ya kwanta a ainihin dakinsa dake gidan Alhaji hamza kibiya. Mamaki ya qarasa cikata,ba shakka fu'ad ne,kuma dakin ya mata kama da dakunan gidan Alhaji hamza,sun dawo kenan kaman yadda yake shaida mata dazu da sassafe kan suna hanya?.

Daga ita har bokan ba wanda ya samu cewa wani abu dif hoton dake cikin qwayar ya bace kaman an dakeshi harda tartsatsin wata wuta.

"Kin gani ko?,ba mutumin da muka sha wahalar kawoshi zuwa garemu saishi......baya ga haka kinga yadda surarsa ta dauke da gaggawa......abinda ke bamu tabbacin aikinsa yasha banban da dukka ragowar aiki da muka taba yi a baya......akwai tashin hankali......akwai wahala.......akwai kuma qalubale!!!" Ya furta da kakkausar muryarsa mara dadin amo da sauti bare sha'awar saurare.

Dukkan kayan aikin nasa ya tattara ya zuba cikin qwarya daya daga cikin qorai biyu dake gabansa,take suka bace bat tamkar ba'a taba halittarsu ba a wajen.

Jajayen idanunsa da babu rahama,musulunci ko imani a ciki ya daga ya kalli maamah dake dubansa babu ko qiftawa. *D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 54

Idanu yadan zuba mata na wasu mintuna da har sai data dan sha jinin jikinta. Sai kuma ya saki wani busashen murmushi da yafi kama da kukan jaki yana kallonta

"Ba shakka kin haifi jarumi......kin haifi yaron da taurarinsa suke da tsananin hasken da ba kasafai ake samun galaba ayi kutse a cikinsu ba ko asha kansu.......yaronki yana tattare da abubuwan al'ajabi da baiwarwarki masu yawan gaske wadanda ko ke uwar da kika haifesa bakisan yana dasu ba......cikin mutane dubu guda daya ake iya samu irinsa......". Kai kawai take jinjinawa tana sauraronsa. Tun sanda ta haifi fu'ad din tasan daban yake da sauran yara,to amma a yanzun kalamansa daga mata hankali sukeyi,kamar sunason shinshina mata rashin nasararta ne......kamar suna shinshina mata rashin yiwuwar aikinta?.

Maganarsa ta gaba ta bata amsa ta kuma yanke mata dukkan zatonta

"Aiki a kansa ba qaramin abu bane me girma......akwai tsari a jikinsa......yana da addu'a sosai tare da kare kowanne abu da musulunci yayi umarni akai.....baya shan giya.....baya zina.......baya kallace kallacen abubuwan haramun......hasalima azumin da addininku yace a dinga yi litinin da alhamis baya wuceshi.....abinda zai bada mamaki banda wannan uwar goyon nasa da uban goyonsa ba wanda yasan yanayin wannan azumin koda farouq makusancinsa......."

"Kana nufin yanzu mallakar da nakeso ayi masa.....da shiga tsakaninsa da iyayen goyonsa bazai yiwu ba kenan?" Ta dawo dashi zuwa ga ainihin amsar da takeso taji.

"Zaki iya samun biyan buqata.....zaki kuma iya samun faduwa......biyan buqatarki ya ta'allaqa da adadin sadaukarwar da zakiyi da kudaden da zaki ajiyewa shaqiqanmu don suyi miki yadda ya dace......amma fa....." Ya fada yana daga yatsa

"Tabashi abune da zai iya zuwa da hadari......mafi qarancin sakamako shine a gaza yin nasara a kansa......muddin rashin nasarar ta zarta haka kuwa.....dani da dukkan wani shaqiqi da mukayi aiki dashi zamu iya samun nakasa,harda shudewa daga rayuwa ma idan ta dauro,saboda haka......aikinki aikine me tsadar gaske " Yayi maganar yanayin muryarsa daga qarshe yana canzawa alamu dake nuna saukar mutanen boyen da yake aiki tare dasu a kansa.

Tsoro yadan shigeta kadan amma ta dake

"Kamar nawa zai kai?" Ta fada a dokance

"Kalli nan!" Taji an furta daga bakin mutumin amma da mabanbantan muryoyi marasa dadi da batasan mutum nawa bane suka hadu suke maganar.

Waiwayawa tayi tana duban inda ya daka,saiga lambobi a jere wanda data dubesu da kyau suka bayyana kansu a matsayin million goma.

Sosai adadin ya daketa,duk da tasan a qa'ida tana cikin arziqin data bawa wannan adadin baya amma kuma batakai ga samunsu ba zuwa yanzu. Ta waiwaya ta kalli hajja dake zaune tana kallon komai,don dokarsa shine me matsala dashi yake magana. Da idani ta mata tuni da tsarinsa,baya yanka kudi a nemi ragi.....daya daga cikin kusakuren da zaka iyayi wanda zai tunzurashi kenan.

Kamar wadda wuyanta ya qage ta maido dubanta gurin,saidai zuwa sannan lambobin da hasken da suka nuna mata yawan abinda zata biya din ya shafe daga wajen ba komai. Ta maida kallonta ga duqurqushin bokan da kamanninsa suka juye,saita gyada kanta

"Na karba na aminta"

"Karki qara minti daya a wajen nan......kizo da sadakin aikinki kuma nan da kwanaki uku kacal" Daga haka ya bace shi da dukkan sauran tarkacen dake wajen,sai gurin ya rage daga ita sai hajja din. Zumbur suka miqe kaman yadda ya umarta,suna riqe da hannun juna suka fara fitowa daga sarqaqiyar har suka cimma inda suka faka motarsu.

Sau biyu hajja tana juyawa tana kallon maamah wadda ta kafe kwaltar da driver ke zabga gudu akai. Tunda suka fito daga wajen bata ce komai ba,magana bata hadasu da kowa ba. Tun a dazun ta fahimci tayi nisa ne qwarai a tunani,kaman ta qyaleta amma sai ta kirayeta don tanaso taji ta bakinta

"Banji kince komai ba tunda muka fito?" Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke sannan ta dora idanunta akan na hajja din

"Daga yanayin ayyukansa,da kuma bayanansa kawai na gamsu cewa aikinsa me zafi ne......abinda kawai ya tsayemin a rai yanzu shine ta yadda wadannan kudaden zasu samu" Tayi maganar alamunta suna nuna lallai lallai a matse take da buqatar mafita

"Danki ne,dole ki bashi umarni yabi don babu wata uwa sama dake......idanma hakan bai yiwu ba,cikin kadarorinki ki saida wani abu.......ko kice masa wasu zaa yiwa wani abu da kudin da zarar yasa anyi abun ki saida abun kiyi zarafin gabanki". Ajiyar zuciya ta sauke ranta yana mugun baci

"Yanzu har takai idan ina da buqatar abu a wajen dana saidai nayi qarya ko na biyo ta wata hanyar?" Ta yiwa hajja tambayar.

"Biyan buqata ai yafi dogon buri,kome ya faru.....kuma kome kika saida,wuyarta aiki yayi yadda akeso......sai kin maida ninkin baninkin da bakisan adadinsa ba......sai kin karba kin gaji......saikin tara fiye da yadda kike buri......saikin zame musu tamkar abun bautarsu wajen yi miki biyayya.....a yanzun da zan kira auwal dake wata qasar,nace masa ya dawo nigeria yau yau inason ganinsa.......na rantse miki da Allah a qasar nan zai kwana,koda babu jirgi bazai kwana a gida ba saidai a airport.......saidai idan nice nace masa ya koma gida ya kwanta ya taso gobe......koda ya koma bashi da cikakken nutsuwa har sai gari ya waye ya kawo kansa gareni......bari yau zan nuna miki qarfin ikona ki gani da kanki" Ta fada tana fiddo wayarta daga jakarta.

Kai ta jinjina kawai tana dubanta,tana jin inama ace itace hajja?.....tana hasashen ranar da wannan damar zata samu a hannunta?.....tabbas saita sanya aminatu kuka da idanunta........sai ta sanya zuciyar aminatu da hamza sun buga da qasqancin da zasu gani daga yaran da su suka rainesu har suka zama abinda suka zama a yanzu

(Tabbas gaskiya ne da akace ka guji sharrin wanda ka kyautatawa.......me makon jin dadi kyakkyawan fata da kyakkyawan mu'amala ta shiga tsakaninsu da mutanen da suka maida mata 'ya'ya mutum.....amma ga nata salon sakamakon,Allah kayi mana tsari daga sharrin dukkan wani abu me sharri mutum ko aljan,me rai ko maras rai ameen ya hayyu ya qayyumu).

Bugu daya tak aka daga kiran da hajjan tayi,muryarsa ta fito tarwai yana gaidata. Cikin kulawa ta amsa masa sannan tace

"Kaga yahaya.......naje unguwa ne sai na sallami driver da xummar zan tuqo kaina na dawo gida......."

"Me yasa hajja?,ta yaya zakiyi tuqi da kanki?" Ya fada a tsananin firgice kaman wanda akace masa ta hallaka. Murmushin qasaita ta aje

"To ai yanzu ma gashi na kasa dawowa din da kaina duk kasala ta rufeni...."

"Bari na kira driver din ya dawo ya maidaki" Ya furta da hanzari

"Kaga dakata.....wanne irin driver?" Ta fada tana bata rai

"Yi haquri hajja,me kk so?" Ya sake fada a rikirkice

"Matarka nakeso ka turomin ita zata maidani......kace ta kirani na bata kwatancen inda nake yanzu haka ina jiranta......kada kuma ta batamin lokaci" Ta fada tana bata rai

"An gama" Ya fada zuciyarsa na rawa.

Ta rigashi ajiye wayar ta waiwaya tana kallon maamah cikin murmushi

"Kinsan matar da nace a kiramin?" Kai maamah ta girgiza tana shakkar yiwuwar wanzuwar umarmin da hajjan ta bada yanzu yanzu

"Matarsa ce......itace taso dagamin yatsa taso tayi fito na fito dani,a zatonta tana da malaman da xasuyi mata aiki fiye da nawa......tanaso ta mallaki yahaya ta mallakeni.....har na sanya ya saketa na sakashi ya dawo da ita don tazo taga iyakarta......taga iya mizanin nawa aikin.....don tazo ta banbance tsakanin aya da tsakuwa,ta sake kuma fahimtar da gaske fa shi ruwa ba sa'an kwando bane......ita kanta a yanzun sai yadda nace mata,duk dana fahimci kanta yana fusga wani lokaci kaman wasu abubuwan idan nayi mata tana jin ciwonsu,shi yasa nakeson na qarasa horata da kyau" Kai kawai maamah take jinjinawa,abun yayi mata da kyau.....salon kuma ya burgeta yahau mizani da gwargwado na abinda take hasashen shimfidawa kanta. DA FUAD DA MUSADDIQ DAMA MATAYEN DA ZASU AURA SU ZAMA QARQASHIN IKONTA. wannan shine cikakken iko da isar UWA. Ta fada a ranta

"Wannan shine cikakken iko da isa.....ki katange komai kaman yadda sanda kk sha wahalar komai din ke daya kk sha" Hajja ta fada tana jinjina kai

"Indai ni na haifi fuad ya zama tilas ya fidda kudaden nan ya bani.....zan motsa masa qwanjina.....zan kuma banbance masa uwa da mahaifiya a wannan lokaci karo na farko" Maamah ta sake fada a ranta.

Ya jima riqe da wayar bayan gama waya da mahaifiyar tasa yana juya wayar a hannunsa. Sassa biyu na zuciyarsa kowanne na qalubalantar dan uwansa.

"Tayi daidai,ko mutuwa hajja tace muyi daidai ne......ai ta isa....girmanta yana da yawa,to laifin me ma tayi?,koni ta kira zuwa zanyi bare matata,komai tayi a kowanne lokaci ko yanayi daidai yake" Daya sashen yake fadi,yayin da daya sashen zuciyarsa yake cewa

"Ta yaya tana tsaka da hidimar gida,ya tabbatar yanzu haka tana can tana yiwa hajjan girkin rana daya zama wajibi aka kowacce matar danta tayi mata shi kulli yaumin rana da dare ba fashi......(tsarin girkin abincin gidan tsarin girki ne na bai daya,duk da irin girma da wadatar gidan tukunya daya ake dafa abincin safe rana dana dare,raba girki ne a tsakanin faccaloli tamkar kishiyoyi,kowacce zatayi kwana biyu 'yar uwarta ta karba,hakanan a tattare a babban dining room dake dauke da family dining table akecin dukka abincin. A nata fadin don a tattala mata dukiyar 'ya'ya,kuma dukkansu zasu samu sauqin kashe kudi a gidajensu,tunda kome zaa siyo hadin gwiwa zaayi a kawo......amma kuma ta gefe daya.....tsabar nuna isa izza da mulki ne,da kuma dabarar karantar motsin kowa cikin gidan ba tare data shiga sashen kowa ba don ta tattaro kowa din waje daya.

Readers Also Read