A d u n i y a ta complt by huguma - Chapter 19
A d u n i y a ta complt by huguma Chapter 19: A d u n i y a ta complt by huguma Chapter 19. "Ba rashin kunya tayi ba muhammadu......fada ta yiwa…
4,489 words
"Ba rashin kunya tayi ba muhammadu......fada ta yiwa musaddiq,kuma ai ta fadi gaskiya ne,ta kuma yi daidai,sun tafi yawonsu sun barni,a jikina kuma babu inhaler kwata kwata,a nata ganin indai hakan taci gaba da kasancewa komai ma yana iya faruwa". Shuru ya ratsa tsakanin bayanin anni,yana ji kawai annin tana son bata kariya ne saboda halinta na bawa kowa uzuri komai girman laifin da ya aikata mata
"Is okay....." Ya fada yana sauke siririyar ajiyar zuciya a qoqarinsa na fesar da bacin da ranshi yayi
"Ya jikin naki anni?"
"Jiki alhamdulillah na warware"
"Suna kula dake kuwa?" Ya sake tambayarta da wannan seriousness din nashi. Murmushi ta saki kadan
"Qannenka suna qoqari sosai,ina samun kulawa tamkar kana nan.....saidai kewarku,ina fatan komai yana tafiya kaman yadda aka zata?,kowa kuma yana lafiya?" Murmushi ya saki,wanda mutum uku keda wannan baiwar sakashi murmushin koda baiyi niyya ba,anni abba da farouq kada ma farouq din yaji labari. Abune me wahala ka tsinci murmushi akan fuskarsa,akwai mutane da yawa dake da tambayoyi da yawa a kansa
Anya kuwa ya taba dariya? Wannan kuwa yana murmushi?.
Wasu tambayoyin na isa kunnensa ta harshen farouq,wasuma kam baisan ana yinsu ba.
"Ba zamu wuce kwanaki hudu ba anni in sha Allah". Farinciki ya wadaci fuska da zuciyarta
"To ma sha Allah.....amma baka shaidamin ba me babban suna?,banda na tambayeka da ba zaka gayamin ba ko?".
"Aah anni......banason na sanyaki wannan hidimar me yawa" Murmushi ta sake saki
"Hidima ai bata qarewa Muhammadu muddin akwai rai a jikina.....fatan da zakuci gaba da yi mana shine Allah ya qara mana lafiya....."
"......da nisan kwana me amfani" Ya qarashe fadi. Qaramar dariya ya sanyata a wannan karon
"To da nisan kwana me amfanin mu daku gaba daya".
Koda suka gama wayar baiko motsa ba a wajen,yayi zaune da wayar kawai a hannu yana juyata. Duk yadda zai fasalta anni a rayuwarsa da zuciyarsa bazai kwatantu ba. Ita din uwa ce data amsa sunanta na uwa. Wadda tayi sadaukarwa da yawa cikin rayuwarsu,sadaukarwar da tayi musu ba qarama bace,sadaukarwa ce da UWA kadai ke iyayi wa danta.
Asthma dinta bata taba hanata taba ruwa saboda su,asthma dinta bata taba hanata sammakon tashi koda da sassafe ne a lokacin da hazo da sanyi suka lullube sararin samaniya......a yanayin da kuma yafi zama barazana ga masu lalurar......asthma dinta bata hanata tsaftace musu muhallin kwanansu......bata hanata dafa musu abinda zasuci *D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 50
koda ita din bataci ba,bata kuma hanata kulawa da lafiyarsu koda ita din bata da cikakkiyar lafiya. Har tsakiyar zuciyarsa yana jin wata qauna me girma tana tabashi game da anni,tayi musu abinda baki bazai iya fadi ba,zuciya da ruhi ba zasu iya mancewa ba. Ta musu hidima da jikinta da kudinta da lokacinta harma da lafiyarta,irin hidimar da ya debe tsammanin zasu sameta,irin hidimar da suka buqaceta a yunwace daga wajen wadda tayi silar zuwansu duniya amma ta gagaresu.....kulawar da baiyi tsammanin zasu sameta ba daga gurin kowacce mace a duniya. Baiga abinda zai samu a duniya ba da zai manta da anni.....baya tunanin akwai abinda anni zata nema daga gareshi ta rasa.
Yana shirin sauke wayar tasa don ya tattara tarkacensa ya wuce daki ya samu bacci koda na awa biyu ne kafin zuwan lokacin sallar asuba sai kiranta ya shigo.
Kamar ko yaushe ya zubawa kiran idanu,a duk sanda zata kirashin sai ta tuna masa da abubuwa masu yawa. Aduk sanda kiranta zai shigo wayarsa saita tada masa wani abu daga can qasan zuciyarsa.
Bashi da wani zabi da ya wuce ya daga din,sai ya sake zama sosai ya ya dauki wayar yana karawa a Kunnensa,
Cikin jin isa da izzar cewa ta haihu.....cikin isa da jin izzar ita din a yanxu wata abace cikin duniyar.....cikin jin izzar ta isa takai qololuwar gata a cikin jerin iyaye mata ta amsa sallamarsa.
"Barka da dare.....an wuni lafiya?". Maimakon ta amsa masa saita sake daidaita kanta,a dake take masa magana
"Yanzun ace bankai kima da martabar da a kullum zaka kirani kaji ya na kwana ya na tashi ba?" Ta maida masa gaisuwar da qorafin abinda me masa suya a qirji.
"Afwan.....kiyi haquri" Ya zabi furtawan. Har cikin zuciyarsa,har kuma tsakaninsa da Allah kirantan kaman yadda take buqata wani baqon abune cikin rayuwarsa dama lokutansa. Yadda ta zamewa rayuwarsu baquwa haka dukkan wata mu'amala da zaiyi da ita take zama baquwa a wajensa. Koda yayi niyyan yin hakan saboda sauke nauyi da haqqin haihuwa dake wuyansa sai ya manta sam sam,tunda abune da aka fareshi bada dadewa ba,sabo dashi kuwa zai dauki lokaci kafin ya shiga jiki da zuciya,bayan haka ma......kwata kwata mu'amalar dake a tsakaninsu wata irin tattaurar mu'amala ce da babu taushi a jikinta bare ta shiga zuciya da kyau ta tsayema tunani.
"Koda baka nemeni ba ni bazan zubewa duniya ku ba.....ku zama inuwar giginya na nesa kasha dadi...." Ta fadi tana watsa hannuwa ba tare data tuna da kuskuren rayuwarta na farko ba.
Numfashi ya aje,maganartata ta zama tamkar wani tuni ne daya dace ace kanta da kanta ta yiwa shi
"Ba zata zubewa duniya su ba....." Baisan zubewa ta nawa ya rage tayi musi ba,kalamanta a kullum sake haska masa ita yake,yayi imani yana kuma sake samun gamsuwa da dalilai masu tarin yawa dake bayyana masa lallai AKWAI DALILIN dawowarta cikin rayuwarsu......lallai ta dawo ne bawai da sunan nadama ba ko gyaran kuskure......AKWAI DALILI AKWAI KUMA HUJJA.
Wasu yana kallonsu shimfide a zanen tafin hannun qaddararsa,wasu kuma baisan daga inda zasu soma bullo musu ba.
"Ba'a canzawa tuwo suna Muhammad,kuma ko ma meye ka zama sai dana haifeka sannan ka zama din......mahaifiya daya ce kuma ni dince dai". Idanunsa ya lumshe na wasu sakanni kafin ya samu budesu. Ba abinda maganganunsa ke haddasa masa sai sake jagula duk wata qanqanuwar nutsuwa tasa da yake qoqarin samarwa kansa.
"Kiyi haquri" Ya sake maimaita mata kalaman da ta dade da haddacesu daga bakinsa.
"Yaushe zaku dawo?,idan ba nan kusa bane dawowar taka ka sanarmin......don nasan sai yadda akayi dakai,sai kuma abinda aka shimfida maka".
Yaji saukar kalamanta sosai har saman zuciyarsa. BATA SON AHALIN ALHAJI HAMZA KIBIYA ya dade dayin wannan karatun a qanqanin lokacin data duro cikin rayuwarsu......ya kuma san halinta tun daga sanda ya fara rarrabe abubuwa har zuwa sanda ta fice daga rayuwarsu. Idan batason abu bata sonshi kenan......dadi ko wahala basa sauyata akan abun. Idan taqi taqi kenan.....hakanan idan taso taso kenan......bata ja da baya akan duk abinda ta sanya a gaba......bata rasa ABUN HARINTA komai dadewar lokaci.
Wadannan abubuwan ya sanya ya sanya dukkan wata nutsuwa da karatu nasa a kanta......ya sanya duk wani nazari da dogon hange da tsinkayensa a kanta,yasan wacece......sanin da ita kanta batasan bata kuma yi zaton yakai zurfin haka ba.
"Ba zamu wuce satin nan ba in sha Allah" Ya amsa mata kamar yadda ya amsawa anni a dazun.
"Har sai ankai sati?" Ta masa tambayar a zaqe,har abun yadan so bashi mamaki,don sam salon tambayar nata baiyi kama da ta zaqu ko tsahon kwanakin sun mata yawa da zasu bayu ga ganinsa ba,tabbas yasan akwai dalilin tambayar a qasa.
"In sha Allah" Ya bata tabbaci yana jiran dalili na gaba
"Kudi nake buqata ka turamin ta account dina akwai amfanin da zanyi dasu......kada suyi qasa da million daya" Tayi maganar kanta tsaye cike da karsashi da qwarin gwiwa kaman yadda hajja ta kwatanta mata.
Mamaki kadan ya kamashi.....saidai ya ajeshi a gefe
"Akwai abinda baki dashi?,cikin gidan ko sutura ko wani abu makamancin haka?,ko akwai wanda kike da buqatar ayi masa wani abun?"
"Duka babu ko daya.......shin waima sai ina da wannan buqatun zan buqaci kudi daga wajenka?,yarinya ce ni qarama ko kuwa?,ko banyi isar da zaa dauki tsabar kudi a bani ba har sai akwai dalili ko hujja?"
"A'ah......"
"To dakata......ba sharhi nakeso ba......kayi abinda nace daga yau zuwa gobe". Sai yaji alamun yanke kiran,abinda ya tilasta masa sauke wayar daga Kunnensa yana binta da kallo.
Yatsunsa kawai ya dora saman goshinsa yana murzasu a hankali,kadan kadan yake furzar da iska me zafi daga bakinsa. Tabbas yasan da akwai wani abu......akwai wata a qasa......
Wanzuwar kudi a hannunta kwata kwata ba alkhairi bane,kuma ko yanzun bayajin alkhairi ne ya sanya ta nema.
Cikin lokaci qanqani yaji jijiyoyin kansa sun qara adadin gudunsu da kuma harbawarsu,abinda ya haifar masa da fara jin alamun ciwon kai. Bayason hayaniya......bayason matsala kwata kwata,wannan ya sanya yake nesa da mutane da al'amuransu,banda kasuwanci daya daukoshi tsundum ya jefa cikin mu'amalantar mutane qarfi da yaji.
Ba wani karsashi ko qwarin gwiwa ya dauki dukan abinda yasan yana da buqata,a maimakon tattare takardun nasa gaba daya da yayi niyyar yi ya kuma shiryasu kamar yadda ya saba. Yana da wani irin tsafta da duk abinda yayi amfani dashi zai wahala ka sameshi ba'a killace ba.
Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya tura qofar dakinsa idanunsa akan dakunan abba da saddiq daya tabbatar zuwa lokacin sun jima da yin bacci,wani lokacin sai ya dinga ji kamar su kadai ne basuyi sa'ar rayuwa ba.....sai ya dinga ganin kamar kowa ya dace da rayuwa me kyau amma banda su. Duk sanda irin wannan tunanin ya fado masa yakanyi qoqarin korar shaidanne daga ransa.
A gefan gadon ya zauna,ya miqa hannu ya kunna bedside lamp,dan siririn hasken da baida takura da yawa ya bayyana. Hannunsa ya zura qasan drawer din da fitilan take kai,ya ciro wani mini wallet dinsa,ya bude ya sake zaro wani qaramin hoton dake ciki.
Duk da hoton baida cikakkiyar kala amma fuskar mutumin ta fita sosai,kamannin nan nasa da murmushinsan nan da idan ya kalla sai yaji kaman idan ya kirashi zai amsa.
Wani abu ya tsaya masa a wuya,yayin da idanunsa suka sauya launi,gefe daya wani qaqarfan abu da ya jima yana kokawa dashi akan maamah din ya fara taso masa,sai ya fara hadiyar zuciya kadan kadan yana qoqarin hadiye bacin ranshi,tamkar me hadiyar lomar abinci,don daga inda inda kake kana iya hangen Adams Apple dinsa daya zamewa wuyansa dama fuskarsa ado yana kaikawo daga sama zuwa qasa.
A duk sanda ya kalli fuskarsa cikin hoton sai yaji duk duniya ba wanda ya kaisu maraici......a duk sa'ilin da zai kalli wannan jarumar fuskar sai yaji zuciyarsa ta cika da qiyayyar kowacce d'iya mace a duniya idan ka debe anni da manal......wata irin wuta ce take ruruwa a zuciyarsa a kanta......har yakanji kamar bazai iya sake kusantar muhallin da take bama ballantana yaci gaba da accepting nata ko kyautata mata a matsayin uwa.
Fuskar abban wata fuska ce da a kullum take tunasar dashi gwagwarmaya da ainihin ma'anarta.....fuskar tasa fuska ce dake karanta masa tare dayi masa bitar cusgunawa....uzzurawa da azabtarwa irin ta diya mace. Kowanne hoto nasa da abinda yake karanta masa.....hakanan da abinda yake tunasar dashi. Ko kusa ko alama....ko sau daya.....hakanan koda wasa bai taba sha'awar aure ba ballantana wata diya mace. Yana kallonsu a wasu halittu ne na daban da babu imani ko tausayawa cikin lamuransu.
Sanadin ciwon abban....da silar data sanya ya dinga ci gaba abune da bayason tunawa,abune dake dake tilasta zuciyarsa juyawa MAAMAH baya da dukkan abinda ya danganceta. Koda ya tuna da abin a sanda take daura dashi yakanji baya buqatar kallon fuskarta ko kuma sauraren muryarta,yanaji cewa ba abinda zai bashi sukuni face yayi nesa da ita.
*_AKWAI WANI SIRRI.....AKWAI WANI BOYAYYEN SIRRI CIKIN DUNIYARSA_*
*******Sannu a hankali take tafiya cikin daya daga cikin layukan da suke zame musu turba kuma hanya ta isarsu gida a duk sanda suka rasa samun abun hawa ko kuma kawai jin rikici irin na dalibin dakan qirqirarwa kansa tafiyar qafa haka siddan.
Ita daya a hanya amma tanata mamakin yadda yau aka raba musu lokacin tashi daga makarantar alhalin tunda suka fara tsahon shekarun tare ake tashinsu. Ta cika tayi fam akan yadda nadra din da haneefa sukayi gaban kansu suka taho gida abinsu ba kamar yadda suka saba ba abinda basu taba yi ba.
Gefe daya kuma na zuciyarta ya cika da saqe saqe tare da tunanin yadda zata qarqare haddace ayoyin qarshe na shafin da a yau zata bada haddarsa a islamiyya. Kaman daga sama,babu zato kuma ba tsammani taji an finciki qaramar jakar da take dan cillata a hannunta wadda ke dauke da muhimman abubuwa da dama. Sanda ta daga kai kuwa a firgice barawon ya soma nisa da ita yana gaya mata
"Idan kina da gata,ko kina da me qwatoshi ki turo shi" Sai ya juya cilla sassarfa ya fada wani lokon dake daura dasu.
Ko wanne sashe na jikinta rawa yake,tayi wata irin tsorata da bata taba yin irinta ba. *D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 51
Abune da bai taba faruwa da ita ba koda wasa,ta waiga gabas da yamma kudu da arewa,ba kowa a layin,babu gicci ko wulqawar kowa,ko cutas da ita zayayi zaiyi ne hankali kwance,abinda ya sake kada mata hankali kenan,ta soma yunqurin tattara dukkan qoqarinta wajen ganin tabar layin.
Taku uku tayi ya shawo kwana. Hannunsa riqe da jakartata da yanzu yanzu aka wafceta. Birki taja ta tsaya,gudun zuciyarta yana sake qaruwa kaman zuciyarta zata fito ta bakinta. Ta qura masa idanu tana kallonsa kaman yadda shima ita yake kallon. Guduwa takeson tayi amma ta kasa kaman an kafeta a wajen.
Duk taku daya da zaiyi yana sake ganin kamanni na jini da kuma yanayinta da SABREEN din. Yana mamakin yadda ta iya boye komai nata,yadda ta iya bad da bami,ta iya nutsewa da narkewa cikin sararin duniya ba tare da ka iya gano daga ina take fitowa ba ina kuma take komawa?.
"Karkiji tsoro......ni ba cutar dake zanyi ba.....jakarki na karbo miki,nazo wucewa naga abinda ya faru,karbi jakarki" Baya taja kadan,bata jin aminta dashi sam sam a zuciyarta. Wani irin raino da horo sabreen ta yiwa kowannensu na rashin yarda da baquwar FUSKA muddin sunanka NAMIJI.
"Da gaske nake miki.....ba cutar dake zanyi ba,idan kuma baki yarda ba ga jakarki nan" Ya fada yana ajiyeta a tsakaninsu sannna ya juya ya fara takawa yana barin wajen fuskarsa shimfide da murmushi,qasan zuciyarsa kuma fes cike da murnar samun CIKAKKIYAR NASARA da kuma tabbacin DAUKAN FASA mafi ciwo a gareta.
Sai data tabbatar ya bada tazarar da koda ya juyo zuwa gareta zaiyi wahala ya cimmata sannan ta taka ta isa ga jakar,ta tsugunna ta dauka,ba tare data damu da datti da qurar data debo daga qasa ba ta rataya tana maida idanunta kansa.
Tafiyarshi yakeyi baiko waiwayota ba,ta kalli jakar ta kuma kalleshi,sai ta buda bakinta a hankali tana furta
"Na gode". Cak ya tsaya tamkar dama yana dakon martaninta ne,sai ya waiwayo yana sake fadada fara'ar fuskarsa
"Nima na gode.....sunana....." Dakatawa yayi kadan saboda tuna wani abu da yayi
_"Tana da wayo,tana da hadari.....da alama kuma akwai abinda ta taka_ kalaman suka dawo masa kai fes
"Sunana BASSAM....kefa?" Ya furta yana murmushi tare da samun gamsuwar lallai sunan zaifi saurin isar da saqo a maimakon ainihin sunansa na NASEER. Bashi da buri baya kuma fatanbta fahimci komai har sai zuwa sanda komai din ya kammala......har sai zuwa sanda shi da kansa zai mata bayanin komai. A lokacin da yake buri da kwadayin jin sheshsheqar kukanta......a yanayin qunci baqinciki da kuma tarin damuwa da yake fatan ta hallakata......koda bata hallakata ba yana fatan tayi mata mummunar illar da koda gaba ba zata qara gigi kasada ko gangancin shiga shingen mutane irinsa ba.
"Kefa 'yammata?" Ya tambayeta cikin lanqwasa murya da tausasa harshe gami da sanya wani amo me sanya nutsuwa ga duk me saurare.
Lokaci daya ta danji ta samu nutsuwa kadan,sai ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ta bashi amsa
"Huda" Ta furta a nutse tana jin wani iri da kiranta da sunan 'YAMMATA da yayi,karo na farko cikin rayuwarta da wani ya taba kiranta da wannan sunan.
Murmushi ya sakar mata yana gyada kanshi gami da lumshe ido yakuma budesu a lokaci guda
"Nice name.....duk wanda ya baki wannan sunan ya iya zaben suna". Maganar tasa ta sanya fitar murmushin dole a saman fuskarta. Tadan murmusa kadan,abinda ya sake sanyashi ganin kamanninta muraran da sabreen. Wutar daukan fansanshi ta sake ruruwa cikin ransa.
Kai ta jinjina a nutse tana dan sadda kanta qasa kadan
"Autyna ce" Ta samu kanta da bashi amsa
"Antynkin nan tana ja da yawa.....ta iya zaben sunaye" Ta fada da ma'ana biyu,a zahirance kuma da harshen da ba kowane zai fahimci boyayyen sirrin dake qasan zuciya ba.
Dagowa tayi a karo na biyu ta sake kallonsa,sai taji wani dadi zuciyarta tana saki kadan. Duk wanda zaya so sabreen a wajensu basu da kamarshi......kaman yadda suke nisantar wanda zai kawo suka a kanta ko wanene.
"Nadan rakaki kadan ko?,ki fita daga layin nan,don har yanzu ban gamsu da sahihancinsa" Ya fadi yana duban gefe da gefansa bayan ya zube dukka hannayensa cikin aljihu.
Tayashi duban itama tayi gabanta yana dan faduwa,ta yaya zata iya jerawa dashi wai?. Amma ko kafin tace komai ya fara takowa zuwa inda take tsayen yana jifanta da murmushi,tadan ja baya kadan dole ta fara takawa ya rufa mata baya
"Kada ki damu,bawai zamu jera bane,ba wanda zaisan tare muke......kawai dai zanyi gadinki har ki aminta" Kalmar aminci daga bakinsa ta sanya taji ta sake,sai taci gaba da tafiya,shi kuma yana biye da ita da 'yar nisan tazara a tsakaninsu.
Duk wani taku nata guda daya yana lasafta yadda komai zai wakana......a yanzu bayan wutar daukan fansa dake ransa,wata wutar daban ta soma rura kanta da kanta a zuciyarsa.......bayajin koda ba komai tsakaninsa da sabreen zai iya qyale wannan danyar 'yar shilar ta wuceshi. Duk da bata qarasa 'yar uwarta ba a komai.......amma zata sama masa nutsuwa yayi yaqinin hakan ko yaya take kaman yadda ya dade yana tsara zai samu daga yayartata.
Bai tsaya ba har sai da qafafunta suka isa babban qofar gidan nasu,sai ya samu waje nesa kadan saboda gudun bacin rana da bacin aiki,ya tsaya kawai yana jifanta da wani mayataccen kallo tamkar mayunwacin zaki.
Har ta sanya qafafunta sai ta dakata ta waiwayo,suka hada idanu abinda ya bashi damat jifanta da wani shu'umin murmushi. Itama murmushin ne ya subuce daga bakinta tana jin cewa ya kyautata mata matuqa,abinda ba kasafai suke samunsa daga wajen al'ummar da suke kewaye dasu ba,don haka wannan din ya qawatar da ita. Bakinta ta bude a hankali ta furta kalmar
"Na gode sosai". Duk da tasan ba lallai ya iyajinta ba,amma zai karanci bakinta. Ya kuma karanta din,sai ya daga mata kai don haka ta juya tana shigewa cikin gidan.
Haka kawai murmushi ke fita a fuskarta tana tuna yadda komai ya kasance. Badan shi ba Allah ne kadai yasan abinda zai faru da ita a wannan qonannen layin da babu kowa. Ba yadda kuma zatayi,nan dinne dai hanyar wucewarsu tilo guda daya,inda da wata hanyar tabbas ba abinda zai sanyata ta sake bi ta nan wajen.
"Ke dawa kike murmushi ke daya?" Sabreen dake tsaye gaban fridge dinsu tana duba adadin pure water da lemon daya rage musu a ciki ta fada hannunta dafe da murfin fridge din. Cikin sauri ta gyara yanayin fuskarta tana qoqarin adana takalmanta data shigo dasu
"Ba kowa adda...." Idanunta ta zube mata sosai tana son karanto wani abu amma bata samu nasarar gano komai ba,saidai duk da hakan haka kawai takejin bata nutsu da irin amsar huda din ba. Emotions ke sauya yanayin fuskar mutum,walau na farinciki ko baqinciki,dole idan ya nuna saman fuska to akwai wani labarin a qasan zuciya.
Sakin fridge din tayi bayan ta rufeshi tana takowa tsakiyar dakin
"Wacce irin tafiya kukayi ne yau ke dasu nadra?,kinsan dai banason kuna raba tafiya ko?" Ta fadi tana zama idanunta still akan fuskar huda din.
Fuska ta bata ba kaman dazu ba tana duban sabreen
"Wallahi dama nace zamu hadu dasu.....kawai adda ina fitowa na samu wai sun wuce gida?,yau bansan me yasa aka rarraba mana lokacin tashi ba" Ta qarasa maganar fuskarta a bace da gaske. Idanunta tadan dauke daga kanta tana sauke numfashi
"Banason irin wannan tafiyar,kome raba lokacin su dinga jiranki" Cikin ranta tana jin abun kwata kwata baiyi mata ba.
Qaramar dariya ya sakarwa kansa bayan ta shige gidan. Fara takawa yayi hankali kwance yana barin layin. Tabbas shima zai buga nasa wasan yadda ya dace,zaiyi wasa da rayuwarta da kuma hankalinta yadda ya kamata......zai gigita mata rayuwa ya dagula dukkan wani lissafi nata......zai guntule dukkan wani farinciki nata kaman yadda ta gurgunta ta kuma dagula rayuwa da nutsuwarsa. Yanaji a ransa abun zai bashi nishadi qwarai,zai kuma qarasa goge baqinciki qunci da takaicin data qunsa masa.
********Cikin nutsuwar nan tasa yake saukowa daga matakalar jirgin riqe da kyawawan briefcase guda biyu. Tasa data Alhaji hamza kibiya.
Biye yake da dattijon,yana aje tasa qafar a duk muhallin da ya cire. Kamilallen dattijon da adadin furfurar dake baibaye a fuskarsa da kuma gashin kansa suka sake tabbatar da dacewar sunan dashi. Cikin kamala yake komai nashi,sanye da shadda dinkin babbar riga da maroon hula dara sak ainihin shigar marigayi malam aminu kano.
Muhammad fu'ad jadda,mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources wanda ke biye dashi a baya. Sanye cikin dinkin kaftan da yayi matuqar qara masa kwarjini da wani irin haiba me cika idanun me kallonsa. Idan ka kallesu shida Alhaji hamza kibiya din zakayi tsammanin shine ainihin mahaifi gareshi saboda yadda tsahonsu yake kusan daya da kuma murjewar jikin. Bayansa kuma sadiq ne janye da luggage dinsu. Shikam t.shirt ne jikinsa da trouser,ya lullube qafafunsa da lafiyayyen boots ba kaman fu'ad ba dake sanye da wani lafiyayyen halfcover ba dan qasar itali da aka samar dashi da dinkin hannu(sau da dama mu a nigeri muna raina takalman hannu,amma a qasashen qetare babu takalma masu daraja da tsada irin handmade shoes,wani ma kana ce masa handmade ne ka bata show din😂,nija my nation 🫡😂).
Tare suka jero kafada da kafada shi da Alhaji hamza din zuwa muhallin da farouq yafi tsaiwa a duk sanda yazo daukosu daga tafiya irin wannan. Ko a yanzun da suke nufar mota don isa gida ma duk hirar akan kasuwanci ce. Abun yana bawa Alhaji hamza mamaki. Duk qwarewarsa da qaunarsa da kasuwanci fu'ad din ya shallakeshi. Kowacce rana kowacce safiya,kowanne dare da wuni plan din rayuwarsa da komai nasa yana kan kasuwanci. Me za'a bunqasa?,me za'a qirqira?,me kuma za'a gyara?,ina ne nasara take a bunqasata?,ta ina faduwa take ayi hanzarin bawa gurin kulawa da kariya?. *D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 52
Yana jingine da motar yana kallonsu,idanunsa fes a kansu. Yana masa dadi yana kuma sanyawa ya manta cewa fu'ad ba dan uwansa bane na jini a duk sanda ya ganshi kamar haka da Alhaji hamza din. Yana alfahari yana kuma qara ninka alfaharinsa akan muhammad fu'ad din. Shi kansa ya sallama......jajirtaccen mutum ne da jajircewa take a cikin jinin jikinsa.
Ya maida idanu a hankali akan yanayin takunsa. Tafiya ce me cike da ginshira gami da cikakken kuzari da karsashin da zai bayyana maka adadin cikakkiyar lafiyar da yake da ita.
Daga abban har fu'ad din hankalinsu baya wajen,yana duba wani qaramin takardu da suke dauke da bayani da taswirar burinsa na gaba wato ginin katafaren kamfanin samar da kayan ado na sarqoqin mata da zai dinga amfani da wani sashe na ma'adanan da yake haqowa.
Tun daga fitowarsu gaba daya security guards dinsa da ya bari a gida kowanne ya koma kan aikinsa. Dukan inda ya ajiye qafarsa nan suke maida tasu.
Murmushi ya subucewa farouq,ya dawo kenan,kuma yanzun za'a fara. Bayaso abba ne ya tilastashi daukan guardsmen duba da yanayin qarancin tsaron da ake fama dashi. Uwa uba ma zaiyi wahala a nasibin rayuwa daya samu......da irin mu'amalarsa ace ya zauna haka gayansa yana yawo babu masu tsaron lafiya tattare dashi.
Wani lokacin idan yaso yana kubce musu ne yayi fitarsa shi kadai a mota yasha iska ya dawo. Ba kasafai ya fiya son fita qasashen waje sai idan harka haka ta taso takai kayan da sunyi yawan yayi wakilci......amma yanzun ya koyi fita din lokaci bayan lokaci haka siddan ma don ya samu ya sarara yayi rayuwarsa shi kadai. Mutum ne da bayason matsi,bayason takura,zai iya rayuwa me dogon zango shi kadai a wani muhalli na daban,shi yasa ko a yanzun a sassansu gini ne me zaman kansa dake dauke da bedroom and parlor da toilets kowa shi kadai. Saddiq da musaddiq sun hade dakunansu saboda kowa nashi apartment din ya masa girma. Amma oga fu'ad shi daya ne a nashi,hakama farouq,sai shi farouq din da lokaci bayan lokaci yakan dawo sassan fu'ad din yayi kwanaki yana kwana a nan sannan ya koma wajensa.
Kullum ya hangi fu'ad din daga nesa ba abinda yake tunawa sai wannan matashin dan bautar qasar,mara tsoro kuma mara shakka,cikakken jarumin daya shiga yankin daba nasa ba,yayi abinda koda haifaffen yankinne ya aikata bazai sha ba.....ya kubuta da tarin nasara. Farouq yadan sake murmusawa yana tuna yadda yaci wahala bayan uban gudun da sukayi,ya tuna yadda fu'ad din yayi jinyarsa tamkar ba dashi akayi gudun ba
"Ba abinda nakeji man.....ni dakai ba daya bane,sau nawa ana gaya maka ka dinga gym saboda yuwuwar samuwar irin wadannan lokutan na qwatar kai?,sai kuyita zama kaman mata,baku da wani banbanci dasu?" Ya tambayi farouq din a wancan lokaci yana dage masa dukka girarsa bayan ya bashi maganin ciwon jiki yasha.
"Yanzu wannan pain killer din da kake fana dashi......da warm water da fenugreek kake sha da yafi maka amfani". Harara ya balla ma fu'ad din yana dubansa
"Ba zaka qarasa kasheni ba da wadannan home remedies din naka ba" Sai ya juya ma fu'ad din baya yana sauke numfashin wahala yabar fu'ad din da sakin siririn murmushin nan nasa me tsada. Miqewa yayi yana dauke cup din
"Idan home remedies bai kasheka ba......son jiki da rashin exercise....aci a kwanta duka ya kasheka......naga wanda zai aureka da qaton tumbi" Ya qarasa maganar yana jefa kwalin lemo a dutsbin. Duk da farouq na cikin yanayi a sannan saida murmushi ya qwace masa.....fu'ad mahadin rayuwarsa ne kuma mahadin zuciyarsa ne kaman yadda ya tabbatar a wajen fu'ad dinma haka yake.
Kafadarsa y Ta dama yaji an daka
"Murmushin me kake kai kuma?" Sassanyar muryar nan tasa sake cakude da wani deepness ta shiga kunnen farouq. Kallonsa ya dora saman fuskar fu'ad din yana jin yawan kewarsa da yayi
"Ina nan ina kallon gujajjen dan bautar qasar nan da bai kammala service dinsa ba sai a garin kano". Murmurshin nan da shi daya ke iya fidda masa shi daga kan fuska ya saki kadan yana sake kaiwa kafadarsa duka. Dariya kadan ya saki shima farouq din
"Ina hasaso yadda zasu cinye namanka danye duk sanda suka fahimci daga ma'adanin qasarsu ne aka samar da attajirin nan mamallakin jadda diamondchore company........" Murmurshin ya sake sanyashi saki,sai ya saka tafin hannunsa saman wuyansa yana dan karyar da wuyan kadan
"Naman muhammad jikan jadda yafi qarfin cinsu umaru...." Ya bashi amsa da anihin sunansa,abinda ya sanya farouq din sakin dariya sosai. Kafadar fu'ad din yadan bubbuga