Kenza eBookz

A gidana complete novel - Chapter 1

A gidana complete novel - Chapter 1

A gidana complete novel Chapter 1: A gidana complete novel Chapter 1. [10/27, 10:33 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: *A GIDANA*

4,482 words

[10/27, 10:33 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: *A GIDANA*

In the name of Allah the most Beneficent the most merciful. Praise be to Allah lord of the words. The beneficent the Merciful. Master of the Day of judgement. Alone we worship;Alone we ask for help. Show us the straight way The way of those on whom Thou has bestowed the Grace, those whose portion Is not wrath, and who do not go astray.

聽聽 Gaisuwa tare da jinjina da fatan alkairi gareku daukacin masoyana, ina mika sakon gaisuwa gareku, dafatan kowa yana lafiya, musulmai da suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansu, mu da muke da rai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, masu ciki Allah ya saukesu lafiya, wadanda ke neman haihuwa Allah ya basu, masu neman aikin yi Allah ya taimakesu yasa su samu Ameen suma Ameen. _Oh ina fatan me karatu yayi saurin cewa Ameen..... lol duk da nasan ke ko kai ka fada.........._

Dafatan za'amin uzurin jina shiru da akai馃槃

_Sai dai dan Allah inaso mai karatu yamin uzuri akan wannan littafin bazan samu damar yin posting kullum ba saboda wasu dalilai._

Nagode馃グ

馃崁 *A GIDANA*馃崁

*_Na Ayusher Muhd_*

*Shafi na Farko*

Da sauri ta gama shafa hoda sannan ta dau dankwalinta ta daura, agoggo ta kalla sannan ta jawo jakarta da sauri, ta bude wardrobe ta dauko mayafinta ta rike a hannu ta fito.

Kitchen ta nufa dan tasan yana ciki, tana shiga ya juyo ya kalleta yace "Honey an fito?"

Rugumeshi ta matso tai tace "Yau wani irin bacci ne ya kammani dakyar ma bude idona."

Murmushi ya mata sannan ya sumbaci kuncinta yace "your tea."

Dauka tai ta kalleshi sannan ta sumbaceshi itama tace "Thanks love."

"Kin manta ni zan kaiki?" "Oh! Ashe fa na sallameshi."

Kai ya girgiza yace "Honey a rage fada, dan Allah drivers nawa kika kora?"

"Ka zauna zani da kaina." Ta fada tare da juyowa, da sauri ya riko hannunta yace "na manta sune basaji."

Harararsa tai tace "wato ni uwar fada ko?"

"Nooo inji wa? Yanzu na dau mataki?"

Murmushi tai tace "ni ka bari na tafi da kaina yafi sauki."

Key dinsa ya dauko wanda ke saman fridge yace "muje."

Falo suka fito hannunsu rike da juna, Goggo suka gani zaune tana kallo a falan.

Kusa da ita ta karasa tace "Goggo ina kwanan mu?"

Goggo ta kalleta tace "ni jiya mantawa kikai kince zaki bani kudin anko?"

"Oh na manta, amma ni Goggo wai wani anko ne ku manya daku?"

Fuska ta hade tace "ba sai kin fadamin magana ba, in bazaki bani ba kawai kice bazaki ban ba, fadar maganar na menene?"

Kallan agogo tai ganin lokaci na wucewa tace "zan bashi sai ya kawo miki."

Da sauri tai gaba "ke wlh Goggo, ina laifin ki bari sai ta dawo? Bayan na fiki bukatar kudi yanzu."

Harara ta maka mai tace "wannan damuwarka ce, kuma wlh ka kawon kudina yanda aka baka."

Binta yai da gudu, tana tsaye gaban motarshi yai saurin bude mata sannan ya zagaya ya shiga gun driver.

Yana zama ya tada motar yaja suka bar gidan.

Mai gadin daya bude ta kalla tace "zan turama kudi kaba mai gadi nashi naga wata yazo karshe, sai kaba Goggo na ankon, dan ko tambayarta ban ba nawa ne."

Yai saurin cewa to, kallansa tai tace "ka cinye kudinka ne?"

Kallanta yai sannan yadan sosa keya, ajiyr zuciya tai sannan tace "zan turoma dan dama anyi albashi, sai dai Honey plz adan rage kashe kudi."

Kallar tausayi yai yace " sry Honey."

Murmushi tai ta riko hannunsa da hannunta dayan hannun koma ta dan kurbi tea dinta sannan ta sakeshi ta zuge jakarta ta dauko wasu takardu tana dubawa.

Kallanta yai yace "in kaka nustu kina aiki you look soo......"

Kallan data masa ne yasashi yin dariya ba tare da ya karasa ba, tace "Honey a nemo wani driver din."

Ajiyar zuciya yai yace "wannan karan bari muga wanda zamu samo wata nawa zaiyi."

Kallansa tai tace "zaka fara ko? Wannan sai ya shekara 2 zuwa 3"

Dariya yasa yace "muna fata, amma indai wannan Honey dince hmmm."

Takardun hannunta ta cigaba da dubawa hakan yasashi yin shiru.

Suna isa yai parking, kallansa tai tace "bari na turama yanzu yanda zaka cirar mata nata dana mai gadin."

Yace to.

Nan ta dau waya ta tura mai kudi sannan ta dau jakarta ta fito, harta kusa shiga taji ya kirata, juyowa tai ya taho da sauri rike da tea dinta ya mika mata, thanks ta fada tare da nuna cup din alama ta amsa ta gode.

Ciki ta shiga, tana shiga cikin bakin kofar ta hade fuska tamau, duk inda ta wuce gaisheta sukeyi tana amsawa tana wucewa.

Tana shiga office dinta ta ajiye jakarta da tea din sannan ta juyo ta fito, gun program din ta fara shiga, kallan masu aikin gun tai wadanda ke kokarin ganin komai ya tafi daidai tai tace " acanza wannan background din is too light."

Da sauri yace "okay."

Kallan jikin camera's din tai kafin tace "meye hakan? Sau nawa zance a rage contrasts din nan?"

Da sauri yace "am sorry, yanzu zan gyara."

Dan ajiyar zuciya tai sannan ta duduba hasken light din gun sai da ta tabbatar komai yayi ta kalli agoggo sannan tace "is live so you have to be extra careful."

Da sauri sukace okay.

*********

聽 Da sauri ya fito daga soronsa ya fita waje, dan yanda ake kwalla sallama sannan daga jin muryar ya fahimci wanene.

Dan dattijon na ganinsa ya murtuke fuska tamau ya kalleshi rai a bace yace "Khalid karka batamin rai kar kuma ka bata min lokaci bani kudina."

Khalid ne ya kalleshi yace "Malam Mamman dan Allah kayi hakuri, ga dubu daya dazun nan aka biyani kudin fenti, gobe insha Allah......."

Dubu dayar ya amsa yace "karfa ka maidani dan iska, nan nan ubanka yai hatsari kazo kamar zakai min kuka na ara maka dubu goma ka kaishi asibiti yau wata hudu kenan amma haryanzu dubu biyar ka bani da wannan ta yau kenan, nifa shi yasa banasan harka da matsiyata wlh, ubanka yaki barinka kai aikin noma wai shi a dole sai kayi boko, to dakagama bokon uban me ka tsinana? Uban me kake dashi? Dubu goma ta gagareka biya a wata hudu? To wlh ni bazan dauki iskanci ba."

Khalid yace "kayi hakuri insha Allah zuwa karshen watan nan zan hada maka."

Tsaki yaja sannan ya wuce yana tafe yana masifa.

Shiru khalid yai sannan ya wuce ciki.

Mahaifiyarsa na tsaye a tsakar gida yana shigowa ta matso tace "Malam Mamman ne ko?"

Murmushi yai yace "eh amma bakomai Umma, ina Asiya? Ta biya kudin makarantar dana bata jiya?"

Tace "ta biya, haryanzu ba labari?"

Yace "Karki damu Umma insha Allah zan samu aiki." Idanunta ne suka ciciko tace "shekara 4 kenan da gama karatunka, sai dai haryau babu labari sai uban wahalar siyan form kake kana zuwa yin jarabawa."

Murmushi yai sannan ya danyi gaba yace "kiyi tamin addu'a, lokaci ne."

Kallan tausayi tamai, ciki ya shiga inda mahaifinsa ke kwance ba lafiya, saboda hatsarin motar dayai wanda yasa kafarsa daya ta samu matsala, ya dade yana sana'ar tokin mota sai dai lokaci daya tsautsayi ya hau kanshi komai ya zama labari.

聽 Kusa dashi yaje yace "Abba kanasan wani abu ne? Dan zan wuce gun sana'ar mu ne."

Hannunsa ya riko yace "Allah ya taimaka, in inasan wani abu zan sanar da mamanka."

To saina dawo. Abinda ya fada kenan ya mike.

Abba yace "adawo lafiya Khalid."

Fitowa yai daga dakin ya kalli Umma yace "na wuce."

Wayarsa ce tai kara ya dauka da sauri, Salmanu! Ya?"

"Kana ina?" 聽 "Ina danbatta ya akai?"

Salmanu yace "zaka samu zuwa kano yanzu? Dan wlh wani aiki ne muka samu gidan akwai maiko, kai sauri kazo."

Da sauri Khalid yace "turomin address din gani nan zuwa."

Nan ya kashe wayar yao waje da sauri.

Jakarsa kawai ya dauka a soro ya fita, yana zuwa ya samu mota ya hau ya nufi kano.

**********

A bangaren Adamu kuwa yana ajiyeta yai wata yar kara tare da duba account dinsa, gani kudi yasashi yar taka karamar rawa daga zaune, da sauri ya juya kan mota ya nufi Atm, yana zuwa yaciri kudin Goggo da za鈥檃 bata dana mai gadi, sannan ya ciri dubo goma yasa a aljihu, kida ya saka a motar yana tafe yana kada kai, yau akwai jin dadi a majalisa.

Jin dadin yanayi yasashi kawai yai ta dan yawo a gari, nishadi kawai yakeyi ji yake duk duniya ba wanda ya kaishi jin dadi.

Tsayawa yai yana kallan wanda ke kokarin tsalaka titi.

Fuskar sa ya kara kallo sai dai ya tsallaka titi, da sauri yaja mota ya nufi gefen titi yana binshi.

Horn din motar dayajine ya sashi dakatawa, juyowa yai cikin mamaki dan dai ba tare hanya yai ba.

Juyawa yai zai cigaba da tafiyar sa yaji ance 鈥淒anbatta.鈥�

Cikin mamaki ya juyo, bai gane mai maganar ba hakan yasa ya dan matso kadan.

Hannu ya daga mai tare da nunashi yace 鈥淒anbatta kaine wlh.鈥�

Khalid ya kalleshi yanzu kam ya ganeshi cikin mamaki yace 鈥淎dam?鈥�

Dariya Adam yai yace 鈥淒anbatta cinye duu daga ina haka?鈥�

Yace 鈥渄aga danbatta saukata kenan.鈥�

Shigo na karasa dakai.

Kallansa yace 鈥渒arka damu yanzu zan nemi taxi ko bus.鈥�

Dariyar dake neman kofcemai ya kara dannewa yace 鈥渟higo dalla.鈥�

Ganin suna bata lokaci yasashi zagayowa ya shiga.

Adam ya kalleshi yace 鈥渋kon Allah, kwaro ashe da raban zan ganka.鈥�

Ran Khalid yadan soso sai dai bai nuna ba yace 鈥渋nasu Zakar?鈥�

鈥淪una nan lfy, sai dai duk yanzu kowa hidimar gabansa yakeyi, kasan yanzu Zakar yana aiki a kaduna, Mansir kuma yana aiki a Abuja.鈥�

Khalid yai yake 鈥渕asha Allah.鈥�

Adamu ya kara kallan jikinsa yace 鈥渒waro ya? Kaifa? An fara aiki? A wani asibitin ko babban company?鈥�

Khalid ya kalleshi yace 鈥渕e kake nufi?鈥�

Adamu yai dariya yace 鈥渕e nake nufi kuwa? Kawai dai naga ne kai jarabawarka bazata wahalar dakai ba, duk fa shekararmu kai kadai ne ka fita da A class kaga kuwa ai kai sai babban company.鈥�

Adamu ransa ya baci, kallansa yai yace 鈥渁i ba wannan bane hujja komai lokaci ne.鈥�

Kai ya jinjina yace 鈥渉aka.鈥�

Sannan ya ja mota, shiru sukai kafin Adamu yace 鈥測anzu dai ba aiki kenan kake san cewa ko me?鈥�

鈥淓h.鈥� 鈥淥h Allah kenan yanda kaci karatu waya taba kawo haka?鈥� Kallansa yai yace 鈥渟aukeni anan, anan zan sauka.鈥�

Nan?

Khalid yace 鈥渆h.鈥�

Adam yai parking sannan yace 鈥渢o ya? Ko na samoma aiki? Dan ni bana aiki kasan ni banasan wahala sannan jarabawa ta ma dai to, sai a hankali, sai dai matata akwai kudi, tana neman driver ko kana sha鈥檃wa na samoma?鈥�

Kallanshi Khalid yai cikin mamaki, Adam yace 鈥測a? Baka yarda bane? Wlh bana aiki, sai dai ta ko ina a jiki nake.鈥�

Khalid yace 鈥渂a laifi.鈥�

Har ya bude motar zai sauka Adam ya zaro kudi yace 鈥済a wannan.鈥�

Khalid ya kalleshi yace 鈥渘o, karka damu.鈥�

鈥淣a manta ashe Mr Right ne, nasan bazaka amsa ba, amma ga numberta in kanasan aikin kamin magana.鈥�

Numbersa ya rubuta a jikin paper ya bashi.

Khalid ya amsa kawai ya fita rai a bace.

Adam yana ganin ya fita ya tuntsire da wata muguwar dariya, da sauri ya kira Zakari.

Nan ya fesa mai, ya kira Mansir shima ya fesa mai.

Dariya kam yashata har cikinsa sai daya amsa, sai a lokacin ya tuna ashefa baici abincin safe ba......

Khalid kam yana sauka ya nemi taxi ya karasa inda zaije.

*Ayusher Muhd馃弻馃徎鈥嶁檧* [10/27, 10:33 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁 *A GIDANA*馃崁

Haske Writers Association馃挕

Shafi na biyu

Wattpad/@AyusherMohd.

******

聽 Khalid yana sauka ya wuce inda Salmanu yamai kwatance, ganin anata aiki agun yasa ya gane ya iso, da sauri yasa hannu ya dauko wayarsa ya kirashi.

Jiki a sanyaye Salmanu ya daga yace "Khalid!"

"Na iso, kana ina?"

Salmanu yace "bari nazo." Ya kashe wayar. Bai jima ba sai ga shi nan ya fito, Khalid na ganinsa ya matsa gun da sauri yace "ya? Har an fara?"

Cikin rashin jin dadi Salmanu yace "Khalid kayi hakuri wai mutanen da sukeso sun isa, ma fada musu akwai sauran daya da zai karaso yanzu sunce wai a'a iya mutum biyar zasu dauka."

Murmushi yai tare da dan dafashi yace "bakomai, shiyasa duk kai wani iri?"

Kallansa yai yace "Allah duk abin ne yaban haushi, gashi ni kuma wlh kudin nakeso kasan ina tara lefe da wlh na barma kayi."

Khalid yai dariya yace "Just forget, kaidai yanzu ka shiga kayi aikinka, kafin kai laifi."

Salmanu ya dauko dari biyu yace "gashi dan Allah na asarar mota dana saka."

"Kai ka sani? Ko na sa kaina?"

Salmanu yace "ni na saka wlh."

Khalid ya zare hannunsa daga kafadarsa yace "Good luck ni nayi nan."

Yai gaba ya barshi rike da dari biyun, Salmanu ya bishi da kallo a ransa yana jin haushin wannan lamari na kasarmu, bazai manta yanda Khalid yai karatu a makaranta ba, duk wani abu da za'ai a faculty's dinsu, shine yake wakiltarsu, shine yi musu tutorials da sauransu amma dan bashida hanya gashi nan ko karamin teaching ya kasa samu.

Khalid kam yana tafe yana tunanin kalaman Adam, ba shakka ransa ya sosu da yanda ya mai magana, dan duk wanda ya kalleshi ya kalli yanayinsa yasan yanayine na dauriya da wahala, amma wai tambayarsa yakeyi wai wani company din yake aiki? Murmushin takaici yai tare da sa hannu a aljihunsa, dauramai dari uku.

Ajiyar zuciya yai dan wata yunwa da yakeji gashi kuma kudin motar komawa ma yamai kadan.

Mezai danyi yadan samu kudin da zaici abinci ya kara kudin mota?

********* "Duka duka anan muka kawo karshen shirin mu na Yammacin mu a Yau, sai mun hadu daku a shiri na gaba.

Ni Zainab Aliyu Tahir nake cewa mu huta lafiya."

Ana dauke camera daga kanta ta shiga bubuga kafadarta saboda dan gajiyar datai, kallanta staffs din gun sukai sukace "Hajiya akoda yaushe ke ta dabance, in kina shiri gaba daya komai tsayawa yakeyi, mu kanmu rasa wayar da zamu dauka da texts din da zamu karanta mukeyo."

Kallan mai maganar tai tace "kuma sannunku da kokari."

Ruwan dake gabanta ta dauka ta sha sannan ta mike tace "Ina Ramla?"

Bata nan, dazu kuma tana nan a tsaye.

"A ce mata ta sameni a office." Ta fada tare da wucewa.

Zama tai a office dinta tare da daukan wasu takardu tana dubawa.

Knocking din datajine yasa tace "shigo." Ramla ta shigo cikin yanayin tsoro dan ta tabbatar laifi tai, ko kofar bata maida ta rufe ba ta watso mata takardun dake hannunta. Gaban Ramla ya fadi ta kalleta a tsorace.

"Me kika dauki media?" Murya na rawa tace "media? Aunty Zee?"

Fuska ta daure sosai, tace "ya akai kika samu aiki a nan?"

Bakinta na rawa tace "munyi interview......"

Bashi nake tambayarki ba, kallanta tai a tsorace tace "munzo munyi audition...."

"Kin min shiru ko sai ranki ya baci? Karatun aikin jarida kikai ko me?" Da sauri tace "shinai."

"Then uban me kika rubutamin?"

Idanunta ne ya ciciko tace "binciken da kikace naje nai...."

Ki koma kije ki sake report din nan sannan don't expect me in sake kiranki na miki bayani, ma tabbatar kinsan halina kinji me nakeyi in har nama mutum magana."

Hawaye ne suka zubo mata tace "insha Allah." Haka ta tsugunna ta shiga kwashe takardunta, tana gamawa ta fita tana hawaye.

Zainab ta dansa hannu akanta dake dan sara mata, agoggo ta kalla, ta kusa tashi, nan ta dau waya ta kira Adam.

********

Shikam Adam yana rabuwa da Khalid ya wuce majalisarsu ta yan zaman kashe wando, suka sha hira da gulma, akai ta fasamai kai akan yanda ba cas ba as sai jin dadin rayuwa da yakeyi.

Dariya yasa sosai yace "nifa dama can ba mutum bane mai san wahala dan dai Allah bai bani dama bane, shiyasa yanzu da Allah yaban dama nake morar jin dadi na."

Nazifi ya kalleshi yace "wai da gaske kake ma ka nemi aikin kuwa?" Yace "tab ai ko form ban taba siya ba, itadai ta dauka samune banyi ba."

Nazifi yace "Shegen aikai Allah ya maka baiwar sanin yanda zaka so kanka."

Adamu yace "kasan Ita akwai san bin abu yanda ya kamata, danace tasa a nemomin aiki fa cewa wai corruption ne."

Nazifi yace "ai shiyasa nakejin haushin yar iskar Kubran nan, sai anyi magana tace batada kudi, ni wlh haushi take bani, da alama aure zan sake wlh, kuma Hajiya zan nema nima."

Wata muguwar dariya Adam ya saki yace "tab amma lalai kai dan mugun san banza ne, irinsu Zee dita an fada maka sunada yawa ne??" Nazifi yace "mudai yau mijin Hajiya dan Allah ka dubemu mu dan tauna mai yaji yaji."

Nan ya zaro dubu biyo aka siyo musu balango suka ci suka kora da lemo, sannan ya mike ya nufi gida.

Goggo na zaune tanata kallo tana dariyar ta ya shigo. Tana ganinshi ta mike tace " Ina ka tsaya ne?"

Kallanta yai sannan ya kalli Tv yace "wai Goggo dan Allah bakya gajiya ke da kallo ne? Kullum kina gaban kujera kina kallo."

Tace "wannan ba damuwarka bane, sannan in na zauna a dakin ma me zanyi? Ba gwara nai kallo na debe kewa ba, ni ba wannan ba, bani kudina."

"Wai nawane ankon? Ai baki fadi kudin ba."

Kallansa tai tace "ban san fa iya shege ce maka akai bansan me nake ba? Ni bani kudina bansan jan magana."

Dubu biyar ya zaro ya mika mata yace "gashinan, amma wlh nasan ankon nan baifi dubu 3 ba."

Amsa tai sannan tace "wai ni Adamu wannan kudinka ne?" "Na matata ne." Komawa tai ta zauna tace "daga baya kenan, kudi ba naka ba sai bin ba'asi, wannan da kaine ma kake aikin kila ba ci zanyi ba."

Wucewa ciki yai ya kwanta, kan kace me bacci yayi gaba dashi.

Baccinsa yasha sosai, dan wayar Zainab ce ta tasheshi.

Yana ganin sunanta ya kalli agoggo sannan ya mike zaune.

"Honey kana ina?"

Cikin maganar bacci yace "ina gida na sha bacci ne." Tace "nakusa聽 tashi inka samu driver din ka turoshi yazo ya dauken."

Da sauri yace "yanzu zanzo, bansamu ba tukunna."

Kashe wayar tai sannan ta duba laptop din dake gabanta, tana gamawa ta fara hada kayanta.

Adam kam suna gama magana ya sauko daga kan gado, da sauri ya dau key zai fita yaji fitsari, nan ya koma toilet yai sannan ya fito ko Goggo baima magana ba wacce ke zaune tana kallo tana cin abinci.

Da sauri ya shiga mota ya ja ya fita, dole na nemo driver bazan iya yawon nan ba, tuno da Khalid dayai ne yasashi yin dogon tsaki, ya akai ban amshi number shi ba? Ai da masifa da sai na sashi yin aikin nan.

Yana isa ya kirata a waya. Nan tai sallama dasu ta fito.

Tana shiga ya kalleta cikin kulawa yace "Ayya Honey da alama kin gaji."

Murmushi tai tace "kawai dai fadan da ake sanine yake sani gajiya."

Hannunta ya riko ya sa akan kuncinsa yace "nasan duk wanda yaga shirin ki na yau zai ce waccece wannan? Ni kuma da ina gun zanyi saurin cewa My Wife, da magana ne."

Yanzu kam dariya tadanyi sannan ta zare hannunta tace "Honey."

Yace "kinga gashi harna saki kin ware."

Murmushi tai sannan tace "as always."

Mota ya tada dannan ya juya suka hau kan titi, kallanta yai yace "Honey zaki iya tuna Kwaro? Cinye du?"

Kallansa tai tace "wanda kake yawan labarinsa? Wanda ya maidaku hoto?"

Da sauri yace "shi shi, ai na fada miki komai malamai sai dai suce shi ko?" Tace "eh, ya akai?"

Wata dariya ya sheka yace "kinsan yau na ganshi?"

Kallan mamaki tamai tace how?

Cikin zumudi yace "a hanya, kin ganshi?" Ha ha ha unbelievable wai bai samu aiki ba, sannan kina kallanshi kamar talakan kauyen."

Kallansa tai yanda yaketa dariya tace "lalai Honey to menene na dariya?"

Kallanta yai yace "can you imagine?"

Tace "a yanayin kasarmu sosai, saboda mutane nawa ne suka dace suka cancanta a basu aiki amma suna nan ba labari?"

Dariya yake sosai yana cewa "ban taba kawowa ba wlh."

Kallan mamaki take mai, dan haryanzu bataga abin dariya ba.

Da kyar ya gama dariyar sannan yace "ai naji haushi wlh ban amshi number shi ba."

Kallansa tai batace komai ba. Yace "namai rayin aikin driver dinki ai, wayyo Allah ubangiji yasa ya amsa."

"Driver?" Ta fada tana kallansa, yace "eh."

Wani murmushi tai sannan tace "baka tunanin u hurt his pride?"

Yace "taimakon sa zanyi ai, dayaje yana neman abinyi ga aiki a gida?"

Kanta tasa jikin window dan ta kasa fahimtar me yake nufi.

Adam ya jawo hannunta yace "me? Bakyaso?"

Tace "no, kawai dai ina ganin kamar bai kamata ba, abokinka ne fa?"

Ganin yanda ta dau lamarin yasa yai saurin canza maganarsa yace "na san bai kamata ba, amma bansan yands zanyi na taimakeshi ba, kins gani nima fama nake da neman aikin nan."

Murmushi tai tace "na fahimta yanzu, amma dai still da baka mai zancen ba, ba lalai ya fahimci dalilinka ba."

Hakane kuma, gashi banda numbersa.

Tace "kawai dai Allah yasa yai calling dinka back sai ka nusar dashi."

Kai ya jinjina sannan yace "Thanks."

Dame?

"Komai ma." Murmushi sukama juna.

***************

Khalid kam mariri ya shiga yaje gun masu ruwa ya amsa kura akan zai biyasu duk kaiwa daya, haka yai tayi ya hada dubu daya ya nemi abinci yaci yahau mota ya koma gida.

Yana shiga danbatta ya tsaya yasai lemon fata ya wuce gida.

Suna zaune a tsakar gida Asiya na alawar madara da take kaiwa makaranta ya shigo.

Yana tafe su Asif na binsa a baya shi da Amir, wanda ya kamosu daga wajen wasan kwallo.

Bayan sun gaisa da Umma ne ta kalleshi tace "an dace?"

Yace "naje wlh wai sun cika, amma insha Allah........."

聽 Umma ce tai ajiyar zuciya ta kalli Abba dake zaune yayi shiru, tace "Khalid bayanda za'ai mu samu ko dubu uku ne?"

Kallanta yai yace "wani abu ya faru ne? Tace "dazu daka fita Amir yana wasa ya bige Abbanka aka fama ciwon sai da muka kira mota muka kaishi chemist aka gyara, gashi bashin gun Karima naci, ka santa."

聽 Kallan Abba yai ya matsa da sauri yace "Abba ya jikin?"

Abba ya share kwallarsa yace "Khalid kayi hakuri inata karama nauyi."

Da sauri khalid yace "ko kadan Abba."

Umma dake share hawayenta itama tace "Khalid gashi yau ba komai a gidan, kokon dana saida shi na mana abincin rana dashi."

Kuka ne yadan kwace mata, hankalinsa ya tashi, gata tana kuka ga Abba ma na hawaye, Asiya ma daurewa kawai tai amma sai da kwalla suka zubo mata.

Bai san sanda yace "Umma na samu aiki."

Da sauri ta kalleshi Abba ma ya kalleshi yace "Da gaske? A ina?"

Idanu ya runtse, me yace? Me ya kaishi?

Umma ta kalleshi tace "nasan wasa kakeyi, wannan lamari dame yai kama? Sai bani jari kake yana karyewa, duk wahalar da kakesha haryanzu........"

Da sauri ya zaro takardar dake aljihunsa yace "kingani number wanda ya daukeni ne, matarsa ce take neman mai tuka mata mota shine yakeso in amshi aikin."

Matarsa? Abba ya fada yana kallansa, sannan yacigaba "kana ganin abinda ya sameni a aikin tukin mota banaso kaima ka gadoni."

Asiya ce da sauri tace "Alhamdulila yaya indai har driver suke nema聽 da alama sunada kudi kenan? Nawa zasu dinga biyanka? A ina zaka zauna tunda dai nasan a kano ne."

Yace "to Hajiyar tambaya."

Umma ce ta kalli Abba tace "shekararka nawa kana aikin? Ai tsautsayine da kaddara."

Sannan ta cigaba "kai Alhamdulila."

Khalid ya kallesu dan baisan me zaice ba......

Ni kaina jinai bansan me zance ba....lol

*Ayusher ce* [10/27, 10:33 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁*A GIDANA*馃崁

Haske Writers Association馃挕

Shafi na uku

Wattpad/@AyusherMohd.

Khalid na shiga dakinsa ya zauna abakin gadansa ya dafe kansa yana kallan number dake hannunsa, ajihar zuciya kawai yai dan baimasan tuno abinda ya faru. Kirim ya maka kanshi akan gadon dan takici.

********

Cikin bacci taji hannunsa a cikin rigarta, juyowa tai ta kalleshi.

Kara matsowa yai yace "kin gaji ko?"

Murmushi tamai duk da dai ba gani yake ba saboda duhun dakin, sannan ta kai bakinta cikin nata........

Bayan sunyi wanka ne ta kalli agoggo, karfe 2 na dare kasancewar gobe asabar yasa bata damu ba, zuwa yai ya kwanta kusa da ita, sun danyi shiru kafin ta nisa ta kalleshi cikin kulawa tace "Ko muje asibiti?"

Shima juyowa yao saitin da take kallansa yace "kin matso ne?"

Kai tadan girgiza kadan tace " i feel like kamar yin planing din danai farkon auran mu ne yake neman ja min matsala, sannan ina tunanin ko ba kaiba nasan Goggo nasan ganin jikanta."

Jawota yai jikinsa yace "karki wani damu, ni ba abinda yake damuna, let's try slowly."

Murmushi tamai sannan ta kura mai ido, a koda yaushe wadan nan kalan nasa ne yake sa take ganin duk abinda tamai bata fadi ba, tana sanshi sannan tana san a sota, shiyasa ko yan uwanta sunyi maganar rashin aikinshi abin bai damunta.

Iska ya hura mata yace "kallan fa?" Murmushi ta dake mai sannan ta sumbaci goshinsa a hankali cikin rada tace am touched.

Kallan juna sukai a hankali sukai murmushi, bacci ne ya daukesu suna yar hira sama sama.

Yau da yake asabar ce basu tashi ba bayan sunyi sallar asuba sai karfe goma sha daya.

Sha dayan ma ahi ya fara tashi, yana shiga toilet ta bude idanunta, agoggon wayarta ta kalla sannan taga sako ya shigo mata.

Tana karantawa ya fito, kallansa tai tace "Honey wai anjima su Nusaiba da Nabila zasuzo, dama tun shekaranjiya sukace zasu tambayi Dady ko zai barsu."

Kallanta yai yace "yau din nan?"

Tace "Hmm kana tsoro ne?"

Dariya yasa yace "bari na dauko Panadol na ajiye kusa da ni."

Itama dariya tai tace " Mutanen Goggo."

Mikewa tai ta shiga toilet, zama yai a bakin gado yana kallan wayarsa, Khalid please ka kirani ko text kamin.....

Tana fitowa suka fito falo tare, Goggo na zaune tana shan shayi tana kallo suka fito, gaisheta tai sannan tace "Goggo anjima su Nusaiba zasuzo."

Da sauri ta kalleta tace "har an kuma yin wani hutun?" Adam ya kalleta yace "wace tambaya ce wannan Goggo?"

Kallan Zainab tai wacce ke kallanta cikin rashin fahimta sai tai saurin wayancewa tace "ah wai nagane kamar basu dade da zuwa waccan hutun ba, ko da yake kwanakin yanzu ai ba wuya."

Zainab ta fahimceta sai dai dauke kai tai daga manufarta ta barshi a yanda take nufi da cewa "lokaci yanzu ai ba wuya."

Goggo tai dariya tace "yan dambe mutane na."

Itadai Zainab batace komai ba ta wuce kitchen.

Adam ne ya kalli Goggo yace "Ko ba kyasan suzo ai bakya nuna haka ba."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull