A gidana complete novel - Chapter 2
A gidana complete novel Chapter 2: A gidana complete novel Chapter 2. Wani kallo tamai tace "kaima so kake suzo? Yaran da suna zuwa ba nutsuwa a gidan nan,…
4,488 words
Wani kallo tamai tace "kaima so kake suzo? Yaran da suna zuwa ba nutsuwa a gidan nan, fada sai suyi kusan sai hudu a rana daya."
Mikewa yai yace "kedai Goggo kallanki ne bakyasan su tare miki tv da kallab india da korea, na fa sani."
Bata kulashi ba ta cigaba da cin breadin ta.
Kitchen ya nufa ya tadda ita tana fere dankali. Yasan halinta tunda yaga bata kulashi ba harya shigo kitchen din to batasan a mata magana a wannan lokacin.
***********
Yau tun safe duk wanda yazo siyan koko sai Umma ta fadamai ai ya samu dan karamin aiki a cikin garin kano, badai wani aiki bane sosai amma babbar mace Hajiya zai dinga tukawa.
聽 Yana daga cikin daki yaji ana mai Allah ya sanya alkairi, a lokacin yana zaune yana duba result din wani test da sukaje sukai, jin yanda matar ke mai Allah ya sanya alkairi ne yasashi mikewa, tana fita ya shigo cikin gidan, Umma na zaune tana dama koko, sai daya gaisheta sannan yace "Umma badai harkin fara fadawa mutane na samu aikin tuki ba?"
Cikin farinciki tace "yanzu Salamatu tazo takemin zancen Salmanu na hada lefe shine nake mata zancen? Da wani abu ne?"
Dan huci yai kafin yace "ai da kin bari na soma aikin sai ki fada musu, in abu yazo da tsautsayi fa?"
Cikin tashin hankali tace "akwai matsala ne?"
Ganin yanda tai yasa yai saurin cewa "a'a kawai dai da kin bari sai dana fara."
Umma tace "ai salamatu da Karima kwai na fadawa." A ransa yace ai su kadai bakinsu radio ne, amma a fili baice komai ba.
Gun Abba ya shiga wanda ke kwance, Abba yace "yanzu dama zan sa a kiraka, dan taimaka ka kaini bayan gida."
Nan Khalid ya dagashi suka nufi toilet, sai daya gama sannan ya kirashi suka fito.
Abba yai dariya yace "ai wasa wasa wannan dabarar ta bature ta taimaka, yanzu kaga da bandakinmu na da ne sai dai in san yanda zanyi, ga kafa daya babu gashi kuma tsugunno ake, kaga kuwa wannan dakasa aka sa mana na zama ai yafi."
Murmushi kawai yai baice komai ba, sai da Abba ya zauna sannan yace mai "Khalid!" "Naam Abba."
Ya kalleshi fuskarsa cikin kulawa yace "ka fahimci mahaifiyarka, tsabar zumudi ne yasa ta kasa yin shiru."
Khalid yace "na sani Abba."
Dan dariya Abba yai yace "yaushe zaka fara aikin?"
Yace "hmm."
Abba ya kalleshi yace "akwai matsala ne?"
Shiru yai yana kallan Abban, yana san sanar mai gaskiya sai dai yana tsoron yanda zasu kara shiga damuwa tun balle in sukaji matar abokinsa wanda sukai makaranta tare ne ya tabbatar sai sunji ba dadi, hakan yasa kawai yace "a'a anjima zanji sanda zan fara."
Abba ya saki fuska cikin jin dadi yace "Allah yayi albarka yasa a fara a sa'a, duk da ina tsoronka da tukin mota sai dai ina fatan ka fara dashi a hankali kuma ka cigaba da duba aikin yi, yanda kake da jarabawa mai kyau din nan banda dai kasarmu ta zama abinda ta zama ai aiki kam bai kamata ka rasa ba."
聽 Khalid yace "Amin Abba insha Allah lokacin da za'a samu aikin zai zo."
Abba yace "haka ne, Allah yasa a dace."
Amin yace sannan ya mike ya fara gyara mai zaman sa.
Umma ce ta kirashi ya fito ya dau abincinsa ya shiga daki.
Shiru yai a cikin dakin ya zubawa koko da kosan ido yana tunanin mafita, takardar dake rike a hannunsa ta number waye Adam yake ta bi da kallo.
Yanzu ya samu ya biya kudin makarantarsu Asiya, nan gaba kadan zai sake biyan wani tunda rabi yake badawa a farko sai ya cika rabin daga baya, ga bashi, ga hidimomin gida, ga jikin Abba, idanunsa ya runste saboda yana ganin zaben abinyi a wannan lokacin sam ba nashi bane.
Abincin yaci yana gamawa ya dau wayarsa ya kira Salmanu, ya kuna kanon ne? Salmanu yace eh wlh, ai naji haushi da baka samu aikin nan ba, gashi haryanzu ba wani labari."
Khalid yace "bakomai ai aiki lafiya."
Ya kashe wayar yi shiru yana kallan wayarsa, mikewa yai da sauri ya shiga cikin gida yai wanka, yana gamawa ya fita waje dan ganin abinyi, ya bari akan in dai har yamma bai samu wani abu ba to fa lalai zai kira Adam.
*******
Karfe biyar na yamma tanata girki, Goggo ta shigo kitchen din tace "dame za'a tayaki? Naga yau sai girke girke kikeyi."
Tace "barshi wlh Goggo ai na ma gama."
Goggo tace "to ki bar wanke wanken nayi."
Zainab tace "su Nusaiba in sun huta sayi."
Kamar da wasa tana rufe baki taji karar bude gate, da sauri ta dauraye hannunta dan dama duk ta juye abincin a flask, ta nufi falo cikin tsananin farin ciki.
Goggo ta kalleta tace "goben nan za'a jiku kina musu fada."
Tana bude kofar waje ta hangosu suna fito da akwatinsu daga mota.
N square abinda ta fada kenan suka waigo ai suna ganint suka bar akwatin suka nufota da gudu suka rungumeta.
Cikin farinciki tace "Welcome."
Dagowa sukai suna dariya Nabila tace "kai wasa wasa Allah Aunty na gaji, tafiya taki karewa."
Nusaiba tace "har wani tafiya taki karewa banda uban baccin da kika maka a hanya."
"Yaushe nai baccin? Dan na rufe ido shine......"
Da sauri tace "zaky fara ne?" Ta fada cikin hade rai, sun san halinta akwai fara'a da wasa da dariya amma fa in taso, sannan in ta birkice to fa ba kanta.
Da sauri suka guntse bakinsu sannan suka jawo akwatin da kayan da suka taho mata dashi suka nufi ciki.
聽 Goggo tana falo suka shigo, "oyoyo oyoyo ga mutanen nawa sun iso."
Nusaiba tace "Goggo."
Goggo ta kara ware fuska tace "lale lale maraban inji larabawa."
Nabila tasa dariya tace "Marhaba suke cewa Goggo, yau kuma garin larabawa muka nufa?"
Zainab tace "koma me suke cewa tunda kin gane na miye wannan dogon sharhin.
Gate aka sake bude wa wanda yasasu juyawa, Nabila tace "Ya Adam na yawo......."
Kallan da Zainab ta mata ne yasa tai gum.
Shiga da jakakkunan nasu sukai dakin da suke kwana, suna fitowa ya shigo shida Dauda driver wanda ya kawo su Nusaiba.
Yana shigowa yace "My headache kuna ina??"
Fitowa sukau daga daki, Nabila tace "bayan munyi fushi, kasan zamuzo ka fita."
Dariya yai yace "ai yanzun nan na fita nima ko Honey?"
Ya fada yana kallan Zainab, tace "ko yanzu ya fita ko dazu ya fita meye naku a ciki?"
Goggo ta kalleshi cikin takaici, ya bari kowa ya rainashi, kallan Goggo yai sannan ya dauke kai dan ya gane wani abin bai mata dadi ba.
Zama sukai bayan sunyi sallar da ta riskesu a hanya aka fara cin abinci.
*********
Khalid ne ya dawo gida bayan yawon daya sha a garin na dan batta, can ya samu jiran shago yadanyi aka biyashi, shiru yai a cikin daki kawai ya gama yanke shawara zai fara wannan aikin sai dai sai yaji abubuwa guda biyu, na farko shi bashida gun da zai zauna a kano sai abu na biyu baisan aikin da za'a kankantar dashi.
Yana cikin tunanin nan bai fargaba kawai yaji ance Hello!
Shiru yai daga can bangaren Adam dake zaune ana hira ya mike yai daki ya kara cewa "Hello!"
Khalid ya daure yace "is me Khalid Danbatta."
Cikin mamaki Adam ya kalli wayar sannan ya kara karata a kunne yace "who?"
"Khalid Usman Danbatta."
*Ayusher Muhd* [10/27, 10:33 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
Haske Writers Association馃挕
Shafi na hudu
Wattpad/@AyusherMohd.
Adam cikin mamaki yace "Khalid!" "Eh nine." Adam ya zauna a bakin gado yace "ya gida khalid? Inatajin ba dadi dama ban amshi numberka ba."
"Is okay, maganar aikin nan." Idanu Adam ya zaro kamar yai dan ihu amma sai yace "eh tana nan? Kana so ne?" Khalid ya matse hannunsa saboda jin ba dadi da yakeyi, yace "eh, sai dai zan fara duba inda zan zauna da albashi da sanin yanayin lokacin aikin da sauransu."
Adam da sauri yace "kar kaji komai, ai kawai in dai ka shirya kazo gobe saboda litinin tanada aiki, ba wani matsala."
Cikin mamaki Khalid yace "ba matsala kamar ya?"
"Eh in kazo goben ma tattauna, amma ba wani abun ka kirani gobe in xaka taho zan turo ma da address, abinda kawai yace kenan ya kashe wayar da sauri." Wata irin kara ya saki wanda su kansu dake falon sai da sukajishi.
Zainab ta miki da sauri ta nufi cikin dakin, yana ganinta ya maida fuskarsa, cikin mamaki ta kalleshi tace "Honey lafiya?"
Murmushi yai sannan yace "bakomai dama munyi waya da Kwaro ne shine yace zai fara aikin." "Kwaro?" Ta tambaya cikin mamaki.
Kin mantashi? "Ohh friend dinka?" Da sauri yace "eh." Kallan mamaki tamai ta matso kusa dashi tace "wai da gaske abokinka ne zai zama driver na?"
Hannu yasa ya jawota ta zauna kan cinyarsa yace "neman aiki yake sosai, da alama yana cikin wani hali, kinga ba dadi na cemai kar yai bayan ya kirani akan yana san aikin."
Idanunsa ta kalla sannan tace "amma gani nake bai dace na kamar."
Karki damu, a yanda kike din nan ma nasan ba dadewa zaiyi ba zaku rabu, dan banaji zaku jitu da halayensa."
Wani irin murmushi tai sannan tace "kasan haka kace yazo?"
Karkace kai yai yace "I feel bad for him."
Shiru tai kawai batace komai ba, ajiyar zuciya yai kamar wanda yake cikin wani halin wanda yasata kallanshi, yace "matsala daya, banaso ya dinga kalleminke, shiyasa nake neman manya magidanta."
Harararsa tai cikin wasa tace " banda wanda akemin a tv?" Ahhhh, ya dafa kai sannan ya kwanta akan gado yace "shikenan ni an gama duk kallemin matata."
Mikewa tai tace " zolayar ta motsa kenan?"
Mikewa yai shima yana dariya yace "gobe zaizo, sai dai bansan ko yanada gun zama ba."
Da sauri ta kalleshi tace "sai ya nema ai wannan ba damuwa ta bace."
Dariya yai yace "bari dai yazo goben muji."
******
A bangaren Khalid kuwa yana kashe waya yai shiru yana maimaita kalaman Adam, kafin ya mike ya nufi cikin gida dan sanar dasu Umma tafiyar fa gobe ce.
Umma na zaune akan tabarma kusa da Abba, suna hira.
Yana shigowa tsakar gidan Umma tace "Khalid dan halak, muna maganarka sai kaga."
Murmushi yai sannan ya karaso yana cewa "Su Amir ba'a dawo ba?"
Tace "ba dadewa zaka jisu, dan lokacin tashin nasu yayi ai.
Zama yai daga gefe yace "Abba ya jikin?" Abba cikin sakin fuska yace "kasani yau inajin wani karfi, duk da ba sana'ar da nake fatan kayi bane ka samu a kalla dai nasan zaka samu abinda zaka taimaka mana ka taimaki kanka har a hankali kazo kai aure, wannan tunanin yasa naji yau jikin nawa garau."
Kallansa kawai yai sannan ya dan murmusa duk da abin bai kai kasan ransa ba, Umma ce tai saurin cefewa da cewa "Nikam kasan yar gidan kyauta?"
Ya fahimci me take nufi sarai amma sai cewa "Zahriyya datai aure?"
"A'a Habiba wacce ta gama makarantar secondary bana."
Yace "ohh wannan yarinyar? Badai harta gama makaranta ba?"
Umma tace "ta gama wlh shiyasa dama nace......."
Eheeem ya isa haka nan, abinda Abba yace kenan wanda ya sata yin shiru.
Abba ya kalli Khalid yace "ko zaka zauna a gidan kawunka Idris? In har gurin zama zai wahalar dakai a kanon?"
Kallan Abba yai sai dai shikam baisan zaman gidan nan sam, shiyasa lokacin da yake makarantar Buk duk abin duniya ya dameshi shi yasa ya koma cikin hostel yake dan zaman wani shagon ana biyansa ga kuma wanda Abban yake turamai ya samu yake biyan na hostel dan sam baya san gidan nan basu da tarbiyya ko kadan, sai dai a lokacin cema Abba yai kawai yafisan can saboda karatun dare.
Abba ya kalleshi yace "ya akai? Bakasan can din ne?"
Khalid yace "a'a bari goben in naje muka gama zan shiga can din."
Umma tace "ah gobe ne? Da wuri haka?"
Yace "yanzu mukai waya dashi, sai dai ban sani ba ko in naje goben zan dawo ko kuma sai juma'a bandai sani ba sai naje can din."
Abba yace "masha Allah ba laifi ai."
Khalid yai shiru kafin yace "Abba!" Abba ya kalleshi cikin kulawa, yace "na fadawa Salmanu zaizo da yamma ya dauki laptop dina, zai saida ita in yaso sai ya baku kudin a samu a rage wasu abubuwan kafin Allah ya kawo yanda za......."
Katseshi Abba yaida cewa "a'a kul, na fada maka ba tun yau ba in har ba kudi ka samu zaka sai wata ba karna kuskura naga ka saidata, bayan duk abin karatunka a ciki kakeyi, sannan kace zaka sai data?"
Khalid ya kalli Umma wanda itama bata yadda da shawarar ba, zaiyi magana su Amir suka shigo da gudu.
"Kun daina gudun nan ko kuwa?"
Da sauri suka daina dan sun san halinshi.
Asiya na biye dasu, duk saida suka gaishesu da gida, Asiya tace "Yaya! Ya salmanu na sallama dakai."
Khalid ya mike yai waje.
聽 A yanda yaga Salmanu ne yasa hankalinsa ya tashi, Salmanu na ganinsa ya matso kusa dashi, idanunsa sunyi jaa da alama ma har hawaye sun zubar, Khalid cikin mamaki dan bai taba ganinsa haka ba yace "Salmanu menene? Meya faru?"
Da alama baima san ta inda zai fara magana bane dan duk a rikice yake.
Khalid ne yasa hannu biyu ya riko kafadarsa ya girgizashi yace "Salmanu? Menene? Rasuwa akai?"
Salmanu ya zubamai ido kamar wanda baya hayyacinsa yace "Wai ansa auran Nazifa dazu."
Gaba daya ya kasa fahimta yace "bangane ansa ranarta ba, ba dakai aka saba kenan ko me?"
Salmanu wasu zafaffan hawaye ne auka zubo mai yace "Khalid kwana biyu dama duk bansan meke damun Nazifa ba da mamanta, har yayenta ma, dan duk sanda naje zasucemin ko bata nan, ko tai bacci, ni duk ban kawo komai a raina ba saboda duk garin nan kowa shaida ne akan yanda muke san juna, yarinyar nan tun tana primary....."
Khalid yace "na sani nasan wannan, ni bangane an sa rana ba."
Salmanu ya goge kwallarsa yace "kanar yanda kaji din nan haka yanzu ina dawowa daga kano aka fadamin, ina zuwa gidansu yayanta yake fadamin, wai Alhaji Badamasi."
Khalid ya fahimci kwanan zancen, wato sunga kudi, sai dai ba'ama Salmanu hallaci ba, kusan shekara kenan yana ta faman hada lefe dan so yake ya mata lefe na fitar kunya amma ynzu a mai haka,m? Bayan tun tana primary hartakai secondary komai shi yake mata, hatta provision in zata koma skul shi yake mata.
Ran Khalid yakai matuka gun baci wanda takaici ya kamashi yace "yanzu wani irin cin mutunci ne wannan?"
Salmanu ya kalleshi cikin karayar zuciya yace "taya zan iya rayuwa ba Nazifa?"
Haka ya juya dan yace yana san kadaicewa y tafi, Khalid yabi bayansa da kallo, shi yasa fa shi sam harkar soyayyarnan bata gabansa, karshe ma shi bai yarda da ita ba.
Haka ya shiga daki yana hada kaya cikin takaici.
*********** Wajen karfe 11:30
聽 "Wallahi bazanyi wanke wanke ba sai dai ke kiyi ni shara zanyi."
"To ni bazanyi wanke wanken ba nima shara nakeso."
Fadansu ne ya sa Zainab ta farka dan cikin bacci taji ana fada.
Mikewa tai ta kalli Adam wanda da alama baijisu ba,聽 fitowa tai suna tsaye a falo suna fada Goggo na zaune tana kallo ko kulasu batai ba, hankalin ta ma sam baya kansu.
Zainab na rufe kofa suka juyo sauri suka kalleta, kallansu tai tace "mekenan?"
Nusaiba tace "Aunty......." Ku wuce duk kuyi komai tare, wai sai yaushe zaku girma da fada ne?"
Nabila zatai magana, Zainab ta kalleta. Da sauri sukai shiru, kitchen suka nufa kowa fuska a hade.
Zainab ta kalli Goggo tace "Goggo kina kallansu amma bazaki hanasu ba?"
Goggo ta kalleta tace "ni? Ina na isa? Ai ni ba a bakin komai nake ba a gidan nan, yara sunzo gidanki ai sun fini iko da gidan."
Zainab kallanta kawai take sai dai kalaman sun bata bata rai sosai, tace "Goggo me yasa wani sa'in in kina magana sai ma dinga gani kamar magana kike fadamin?"
Goggo ta mike tace "magana? A ina? Bayani kawai na miki, sai dai in ke kika fassara, ni ina na isa na fada miki magana?"
Zainab zatai magana, kawai ta fasa dan ta kula ranta ne zai baci, in kuma ranta yabaci to lallai da matsala, juyawa tai kawai ta shiga ciki.
Goggo ta bita da kallo tace "wannan da badan mune a karkashinki ba wlh da kece a kasana dasai na koya miki yanda ake lallaba uwar miji."
Tai tsaki sannan ta zauna ta cigaba da kallanta tana dariya.
Zainab kam daki ta wuce, wayarta ta dauka missed calls ta gani kala kala daga gun aikinta, da sauri ta kirasu, nan aka sanar da ita air advertising din da suka dade suna nema ne ya taso, sannan an kammala musu website din da suka sa a canza musu,tazo suyi meeting.
Da sauri ta shiga toilet tai wanka ta fito, ta hau shiryawa
********
Khalid kam karfe goma yai sallama da gida bayan ya samu a daren jiya ya saida wayarsa ya nemi karama mara internet, yaba su Umma kudin saboda lamari sannan ya bada dubu biyu a kara ba masu bashi, da wannan yai sallama dasu akan zaije ya dawo a yau in ya samu hali.
Har ya shiga mota yana tunanin abinda akawa Salmanu wanda ya bata mai rai matuka.
Address din da Adamu ya turomai jiya da yamma ya dinga dubawa聽 ganin ya kusa isa gidan yasa ya kirashi a waya.
*****
Adam na bacci yaji motsinta a toilet, ohh cikin layin bacci ya duba wayarsa, mikewa yai ganin yasha bacci, yana zama wayar Khalid na shigowa.
Da sauri ya dauka yace "kwaro!"
Khalid yace "Adam gani nan na kusa isowa, in nace gidan Journalist kawai shikenan?"
Adam yace "eh sai ka iso."
Da sauri ya kashe ya mike daga kan gado, fitowatai daga toilet da sauri ta kalleshi a tsaye tace "ka tashi?"
Yace "eh, tace "taimaka plz ina shiryawa ka dan dubamin email din nan." Ta dau wayarta tana mikamai, amsa yai yace "gun aiki zaki?"
Tace "eh."
Amsar wayar yai ana karanta mata, da sauri take sa kayan, tana gamawa ta gyara fuskarta, daidai nan ya gama ta amsa tace "thanks Honey."
Kiss tamai sannan tace "i have to drive shiyasa nace ka karantamin tun anan, sai nai tunani a hanya."
Yana kokarin sanar da ita Khalid din yanzu zaizo ta dau jaka ta fita da sauri, biyota yai yana cewa "Honey dama......."
Kallansa tai tace "kar ka damu zan samu abinci naci acan, tnz."
Da sauri ta wuce kitchen, ta kalli Nusaiba da Nabila tace "Allah yasa naji labarin kunyi fada."
Baki suka rufe, tare da cewa "adawo lfy."
Da sauri ta fito ta kalli Goggo tace "Goggo na tafi." Tace "yau fa lahadi."
Tana tafe tana cewa "abu ne ya taso mu director's ne kawai zamuyi meeting."
"Darastas??? Me kenan?" Adam ya girgiza kai yai waje.
Tana fitowa waje shi kuma yana turo kofar gate din.
Kallansa tai sannan shima ya kalleta.
Adam da ya fito ne ya kalleshi shima.
Fuska dauke da mamaki tace "Who?"
Khalid zaiyi magana Adam ya dawo gabanta yace "Khalid ne." Khalid? Cikin mamaki ta kalli Adam, da sauri cikin magana mara sauti yace cinye duu... kwaro."
Key din hannunta ta cilla mai ya cafe tace "drive."
Khalid ya kalleta cikin rashin fahimta, wucewa tai cikin mota ta bude kawai ta shiga.
*Ayusher Muhd* [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁 *A GIDANA* 馃崁
*Haske Writers Association*馃挕
*Shafi na biyar*
Wattpad/@AyusherMohd.
Khalid ya kalli Adam wanda ya gunste dariyarsa,daga cikin mota tai knocking din glass din motar, tana rike da tablet dinta tana duduba abubuwan da sukai discussing waccen meeting din, Adam ya kalli Khalid yace "sai kun dawo ma tattauna.
Ya shige ciki da sauri, Khalid ya nufi jikin motar sannan ya bude mazaunin gaba ya shiga tare da tada motar.
Bai mata magana ba itama haka batabi ta kanshi ba, mai gadi ne ya bude gate suka fita, suna fita daga gidan yaja gefen titi yai parking.
Sunyi minti biyar a haka saboda ita dube dubenta kawai takeyi, ganin shiru kamar ba'a tafiya yasa ta dago ta kalli waje, cikin mamaki ta kalleshi tace "ya naga ba'a tafiya?"
Bai juyo ba yace "bansan ina zamu ba." "Ai sai ka tambaya, saboda sauri nakeyi." Shiru yai baice komai ba wanda hakan yasata dan jin haushi tace " muje Gamji Tv station."
"Bansan inda yake ba."
Da sauri ta kalli agoggo taga tana bukatar hanzari. kallansa tai sannan ta bude motar da sauri ta dawo inda yake a zaune.
Kallanta yai itama ta kalleshi tace "am sorry but sauri nake kwatance bazai yiwu ba, can you please go that side?" Ta fada tana nuna mai dayan gun.
Fitowa yai ya zagaya sannan ta zauna a gun, da gudu taja motar, tana kallan agoggo.
Juyawa yai ya maida kanshi waje yana kallan hanya, sai dai kasan ransa gaba daya tunani yakeyi, wani irin aiki ne wannan? Ba'ai bayani? Salman ne ya fado masa, dan tsaki yai wanda shikanshi baisan yayi ba.
Karaf a kunnenta, kallansa tai cikin mamaki gani tai hankalinsa ma bai kanta, tsakin na menene? Ta fada a cikin ranta, wanda abin ya dan mata zafi, dan bata fahimci me tai ba balle a mata tsaki haka.
Gaban Gamji tv tai parking, fitowa tai kawai ta bude baya ta dauko kayanta dake baya, kallansa tai tace " bansan ko zan dade ba, in nai 1hr ban fito ba ka koma gida in na gama zan kora Adam sai yama magana."
Ta juya kawai ta shige cikin building, mamaki ne ya kamashi ya kwantar da kansa akan kujera, idsnunsa ya rufe a hankali.
Wayarsa yaji tana kara ya zarota a cikin aljihunsa, ganin Abba ne yasa ya daga da sauri.
Bayan sun sake gaisawa Abba yace "munji baka kira ba ko baka isa bane?"
Yace "na isa dazu." "Kaje gidan?" Eh kawai yace tare da saurin cewa "ya jikin?" Abba ya fahimci baisan maganar da alama ko ba shi kadai bane hakan yasa yace "da sauki, anjima mayi waya." Ya kashe wayar, Khalid yai shiru yana kallan wayar dan to baisan me zai cema Abba ba in ya tambayeshi ko ya ake ciki? Bayan shi kansa baisan ya ake cikin ba.
Yana nan a zaune yana yan tunaninsa jefi jefi yana kallan agoggon wayarsa.
*******
Zainab tana shiga ta wuce office din meeting dinsu, suna zaune suna tattaunawa ta shiga.
Tana shiga ta samu guri ta zauna, dan daga director din sai ita a matsayi, tana zama ta amshi takardun proposal din da akai accepting tana dudubawa, nan ta shiga bayani tare da kawo yanda za'a cin ma manufar, gaba daya kowa yayi shiru yana sauraran jawabinta, har ta kammala sannan tace "ya suke gani?"
Nan kowa yai naam da abinda ta kawo dan dama indai agun harkar aikinta ne ko director din da ita ya dogara saboda tsabar sanin aikinta datai da kuma darajashi datai, nan suka gama taron akan abinda tace shi za'ai, ta mike zata fita ne director din ya mata magana.
Dawowa tai ta zauna tare da kallansa. "Zainab naji Ramla tayi laifi ayi hakuri a sassauta mata."
Kallansa tai idanunta tsam tace "ni director kai ka kawota ne?"
Da sauri yace "ni kuma? Interview taci aka bata aiki."
Murmushi tai kafin tace "banajin ranar danai interview naganta a ciki, kafi kowa sanin inada rike mutum duk yanda naima interview zan ganeka balle wanda yaci."
Director yai dariya cikin zolaya yace " yo inbanda abinki dani fa akai interview din nan akai audition duk nasan wadanda sukaci sai dai kin manta ta ne."
Murmushi ta sakeyi dan ta fahimci neman karewa yake da alama shi ya kawo ta ko daga sama dashi ne. Tace "Ah Alhamdulilah tunda dai ba yarinyar ka bace."
Ransa ya sosu da maganar me take nufi da yarinya? Sai dai ba yanda ya iya da Zainab saboda itace ta kawo cigaban da suke dashi yanzu, itace ta jajirce ta maida gidan tv dinsu ya zama abinda ya zama, inba ita yasan komai ya wargaje, amma da badan haka ba da....... Kallansa tai tace "maganar Ramla ka cireta daga mai dauko rahoto dan inba haka ba zan koreta da kaina, ka maida ita wani bangaren." Bata jira amsarsa ba tace "zan wuce inba wani abin."
"To shikenan zan duba inda ta dace." Abinda ya iya fada kenan, ta mike ta fito daga office din, tana rufe kofa tai dan ajiyar zuciya na takaici, haka kawai ga mutanen da sukaci ta bada list dinsu a kan su sukaci amma tazo ta tadda a cikin mutum goma da kana dauka mutum hudu ne kadai aka ba aikin ragowar shidan ba ci sukai ba aka basu, gwada su biyar din ma sunyi interviewe faduwa sukai amma ita wannan Ramlan ba wanda ta ganta sai ranar first day din sabon ma'aikatan."
Agoggon hannunta ta kalla, hawanta kusan biyu kenan ta san ya tafi, hakan yasa ta shiga office dinta tare da kiran number Adam.
Shikam Adam tana fita ya shiga yai wanka ya tafi majalisa, suna zaune suna hira wayarta ta shigo.
Mikewa yai ya matsa gefe, yana ji suna tsokanansa yaran Hajiya zata bada aike ne?
"Honey kin taho ne?"
Tace "a'a kayima Abokinka magana ya dawo ya daukeni."
Cikin rashin fahimta yace "ya dawo ne?"
"Kana ina?" Tambayar data jefeshi da ita kenan, sam batasan majalisa dan tasan gulma kawai akeyi, cewa yai "naje siyoma Goggo maganin zafi ne."
Ayya, to bari na kira Nabila.
Kashe wayar tai ta kira Nabila, mamaki ne ya kamata da Nabila tace mata ba'a bataji alamar shigowar mota ba, harta kara dubawa tace ba motarta a gidan. Wayarta ta daga ta kara kiran Adam tace "baya gida fa."
Adam yace "inata kiran wayarsa kuma a kashe."
Fitowa harabar gun tai inda suke ajiye motoci amma bata ganshi ba, cikin bacin rai tacema Adam badai ya gudu da motar ba?
Shiru Adam yai yana nazari, bafa haka khalid yake ba ya tabbatar sai dai san rai irin na dan Adam sai cewa yai "ah haba?"
Zainab cikin dan zafin rai tace "badai bakasan halinshi ba?"
Shiru Adam yai duk da yasan ba halinshi bane amma sai cewa yai "na sani amma kinsan mutanen yanzu in aka rabu sai su can........"
Kashe wayarta tai saboda yanda taji ranta ya baci matuka, sam batasan in ranta ya baci ta cigaba da magana dan zata iya fadan abinda bai dace ba wanda daga baya zai iya sata dana sani.
Rai a bace ta fito wajen station din, ranta yakai matuka gun baci, tabbas sai tasa an nemo mutumin nan duk inda ya shiga kuwa.
聽 Tana fita taga motarta a gefen station din, tsaya tai cikin mamaki sannan ta karasa gun tana kallan motar.
Yana zaune a mazaunin driver yana dadana wayarsa.