A gidana complete novel - Chapter 3
A gidana complete novel Chapter 3: A gidana complete novel Chapter 3. Kai ta juya gefe tare da jin ba dadi na zargin datai ba tare da ta bincika ba.
4,492 words
Kai ta juya gefe tare da jin ba dadi na zargin datai ba tare da ta bincika ba.
Juyawa tai ta zagaya inda take zama sannan tai knocking din glass din, madannin bude motar ya danna ta bude ta shiga, baice komai ba tana zama ya tada mota suka hau kan hanya.
Shiru tai batace komai ba sai dadana tab dinta takeyi, shikam ko juyowa baiyi ba tukinsa kawai yakeyi.
**********
Adam kam tana kashe waya yai shiru cikin mamaki yace meke faruwa? Ba yanda za'ai khalid ya gudu, to ina ya shiga?
Da sauri ya musu sallama sannan ya ja motarsa ya nufi station dinsu.
Yana isa ya shiga ciki, yana shiga ya hadu da wani wanda yana ganinshi ya ganeshi matsowa yai ya gaisheshi, Adam yace "Zainab fa?"
"Ta tafi dazu."
Kai ya jinjina sannan ya juya tare da kiranta a waya.
Tana zaune cikin mota ya kirata.
"Honey Kina ina? Nazo bakyanan."
A hankali tace "ina hanya, kaje ina?"
Yace "nazo daukanki mana."
Da sauri tace " na sameshi a waje ai mun taho."
Sai data fada ta kalleshi kadan, karya gane zargin da sukamai.
Shikam baimasan metake yi ba, jitai yace "left or right?"
Kallan hanya tai sannan tace left, tace "Honey sry ka taho gida."
Kashe wayar yai yana cewa "nimadai kwai soko ko me nake anan?"
聽 Yana shiga mota ya tuna karyar dayai da sauri ya kira Goggo, itakam tana zaune tana kallo batamasan yana kira ba.
Haushi ya kamashi ya cilla wayar kujerar dake gefensa matsalar Goggo kenan, tana can tana tainannan kallanta batamasan yana kira ba.
******
Khalid left or right? Abinda kawai yake ce mata kenan in yaga ya kasa gane inda suka biyo dazu, suna shiga cikin harabar gidan ta fito tana kokarin shiga ciki.
Mamaki ya kamashi yace "Excuse me."
Tsayawa tai tare da juyowa sannan ta nuna kanta alamar ni?
Yeah.
Haka yace mata wanda yasa ta kara kallansa batace komai ba.
Kallanta yai yace "lokaci na wucewa inada abubuwan da zanyi sorting a yau din nan, and it seems like bakida niyyar yimin bayanin yanda aiki na yake da abubuwan da ya kamata nayi da sauransu.
聽 "Am sorry amma you have to told me saboda insan abinda ya kamata nai kafin dare yai, ba'a gari nake ba, inasan komawa."
Gaba daya jitai ma ta rasa bakin magana, yau take ganin ikon Allah, yana mata magana kamar itace take aiki a karkashinsa?
Sannan Excuse me?
Meya dauketa? Ko dan tana matar abokinsa yana tunanin wulakantata? Harda tana tausayinsa tana ganin Adam yaci zarafinsa ashe shima dan rainin wayau ne?
"Excuse me, naji kinyi shiru."
Excuse me? Again?????
聽 Ranta ya baci, kallansa tai cikin bacin rai sai dai yanda yake kallanta da jiran tamai magana yasata juya kanta abokin Adam ne, cool down.....
Bude kofar da akai ne yasa ta kalli kofar, Nusaiba ce ta fito da gudu ta rungumeta, kallan Khalid wanda ke tsaye ta tsaya tana yi, Zainab ta zare ta sannan ta kalleshi tace " bari Adam ya karaso sai kuyi magana."
Haka kawai tace ta shige ciki.
*Ayusher Muhd* [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁*A GIDANA*馃崁
*Haske Writers Association*馃挕
Shafi na shida
Wattpad/@AyusherMohd.
Duk yanda yaso karya nuna bacin ransa amma wannan lokacin ya kasa, mekenan? Dan yana neman abinyi shine zai zama wulakantace? Ai ta tsaya taji mezaice.
聽 Zainab kam tana shiga ta tsaya a jikin kofa sannan tace was i mean? To mezance? Yanata wani cemin excuse me, ko suna nane hakan ai sai haka, juyawa tai taga bataga Nusaiba ba.
Nusaiba kam tsayawa tai cak ta kasa dauke ido daga kansa, can ta hangota zaune kusa dashi ta sa kanta a kafadarsa tana bacci.
Sam baima kula da ita ba sai dayaji an bude kofar, Zainab ta kalleta tace 鈥渕e kike anan?鈥� Gaba daya Nusaiba batama san tana yi ba, jin magana ne yasa ya kalli gun, sai yanzu ya kula da yarinyar dake tsaye agun. Zainab ta kalleta sannan ta kalli inda take kallo, hada ido suke wanda Khalid yai saurin kauda kansa, Zainab tasa hannu ta juyo da ita saitinta tace 鈥渓afiya?鈥�
Nusaiba tace 鈥淎unty kamar mafarki nake ko?鈥�
Kallanta tai sannan tace 鈥渕afarki anan?鈥�
Nusaiba ta daga kai tana wani irin murmushi, Zainab ta ja hannunta suka shiga ciki.
Khalid waya ya dauko ya kira number Adam, Daga can Adam yana tafe yana shan kidansa, parking yai a gaban wani shago ya shiga ciki, shago ne dayake ta ganinsa satin nan da alama ba鈥檃 dade da budeshi ba. Shiga yai yana kallan kayan dake cikin shagon, shago ne na kayan sawa, na mata dana maza.
Haryana kokarin fita yaga wani takalmi, wanda ya dau hankalinsa, dawowa yai da sauri ya daga takalmin, duba size din da yake sakawa yi ya nufo gun biya yana kokarin bada kudin ta nufo gun rike da wata riga ahannunta, abaya ce rigar, duk rigar jikinta tayi kacha kacha.
Mikama mai biyan kudin tai, kallanta yai sannan ya kalli Adam yace 鈥渄ubu goma ne.鈥�
Adam ya mikamai katinsa ya biya, hankalinsa a kwance.
Haryadanyi gaba yaji yana cemata 鈥渄ubu biyu.鈥�
Kallansa tai tace 鈥渕alam dan Allah kabarmun dubu daya da dari biyar wlh jakata aka sacemin duk kayana dana taho dashi, dubu biyun nan dake jakata su kadai gareni.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渒iyi hakuri hajiya amma ba shagona bane.
Harzaj juya ya dawo ya mika katinsa, ba tare dayace komai ba, mai shagon ya kalleshi yace zaka biya? Adam ya juya kai, nan ya sa pin dinsa ya biya ya juya yai gaba.
Da sauri ta biyoshi tana cewa 鈥淢alam! Malam!鈥�
Adam sai dayaje gaban mota ya juyo matsowa tai da sauri tace 鈥渘agode, ka taimakeni, zuwa na kenan garin kano aka sacemin kayana gaba daya........鈥�
Wayarshi datai kara ita ta katseta? Daukan wayar yai ya shiga mota ya ja yai gaba.
Khalid ya?
Daga can Khalid yace 鈥淎dam dan Allah kana ina?鈥�
鈥淕aninan a hanya yanzu zan karaso.鈥�
Khalid yai ajiyar zuciya baice komai ba.
鈥淲ani abin ya faru ne?鈥� Ya fada a ransa yana cewa yasa ai Khalid bazai taba jurar halin Zainab ba wannan aikin nasu ya basu wata daya in anyi nisa.
鈥淣o sai kazo.鈥� Adam yace okay, ya kashe wayarsa, yana tafe yana shan kidansa, hankalinsa a kwance, tunowa dayai da Goggo ne yasashi kara sauri, yasan kila ma ta fada, mai yakaishi tsayawa a shagon can? Sam yama manta abinda ke gabansa.
*******
Zainab kam suna shiga ciki ta makama Nusaiba harara tace 鈥渒in gama mafarkin?鈥�
Nusaiba ta kalleta ta matso kusa da ita kamar zata shige cikinta tace 鈥淎unty wanene dan Allah?鈥�
Zainab ta kalleta tace 鈥渨a?鈥�
Nusaiba ta kalli window tana nuna mata Khalid dake tsaye yana waya.
Zainab tace 鈥渕enene damuwarki dashi?鈥�
Kara rike ta tai tace 鈥淎unty dan Allah ina gama secondary ku aurar dani, ku bani shi.鈥�
Kallan mamaki Zainab ta mata kafin ta girgiza kai tace 鈥淣usaiba da alama kin samu matsala.鈥�
Tai ciki tana cewa 鈥渋na Nabila?鈥�
Tana daki, Zainab ta wuce cikin dakin nasu.
Nabila na zaune akan gado tanajin an bude kofar ta boye abinda ke hannunta da sauri.
Zainab ta maida kofar ta rufe sannan ta nufo inda take, Nabila ta kalleta tace 鈥淎unty kin dawo?鈥�
Zainab ta matso bayanta tasa hannu ta zaro abinda ta boye, littafi ne na makaranta ta bude cikin litaffin tare da girgizashi.
Hoto ne ya fadi daga cikin littafi, Zainab zata dauka Nabila tai saurin daukewa ta boye.
Mika mata hannu Zainab tai tace 鈥淏ani.鈥�
Nabila ta kalleta idanunta suka ciciko, Zainab ta hade rai tace 鈥渂akiji ba?鈥�
Jiki a sanyaye Nabila ta mika mata hoton, tana amsa ta juya baya hoton, sai dai me? Gaba daya yanayin fuskarta ne ya canza, idanunta suka canza, a hankali ta dago ta kalli Nabila wacce hawaye suka zubo mata.
Zainab ta zauna kusa da ita, ta zuba mata ido cikin tausayawa. Nabila ta share hawayenta tace 鈥淎unty.鈥�
Zainab ta sa hannu ta karasa goge mata hawayen sannan ta kalleta tace 鈥渂adai haka kikeyia makarantar ba?鈥�
Kai ta girgiza da sauri alamar a鈥檃 sannan tace 鈥渘a dade Allah banyi ba.鈥� Zainab tai murmushin yake tace 鈥渒afin mutanen gidan wu gane, ki tashi ki ware, ina mai bakin tsiwar tawa take ne? Ina mara hakurin nan da neman fada yakene?鈥�
Nabila tasa dariya tace 鈥渒ai Aunty.鈥�
Zainab tace ba haka bane?
Nabila tana dariya ta mike tai waje.
Shiru Zainab tai a dakin, tare da kara kallan hoton hannunta, raunin datake boyewa nata kar a sani shine ya nemi tasowa, hannunta ne ya fara rawa da sauri ta mike tare da bude windown dakin dan tasha iska saboda zuciyarta tayi nauyi.
Wani nannauyan ajiyar zuciya ta saki tare da kallan waje, Daga can gefe ta hangoshi tsaye yana waya, Excuse me! Excuse me!
Abinda ta tuno kenan, ko baka san sunana ba ai sai kawai kai maganar da kakesan yi Excuse me din na menene? Taja dan gajeran tsaki tana neman zuge window din taga ya kalli gefe, sai kuma taga ya dan daga hannu kadan ba wani alamar sakin fuska hannun dai yadan daga.
Da sauri ta fito daga dakin ta nugi falo, Nusaiba!
Abinda ta fada kenan, Nusaiba ta kalleta da sauri, sannan ta zuge labulen windown.
Zainab ta kalleta, da sauri ta boye a bayan labule tace 鈥淎unty gaisheshi kawai nai.鈥�
Nabila wacce tana fitowa kitchen tai ta zubo abinci tace 鈥渒aryane kafeshi tai da ido wanda inaji daga nan sai daya kware.鈥�
Zainab duk yanda taso ta hade rai sai datai dariya tace 鈥渞uwa yakesha kenan?鈥�
Nabila tace 鈥渆h mana.鈥�
Nusaiba ta sa dariya harda faduwa tace 鈥淜anwa uwar hadi, wlh andaiji jiki.鈥�
Nabila ta kalli Zainab tace 鈥淎unty wanene?鈥�
Zainab tace 鈥渙h bakimasan me ake cewa ba kike shiga abinda bai shafeki ba, ni ina Goggo ne?鈥�
Nabila tace 鈥渢a tafi siyo anko wai ita da kawayenta........鈥� ta karasa maganar tana dariya.
Nusaiba ma dariya tasa tace 鈥渨ai anko, ina Goggo ina anko?鈥�
鈥淢eye naku a ciki? Kunga ku kiyayeni da wannan bakin naku.鈥�
Jin karar gate ne yasa Nusaiba ta bude labule, Oh Uncle, ko ina yaje?
Hala majalisa, Nabila ta fada tare da zama.
Shiru Zainab tai tana tunanin abinda yace mata, ciki ta wuce kawai ta shiga daki, alwala tai kawai ta sa hijab ta tada sallah.
***** Adam na parking ya matso gun Khalid dake jiransa, hannu ya mikamai suka gaisa yace 鈥淜waro ya?鈥�
Khalid yace 鈥淎dam please ka daina kirana da haka.鈥�
Dariya Adam yai yace 鈥淭o Kwaran danbatta shikenan?鈥�
Khalid ya fahimci rainin wayau ne shiyasa bai tankashi ba yace 鈥渟o nake naji me da me zandinga yi saboda in san yanda zan tsara komai.鈥�
Tsara komai? Kaida kazo aiki? Abinda Adam y fara kenan a ransa amma a fili yai dariya yace 鈥渄a farko dai sai kayi hakuri dan Hajiyar akwai fada kamar.....鈥� yamai rada a kunne, wanda nima banjisu ba.
Sannan ya dago yace 鈥� abu na biyu gaskiya aiki ne ya ganka saboda journalists ce babba wacce kuma take uwar aiki wato agoggo kenan, dan ko na kasa da ita sun kawo report na abinda suka dauko wani abin bata yarda dashi harsai taje da kanta ta gani, ta tantance, sannan sau da dama takan je gurin da kanta dan rashin yarda da aikinsu, tafisan ayi a gabanta.
To kaga duk wannan lamari kaine zaka dinga jelar kaiwa da dawowa, sannan sukan tafi wani garin dan dauko rahoto ko kuma meeting nasu na yan gidan tv da sauransu.
Abu na karshe tana fita karfe bakwai da rabi na safe ta dawo karfe shida na yamma, sannan daga gun aikin tana yawo sosai.鈥�
Khalid ya kalleshi sannan yace 鈥� nagane, weekend fa kamar yau?鈥� Adam yai dariya yace ai kai bakada hutu dan wannan bansan kai na nawa bane a wadanda ta kora wani da kanshi ma yake gudu saboda wahala.
Khalid ya kalleshi yace 鈥渘i ba wannan bane damuwata, abu daya nakeso in fada, zan fara aikin nan ina naiman nawa aikin, da zarar na samu aiki zanyi resigning.鈥�
Adam yana dariya yace 鈥渂akimai sai dai fa karka manta neman aiki yanzu a kasarnan sai da hanya, waya sani ko in ka daure Hajiya ta nemar ma.鈥�
Ba karamin sosa mai zuciya wannan kalaman sukai ba, murmushi yai yace 鈥渘i Adam wani aiki kake ne? Naga har weekend kamar kaima kana aiki?鈥�
Ran Adam ya baci wanda ya bayyana a fuskarsa, kallansa yai yace 鈥渕enene?鈥�
Khalid yace 鈥渂akomai kawai dai tambaya nai naji kamar rannan kacemin kai matarkace mai kudin ko? Ita take baka, haka dai kamar naji, amma sai nake tantama dan nasan yanda kake da san kai abu da kanka kamar bazaka yarda ka zama mijin Hajiya ba.鈥�
Fuskar Adam ta murtuke sosai yace 鈥渕e kakesan cewa ?鈥�
Khalid yai dariya yace 鈥渕e zance kawai cewa zanyi ko dayake mijin Hajiyar ma matsayi ne.鈥�
Adam ya washe baki yana dariya yace 鈥渟osai ma dan banaji irinku zasu samu.鈥�
Khalid yace 鈥渟osai, bare kuma ni kasan bansan a bani, bari na wuce zanje Cafe ne.鈥�
Adam sam bai fahimci magana ya fadamai ba yace 鈥渁 ina zaka dinga kwana? Muna da dan daki, ya fada yana nuna wani daki can dake gefe, da sauri Khalid yace 鈥淪aida safe.鈥�
Ya mika mai key, haryayi gaba ya dawo yace 鈥淪orry Adam me nene salary dina sannan yaushe za鈥檃 dinga bani? 鈥淎m sorry but inasan sani ne dan na san yanda komai yake tafiya.
Adam yace 鈥済obe in kazo zata baka contract din sai ka sa hannu, dan nima bansan yaushe take biyansu ba.鈥�
Khalid ya mika mai hannu sukai sallama ya tafi.
Yana fita yabi kofar gidan da kallo, tabbas dole ya kara zake dantse ya nemi aiki dan bazai iya jurar wannan aikin ba.
*************
Wajen karfe 9 na dare ta shigo dakin yana zaune yana latsa waya ta shigo, kwanciya tai tare da rufe idanunta, kallanta yai yace 鈥渢un dazu nakeso kizo muyi magana kiji yanda mukai da Khalid.
Kallansa tai sannan tace 鈥淒azu kaje majalisa ne?鈥�
Da sauri yace 鈥渁鈥檃 takalmi naje siyowa.鈥�
鈥淢eyasa kamin karya to kace kaje siyoma Goggo magani?鈥�
Yace 鈥淪orry honey lokacin ina bank ne banasan yin doguwar magana.鈥�
Ido ta kuramai, sumbatarta yai yace 鈥渂anace miki na daina zuwa ba? Ko baki yarda dani ba?鈥�
Murmushi tai ta rungume shi tace 鈥渒aima kasan duk duniya kai kadai ne namijin dana yarda dashi.鈥�
Kanta ya shafa yana fada mata yanda sukai da Khalid, kallansa tai tace 鈥淗oney are u sure wannan mutumin zai yi? Nifa sam hankalina bai kwanta dashi na, sai naga kamar ma fada yakemin.鈥�
Dariya sosai Adam yai kafin yace 鈥淵au wacece wannan anya Zainab ce?鈥�
Tace 鈥淎llah ni yau saura kadan ma na koreshi.鈥�
Adam yace 鈥渂a fada yake miki ba haka maganarsa take, kinsan a skul sam bashida friends na kudakud? Duk wanda kika gani dashi to fa morarsa yake, saboda iliminsa ne yasa muke juremai, sai daga baya kowa ya gane haka yanayin maganarsa yake.鈥�
Zainab tadan tabe baki tace 鈥渟ai kace shi kadai ne bashida friends.鈥�
Adam yace 鈥渒e da shi akwai banbanci, ke kece bakyasan friends din, shi kuma mutane ne bazasu iya jurar halinsa ba, kinsan daga farko kowa ya dauka dan mai kudi ne?鈥�
Murmushi tai tace 鈥渨hy?鈥�
Nan ya fara bata labari hartai bacci.
Wajen karfe uku ta farka a zabure, addu鈥檃 ta shiga yi ta kalli Adam wanda ke kwance yana bacci, mikewa tai ta fito falo, kofar dakin su Nabila ta bude, suna kwance suna barcinsu wanda hakan ya sata murmushi.
Dauko hoton dazu tai ta zauna a falo tana kallanta? A hankali tai murmushin dayafi kuka ciwo tace 鈥淢amana.....鈥�
Nabila wacce taji sanda aka rufe kofa itace ta bude kofa, kallan Zainab tai da sauri ta taho gunta ta rungumeta.
Zainab ta kalleta tana hawaye ta rike hannun Nabila tace 鈥淣abila ba abinda ake miki?鈥�
Nabila tana kuka tana cewa 鈥渒ema Aunty kinsan bazan bari ba.鈥�
Zainab ta daga kai tana murmushi tace 鈥渘a manta My boss ce.鈥�
Nabila tai shiru cikin yanayin damuwa, Zainab ta kalleta tace 鈥淢aman Nusaiba na takura miki ne?鈥�
Tace kema kinsan ni, Aunty karki bari Uncle ya miki abinda Dady yama Mama, shi yasa sam nikam banaji zan iya aure har na mutu, Aminiyarta, a kullum......鈥�
Ya akai kika sani? Tambayar da Zainab ta jefe ta dashi kenan tare da mata kallan zargi.
*Ayusher Muhd.* [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁 *A GIDANA*馃崁
*Na Ayusher Muhd*
*Haske Writers Association*馃挕
*Shafi na bakwai*
Wattpad/@AyusherMohd.
聽 Idanunta Zainab ta kalla tace "Nabila!"
Nabila ta mike da sauri tace "ba abinda na sani, kawai dai maganar ce tazomin."
Zainab ta kalleta, da sauri ta shige daki ta maida kofar ta rufe.
Shiru Zainab tai tare da zubama kofar ido, kafin ta mike ta nufi daki, agoggo ta kalla taga karfe 4, computee dinta ta dauka ta koma falo ta zauna. 聽 Wajen karfe biyar ta mike ta shigo daki ta kalli Adam dake ta baccinsa, kusa dashi ta zauna sannan ta dan tabashi, tace "Honey a daure atashi aje masallaci."
Batare da ya bude idansa ba yace "bacci nakeji, nayi anjima."
Hannu tasa ta jashi ta zaunar dashi akan gadon, a hankali ya bude idanunsa yace "Honey Allah bacci nakeji."
Fuska ta hade tana kallansa batace komai ba. "Na tashi shikenan?" Ya fada tare da bude idanunsa sosai, sakeshi tai sannan tai murmushi tace "ko kaifa."
Yake ya mata, gira ta daga mai ta nuna mai toilet da ido.
Ajiyar zuciya yai sannan ya mike yai alwala yana fitowa ta mikomai jallabiya ya saka yana ta dan zumbure zumburenshi kai kace yaro ne aka kwacemai alawa.
Fitowa yai daga gidan ya nufi hanyar masallaci. Suna idar sa sallah shine na farkon mikewa ko addu'a bai tsaya ba ya fito, ganin Nazifi a masallacin yasashi saurin bi ta baya, dan bacci yakeji bashida lokacin tsayawa magana.
聽 Daga kungun da zai shiga kwanar gidansu yaji motsi, cikin tsananin tsoro ya matsa da sauri tare da zaro wayarsa ya haska fitila yana cewa "waye nan?"
Ganin ana kara buyewa ne yasashi kara matsowa gun yana haska fitilar duk da tsananin tsoron da yakeji.
Yana neman karasawa daf da mai boyewar aka saki kwalin da ake boye fuskar dashi. A tare suka saki wani kara, yaja da baya da sauri, bayan sun gama karar ne ya haska fitilarsa a tsorace.
Tsayawa yai cak yana kallan ta, haska kansa yai hakan yasa ta gane shi.
Kallanta yai yace "bake bace ta dazu? Me kike anan?"
Kanta ta saukar kasa tace "komai na wa an sace kuma makaranta nazo, gashi bansan kowa ba, banko biya kudin hostel ba. To me kike anan kina mace?
Bansan ya akai na ganni anan ba, shiru yai yana kallanta kafin yace "bakisan kowa ba a kano?"
Kai ta daga alamar eh, shiru yai yana kallanta kafin yace "to ki koma garinku mana in safiya tayi?" "Ban isa komawa ba inba haka ba mijin mamanmu dukana zaiyi."
Shiru yai yana kallanta bai fahimceta duka ba, kamar yace ta biyoshi kuma yafi kowa sanin matarsa, da sauri yai gaba bai kara waigowa ba ya shige gida. Yana shiga yai ajiyar zuciya yace " ashe dai inada tausayi."
Kai ya girgiza da sauri ya shige ciki.
A zaune ya taddata a falo taba kan sallayabga laptop dinta a gefe, da sauri ya wuce daki. Ta fahimceshi wato kar ta mai magana shiyasa ya shige, yana shiga ya kwanta, kan kace me bacci yayi gaba dashi.
***********
A bangaren Khalid kuwa bayan yabar gidan cafe ya wuce ya duduba aiki, sai wajen magrib sannan ya nufi gidan kawu.
Sam ya tsani zuwa gidan dan yana shiga layin yaci karo da babbar 'yarsa mace, anci uban kwalliya a gaban mota itada saurayinta. Yi tai kamar bata ganshi ba shima ya dauke kai.
Ji yake kamar karya shiga gidan, ya dade a tsaye a kofar gidan yana tuno bakincikin halayensu daya sha farkon zuwansa, harya juya da niyyar komawa danbatta inyaso da sassafe sai ya dinga fitowa yaji ance "Khalid?"
Juyawa yai, dan ya san wanene, Kawu ina wuni?
Abinda yace kinan yana rusunawa, Kawu ya dafa kafadarsa yace "ina zaka da?" Muje muje, ya jikin Baban naka?
Da sauki, ai naso kara komawa sai dai bana zama ne nima.
Khalid dai baice komai ba, haka suka shiga ciki inda suka wuc falansa yasa a kira matan nasa.
Su uku ne suka shigo kowa sai yace "khalid yau kaine a nan?"
Bayan ya gaisu ne Amaryar ta kalleshi tace "da alama an dace an samu aiki kenan."
Kawu yai saurin cewa "haba?" Khalid yai murmushin yake kawai, nan ya zauna sukaci abinci tare bayan sunyi sallah, nan ya fito ya wuce bangaren maza, yaran gidan sam basu da tarbiyya suna ganinshi fa amma kaf dinsu ba wanda yamai magana, kowa harkar gabanshi yakeyi, sai shine yace sannunku, kawai ya wuce dan dakin da yake zama, shi da Annur wanda yake karami ne shekarar sa 15 yanzu, Annur shima baya nan, jikinsa ne yai sanyi badai shima harya shiga sahun su ba?
Ajiye yar jakarsa yai sannan yace "bazan iya zama anan ba, daga gobe gwara na dinga zuwa daga danbatta da safe, kwanciya yai yana jin haushin amsar aikin nan dayai.
********
Haryai bacci baiga Annur ba sai da safe daya tashi ya ganshi yana bacci, tashinsa yai yace "sai a tashi a shirya ko?"
Annur yana mikewa ya rungume Khalid yace "ya Khalid."
Khalid ya tureshi yana dariya yace "mutum dai ya tashi kafin ya makara.
Annur yana dariya yace "jiya kawai na dawo naganka?"
"Kana ina har wajen 11?"
Annur yace "muna can muna hida da friends din mu."
Kamar Khalid zai sake magana sai ya fasa, shiryawa kawai yai ya dau jakarsa da niyyar zai dawo ya fita.
Mota ya hau ya nufi gidan.
聽 Karfe bakwai da minti takwas tamai a cikin gidan, tsayawa yai a waje suka dan fara hira da mai gadin.
A ciki kuwa Zainab ta gama shiryawa dan dama bata koma bacci ba, tana fitowa daga daki taga goggo ta fito tana murza ido, Zainab ta gaishet tana cewa "Goggo adan dai rage kallan nan, kamar yana yawa."
Tana fada ta nufi kitchen, Goggo tsayawa tai ranta yai mugun baci, harara ta bita dashi tace "wannan yarinya da ace ta hada jini da Ado da bamusan yana zata kareba, to sai kuma kikai sa'a bakuda hadi dashi yar kwal......"
Ganin Zainab ne yasa ta kalleta ta saki dariya tace "Gwara dai ki tafi da ko dan shayin ne, amma ace mutum ko abincin safe baya ci?"
Zainab tace "na wuce." "To adawo lafiya, dan Allah ki tahomin da goro."
To kawai tace ta fita, tana fita Goggo ta tabe baki tace "a haka dai, an kasa bani jika sai feleke kamar, kamar."
Ta kunna socket ta zauna tana cewa "dole nasha ruwan tea dan sam jiya ranta ya baci dasu Nusaiba suka dafa macaroni, haka tasha kunu ta kwanta."
Zainab na fita ta ganshi suna magana da mai gadi, agoggon hannunta ta kalla, bakwai da ashirin, sam bati tunanin ganinshi ba, ta fitone ta fara aiki a cikin mota kafin ya karaso."
Tsayawa tai a bakin kofar, yana ganinta ya nufo inda take, kusa da ita yaje ya mika mata hannu, kallansa tai tace "no am okay, zan iya dauka."
Ta fada tare da dauke kai, "no ina nufin key."
Da sauri ta kalleshi, haushin kanta ya kamata, rikemin, ta fada tana mikamai tea din, ya amsa ta juya ciki, tana shiga ta fito, mikamai tai ya mika mata tea din sannan ya amsa ya wuce ya bude motar, wani irin kallo tamai sannan ta wuce ta shiga.
Sun fara tafiya taga anzo kwana, kafin yai magana tace "nan zakai."
"Na gane hanyar." Juya kai tai dan dama batasan ya fara mata zancen left da right din nan ne yasata yin magana dan ba karamin haushi taji jiya ba.
So take ta tsaya ta sai biscuit dan na office dinta sun kare, kallansa tai tace "Excuse me dan gangara gefen titi nan."
Neman gangarawa yake ta kara cewa "Excuse me daga dan can."
Karasawayai yai parking, ta fita daga motar, tana fitar tai murmushin jin dadi tace "kaji ko da dadi."
Shikam sam bai kawo komai ba, harta dawo ta shiga.
A cikin tv station din yai parking, ta kalleshi tace "zaka iya zuwa ka dawo, in ina bukatarka zan nemeka."
Okay.
Shiru sukai sannan ta daure ta mikamai wayarta tace "zan kida Adam in na kusa gamawa."
Okay Ya kara cewa, fitowa tai ta shiga ciki.
Tana shiga bakin gun ta hade fuska tamau, ko ina ta wuce gaisheta akeyi tana amsawa, kayanta kawai ta ajiye ta dawo ta hau aikinta.
***********
Karfe sha daya ya farka? Mika yai sannan ya fito daga daki, yana tafe yana hamma, a falo yana goggo tana ta maka dariya, kallanta yai ya girgiza kai, ya matso yana cewa "wlh Goggo jin dadinki yayi yawa."
Kallansa tai tace "kai kuma fa? Wai kai dan Allah bakajin kunya? A matsayinka na namiji kullum a gida?"
"Kedai kiyi kallanki dan ni ba kunyar da nakeji, ina wadancan yan rigimar?"
Suna kitchen dan wulakanci sai yanzu suke abincin safe
Dariya ya mata yace "to ai da ke kinyi Goggo ni me kikeyi ne a gidan?"
Tace "amma in basa nan ai inayi, in suna nan kam bazan ma katti abinci ba."
Kai ya girgiza, ya mike yana cewa "Goggo ta tv ni wai kina kallan shirin sirikarki ma?"
Tace "ina kallo mana, ba gwara ni ba kai sai karyar kana kalla bayan haryau bansan a inda kake kallan ba."
*AYUSHER MUHD* [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
Haske Writers Association馃挕
Shafi na takwas
Wattpad/@AyusherMohd.
*********
Bude kofar tai sannan ta shiga cikin inda ake editing.
Suna ganinta kowa ya zauna daidai, tare da maida hankali kan aikinsa.
Fitowa tai ta bude cikin news room suma gyare gyare sukeyi tana gamawa ta fito, da niyyar wucewa dan ta shirya saboda program dinta.
Tana shiga taga Ramla a zaune tana waya. Sam bata kula tana bayanta ba sai da Zainab ta karasa gun, Ramla na juyowa sukai ido hudu da Zainab da sauri ta mike daga gun da sauri tare da cewa "Good Morr.."
Kallan da Zainab ta mata ne yasa ta yin shiru, sannan tace "ba laifi dan dama irinku kallo daya mutum dai muku ya fahimta."
Ramla cikin mamaki tace "ya fahimci me?"
Zainab ta mata alama da kai akan ta fita, Ramla idanunta suka ciciko, ta bude baki zatai magana聽 Zainab ta kalleta wanda hakan yasata yin shiru, hawaye ne suka zubo mata tasa hannunta share sannan ta fita.
Tana rufe kofa Zainab ta dan sauke numfashi kadan cikin takaici, sannan ta wuce ciki.
Ramla kam fitowa tai cikin station din tana dan hawayenta.
Kusa da wata mota ta tsaya ta share hawayenta sannan ta dau waya, bata dade da dialing ba aka daga, daga can ta fashe da kuka tana cewa "Yallabai.....kawai tasa kuka.