Kenza eBookz

A gidana complete novel - Chapter 4

A gidana complete novel - Chapter 4

A gidana complete novel Chapter 4: A gidana complete novel Chapter 4. Daga cikin mota Khalid dake zaune yana waya da Abbansa ya kalli jikin windown.

4,499 words

Daga cikin mota Khalid dake zaune yana waya da Abbansa ya kalli jikin windown.

Sallama sukai ya kashe tare da rufe idanunsa, kuka ta cigaba dayi tana cewa "Nikam matarnan ta tsaneni wlh, yaufa saura kadan ta kirani karuwa..."

Ta kara sa kuka, haushi ya kama Khalid ya kalli jikin window din gashi ta tsaya jikin kofar ba dama ya fita.

Ta cigaba "ni dai Allah bata sona, wai tsoran Zainab din kake?"

Can kuma ta kara sa kuka, sannan ta kashe wayar, tana kashewa ta kalli madubin jikin motar dan gyara fuskarta.

Kallanta taga anayi, idanunta zato da sauri sannan ta sa hannu dan bude motar, Khalid ya bude motar sannan ya kalleta.

Sai yanzu ta kalli jikin mottt are da take, gabanta ne ya fadi dan tasan motar Zainab, idanunta ne suka fifito ta kalleshi sannan ta danyi yake tace "ashe da mutum a ciki."

Khalid ya fito ya rufe motar yana neman tafiya.

Da sauri tace "kaji me nace?"

Kallanta yai sannan yace "daga ina?"

Ta dan motsa baki sannan tace "kaji daga farko har karshe kenan?"

Juyawa yai bai amsa ba, tai saurin cewa "dan Allah kayi hakuri karka fadawa Assistant director Zainab."

Ta ina zan fada mata? Abinda yake tunani kenan, da sauri tace "dan Allah, karka fada mata."

Juyowa yai ya kalleta, mota ta nuna mai tace "ba motarta bace?"

Sai yanzu ya gane, juyawa kawai yai ya wuce, dan wata irin yunwa yakeji, Ramla ta saki ajiyar zuciya tace "shikenan na gama yawo, you are fired."

**********

聽 Adam ne yai shiru a falo, Goggo nata waya tana ma mai dinki bayani akan dinkinta, Nabila da Nusaiba na gefe suna dane dane a waya, wata nannauyan ajiyar zuciya yai wanda Goggo tana waya tadan kalleshi, mikewa yai ya fita, bai dade sosai ba sai gashi ya dawo.

Goggo ta kalleshi tace "ina kaje?"

Kallanta yai yace "Goggo!" Ta kalleshi ya mata nuni da daki.

Mikewa tai ta fito suka nufi daki, tana shiga tace "menene?"

Kallanta yai tare da zama yace "Goggo yarinyar can na bukatar taimako" kallansa tai tace "wace yarinya kenan?"

Labari ya bata na yarinyar sannan yace "Zainab bazata taba bari a taimaketa ba."

Goggo tace "ka sani kazo kana fada? Kai ba ka saki jiki komai sai dai a maka ba."

Yace "wai Goggo ba a dalilina kikejin dadin nan ba? Meyasa komai nazo miki dashi sai ki dinga fadamin magana?"

Goggo tace "to ya kake so ayi? Kafi kowa sanin Zainab, ko kawarta ka taba gani a gidan nan? Daga ita sai kanenta sai ni? Sai dai in kanwa ce dakai amma inba haka ba wa ka isa kawowa gidan nan?"

Shiru yai kafin ya kalleta da sauri yace "Goggo!"

Kallansa tai yace "in mukace mata Sadiya ce fa?"

Cikin mamaki ta kalleshi tace "mene?"

Yace "in muka dan kawota akan Sadiya ce in tai kwana biyu sai mu sallameta, bayan ta gama cike abin makarantarta."

Goggo ta saki baki tana kallansa tace "ne kake cewa?"

Kallanta yai yace "Goggo bakiganta ba haryanzu fa tana waje, abin tausayi."

"Ni wai yaushe ma ka fara tausayi ne? Sannan a ina ka santa balle kasan halinta? In aljana ce fa?"

Wata dariya ya saki yace "wani irin zance kike."

Tace "lalai Adam bakada hankali wasa wasa, kanwarka? To in abu ya tashi Sadiya tazo daga kura fa?"

Yace "lokacin sai musan me zamuce kuma hali ma irin na Zainab ganewa zatai."

Kallansa tai galala kafin tace "ka samu matsala wlh, kuma ni ba ruwana, in da raban garin taimako......"

"Haba Goggo meyasa kike haka ne? Taimako na kwana daya zuwa biyu sai ya zama haka?"

Tace "ni wai yaushe ka zama mai taimako ne?sannan taya zaka shigo da ita?"

Shiru yai kafin can yace "dama yanzu nake tunanin in shigo da ita a boye inyaso intai wanka sai.....".

Shiru yai dan kansa ya kulle, Goggo tace "sai me? Sai na bata kayana tasa?" Tai maganar cikin gatse, da sauri yace "eh sai ki bata ta saka yanda inta dawo sai nace mata ga Sadiya tazoyin kwana biyu, a yanda take dawowa a gajiye ma ina zata ganeta? Sannan gobe kinga da safe zata sake fita, kinga tana gamawa sai mu sallameta."

Kai zaka biya mata kudin makarantar? Tambayar da Goggo ta jefeshi da ita kenan, kallanta yai sanan yace "Goggo wai meyasa kike haka?"

Tace "to wa zai biya mata? Zainab?"

Yace "in taji Sadiya ce ai zata taimaka."

Goggo ta mike tace "can kai ka sani ba abinda ya dameni, nidai wlh kaja aka ganeka abu ya shafeni ranka ne zai baci."

Adam yai shiru yana kallanta.

聽 ************

聽 Zainab na zaune a office tanacin biscuit da juice, badai yana waje ba? Abinda ya fado mata kenan? Mikewa tai bayan ta gama hartayi hanyar waje sai kuma ta koma ta zauna tare da cewa "ai yau dole yaje ya dawo saboda zaman yayi yawa.

Da wannan ta cigaba da aikinta, wajen sallar la'asar taga kiran Director, tana kallan wayar har sai da ta katse, sake kira akai ta kalli wayar sannan ta daga.

Zainab!

Tace "Yallabai ina wuni?"

Daga can ya amsa yana cewa "ya aiki?" Tace "lfy."

"Ashe Ramla tayi laifi? Ayi hakuri kinsan yaran nan ne wlh sai a hankali."

Tace "saboda haka ka kira?" Yace "no dama ina san fada miki ne wannan proposal din sunce gobe aje a musu presentation."

Tace "that's nice, zan shirya power point."

Yace "yauwa, sai gobe."

Nan sukai sallama ta kalli wayar sannan ta girgiza ki.

Sai karfe shida ta tashi? Ramla naganinta ta boye, Zainab ta wuce tana kiran Adam, duk da dai jikin ta na bata ya dawo.

Motar ta gani a waje hakan yasa ta nufi gun.

Ba kowa a ciki, hakan yasa ta dan wawaiga, daga gefe ta hangoshi ya nufo gun, da alama zama yai a gun.

Bude motar yai, ta bude baya ta shiga.

Shiga yai yaja suka fara tafiya.

Shiru suka danyi a motar, tana kallan wayarta, can tace "badai a waje ka zauna ba ko?"

Baiyi tunanin dashi take ba sai dayaji shiru alamar ba waya take ba sannan yace "cafe naje."

Shiru sukai ba wanda ya sake magana har suka kusa isa, daurewa tai tace "gobe daga gun aiki zamu fita zuwa kaduna, in na shiga gun aiki 1hr zanyi a ciki sai mu wuce."

Okay kawai yace suka karasa ciki......

*Ayusher* [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁

Haske Writers Association馃挕

Shafi na Tara

Wattpad/@AyusherMohd.

Harta bude kofa zata fita tadan juyo, kallansa tai tace " yanzu zaka wuce?"

Yanzu kam ya juyo yadan kalleta kadan yace "eh zan wuce danbatta ne."

Danbatta? Ta fada cikin mamaki, juya kansa yai yace "eh."

Fitowa tai batace komai ba, tana neman bude kofa taga an bude da sauri, Nusaiba? Ta fada tana kallanta.

Sam batama kula da ita ba ta wuce gun Khalid da gudu? Yana rataya jakarsa a baya taje kusa dashi tace "Ina wuni?"

Khalid ya kalleta murmushi yai sannan yace "ya gida?"

Tace lfy kalau, ga wannan. Ta mika mai coke mai sanyi tace ga wannan kasha rana.

Kallanta yai sannan ya amsa, Zainab ta saki baki tana kallan ikon Allah sai jitai an rikota, juyawa tai ta kalli Adam wanda ya sa dariya yace "kwaro da alama kayi kasuwa."

Nusaiba ta rufe ido da sauri, ta juya ciki da gudu, har tafa dan bige Adam dake jikin kofar kadan.

Adam ya kara sa dariya, Zainab ce taja hannunsa suka shiga ciki. Khalid ya juya ya fita.

Tasha ya wuce kawai ya hau mota ya tafi danbatta.

Bayan magrib ya isa, dukansu na zaune a waje suna cin tuwo sukaji sallama, da gudu su Amir suka tashi suka nufeshi suna cewa Yaya yaya

Khalid ya rungumesu sannan ya shigo ciki, Umma da Abba sunyi zuru suna kallanshi. Asiya kam mikewa tai ta dauko plate ta ajiye, Khalid ya kalleta yace "yauwa kanwata nagode."

Umma ya gaida sannan ya gaida Abba ya tambayi jikinsa.

Abba ya kalleshi yace "meke faruwa?"

Khalid yace "kawai ina tashi naji gida nake so."

Asiya tasa dariya tace "sai kace dan boarding yaya."

Yace "dama inasan kaiki boarding da alama na kusa."

Dariya tai tace "boarding ina Ss2?"

Abba yace "ban gane ba? Yanzu kana tashi kawai ka taho?"

Yace "eh Abba naga hakan yafi sauki, nawa ma tafiyr take daga kano zuwa danbatta?"

Umma tace "to yanzu ci abinci kai sallah ka huta." Ta kalli Abba tace "tunda yaga hakan yafi sauki sai ka barshi, sanda yaga bazai iya ba sai yaje can din."

Khalid yace "yauwa Umma."

Abba yai shiru bai kara cewa komai ba, Khalid ne ya zuge jakarsa ya ciro coke din nan yace "ga coke Abba."

Abba ya amsa yana cewa "to nagode."

Nan suka ci abinci, suna gamawa ya mike ya shiga daki.

*********

Fitarsa Sallar isha'i ya hangota a inda ya barta, meke damun yarinyar nan? Wai ba mutanene a unguwar da ba wanda zai taimaka mata?

Wucewa yazoyi tare da dauke kansa kamar bai ganta ba, ji yai ance "bawan Allah."

Gabansa ne ya fadi, ya juyo ya kalleta, tasowa tai daga inda take ta matso kusa dashi tace "ka taimakeni ka bani gun kwana dan Allah, jiya ruwan da akai tsakar dare a kaina ya kare, gashi ko ruwa ban samu nasha ba bare abinci."

Adam yai shiru yana kallanta, idanunta ya kalla duk ya jeme alamar wuya, yace "biyoni." Nan tabi bayanshi da saurinta.

Shiru yai a bakin kofa gabansa na duka uku uku, cewa yai tsaya anan sannan ya shiga ciki, mai gadi ya kalla yace "Bala duba min ban dakinku ko kunbar fanfo a kunne, naji karar ruwa."

Cikin mamaki Bala yace "fanfo?"

Adam yace "eh duba."

Nan Bala yai hanyar bandaki, da sauri ya mata alama data shigo, ta shigo da sauri.

Adam ya nuna mata wani daki a can gefe, ta nufeshi da sauri.

Tana shiga Bala na fitowa yace "nikam banga komai ba."

Adam yace to kila ba nan gidan bane ya wuce. Dakin ya shiga ya kunna fitila.

Tana tsaye, dayake dakin ba komai sai katifa katuwa dake kasa.

Adam ya kalleta yace "ki zauna anan zuwa dare zan ce ki shigo ciki."

Kallansa tai tace "zan iya zama? Karna ja wani abin ya faru." Yace "karki damu zan kawomiki abinci, anjima zaki shiga ciki, ba dadi ne ban sanar asu ba su ganki."

Tace "nagode Allah ya saka da alkairi." Fitowa yai ya wuce ciki.

Zainab na zaune a falo, Goggo na kan kujera daga gefe suna kallan sautin arewa wato inda Zainab ke aiki, gefe kuma Nusaiba ce da Nabila.

Zainab dake zaune tana cin abinci tna dan kallan tv din ta kalli Nusaiba tace "Wato harda daumin coke kiyi gwaninta dashi?"

Nabila tace "to da Aunty bakisan meta kinkimo zata kaimai ba."

Zainab tace me?

Abinci ta zuba a flask, ta sa coke tasa robar ruwa tasa apple a basket wai zata kaimai yai lunch.

Zainab batasan sanda tai dariy ba tace "sannu matarsa."

Nusaiba tace "Aunty dan Allah ku auramin shi."

Goggo tasa dariya tace "yaro yaro ne, wato wannan zamani ba kunya, wai yarinya ke cewa a mata aure."

Nusaiba zatai magana Adam ya shigo yana cewa "in kina sanshi tsaf zan aura miki shi."

Da sauri tace haba?

Zainab ta dan harareshi tace "karka tunzurata batasan gatse ba."

Tana gama cin abinci ta wuce daki, tana mikewa Goggo tasa cassette, Nabila tace "mu dai Goggo ki bari mu gama kallan shirin da ake."

Adam yai saurin mika ma Nabila remote yace "sa abinda kikeso."

Goggo ta kalleshi fuska a hade, yace "Goggo magana zamuyi." Yai maganar cikin rada.

Mikewa tai ta nufi daki, Nabila na cewa "Goggo fushi kikai?"

Adam yace "bari naje naji."

Nan yai ciki, suna shiga ya zauna kusa da ita yace "Goggo ya zanyi yrinyar tana dakin wajen can."

Kallansa tai galala tace "mene?"

Yace "baki ganta ba wlh duk ta rame."

Goggo tace "to meye damuwa ta?"

"Wai Goggo meyasa kike min haka? Taimakon rai zamuyi, dan Allah ki taimaka ma yarinyar nan.

Tace "naji amma kwana biyu, inta wuce kuma wlh duk abinda ya biyo baya kar ka sa dani."

Yace "ta ina ma zata wuce? Ai tana gamawa zan sallameta."

"Ynzu ya zakayi?"

Yace "idan wadancan rigimanmun sun kwanta zan shigo da ita tai wanka ta kwanta a dakinki, kinga ita da sassafe take fita, to inta dawo sai ince mata tazo."

Goggo ta tabe baki tace "wato kwakwalwarka bata tashi yin banban tunani sai kanasan abu."

Dariya yai yace "Yanzu zan kawo abinci na ajiye anan dakin karda daddare a gane in aka kamani ina zuba abinci."

Tace "can kai ka sani, nidai ka tabbatar randa zani bikin nan na yar kawata kai ka kaini a mota."

Yace "an gama Hajiya Goggo."

Fitowa tai ta dawo falo, shikuma ya wuce daki.

Zainab na ganinshi ta dan matsar da laptop din data kunna tana cewa "gobe kaduna zani."

Kaduna? Ya dada tare da zama kusa da ita, tace "eh wlh zamu presentation."

Ya kwantar da kansa akan cinyarta tasa hannunta acikin gashinsa tana cewa "ko zaka kaini?"

Idanu yadan zaro, yace eyee, dariya tadanyi tace "just joking, harna fadawa abokinka."

Sun danyi hira kafin ya fito falo, yana ganin yaran sun bar falo ya fita ya shigo da yarinyar da ko sunan ta bai sani ba.

Dakin Goggo yai da ita, sannan ya fita, Goggo na zaune a falo tana kallansa har suka wuce ciki, itadai sam hankalinta ya kasa kwanciya da wannan lamari, mikewa tai ta dau abincin da aka zuba tai daki.

Tana zaune a kasa, jikinta duk yai datti, Goggo ta kalleta sannan ta nuna mata toilet da kayan da ta fito dashi, ta juya ta fita.

Adam ya kalleta yace "kiyi wanka kici abinci ki kwanta mayi magana gobe."

Kai ta daga mai alamar to, sannan tace "nagode nagode...."

Hawaye suka zubo mata.

Adam ya juya ya fita....

***********

Tunda tai sallar asuba bata koma ba ta tsaya gyara slide din da zasuyi presenting. Karfe bakwai ta mike tai mikar gajiya sannan tai wanka ta shirya, Adam na kwance nata sharar baci.

Kayanta ta kwasa ta fito, yana tsaye a waje sanda ta fito, murmushin da batasan dashi bane ya fito, tabbas tanasan mutum taga yasan aikinshi, lalai kasarmu tana cikin wani hali ace masu kwazo da san aiki sune wadanda basuda aikinyi.

Tana shiga yaja suka tafi, ba abinda wani yace a cikinsu har suka isa cikin station din, yana parking tace "yanzu zan fito."

Ba matsala

Abinda yace kenan ya fita.

Ciki ta shiga, tana shiga ta daure fuska sosai, sunyi meeting dinsu sun gama, nan wadanda zaku rakata suka shiga tasu motar sukai gaba akan sai sun hadu acan, dan sun san bata yawo da mutane a motarta.

Zainab na fitowa taji karar text a wayarta, kallan wayar tai ta bude, Wlh Zainab sai naga karshenki, yadda kika koran daga aiki shekara biyu kenan na rasa wani aikin, ni zan zama ajalinki wlh

Tana gama karantawa tai tsaki tare da wucewa ta shiga office dinta, printing dinsu tai sannan ta kara duduba komai ta fito waje.

Mota ta shiga suka dau hanya.

Tun da suka fara tafiya mota ke binsu a baya, Khalid ya kula da hakan sau dai da alama ita bata sani ba tana ta dube dube a tablet.

Daurewa yai yace "tare muke da wadancan?"

Juyawa tai ta kalli bayansu, sannan tace "a'a wadanda muke tare sun wucemu da kusan 20min."

Shiru yai yana kara kallan motar ta glass, kallansa tai tace "menene?"

"Bin mu suke." Bin mu? Ta maimaita cikin tsoro, text din dazu ne ya fado mata.

Kallanta yai ta glass yace "kinsan su waye?"

Bakinta na rawa tace "a'a"

Tunowa da mai kukan jiya yai, kai ya girgiza da sauri yana cewa may be hanyarce daya.

Jitai yace "bari muyi kamar zamu siya abu muga."

Tace to

Kusa da masu sai da kwan zabi suka tsaya nakan hanya, Khalid ya juya baya, gani yai motar ta tsaya a bayansu kadan, yanzu kam yasan tabbas binsu akeyi, kurawa motar ido yai, maza ne a cikinta kusan guda biyar.

Kallanta yai itama kallansa take, yace "kin ma wasu laifi ne?" Shiru tai hakan yasa yace "please ki fadamin insan ya zamuyi, ga meeting kina dashi ga wadanan, in muka tsaya biye musu zaki rasa abinda zaki je yi."

Wayarta ta ciro ta bude text din ta nuna mai, karantawa yai sannan yace "kinsan number?"

Tace "a'a amma daga alamun text din cikin mutanen dana kora ne."

Baisan sanda yai wani murmushi ba.

Fuska ta hade tace "meye?"

Yace " seat belt."

Sawa tai tana kallansa haryanzu so take taji murmushin rainin hankalincan na meye."

Ganin bashida niyyar magana yasa tace "tsoro kake?"

Batare da ya juyo ba yace "me nayi da zan tsorata? Mai laifi ai shine da tsoro."

Yana kaiwa nan ya fizgi mota da gudu.........

(Ai nikam jinai motata ta makale, ashe gudu sukai suka barni a baya......)

*Ayusher Muhd.* [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁

Haske Writers Association馃挕

Shafi na Goma

Wattpad/@AyusherMohd.

*Excuse me a Zauren BieBie nake? Excuse me nan ne Zauren BieBie?....* Lol kuna sani Dariya da sarar nan, wannan shafin naku ne duka wadanda ke left da wandanda ke right....One Love

*********

Kanta ne taji yana juyawa yanda yake gudu da motar, ga hanyar sam batada kyau kallansa tai tana san mai magana taga ya ja motar sun shiga wata kwana a Zaria.

Suna yin kwanar yai parking, ya fito daga motar ya rufe sannan ya dawo titi, sai a lokacin motarsu tazo da gudu suka wuce a tunaninsu sun wucesu ne.

Juyowa yai tare da ajiyar zuciya sannan yai dan murmushi dai kace me aikin security.

Karasawa yai jikin mota, ya bude sannan ya shiga juyowa yai ya kalleta, itama shi take kallo tace 鈥渇ada kukai?鈥�

Fada? Ya fada cikin mamaki sannan yace 鈥渘i da banda laifi akan me zanyi fada da wani?鈥�

Fuska ta hade tace 鈥渄a wa kake kenan?鈥�

Baice komai ba sannan yasa key ya tada motar, idanta ne ya dan fito tace 鈥渋n kuma basu tafi ba fa?鈥�

Yace 鈥渟ai muji me suke so.鈥�

Haushi ya kamata batace komai ba, juya motar yai suka koma kan titi, suna fita daga cikin garin Zaria suka tadda motar nan a gefen titi, kallansa tai tace 鈥渟une?鈥�

鈥淢e kika musu ne haka?鈥� Shiru tai batace komai ba sai tsoron abinda zai faru fa take.

Khalid yana zuwa kusa dasu suka hau kan titi tare da nunamai yai parking. Khalid ya kalleta yace 鈥渟aura hour nawa?鈥� A hankali tace 2

Bude kofa yai ya fita, kusa dasu yaje yana neman mika musu hannu suyi musabaha, babba cikinsu ya buge hannunsa yace 鈥渕atarcan zaka bamu.鈥� Cikin mamaki Khalid yace 鈥渨acc kenan?鈥�

鈥淜arfa ka raina mana hankali ta cikin motar can, ba Zainab Aliyu Tahir bace?鈥�

Khalid ya kallesu yanzu kam ya gane aiki su akai basu mansan ta ba.

Murmushi yai yace 鈥渨ai dama Zainab kuke nema?鈥�

Eh, bamu ita.

Dariya yai yace 鈥渂a ita bace, yayarta ce wannan sunan ta Zarah, baku ganta bane? Zo ku duba ku gani.鈥�

Cikin mamaki suka karasa jikin motar, wanda ganin an nufota yasa gaba daya hankalinta ya gama tashi.

Gani tai Khalid ya bude kofar wanda idanunta suka firfito shikenan ya zo ya bada ita, Adam, Nabila, rayuwata........

Muryar Khalid taji yace 鈥渒un ganta?鈥�

Ido suka kura mata dayan ya kalli dayan cikin yaren nufe yake mai magana wai itace? Yace kamar ita kamar ba ita ba.

Khalid yai dariya yace 鈥渉ala bakwa kallan program dinta ne amma da kuna gani zaku ganeta.鈥�

Shiru sukai suna kara kallanta, Zarah wai sun dauka Zainab ce ke?

Zarah? Me mutumin nan ke shirin yi? Ta fada a ranta cikin mamaki, murmushi yai yace 鈥渕un biya ta tv station ne saboda zamu koma kaduna inda muke da zama.鈥�

Shiru sukai suna kara kallan Zainab.

Khalid ya rufe kofar sannan ya kallesu yace 鈥渁mma me yayarta ta muku?鈥�

Ba mutawa ba aiko mu akai, kasan inda take? Suka fada suna kara kallan pic din da aka turo musu, amma itafa ance yau zata kaduna sannan ya akai kuka hau motar da aka nuna mana tata?鈥�

Khalid yai dariya yace 鈥渋ta ga wuce da ragowar staff din, saboda tana sauri dan 10 zasuyi meeting din, da tare zamu taho to mu bamu shirya ba.鈥�

Yanzu kam sun dan yarda dan dama hoton ba yanzu tayi shi ba.

Khalid yace 鈥渒uyi hakuri dan Allah karku ma yayarta komai, bansan meya faru daku ba.........鈥� Malam karka soma mana wa鈥檃zi whve ka bamu gu, neman halak dinmu muke.

Khalid ya shiga mota yaja ya bar gun.

Zainab ta kalleshi tace 鈥渕e ya faru? Naga sun barmu mun wuce.鈥�

Shiru yai kafin yace 鈥� i just trick them hope bazasu gane ba har mu isa.鈥�

Ajiyar zuciya tai sannan ta sauke window dinta tare fa shan iska, shiru tai tana tunanin wanda ya aiko a kamata a cikin mutane sama da 8 data kora daga gun aiki daga sanda ta fara zuwa yanzu.

Shiru tai tana tunanin ya akai yasan gana program? Sannan ya akai yasan basu ganeta ba? Ya akai yasan bazasu fahimci ita din bace?

Tadan kuramai ido tana tunanin lamarin.

Kauda kai tai a hankali tace 鈥淭hank You.鈥�

kallanta ya danyi ta glass amma baice komai ba, yana tunanin me tama mutane haka?

************

Kusa da Goggo ya zauna a falo cikin rada yace 鈥渢ana ina Goggo?

Harara ta makamai tace 鈥渁ika fini sanin inda take.鈥�

Mikewa yai ya nufi dakin goggo, Nabila ta dago ta kalleshi amma bata kawo komai ba.

Kofar dakin ya tura, a hankali saboda yana tsoron kar ya kwankwasa su Nabila dake falo suyi tunanin wani abin.

Tana kwance a kasan katifa daure da zani sai dai zani ya sauko kadan wanda hakan yadan bayyana saman kirjinta, da sauri ya juya baya, sannan ya juya zai fita.

Jiyai ance waye? Ta fada tare da saurin jan bargo ta luluba.

Yace 鈥測ahkuri bansan bacci kike ba.鈥�

Ya Adam? Ta fada cikin alamar tambaya, juyowa yai da sauri yace 鈥測a akai kikasan sunana?kin sanni ne?鈥�

Kai ta girgiza da sauri tace 鈥渁鈥檃 jiya a gun Goggo naji tace 鈥淎damu.鈥�

Ajiyar zuciya yai sannan yace 鈥渄ama fada miki zanyi daga yau zamanki a gidan nan sunanki Sadiya,sannan gobe zakiji ki gama registration dinki daga nan sai ki koma gida.鈥�

Nagode amma me yasa zan boye sunana?

Yace 鈥渕atar gidan batasan kina nan ba sannan ba dadi taga na kawoki bayan ban sanki ba.鈥�

A hankali tace 鈥渒ayi hakuri, sannan nagode Allah ya saka.鈥�

Murmushi yi sannan yace an jima zansa ki fito a matsayin zuwanki kenan ku gaisa da mutan gidan.鈥�

Kai ta daga alamar fahimta, zan shigo miki da abinci, da sauri tace nagode.

Murmushi ya sake yi sannan ya juya ya fita.

Yana isowa falan Goggo tamai wani kallo sannan tace 鈥渟amin kati a waya ina san kiran mai dinki.鈥�

Ba musu yace to.

Nabila tasa dariya tace 鈥測au basa banba, Uncle baice wai Goggo meyasa katinki ke saurin karewa? Tai maganar cikin kwaikwayon sa.

Dariyar borin kunya yai yace haka nakeyi? Nusaiba tace 鈥渟osai ma.鈥�

Suka sa dariya, Goggo ta kalleshi cikin jin haushi.

********

Sun gama meeting komai ya tafi yanda take so, suna gama sa hannu aka kawo musu abinci, kallan mai ajiye musu abincin tai tace 鈥渄an kaima driver na yana waje.鈥�

Okay tace tana gamawa ajiye musu ta dauko take away din da juice ta fito waje, ganin batasan motar ba yasa ta koma ta sanar mata batasan waye ba.

Zainab ta amsa ta fito dashi.

Yana zaune cikin mota yana karanta wani littafi a hanunsa, mikamai tai yana amsa ta juya ciki.

Cikin mamaki ya kalleta yau me ya sameta.

鈥淓x....Ina magana.鈥� Baisan dame zai kirata ba.

Hartayi gaba ta juyo ya nuna mata alamar na meye? Tace 鈥渁n ba kowa ne kaine ba鈥檃 gani ba.鈥� Ta fada ta juya ta koma.

Sai kara jinjina ma Zainab sukeyi, suna kara nuna mata jin dadinsu nayin aikin da ita, daya daga cikin directors din yace 鈥測anda kike workaholic din nan ha mijinki yake?鈥�

Murmushi kawai tai bata ce komai ba, dan duk yanda take da mutum indai aiki ne ya hadasu batasan harkar rayuwarta ya shigo ciki.

Shima jin tayi shiru yasa bai sake cewa komai ba sai suka sako wani hirar.....

*Ayusher Muhd* [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁

Haske Writers Association馃挕

Shafi na Goma Sha Daya

Wattpad/@AyusherMohd.

聽 Su Nabila na shiga daki Adam ya mike da gudu yai dakin Goggo, haushi ya turnuketa ta bishi da wata harara ta kaici tare da cewa "meye hakan?"

Adam ya mata nuni da daki sannan ya ruga, kai ta girgiza tare da jan tsaki na takaici, kwankwasa mata yai a hankali, sannan ya tura, riga take sawa da sauri ya koma ya maida kofar ya rufe yana cewa ni bana tashi zuwa sai tana wani abin?

Karasa sa rigar tai ta bude kofar tana kallanshi fuskarta dauke da murmushi. Kallanta yai yace "hakuri na bude kina shiryawa."

Tace "bakomai ai masan ba da saninka bane."

Yace "ki dauko jakarki ki fito a matsayin yanzu kika zo."

To tace ta juya da sauri ta dauko jakarta ta fito a gaba ya sata har zuwa falo, har kasa ta tsuguna ta gaida Goggo, Goggo ta kalleta tace "ni kin tabbatar sace miki jaka akai?"

Kallan mamaki tama Goggo sannan ta kalli Adam, da sauri yace "Goggo wai meyasa kike haka ne? Bana fada miki ba?"

Share hawayenta tai tace "kiyi hakuri."

Goggo ta kalleta a haka dai gata mutum sai dai itafa tana mamaki ace kaf garin nan ba wanda ya tausaya mata ba kuma wan.........."

Adam ne yace "Goggo ki sake da ita kar Zainab ta gane wani abin." Goggo ta maida kanta kan Tv harta fara kallo ta mike ta shiga kitchen ta dauko juice ta zauna tana sha tana kallanta.

Da Adam da mai suna Sadiya wacce ko sunanta na asali bamu sani ba sukai shiru.

Can Adam yace zauna. Zamanta ta gyara sannan ya kwallawa Nabila kira itada Nusaiba.

Fitowa sukai gaba daya fuskarsu a hade.

Adam yace "Rigimanmun mu ya akai?"

Nusaiba ta turo baki tace "Dady yace gobe zai turo a daukemi."

Wani dadi ne y kama Goggo da Adam, wanda har Goggo bata san sanda tace "masha Allah hakan yayi dai dai."

Nabila ta kalleta tace "Goggo ai ba sai kin nuna murnarki a fili ba mun san dama dadi zakiji."

Goggo ta sa dariya tare da wayancewa tace "ba haka bane, ai zamanku a gidan yafimin dadi, ni da da nake zama ni kadai in Adamu ya fita? Yanzu kuwa kuna nan muna shan hirar mu?"

Nabila dai bata ce komai ba, sai yanzu suka kula da budurwar dake zaune a kasa.

Nabila cikin mamakin tace "wannan kuma fa?"

Adam ya sa dariya yace "Sadiya ce yau tazo daga Kura."

Sadiya? Suka tambaya a tare

Da sauri ya kalli Goggo yana mata nuni datai magana.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull