A gidana complete novel - Chapter 5
A gidana complete novel Chapter 5: A gidana complete novel Chapter 5. Goggo tace "baku san Sadiya ba? Kanwar Adam ce ai mahaifinsu daya."
4,482 words
Goggo tace "baku san Sadiya ba? Kanwar Adam ce ai mahaifinsu daya."
Kallan Goggo yai cikin mamaki, tace "Sadiya ga kannan Zainab ku gaisa."
Nusaiba ta kalleta tace "amma kinfi Uncle kyau kuma bakwa kama, da alama ke mamanki kikayo."
Murmushi tai, Nabila kam kallanta kawai take amma batace komai ba.
Kallan Goggo tai tace "yau da wake zan dafa wlh."
Goggo tace "da dai ni kike dan kinsan bansan da wake."
Nabila tana dariya tace "sai kisa miya akwai ragowar ta jiya.
Tana yin kitchen Nusaiba ta bita.
Suna shiga Adam ya kalli Goggo yace "Goggo wani mahaifinmu daya?"
Tace "to kana san nace mahaifinka da mahaifiyarta daya bayan bakwa ko yanayi? Sannan in tsautsayi ya kawo Sadiya nan kusa fa?"
Sadiya tazo聽 nan tai me?
Haka dai ka iya ko kunya ma bakaji, sau nawa tana ce ma zakato kana hanata?
"To wai tazo tai me? Ni kinsan bansan takura."
Goggo tace "can kai ka sani, baka dauki na jininka ba gashi kana kinkimo da titi ai."
Sadiya tai kasa dakai, Adam ya kalli Goggo yace "wai Goggo meyasa kike haka ne?"
Goggo ta dauke kai tana shan juice dinta ta cigaba da kallanta.
Adam sai kokarin jan Sadiya da hira yake dan ta saki jikinta.
************
Bayanta tadan buga saboda ciwon da yake mata, sannan ta mike ta musu sallama, nan kowa ya shiga jinjina mata suka fito ita da staff din da sukazo tare.
Tana saukowa daga kan matatakalar da waje waya ta shigo wayarta, bata dauka ba saboda tana kara yin sallama dasu, suna karasa saukowa ya rage daga ita sai staff dinta ne, babban ya kalleta yace "Hajiya kinyi ba karya wlh."
Murmushi tai tace "sannunku da aiki kuma, thanks to you komai ya tafi normal."
Nan suka yi murmushin jin dadi.
Inda motarta take suka nufa, bakowa a motar hakan yasa ta dan wawaiga, sannan tace "kuje ku hau hanya, maybe ya dan fita ne."
Ah Hajiya bari mu jira ki fara tafiya.
Hira suka dan cigaba dayi jefi jefi take sa musu baki saboda bata fiya san yin hira fa na kasa da ita ba.
Khalid ne ya hangosu daga nesa hakan yasa ya kara hanzari dan isowa, yana karasowa yace "kuyi hakuri nadan je Massalaci ne."
Kallansa tai cikin mamaki, yau meke kanshi harda bada hakuri?
Zatai magana wayarta ta sake kara, nan ta dau wayar sai kuma ta kalli Khalid.
Kallanta yai cikin mamaki, sannan ya kalli wayar hannunta wanda baya iya gani.
Hello, ta fada tare da dan matsawa daga gun su.
"Hajiya Zainab! Wato kin gudu ko?"
Gabanta ne ya fadi tace "wanene?"
Wata muguwar dariya ya saki yace "wanene? Tambaya ma kike?"
Juyowa tai ta kalli Khalid, ganin haka yasa ya matsa kusa da ita, daurewa tai tace "mekake nema da ni ne? Koma wanene in dai har ya sanni na tabbatar yasan bana tsayawa maganar da batada amfani a waya, in kana da abin cewa ka tareni ka fadamin."
Tana kaiwa nan ta kashe wayarta tare da kallansa. Are you akay? Abinda yace mata kenan ta daga kai alamar eh, hannu ya mika mata yace muga number.
Mikamai wayar tai ya karanta number sannan ya mika mata sawa yai a wayarsa sannan yace "ko zakibi wadancan ku wuce?"
Cikin mamaki tace "why? Ni bana shiga motar da ba tawa ba."
Yace " i think suna nan kar su kara biyo mu, sannan in mun samu mun wuce dazu yanzo ba abinda zamuce musu da zai sa su yarda."
Shiru tai kafin ta daure tace kai fa?
Zan taho.
Abinda yace mata kenan yai shiru, ganin hkan ne mafita yasa ta nufi gun staff din ta sanar dash zata bisu mamaki ne ya kamasu, duk da ba haka suka so ba dan sun san har su isa kuma bazasu sake ba.
Harta bude mota zata shiga ta juyo ta kalli inda yake, in suka kamashi saboda ita fa?
Anya hakan shine daidai? Karta ja mai bayan bai san hawa ba baisan sauka ba.
Kayanta ta ajiye a motar sannan ta dawo yana kokarin shiga motar,cikin mamaki ya kalleta. Tace "ba haka kawai nake korarsu ba, duk wanda na kora yayi abinda bai dace bane, wannan muryarsa tamin kama data Dauda wanda na kora shekara biyu da suka wuce, kamashi nai yana neman lalata yarinyar da tazo neman aiki."
Tana kaiwa nan ta juya harta isa bata juyo ba ta shige motar suka ja suka tafi.
Shiru yai a gun kafin shima a ya shiga.
Sai wajen karfe shida suka isa garin Kano, gidsnta tace a wuce da ita, nan ta nuna musu suka ajiyeta, tana sauka sukai ajiyar zuciya a tare, sannan suka sa dariya.
Ahhh so awkward.
********
Bala ne ya bude mata kallan sa tai bayan sun gaisa tace "Yana hanya, zai karaso."
To Hajiya dama na ganki ne a wata motar."
Murmushi tai dan yanda ya kalleta dama tasan me yake nufi.
Ciki ta shiga, Nabila da Nusaiba ne sai wata a falan.
Mamaki me ya kamasu ganinta ta shigo, Nusaiba ta leka ta window da sauri, ganin ba mota yasa ta kalli Auntyn tata tace "Aunty ya haka?"
Jakarta ta mika mata ta amsa Nabila ta amshi ragowar kayan hannunta, tana cema Nusaiba wato ke in zan fita ko in zan dawo ba mi kike nema ba ko?
Dariya tai tace "ai ke Aunty tawa ce shi kuma, wanda zan aura ne"
Nabila tasa dariya tace " a ina zai aureki bayan baimasan kina yi ba?"
Zainab ta karasa ciki, turus ta tsaya tana kallan abinda ta gani a falan ta, Nabila ta kalla wacce tai saurin cewa "Sadiya ce kanwar su Uncle."
Zainab ta kara kallanta, kasa tai dakai tare da saurin cewa "Aunty Ina wuni?"
Zainab cikin mamaki tace "Sadiya?"
Tace eh nice.
Zainab tai shiru tana kallanta kafin tace "ya kura?"
Sadiya ta kalleta tace "lfy kalau."
Zainab ta kara kallanta anya ita ta gani a bikinta?
Nabila ce ta kalleta tace "Aunty Menene?"
Ciki ta shiga tana duba agoggo tare da cewa "ina Adam?"
聽 Ya kai Goggo gun mai dinki.
Shiru tai tare da kallan agoggo, gata batada numbershi balle taji halin da suke ciki.
Sadiya ta kara kalla tace "sai naga kamar kin rame."
"Na danyi rashin lafiya ne shiyasa."
Kai ta jinjina alamar fahimta sannan ta dau wayarta ta kira Adam.
Yana ganin kiranta ya gyara murya yace "Honey."
Tace "Honey kun kusa gamawa?"
Yace "yanzu muka iso, kinga Sadiya?"
Tace "Eh na ganta, ka kira Abokinka kaji yana ina?"
Ba tare kuka dawo ba?
Eh ka kirashi in kaji ka fadamin.
To ya ce ta kashe wayar, Nusaiba ta matso da sauri tace "ina Uncle din nawa yaje?"
Wani uncle din naki kike nufi? Dariya tai tace "to yayana?"
Zainab ta girgiza kai kawai, kallan Sadiya tai wacce tai kasa da kanta.
Taci abinci?
Nabila tace "eh."
Zainab tai ciki, Nabila tabi bayanta.
Juyowa tai tace "lafiya?"
Nabila tace "Aunty kin tabbatar kanwar Uncle ce?"
Zainab cikin mamaki ta kalleta tace " me kike san cewa?"
Nabila tace "kawai na gane basa wani hira."
Zainab tasa dariya tace "kinada matsala Nabila, to in ba kanwarsa bace wacece? Me kika dauki Adam?"
Dariya tai tace "shirman nawa fa?"
Zainab tace "da alama kam, ki cire abin nan a ranki kiyi rayuwarki yanda ya kamata."
Kai ta jinjina sannan tace "Dady yace gobe zamu wuce"
Zainab tace "hutu ya kusa karewa ko?"
Nabila tace eh.
Murmushi sukai a tare Nabila, Zainab tace "a hakan ma na gode, dan in baku zo ba banaji zan dinga ganinki."
Nabila ta matso ta rungume ta, Zainab tai murmushi mai tattare da ma'anoni kala kala.
*Ayusher* [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
Haske Writers Association馃挕
Shafi na Goma Sha Biyu
Wattpad/@AyusherMohd.
聽 Tana tsaye a dakinta rike da wayarta, tana duba agoggo, anya ta zauna anan bayan abinda yake kokarin faruwa a dalilinta ne?
Sadiya na zaune a falo duk motsin datai idan Nabila akanta, wanda har ta daure tace "Lafiya?"
Nabila tace "lafiya kalau tunani nakeyi."
Sadiya ta dauke kai, yanda tai da kanta ne yasa Nabila ta kalleta har zatai magana sai ta fasa, jin an bude gate ne yasa Zainab ta fito daga dakinta.
Muryar Nusaiba taji tace "ashe Uncle ne."
Nabila tace wani uncle din tunda ke Uncle din naki biyu ne? Nusaiba ta harareta tare da juyawa ta dawo ta zauna. Nabila tasa dariya tace "Uncle din Aunty ne kenan, da dayan ne da munga fuskarki tafi haka."
Zainab kam Adam na shigowa bakin kofa tace "Honey dan zo."
Gabansa ne ya fadi, gaban Goggo ma ya fadi, a tare suka kalli Sadiya wacce ke zaune yanda suka barta, kallan Goggo yai wacce ta bugamai kallo ta mai alama da ka gani ko?
Adam ya kalleta yace "inzo?"
Tace "eh"
Sadiya ya kara kallo sannan ya nufi daki, a tsaye take hankalinta a tshe, a bakin kofa ya tsaya tace "shigo mana."
Gabansa na faduwa ya maida kofar sannan ya kalleta yace "lafiya?"
Yi maganar cikinsanhin jiki, kallansa tai tace "meya cema? Yana ina?"
Ajiyar zuciya yai yace "na kira bai dauka ba, amma wai lafiya?"
Tace "sake kira."
Kallanta yai sannan ya hau kiran Khalid, sai data katse ya sake kira sannan Khalid ya daga.
Alama ya mata da an daga sannan yace "Khalid kana ina ne haka? Zai......"
Hannunta ga harde tamai alamar X kenan karya fada, Khalid daga can yace " yanzu zan karaso, ina kan babban layi."
Adam ya kashe tare da kallanta yace "yana hanya, wai meke faruwa ne?"
Kallansa tai kamar zata fadamai sai kuma tai shiru, tace bakomai.
Shiru tai tana kallanshi a ranta tana cewa "honey am sorry, banso kaima ka shiga fargabar da nake ciki, in na san abinda ke faruwa na sanar maka."
聽 Menene?
Murmushi tai tace "Honey sai naga Sadiya?" Yace "eh wlh dazu kin fita sai gata, kinsan ta dade tana damuna akan tana san zuwa."
Zainab tace ta kyauta, dama su Nabila zasu tafi gobe da safe sai ta koma dakinsu."
Da sauri yace "ai itama jibi zata tafi, ta zauna agun Goggo."
Fuskarta dauke da mamaki tace "jibi kuma?"
Yace "eh makaranta ta samu anan Northwest ne ko Buk? Shine tazo registration."
Hannu tasa tadan bigi kafadarsa cikin wasa tace "ko kunya wai kake cewa ko nan ko nan, gobe zata registration din kenan?"
Yana dariya yace "eh."
Tace "kuje tare zan turo ma kudi, ka tambayeta nawane kudin."
Kallanta yai cikin jin dadi sannan ya jawota jikinsa yace "Honey na gode sosai."
Murmushi tai tace "Kanwarka ce, da ita da su Nabila daya suke."
Dan huce yai kadan sannan yace "nagode Honey."
Dagowa tai t kalleshi sannan tace " naga bata saki jiki ba, ko dan farkon zuwanta ne?"
Yace "ai dama ita magana bata dameta ba sosai."
Tace "wa?" Sadiyan taka da kake cewa tana damunka da tsinaniyar magana?"
Wata dariya yasa sannan yace "Sadiya kam akwai surutu kila dan bata taba zuwa bane"
Jin karar bude gate ne yasa ta fito daga dakin, Adam ya biyota.
Goggo ce ta kalleshi da sauri dan tana zaune a falo ko kayanta data anso bata je ta ajiye ba data anso.
Ganin yanda ya fito fuska a sake ne yasa tasan ba abinda ya faru, nan ta mike ta nufi daki.
Sadiya Adam ya kalla yace "Sadiya kiyi godiya Auntynki ta biya miki kudin makaranta."
Sadiya ta kalleta tace "Aunty nagode Allah ya saka da alkairi......." hawaye ne suka zubo mata, Zainab zatai magana Nusaiba tai tsale tace "My yaya ya dawo."
Zainab ce ta wuce waje, Adam ya kalleta kawai sannan ya kalli Sadiya dake hawaye ya xauna akan kujerar dake kusa da ita yace "kukan na meye?"
Kallansa tai tana share hawaye tace "na rasa me zance ne."
Murmushi yai yace "to kinyi ya isa haka nan, kai ta daga alamar to.
Duk maganar a hankali yakeyi, dan dama Nabila bata falan yanzu da alama ta shiga daki, ita kuma Nusaiba na jikin window tana kallan Khalid.
Zainab ce ta fito ya rufe motar kenan ya goya jakarsa, juyowar da zaiyi taga gefen bakinshi na jini.
Idanu ta zaro hankali a tashe ta matsa tace "lafiya?"
Kallanta yai,tace "su sukama?"
"No ba wani abun, zan wuce sai gobe da safe in Allah ya kaimu."
Ya mata sallama yana neman wucewa, da sauri tace "meyasa suka dakika bayan ba kaine da kaifi ba?"
Baisan sanda ya juyo ba, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa har ya juya kuma sai ya kara juyowa yace "Ko am sake kiranki karki daga, inso samune ma kiyi blocking din number."
Batace komai ba, sannan yadan murmusa kadan yace "sannan ba dukana akai ba, sai da safe."
Ya fita, yana tafe yana cewa wai ka bari aka dakeka sai kace wani yaro, shiru yai yana tuno abinda ya faru.
Ko garin Zaria bai kai ba ya fahimci suna binshi a baya, hakan yasa ya gangara gefen titi yai parking din motarsa, suka karaso sukai parking kusa dashi.
Fitowa sukai suka zagayeshi ganin ba kowa a motar yasa ransu ya baci.
Babba ne ya kalli Khalid yace "ina take?"
Khalid yace "wa kenan?"
Cikin masifa yace " ina take?"
Khalid yace "wanda ya turoku bai fada muku ba a wannan motar ta taho ba?"
Wannan kalma ta hasala su hakan yasa bai an kara ba yaji an makeshi wanda yasa shi ya fadi, har gefen bakinsa ya fashe.
Dagowa yai rai a bace yace "me kenan?" Wnda ya nausheshin yace "kana tunanin tsoranka mukeyi?"
khalid ya goge gefen bakinsa sannan ya make wanda ya bugeshin, shima gefen bakinsa ya fashe, hannunsa dayamai zafi gun naushin yadan yarfe sannan ya kallesu yace " na kira police na tabbatar sun kusa isowa yanzu, in munje police station ma karasa maganar acan."
Jin zancen police ne ya sa suka kalli hanya da sauri, babban yace "mu zaka rainawa hankali?"
Khalid yai murmushi yace "dan Allah kar ku tafi, dan nafiso muje police station din a dau mataki akan ku."
Cikin yaran nupe dayan ya fara mai magana, anya ma tsaya? In aka kamamu fa an kama Banza?"
Khalid ya kalli Ogan yace "bani wanda ya aikoku a waya muyi magana dan daga yanda wayarka ke kara tun dazj nasan shine"
Ogan ya kalli Khalid sannan ya zaro wayar yana neman dagawa Khalid ya warce.
Dayake jin ogan yai sanyi yasa bai kwace ba, sai leka titi suke.
Khalid ya daga wayar yana ji akace "kun biya bukatar taku? Na fada muku ai xsku sha romo gans kudi ga na can ciki."
聽 Khalid yayi mamakin jin wannan kalamai, yace "ohhhh am really sorry amma abinda kake neman yiwa matar aure bazai taba faruwa ba."
Jin haka ne yasa yace "waye kai?"
Khalid yace "wanda yasan daraja da mutuncin mace!"
Waye kai? Uban waye kai?"
"Ka shirya zuwa police station dan yanzu za'a tafi da yaranka, kaga lalatar daka nemi yiwa yarinya sai ya bayyana a idan duniya."
Hankalinsa ya tashi, wanda Khalid ya mikawa Ogan wayar da gudu suka shige mota suka arta a guje.
Ran Khalid ya baci dayaga haryanzu ba alamun yan sandan daya kira, idanu ya rufe tare da yin karamin ajiyar zuciya, nigeria kasata abinda ya fada a fili kenan tare da murmusawa, yanzu da itace aka kama har a gama lahanta mata rayuwa ba wanda zaizo cetanta.
Ransa ba karamin baci yai ba ganin ya dade a gun yan sandan basuzo ba yasa ya juya ya bar gun.
Yana tafe kalaman mutumin nan namai yawo, wani irin rashin imanine wannan? Kai laifi dan an hukuntaka sai ka nemi hanya mafi muni kace dashi zaka rama.
聽 Wayarsa ce聽 ta hau kara wanda ya dawo dashi daga tunanin dayai, ganin Adam ne yasa ya daga dan dama so yake ya kirashi.
Adam yace "Khalid ka wuce ne?"
Yace "yanzu zan hau mota naga magrib tayi."
Adam ya kalli Zainab da ta wasie tana dadana tablet dinta yace "ka dawo ka kwana anan dan Allah kaga dare yayi."
Khalid yace "karka damu yanzun nan zakaga na isa gida."
Adam yace "yau dai kadai yanda kasha doguwar tafiyar nan ka zo ka kwana anan."
Yace "to zan wuce gidan kawuna na kwana acan."
Adam yace "shikenan."
Har zasuyi sallama yace "Adam."
Adam yace "naam"
Yadanyi shiru saboda baisan yanda zaiyi yace mai karyabar matarsa ta dinga fita ita kadai ba, daurewa yai yace "ai kun shiga gida kenan ko?"
Dariya tambayar taba Adam yace "eh."
Khalid yace "to shikenan sai da safe."
Nan sukai sallama ya dan sosa kansa na jin haushin yanda yai tambayar.
********
Kallan Zainab Adam yai yace "yace a'a"
Tace "me?"
Yace "kikace wannan abokin naka ya kwana anan mana tunda tafiya mukai doguwa."
Ta sa dariya tace "wai dan nace haka ne ka kirashi? Tab lalai Honey kaima."
Tana kaiwa nan ta mike ta shiga toilet.
Tana rufe kofar tace dan an tausaya ma shine zaka wulakanta mutane? Kai ta tafiya din kafi ruwa gudu.....
Harya kwanta yaji kishir ruwa ta dameshi, mikewa yai ya fito a hankali ya nufi kitchen.
Ruwa ya dauko a fridge ya fara sha, daga gefe yaji kamar a na nufo kitchen din, da yake fitilar wayarsa ya kunna kawai ya haske wanda ke tahowa.
Sanye take da vest dinta sai zani data daura, ganin shigarta ne yasa yai saurin sauke fitilar tare da maida fridge din ya rufe.
Nabila dan haskamin hanys zan fadi dan Allah.
Abinda ta fada kenan cikin sanyin murya.
Adam ya haska mata hanya sai dai bai san sanda yake kara kallanta ba, harta karaso.
Kusa dashi ta tsaya wanda hakan yasa ya haska kansa yace "nine ba nabila ba."
Tace "Yaya baka kwanta ba?"
Yace "na kwanta ruwa naji ina san sha na taso."
Amma ki dinga sa hijab in zaki fito, ko bakiga da maza a gidan ba?
Ta kallesh tace "kai kadaine a gidan yaya, sannan bansan zan ganka ba, ga zafi nakeji, na kuma san kai ba masu halin banza bane."
Murmushi yai yace "hakane."
Sha ruwan zan tafi na kwanta.
Tace to nan ga fara shan ruwa, a zabure tai tsale ta matsa inda yake ta kankameshi kam jikinta na kyarma.
Hankalinsa a tashe yace "Sadiya Sadiya menene?"
Kyarma jikinta kawai yakeyi gashi ta matseshi tsam, da kyar ya banbareta yana jijigata, har yana neman kunna wuta ne yasa ta farfado.
A tsorace yace "lafiya?"
Tace "abu nai?"
Yace "eh yanzu kika kankameni."
Hawaye ne suka shiga zubo mata wanda tausayinta ya kara rufemai zuciyaaaaaaa
鈽樷槝鈽樷槝鈽樷槝鈽樷槝鈽樷槝鈽樷槝 [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
Haske Writers Association馃挕
Shafi na Goma Sha Uku
Wattpad/@AyusherMohd.
*Jinjina Gaisuwa tare da Fatan Alkairi a Duk Inda Kuke Billy Galadanci da BillynAbdul....May Allah Always Help and Bless You馃グ馃グ馃グ馃グMuch Love*
聽 Cikin mamaki Adam ya kalleta yanda take hawaye ne ya bashi tausayi, yace "Sadiya?"
Hawayenta ta share tace "Yaya bansan meke damuna ba wannan larura tawa ni kaina na kasa ganeta."
Larura?
Ta kalleshi, zatai magana kenan sukaji alamun bude kofa, da sauri ta ja hannunshi suka bar kitchen din. Store ta turashi, sannan ta shiga tare da barin kofar a bude kadan tana lekawa. Kuna wutar falan da akai ne yasa ta fahimci wacece, matsowa yai yace " wacece?"
Nunamai Nabila dake kale kalan falan tai, yace "to me muke anan? Laifin me mukai muke boyewa?"
Nabila ta kalla wacce ta shiga kitchen nan ma taga ba kowa, tabbas taji alamun magana tana bacci, ganin bakowa ne yasa ta koma daki, tana rufewa Adam ya kalli Sadiya wacce tace "yaya yahkuri ina tsoron me zatace ne in ta ganmu muna magana tsakar dare mu biyu."
Yace "ni dake a matsayin jini daya muke ko kin manta ne?"
Kanta ta saukar kasa tace "na manta yaya, yahkuri."
Murmushi yai yace "bakomai, jeki kwanta dare yayi sosai."
Kai ta daga alamar to sannan ta juya ta fita, tana fita ya fito ya nufi kitchen ya hau kwankwadar ruwa sannan ya juya ya shige daki ya kwanta.
Sadiya kam a hankali ta shiga dakin, Goggo nata jan uban munsharin bacci, ta kwanta a inda take kwanciya wato kasa.
Shiru tai tana tunani, kafin bacci ya dauketa.
Kamar yanda ta saba karfe bakwai ta gama shiryawa, Adam dake kwance yana bacci ta kalla sannan ta sunkuyo ta sumbaci kuncinsa, bargon ta gyaramai sannan ta dau kayanta ta fito daga dakin.
Sadiya ta gani tana ta wanke wanke tare da gyare gyare a kitchen.
Cikin mamaki tace "Sadiya me kike haka da safen nan?"
Nan ta tsugunna har kasa ta gaisheta, Zainab ta amsa tace "amma ke da zaki kwanta ki huta me kike a nan?"
Murmushi tai tace "Auntu kawai sai na hau kwanciya? Gwara dai na taimaka da wani abin."
Zainab ta fara hada tea dinta tana cewa "da sai ki bari in an tashi amma ba da sassafe haka ba."
Sadiya tai kasa dakai alamar kunya, Zainab cikin jin dadi tace "nagode."
Sadiya tace nice da godiya Aunty. Zainab ta dau tea dinta ta fita.
A waje ta ganshi yana goge motar, karasawa tai gun, ganin bai ganta ba yasa ta danyi motsi da kafarta.
Khalid ya juyo ya kalleta tare da cewa "oh bansan kin fito ba."
Inda aka bigeshi jiya ta kalla sannan tace "hannuna." Da sauri ya bude motar sannan ta sasu a ciki, shiga tai ciki ta zauna, sannan ya shiga shima.
Harya tada mota sai ji tai ance "Ina kwana?"
Mamaki ne ya kamata wanda har saida tace "dani kake?"
Baice komai ba ya fita da motar, kallansa tai sannan tace "daga jiya zuwa yau ka canza yanayin da kake kallo na ne?"
Cikin mamaki yace "name kenan?"
Tace "gaisuwar ta mecece? Ko dan abinda ya faru jiya yasa ka fara daukata abar tausayi?"
Jiyai baisan me ma zai ce mata ba hakan yasa yai shiru bai ce komai ba, dauke kai itama tai ta cigaba da dube dubem takardarta.
Yana san yaji ko number ta sake kiranta amma baisan ta yanda zaice ba, hakan yasashi yai shiru, dan jiya baccin dayai kalilan ne, yana ta mamakin wannan lamari, wato dan ankori mai laifi sai ya nemi lalata ma matar aure rayuwa saboda kawai cikar burinsa na daukan fansa? Lalai bata san me mugun nan ya shirya a kanta ba da........"
Jin wayarta na kara ne yasa ya kalleta ta glass din mota, jiyai tace "Nabila!"
Hakan yasa ya maida kansa titi, daga can Nabila tace "wai Aunty harkin tafi?" Tace "eh da wani abin ne?"
Cikin shagwaba Nabila tace "yaufa zamu tafi."
Oh my Gosh!
Abinda ta fada kenan sannan tacigaba " wajen nawane?"
Tace "bansani ba wlh amma nasan bai wuce rana."
Zainab tace "ba matsala zan dawo lokacin lunch sai muyi sallama na koma."
Nabila tace "okay in naga an kusa lunch da kaina zan kiraki, nasan inkika shiga aiki mantawa zakiyi."
Zainab tai dariya sannan tace "to ki tabbatar kin kira." Nan sukai sallama ta kashe wayar, harta danyi shiru sai tace "wajen 12:30 zaka dan maidani gida."
Okay! Abinda yace kenan, shiru tai, har suka isa.
Suna isa ta fita tai ciki, juyawa yai da motar ya nufi police station, duk da dai yasan a banza zashi amma yana fatan y hadu da nagari.
Bayan ya shiga ciki ne ya sanar da su wata number yake so su bincika suga na wanene, officer din ya tambayeshi number wacece? Matarka ce ko mamanka? Ko kuma Yayarka ko kanwarka?
Kallansa yai yace "kanwatace."
Yace "wanene ke kiranta?"
Khalid ya kalleshi cikin jin haushin tambayar ya kai da aka fadama ana san ka taimaka ka nemi me number zaka tambaya wai number waye?
Ganin yanda Khalid ya ke kallansa ne yasa yace "oh ashe fa haka kace ko?"
Ran Khalid ya fara baci, daurewa yai yace "eh ga number."
Sai da ya gama karantawa sannan yace " yauwa meye sunansa ma? Sannan a ina zamu nemeshi?"
Khalid ya kalleshi yace "barshi kawai, dan da alama ba a nan ka dace ba."
Ya juya a kufule ya bar gun, Officer ya bishi da zage yana cewa a gidan uwarka na dace? Dan************
Khalid ya shiga mota rai a bace yaja ya bar gun, waya ya daga ya kira Salmanu, daga can ya daga yace "Khalid."
Khalid yace "Salmanu kasan wani a police station? Number nakeso amin tracking."
Salmanu yace "bansan kowa ba wlh sai yayan waccen."
Khalid yace "wanda suka yaudareka? Basu indai sune."
Nan ya kashe wayar ya juya can tv station din, yana isa ana turomai text na interview yana karantawa ya kifa wayar dan yanzu yama daina sa rai.
**************
聽 Goggo tana zaune akan kujera tanacin soyayyen dankali da kwai da Nusaiba ta soya musu, tana ci tana kallanta a tv.
Ita kadai ce a falan dansu Nabila na daki suna hada kaya, Sadiya kuma na wanka.
Fitowa yai daga daki yana mika, alamar yanzu ya tashi, Goggo ta kalleshi ta tabe baki tare da shan shayinta ta cigaba da cin dankalinta
Kallanta yai yace "Hajiya Goggo abinci akeci ne?"
Kallansa tai sannan tace "wai kai bakajin kunyar rayuwarka?"
Kallanta yai yace "me kuma nai?"
Tace "kalli karfe nawa? Ka baje kana uban baci kamar kasa, ko kunya ma bakaji."
Agoggo ya kalla karfe sha daya da kwata yace "to wai Goggo menene dan nai bacci? Kemafa kallan ki kike, kici kisha ki kwanta."
Ta harareshi tace "can ta matsema, nidai ina tuna ma ran asabar zaka kaini biki ran lahadi kuma za'ai dinner da daddare."
Wata dariya ya saka kafin yace "wai da gaske dinner din zakuyi?"
Tace "mu kawayen uwar amarya ne meye in munje?"
Yace bakomai Allah ya taimaka.
Tace "waccen magen daka kwaso yaushe zaka kaita makarantar ta gama ta tafi? Nifa kasan bansan a takuramin a dakina."
Yace "Zainab tace ta zauna adakinsu Nabila insun wuce yau."
Goggo ta kalleshi cikin zargi tace "ita da saka sallama gobe meye naka nacewa ta koma can?"
Yace "bani na fadaba Zainab ce tace saboda ke."
Goggo tace "to koma menene ka tabbatar ka sallemeta gobe."
Yace to naji, tana ina?
Tana daki.
Ta cigaba da cin abincinta. Dakin ya nufa ya kwankwasa, daga ciki ta bude.
Kallanta yai yace "inkinshirya ki fito kici abinci kafin na shirya sai muje."
Tace "kai kaci abinci?" Yace "ba matsala muje ko acan na samu wani abin."
Tace "to."
Fitowa tai sanye da kayan Goggo wanda sun mata yawa, yace "ina zuwa."
Sa sauri ya nufi dakinsu, Goggo ta bishi da ido. Yana zuwa ya bude drawer din kayan Zainab, kayan da ta dade batasa ba ya dauko guda biyu sannan ya dawo da sauri聽 Goggo ta kara binshi da kallo.
A bakin kofa ya tadda ita ya mika mata, kallansa tai tace "na waye?"
Yace "kayan Zainab ne bata sashi saboda ya mata kadan,ki gwada ko zai miki"
Ta amsa idanunta suka ciciko yace "kar ki fara kukan nan naki."
Ta kalleshi tace "Yaya nagode."
Juyawa yai da sauri dan shiryawa.
***********