A gidana complete novel - Chapter 6
A gidana complete novel Chapter 6: A gidana complete novel Chapter 6. Bayanta tadan mike saboda dan gajiyar data taso mata sannan ta kalli agoggon…
4,484 words
Bayanta tadan mike saboda dan gajiyar data taso mata sannan ta kalli agoggon hannunta, ganin lokacin ya kusa yasa ta jawo drawer din kusa da ita hoton dake ciki ta ciro, a hankali tasa hannunta ta goge sannan ta kura wa hoton ido, idanunta ne suka fara canza kala da sauri ta maida hoton ta rufe.
Sannan ta mike da dau wayarta.
*************AYUSHER********** [10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
Haske Writers Association馃挕
Shafi na Goma Sha Hudu
Wattpad/@AyusherMohd.
*Ayusher Muhd*
Baki Goggo ta saki dataga Sadiya ta fito daga daki sanye da kaya, duk da bata san Zainab da kayan ba amma tasan ina zata samo kaya inba na Zainab ba? Sadiya ta matso ta tsuguna a gefen Goggo ta gaisheta, Goggo ta amsa tace 鈥淜in shirya?鈥� Tace 鈥渆h.鈥� 鈥淭afi da wannan kitchen ki zubo abinci.鈥� Ta mika mata plate din hannunta. Sadiya ta amsa ta mike ta nufi kitchen, Goggo ta kwafa ta maida kanta kan tv.
Nabila ce tafito daga cikin daki, zama tai akan kujera tare da kallan Goggo tace 鈥淕oggo naso ina nan za鈥檃i bikin nan inje rakiya.鈥�
Goggo ta kalleta tace 鈥渋nkinje wa kika sani?鈥� Nabila tadan tabe baki tace 鈥渂a sai kin fadi haka ba Goggo nima neman magana ce, ko ina nan ba zuwa zan ba.鈥� Dariya tai tace 鈥渘ima naso kina nan muje tare wasa nake miki, ai tafiya da dan rakiya yafi dadi.鈥�
Nabila tace 鈥淯hm.鈥�
Goggo ta harareta ta kasan ido a ranta tana cewa wannan yarinya da tsinanen neman magana take. Adam ne ya fito daga daki yana sa mabalin riga.
Wai harkai wanka ko me? Goggo ta fada tana kallansa, Nabila ta kalleta tace 鈥渢o in banda abinki Goggo dakalw yai?鈥� Goggo ta kifa mata harara tace 鈥淣abila wai meyasa bakinki baya shiru ne? Nabila ta kalli Adam wanda shima kalaman Goggo sun bata mai tace 鈥淯ncle dan Allah ka taimaka ka daumin hoto ka turamin.鈥� 鈥淗oto? Nawa?鈥� Alama ta mai da Goggo tace 鈥渋n zamusha ashoki.鈥� Adam yai dariya yace 鈥渁ngama, nayi alkawarin turuwa.鈥�
Sadiya ce ta dawo dauke da plate biyu, ajiye daya tai a kusa da Goggo sannan ta ajiye ma Adam a inda yadan fiya zama tace 鈥測aya gashi.鈥� Ta koma kitchen, daga ciki tace 鈥測aya sugar fa?鈥� Yace 鈥渒adan.鈥� Jim kadan ta fito da cup ta ajiye mai sannan ta zauna.
Yace 鈥済odiya nake kanwata.鈥� 鈥淜anwa?鈥� Goggo ta fada ba tare da ta sani ba. Nabila ta kalleta tace 鈥淕oggo me kike nufi?鈥� Adam ne ya kalleta da sauri, dariya ta saki tace 鈥渄ubamin ki gani Nabila, maza basa tashi cewa mace kanwarsu sai ta musu aiki.鈥�
Nabila ta kalli Sadiya wacce tai shiru tana cin abicinta, wai Sadiya bakya magana ne?鈥� Murmushi tai ta kalleta tace 鈥渋nayi.鈥� Nabila ta kalli Adam da Goggo tace 鈥渨ai haka take? Ni sai naga kamar ba haka ya kamata 鈥榶a da uwa su dinga yi ba.鈥�
Adam ne ya kwashe da dariya harya kusa kwarewa yace 鈥淏aki gansu a daki bane su biyu, sun iya kus kus cikin dare.鈥�
Nabila ta kalleshi sannan ta kalli Goggo wacce itama kallanshi take tace 鈥渋rin wannan dariya?鈥� Goggo tace 鈥渒uyi ku gama ku wuce lokaci na wucewa.鈥� Adam ya mike ba tare da ya kara cin komai ba ya dau plate da cup din yai kitchen, ajiyewa yai ya fito yai waje. Sadiya ta mike itama ba tare da ta karasa ba ta kai kitchen ta dauko hijab ta fito. Harzata fita Nabila tace 鈥渟aduwar alkairi.鈥� A hankali tace 鈥渂azamu sameku ba?鈥� Tace 鈥渆h, sai kun dawo.鈥�
Sadiya ta fita, a bakin mota ta tarada Adam ta bude ta shiga shima ya shiga, Nusaiba ce ta fito da gudu tace 鈥淵ayanane?鈥� Nabila dake zaune ta mike tace 鈥淎llah ya baki lfy dan wlh bakida ita.鈥�
Cikin masifa tace 鈥渒e kika dauranun rashin lafiyar?鈥� Nabila ta daga kafada tace 鈥渒ika daurawa kanki dai.鈥� Cikin masifa Nusaiba tace 鈥渒e kuma meye naki a ciki?鈥� Nabila ta fara hamma tace 鈥渁hhh nagaji.鈥�
Ran Nusaiba ya kara baci, Goggo ta kalleta tace 鈥渇adan karshe ake mana?鈥� Nusaiba tace 鈥渁i munsan murna kike da tafiyarmu.鈥� Goggo tace 鈥渘i mikon ayaba a kitchen da alama neman magana kikeso.鈥�
Nusaiba ta wuce kitchen ta dawo da ayaba ta mika mata. Goggo ta amsa ta maida idanta kan tv.
*************
Zainab ce tai knocking din glass din baya, Khalid ya bude motar ta bude ta shiga. Zama tai sannan ta kalleshi a ranta tace baya gajiya da zama a mota? Khalid ne ya tada motar sannan yace 鈥渕uje?鈥� Tace eh. Nan ya fara tafiya, shiru sukai a mota kafin wayar Khalid tai ringing, dauka yana a handsfree yace 鈥淪almanu zan kiraka.鈥� Yana neman kashewa cikin tashin hankali yaji Salmanu yace 鈥淜halid yanzu bayan munyi eaya na fito zanje siyo kunun aya, naga Asiya a hanyar gidanmu.鈥� Asiya? Khalid ya tambaya, Salmanu yace eh? Wai tsaytsayi ya samu Abba, da alama bandaki ya shiga ya nemi bin bango da kanshi ya fadi.
Cikin tsananin tashin hankali Khalid yace 鈥測anzu Abban yana ina?鈥� Ya fada yana neman daukan wayar dan ya kashe handfree din. Salmanu yace 鈥渕unje Chemist sunce mu wuce asibiti cikin gaggawa, to gashi munzo asibitin su kuma sun ki karbarmu tukunna.鈥�
Khalid hankali a tashe yace 鈥渂ari na taho, zanzo yanzu.鈥�
Zainab da tunda aka fara wayar hankalinta ke kan Khalid tana ganin ya ajiye ga kalleshi. Juyowa yai ya kalleta yace 鈥渁m soryy bansan ya za鈥檃i ba Abbana ne bashida lafiya da alama dole naje.鈥� Kai ta daga alamar to sannan tace 鈥渁mma naji yana cema ba鈥檃 karbesu ba.鈥� Yace 鈥渆h zanje inga meza鈥檃i. Zainab tace 鈥渋nba damuwa ka kawosu nan asibitin Zaks, mai asibitin matarsa tare mukai makaranta.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渕ungode zanje in abin bai yiwuba sai mu taho nan din, nagode sosai.鈥� Tace 鈥渢o ko zaka kaini gida sai ka wuce da motar?鈥�
Kallan mamaki ya mata, kanta ta kawar gefe. Komawa yai ya zauna daidai sannan ya maida motar titi ya cigaba da tafiya. Can ya daure yace 鈥渒o na maidake station din sai na wuce?鈥� Tace 鈥渁鈥檃 zan tafi da kaina, ka wuce.鈥�
Shiru yai yana tunanin halin da Abba yake ciki, yana neman shiga gate tace ya ajiyeta anan, nan yai parking ta fito, harta rufe kofar tai saurin budewa tace 鈥淥hh akwai wani dr Sabir a asibitin Danbatta, ta dauko wayarta tak searching din numbersa sannan ta mika mai wayar tace 鈥渒a kirashi zan mai magana yanzu.鈥�
Khalid ya karanta number sannan ya mika mata wayar, kallanta yai tana amsa ta wuce ciki.
Juya kan motar yai ya dau hanyar danbatta.
Zainab na shiga gate ta tsaya ta kira shi, sai da wayar ta kusa katsewa ya daga 鈥淶ee?鈥� Tace 鈥淪abir kana danbatta ne haryanzu?鈥� Yace 鈥渆h nemana kike ne?鈥� Tace 鈥渘o abokin mijina ne zai nemeka yanzu plz.鈥� Yace ok, sanin halinta yasan yanzu zata kashe wayar yai saurin cewa 鈥渟hikenan?鈥� Tace 鈥渁kwai wani abu ne?鈥�
Dariya yai yace 鈥淶ee kenan, abinda zakicewa wanda ya soki na shekara da shekaru kenan?鈥� Tace 鈥渘agode da taimako.鈥� Ta kashe wayar, daga can Sabir ya kalli wayar tare dayin murmushi yace 鈥淶ee kenan鈥�
*******
Sai da sukai nisa yace 鈥渘orthwest ce?鈥�
Tace 鈥渆h.鈥� Nan suka dau hanya, kallanta yai kadan yace 鈥渄azu Nabila ta tsorata ki ko?鈥�
A hankali tace 鈥渆h.鈥� Yace 鈥渉aka take, halinsu daya da yayarta sai dai ita akwai bin didigi.鈥�
Sadiya tai murmushi tace 鈥渕eyeasa basa yarda da mutane?鈥�
Adam ya kalleta yace 鈥渒arki damu da wannan.鈥� Tace to. Sai da suka tsaya suka cire kudi ya bata sannan suka karasa northwest yace 鈥渋n rakaki ne?鈥�
Da sauri tace 鈥渁鈥檃 zan je in gama, ko zakaje ka dawo? In ma gama sai ma fadama?鈥�
To kawo wayarki na sa miki numberta, nan ta mika mai yar nokia din nan me touch ya amsa ya saka mata sannan yace 鈥渋nkin gama ki kirani.鈥�
Harzata fita ta juyo tace 鈥測aya nagode sosai.鈥�
Murmushi yai yace 鈥渒arki damu.鈥�
Shiru tai tana kallansa, wanda harya tsargu yce 鈥渕enene?鈥� Tace 鈥渂an taba ganin mutum irinka ba.鈥� Kansa ya shafa yace 鈥� da gaske.鈥� Ta daga kai alamar eh, tace 鈥渋rinka mata ke fatan samu? Aunty tayi dace.鈥� Kallanta yai yace 鈥渉aka kike tunani?鈥� Tace eh. Yace yau ce rana ta farko da wani ya fadan haka, kowa cewa yake nayi dace.鈥� Kai ta girgiza da sauri tace 鈥渄uk da bansan halayen mutane sosai ba amma nasan itace tai dace, itama tanada kirki sosai ina kuma mata godiya.鈥�
Washe baki yai, wayarta ce ta fadi tagun kafarsa, da sauri tasa hannu zata dauka, shima yakai hannu zai dauka hannayensu ne suka hadu, kallanta yai, itama kallansa tai sannan tai kasa dakai tare da dauke hannunta.
Dagowa yai ya mika mata wayar, ta amsa tace 鈥渘agode yaya.鈥�
Jeki inkin gama ki kirani. Tace 鈥渘agode.鈥�
Fitowa tai ya juya ya tafi.
Sai da motar ta kure sannan na kalli fuskarta, a hankali naga wani murmushi wanda ya fito daga gefen bakinta, ya sunan murmushin nan? Me yake nufi? Wa tayiwa? Abinda ya ziyarci kaina kenan ganin salaha Sadiya dauke da wannan murmushi yasa naji kaina ya juya........
*********Ayusher******* [10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
Haske Writers Association馃挕
Shafi na Goma Sha Biyar
Wattpad/@AyusherMohd.
*Ayusher Muhd*
Juyawa tai hankalinta a kwance ta shiga makarantar, hannu tasa a jakarta ta dauko wayarta wacce na gani daga mai touch ta koma iphone, baki ma sake ina kallan ikon Allah, number ta danna sannan ta fara waya. Kana ina? Kazo ina jiranka a northwest. Tana kai nan ta kashe wayarta, maimakon ta shiga ciki wucewa tai gefen inda motoci suke ajiye tana dadana waya, batai minti goma ba sai ga wata mota nan mai masifar kyau ta karaso, budewa tai ta shiga sannan yaja suka bargun. Kallansa tai bayan sun fara tafiya tace "ina abin?" Nan yasa hannu gefen kujerarsa ya ciro wasu takardu ya mika mata. Amsa tai tana dubawa sannan tai tsaki sannan tace "tsaya." Nan ya ja gefen titi ya tsaya, kallanta yai cikin kaguwa yace "Booboo na muje hotel din plz, am in a hurry...." ya fada yana daure hannunsa akan cinyarta. Doke hannun tai tace "sai yaushe zance ma ka barni na gama abinda yafi komai mahimmanci a rayuwata?"
Kallanta yai jiki a sanyaye yace "kiyi hakuri, amma ya abinda kikeyi?"
"Haushi yasa ma abin baya birgeni, I didn't expect him to be that easy."
Ta kalleshi sannan tasa hannunta a saman goshita ts kwantar da kanta kan kujera, wani kwafa ta saki wanda ya sashi shan jinin jikinsa yace "muje?" Tace "kaini naci abinci dazu na kasa ci saboda wannan yar iskar yarinyar."
Yace "wacce?" Tace "Nabila take ko wa? I hate that girl."
Murmushi yai yace "me kikesanci?"
"Kaini Cilantro Restaurant." Yace okay.
********************
聽 Zainab ce ta shiga cikin gida bude kofar falo tai, wanda yasa su kallan kofar. Zainab ce ta shigo a tare sukace Aunty? Zainab ta kallesu tace "wannan kiran fa? Bakuso dawowa ta bane ko laifi kukamin?"
Dariya Nabila tai tace "munji ba alamar karar gate ne bare na mota."
Da gudu Nabila ta tashi ta bude kofa, ganin ba mota yasa ta juyo da sauri tace "Aunty harya tafi?" Ta fada kamar zatai kuka. Zainab tace "eh ya wuce yanada abinyi."
Zama tai a kasa dabas kawai ta sa kuka, Zainab cikin mamaki tace "menene?" Nabila ta girgiza kai tace " malama dan jeki waje kiyi kukan asarar ki, mu dan Allah karki cika mana kunne." Haushi ya kamata ta taso ta nufo kan Nabila, da gudu Nabila ta mike tai bayan Zainab wacce ta shiga tsakiyar falan.
Zainab ta kalli Nusaiba tace "Nusaiba menene kuma?"
Nabila tana dariya tace " saboda wanda take dakon sanshi baisan tanayi ba, ya tafi batamai sallama ba."
Zainab ta kalli Nusaiba wacce ke kokarin jawo Nabila. Tace "wai dama da gaske kike? Lalai." Ta kalli Goggo wacce ke kallansu tana cin cincin."
Nusaiba ta kalla tace "Nusaiba kin wuce kin zauna ko kuwa? Ke kuma in sake jin bakinki." Ta fada tana kallan Nabila. Wucewa tai ta zauna, Nabila tai kitchen, Zainab ce ta kalli Goggo tace "Goggo an tashi lfy?" "Lafiya kalau, sun tafi makarantar."
Zainab tace "oh nama dan sha'afa." Ta fada tare da wucewa daki, tana bude kofar dakin tace "Nabila." Nabila data sha ruwa ta taho da sauri ta bita dakin.
Zainab na zaune a bakin gado ta shiga. Zama tai kusa da ita tace "Aunty!" Zainab ta juyo gaba daya ta kalleta yanayin fuskarta ne ya canzs zuwa tausayi, Nabila tace "Aunty daina, daina kallo na haka."
Zainab ta kamo hannunta sannan tadanyi murmushi tace "Nabila nagode."
Idanunta ne suka ciko amma fuskarta na kokarin bayyana murmushi tace "karki damu Aunty kedai kiyi kokari ki cigaba da zama cikin farinciki, shikedai ne abinda nake nema kuma na tabbatar Mama da tanada rai abinda zata nema kenan."
Zainab ce tai murmushi tace "sai kace kece babba." Nabila tai dariya tace "in na nuna miki na girma sai hankalinki yafi kwanciya."
Zainab ta jawota ta rungumeta tace "in wani abu ya faru ki kirani kinji?"
Nabila ta goge kwallarta tace "To Aunty." Zainab ta dagota tace "Dady fa? Yana nuna miki banbanci?" Kai ta girgiza tace "bansa a kaina ba bare na gani." Zainab tai dan ajiyar zuciya tace "in an kusa visiting kimin magana zanzo muku."
"Kin tabbatar? Kinsan zaku hadu da Dady da maman Nusaiba?" Wannan damuwarsu ce insun gani sa tafi, inata kin zuwa miki saboda banasan kisan meke faruwa amma tunda kinsani banga abinda zai hanani ganinki ba."
Nabila tai dariya tace "Shikenan zan kiraki."
Jakarta ta zuge ta dauko kudi, mika mata tai dubu goma tace ke biyar Nusaiba biyar, Nabila ta amsa tace "mungode." Zainab tace "in kara miki?"
Nabila tace "a'a abubuwa sun miki yawa, Aunty wai haka zaki cigaba da zama komai kece keyi?"
Murmushi tai tace "yana neman aiki, sannan banajin wani abin dan nayi komai, na tabbatar saboda hallarcin danamai bazai taba cin amana ta ba kamar wani wanda baisan hallacci ba."
Nabila ta sake dariya tace "dukda bansani ba nasan da Dady kike, wai dan Allah meya faru takamaimai."
Zainab ta mike tace " zan fada miki amma ba yanzu ba."
Nabila tadan turo baki tace "shikenan."
Dariya Zainab tai tace "borin ya motsa ne?
Nabila tai dariya itama tace "Aunty Allah ki dinga rufe kitchen dinki lamarin ciye ciyen goggo yayi yawa, ke kina can kina aiki danta na tsinanen bacci da jin dadi ita kuma sai ci da tsinanen kallo."
Zainab ta dan bige kanta kadan tace "wayace miki ana maganar manya haka? Kuma mamar Adam kamar mahaifiyata take."
Nabila tadan tabe baki.
Zainab ce ta mike ta bude drawer dinta, agamfa ta dako irindaya guda biyu da mayafinsu, tace gashi, sannan ta dauko jaka guda biyu suma iri daya.
Nabila tace "yaushe kika siya?" Dariya tadanyi tace "duk sanda na samu naje siyayya ina siyowa saboda nasan zakuzo."
Nabila cikin jin dadi tace mungode. Da gudu ta bude kofa tana kiran Nusaiba, man Nusaiba ta zo sukaga kaya suka hau murna.......
Adam kam tun bayan daya ajiyeta jikinsa a sanyaye ya dawo gida, shikansa baisan meya sameshi ba.
********
Gudu yake harya isa Danbatta, yana zuwa ya tada Abba a kwance akan gado a Er amma ba kowa a gunsa sai wata nurse, hankalin Khalid a tashe ya nemi number nan ya kira, Sabir ya dauka ya sanar dashi Zee ce ta bashi number din. Nan ya ce gashinan zuwa, Umma kuka kawai takeyi, Asiya ma haka, shikam Abba gaba daya da alama baisan waye a kanshi ba sosai, sai jini dake zuba a ta kasan inda akamai aikin, Sabir na zuwa ya sallamesu waje, nan ya fara aikinsa na ganin ya daidaita abinda ke faruwa.
Shikam Khalid na zaune kusa da Umma, Asiya na gefensa.
Salmanu ne yace 鈥渂ari naje na dawo Khalid.鈥�
Khalid ya mike yace nagode Salmanu. Nan ya wuce, Umma ce ta kalleshi tace 鈥渁 ina ka sanshi?鈥� Yace 鈥渨acce nakewa aiki ne taban numbersa ta sanshi ne.鈥�
Umma tace 鈥渁mma mungode mata da alama mutumiyar arziki ce, Allah ya biyata.鈥�
Khalid yai murmushi a kasan ransa yace 鈥渄a alama kam.鈥�
Sun dade kafin Dr Sabir ya fito, sanar dasu yai ba matsala sai dai ya samu barci abashi ya huta.鈥�
*********
Shigowa Adam yai Gogo ce kadai a falan tana ta cin cincin dinta, Adam ya kalleta ya zauna a kusa da ita, kallansa tai tace 鈥淪allamar kenan?鈥�
Yace 鈥渘ayi kina ta kallo ina zakiji.鈥� Harara ta maka mai tace 鈥渒ai ka sani, ka kaitan?鈥� Yace 鈥渆h sai ta gama zata kirani.鈥�
鈥淶adai ta gama yau ta kama gabanta ko?鈥�
鈥淓h gobe zata tafi.鈥� Tace 鈥渁h to dan ni bansan bikin nan ya tashi tana gidan nan.鈥� Meyasa? Tace 鈥渢ambaya kake? Wayasan me zata sata in ba kowa a gidan? Ita waccen tana aiki, ni ina hidimar biki kai kuma kana can kana uban bacci.鈥�
Dariya yai yace 鈥淕oggo kenan.鈥� Karar shigowar mota sukaji yace 鈥淶ainab ce?鈥� Tace 鈥渋ta tana daki da yara sai dai mai daukan nasu ne kila.鈥�
Adam ya leka yace 鈥渙h shine kuwa.鈥�
Nan ya wuce daki ya sanar dash.
Kayan suka nunamai ya tayasu murna sannan suka fita dan kara shiryawa. Zainab ta kalleshi, karasowa yai ya rungumeta tsam a jikinsa. Murmushi tai tace 鈥淗oney.鈥� Yace 鈥淚na sanki Honey harbansan yawan adadinsa ba, nagode da kasancewarki cikin rayuwata.鈥�
Murmushi tai ta dago ta sumbaceshi tace 鈥渘ima nagode da shigowarka cikin rayuwata.鈥�
Tare suka fito, Zainab tai kitchen, gani tai anyi abinci, murmushi tai ta deba ta zuba ma wanda zai kaisu sannan ta kira Nusaiba ta mikamai, itama ta zuba kadan taci.
Nan su Nabila sukai sallama, suka shiga mota.
Nabila tace 鈥淕oggo asha biki lafiya.鈥� Goggo tai dariya tace 鈥渢o, kuma kusha makafanta lfy.鈥�
Nan suka kara sallama suka tafi tare da fatan Allah ya saukesu lafiya.
Zainab ta bisu da kallo kafin tace 鈥淗oney ajiyeni a office.鈥� Yace to. Nan ta shiga suka tafi...........
*******AYUSHER MUHD********* [10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁 聽 聽聽 ......................
聽聽 *H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
Shafi na Sha Shida
A hayarsu ne yana tafe sundanyi shiru, kallanta yai yace "Yau Honey ba bacci sosai." Kallansa tai tace "yanzu na daina ai, waccen zuwan nasu kaga na damu?" Murmushi yai sannan yace " Dadyn fa? Haryanzu bakwa ko waya?" Yanayin fuskarta ne ya canza ta juya kanta zuwa jikin window. Dariya yai yace "sorry Honey bansan ya akai zancen nan ya fito daga bakina ba."
Bata tankamai ba har ya kara cewa "Honey ina Kwaro yaje ne?" Kallansa tai fuskarta haryanzu ba a sake ba tace "yaje wani guri ne." Ta rasa meyasa ta samu kanta dakin fadamai babanshi ne baida lafiya." Kafin yace wani abu tace "Sadiya fa?" Kallanta yai da sauri, tace "menene? Da matsala ne?" "A'a tana makaranta inta gama zata kirani." To kawai tace tai shiru, suna zuwa ta sauka ta shiga shiru yai yana kallanta harta shiga ciki.
Office din editing ta fara shiga ta duduba ta wuce office dinta. Shiru tai akan kujera tana kallan takardun da zata duba, waya ta dauka ta kira ciki, kace tazo. Nan ta ajiye wayar, Ramlah ce ta kwankwasa, Zainab ta bata izini ta shigo.
A tsorace ta gaisheta, Zainab ta kalleta tace "ina report din danace ki kawon?" Ramlatu tace "Am sorry yanzu nake karasa editing."
Wani wulakantacen kallo ta mata tace "yanzu kike me?"
Yawo ta hadiya ta kalleta tace "banida lafiya........" Bakida lafiya? A tsorace ta daga kai, Zainab ta dau wayarta ta kira director sannan tasa wayar a handsfree tace "Sir wannan wacce bansan ta yanda akai ta samu aiki anan ba." Daga can cikin rawar jiki yace "Ramlah?" Tace koma wa sunanta bai damenba sai dai kai da ka kawota inaso ka sanar da ita wannan shine dama na karshe da zan bata, idan harna kara bata aiki batamin zata taradda takardar kora a saman kafarta."
Director ya canza yanayin maganarss yace "Yahkuri Zainab, ni kaina bansan amfaninta ba, kiyi hakuri zan ja mata kunne." Bata bashi amsa ba ta kashe wayarta, kallanta ti tace "dafatan kinji?"
Ramlatu wace ranta ya gama baci da yanda Director ya wulakantata yasa ta saukar da kanta kasa, Zainab tace "banida damuwa da duk iskancin da zakiyi, am i your mother? Ko nice babanki? Banida hadi dake rayuwarki ce sai dai inzakiyi iskancinki kije kiyi a hotel amma nan gun aiki ne, idan baki kawon report din nan in an hour ba bansan me zai biyo baya ba, Get out." Ta nuna mata hanyar kofa, Ramlatu tana hawaye ta fita, tana fita ta shige toilet tasa kuka.
Zainab kam tana fita taja tsaki, ranta ya kara baci, wani abu ta hadiya na bakin ciki, maimakon ta duba takardun dake gabanta kwantar da kanta tai tare da rufe idanunta.
Mahaifiyarta ta hango kwance a kasan tiles, ga jini a malale ta kasanta, ita kadai a gida babu kowa, hawayene suka gangaro ta gefen idanunta wanda batabi ta kansu ba, hangota tai a rikice tana kuks ta rasa ta yanda zata taimaki Ummynta, kusa da ita kawai taje tana kuka tare da rike hannunta. Kuka take sosai, a hankali Ummy tace "Uwata ki dsu wayata ki kira Kamisu driver."
Kalan cikinta wanda taketa murna zata samu kani ko kanwa tai, a tsorace tace "Ummy! Ummy....." Jinin dake zuba ta kalla da sauri taja wani wahalalen numfashi sannan ta bude idanunta tana hakki.
Bakinta ta shiga motsawa tana kokarin maida kukan dake neman kwance mata ta shiga kokarin yi, da sauri ta jawo takardun dake gabanta ta fara dubawa.
Wayarta ta daga ta kira Sabir, daga can ya amsa yace "Zee!" Tace "ya? Ya kiraka?" Eh tun dazu harna gama na dawo office dina, hatsari yai ne?" I don't know. Yace "okay, amma meye hadinki dashi? Shine mijin naki?" Dan karamin tsaki tai tace "kaifa matsalata dakai tambayar abinda baishafeka ba, nagode." Bata jira mai zaice ba ta kashe wayarta.
Harkarta ta cigaba dayi, sai dai kasan ranta a ciki yake da tausayin mahaifiyarta da kuma tsanar mahaifinta.
鈥�************
Sai yamma lis sannan ta koma northwest ta naka ma Adam kira, yana zaune a majalisa ana hira yaji wayarsa tai kara, mikewa yai da sauri ya matsa sukasa mai dariya Yaran Hajiya ya amsa kira.
Adam yace "kingama?" "Eh yaya nagama." Okay bari na taho. Ya kashe wayar ya musu sallama, da sauri ya fada motarsa ya shiga y nufi makarantar. Tana bakin inda ya ajiyeta, yana yin parking ta shiga ta zauna, juya kan motar yai suka fara tafiya ba tare da kowa yayi magana ba, can sai da suka danyi nisa tace "Yaya nagode sosai." Ya kalleta yace "bakomai, kingama ko?"
Tai shiru tare da yin kasa dakai, kallanta ya sakeyi yace "baki gama ba?" Kai ta daga alamar eh tace "bangama ba yaya, kayi hakuri." Dariya yadanyi kadan yace "hakurin me? Ki zauna ki karasa a hankali, gobe zaki koma kenan?" Tace "gobe Friday kuma ko naje ba zan iya gamawa in bazan takurama ba inasan in bari sai Monday."
Adam ya kalleta, kasa tai dakai tace "yaya kayi hakuri." Da sauri yace "bakomai, kizauna sai monday din."
Shiru suka danyi kafin tace "Yaya kayi hakuri akwai lokutan da zakaga ina abubuwan da basu dace ba dan Allah inkaga haka kayi hakuri kamar yanda nacema rannan inada larura ne wlh wanda nikaina bana sanin abinda na aikata."
Kallan ta yai har yadansa tari yace "aljanu?"
Dariya tai jin yanda yai maganar, tace "a'a ni kaina bansan menene ba, saboda hakan ansha min duka."
Duka? Ya tambaya tare da dan kallanta. Tana wasa da hannunta tace "eh yaya, kayi hakuri." Idanunta ne suka ciciko jiyai tausayinta ya kara kamashi, yace "ya isa hakanan bansan yawan kukan nan."
Share hawayenta tai da sauri tace "nadaina, duk abinda bakaso bazan sake yi ba." Tai maganar tana girgiza. Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa yace "to." Wani dadine ya kamashi a kasan ransa, yau gashi shine yake bada umarni ya saba a komai sai dai shi a bashi.
******** Ganin jikin Abba ya dawo daidai yasa Khalid ya fito yai ma Umma sallama akan sai ya dawo, kallanta yai yace "zan tambaya in za'a iya biyana da wuri inyaso sai na baki saboda yin abinci ga yan kananan kudadanen da ake amfani dasu a asibitin."
Tace "To khaleed, sannu Allah ubangiji ya daukaka ka, ya baka damar da zaka taimakemu." Yace Ameen. Asiya ya kalla yace "in na dawo Umma zata koma gida dan haka kije gidansu Salmanu, kafin nan, ko kuma ni nace yazo ya zauna a dakina kafin na dawo."
Umma tace "yazo din yafi sauki sauki." Yace to, sai na dawo.
Fitowa yai ya dau hanya, bai tabajin dadin aikinsa ba irin yau, a da ya dauki aikin ne akan rashin abinyi, sai dai taimakon data mai yau tabbas yass ya kara girmamata a idansa, haushi ne yadan kamashi da ya tuns ba yanda zaiyi ya kama wannan mutumin.
Haka ya isa station din har lokacin fitowarta yai. Zainab na fitowa ta hango motarta, karasawa tai ta shiga tare da ajiye kayan dake hannunta.
Khalid ba tare da ya juyo ba ya dan kalleta ta madubi kadan, gaba daya yanayin damuwa ne karara a fuskarta, daurewa yai yace "Nagode sosai da sosai." Kallansa tai tadanyi murmushin yake tace "is okay."
Shiru yadanyi kafin yace "jikin nashi da sauki." I know, abinda tace kenan ba tare da dogon nazari ba. Khalid yace "kin sani?" Shiru tai cikin waskewa tace "tunda kaje asibiti i will assume that." Oh yace sannan ya tada motar, shiru tai ta zubawa window ido, yauce rana ta farko dayaga bata aiki a cikin mota, da alama an bata mata raine, ko mutumin nan ne? Abinda ya fado mai kenan, shiru yai yana tunanin yanda zaiyi ya tambayeta, daurewa yai yace "wannan ya sake kira?"
"Wa?" Daga yanayin tambayarta ya fahimci baisake ba, shikenan. Jin yace haka yasa ta fahimci yanayin da take, juyawa tai ta dau tab dinta tana dubawa duk da dai ba wani abu take ba amma batasan ya fahimci tana wani halin.
Yana sauketa ta wuce ciki, Goggo na zaune a falo tana waya da alama wannan bikin daya ishemu shi take magana akai, wanda mu kanmu mun kosa asabar tayi wato jibi a gama bikin nan mu huta.
Zainab bata tsaya a falo ba wucewa kawai ciki tai, Goggo ta bita da kallo, Sadiya dake daki a kwance ma batasan ta dawo ba.
Adam ta gani kishingide yana kallo a laptop dinta, yana ganinta ya taso da sauri yace "Honeyyy...." Ya bude hannayensa alamar rungumeta, hannun tadan ture ta wuce toilet, tana fitowa ta ganshi a inda ta barshi ya shagwabe yace "Honeyyyy...." ya kara bude hannu.
Murmushi tai sannan ta shiga jikinsa ya rungumeta, dagowa tai ta kalleshi sannan ta canza kayanta, yace "Honney su Nabila sun isa?" Ta kalleshi tace a'a kawai, fitowa falo tai ta nufi kitchen.