A gidana complete novel - Chapter 19
A gidana complete novel Chapter 19: A gidana complete novel Chapter 19. Kallansa tai tace "hukuncinsa korar wata shida." Yace "wanda kuma ya ke da alaka…
4,491 words
Kallansa tai tace "hukuncinsa korar wata shida." Yace "wanda kuma ya ke da alaka wace bata aure ba tsakanin sa da dan uwan aikinsa fa? Alaka wacce take dauke da ayar tambaya mai karfi fa?"
Kai tsaye tace "korar sa za'ai"
Cikin jinjina kai da gamsuwa ya kalleta batare da ya dauke idanunsa akanta ba yace "menene tsakaninku da saban ma'aikacin da kika dauka Khalid?"
Kallansa tai cikin rashin fahimta tace "wani Khalid din?"
Director Kabir yai wani murmushin jin dadi yana tuno takardar da aka ajiye kai akan kai amfani da Khalid in taki saduda, tabbas akwai abu tsakaninsu, yayi kata driver, a gidansu ma ta xauna da auranta ya mutu sannan yanxu kusan kullum tare suke tafiya."
Menene tsakaninku?
Tace "meye tsakanin mu kuwa?"
Kallansu yai yace "ba abu a tsakaninku ku kika zauna a gidansu?"
Kallansa tai da sauri.
Kallanta ya sakeyi cikin jin dadi yace "Binciken mu ya nuna karatun degree na Maths yai ba yanda za'ai ya rubuta amsoshi masu zafi akan karatun da bai da alaka dashi, in har ba bashi akai ba. Abu na biyu yaran nan kin nuna baki da alaka dashi kuma mutane uku na tambaya sun nuna kin sanshi, sai a lokacin ma na tuna abinda kikamin akan nayi rejecting din takardarsa ta neman aiki."
Me tama akanshi?
Murmushi yai yace "nan tazo tacimin mutunci akan nacuceshi taya zan hanashi aiki bayan yaci? Har takardar ajiye aikinta ta rubutamun saboda shi."
Kallansa kawai take gaba daya ma tama rasa me ma zatace mai saboda gaba daya bata taba kawo jin abu makamancun haka bama, bata kawo abin nasu har yakai haka ba.
Kabir yace "mu kirashi mu tambayeshi alakarku da sanda kika turamai tambayoyin jarabawar? In har sharri muke miki?"
Kasa magana tai kawai sai kallanshi da take.
Can ya dauke kansa daga kanta yce "ance ma akanshi kika rabu da mijinki."
Idanunta na kansa ita kadai tasan abinda take ji a cikin ranta. kallansa tai kafin ta saki wani murmushi, kallanta yai yace "in har ba abu tsakaninku kina san wanke laifinki yanzu a kirashi ki koreshi daga aiki da kanki, wannan zai nuna mana tabbas ba abu a tsakaninku."
Farcenta kawai take karzawa yanzu kam ta ma dauke ido daga kansa, kanta na jikin desk din dake gabanta.
Yanzu ne CEO din su yai gyaran murya sannan yace "Zainab ke muke sauraro."
Dagowa tai ta kalleshi idanunta sunyi jaaa, tunowa take da sanda Khalid ya samu aiki Umma ta kirata cikin doki tana fada mata, cikin xuciyarta tace "Ya Allah!"
Samun kanta tai dayin murmushi tace "Duk da nasan kuna san korata ban taba tunanin zaku kaskantar da kanku ku je wannan matakin ba, duk cikinku na san yanda kuke jin haushin ni kadai ce mace a cikinku, na san ynda kuke jin haushin komai ta hanuna akeyi."
Kallan Kabir tai tace "Weldone da kokari, nasan duk wannan abinda kake dan na baka plan din danai wata uku ina shiryawa ne, ba sai kunje wannan matakin ma lalata min mutunci na da shi kansa ba, i will live."
Kallanta sukai da sauri, ta hadiyi wani abu tace "sai dai."
Ta dago ta kallesu daya bayan daya tace "Inaso kusan wani abu, na muku alkawari a wannan indai har inada rai da lafiya a daidai wannan lokacin nan da shekara biyu sai kunyi zaman meeting na neman mafitar yanda zaku gyara matsalar dake faruwa a tv station din nan, na muku alkawari nan da shekara biyu in dai ina da rai inda zan koma aiki sai ya wuce wannan gidan naku daraja da daukaka, zan gani in hakkina da kuka ci zai barku, ko baku ceba banaji zan iya cigaba da aiki daku."
Mikewa tsaye tai tace "Zaman da mukai a wannan wuri yasa na fara tausayin kaina, mijin dana rabu dashi da mahaifina, na yanda na sadaukar da komai akanku na sadaukar da duk wani lokaci na ina faman ganin na daukaka wannan guri, abinci wannan sai nayi da gaske nake ci, sai na tashi tsakar dare na hau aiki duk saboda neman ci gaban mu, bansan sakkayar dazan samu ba kenan."
Director Kabir ne yace "ke mutane nawa kika kora ba tare da hakkinsu ya kamaki ba?"
Kallansa tai ranta a matukar bace tace "duk wadanda na kora fadamin wanda bai aikata babban laifi ba? Sannan cire gurbatatu danai ba shine yasa muka samu ci gaba ba?"
Yace "Kema ai babban laifin kikai."
Kai ta daga cikin takaici tace "hakane ashe babban laifi nai."
Sallama ta musu ta juya, gaba daya shiru sukai, har taje jikin kofa ta dawo tadau maker mai makon tai rubutu a whiteboard din dake meeting room din ta wuce jikin kofa ta rubuta musu resignation letter ta cila maker din ta fita.
Office dinta ta wuce gaba daya ji take kamar zata fadi saboda jirin da takeji.
Hannunta rawa yakeyi sam ta kasa bude kofar, makulin ma ta kasa sashi a jikin kofar.
Khalid daya taho dan ganin ko sun gama ne ya karaso, ganin abinda ke faruwa yasa ya karasa da sauri ya amshi key din.
Kallansa tai idanunta basa gani sosai, yana budewa ta shiga ciki, bayanta yabi da sauri shima yace "Are you okay?"
Juyowa tai ta kalleshi sannan ta kara rufe ido ta bude, murmushi ta kakaro tace "yeah, can you help me?"
Da me?
I need to pack.
Cikin rashin fahimta yace "pack?"
Kai ta daga tace "in an tashi please."
Shiru yai tare da zuba mata ido, tabbas akwai babban abinda ke faruwa da ita kuma tana neman kadaicewa, hakan yasa ya sauke jakarsa ya ciro flask din ya ajiye yace "inji Umma, in an tashi na dawo."
Juyawa yai har yaje kofa ya juyo ya kalleta, tana tsaye haryanzu.
Tana ji ya rufe kofa alamar ya fita ta zube a kasa, gaba daya jikinta ne ya shiga karkarwa, zuciyarta na wani irin kuna.
Wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mata, kawai ta fashe da kuka.
Tayi koka har ta gaji.
****** Khalid kam sam ya kasa maida hankali akan aiki, tabbas akwai abinda ke faruwa, menene?
Ramatu ce ta shigo tana dariya, kallan Su tai tace "Hajiyar gadara dai an ajiye aiki."
Da sauri Khalid ya kalleta, yace "aiki?"
Yanda damuwarsa ta fito karara ne yasa Ramatu tace "eh yanzu, ahhh masamu hutu haba kullum cikin takura"
Idanunsa ne suka sauka akan Afreey wacce yaga tana murmushi ta kasa, Nazifi ne yace "ban gane ba? Waya isa ya sata ta ajiye aikinta?"
Ramatu tace "ina na sani?"
Shiru Khalid yai yana tunanin meke faruwa? Adam Ne? Raziyya ce? Ba shiri ya hau bincike a facebook da instagram sai dai baiga wani sabon posting daya shafeta ba.
Har aka tashi zuciyarsa ta kasa nutsuwa.
******
Jiki a sanyaye Adam ya shigo gida, zama yai a falo akan yar katifarsu yai shiru ya baxa uban tagumi.
Goggo data fito daga bandaki ne ta kalleshi tace "kai kuma fa?"
Kallanta yai ya sauke wata ajiyar zuciya.
Zama tai tare da jawo mai tana shafawa tace "kai fa kayan haushinka yama yawa, meye hakan?"
Kallanta yai yace "Goggo yanzu Zainab ta tafi."
Da sauri tace "Zainab?"
Kai ya daga alamar eh yace " Goggo yaune karo na farko dana taba ji Zainab ta rokeni abu."
Kallanshi tai ta matso tace "komawa takesan yi?"
Kai ya girgiza yace "Rokana tai na kyaleta haka nan." Hawaye ne ya zubomai ya kalli Goggo yace " Goggo ya zanyi."
Kallansa tai ta koma dabas ta zauna zuciyarta na kuna ta kasa magana itama.
Can tace “ka hakura kenan?” Ido ta kuramai tace “ko ukun kai da gaske?”
Dan kai ya kauda yace “ko ukun nai in na dage biyu nai ai ba yanda za’ai.”
Cikin takaici takai mai bugu, tace “kai dai wlh kaji asara, da alama ka fara hauka, ni anya ma kudin nan da aka baka a takarda na gaske ne?”
Kallanta yai yace “kema kina tunani haka ko?”
Tace “to akan me za’a baka uban kudi ba tare da kayi wani abu ba?”
Yace “nima abinda ke ban mamaki kenan, sannan Afreey fa dama can ba wai kyauta gareta ba.”
Afreey? Meye hakan suna kamar na aljanu?
Dariya yasa yace “ke ina kikasan sunan gayu?” Tsaki tai tace duk kai kaja mana da kun haihu da Zainab ta isa ta koremu?
Haushine ya kamashi, tace ni tsinaniyar magen ma har yau banganta ba, ta ja mana bala’i tai gaba.
******
Kayanta kawai take ta hadawa, wayarta dake kara ta jawo ganin sunan Dady yasa ta dauka da sauri.
Dady bayan sun gaisa yace "ashe basu dade da tahowa ba?"
Tace "eh wlh ni suka tsaya jira kuma na shiga meeting."
Yace "kinje gidan Auntyn naki?"
Tace "na kirata a waya tace zata samomin wace zata zauna, haryanzu batace komai ba."
Shiru yai sannan yace " komai dai lafiya ko?"
Hawaye ne suka zubo mata tace "Dady na ajiye aikina yanzu."
Da sauri y mike tsaye yace "meya faru?"
Share kwallar ta tai tace "wani gun zai nema nan gaba daya abin nasu ya baci."
Shiru yai dan yasan tabbas da wani abu, can yace "ki dawo gida, dan dama hankalina ba'a kwance yake da barinki ke kadai ba, in har ba aure kikai ba bazan bari ki cigaba da zama ke kadai ba, in ba so kike a fara miki fassara akan zaman kanki kike ba."
Aure?
Yace "eh shi kadai ne zai sa na barki ki cigaba da zama a kano, tunda har kika ajiye aikinki to ki shirya wani satin zanzo daukanki."
Dady amma......
Kashe wayar sa yai cikin mamaki tabi wayar da kalli, dady ne kuwa? Taya Dadynta zai mata fada haka? Ko ta bakinta bai nemi ji ba?
Aure? Tafiya? Ta ya zata koma bayan yanzu ne take da dalilin zama a kano?
Dady kam yana kashe wayar yai shiru, shikansa mamaki yake yanda yai maganar sai dai yasan dole ne yai haka in ba haka ba baxata taba yadda ta dawo ba shi kuma gaskiya bayasan barinta sam a can ita kadai.
Khalid ne yai knocking a hankali ya shigo.
Kallanta yai, itama kallansa tai.
Shiru yai baisan me zaice mata ba, itama shiru tai dan kanta a cike yake da tunani.
Duk ta hada kayan hakan yasa ta mike tadau box daya matsowa yai ya amsa daga hannunta ya kara dayan akai.
Kallanta yai yace “kofar.”
Karasowa tai ta bude mai kofar, ya fita.
Jakarta ta dauko da flask din Umma. Kallan staffs din tai duk sun fito kasa suna jiranta.
Wasu harda hawaye wasu kuwa tasan na karya ne, kallan Tv Station din tai tace “in Allah ya yarda nan da shekara biyu sai kun nemi yafiyar abinda kuka min.”
Haka ta shiga musu sallama kafin ta wuce jikin motarta.
******* Ayusher🏌🏻♀ [ yusher🏌🏻♀
🍀A GIDANA🍀 .........................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
#OneLove❣
_Your special page is here my dear fans, much love🥰🥰🥰_
{46}
Bala ne ya fito mai da ledar, amsa yai jiki a sanyaye ya juya yabar gidan.
Wayarsa dake kara tun dazu ya zaro 20 missed calls ya gani, guda takwas daga Afreey ne ragowar kuma Nazifi ne. Number Nazifi ya kira, ringing daya ya dauka cikin rada yace "Khalid kana ina?"
Bai jira yace wani abuba yace "kai maza kazo.”
Kashe wayar yai sannan ya shiga adaidaita ya karasa. Yana shiga yaga ba kowa program room ya nufa anan yagansu a tsaye sun nutsu ana wani program.
Kallan inda ake program din yai, su uku ne agun ciki harda Afreey.
Muryar Nazifi yaji yace "Khalid biyoni."
Bayansa yabi suka shiga editing room, ransa a bace yace "ina kaje?"
Shiru Khalid yai kafin yace "Am sorry."
Nazifi yace "kasan fadan da akamin akanka? Ance bana kula daku? Wannan abinda kai ka jama kanka dan dama na sa sunanka akan masu dauko rahoto yaune amma abinda kai yasa na cirw sunanka nasa wani, dan haka wannan satin duk kayishi a editing room din nan."
Ya juya yai waje.
Juyowa yai ya kallesu sannan ya gaishesu.
Nan ya matsa ya zauna tare da amsar aikinsa.
Afreey kam gaba daya hankalinta nakan Khalid, ana gama shirin ta sauko da sauri ta nufi editing room inda Nazifi yace mata yana can.
Ko kallanta baiyi ba har ta gama wayancewarta na wai tazo ganin yanda ake ne. Kuda da Khalid taje a hankali tace “Khalid please inasan muyi magana.”
Kallanta yai, sannan yace “kijira lunch time nima inasan magana dake.”
Wani sansanyan Murmushi ta saki tace “nagode Khalid.” Fita tai cikin wani irin yanayi wanda ita kadai tasan yanda take ji.
Ai kam ana tashi lunch ta kirashi a waya, ringing uku ya daga tace “Khalid!”
“Mu hadu a waje.” Abinda yace kenan ya kashe wayar. Sai dai abinda yaban mamaki wai gani nai hakan yasata jin dadi.
Mikewa tai da sauri ta fita.
Tana tsaye ta zubawa kofar gate dinsu ido tana jiran ganin Khalid, sai murmushi take ita kadai.
Minti goma da tsayuwarta ta hangoshi, cikin wani yanayi ta zubamai ido tana ji kamar ta ruga a guje ta rungumeshi, da alama burinta na shekaru dayawa ya kuda cika.
Har ya iso idanunta na kansa, kallanta yai da sauri ta matso kusa dashi ta “Khalid!”
Cikin idanunta ya kalla yace “Tambaya nake san miki.”
Da sauri ta daga kai alamar tanaji, kallanta yai yace “Me kikeso game dani?”
Tace “Khalid kaima ka sani, auranka kawai nake san yi, ka xama nawa ni kadai.”
Murmushi yai yace “hakane, na tabbatar dama amsar kenan, to menene abu na farko da zai kaimu ga auran da kikeso?”
Idanunta ta zaro cikin wani yanayi, tace “Khalid?”
Kallanta yai yace “me? Kin kasa magana ?”
Shiru tai tana kallansa zuciyarsa na bugawa da karfi saboda tsananin san da take mai.
Kallanta yai yace “ya akai?”
Hawaye ne ya gangaro daga idanunta tace “Khalid bansan wani irin so nake maka ba, ji nake zan iya halaka duk wanda ya shiga tsakaninmu.”
Yace “ai ba sai kin fada ba naga hakan sau biyu kenan, kina hauka da sunan so.”
Kallansa tai tace “hauka?”
“Badai ke a naki haukar soyayya kike min ba?”
Yanayin fuskarta ne ya canza tace “me kake nufi ?”
Yace “inasan inga inkin aureni me zakiyi dani, na farko ko da da kankanin lokaci ban taba sanki ba, na biyu har a wannan lokacin ina mamakin yanda akai taimako ya koma haka, na taimaka miki wanda da alama shi ya maidake haka, na uku ina tunanin me zanyi wanda zan kuntata miki har abada kamar yanda kika kuntatamin da mutane akan wani shirme da kike neman kiranshi da sunan so.”
Gaba daya yanayinta ne ya canza idanunta suka kada sukai jaaa, bakinta na rawa tace “Me ne?”
Yace “me? Kinasan na cigaba?”
Bakinta na rawa tace “Khalid?”
Wani banzan murmushi yai yace “baki taba tunanin me yasa ban taba nuna bacin rai akan abinda kike ba? Ko kinfiso na fito na sanar dake haukar da kike ta isa haka nan? Sannan sai kiyi abu ki sanar dani, wato me zan iya?”
Hawaye ne suka shiga zubo mata idanunta na kansa, tama kasa magana, Khalid ya cigaba “ Badai zaki cigaba da kiran abinda kike a sunan so ba?”
Tace “Khalid kasan yanda nake sa........”
A kufule yace “so? Are you kidding me? Am i your toy? Taya ma zaki nemi bata min suna sannan kice kina so na? Abinda kike tunanin kin ma Zainab ba ita kika ma ba ni kikawa.”
Da wani ido kike san na cigaba da kallan mutane? Sannan kice so? A skul da kika ma Saudah sharri akan tai satar answer da wa kika hada? Cewa kikai ni na bata paper din data shiga dashi, dalilin hakan kinsan tashin hankalin dana shiga a wannan lokacin? Kinsan yanzu zuciya ta tashin hankalin da take ciki? Sannan ki kirashi da so?
Hawayenta ta share tace “amma kasan duk dan ka dawo gareni nai.”
In dawo gareki? Ko a mafarki bana fatan hada hanya dake karshe kenan
Bakinta na rawa tace “to in har bansameka ba kuwa duk duniya sai dai ka zauna kai kadai ba wanda ya isa ya sameka.”
Dariya yai yace “ohhhh is that what you hate the most? Yanzu kinsanar dani abinda ya kamata inyi, nagode da shawara sai na kawo miki IV.” Har ya fara taku biyu ya juyo yace “Ahhhh ko na baki IV din ba gayyatarki nake ba.”
Ya juya ransa a matukar bace.
Zubewa tai tsuguna a gun, bata ma duba yanayin kan hanyar da take ba balle ta duba mutanen dake wucewa.
Kuka kawai take tana tuno kalmar hauka da ya jefeta dashi, tunowa tai farkon haduwarsu randa ya taimaketa randa kuma ta fara sanshi.
Kasancewar ita yar masu shi ce yasa sam banda gadara ba abinda take a makaranta, duk saurayin daya zo mata da sunan so sai ta caba mai maganar da bazai taba mantawa ba, ko juice ne a hannunta sai ta watsa wa mutum, wannan dalili ne yasa yan islan skul din sukai meeting akanta akan zasu kamota su lalatata saga uban abinda take wa wulakanci, sannan dukansu su biyar sai sunyi amfani da ita.
Haka suka hada baki da friend dinta wacce ita kanta haushinta takeji suka sa ta jawota inda suka tsara haduwa can karshen inda ba mutane sai daji daji.
Afreey tunda suke tafiya takema Amrah kawarta magana akan ita haryanzu basu zo inda zasu ba.
Tana nema juyawa tani an cafko ta, a zabure ta kalleshi, gani tai duk mazan sun fito suna wata dariya, a tsorace ta fara kokarin kwace hannunta sai dai hannu yasa ya fizgeta can bayan wani gini da ake yinsa sukai da ita.
Bakinta suka toshe ba damar yin kara, sai ture ture take. Khalid dake zaune a kangon yana karatu ne yaji suna dariyar mugunta tare da jin dadi.
Daya daga cikinsu ne ya wanka mata mari yace “ni kika zubawa juice a jikina ko? Yau sai na fanshe bakin cikin danasha.
Ya fada tara da jan rigarta daga sama sai data yage.
Kuka kawai take tana tuturesu, jin magana sukai ta bayansu, Khalid na kallansu yana waya “eh suna nan inda nake.”
Okay sir.
Kallan su yai tare da sa wayar a handsfree yace “Eh sir nasa.” Muryar Discipline master dinsu sukaji yace “dan******kun zo office dina ko sai na kira iyayenku? Duk naji muryarku kar ku kuskura wlh nazo nan dan duk sai na koreku.”
Idanu suka zaro ai a tsorace suka fice daga gun.
Kallanta Khalid yai da sauri ya juya baya ganin rigarta a yage.
Yace “ki tsaya bari na samo abu ki rufe jikinki.”
Har zai fita tace “dan Allah karka tafi, tsoro nake.”
Bai juyo ba ya wuce ciki, sallayarsa ya dauko ya mika mata ta baya, amsa tai tace “nagode.”
Haka ta rufa sallayar suka fito tare, hawayenta kawai take sharewa.
Idanunta ta runtse tana hawaye tunowa da wannan lamari datai.
Yana san ce mata bai taba santa ba? Kome?
******
Bank din Goggo ta kalla cikin jin dadi tace “kaga sai mu samu mu bude wani abu kasuwanci ko tabir na shayi zaka bude?”
Shayi? Wa? Ni? Ya fada yana kallanta.
Tace “a’a mantawa nai nice zan zauna a gun.” Tai maganar cikin gatse.
Dariya yai yace “Goggo tawa, wlh kuma kyau zakiyi.”
Bakin ciki ne ma ya hanata tanka mai, suna shiga suka hau layi duk su biyun.
Har an kusa zuwa kansu Adam yaji an dafashi ta baya.
A tsorace ya juyo, idanunsa ne suka fito sosai yace “Sadiya?”
Razy ta karkatar dakai tace “Adam”
Goggo da sauri ta juyo jin yace “Sadiya.”
Idanu ta zaro a zuciye tasa hannu ta cakumo ta, Jamil ne ya matso da sauri yace “meye hakan?”
Goggo ranta a mugun bace tace “tsinaniyar wanda iyayenta suka tsine mata ai ban taba sa ran zan ganki ba yar banza wlh yau sai kinci ubanki.”
Staffs din bank din ne suka kallesh, Security ne ya matso da sauri yace “Baba meye hakan kike mana anan? In rigima zakuyi ki bari sai kun fita can.
Cashier ne ya kalli Goggo wacce aka zo kanta, Goggo hannunta na jikin Razy ta jata zuwa can.
Shikam Adam gaba daya ya saki baki yana kallan ikon Allah.
Goggo na mike cheque Raziya ta kalleta tace “Yanzu Goggo sai da kika sato cheque din nan?”
Da sauri Goggo ta kalleta tace “an sata din in naki ne.”
Kallan Razy yai yace “sata?”
Goggo ce ya kalleta tace “agun ubanki na sata?”
Adam ne ya matso yace “namu ne wlh, bamu akai.”
Fuskarsa dauke da Zargi cashier din yace “baku akai? Wa?”
Yace “Safiyya nata ne, kawatace a skul.”
Razy ce tai murmushi tace “ta ina kawa zata ba......” Hankadata da Goggo tai ne yasata yin shiru, Security ne ya taso da sauri ya kallesu.
Cikin xargi yace “ku kira number.”
Nan Security yai gefe dasu, Goggo takaici kamar zatai ihu, Raziyy ta kallesu tace “ni dai na wuce, shaida na bada kuma na isar.”
Goggo a kufule tace “wannan ‘ya Allah ya kwashe miki albarka, kin kashe mai aure dan abin arzikin ma bazaki barmu mu dauka hankalinmu a kwance ba?”
Razy ta tabe baki a ranta tace na barku lafiya.
Adam ta kalla tace “bata dauka ba?”
Kai ya daga sannan ya sake kira.
Afreey dake tsugun ne ta gaji da kiran waya a zuciye ta dau wayar, Adam da sauri yace “Afreey ko zaki samu zuwa nan bank din Zenith? Na kan titi hotoro? “Inzo inyi me?”
Yace “cheque din da kika bamu ne ake zargin sata mukai.”
Kashe wayarta tai dan haushi ma ta kashe wayar gaba daya.
Hello Hello Adam ya shiga fada, Security din ya kalleshi yace “ya?”
Adam yace ta kashe amma wlh ita ta bamu Duk barayi abinda suke cewa kenen, ku fita ku baku guri.”
Da sauri Adam yace “to baku cheque din.”
Yace “a baku? Kun fita ko sai mun kira police? Ke kuma Baba ki dinga sanin inda ake kawo miki kudi dan gudun sata”
Haka ya korosu daga bank din.
Goggo ji take kamar ta kurma ihu, tana tafiys takalminta ya gurdeta ta kusa faduwa, rai a bace ta cilar da takalmin tai gaba.
Adam na binta a baya, duk taku daya tsinewa Kuliyar nan take.
*********
Dady ne a zaune a falo shi da Zainab, Basma ta ajiye tiren abinci sannan ta fita dan ta fahimci magana zasuyi.
Zainab ce ta kalleshi tace “Dady bakada lafiya ne?”
Kallanta yai yace “meke faruwa? Nasan haka kawai bazaki ajiye aikin nan ba.”
Shiru tai yace “Zainab.”
Nan ta sanar dashi kadan daga cikin abinda ya faru, ransa yayi matukar baci yace “tun zamanki iddah naso yanke wani hukunci amma sai na fasa, naso na bude miki naki gidan tv din na kanki, wannan ne kadai zai sa ki samu nutsuwa sannan shine zaisa ki rage yawan aikin da kikeyi, bazan hanaki aiki ba dan ni kaina ina alfahari da aikinki sai dai aikin yayi yawa.”
Zainab tace “nawa?”
Dady ya daga kai yace “haka nake fata sai dai....” Yai shiru. Tace “Dady”
Kallanta yai yace “baxan iya barinki ki fara aikin ba sai kinyi aure.”
Idanu ta zaro tace “aure kuma?”
Yace “sosai, duk inda kika ga mace to tana bukatar kulawar namiji, tun daga sanda aka haifeta Allah yaba mahaifinta hakkin kula da ita har sai tayi aure, bayan tayi aure Allah yaba mijinta hakkin kula da ita, sannan idan ta tsufa hakkin kula da ita ya koma kan d’anta, haka Allah yai mace a karkashin namiji wannan dalili ne yasa in har kinasan na bude miki to lalai ki kawon miji na aura miki, in kuma ba haka ba sai dai ki cigaba da zama a gida ko aiki bazaki kara nema ba.”
Kallansa tai da sauri tace “Dady!”
Yace “akwai d’an abokina wanda matarsa ta dasu, in har kina ganin ba matsala zan turoshi ku gaisa.”
Shiru tai tama rasa tunanin me zatai.
Dady yace “in har kinasan Tv Station tare da daukan fansan abinda aka miki to ki kawon miji, ni kuma na miki alkawarin baki gudun masa ta ko mai dan ganin kin cin ma nasararki.”
Yana kaiwa nan ya jawo abinci ya zuba.
Shiru tai gaba daya kanta ya kulle, miji? Ina ta ganshi? Gashi bataji zata iya sati a zaune ba aiki? Balle taita zama a haka????
********
Hannunsa rike da wayarsa sai juyata yakeyi, number Zainab ce akan alan wayar.
In na kira ince me?
Ajiyar zuciya yai tare da jan bargo.....
****** Ayusher🏌🏻♀
🍀A GIDANA🍀 .........................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
#OneLove❣
Obsession is the single most wasteful human activity, because with an obsession you keep coming back and back and back to the same question and never get an answer.
{47}
Afreey na shiga gun aiki a bakin kofar Kabir ta tsaya, daren jiya ta gama yanke shawarar abinda zatai da hukuncin da zata dauka.
A hankali tai knocking, Secretary dinsa ne ya bata izini bayan ta shigo ta kalleshi tace "gun Director nazo."
Kallanta yai sannan ya mike tare da sanar dashi. Director Kabir dake zaune yana duba plans din da Zainab ta bari cikin jin dade yake ware wanda yake ganin za'a fara. Afreey ce ta shiga bayan an mata izini, yna zaune yana duba takardun ya amsa sallamarta.
Harta zauna bai dago ba sai can ya dago ya kalleta yace "oh kece?"
Kai ta daga alamar eh sannan tace "Nice na ajiye ma takardar nan ma.”
Takarda? Ya kalleta kafin yanayinsa ya canza zuwa mamaki yace "kece?"
Kai ta daga tana murmushi tace "nasan in na fada sai ka fi fahimtata."
Fuskarsa haryanzu dauke da mamaki yace "amma ya akai kikasan haka? Sannan haryaushe kikazo da abu zai hadaki da Zainab?shiyasa ban kawoki a raina ba sam.”
Bata bashi wannan amsar ba tace "Zansa Abbina yadau nauyin shiri guda uku."
Baki ya bude cikin mamaki yace "uku?"
Kai ta daga alamar eh sannan tace "zansashi yai signing din 3yrs contract."
Cikin tsananin jin dadi yce "Safiyah! Da gaske?"
"In yau kake so ai signing din zan sanarmai kuyi a yau din nan."
Gaba daya wani irin zumudin jin dadi ne ya kama Kabir, tace "amma da sharadi."
Sharadi? Koma meye fada yanzun nan zan miki menene shi?
"Khalid!” Tadan numfasa sannan tace “shi nake so ka kora."
Khalid? Waye.......Khalid? Ya sake tambaya.
Tace "eh"
Kallanta yai cikin mamaki yace "a wani hujjar zan koreshi kenan?”
Tace "in anyi amfani dashi an kori Zainab shima za'a iya amfani da ita a koreshi."
Kallanta yi yace "Am sorry sai dai hujjar da kika fada ba naji zatai tassiri."
Cikin mamaki ta kalleshi, murmushi yai yace "Badai kina tunanin shine dalilin dayasa Zainab tabar nan ba?"
Tace "ba shi bane?"
Dariya yasa yana kallanta kafin yace " kin tabbatar zaki sa yadau nauyin shiri uku?"
Kai tsaye ta dauko wayarta ta dannawa babanta kira.
Ringing biyu ya dauka yace "Baby!"
Tace "Abbi taimako mukeso a gun aikin mu, can you please help us?"