Kenza eBookz

A gidana complete novel - Chapter 18

A gidana complete novel - Chapter 18

A gidana complete novel Chapter 18: A gidana complete novel Chapter 18. Kallansa tai tana murmushi tace “me kake a wannan unguwar?”

4,494 words

Kallansa tai tana murmushi tace “me kake a wannan unguwar?”

Dariya yai yace “me nake kuwa inba zama ba?”

Baki ta tabe tace “Shekaru dayawa.”

Juyowa yai ya kalleta gaba daya yce “Afreey yaushe rabo? Ban taba tunanin zan kara ganinki ba.”

Bai jira tace komai ba yace “Khalid fa? Kin sake ganinshi.”

Kallansa tai tace “me kake tunani?”

Dariya ya saka sosai yace “ai yasin kin ganshi, wai haryanzu dai? Na d’auka ai an wuce gun.”

Murmushi tai tace “wuce gun? Tadan sauke ajiyar zuciya tace “Ahhhh bansan ya zanyi na wuce gun nan ba.”

Dariya ya sakeyi yace “ya akai kika san inda naka?”

Juyowa tai ta zubamai ido, da sauri yace “yahkuri bansan wannan kallan kinsani.”

Murmushi ta sake sannan tace “ina matarka?”

Matata? Kinsan Zainab ne?

Kai ta daga mai alamar eh sannan tace “kun rabu ne gaba daya?”

Shiru yai yana kallanta, tace “taimakonka zanyi”

Taimako?taya?

Tace “ Taimakonka zan ta dawo gareka.”

Zabura yai da sauri yace “taya?”

Kun rabu gaba daya? Uku kai?

Da sauri yace “a’a” Tace “then?” Shiru yai yana tuna uku yai, amma ya zaiyi? Shidai wlh auransa yake so.”

Kallanta yai yace “biyu ne, amma taya zaki taimaken.”

Shiru tai tana kallansa tace “Zainab tasan Khalid ne?”

Dariya yasa nan ya sanar mata ai shi yai recommending dinsa ta daukeshi driver, yana dariya yace “na dade rabona da Khalid ko sanda naje gidansu gun Zainab ban sameshi ba.”

Idanunta zaro tace “bangane ba? Gidansu?”

Dariya yai yace “to uwar kishi taimakonta yai a ranar, Zainab na sona haryanzu ni nasani, bazasu taba jituea da Khalid ba kinsan halayensa ita kuma bazata dauka ba.”

A ranta tace love bai maida ta ba dai. A fili tace “ meya rabaku?”

Kallanta yai sannan yace “bazan iya fad’a ba.”

Tace “bai damen ba koma menene, sai dai in har kana san ka dawo da ita sai dai ka d’aura mata laifi ka samu abu kace ita tai maka wannan ne zaisa a fara tausayinka ita kuma mutane zasu fara zagin halayenta, balle dama can mutane dayawa basan halayenta suke ba, kaga hakan zaisa tai tunanin koma maka, dan ta kare aikinta.”

Shiru yai yana nazari kafin yace “ni ba abinda tamin, me zai sa ince tamin?”

“Bakasan ta dawo ma kenan?”

Da sauri yace “ina so mana, sai dai Zainab ina ganin ko za’a kasheta bazata......” shiru yai bai karasa ba.

Kallansa tai tace “To mai zai hana ka fito cikin hira ka zubar da hawaye kana neman ta yafema ku maida auranku? Wannan zaisa mutane tausaya ma kaga za’a fara zaginta in akaga taki maida auranta, wasu zasu fara aibata zaman da take ita kadai wannan zai sa ta dawo ma, na tabbatar yanda takesan aikinta bazataso wani abu yasa ta rasa komai ba.”

Shiru yai yana kallanta yace “Taya zan so a zagi Zainab?”

Fuska ta hade tace “tunda bakasan a zageka sai ka hakura da ita.”

Da sauri yace “wannan ne bazan iya ba”

Enveloped ta mikamai ya amsa tare da budewa, check ne na dubu d’ari, idanu ya zaro cikin tsananin mamaki ya kalleta yace “na meye?”

Tace “Taimakon ka nai sai kaima kai kokarin taimakon kanka, nima duk sanda na nemi taimakonka akan Khalid you have to help me.”

Shiru yai kafin yace “shikenan an gama, nagode sosai Afreey nagode nagode.

Yanda yake mata godiya ne yasa tai shiru tana kalansa, dubu daya ta mika mai tace “ka hau mota.” Amsa yai ya fito taja motarta ta tafi, baki ya sake yana kallan motar har ta kule.

Wani alheri ne yake faruwa dashi haka? Da alama Allah ne ya dubesu.

Wani irin tsallen dadi yai, ai da kafa ya taka a hanya ya tsaya gun mai balango ya siyo na d’ari biyar ya siyo lemo ya taho gida cikin nishad’in da kai kace talauci aka yanke mai.

Goggo kam mamaki ne ya hanata ma cin balangon sosai, sai kara kallan check din take zuciyarta na kara sanyi, kallan Adam tai tace “shawara ta biyun tafi kaga ai ba mutuncinta kaci bako?”

Da sauri yace “haka na gani, ai gaba daya na rasa farin cikin da nake ciki.”

Dariya suka sa cikin jin dadi, Goggo kam wani irin nishadi takeji, kallansa tai da sauri tare da tsuke fuska tace “ba uku kacemin kayi ba?”

Yace “haka na dauka amma yanzu dana nutsu na tuna biyu nai ranar ma dan bana hayyacina ne.”

Cikin jin dadi tace “haba? Shine baka fad’a min ba? Bari nai maza na fara had’a kayanmu yanda daga an kammala komai mu koma, yan bakin ciki naga yanda zasuyi.”

A tare suka sa dariya, Adam a ransa yace “in na dage biyu nai ai dole ta koma tunda ba aurene da ita na, ko takardar ta dauka sai nace ba ni na rubuta ba.”

Kallan Goggo yai shima yasa dariya cikin jin dadin abinda ya samesu.

Tana kwance akan doguwar kujera har lokacin tashinta yai batama sani ba dan baccin dabatai ba daren jiya shi ne ya dauketa, da yake yau batada amfani ba wanda ya bi ta kanta sai gulmarta kawai da ake.

Khalid kam ganin ya kira sau uku bata dauka ba kawai ya share, lokacin tashinsa nayi ya duba yaga duk yan aikin rana ma sun tafi, mikewa yai ya dau jakarsa yana kokarin fitowa.

Juyawa yao ya kalli office dinta, ganin wutar ta a kunne ne yasa ya nufi office din.

Knocking yai, kamar a mafarki taji knocking, a hankali ta bude idanunta, cikin hanzari ta mike hankali a tashe.

Kallan agoggo tai sannan ta bada izini. Khalid ne ya bude kofar ya shiga, kallansa tai da sauri ta kauda kanta gefe tana tunanin da alama fuskarta duk tayi abin bacci.

Khalid ne ya kalleta yace “bakyajin dadi ne?”

Bata kalleshi ba tace “I don’t know what’s wrong with me.”

Yana tsaye a gun yace “maganar gidan, nama wanda yai posting din a instagram ya turomin address din.”

Juyowa tai da sauri tace “can you send it to me?”

Wayarsa ya dauko ya tura mata sannan yace “zan wuce.”

Harya juya tace “Ammmm....”

Tsayawa yai sannan a hankali ya juyo ya kalleta, kallansa tai itama sannan tace “Can you help me?”

Yanayin yanda ya canza kallan da yake mata ne yasa ta juya kai, tace “i just feel like Director Kabir akwai abinda zai shirya akai na, i made a mistake dana bashi duka plans din danai, wannan karan they will try to use this against me.”

“But how can they do that? Bayan ba laifinki bane?”

Mikewa tai tare da d’aukan jakarta kusa dashi ta nufo, tace “Dole na nemo abinda zan kwaci kaina dashi, dukansu na saman nan basona suke ba.”

Kallanta yai yace “Do you have to do that?”

Tace “ko na rufe bakin Adam tunda suka san maganar sai sun dinga tuno abubuwa, i know they don’t like me amma banyi zatan wannan abin zai sa suyi tunanin janshi haka ba.”

Kallanta kawai yake baice komai ba, kallansa tai tace “wannan kallan fa? Yanzun ma cewa zakai lefinane?”

“Maybe.”

Takaici ne ya kamata ta bude kofar ta fita, ga mamakinta ganintai ya fito shima kafin ta rufe office din taga yana neman tafiya.

Rufe Office din tai sannan ta taho, yana sauka daga kan steps din dazai sada ka da kasa, jitai yace “Do you ever think about that?”

Itama bata kalleshi ba tace “what?”

Yace “dalilin dayasa dul wanda ke tare dake bai xaune dake zuciya d’aya.”

Kasa daga kafarta tai balle ta sauka, shiru tai batace komai ba wanda hakan ya sashi ya juya ya kalleta.

Ganin yanayinta ne yasa yace “Don’t mind me.” A ransa yace Khalid meke damunka dasan fadan abinda bai dameka ba?

Daurewa tai ta kalleshi tace “can you drop me?”

Baisan sanda yadan murmusa ba yace “a matsayin wa?” Tace “d’an Umma.”

Murmushi yai yace “then you have to change your tune, in za’a miki abu you have you have to differentiate between favour and order.”

Ita kanta samun kanta tai da murmushi tace “meyasa kake san kamin gyara akan duk abinda nai.”

Kallanta yai a tare sukace “I don’t know.”

Murmushi ya sake ya kalleta tace “i know haka zaka ce.”

Bai ce komai ba ya karasa sauka, itama sauka tai.

Afreey dake zaune cikin mota ta dunkule hannunta tana wani irin hucci na tsananin kishi.

Shiga tai ta zauna a gaba kanta dan kanta ciwo yake da alama baccin datai mai nauyi ne yasata, Khalid yazo shiga yaga Afreey a motarta tana hucci, ido ya zuba mata yana kokarin yin nazari akan ta, Zainab jin shiru yasa ta bude idanunta, ganinsa tai ya zuba ido yana kallan abu, juyawa tai ta kalli inda yake kallo.

Afreey ta hango, kallansa tai sannan ta kalleta.

Fitowa tai daga inda take ta nufi inda yake, bani key din.

Kallanta yai, gani tai ya mika mata ba musu, wani takaici ne ya kamata kawai ta shiga motarta rai a bace taja.

Khalid ne ya nufi inda Afreey take ya bude inda take zaune yace “Safiyya!”

Kallansa tai bakimta na rawa saboda tsananin kishi.

Yace “will you stop that?”

Me?

******

Ayusher🏌🏻‍♀ [12/12, 9:43 PM] Ayusher Muhammed: 🍀A GIDANA🍀 .........................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

#OneLove❣

You have come a long way and have won many battles. Whenever you're faced with a difficult or challenging situation, you'll overcome it. Yes, you can.

{43}

Kallanta yai yace "Saboda ni kike aiki anan?"

Kallansa tai itama tace "korata zakai in saboda hakan ne?"

Shiru yai yana dan tuno kadan daga cikin abinda ya faru a Buk yace "Sai yaushe ne zaki nutsu ki kula da rayuwarki? Meyasa bakya tunanin rayuwarki ta nan gaba?"

Zuciyarta cikin kuna tace "Sai yaushe zaka dawo gareni?" Tai maganar idanunta na cicikowa suna neman kawo ruwa.

Wani takaici ne ya kamashi yace "abinda kikeso kenan?"

Hawayenta ta shiga kokarin maidawa tace "bazai yiwu ba?"

Yana kallanta yace "badai ni kike jira na fad'a da kaina ba?"

Wani takaici ne ya kara kamata dauke da wani zafin kishi tace "indai har ni bazan sameka ba to sai dai ka zauna haka, in har bazaka dawo gareniba ba wacce ta isa ta sameka."

Wani mugun kallo ya mata yace "Safiyya wai meke cikin kanki ne?"

Kallansa tai tana hucin kishi, yace "can you please stop? Banasan kisani yimiki kiyayyar da baxata taba gogewa ba."

Ranta a bace ta kauda kanta, kallanta yai sannan cikin takaici ya juya.

Harya isa gida hankalinsa gaba daya ya kasa kwanciya, ya tabbatar Afreey akwai abinda take amma daga gun wa? Taya zaiyi ya taimaki Zainab? Dan baisan me zai ce mata ba in ya ganta a wani hali.

Yana kwance shiru a cikin dakinsa, yana nazarin mafita, abincin daya shigo dashi daga cikin gida ya kalla, yunwar dake damunsa ce yasa ya zauna tare da sa hannu dan cin tuwon dawa miyar kubewa da Umma tai.

Loma d'aya yakai ya fito da idanunsa da sauri, mikewa yai ya saki murmushi yana cewa ya akai banyi wannan tunanin ba?

Da sauri ya tsame hannunsa sannan ya dauko wayarsa, number Zainab ya kira.

Tana kwance a falo, Nabila da Nusaiba nata hada kayan tafiya, laptop dinta ce a gabanta tana dadannawa da alama wani abu take dubawa a ciki.

Kallan wayarta tai dake kara sannan a fili tace "sai yanzu?"

Hararar wayar tai wanda ni kaina harna dauka bazata dauka ba sai kuma naga ta daga da alama ringing din karshe ne kafin kiran ya katse.

Daga can yace "Hello!"

Shiru tai batace komai ba wanda hakan yasa ya kalli wayarsa dan ya dauka ba'a daga ba, ganin alamar ta daga yasa yace "naga kamar bacci kike in kin tashi na kira."

Sauke wayar yai yana jira yaji tayi magana jin takiyi yasa ya kara cewa "hello!"

Murmushi tai sannan tace "na riga na saba da bakar maganarka sannan na gane kanafadan ta ne dan na maida murtani."

"Ummmmmm""

Hade fuska tai tace "ya akai?"

Mikewa tsaye yai yace "ya kike gani in kika amshi aikinki?"

Da sauri tace "you mean?"

Yace "eh, duk abinda suke shirin miki basu isa su miki ba in har kina program dinki, saboda ganin bakya nan zai sa mutane tambayar abinda ke faruwa, waccen karan ance kin yi tafiya ne wanna fa? Hakan zai sa a shiga nemanki, ba hujja garesu ba sannan basu da ikon shiga rayuwarki, tunda sun san hakan, sannan a cikin shirin ki bayyana mutuwar auranki da kanki, kin riga kin tsoshe abinda zasuyi amfani dashi."

Cikin gamsuwa da abinda yace da jin dadi yasa tace "nima yanzu nake tunanin sauke website dinmu da duk wani program da na saka a youtube"

Shima cikin gamsuwa yace "hakan yayi"

Dan gyara kwanciyar ta tai tace "hmmm" "Nagode"ta fada a hankali. Sarai ya jita hakan neya bayyanar da murmushi a fuskarsa. Can yace "ya zakiyi da Adam?"

Tace "zan je gidan Gobe da rana."

Okay yace suka dan yi shiru, basu taba doguwar waya haka ba dan waya ma bayinta suke ba sai da dalili shiyasa duk suka samu yanayin wani banbarakwai.

Khalid ne yace "shikenan, sai da safe."

Tace "Allah ya tashemu." Tai saurin kashe wayar, shiru tai tana nazari, tabbas shawarar da Khalid ya bata sosai ta gamsu da ita.

Ai mikewa tai ta zauna ta fara harhada abubuwan da zata gabatar a gobe, waya tama daya daga cikin masu dauko rahoto tace "ya turo mata na gobe." Ba musu ya tura mata dan dama sau da dama takan tambaya shiyasa bai kawo komai ba.

Da safe ta shirya tana rufo kofar daki Nabila na fitowa daga nasu dakin hannunta dauke da robar ruwa.

Zainab ta kalleta tace "Hajiyar bacci ya akai kika farka?"

Nabila ta kalleta tace "Allah Aunty zan daina kwana kan gado da Nusaiba kullum da ciwon jiki nake tashi, ta dinga makamin kafa kenan."

Dariya Zainab tai tace "shikenan sai ki koma dakin Goggo."

Hade fuska Nabila tai tace "ni wlh sunansu ma bansan naji an kira." Ta kalli Zainab tace "Aunty haryau bazaki fadan abinda suka miki ba?"

Kusa da ita ta matso ta dafa kafadarta tace "zan wuce Mamman yace sai rana zaku wuce ko?"

Tace "Hmmm kikace zaki kaimu gun Asiya."

Kallanta tai sam ta manta tacewa Umma zata kawosu, gashi har hutu ya kare, ga Dady tasan yanzu zai fara fada akan zamanta ita kadai, next term kuna dawowa zan kaiku.

Hannun Zainab ta kamo, juyowa Zainab tai ta kalleta, a hankli ta sakar mata murmushi.

Nabila ta maida mata tace "jiya kin samu bacci?"

Hmmm ta fada tare da daga mata kai. Nabila ta saki hannunta tace "karki manta kizo kafin mu tafi."

Kai ta daga sannan ta fita.

Mamman nata goge motoci biyun dake waje dan Dady ya sai mata mota a ciki ma suka dawo. Kallan Mamman tai ta gaisheshi, da sauri ya karaso yana gaisheta, murmushi tai tace "zan wuce dakaina."

Yace "ki bari na ajiyeki" "A'a inada inda xani ne daga can."

Ba musu ya mika mata key sannan ya tsaya ya bude mata motar ta shiga sannan ya rufe, jan motar tai ta fita.

****** Khalid ya gama shan tea da Tsame ya dau kajarsa xai fita sai ga Umma.

Kallansa tai tace "ungo wannan ka kaiwa Zainab."

Kallan flask din yai ya amsa tare da budewa, ganin tsame yasa ya rufe yace "Hajiya Umma."

Tace "Allah yasa zata iya ci, sannan kace karta kuskura ta sa komai a kular."

To Umma, jakarsa ya bude ya saka sannan ya shiga yama Abba sallama ya fita.

Zainab na shiga ta wuce fitting room ta shirya sosai, ba tare da ta ma wanda ya amshe da shirin nata magana ba.

Wucewa tai Direct dakin shirye shirye, kawai taja ta zauna.

Nazifi wanda shi yake gabatar da shirin a maimakonta yana shiga ya ganta a hakkimce, yanda yaga alamun fuskarta ne yasa yasan ba wasa, kusa da ita yaje ba musu ya mikamata takardun hannunsa tare da mata barka da cigaba. sannan ya juya zai tafi. Nazifi! Juyowa yai ya kalleta, alama tamai daya zauna, kallanta yai yace "naam?"

Tace "let's do it together."

Da sauri ya kalli gun masu cameras sannan ya kalleta, alama tamai daya zauna.

Da sauri ya zauna tare da dan matse kafafunsa alamar rashin sakewa.

Khalid dake tsaye a gun camera yana ganin abinda ke faruwa, har suka fara gabatar da shirin, sannan ya juya.

Director Kabir dake ta faman hada kan manyan gun aikinsu dan suzo ayi meeting akan Zainab.

Ramlatu ta kirashi ta sanar dashi abimda ke faruwa, ba karamin tashin hankali ya shiga ba.

Cikin hanzari ya juyo tare da sanar dasu su iso suma.

Zuciyarsa fal take da takaici, tare da kara shan alwashin korar Zainab koda zai rasa komai nashi ne kuwa.

Yana isa tana kammala shirinta, daga karshe ne ta mikawa Nazifi takarda bayan an dan tafi nuna rahoto. Kallanta yai da sauri, tasani sarai mamakin abinda ke jiki yakeyi hakan yasa ta daga mai kai alamar eh.

Ana dawowa daga rahotanni, Nazifi yace "ga shirin namu ya kawo karshe, akwai abinda ke yawan damuna."

Yadanyi dariya ya kalli Zainab yace "gaba daya yanzu zamanin na rasa meke faruwa a ciki, sai kaga mace da namiji anyi auran soyayya mai karfi amma wata uku sai kaji aure ya mutu, me kike tunani yana kawo wannan matsalar?"

Dariya Zainab tai tace "ai ku maza ku za'a tambaya, dan kune masu sakin kaga kune kuka san menene ya ke sa kuke yinsa."

Ta kalleshi tace "ni kaina watan ni hudu da suka gabata nawa auran ya mutu, kaga kuwa kai ne zaka amsa wannan tambayar."

Nazifi yace "Inalilahi bamuda labari, ba dai hutun da kika dauk......

Dariya tai tare da daga kai sannan tace "shi dan adam kowane da nashi kaddarar da Allah yake dauramai shi yasa a koda yaushe muke rokon Allah ya bamu ikon cin jarabawarmu."

Nazifi ya jinjina kai........ nan suka kara tattaunawa akan matsalar aure sannan sukai sallama.

Director Kabir ta kalla wanda ke tsaye a jikin kofa ransa a matukar bace. itama kallansa tai sannan ta shiga yima Nazifi magana ba tare da ta tanka mai ba.

A zuciya ya juya.

Yana shiga yaga envelop doguwa akan desk dinsa, budeta yai ransa duk ba dadi, dan ya gama sadaukarwa Zainab ta riga tayi winning ba abinda ya isa yayi.

Abinda ya gani a ciki ne yasa ya zauna akan kujera da sauri yana kara karantawa.

Zainab ta kalli Khalid wanda ke printing, sannan ta wuce.

Tana shiga office dinta ta saki murmushi tare da yin ajiyar zuciya, xama tai ta jawo flask dinta tana kurbar tea tare da duba abubuwan data sauke.

Wayar cikin office dince tai kara hakan yasa ta daga.

Director Zainab ki shigo akwai Emergency meeting nan after lunch .

Okay kawai tace ta ajiye wayar, nazari ta shigayi tana tunanin me za'a tattauna.

Mikewa tai ta dauko key din motarta, ta fito.

Mota ta shiga ta wuce gidan su Adam.

Goggo na zaune tana kallo, yau kamar nela sun san farin cikin da take ciki suka kawo mata wuta, gefe dankali da kwai da suka ci suka koshi ne harda ragewa a gefe, ga kofin shayi nan a gefenta tana kallo tana sha.

Adam ne ya kalleta yace "wai Goggo idanki baya zafi?"

Zafin me? Kallo mana.

Tsaki tai tace "ni wannan tv din ma ai a dole nake kallo da ita, yo meza'ai da wannan yar fucikar tv din? In na tuno ta gidan Zainab sai maji raina ya baci, duk kai........"

Kallan ta yai sai ta wayance tace "yaushe zaka bank ka tattalo mana kudin?"

Dariya yasa yace "yanzu ma."

Lalitarta ta bude tace "kai inaji tare zamu tsoron baka kudi nake."

Shikenan sai ki shirya.

Zatai magana akai sallama, taran Asabe ne ta bude labule tace "A'a d'an nan ya akai? Ta fada tana dan toshe tv dinta da labule ta dauka abinda yazo kenan.

Yace "ana sallama da Adam ne."

Goggo ta kalli Adam tace "kaji!"

Wata dariya yasa yace "wato Allah yamin farin jini ta ko ina wlh."

Mikewa yai yana kade riga cikin isa da takama.

Yana fita ya ga motar Zainab, idanu ya zaro da sauri ya nufi motar.

Kallansa tai sannan ta budemai yai saurin bude kofar ya shiga cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa.

Kallanta yai yace "Honey!"

Kallansa tai ta zubamai ido wanda harya sa ya sosa sumar kansa tace "Bani wayarka."

Da sauri ya mika mata, duk hotunan da sukai tare ta goge sannan ta mikamai.

Kallanta yai yace "me kikai?"

Tace "hotunan mu na goge." Da sauri ya duba hotunan ko d'aya babu, kallanta yai yace "Honey!"

Da wa kake?

Shiru yai kafin yace " Honey dan Allah bazan yi maganar hoto ba amma dan Allah ki amince mu maida auran mu? Kinji?"

Kallansa kawai take tama rasa me zata cemai, yace "Honey na tuba ki yafemin, Allah nayi laifi amma wlh abinda kike tunani bai faru ba, dan Allah Honey ki........."

Wata irin dariya tasa wanda kana ji kasan ta bakin ciki ce dariya tai sosai dan ni kaina bantaba ganin Zainab na dariya haka ba, cikin dariyar tace "mu maida aure?"

Kai ya daga da sauri.

Kallansa tai sannan tace "yanzu nake nazari iya zaman danai dakai har yai baka taba nuna min jarabawarka ba, dauko takardunka ni da kaina zan samoma aiki."

Kallanta uai kabansa ya shiga faduwa yace "takardu?"

Tace "eh dakosu."

"Zan dauko amma Honey ki am........"

Shiru tai tana kallansa, can tace "Adam haka kake tun dama ko kuma yanzu ne na maidaka haka?"

Cikin rashin fahimta ya kalleta, zuciyarta na kuna tace "wad'an nan dabi'un naka sababbi da nake gani yasa na shiga tunani, dama can haka halayenka suke? Boyewa kai saboda ni ko kuma nice bayan aurena ka koma haka?"

Kallanta yai yanayinsa duk ya canza.

Idanunta ne suka ciciko tace "Wani irin rayuwa mukai nida kai har shekara 4? A kwanakin nan wannan amsar haryanzu na kasa samota."

Cikin sanyin murya yace "Honey!"

Tace "in har kanada imani da tunani ko cewa akai kamin abu zakamin? Bayan abinda ka aikata min? Har sai ka karamin da abinda zai sa na tsaneka har karshen rayuwa ta?"

Kallanta yai hawaye ne suka gangaro mai, itama hawaye ne suka zubo mata tace "na rokeka da Allah Adam ka kyaleni, jiya da kyar nai bacci ina tunanin tambayar da akamin wacce banida amsarta, an tambayen dalilin daya sa duk wanda nake tare dashi baya zaune dani zuciya daya, na dade ina tunanin wani irin shiga hakkinka nai a zaman mu da zaka sakamin da haka.”

Da sauri yace “ba abinda kikamin Honey, ni din ne bazan iya hakuri dake ba.”

Yanayin kallan da takemai ne ya canza tace “da alama kanka ba daya ba Adam, na rokeka da Allah ka barni nai rayuwata, ka barni naji da abinda ke damuna plz.”

Shiru yai baice komai ba, kallansa tai tace “zan wuce, inada meeting.”

Kallanta yai jiki a sanyeye ya fito taja motarta ta tafi.

Ganin time din ya kusa yasa ta kara gudun mota, tana isa ta shiga ciki, wucewa tai gun meeting din tana bude kofar taji gabanta yayi wani irin faduwa, da sauri ta shiga yin addu’a a ranta.

Khalid ne ya kalli Mai maganar, cikin gulma yace “sun shiga meeting da alama akan Director Zainab ne.”

Nazifi ne yace “wai matsalar ta meye? Rayuwartace fa menene dan auranta ya mutu? Ita take da kanta? Ko ita ke san ta kashe auran nata?”

Ramatu cikin fishi tace “ita mutanen data kora saboda rayuwarsu fa?”

Da sauri mutanen gun suka fara bin bayanta, Khalid wanda ke zaune ransa yafara baci matuka.

Afreey ce ta kalleshi cikin kuluwa.

Nazifi yace “dukansu abinda sukai ya shafi aikinsu san kai kawai kuke yi da muna bakin ciki.”

Nima nace haka ne🙄plz ku bat Zee tasha ruwa ya tsirga mata😒

****** Ayusher🏌🏻‍♀ [12/14, 9:30 PM] Ayusher Muhammed: 🍀A GIDANA🍀 .........................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

#OneLove❣

Always Turn your wounds into wisdom.

*Congrats SURRYHAMS Barka da kammala littafi, Allah ya kara basira da zakin hannu, will miss Khal and Bahi our cute love birds😘*

{44}

Tana kokarin fita daga motarta wayarta tai kara, a hankali ta sa hannu ta dauketa, sunan Swt Sis ne ya bayyana a alan wayar tata, a hankali ta rufe idanunta cikin wani yanayi sannan ta dauka.

Nabila daga can tace "Aunty? Muna ta jiranki."

Cikin wani yanayi mai sanyi tace "Nabila kuyi hakuri bazan samu zuwa ba wlh." Da sauri Nabila tace "wani abin ya faru ne?"

Tace "bakomai meeting zan shiga yanzu ne, in na fito zan kira Dady." Jiki a sanyaye Nabila tace "shikenan mu zamu wuce, in kin fito mayi waya."

Kai ta daga kamar tana ganinta tace "shikenan, akwai jakata a daki na ajiye muku kudin skul ki daukar muku."

Mundoge, Aunty dan Allah ki kula da kanki.

Cikin jin dadi tace "to Nabila nagode." Kashe wayar tai sannan ta zubawa Tv Station din ido tana kara tuno farkon zuwanta da yawan canjin da aka samu daga fara aikinta zuwa yanzu.

Bude kofar motar tai sannan ta fito.

Komawa yai ya xauna a karo na biyu kenan yana zuwa nemanta batanan, haka kawai jikinshi yake bashi ba daidai ba kallan Afreey yai wacce ke zaune tana dane dane a waya, Nazifi ne ya shigo yana cewa "Manya zasu shiga emergency meeting yanzu."

Kallansa Khalid yai, wani daga cikinsu yace "na meye meeting din?"

Nazifi yace "shi ke damuna."

Ramatu ce tace "akan Hajiyar gadara ne ka sani."

Kallanta Khalid yai, juyawa tai ta koma ta zauna cikin jin dadi.

Zainab ce ta tura kofar dakin taron sannan ta shiga.

Duk suna zaune wanda hakan yasa tasan sun gama tattauna abinda zasu ce mata kafin tazo. Shiga tai ta gaishesu sannan taja kujerarta ta zauna.

Director Kabir ne ya kalleta sannan yace "Zainab munaso mu miki tambayoyi kuma muna fatan jin amsoshi gamsassu daga gareki."

Kallansa tai batace komai ba. Takarda ya mika mata yace "wanene ya saka law din nan akan duk wanda ya bari harkar personal life dinsa ta shiga cikin aikinsa za'a dau mataki a kansa?"

"Nice" abinda tace kenan ba tare da tai karin bayyani ba. Yace "yanzu abinda ke faruwa fa menene?"

Tace "banida hadi da abinda kefaruwa, banga dalilin da zaisa a dinga hada rayuwata da wanda banda alaka dashi ba."

Kallan juna sukai, Kabir yace "kenan kina san cemana wannan abin bai shafeki ba?"

Wai akan me za'a dinga jan abinda ba wani abu ba ya zama wani abu? Sau nawa wasu na samu matsalar zaman takewa? Akanta aka fara ko a kanta za'a kare?

Kallansa tai sosai tace "me Adam yai? Me nai? Dan wani ya dau hoton mu ya daura a instagram da facebook ni na daura? Sannan ba aure tsakanina dashi dan ya kama gabansa laifi na ne kenan?"

Murmushi yai yace "hakane, to wani hukunci kike tunanin zakima wanda ya fitarda tambayoyin jarabawarmu yaba wanda yake so yaci?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull