A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 100
A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 100: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 100. ****** ********* ****** Bai dade da fita ba sai ga wayan ta…
3,281 words
****** ********* ****** Bai dade da fita ba sai ga wayan ta ta bugo min tana fada min ta sauka lafiya nan na yanka wani ihun murna na nufi falo da zuman fada mai yana zaune ya cin fruit don yanzun ya rage yawan cin abin sosai kamar baya sai dai fruits da yan sauran abubuwan gina jiki kawai. Murmushine a fuskan shi na iso da murna na nace yaya yace kun zama su mama yau ko nazauna ina fadin wallahi fa. Nace yaya na tafi asibitin ne na dubo ta yace dauki bai bari ki tsaya mu tafi tare ke nan ko? Naji kunya nace sorry barin tsaya kagama mu tafi, nasan zolayana yake yana ta shiririnta ci har yagama muka kama hanya zuwa asibitin da ta haihu din. Nice nai driving din mu yana gefe zaune sai waya yakeyi yana fafin sister shi ta haihu ta samu baby boy. Muna shiga dakin muka samu yan uwa da abokan arziki harda mummy a gurin don itace tazo daga gidan mu. Yaron yana nade a cikin showel a,saka mai rigan sanyi sky color mai kyau ta jarirai a jikin shi. Ita ko maryam tana kwance saman gado sai murmushi takeyi na karbi yaron na mikawa yaya shi ya dan kalle ni yace Fatima ban fa iya daukan yaro ba fa. Na gyara mai tare da nuna mai yadda za rika yaron ana muna dariya yaya idan naku yazo yaya zakayi inji sister din Bashar nace ai shine fadila Inda maryam take a kwance ya taka yana ce mata sannu yar gidan maji yau kan kin san kin shigo duniya ko? Murmushi tayi cikin jin kunya tace kai haba yaya dama ban san nashigo bane yace to yaya jikin naki normal dai kike ko don naga dan nawa so health dashi. Murmushi kawai tayi tace ummhumm yaya Bintu over to you now ko ni kan na sauke na huta . Ke ban son Bintun nan na fada maku ku daina kiran ta da aanan sunan kauyawan hakana please mutum da sunan shi mai kyau kuna bata mashi da,wani Bintu can. Kai malam yayane kuma mutum yayi fitan kutsu haka shine zaka kama min mata da fada tana kwance a gadon asibiti. Kai dan iska wallahi jawa matar ka kunne duk ranan da naji sunan nan haka a,bakin ta ba hauhuwa tayi ba ko duniya ta haife ranan sai na nashi shegen bakin nan nata. Aiko da sai fada kawai za,a raba mu dakai donbda sai na rama mata yace ga Fatima zaka ramay ko ankan wa . Bashar yace akan ka dai kaida kai min laifi ba kaunats da bataji tagani ba yace ko zaka gwada ne yanzu Baba. Tun da kaga yau ka zama Baba kana gani kamar karfinka yazo ke nan ko yaro. Yaro fa kace min maye kagani anan kuma ni yanzu ai sai dai baba kawi aka bushe da dariya a gurin. Naso yaya ya barni gurin Maryam amma yace mu koma gida gobe zai kaini na wuni a can yanzu mutane sunyi yawa sosai. Haka na tafi gashi muna son kebewa da maryam nasha labarin abinda tasha. Muna hanya yana waya ina tuki ban yi magana ba saida ya gama waya ya furza iska nace kana can kana fada ga abinda ya dace kaiwa fada akan shi. Yace may ke nan fa ? Nace kiran mamana da Majin da kukeyi mana don Allah ua kamata ku canzawa mama suna hakana please. Kuma fa yaya duk kaine ka saka mata wanan sunan don Iyya ta fada min wai baka iyannkiran ta maijidda da baba ke kiran ta shi ne ka dafa mata wai maji can. Mirmushi yayi ya shafo kan shi yace na dai ganecwallahi Iyya Rabi tana min tonon silili a gidana . Nace lah may ye laifin iyya yaya don ta ban kado min sirin baya tafa fada min irin yadda kai ta wahal da su mama wallahi. Yace hummm yai shiru tare da kwantawa da kyau saman kujeran mota ya rufe fuskan shi da hular kan shi kawai. Mun kusa shiga kwanan layin mune naji yace Fatima cikin wani irin murya nace na,am yaya yace wallahi yanzun ban san may yasa ba ina matukar son baby nima sosai wallahi tun dai yanzu dana ga na maryam din nan. Please Fatima will you give my baby too please Fatima ina son naga nima na haihu wallahi. Idanuwana na lumshe cikin wani irin yanayi da tausayin kan mu don ya fadi ne a baki amma ni na riga shi furta hakanna raina. To waye mai laifin a cikin ni dashi da muka kasa samo ma kan mu farin ciki irin haka ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYABA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU AKAN KI,,,
Maganan yaya yai matukar tsaya min araina nace a raina wanan kuma matsalar Allah yasan dalilin shi amma har yaushe ma mukai aure da za,a dinga damuna kan haihuwa hakane wai ? Ban fito ba ina dakina don abin yadan damay ni a raina sai nake jin ba dadi a tare dani kawai. Kira,an sheck Ahmad suluiman kano na saka a wayana shine yake tashi ina zaune ina bi a hankali nai makari da gadona ta baya kadan. Dakin yashigo yana saye da doguwar rigar jallabiya a jikin shi yake ce min lafiya kike kuwa ? Dan murmushi ne na kakaro a fuskana nace lafiyata kalau kawai dai sai naji nagaji ne. Yace ok ni zanje gida naga baba nakuma yiwa maji barka daga can don yar gaban goshin ta ta haihu nasan tana can tana murna yau. Nace ba dole ba duk wanda nashi yai ciki kuma ya sauka lafiya ai abin farin ciki ne haka sosai. Nace adawo lafiya yace baza,a sayo komai ba ko idan nafita ? Nace yaya ai akwai komai nake gani adai dawo lafiya muna gaida su kafin na shigo nima. Koda yafita yaje gida bai samu komai ba sai bacin rai kawai don yasamu mama da Baba suna jidali akan Ahmad. Wai yana zuwa duk abinda aka sayawa mama yana koshewa yakai gidan shi shi da matar shi mara kunya suci. Yaya ya samu dakyat yaba Baba hakkuri sai cewa baba keyi idan saye yana da dadi shi ya dinga saya suna amfani dashi mana can. Aishi yace yaji yagani ita yake so ga Imirana nan da lalacewan shi da komai yana fita yana samun nakan shi ai. Amma shi sai darga da rikicin kayan mutane da yasawa ran shi yakeyi duk ya zubar min da mutunci ga mutanen arzikina. Shine yau zuwa gurin wanan gobe yana gurin wancan yana bakin roko da yaudaran daya saka kan shi ciki. Umma dake daki tace ai babu dan kwarai a gidan nan yanzu sai dan son ka don shine mai abin hannun shi. Dama Atika aike butulu ce baki da godiyan Allah yanzu in ma don abin hannun shi ne ai tare dai dake muke cin komai ko ? Yaya ya samu baba ya shiga dakin shi da kyata ya kwanta da murya yana bashi hakkuri sai faman fada yakeyi. Yana cewa nai nadama da zama da matan a rayuwana ni nasan iya tsawon rayuwan da nayi suna,wahal dani suna cutar dani da sauran iyalina a gidan nan. Bai dade ba gurin baba yafita zuwa gurin maji dake zaune falon ta duk abinda akeyi sunaji ita d Amira. Ya gaisa da ita tare da mata barkan haihuwan maryam tace ni wanan gidan fitinan shi yana bani tsoro wallahi. Kullun ba,a san an girma ba sai anyi jidali a tsakani kuma na rashin gaskiya. Karo na farko maji taji yakira ta da mama yace mama hakkuri zakuyi kawai don kowa da irin halin da ke gare shi dashi kuma ake zama da mutum. Nan dai suka dan taba hira kan zancen yadda gidan ya koma yanzu yace shi zai tafi don dare yayi a lokaci. Ko da ya dawo ya samu nayi barci a lokacin ina kwance a dakin shi bai ta daniba shima ya kwanta sai da dare dana falka nagan shi kwance yana barci. Da Asuba yafita zuwa masallaci nikuma na koma part dina nai sallah na kara nadewa a gado na nakoma barci don weekend ne yau. Ya dawo daga masallacine ya samu wayan shi tana ringing a daki da sauri ya daga wayan mamace a layin take kiran shi. A ranshi yace lafiya kuwa maji take kirana da safe haka ? Ya dauki kiran da,sauri yana sallama yana fadin maji lafiya dai ko ? Tace lafiya lau babana na idar da sallah ne nace bari na kiraka naji yaya jiya ka koma kafita da bacin rai a gidan. Yace a ran shi Allah sarki maji ashe takwana tana tunanen shi ke nan tunda ta kurashi da safe haka. Yace lafiya na isa mama tace nima ina zaune ne ina addua akanku Allah ya kara tsare min ku yabaku saukin rayuwa da haske ga,al,amarin ku. Don na fahinci har yanzu su yaya basu san Allah ne mayin yadda yaso ba ga bayin shi. Ya saki ajiyan zuciya yace mama ki kwantar da hankalin ki ai tunda basu iya komai damu muna kanana ba ko yanzun ma Allah bai basu sa,a . Tace kaga kwanaki haka Alhaji sani yazo gidan nan yai min kaca kaca wai ni na hanaka hurda da kowa a cikin yan uwa sai yan uwana dana matanka kawai yanzun ka sani. Don wai yaji labarin irin abin arzikin da kake tura masu a can kauyen su nan kabarsu hakana. Kai maji ni har yaushe ma nakewa iyayyen Fatima ma,wani abu mutanen da ma nake matukar jin kunyan su sosai ban fako je ba tunda mukai aure. Dasu da baba tsoho wallahi suna a raina ina son mu samu lokaci na ziyar ce su. Baba tsohon da yake nufi mahaifin mama dake zaune a Niger state shi da sauran iyalin shi noma ya mayar dasu can sun zama yan kasa yanzu ko. Yace amma zan ga baba sani din sai asamu abinda akai mai bashi ke nan ba. Mama tace kaifa baka da zuciya babana duk wanan abinda sukai maka shi da su yaya maganan su fa daya ne Yadan kwantar da murya yace maji kiyi hakkuri don Allah don kin ga akanki suke sauke haushin su ko yaushe don haka zan masu yadda yake so a zauna lafiya. A hankali mamatace Allah yai maka albarka ya baka ikon kyautata masu ko yaushe. Yace amin maji tace ina fatima yace ta koma barci yau weekend bata fita tace yana dakyau ta dan huta don nasan anjima kadan yau gidan maryam zasu dire. Yace kaman ko kin sani mama aini dai yanzun nasan ni da samun kanta,sai sun gama bukin nan kan. Tace kaima ka sani tsakanin maryam da Fatima ai sai Allah yace da yake muna fukai ne ba sun hade wa sister na kai su biyu. Ba wani hadin kai halinta dai ne sai ita Amira tafita daban a cikin ku sai kace diyar umma. Dariya tabashi cewan da tayi sai kace diyar umma take yace itama dai zatai auren ai ta huta da fadan kowa hakana. Dadai yafi mata alheri taje kowa ma ya huta da bakin halin ta hakanan. Suna gama wayan da mama sukai sallama kowa yana cikin farin ciki duk kan su.
****** ********* ****** Sai da nai barci na mai ista na tashi batare da ya tayar dani ba nata shi wanka na fada nafito ne ina zaune ina shafa mai ya shigo dakin. Shima yai wanka don a shirye yake a lokacin idanuwan shi a kaina yace ashe barcin ba mai nisa bane inace ko sai biyu zaki tashi. Nace cikin murmushi da yau anty maryam ta yankani ai tun fa safe take kirana a waya. Sai da na shirya duk yana zaune a bakin gadona yana dakilar wayan shi tsab na gama nace mashi nashirya yaya. Yadago kai yana kallona yace au yaune zakuyi bukin ke nan da sauri na,ware idanuwana nace yau kuma yaya ? Yace to wanan uban kwalliyan haka dana ga kinyi aina dauka zumudi zai sa kuyi shagalin bukin ne yau ? Yamike yana cewa ni dai yanzun nasan ba a da time dina sai dai yadda Allah yayi dani kawai. Nace haba dai yaya yanzun ne ma fa zan bar gida to eleven fa yanzu ake nema kamata yayi ace ina gidan tun bakwai ai. Eh tunda gaki ungwazoma ba sai kije bakwai kiwa jariri da uwar shi wanka ko. Dariya nayi kawai nace tau ni fa ai yanzun komai zanji amma bazanyi fushi ba tunda ina son abar ni na tafi. Shi yajamu zuwa gidan ya sauke mu a kofan gidan ni da iya don maryam tana dakin ta bata koma gida ba. Uwar mijin ta daine tadawo gidan nasu da zama inda yake zaine na dan kalla tare da gyara tsayin mayafina don gyale na saka yau nace sai mun dawo ke nan yace four zan dawo na dauke ku fa. Kaina na langabe nace haba yaya four fa inace ko sai magariba yace idan kika bata min rai wallahi yanzun zaki shiga ki fito mu wuce nace da sauri iam sorry sir don nasan karamin aikin shine hakan. Ko don ya batawa maryam din rai na bude mota zanfita naji yace ban son fitina fa da kowa kuyi lafiya a watse lafiya nace insha Allahu yaya. Nafita ina cewa mun gode sai ka dawo yaja mota yanajin dadi komai kankantan abu sai nayi godiya akan shi. Ya furta a fili simple life . Muna shiga gidan tun a kofa muke jin hayaniyan mutane yan uwan yaya bashar sun cika gida sai surutu sukeyi. Nai sallama iya tana bayana nagaidasu ina fadin to abani ruwan zafin ajuyo nai mata wanka duk aka kwashe da dariya. Inna dake gefe tana gasa jariri tace hai Fatima kwana nawa ance ma maye ga nama. Daga daki maryam ke fadin ki koma ban so tunda bakiyi farin ciki da zuwan baby naki ba sai yanzun ne zaki zowa mutane. Na daga labulen daki tana zaune da cup din kunun kanwa a gaban ta sai zufa takeyi tako ina nace bura uban nan wani abu ko sai haihuwa wallahi anty kece haka kace kace cikin zafi. Na zauna saman gado ina cewa wayyo Allah na wallahi duk na gaji sai kace nice na haihu wallahi. Ta kurba kunun tare da lumshe idon ta tace da waye ya haihun bake ba ni sunan nai cikine kawai ai dan nakine. Nace kada ki sa na gudu dashi fa yau gidan mu tace aida yayan ki ya tare maku a gida kinko ga jiya da kyat inna ta samu yatafi ya kwanta ya barmu wai shi anan zai kwana nace Allah yabaku maryam. Ke da yaya wallahi kuna sha,anin ku harara ta kara watso min tace kunan daban ne Bintu ? Tace wai da sauri na manta ina gadon asibiti ma nace Bintu ance za,a balbalani balle yanzu ina dakina zaune. Wanan dan rikici halin shi sai shi wallahi yanzun ma cewa yayi wallahi idan nai tsiya dani dake yanzun zamu shiga mu fito tace dako na hada shi da maji wallahi. Nace kina hada shi da ita nabi mijina don ban son fadan nan dakike sa ana mashi ko yaushe. La la la Bintu ni kike fadawa haka yau kan yaya eh lalai kan mage yaji gishiri kuwa. Waya na jawo na fara dan dana nomba sai ko naji ya dauko yana fadin hello na,shake muryana nace yaya love kaji anty maryam tana ce min Bintun daka hana ko. Ya ko hau fada maryam wallahi zan zo na balbalaki tace iyye watau karana kika kai ma ke nan lalai Bintu wai Fatima wuyan ki yai kauri ashe. Nace sorry yaya ta gyara yanzu tace Fatima din kayi mata hakkuri tsuki yaja yace mashiririta kawai kuka sani nace asauka lafiya na kashe wayan. Tace yar iska ke dai kin kirashi da,wayyo kiji muryan shi kawai ba,wani kai karana da kikayi. Indai yayane wallahi naga take taken shi yarinyar har tausayi kike bani don nasan baki da hutu. Nace abu cikin duhu sirine ne tace kwarai kuwa nayarda sirine don nagani yanzu a zahiri. Sai lokacin Iyyan Rabi ta leko dakin tana gaida maryam din na tuna nace Allah sarki iyya na manta fa kina waje kiyi hakkuri kinji. Muna nan dakin sai hira mukeyi shigowan matan yaya Imirana dakin shine yasa muka kwasa muka yo waje can sai ga wasu yan school din mu da suka kare da ita sun shigo. Wasa wasa gida ya fara cika iya ta mike zuwa inda ake aiki takama masu aiki. Shigowan matar yaya Ahmad tanbele ya tashi sai hira take muna ana kwasan dariya wanda hiran nata duk kusan batsa take yi wai ita hira ke nan. Sai ga Umma da mama sun shigo barka da wata kawar mama makwabciyar mu nan muka shiga gaidasu sai dai yadda Jamila matar yaya Ahmed tayi masu banji dadi ba. Don ta nuna rashin da,a sosai a gare su kamar bata san sune ba abin duk ya bamu mamaki ganin su baisa ta fasa abinda takeyi ba sai ma ci gaba datayi da abinda takeyi. Basu dade ba sukai sallama suka tafi har kofa muka rako su ni da matar yaya Imirana Hadiza wace ke da dan matashin ciki yanzu. Gani bai sa umma ta fasa fadin abinda tai niya ba don cewa tayiwa Hadiza ki yi haraman komawa gidan ki don banga abinda kukai wani taruwa nan kunayi ba kamar haihuwan gidan sarki. Tace ai shine zai zo ya dauke ni yace tace to kindai ji na fada maki ki maza ki koma gidan ki ban son irin shige shigen nan. Sai da muka dawo cikine take cewa sai mutum nason ya shigo yan uwan shi amma aita hanashi . Jamila tace walleh ke an nan nikan anso akawo min wanan control din amma tuni na wuce gurin don ban yarda uwar miji ta hanani shakat. Hadiza tace nikan sai lokacin da yazo zan tafi mutum yana cikin yan uwa yana dan walawan shi amma sai duk a takura maka. Jamila takara cewa yanzun dadafa ke akaji inda tsofin gana walleh har yanzu su kishi sukai harda diyan su kosu kegane su kaman kan su a hade walleh cin kan su suke tsakanin su. Kowa gulman dan uwane yakai idan daya baya kusa ni jiranakai watarana su shiga gonana nai masu tas wallahi. Nidai da maryam bamuyi magana ba muna jin su don da mun tanka namu ne zai fita nasu ya boye. Nan dai muka wuni anata faman shiririta irin na matasan mata idan sun hadu zallansu. Sai naji ranan naji dadin haduwan mu haka saboda bamu taba haduwa haka ba tsakanin mu sai bayan sallah la,asar muka fara watsewa daya bayan daya nikan yaya yai min halarci sai yamma lis yazi daukan mu muka koma gida. Yace ma Iyya kada ta damu kanta da zancen girki zai sawo abinda za,aci da dare. A gajiye nake don kai da komon da mukayi a gidan maryam wanka nayi nai sallah muka fito falo yana dawowa shima wanka yayi yafita gidan. Nan muka zauna da iyya muna hira tsakanin mu tana bani labari akan matar yaya Ahmed bata da mutunci ko kadan bama wanda ya zaci har zasu kai wanan lokacin dashi ai. Iyya ta dan tausa muryan ta kamar wani na jin mu tace ke irin su Nafisan Umma ta fa duk harkan su guda. Nace Allah mai iko watau kowa dai Allah ya bashi a dakin shi ke nan ba mai fadawa wani kuma.