A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 99
A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 99: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 99. Mun kai wani lokaci mai tsawo tare da yan uwa ana ta yaushe…
3,189 words
Mun kai wani lokaci mai tsawo tare da yan uwa ana ta yaushe rabo a tsakanina da su wanda yawanci duk wasan su akaina ne su na min wasan kanin miji. Ganin yai shiru nasan halin abina bai faye son surutu mai tsawo ba shi sai dai a dan yi ai shiru yasa na fahinci taron hayaniyan ya dan ishe shi ke nan a lokacin. Na dan mike zuwa gaban shi nace tare da dan rakwafowa gare shi yana zaune ya rike goshin, shi da hannu daya yana dan murzawa a hankali idanuwan shi a lumshe gaba daya. Jin muryana kusa dashi ina magana ina cewa yaya may za,a zuba maka ne kaci ? Bude idanuwan shi yayi ya sauke a fuskana da nake duke gap dashi na kara cewa may zakaci ne yaya? Ya dan sauke min murmushi yana fadin duk abinda kikaga ya,dace dani ki zubo min. Gurin dinin na tafi na fara hada mai abincin gargajiya wanda mun dade bamu ci shi ba sai yau da muka dawo gida. Tare da zuba muna ferfesun kayan cikin rago dana danyen kifi manya masu tsoka sosai. A plate daya muka ci abincin da yake ba,a saman table bane kowa yana kasa nan kowa ya fara diban abinda yake so muna ci muna hira tsakaninn mu. Nice na fara mikewa tare da dan fuskan tar yaya nace zan dan shiga ciki na kewaya wai irin kallo yai min wanda yasa dul wanda idon shi ya kai ga kkallon a lokacin sai yaji wani iri. Don da ido yai min magana na taimaka mashi shima na shige dashi a cikin dakin shi. Hannu na mika mashi ya kamo tare da mikewa tsaye muka shige daki dakin shi muka fara shiga sai da ya shiga wanka na fito zuwa dakina wanda nai watanni ban a cikin shi. Wani kamshi ne mai tuna min da abubuwan da suka shude a baya da dama kamshin dakin nawa ya,tuno min. Maryam ce ta biyo bayana muka zube tare da su a dakin nan na shiga wanka na shirya cikin wani riga dogon milk color mai guntun hannuwa. Na mulke jikina da kayan kamshi masu kyau da tsada na gyara na fito inda kowa yake bayan nayi sallah. Mazan sun fita zuwa masallaci mu matane muka rage a cikin gida sai ga Nafisa da kawayen ya sun shigo taron mu. Da murmu muka tari juna da su kowa yana mamakin dalilin shakuwa na da su darrr ake zaune dasu kamar ana ga masu cuta a jiki ko kuma masu wani aikin kissa. Sun fahinci cewa kowa yana jin haushi zuwan su gidan a lokaci da yake basu da kunya sai cewa Nafisa tayi ni dai ba gurin uban kowa na taho roko ko maula ba gidan dan uwana ne nazo dole kuma nayi yadda kowa keyi. Nam suka so kaurewa da maryam da ita dama ba shiri tsakanin su tun gida Allah ya kawo yaya ya daka masu tsawa tare da masu fada suka daina. Kamar yadda Nafisa tace yadda kowa yayi haka zatayi don gidan dan uwan ta ne hakane kuwa tayi. Don mikewa tayi ta kwaso abinci gudan mai yawa ita da kawayen ta komai na gurin sai da ta debo masu shi duk an saka masu idanuwa na ce su zo muje dakin Iyya can muka zauna tare da ni dasu da ma maryam din . Karshe suka shiga bamu dariya tun maryam na daure fuska har ta shiga dan murmusawa hiran da sukeyi mun dauki lokaci da sune sukace zasu tafi ina tsaraban su don shi ne sukazo tun yau kada a wawashe a barsu. Nace tsaraban ku ya na hanya sai zuwa ranan Thursday ku shigo na baku naku Raina tace kai uwar dakin mu walleh kada ki sa muyo tahiyar banza mu taho bamu ga yan, kudin man, mu kuma bamu ga tsaraba. Nace shim banita nice ku taho ba walleh na,sayo maku tsaraba tun can da sunan ku na sayo shi . Wani ihun dadi suka yi suka tafa tare da shewa shiya sa muka son ki uwar dakin mu don ke dauki duniya simple ba ruwan ki da wani jiji da kai ko kyamatar halin mu gare ki. Nace kai amma dai anty akwai ku da wani irin magana lalura ta Allah shi yaye maku ita bayan ita minana gare ku na kyama tunda dai nagani da idona kuna sallah to miyarage kuma watan azumi anan kuka daukan abin buda bakin ku to mi aka so. Nan dai mukai sallama dasu na fito na raka su har bakin kofa na juyo muna dariya. Yaya Sagir yace Fatima ina kika kwaso wanan gayyan tsiyan haka,wa yan nan mu,amula dasu ba alheri bane fa . Yaya bashar yace ai kuma kaji matsalan mutanen mu ke nan wallahi sai a dinga gudun mutum shi ke kara jefa su ga halaka sosai wallahi . Yanzu yadda kaga Fmta sake da Fatima haka duk yadda ta juya ta zata bi don bata kyamace ta ba kaga zata iya mata nasiha har yai tasiri a kanta idan ma wani magani ne yadda da shakuwa zai sa ta yarda tasha koma may nene. Shiru Sagir yayi yana sauraren maganan bashar yace bai kamata ace kuna nuna mata kyama haka ba kujawo abinku ga jiki da sannu kuna mata nasiha kuna bata taimako har ta gane gaskiya idan tana da rabon dainawa. Amma gaskiya nisan ta kai daga mai shaye shaye yana kara jefa su ne a cikin halaka kawai. Shi kan shi yaya Sagir maganan tayi tasiri sosai a ranshi sai yake ji daga lokacin zai yi kokarin ganin ya jawo Nafisa a jikin shi ya taimaka mata.
****** ********* ****** Washe gari muka tafi gidan su mama muka gaida su suke cewa ai da mu bari suzo su samay mu su tare mu . Yaya yace haba kai ai mune masu neman albarka a gurin ku dole muzo inda kuke mu nema. Mummy tazo dakin mama ta samay ni nan muka zauna ana hiran tafiyan mu tare da mukayi a saudiya. Duk hiran mu Amira na gefe a zaune mugun halinta yana cinta a lokacin bata saka bakin ta ba. Mummy da ta fahinci haka tace aike Fatima sai ki godewa Allah don Allah shi ke azurta bawan ya duk sanda yaso. Yau ga shi kece a wanan kasashen duniya ga yaran gidan mu da suka tashi a cikin daula wasu ko Abuja basu sani ba balle wanan irin kasashen da kika shi ga haka. Maji tace ai ubangiji miskarraziratin ne shi ke yin da yaso da bayin shi a duk inda yaso. Yanzun baga shi ba hajiya da gidan wani akakai wanan auren ai wani abin sai dai mu hanga a cikin gari ko a makwabta kawai. Amma yanzu kinga hikimar manya da mijin da matar komai gida,yake dawowa gaba daya shine ai ake cewa duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau sama baya hango shi. Yaya sadauki dake gurin Baba tun shigowan mu yana mashi bayani akan tafiyan mu irin nasarorin da yayo a gurin wasu masananta da ya saka hannun jari acikin su a waje. Yace to ke tashi mu tafi hakana ko mun bar iyya gida ita kadai mama tace yanzu yarinya na zaune tana hira zakace wai ku tashi ku tafi. Mummy tace yanzun fa ya san dadin iyalin shi bai son zama inda muke kuma . Yai murmushi yace wallahi mummy ba hakana bane kawai da Iyya Rabi da muka bari a gida ne ga kuma mutane suna zuwa taron mu har yanzu. Mummy ai da zaku bamu daki a gidan nan sai munfi jin dadin zama a kusa da ku dariya sosai yaba mummy har saida tayi tagaji don kan ta. Mama ta saki ajiyan zuciya daga inda take zaune bayan mummy ta fita daga falon tace Allah sarki ubana har na rasa farin ciki da jin dadin da zan nuna dana gan ku a gaka wallahi. Yace kai haba maji falalar adduan ki ne fa yakaimu ga haka baki dayan mu ko Amirah yana takalar Amira da yaga ta cika ta batse da shi. Mama tace kai amma babana baka da zuciya duk wanan iskancin da take shukawa mutane don taga ta samu guri. Amma katsaya wani kulata can wallahi Amira da kake gani na kusa fita bayan ta muddin bata fitar da miji tai aure ba mu huta da bakin iya shegen nan nata. Sadauki ya kwantan da muryan shi kasa cikin sanyi yace maji kiyi hakkuri don Allah nima wanan karon na dawo da wanan kudirin a raina ina son naga tayi aure itama ta kama dakin ta hakana ta huta da fadan ki. Damu da ita dukkan mu dole ne muyi maku biyayya kada ki damu maji zata fito da miji itama tai aure badadewan nan ba zamu sha buki insha Allahu. Mama tace Allah ya bada ikon yin hakan ga maryam har tana batun haihuwa ita ko ajikin ta. Sai wanan lokacin Amira tai magana tace ikon Allah maji gama wanda suka aure basu da komai saini da ko auren banyi ba ake min gori. Wani iri naji a raina da magansn da tayi nasan ni takewa gori a fakaice naji sadauki na fadin lokaci ne baiyi ba Amirah wata rana sai labari. Kiyi hakkuri gaskiya ake fada maki ba wai ba,a sonki bane aure shine darajan diya mace zan zo mu zauna dake sai muga may yadace ayi. Baba ya aiko akira mashi sadauki yafita yakoma dakin baba din ina zaune nai shiru don gaba daya jikina yai sanyi da maganan Amira. Don na fahinci so take ta jawo min wani sabon matsala a rayuwa na ganin yadda nai shiru cikin damuwa yasa mama kokarin sani magana tace. Waiko Fatima na kin ko ga yadda kika koma kamar wata diyar larabawa dake can aini da a hanya nagan ki bazan gane ki ba gaskiya babana ya iya kiwo sosai wallahi haka duk uwa ke son ganin diyan ta a cikin farin ciki. Sai aita hakkuri da rayuwa don hakkurin bawa bai taba tashi a banza insha Allahu. Amirah ko maganan mama bai mata dadi bane sai mikewa tayi kawai tashige ciki abinta tabar mu inacewa mama. Mama insha Allahu kuma yaya baida matsalan komai wallahi don duk wanan halaiyar nashi ina gani kamar yanzun duk ya kawu. Sanan mama irin mutanen da yaya yake zama dasu abune mai wuya mutum bai fada cikin halaka irin tasu ba. Amma sai naga shi yana kokarin yaga ya kare hakkin addinin shi a cikinnsu da muka je can. Mama taji dadi tace masha Allahu Allah na gode ma abinda nake matukar son ji ke nan Fatima nan mukaai ta hira iina bata labarin tafiyan mu har haduwan mu da Linda a can da mahaufin ta. Sadauki yana shiga gurin baba ya samay shi zaune yadda ya,barshi da carbi a hannun shi yana tasbihi jin sallaman dan nashi ya dago kai da sauri ya kalli dan nashi mummy tana daga gefen shi a zaune. Yace na manta na fada maka cewa muna umurah an shigo dakin nan nawa an min barna wallahi. Da sauri sadauki yace subbahanallahi baba yace wallahi an kwashe min duk agogaiya na masu tsada dama wasu yan abin amfani na bazan ma iya cewa ga iya abinda aka dauka ba ciki. Sadauki ya saki ajiyan zuciya yace amma baba sai naga kamar barawon waje zai iya shigowa gidan nan kuwa ashe ? Babada mummy sukace ba daga waje bane koma,waye a cikin gidan nan yake daya daga cikin yaran nan ne yai min wanan aikin. Sadauki ya kara ajiyan zuciya yace indon agogo ne aida ka fada min tun muna can da an sayo maka wasu daga can munzo maka dasu ko yanzu naga kamar Fatima ta sayo ma agogo guda biyu a Dubai masu tsada da kudin da abokaina suka bata can. Baba yai murmushin jin dadi yace ikon Allah kaga hukuncin ubangiji ko ? Yace Allah yai maku albarka yabaku zuria masu albarka a rayuwanku. Mummy tace nifa abinda yafi tayar min da hankali shine takardun gidan nan da ba a gani ba har yanzu wallahi. Sadauki a razane yace subbahanallahi may kuma za,ayi da takardan gida da za,a dauka ? Baba yace nayi zaton ko suna ganin kamar takardan wani abune suka hada hardashi akwai dai abinda sukazo nema a gidan nan. Sadauki yace insha Allahu zan sa aimin bincike a tsanake ko za,a gano wanda yai wanan aikin haka. Sun jima suna maganan shida baba da mummy ya kwantar wa baba da hankali yai masu sallama yadawo dakin mama. Nan yasamay mu yake cewa mama ashe abinda ya faru ke nan bayan tafiyan mu anshigawa baba dakin shi. Mama tace ni ina ganin yaran gidan nan ne sukai wanan aiki Allah dai ya shirya ko wanene abin baiyi dadi ba wallahi don ta gurin A C din shine suka shiga yadda ba wanda zai gane an shiga dakin. Muna hanya yake cewa kai gaskiya ko waye yai wanan abin bai kyauta ba takardun da aka dauka yafi tayar min da hankali wallahi. Nace Allah ya tsare kada mai shi yayi wa baba bar na da takardan yace nima shine damuwa na wallahi. Har muka kawo gida ba wanda yai magana a cikin mu kowa da abinda yake tunane a zuciyar shi.
****** ********* ****** Sai bayan kwana hudu kayan mu suka shigo gari nan na fara rabawa kowa tsara ban shi har gida sai da na aika masu kuma nace zan tafi amma sai yaya ya hana yace na bari sai an kwana biyu don zamu koma school lokacin. Maryam ta gama karatun ta saura ni na rage yanzu don haka na koma ni kadai ce ke moving a makaranta. Ga idanuwan mutane a kaina duk da ina kokarin kama kaina a matsayina na matar aure kuma musulma. Amma sai kaji ana gulmana wai suturun danake sawa da motan da nake shiga ya zarta na sauran mutane. Kullun fa a cikin hijjab nike amma mutane saboda sa ido har suna fahintan may ke cikin jikina. Dole ne don duk wanda ya sanni a baya babu mai ganina yanzu bai san akwai canji a rayuwana ba. Banda matsala don ina maida hankalina sosai ga karatuna ba sai na tsaya wani loveying ba akan makin dina. Na dawo a gajiye daga school da wuri na shigo gida don yau Friday na idar da sallah ina kwance saman sallayan da nai sallah hannuna da carbi ina ja. Ya shigo dakin nawa yana saye da farar shadda tasha aiki a jikin ta sosai sai maiko take yi. Na dago kaina a hankali na kalleshi yadda na ganshi na fahinci bai cikin dadin rai a lokacin . Mikewa zaune nayi da kyau ina mashi barka da jumma,a ya amsa min tare da zama a bakin gadona. Inda yake zaune na tako na zauna daga gefen shi na kalleshi cikin natsuwa na sakan mai lalausar murmushi don in isar ma zuciyar shi da sako. Nace wa ya taba min sadaukina kuma yau haka zai bata muna jumma,an haka ? Ya dan kakaro guntun murmushi tare da dan jan guntun tsuki yana cewa . Fatima al,amarin yaran gidan mu ne yake bata min rai wallahi yanzun ace duk yadda Baba yai kokarin ganin ya inganta rayuwan mu amma babu wanda ya mayar da hankalin shi ga abinda ya koya muna. Nace yaya ai yan uwanka duk yan uwan ka ne don haka ni sai naga kaman yanzu abinda ya dace shine ka taimakawa yaya Sagir da yaya Abdul su da ke tasowa yanzu ko Allah zaisa a dace ta gurin su. Murmushi yayi tace tunanen mu yazo daya danaki ke nan abinda na dade ina kudurtawa a rayuwana ke nan a kan su. Zan dauko sagir na saka shi a jikina sosai yadda zan samu Allah yasa muna hannu ko za,a samu dama ga al,amarin. Don kinga yanzu ni nan da wasu shekaru dole na bar zancen buga ball din nan da nakeyi don in girma ya kara kama ni ba zan dawma ga wasan ball ba. Shiyasa yanzun ma nake ta kokarin ganin na samu inda zan kafu da kafana koda na daina wasa ya kasance ina da wani madogara da zamu ci musha a cikin shi. Tausayi ya bani don nasan yaba da nauyi da yawa yanzu a kan shi don duk wani lalurar gidan su shine maiyin a yanzu. Nace bayan duk munyi shiru ba dan lokaci mai dan tsawo kowa na tunane a ran shi. Yaya yan uwaka ne na jini dukkan su kuma bakai kade suke yan uwanka ba a yanzu nima sun zama yan uwana na jini. Duk abinda su Umma suke gwada maka kan su,suke gwadawa, abinda basu so su gani yau Allah ya yayi suna gani da idon su. Kaine kuma mutum mafi daraja a cikin gidan mu a yanzu don haka saka masu da,alheri sai aniyar su ta koma masu. Nakai kaina saman kafadan shi tare da dan shafo fuskan shi nace sai kai tunanen inda ya dace ka saka su. Rugumoni yayi zuwa jikin shi tare da sauke ajiyan zuciya yace maganan ki Fatima ya bani kwarin gwiwa a yanzu sosai zanyi yadda ya dace dasu din zuwa wani sati zajiji may muka shirya akai idan naga bashar. Nace nagode yaya aikin na Alheri allah ya kara daukaka shi akoda yaushe Allah kuma ya tsare muna kai daga duk wani abinnki. Ba mu sake junan mu ba ina makale a jikin shi ina shakan kamshin jikin shi maidadin amowa. Sannu a hankali bayan ya dan samu natsuwa naji yai dan gyaran murya a hankali ya soma yi min magana yana cewa ina ta kokari naga kin fara sana,a Fatima. To amma kuma bazan iya bari kina fita ba akoda yaushe don sana,an mata abune dake yawan dauke masu hankali ga harkokin su na cikin gida. Bazan so hakan ya kasance dake ba Fatima nafi son kalar sana,an da kina gida kudin ki suna shigo maki ga account din ki kawai. Wani irin sanyi ya sauka min cikin raina nai maza nace mashi nima yaya ba zanso abinda zai sani na raja,a da bautan Allah na ba ko kadan. Cikin zuciyana naji kanar nace mai to ko muyi sanan kayan dakin mata show room.kawai sai da ma,aikata maza kawai su zauna a gurin. Amma sai naji tsoron fadin hakan don ban san irin tanadin da yai min ba a zuciyar shi. Yana makale dani a jikin shi yake cewa zan kara dubawa nagani idan akwai wani harka mai sauki da zai yiyu. Amma don Allah koma may nene za,ayi ki yi kokari kiyi adalci tsakanin mu kada ki so kanki da yawa a ciki. Nace mashi insha Allahu yaya bazan raja,a ba ga son duniya akan ka yaya sai naji yayi murmushi kawai alamar yaji dadin a ran shi. Sai da ya mike har ya fara tafiya yake cewa yau fa ina ganin mutumiyar ki kamar tana labor ne don nakira wayan Bashar dazun yake ce min wai suna asibiti da ita tun safe. Da sauri nace anty maryam Allah sarki nan na fara murna da adduan Allah ya raba lafiya .