Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 108

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 108

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 108: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 108. ****** ********* ****** Da,sannu yau Allah yayi mun gama exam…

2,458 words

****** ********* ****** Da,sannu yau Allah yayi mun gama exam din final din mu gaba daya sai dai fatan alherin Allah ya ba da sa,a kawai wa kowa daya zana exam din shi a matsayi finalist. Muna gamawa da sati biyu muka daga zuwa waje da yaya sadauki inda ni kaina ban san tsawon lokacin da zamu dauka a can ba indan mun tafi. Mun fara zuwa kasar hongkong, inda muka share kusan wata daya a kasan muna hutawa kawai. Dani dashi sai dan mu Amir da yanzu yayi wayo sosai zakace watan nin shi ya zarta ya kai shekara ma. Sosai nake jin dadin yadda muke rayuwa a wanan kasan a tsakanin mu ukun nan inda sone da kauna tsantsanta ake gwadawa junan mu. Don kowan mu yana son dan uwa mun shaku da juna fiye da tsanmani komai a tare mukeyin shi. Zai kwashe yai ta yawo da mu muna ganin gurare tare da yin photuna masu kyau. Mun bar kasan zuwa kasar Beselona inda zasu buga kwallo da,aka dauke shi wani contarack mai tsada da kudi masu yawa. Ina zaune ina kallon shi yana shirin abubuwan da yake bukata da zamu tafi dasu a gurin wasan Can ya dago kai ya kalle ni ya sake min laulausar murmushi ya ce kina kallon yadda mijin ki ke fita,gurin neman kudi halaliyar mu ko ? Tsab ya,shirya cikin wasu kananan kaya sai ga wani abokin shi Daniel yazo dashi zamu tafi na,dauki dan jakkan da na saka kayan mu a ciki muka kama hanya sai gurin da za ai wasan ball din. Muna isa ranan naga inda,akasan muhinmancin wasan kwallon kafa don naga taron dan mutum da ban taba gani ba a duniya. Wata baturiya ta karbi Amir a hannu na da sauri tace nima na biyo ta nan muka shiga wani daki ta miko min riga mai tambarin yan wasan inda shima Amir din ta saka mai rigan yan kwallo na yara mai tasu tambarin. Hijjab ne a jikina irin dan karamin nan ta karba taje ta sa aka buga mai tambarin su nasaka rigan saman dogon rigan dake a jikina tare da hijjab din na take na saje da duk wanda yake a gurin. Suka miko min wani dan abin wasa kamar hure wai na rika nikan na samu abin yiwa Amir wasa dashi. Muna fitowa a wani guri da,sai wanda aka yarda dashi zai shiga gurin nan naga yan wasan kwallon duniya birjit dasu suna ta mota jikin su kafin a,shiga filin. Can na hango sadauki rana,na,farko dana fara ganin shi saye da kayan su na yan kwallo yana ganina ya bar abinda yakeyi yanufo ni yana murmushi. Nan sauran abokan shi ke tambayan shi wai matar shi ne da dan shi yadda ya rugumay mune ya tabbatar masu da amsan da suke son ji daga bakin shi. Don hada kaina da nashi dana,Amir yayi guri daya a hankali yake fadin kiyi min addua Fatima Allah ya bamu sa,an wanan wasan da za,a buga a yau. Nace yaya Allah ya tabbatar da alheri yasa a,dace da abinda akazo nema ta hanyan alheri. Yace amin nan yan jarida da sauran median suka shiga daukan mu hotuna kalakala. Kyau, kudi, ilimi yanzu duk Allah ya bani don haka gwargwado zan iya gogaiya a cikin wa yan nan mutane. Muna sahun gaba cikin officials muka fara fitowa bayan yace wa matar nan ta kula damu amana please. Muna futowa guri ya kaure da wani irin ihu wanda yasa na daga kai na kalli fadin gurin sai da gabana ya fadi sosai naga gurin yana juya min. Kujeru aka bamu muka zauna bamufi minti biyar da zama ba suka fito a jere dasu ana taken team din su. Sai flowers ake watso masu ta ko ina can na hango wasu da irin furen da aka bani a hannkali nakewa dana wasa dashi yana dariya. Sai daukan mu hutuna akeyi tako ina nan bayan sunyi taken kasan tasu aka fara shirin fara wasa. Wasa yakai wasa guri ya rude sosai mutane sai faman ihu suke inda sai ranan nan nasan muhinmancin kwallon kafa da kyau. Tun ina kallo ban damu ba,sai gashi da,wasa yai wasa da kaina nake daga Amir ina nuna mai wasan . Wanda idan mutum.ya gani zai dauka cewa wani wasan jin dadi nake mai a lokacin. Har aka tafi half time suka dan huta suna dawowa wasa ya tashi sosa kafin atashi wasan sai da sadauki da wani farin fata suka ci cibiyu babu ko daya . Haba aiko guri kaure da ihin murna nan muka kutsa muka shiga filin akai ta muna hutuna tare dasu suna ta daukan Amir kowa da kalan maganan da yake idan ya dauke shi akai masu photo suna kiran shi little UF. Washegari Naga karamawa ranan sai shaye shaye da lashe lashe da tsotson juna akeyi. Abinda yaban mamaki shine ina zaune na dawo a gajiye wayana ya nuna min sako yashigo. Ina dubawa yaya sagir ne ya turo min da photuna da akai muna a gurin kala kala wasu ma ban san anyi suba ni. Yana tayani murna na mayar mashi da amsa dana gode yayana kawai.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH, , , ,

A hankali na sako kafana waje wanda don samun daula yai wani lub lub dashi fari fatte gwanin ban sha, awa. Yan uwane da abokan arziki birijit a gidan ba masaka tsinke a ko ina na gidan sai motoci xa suka haraban gidan da wajen gidan. A hankali ya zagayo inda nake a tsaye ban yi aune ba sai ganin yan jonarlist nayi a gaba da kayan aikin su. Nan suka fara jero min tambaya ina rike ga hannun sadauki daya makale ni. Sun fara da tambayana suna na da alkata dashi na fara da sallama irin ta addinin musulunci wanda ni ban san ma wai hausa ya canza salo ba inji mutanen dake gurin. Nace sunana Fatima Abdullahi mata a gidan Umar faruq da ake kira da UF dan wasan kwallon kafa na international. Sukace hajiya wani irin farin ciki zaki nunawa mutane a wanan tafiyan da duniya ke ganin kunyi da maigidanki mai tarin nasarori a cikin sa. Nace to Alhamdullahi don gaskiya bazan iya nuna farin ciki da dadin da naji ba a cikin wanan yanayi da muka samu kan mu a cikin sa ba. Sai dai kawai nace nagodewa Allah ubangiji da yakai mijina a cikin wanan matsayin tare da kara godewa Iyayyen maigidan nawa wanda da taimakon adduan da iyayye ke muna muka kai ga wanan matsayin da muke ciki a yau. Nace ina matukar alfahari da godewa Allah da kasancewa mijina a cikin wanan matsayin da ubangiji ya nufe shi da zama a yau. Ina ma kowa fatan alheri a rayuwan shi da fatan kara samun nasara ga duk wani abin alheri da wani ke bukatan yi a rayuwan shi. Mutanen da suka zo taron mu kuma ina mika godiya na a gare su akan lokacin su da suka bayar gurin nuna muna farincikin su a gare mu Allah ya mayar da kowa gidan shi lafiya. Nan suka juya zuwa gare shi suna tambayan shi nashi farin cikin da zai nuna shima. Mai interview din yace Umar faruq Abubakar kayi namijin kokari sosai gurin haska muna kasan mu ga idanuwan duniya a matsatin ka na babban da wasan duniya da ake ji dashi a wanan lokaci tare da kuma jawo wa kasan mu nasarori gurin harkan ci gaban ta. Wanda a yanzu babu abin da zamu ce sai mu maka godiya don wanan halakar nasarorin da kajawo wa kasa zata kawo ragewan zauna gari banza ga matasan da suka gama karatu babu aikin yi a tare dasu. Yace insha Allahu haka nake fata don wanan kamfanonin da za, a bude zai bukaci ma, aikata kimani dubu ashirin da biyar a ko ina na sassan kasan nan maza da mata indan har mutum yana da takardun da muke bukata a gare shi. Dama wanda baiyi zurfin ilimi ba za, a samu daidai dashi asaka shi a inda ya dace. Mai tambayan yace masha Allahu mujin dadin jin wanan dibin nasaran da kasan mu ta samu ta dalilin ka wanda muke fatan samun haka ga sauran matasan kasan nan masu kishin zuci kamar ka nan gaba. Sai dai baza mu barka haka ba ko zaka iya fadawa duniya da masu sauraren mu ko shekaran ka nawa a yanzu. Sai da yai dan murmushi tare dan jawoni a jikin shi kadan yace yanzu shekarana talatin da daya cif insha Allahu. Yace yayan ka nawa matan ka nawa ? Yai dariya tukun yace matata daya gata nan a kusa dani kana ganin ta sai yaro na daya Amir wanda yaci sunan mahaifina watau Abubakar. Yace itace matarka ta farko ko akwai wata a gaban ta? Yayi murmushi yace itace mata ta tafarko kuma ta karshe . Don yar uwata ce aure mukayi na zumunci da ita wanda ta zama muna aure na soyayya daga baya. Hakan yasa mutanen dake tsaye suna kallon interview din wasu suka numfasa daga gefe don jin abinda yace . Mai tambayan yace daga karshe wani irin godiya zaka mika ga mutanen da suka taru a nan saboda kai. Ya dan murmushi tare da daga kanshi ya kalli inda mutane suka taru don shi yace ni Umar banda abinda zance wa tan uwa da abokan arzikin da suka taru a nan don ni kawai da iyalina. Sai dai nace inawa kowa fatan alheri a rayuwan shi kamar yadda suma suka taru anan don ni da iyalina. Ina ma kowa fatan alheri shima mutumin yace na gode da lokacin ka da ka bamu shima yace ya gode. Nan suka jaye kayan aikin su suka bamu guri inda muka shiga gaisawa da mutane dake jiran mu a haraban. Can na hango anty Amira da wani dogon mutum a tsaye daga gefe daya na zare hannuna daga rikon da sadauki yai min na nufi gurin ta. Da dan sauri na na rugumota a jikina itama dai ba laifi ta riko ni din tana dan murmushin yake a fuskan ta. Nace anty nayi missing din ku mun samay ku lafiya tace mun dai yi missing din dan uwan mu kawai Bintu. Nasan magana ta fada min don tana fadan haka bata tsaya ba ta wuce zuwa gurin sadauki mutumin yabi bayan ta tabar ni a tsaye nan. Naji an dafa kafada na ina juyawa anty maryamce tace kada ki damu don ko kin saba da halinta yanzu ai. Shigowan su Nafisa ya katse muna zancen mu nan suka rugumoni da farin ciki suna fadin kai matar yaya kin bamu kewa wallahi sosai. Barin Nafisa da mutumin da take tare dashi wanda ta gabatar mai a matsayin wanda zata aura wai. Yayi ya nufo inda nake tare dasu nafisa nan suma suka shiga gaidashi tare da mashi sannu da zuwa suna mai taya shi murna samun karuwan da yayi. Hannuna ya kama zuwa kofan shiga gidan namu wanda yake a rufe a lokacin don za, abude shi da addua don shiga ciki. Malaman da aka gaiyato ne suka bude gidan da addua tare da fatan gamawa da duniya lafiya. Mun shiga gidan da farinciki gaba daya mutane sai yaba kyau da tsarin gidan suke yi. Abincin da aka girka don taron mu aka shiga ci kowa sai da ya wadata yaci ya koshi zuwa yamma mutane suka dinga watsewa daya bayan daya kowa a cikin farin ciki. Ganin an dan rage yawa sai yan gida tsiraru suka rage ba yawa yasa na juya gurin anty maryam nace zan dan shiga ciki anty . Tare da ita muka shiga dakin da yake a matsayin mallakina wanda yasha kayan alatu sosai na zamani don komai daga waje aka shigo dashi a gidan. Yana zaune tare da Amira da Bashar dasu yaya sagir da yaya Abdul suna hira. Muna mikewa ya bini da wani irin kallo na so da kauna yana cewa maryam ki barta ta huta please koma may ye ai zata labarts maki idan kun natsu. Don nasan bakunan nan naku tab yake da gulman da kowan ku ya tara ya tsiyayawa dan uwa. Nace kai haba dai yaya kana iya raba anta da jini ni da anty maryam sai Allah fa. Yace ai na gani na kuma sani don gashi ta haki zaki barni a nan ni kadai. Kai kade kuma yaya inji Amira yace kin san na saba da matata yanzu bamu raba second a tare. Amma wanan da kike gani naga yau tana son nisanta ta dani idan ban yi niya ba. Amira ta kawar da kai gefe daya don ta fahinci i yanzu ba karamin ji dani yaya sadauki yake yi ba har bai iya boye feeling din shi a gaban kowa. Ga wani irin kyau da haske dana kara tare dani ga wani annuri da take gani yana fita tare dani. Lalai kam Bintu tayi sa, a da dace a rayuwan ta na jajircewa da tayi ta mallaki zuciyan sadauki da ma ruhin shi a baki daya. Lalaikam shima din yayi dace samun Bintu a matsayin matar aure a gare shi don mace mai kyau da addini rahama ce ga namijin daya samay ta. Kalli yadda ta koma yana wani ji da ita da dan shi wanda ko dan kukan yaron bai son ji komai nasu gwanin burgewa. Gaskiya yayi sa, an samun mace mai kyau a rayuwan shi da Rahama ce ai bazai wani jin dadin nunata haka ba a duniya. Ba Amira ba kowa ya kalle mu zancen zuci yake a kan mu don ko mun dace da junan mu sosai. Don sadauki za, ace mutum ne mai sa, a a rayuwan shi ga dukiya mai tarin yawa Allah ya daukaka shi dashi. Ga mace ya samu mai kyau da tarin addini tare da ita ta gyara mai rayuwan shi don duk wanda ya ganshi yasan ya watsar da halaiyar shi ta da can baya. Hassada dangin shedan tuni Amira ta mike tana fadin ita zata tafi gida sai anjima kuma. Sadauki yace haba Amira tun yanzu ki tsaya mana har ayi sallah sai ki tafi gida tunda ba koranki ake ba? Tace no bari kawai na tafi don naga kamar kana son hutawa ne da iyalin ka tafice tana cika tana batsewa a ranta. Ya gurgiza kan shi yabita da kallo don yasan abinda take nufi akan Fatiman shi ne take wanan cikar haka tana batsewa ita kadai. Sun dan jima suna hira akai kiran sallah suka mike zuwa sallah nikan muna dakina mun baje da maryam muna hiran yaushe rabo da ita.

Readers Also Read