Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 19

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 19

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 19: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 19. ****** ********* ****** Fitina yakai fita don Jatau ya saka…

2,513 words

****** ********* ****** Fitina yakai fita don Jatau ya saka mama da baba a gaba daya samu labarin bani garin. Haka magana har takai gidan maigari dole sai da aka kira mama taje da kanta. Nan dai ya koro bayani mama tai tsuru tsuru sai kamay kamay takeyi tarasa na cewa gashi babu kudi don har kudin sadakin ta kashe wai tayi sayayya dasu na aure. An basu sati biyu kacal su kawo mai kudin shi ko su dauki hukunci kan ta nan suka bar gurin kan wanan magana. Suna dawowa gida ta saka baba a gaba kan sai dai ya tafi birni yazo dani a daura aure akai ma jatau don bata san inda zata samo mai kudin shi ba cikin sati biyu. Yana gama sauraren ta yace amma kina da wani magana ni ina zanje cikin kano na dauko Rahama ? Altine ce tasan inda ta kaita kuma suna can tare ban san wanda zan tambaya inda suke ba yanzu don ba wanda yasan gidan yan uwan nata. Hankalin mama ya kara tashi sosai har gurin Inna ta taje cikin kwantar da murya take cewa a tsaya a fahinci juna kada abin yakai ga bacin rai. Inna tace rai shi ya dade baici ba ita ko kano bata taba zuwa ba balle ta ce tasan inda muke. Su dai da suka ci kudin shi sai su tafi can su karata dashi ita babu ruwan ta cikin wanan magana kuma daga yau su fitar da rai ga tinanen zasu hada ni aure da wani jatau a yanzu. Mama ta bar gidan cikin bacin rai take cewa yadda ba, a so sai ankai ga yin hakan Inna tace to bissimillah kuma tai mata kashedi akan zuwa gurin ta don babu hadin kifi da kaska yanzu. Haka ta dawo gids cikin tashin hankali ga kwanaki sai matsowa sukeyi tace idan baba ba zai je nemo mu ba ita zata shirya taje kano da kanta ai mai tambaya baya bata sai ta gano inda muke a kano ta dawo dani an mata aure. Yace bissimillah gaki ga hanya nidai banci komai na Jatau ba balle ya damay ni. Haka tashirya ita da Larai kawar ta suka tafi kano tun shigan su garin hankalin su ya fara tashi duk wanda suka gani a bakin tasha sai su tsayar dashi suce don Allah ko yasan wata Rahama tare da Altine mai kulli kulli. Wasu suyi masu daukan mahaukata wasu kuma su tsaya masu tambayan a wani unguwa sukace daku suke ? Basu sani ba sai a barsu a tafi sun koma kamar mahaukata suka dawo gida cikin dare hankali a tashe. Ko sannu baba bai mata ba shiya tayar mata da hankali ke nan ta haufada tana cewa munafuki dama ashe tare dashi aka hada baki don aga bayan ta ai tasan zaman ta dashi. Hankalinsu har baba ba, a kwance yake ba gashi gidan ya fara yi wa baba tsamin har ya fara kewan Innata a lokacin sai dai yana gundu yanuna yaji masifan mama. Har bakon da mama Altine ta aje gidan ta da iyalinshi sai da mama ta tayar mai da hankali tace yasan inda mama Altine take inba haka ba may zai sa ta aje shi gida bata sanshi ba. Nan sukayi tas da mutumin ya nuna mata yafita kwaya dole ta fita batun shi ta kyale shi don yace idan ta sake shigowa ta tayar mai da iyalin shi hankali kan abinda bai shafe shi ba sai yai mata tsinanen dukan da sai an kaita asibiti ta kwanta. Gidan Lairai taje neman shawara nan dai suka kasa kai mafita ga maganan sai larai ne ke cewa nifa ina ganin mafita daya ne a gareki yanzu shine ki daure ki bashi daya daga cikin yaran nan a zauna lafiya. Cikin mamaki mama tace wa kawar nata Larai yaushe kika fara hassada na a garin nan ban sani ba Jatau ne zan dauki yar cikina naba aure ko may ? Larai tace to may ye a hakan ba mafita muke nema ba ko kina da jakka dari da tamanin da zaki ba jatau ne kudin shi. Nu naga haka shine mafita kawai cikin wanan magana ki samu a zauna lafiya don kin san dai Jatau bai daukan kaddara shi. Aiko mama tai cikin Larai da masifa suka dinga tonon asiri a tsakanin su kaca kaca sukayi tabar gidan Larai a hasale kowa ya kama gaban shi daga ranan. Duk wanda yaga mama a lokacin yasan tana cikin tashin hankali sosai don ko ba, a fada ba duk ta ramay ta fita hayacin ta fa fitinan yaran ta da yai mata yawa. Don babu ragowa ko kadan tsakanin ta dasu sai cin mutunci kamar ba uwarsu ba. Ana cikin haka akace an kama Rukkaiya da mai nama a shagon shi suna lalata wanda dama ba ranan ne farkon yin haka ba a gare su. Nan wani sabon magana ya bi gari kwaaa ga kauye da iya daukan magana ko karami ne balle irin wanan. Da labari yaje wa Inna tace ita kan dai ta godewa Allah da yaraba ta salin alin da wanan fitinanen gida a wanan lokacin. Ranan komawan su gurin maigari yazo dole ba don taso ba ta hada dubu goma da kyat koshi sai da ta sayar da yan kaddarorin ta ta samay su. Bayan ta gabatar da kudin da tazo dasu ne aiko Jatau ya buga kasa yace bai san da haka ba shi kudi shi minamina yake so don ba zai dauki hasara ba baiga mata baiga kudin shi. An kai ruwa rana so sai a gurin dole aka bata zabi idan babu kudi a turasu kotun birni ko kuma ta samu mafita ta bashi kudin shi. Maiunguwa ne ya kebe da ita gefe ya bata shawara ta bashi yarta daya a wuce gurin don idan ta bari aka tafi kotu daure ta za, ayi can babu kuma may sanin inda aka kaita. Kuka ta saka ma maiunguwa tana cewa ya cece ta yai mata rai ita bazata iya ba Jatau yar ciki ta ba yadda yake din nan gashi kazami fa tsufa ga rowa da cin mutunci. Maiunguwa yace ni wanan shawaran shine nake gani kawai mafita a gurinki a wuce gurin don gujewa shigan ki gidan yari. Bata da zabi dole da wanan shawaran suka koma tabarman mai gari nan mai uguwa ya gabatar da shawaran da sukayi da ita. Baba dake zaune yace idan haka zai kashe maganan shima ya aminta da hakan . Aka tambayi Jatau idan ya yarda da hakan yace sai dai yayi maneji don dai shi ba cikin su yaso ba. Mama naji ta dago kai ta kalli Jatau mutum haka a kazance har yake kiran wai maneji zaiyi da yarta. Muryan mai gari taji yana tambayan su daga cikin diyan wacece zata bayar. Nan wani sabon tashin hankali yazo mata to ita wa zata bashi don duk yaran nata ba mutunci ne dasu ba ai. Babu wace zata fahince ta ta fitar da ita wanan kangin da take ciki cikin ruwan sanyi. Sai bude baki tayi tace kai kai Rahama Allah ya isa tsakani dake da uwar ki da kika jefa ni wanan halin haka. Maigari ya matsa mata tace a bashi Rukaiyya nan jatau yace wa shi Allah ya sauwaka mai yarinyar da ta zama ba gari dadi zai aura yagane may gurin ta. Ran mama ya kara baci tai cikin shi da masifa karshe dai da aka kai ruwa akai rana yace sai dai Lawisa dan dama dama zai laba da ita hakana. Haka a kawatse kan za a daura aure nan da sati daya ta tare dakin ta mama ta dawo gida cikin bacin rai ta isa gida har da suma sai da tayi hankalinta ya tashi baci ba sha ta shiga wani hali na tashin hankali.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KI RIKE AMANA DON NAUYI GARE SHI YAR UWA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA DON GIRMAN ALLAH, , , ,

Muna nan jikin yaron yaki dadi dole anty ta kira mahaifin shi a waya take sheda mai yau Nasir jikin ba dadi don har da amai yayi sau biyu Yace yanzu zai turo hamza driver yazo yakai shi asibiti amma ni yanzu na sha magani ba zan iya fita ba gsskiya. Yace ko da mama ce ta kai shi mana asibitin tace ba damuwa tana gama wayan lokacin ina tsaye na rike hannun shi sai cewa tayi ki shirya shi ku tafi asibiti yanzu driver zai zo. Da sauri na dan kalle ta nace asibiti gabana ta fadi na farko ga dare yayi na biyu ban taba shiga ko asibitin garin mu ba balle na birni irin kano san nan ma ni a wurina dan wanan ciwon ne za, a kai har asibiti. Ganin nayi shiru tace dani ko akwai matsalane naga kaman kina tunane akai ? Dan dariyan yake nayi da bai kai ciki ba, kawai nake cewa da ita ba komai anty. Amma gabana sai faduwa yakeyi sosai haka na shirya driver na zuwa muka fito don tafiya asibitin. Can naji tana cewa da driver ya tabbatar da bai barmu mu kadai ba don ni ba kuwa ce ban san gariba sai lokacin nadan ji sanyi a raina. Tafiya mukeyi yayin da Nasir yake kwance a jikina jikin shi yai zafi radau. Amma ni sai faman kallon yanayin garin nakeyi ga kwan haske wutan lantarki ya haske ko ina na garin. Wani katon guri muka shiga naga motoci an parker iri iri a gurin nan ya samu guri shima ya parker tamu motar. Ya bude don ni ban iya bude motan ba ma muka fita ina rike da yaron shine ya karbo family file din su muka bi layin ganin likita. Sai baza ido nakeyi ina kallon yanayin mutanen birni yadda suke harkokin su ba ruwan wani da wani na lura ba mai ko gaida wani sai dan wanan yabi can wancan yabi nan. A haka har aka kira mu Hamza driver yace na shiga da yaron ciki shigan mu office din ya dawo mun da burina na son zama likita ko nurse. Komai na office din a tsare yake nan ya nuna min kujera muka zauna yai muna yan tambayoyi akan ciwon yaro na bashi amsa. Bayan ya gama yan rubutun da zaiyi a cikin takardan ne ya miko min tare da cewa muje lab da yaron. Nafito Hamza ne ya kai mu akai koma suka gane maleria ne kawai ya kama shi nan akai mai allurai muka juyo zuwa gida. Sosai yaron ya samu kulawa a gare ni haka shine ya jawo mun shakuwa dashi fiye da duk sauran yaran da nake dawai niya dasu nata. Shakuwan da yaron da bai yarda koda iyayyen shi yasa anty matukar mamaki take cewa lalai Rahama kinci sunan ki wanan mara yardan ne har yake manne dake haka ko yaushe. Ai Nasir da kike gani tun yana goye baya da yarda sam da kowa ko yaushe yana like dani. Da ya fara wayo ne kuma koni din baruwan shi dani kullun yana make gefe daya shi kadai. Nace anti baku fahince shi bane akwai abubuwan da baya so kuma hallitan shine hakan. Na fahinci ita anty irin rayuwan turawa gare su nabawa kowa freedom din shi don har yaran sai abinda suke so ake masu. Ni kan ai a gare ni ya kwana gidan sauki dama ina da son yara don haka sai nabiye masu amma cikin hikima nake gyara mata tarbiyan su. Ganin yadda ta ya mutse ne a yadda na san ta yar gayu a baya ranan nake cewa da ita Ina son nayi kitso kaina yana damuna. Tace kinga sai mu tafi tare a gyara muna kai ni dai ba kitso zanyi ba sai dai a wanke min kaina kawai. Tace shirya da azahar mu fita mu leka saloon din don kiga guri. Ni dai ban san ina ne saloon ba na dai ce da ita to ne kawai na shirya kamar yadda tace din muka fita. Ita da kanta take jan motan ina ta kallon ikon Allah ashe dama ta iya tukin mota mace da ita. Wani katon shago naga mun tsaya sai mata ke shige da fice a gurin an rubuta a gurin saman wani katon abu da rubutu mai launi tare da hoton mace da gashi dogo da akaja. ASSAMA,U SALOON waje ne dake cike da manyan mata masu fada aji yanayin masu aikin gurin ba namu bane don shigan matan kasan larabawa ke jikin su. Na kara ganin wani guri an rubuta haka PEDICURE & MANICURE Anty tace zo mu fara shiga nan muna shiga na fahinci ba bakuwa take a gurin ba don naji suna cewa a hajiya kwana biyu baki leko mu ba ko lafiya ? Ta dan yi murmushi tace kin san jikin ne sai a hankali yanzu ni tace a fara yiwa ina ta faman kalle kallen abinda akeyi a gurin. Gaba daya naji yan gurin nata faman yaba kyauna da dadawa ni dai bangani ba sunce na kalli mirro amma na kasa don kunya. Har kai na sai da aka yarfa min kitso masu kyau kanana nai mamakin irin saurin mutanen Da akai wa anty sai naga gaba daya ta canza min ta koma kamar wata yar karamar budurwa da ita sai ka rantse da Allah ba itace muka shigo ba a ya mutse. Haka muka dawo gida shar damu tun shigiwan mu mama ke fadi kai kai kai wai ko Rahama ce nake gani ko gizo idona ke yi min. Falo muka zauna sai naga ta baje rigunan da muka sayo a kusa da ita tana fitarwa daya bayan daya ta sake duba su tare da yaba kyawon su. Gaba daya ta miko min su gaba na tana cewa a kashe lafiya sai na samu lokaci akwa wanda zan kara duba maki a cikin kayana sai ki kara. Daga yau bani son ki kara saka komai da kikazo dashi daga kauye don matan gidan nan yan rainin wayo ki dinga kwalliya kamar kowa a nan kina gyara jikin ki a kai akai. Kafin nakai ga godiya ta daga min hannu alaman a, a bata son haka shigowan yaran da suka dawo ne yasa muka mai da hankalin mu gare su baki dayan mu. Yau da kuka Amira ta shigo wai Nasir ne ya buge ta a mota anty tace oya kije gun anty Rama ta cire maki uniform. Kallon mamaki naga yaran na min ai dayan yar gurin zulfa take cewa wanan anty Rahama ce mummy. Gaba daya dariya akasa anty ce a to sunga yau kin sake masu kin zama wata yar birni dake haka nake son kowa yaga yar kauna nawa ya yaba maki don badai kyau ba kan sai dai wani abin kuma. Muka kwasa dani da kayana dasu muka shige ciki a tare gaba dayan mu. Bayan shiga na ne mama ke cewa ikon Allah watau gyara shine mutum mutumin kauye da ta gyara akafi watau.

Readers Also Read