Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 20

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 20

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 20: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 20. ****** ********* ****** ****** Yau tun safe dana tashi banji…

2,706 words

****** ********* ****** ****** Yau tun safe dana tashi banji duriyan ta ba sai ni da mama ne ke faman dawainiya da yaran har suka gama shiriritan su suka wuce school. Lokacin ne nake cewa mama yau ban ga anty ta fito ba don takan fito su gaisa da mama wani lokaci ma a falo zata dan zauna har sai yaran sun fice daga gidan amma yau shiru banji duriyan ta ba. Dakin nata na nufa a hankali na tura kofan dakin don na dubata na hangota rufe a cikin bargo tana rawan sanyi. Da sauri na karasa gurin ta ina cewa anty lafiya kike kuwa maganan ta baya fita don haka na bude bargon da take rufe a cikin sa. Gabana ne yai mugun faduwa don duk ta fita yacin ta cikin murya mai makyarkyata nake cewa anty jikin ne ? Da kyat ta iya cewa Rama taimaka min miko min wancan abin maganin nawa kibani na sha, ga wani irin numfashi da takeyi kamar zata shude a lokacin. Da sauri na dauko abin maganin tana nuna min na juya zuwa waje don na dauko goran ruwa tasha. Hankali tashe nake fadawa mama halin da Anty ke ciki naga hankalin ta yai matukar tashi sosai tabi muka koma dakin tare. Na bata maganin tasha da kyat ganin yadda jikin nata yake nace da ita ko akwai taimakon da zan iya maki anty ? Na tambaye ta cikin dukawa kanta ina son inji may zata ce dani sai alama taimin na rufa mata bargo a jikin ta. Haka muke a kanta cikin tashin hankali yadda naga tana shan wahala yasa na fita daga dakin dakin mu na koma na takure kaina ina faman kuka. Ba abinda nake tunane sai irin taimakon da boyar Allah nan take min yanzu idan wani abu ya faru da ita aiko diyan ta sai na fisu shiga uku. Muryan mama ne naji tana kiran sunana shi yasa ni fitowa daga dakin da sauri da kaga idanuwa baisai amfadawa mutum na darji kuka bane. Mama take tambayana ina kika shige ne tundazu kije Saade na neman ki a dakin ta da sauri na karasa dakin ba laifi na samu ta yaye bargon dana rufa mata a jikin ta. Ba laifi don tabar rawan sanyin da take yi da farko murya a wahale take magana dani. Ramana don Allah taimaka min ki matsa min kafafuwan nan ko zan samu ya sauka min gaba daya. Ba musu na gyara yaye bargon a kafanta na shiga tausa mata kafan ta a hankali ina jin yadda take sauke ajiyan zuciya a hankali. Sai ce min takeyi ta gode jin banyi magana ba yadda muka saba da ita yasa ta dago kai ta kalle ni. Yanayin idanuwa na ne ya nuna mata kukan da sha tace subbahanallahi Rama kuka kikayi ne ? Allah sarki ai wanan ba komai bane don yazo min ma da sauki ai don Allah ya kawo min ke da wuri kin bani magani nasha. Dan fitan nan da mukayi jiyane nasan ya tayar min da ciwon haka amma ya kwana biyu bai motsa min ba da yake na samu hutu yadda ya dace. Tun dare ya fara min gashi ban iya tashi na dauko magani inda yake ke kuma baki da waya a hannun ki. Yakama ta nasai maki waya ki rike don irin haka idan ya taso kina sani nace waya anty tace eh nace ban san yadda ake amfani dashi ba ai. Zaki sani ai baida wuya da ankoya maki zaki gane yadda yake tun ban gani ba nace da ita na gode. Babu wanda ya sake magana cikin mu sai zuwa can a zatona ma ta samu barci ne sai take cewa. Gobe baban su Nasir zai dawo don munyi waya dashi yanzu yake fada min haka. Don haka ina son ki gyara gida da kyau kamar yadda kika saba sai kiyi abincin da zamu tare shi. Amma shi yafi son yaci abinci mai nau,in gargajiya idan zai samu sai ki duba kiga wani yafi maki saukin girkawa a tanadi abinyi. Taci gaba da cewa sai dai idan ya dawo fitinan gidan nan zai dan karu don matan shi zasu dawo don a matse suke ya dawo din daga su har iyayyen su. Don haka abinda nake so dake a gidan nan ki tsaya a inda na aje ki don ba mutunci ne dasu ba. Gabana ya fadi don jin may tace dani tace ina ga ai shike nan zaki iya tafiya ki huta kafin yan rigima su dawo. Sai yamma lis ta samu tafito falo ta zauna har lokacin alama ya nuna bata jin dadin jikin ta sosai ga yanayin ta duk ya dan sauya ko don gyaran jikin da akai mata ne nake ganin canji a jikin ta haka. Aiki nake amma tunane nake a raina don gaskiya ina ganin za, a takurawa rayuwan mu ne idan sauran masu gidan sun dawo. Tunda yadda na fahinta sam babu zaman lafiya a gidan da sauran mata ga alama ya nuna maigidan kamar fitanane yadda yai karfin halin tura mata biyu gidan iyayyen haka kai tsaye kuma aka tsaya ga sai yadda yace za, ayi. Ni dai komai mugun halin su mudfin ina gidan nan bazan bari su kawowa Anty na rashin mutunci ba a gabana ina gani na kyalesu sai dai ayi wanda za, ayi din. Tuwon farar shinkafa na tuka mai da miyan kuka yaji kayan yaji kamshin dadawa yakeyi sosai sai kassan maman rago da nai amfani dashi cikin miyan. Nai ferfesu kayan cikin rago da ban shima hadin hausa nai mai don ban sa kayan an gayun su ba ga miyan. Daga gidan har abinci na kammala gyaran su tsab na koma gurin anty dake daki a kwance na samayta nake fada mata na kammala komai yadda ya dace take cewa kin gama a cikin sa,a don yanzu ya bugo min waya wai sun sauka garin. Su ma matan nashi ina ganin yau zasu dawo gidan don naji yana tambayana ko sun shigo. Nace to anty ki tashi mana ki dan shirya kada a amay ki haka ko ? Murmushi tayi tace kai kaji Rama da wani zance waye bako na a cikin su idan sun samay ni a hakan ? Nace su duka ai tunda sun kwana biyu basu gidan ya kamata su samay ki a shiri ke ma. To yanzu yaya kike son ayi na ce bari na duba maki mai saukin sawa sai ki saka. Duk wanda na ciro sai tace yai mata nauyi da yawa ga kaya shake a wadrove amma bata damu da sakawa ba ita. Sai wani dogon riga light blue mai shara shara baida nauyi tace na miko mata shi ta saka. Rigan yai mata matukar kyau a jikinta sosai gashi dama ta yi gyaran jikin ta sai kyaunta na asali ya fito sosai. Falo ta koma ta zauna nace mata ina zuwa na shige ban dade da shiga ba naji hayaniya a falon amma hakan bai sa na fito ba a lokacin don ba, a nemay ni ba in ba gulma ba may zan fito yi kuma. Duk da dai ina so ganin waye mijin na anty mai irin wanan dukiyan haka mai yawa haka da yai sa, an samun mace ta gari mai halarci irin Anty Sa,ade. Daga kitchen nake jin muryan wata dadtijiya yana tashi da alama fada takeyi don sai na kasa kunne na dakyau naji tana cewa. A kan wanan tsohuwar da ka aje a gida zaka kwaso diyan mutane kuna cuta masu sai abinda tace shine akeyi don ta mai she ka bi can. Dakai da ita Sa, ade duk zan yi maganin ku ne kwanan nan yadda ta hure maka kunne ka tunkuda keyan yaran gidajen su itama haka za, a tunkuda ta tafi nasu gidan. May ma wai kagane ga auren wanan wannan mutu kwakwai rai kwakwai ne wai ni banga abinda kagani jikin wanan maikama da kyankyaso din. Wanan wanan da kake gani bani mussu idan ance ta girmay maka don kana ganin ta haka a fige ne kake mata daukan yarinya karama. Ni dai daga inda nake ba na jin muryan mijin nasu amma matar dake fada naji tana cewa in har tace bata zama da yaran nan don bakin kishin tsiyan ta sai dai ita ta fita tabar masu gidan mai bakin halin tsiya. Yau ko kinki ko kin so duk zasu dawodakun nan su kuma su kwana a gidan nan jarababban baza kawai mai bakin kunatan tsiya. Zuwa can na bar jin hayanitan su haka yasa na fahinci masu fada kila sun tafi ne don naji shiru kamar babu kowa falon. To amma kuma wacexe mai ma anty wanan mugun zagin haka har take kiran ta da tsohowa na ji dai tana fadin wai ta girmi mijin nata shi mijin wani iri ne wai badai yaro ne zai iya tara wanan abinda nake gani ba haka ? Har nagama abinda nakeyi ban ji duriyan kowa ba na koma daki na shige sai da yara suka shigo muyi sallah ne naji suna cewa wai sun raka daddy su sharada gidan su grandma. Ina shirin kwanciya don yau ba fita falo kallo gare mu tunda mai gidan yana gari suna falo da iyalin shi mama kuma har tayi barci a inda tai sallah. Sai ga Nasir ya shigo inda nake yana cewa anty wai mummy kizo ku gaisa da daddy. Nace to tsaya mu tafi tare kaji Nasir na jawo hijjab dina da nai sallah har na nade shi na saka akaina. Nabi bayan yaron muka fita zuwa falon inda iyayyen nasu suke zaune tare da sauran yaran gida baki dayan su. Da sallama na na shigo falon yana zaune saman dan karamin carpet din dake tsakiyan falon nasu, Ya mike kafafuwan shi tare da dora daya akan daya yana rike da wayan shi yana dubawa. Da alama abinda yake a wayan yai matukar dauke mai hankalin shi sosai a lokacin Anty ce na hango ta kishingide a saman dayan kujeran da yake zaune jingine akai. Tana amfani da remote a hannun ta gurin canza channels din tv dake aiki shi kadai a falon da alama tagaji da inda yakai ana news . Kallo daya nai ma inda yake zaune ban iya kara daga kai na koma kallon shi ba, saboda tsaban kwarjin da yai min a idona ga kuma hallita mai cikar zati a tare dashi. Zaka rantse da Allah kace shi din ko saurayine bai ma taba aure ba balle har tara mata har uku haka a gidan shi. Jin na shgo falon yasa anty dago kai tana murmushi take cewa Ramana ga baban su ku gaisa ko. Tun dazu da ya dawo bai samu zama ba sai yanzu ya samu kan shi, gashi yaci abinci sai faman satin tuwon ki yake yi wai ya dade bai ci tuwo mai dadi haka ba. Murmushi nayi nace kai anty kila ma bai yi dadi bane kike zolayana ko ? Fuskan shi a dake duke ya dago kai yana murmushi tare da kallon inda nake lokacin har na kai durkushe ina fadin sannu da dawowa daddy. Yace cikin murmushi yaya na samay ku ? sannu da fama fa ina tajin labarin ki ta waya wurin yara kullun idan muna gaisawa dasu. Sunce yanzu anty tana masu sallah kullun kuma kuna hadda a tare da su don sun karanta kuma na gamsu sosai da karatun su. Na murmusa tare da dukar da kaina kasa ina wasa da yan yatsun hannuna a hankali nace Alhamdullahi. Yace ban da abinda zance dake sai godiya don kinyi matukar kokari gurin taimakawa iyalina da bana nan. Cikin murmushi nace ai yiwa kai ne balle ma ai ba wani aiki don yaran na da saukin kai sosai. Ya dan murmurmusa karo na biyu tare da juyawa inda matar shi take zaune yace lalai wanan anty kan akwai sa,a ance harda nasir ta san yadda take zama dashi ai kinyi kokari. Na mike tare da cewa Allah ya hutar da gajiya yace Allah yasa na juya tare da fara tafiya zuwa ciki. Muryan anty ne kewa dani Rama dawo ki kwashe kayan nan ki shiga dasu ciki cup ne da goran ruwa da akasha. Muryan shi naji yana fadin ashe ba wata babba bace yadda na dauka wanan ta ma kai 18 kuwa ? Tace yanzu dai take seventh don ko da ta gama makaranta kasan irin karatun su na kauye ne ai pushing din mutun din nan don kokarin shi. Ni dai nai simi simi na kwashe kayan zuwa cikin kitchen na barsu nan suna magana a kaina. Yace wa matar nashi yanzu yar wanan abar ce kike nufi an tabawa aure ? Tace sosai kuwa mutuwa mijin yayi don ba yaro bane zai haifi sa, ata ma gaskiya. Ikon Allah wani magana sai kauye ba tausayi ba sanin human right ko kadan a kauye. Anty tace ina son na mayar da ita makaranta taci gaba da karatun ta don tana son karatu a rayuwan ta. Yace dakin kyauta gaskiya don yarinyar na da hankali na gani tace ai Rama akwai hankali sosai wallahi. Sai da safe dana shiga gaida anty bayan tafiyan yara take fada min wai matan gidan ai sun dawo jiya cikin dare. Da maki na ce da ita ashe sun dawo gidan ya cika kake nan yanzu? Tace kin san su da naci kamar masu jiran saukan shi sai ga kowace an dawo da ita daga gidan su a cikin dare. Har uwar yesmin tazo cikin dare don fitina wai a bata yarta a gurin ta zata kwana sai da maigidan ya tsawata mata. Ni dama ya bari na bata yar ta tun daren kowa ya huta haka ko kwasa fitsari ai ya ishi mutane ma. Ni ba don Allah ya kawo min ke ba da ban san yadda zan kwashe da rigiman yaran nan da ya bar min ba. Yasan kuma ba lafiya ke gareni ba gashi fitinan su ya hana ko yar aiki a bar muna a gidan ko mutum yaji dan sanyi. Don haka don Allah Rama kafin su dawo ki hadawa kowa na ta ya na ta su koma wurin iyayyen su kema kya huta ai, da wanan wahala tunda su basu san wahala suka barwa mutane ba ma. Inda sune ai ba zasu dibawa mutum nashi ba kamar yadda yaran ke samu kulawa a nan yanzu. Nan take bani labarin tafiyan ta da yadda ta dawo ta samu yaran ta hannun su tace shine take ganin dalilin barin su gidan da sukayi. Ta tabe baki tare da komawa ta kwanta tana cewa nasan shine dalilin jin haushin da yasa tazo cikin dare wai a bata yar ta ta tafi da ita gurin ta. Nace ai da abari ta tafi da abinta ba shike nan ba kowa ma ya rike nasa a zauna lafiya. Tace wallahi fa kedai Rama ba su da mutunci fiye da tsanmanin ki don sun samu daurin gindi a gurin sarakkan mu ne. Dazu bakiji yadda hajiya tazo tai min tas ba a gidan nan saboda sune kuma tai min haka. Ai indai kina gidan nan zaki gani don kullun aikin ke nan su basu laifi sai nice bare a cikin su nice mai laifin don Allah ya jefani cikin su. Nace anty dama yan uwan shi ne yake aure ? tace eh kusan hakane don ita hindatu yar uwan hajiyan shi ce. Ita kuma zulfa diyan amininahaifin shi ne da suka dade suna tare tun kurciya suke tare kinga ke nan ai sai ace duk yan uwan shi su biyu din. Nace cabdi amma kina fama gaskiya anty tace bari ke dai to yaya na iya da raina Rama ? Ganin ta kwanta na juya zan fice dakin take cewa dawo kiji, da sauri na juyo ban tafi ba tace daga yau wanan girkin wahalan ya kare koda yake ma ina ganin nan da two days zamu bar gidan nan kowa ta kama part din ta daga ita sai nata babu mai ganin wani cikin mu Amma dai duk da haka yau abinda zamu ci kawai anan ni daku zaki girka muna yau din. Nace to anty na juya na fita tare da rufo mata kofan dakin don nasan barci zatayi kila.

Readers Also Read