A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 21
A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 21: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 21. ****** ********* ****** ****** Mama Lauratu ne zaune da yaran…
3,074 words
****** ********* ****** ****** Mama Lauratu ne zaune da yaran ta dukkan su uku sai baba da ke gefe daya zaune saman tabar ma yana sauraren abinda zata fadi. Can ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa ina son ku saurare ku fahinci may nake son fada maku a gurin nan. Bawani magana ba sai maganan kaddaran da ya samay mu a gidan nan wanda ba kowa ne ya jawo muna shi ba sai Rahama da uwarta don sune suka cuce mu haka? Haba mama in zaki magana da kika tara mu kiyi muna amma ki bar kawo muna zancen mutanen da basu san arziki ba a rayuwan su. Rukaiyya ce ke wanan magana cikin hasala tana kokarin dakatar da uwar tasu da ta fara masu dogon sharhi. Mama tace cikin sanyin murya na dauko maganan ne yadda zaku fahince ni da kyau amna tunda baku so bari naje kan maganan da nake son fada maku. Ke Lawisa dai yau Allah ya nufi auren ki da Jatau na hayin dutse don haka Allah ya kadda, , , , Kafin ta karasa Lawisa tai but tace wata Lawisan mama ba dai ni Lawisan ba kan ? Daga inda baba yake zaune ya karba da cewa ke ko Lawisan don an daura auren ki da Jatau bisa ga sadakin da uwar ku ta karba a hannun shi da niyan bashi Rahama Allah bai yi ba. Baba na shirin ci gaba da maganan shi ai Ihun da Lawisa ta sake ne ya hana shi ya karasa zancen shi. Lawisa ta dinga kuka tana durawa iyayyen ta ashar tana bata ga dan kazan abu kaza ba da ya isa ya daura mata aure da Jatau ba. In gaskiya inta mama ta kashe auren ta ita da taci kudin shi taje ta aure shi mana. Amma ita don ba a sonta shine za, a cuce ta a hada da wanan kazamin tsohon ace wai shine mijin ta. Nan suka shiga lalashin ta amma ina kamar kara zugata sukeyi ai a lokacin. Suma su Rukkaiya nan suka shiga fadawa iyayyen bakar magana son ran su ba wanda ya iya magana a cikin su sai sadda da kai kasa da sukayi kawai. A take baba ya tuna da auren da sukai min na Garbati bani so amma dani da uwata ba wanda yaji bakin mu haka aka kai ni salin alin mun danne zuciyan mu dani. Yau gashi diyan mama diyan da yake son su kamar may a ran shi gashi yadda suke masu cin mutunci a bainan jama, a kowa naji don har sun fara tara masu makwabta a gidan don ihu da Lawisa ta yanka ya jawo hankalin mutanen shiya. Basu kai ga ci gaba da magana ba sukaji dir mota sai ga wasu mata biyu sun shigo gidan suna fadin sun zo daukan amarya ne Jatau ne ya turo su don su yan uwan ango ne Jatau. Nan su Rukkaiya suka shiga zagin bakin suna masu rashin mutum ci sai da kyat ranan baba ya gwada masu ta maza haka suka shuga daki da ita tana shiri tana kuka. Ga shi mama sunyi fada da aminiyar ta Larai babu wanda zata nufa a makwabta takai kukan ta. Mama ta shiga daki cikin sanyin jiki tana cewa Lawisa kiyi hakkuri nasan amanane ya koma muna akan ki tun ba aje ko ina ba gashi Allah ya nuna min abinda naso yiwa yar wata ya fada kaina. Nasan na cuce ki na cuci rayuwan ki abinda Allah ya kaddaro muna gani ke nan wanan daren a kan ki Ki daure kije gidan nan don rufin asirin mu da na ki don kin san Jatau ba mutunci ne dashi ba. Kan kudin nan yana iya ya daure ni har uban ki ko ya sayar da dan gidan nan da muka mallaka a duniya. Muryan daya daga cikin matan da suka shigo daukan amarya ne ke cewa ayi a fito da amarya mai akori kura yace zai tafi jigilan shi ne. Yau abinda mama ke son gani a gare sai gashi a kanta burin mama shine ko yaushe tagan mu ni da mahaifiyata a cikin kuncin rayuwa. Idan ta gan mu a haka takan ji duniya yai mata dadi kamar ta zuba ruwa kasa tasha ta kanji a lokacin. Haka aka fito da Lawisa zabban tausayi tana kuka tana tirje tirje aka kada ta a mota sai tabarma da filo da mama ta bayar aje mata dashi tace daga baya zata sayo mata kayan aiki a kawo mata. Aka fito da ita sai guda yara da manyan uguwa suke yi yan gulma suka shiga motan zuwa kai amarya gidan mijin ta. Lawisa sai kuka takeyi a gaban mota zuciyata fam da bakin ciki tausayin kan ta takeyi yadda zatayi rayuwa da tsoho irin jatau a matsayin mijin ta. Haka aka isa gidan da ita tana matsanacin kuka suko mata sai guda da shewa sukeyi yayin da Lawisa take jin kanta kamar tana cikin kabari ne a lokacin. Allah ke nan yadda sukai min sai gashi ya mayar masu da abin su tun a nan duniya sunga kayan su. Har gara nawa akwai rashin sanin ciwon kai da kurriciya a tare dani lokacin kuma gara nawa mijin sau dubu da nata ita. Wani rubaben daki daya gyara mata shi nan aka saka ta daga ita sai yar tabarman kwancin ta don ko katifa bata samu ba a lokacin. Yan uguwa sukai mata nasiha yadda manya keyi idan an kawo amarya yi nayi bari na bari a zauna lafiya kiyi biyayya ga mijin ki da matan shi sai a zauna lafiya da kowa. Daga can kofa sukaji wata tace kada Allah ma yasa tayi mu ai nan ko da may tazo mun fita gidan Jatau ne fa ta shigo. Ashe daya daga cikin sarakan gidan ne tazo ganin gulma taji ana wanan nasihan ta cabe da bada amsa. Su dai basu tanka mata ba suka fice gidan suka barta zaune saman yar tabarman ta ta hade kai da gwiwa tana rusan kuka sai Allah ya isa take aikawa mama da baba a lokaci daya
ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: A Lokacin ne,,,,
IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA YAR UWA DON HAKKIN WASU NE,,,
Zaune take a kofan dakin ta tai tagumi sai faman tunane take tana kulawa tana warwarewa ita kadai a gidan don mijin ta ya fita tun safe zuwa gurin aikin saukalen da yakeyi gurin manyan motoci , Sai idan ya dawo ne suke dora girkin abinda zasuci kullun a haka suke wanan rayuwan wahalan ita da iyalin ta, Yanke shawara tayi a inda take zaune gara ta hada kayan dakin ta ta,sayar ta,dan samu koda tsohon fridge ne ta,saya tana sana,an kayan sanyi ko zata samu kobo yana dan shigo mata a hannun ta, Ba bata lokaci da mijin nata ya,dawo gida batai nauyin baki ba tafara fada mai shawaran da ta yanke, Shiru yayi tare da nisawa inda yake zaune saman tabarman shi, da yake shan iska a kai, yace Halima banki shawaranki ba gaskiya amma ni a nawa tunanen da kiyi hakkuri ki zauna da kayan ki don wanan lokacin da muke ciki lokaci na lahaula ga kowa ba masu kudin ba ba tallakawan ba kowa wiwi yake yi da wanan karnin, Koda kin sayar da kayan dakin ki don kiyi sana,a ina mai tabbatar maki rayuwa bazai bari ka mayar da ko kwatankwancin abinda ka rasa ba a baya kinga hasara da dana sani sai ya hau mutum, Ke dai kawai ki bar kayanki tunda Allah bai hana muna dan abinda zamuci ba a rayuwan mu to ai alhamdullahi komai yanzu sai hakkuri don ba kowa ke samun yadda yake so ba, Matar tanisa tace ni dai gaskiya nayi niyya da kabarni kawai na sayar a samu, dan gurin rage wani hanyan kuma. Ya fahinci bazata dauki shawaran shi tayi hakkuri da jarabbatar talaucin da suke ciki ba don haka sai ya kyale ta tayi yadda take so kawai. Don yanzu ba matan birni ne kawai ke bijirewa girmama wa dokan mazan su ba har ma da matan kauye haka suke don yadda zamani ya juya a lokaci ne muke ciki, Bai gida washe gari baya gida takira dillaliya sukai cinikin kayan dakin ta tazo ta kwashe akan dan kudi kalilan tabar mata su, Ba bata lokaci ta hada kudin tana jiran dawowan maigidan ta ta fada mai ya barta taje ta dan samu abin da tai niyar saye da kudin, Bai mussa mata ba don yasan kudin ta ne don haka ya kyale ta tayi yadda take so da abinta don yana gudun yai magana ta ga kamar yana son wani abune daga cikin kudin, nata. Bata tsaya bayan sallah magariba ta shirya sai gidan wata dillaliya mai sayar da kayan hannu, inda tai sa,a tasamu fridge har guda uku a gidan da akasa a kasuwa nan sukai ciniki ta samu dan babban wanda bai tsufa ba sosai ta saya da kudin nata, Suna barin gidan ta turo mai baro ya daukan mata shi zuwa gida zuciyar ta fam da farin ciki a ran ta, Da mijin nata,ya,dawo yai mata fatan alheri da,daukaka a cikin al,amarin. Tun daga wanan lokacin ne tafara dan sana,a da fridge din nata tana dan samun kwabon kashewa ta fannin ta ita ma, Hakan ne ya kawo mata saukin yan damuwan yau da kullun da take ciki don tana dan samun kudin kashewa a wanan fannin nata.
****** ********* ****** Safiyane duk jama,an gari sai faman zirga zirga suke kowa harkan ga ban shi yake yi ba mai kama hannun yaro daga cikin su. Sai faman sallama ake a gidan gwago Asmau da manyan kuloli gurin sayen masan da take soyawa tun da farar safiya. Gwago Asmau taji dadin kasancewar Bintu da ita a yau din don ba karamin taimaka mata takeyi ba. Komai cikin natsuwa Bintu takeyi ga tsabta sai ta wanke hannu da da kayan aiki kafinta taba shi, Sannu sannu tafara gyara ma gwago aiyunkan ta sabanin yadda take aikin ta a baya in local way, Bintu taba gwago shawaran cewa ta mayar da masan ta na zamani don yanzu akasarin mutane suna fama da lalurar ciwa gyambon ciki watau ulcer, Gwago Asmau tai mamakin yadda Bintu karama da ita tasan wanan dubara gashi kuma daga kauye take zaune, Don Bintu ta bata shawaran cewa yanzu da safe zasu dinga kai nika kuma su toya shi, a lokacin, Gwago Asmau tace kai haba Bintu ni kada ki jawo min hasaran kudi yaya zaki ce na kai nika ranan kuma na soya masa a ranan, Bintu tace wallahi gwago ki gwada masan ki zata samu karbuwa sosai wallahi don duk masu tsoron cin masa don tsamin shi zakiga sun fara sayen shi, Gwago tace yaya zan yi wanan aika aikan haka Bintu na, Bintu tace gwago zamu wanke shimkafan mu fara sai mu barta a jike cikin ruwa ta kwana da safe zamu tsamay mu hada da dan falawa dai yadda muke son shi sai mu hada da dafafan shinkafa da yis da baking powder, Sai a kai nikan shi ayi muna kullun shi na ruwa amma kada a cika ruwa da yawa gurin nikan shi idan an dawo sai k8 dan kara gurorin dafafan shikafa da kaurin shi yadda kike bukatan shi, Sai kawai a fara soyan shi kamar yadda ake masa a koda yaushe, Kai yan nan akwai ki da dabara kamar wata babban mace ke a ina kika koyo wanan masan kuma, Bintu tai murmushi har dan dimple din ta ya lutsa kadan tace nima a gurin wata makwabciyar mu dake masa a bauchi sukai zama, naga tana hakan. Yadda Bintu ta fada hakan sukayi sai dai gwago Asmau sai Allah Allah take kada abin ya bashe su sai da taga zubin farko masa yafito da kyau hankalin ta ya kwanta, Nan da nan masa ya kare masu washe gari masu sayen masa sai yaba dadin masan jiya sukewa gwago Asmau, suna cewa kai masan jiya ga taushi ga dadi wallahi babu tsami ko kadan, don har miyan sai da bintu ta sa aka dan zuba mai dan baking powder kadan, Nan da nan labarin dadin masan gwago Asmau ya dan kewaye shiya, don dadin shi.
Daga gidan malam Habu aka aiko asai masan dubu da dari biyar sai aka samu akasi babu canji a gurun gwago don haka aka ba su masa kawai, sun biyo canjin . Sai da yamma ne gwago ta ba Bintu canji ta kai gidan rayuwan Asmau bai so ba don bata son dabi,ar shiga gidajen mutane ita. Haka yasa tun zuwan ta garin bata je gidan kowa ba, tana cikin gida gurin gwagon ta kawai sai nikan da tafita da,safe tabi almajirai, don taga yadda za,a nika masu kullun masan su. Hijjab din ta ta saka tare da sa dan sifas din roban ta sai gidan duk da dai kwatancen gwago tabi don shiga gidan, A hankali tai sallama daga kofan farko na shiga gidan babu kowa sai flawer a shuke daga can nesa ta hango wani saurayi a duke yana sa takalman kwallo a kafan shi da alama shigar shi ya nuna cewa gurin wasan kwallon kafa zai tafi. lna wuni tace tare da dan duka mashi har kasa batai tsanmani ya amsa mata ba sai cewa tayi don Allah ina hanyan da zan shiga cikin gida canji na kawo na masa. Fuska a murtuke ya nuna mata da hannun shi, ba tare da yai magana ba, Inda ya nuna mata ta nufa a hankali sai dai tana shiga duk ta daburce don gina ne na part din mata hudu ko wace da nata daban, Yanzu ni ina zan nufa ta fadi a ranta batare da tasan wanda zata kaiwa canji ba. Tana shiga tai tsaye tana ta faman kwada sallama ita ka dai a tsaye shigowan wata mata gajera fara mai kiba yasa ta mayar da hankalinta ga matan, Ina wuni take ce mata cikin ladabi matar ta,amsa a,dadare da fadin lafiya, Bintu tace canji aka ce na kawo daga gidan hajiyan masa, kamar yadda ake kiran gwago Asmau, dashi a uguwar, Cikin wani irin kushe fuska take cewa isa mana ki tambaya ciki tun nan ta fahinci akwai kishiya a gidan ke nan , Tanan tsaye sai sake, sake, take a zuciyar ta, tana niyar juyawa ta koma ne taga wata mata baka, tafito daga wani shiya dake daga can gefe tsabare da sauran shiyan , Hannun ta dauke da bukiti da mopa da tsiyatsiya da alamar da ga shara take futowa matar. Itama dai cikin ladabi ta gaida matar da ta gani ta amsa mata cikin sakin fuska. Tana cewa sannu ko kina neman wani ne ko Bintu cikin murmushi don taga fuska, tace dama canji ne akace in kawo inji Hajiyar masa, Au daga gidan hajiyan masa kike ne, ? Eh a nan nake tana kokari miko canjin dari biyar din dake hannun ta din, A shigo mana daga shigowa har zaki tafi zo shigo daga ciki kinji ba mussu Bintu tabi bayan ta zuwa part din da matar ta nufa. Suna shiga dakin taga ashe daga ciki a kwai dakuna da kuma kitchen, a cikin su. Kujeran dake a falon gidan ta nuna mata ta zauna tare da kara gaisawa da ita, Amira Amira matar ke kira daga falo, sai ga wata yarinya doguwa zata dan girmay ma Bintu tafito daga dayan dakin dake part din, Tana ganin Bintu zaune sai kallon ta take da mamakin ko wacece ita, gaida yarinyar mai suna Amira Bintu tayi. Maji gani inji Amira din tana mai kallon uwarta, don son jin mai zata ce mata. Karbi canjin nan jeki sauran dakuna ki tambaya wa hajiyar masa take bi canji dazun da safe, Amira ta turi baki gaba tana cewa ni wallahi in ba dole ba ban sin shiga gurin kowa a gidan nan don dai kawai da mutum ya shiga yanzu za,ace ga abinda yayi kuma. Aiken ki fa nayi Amira kika tsaya mai da naki ba,asin son raki haka Amira taja kafa ta,wuce zuwa sauran sassan gidan, Inda Bintu take zaune maji ta dan kalla tana fadin yi hakkuri kinji har ta dawo muji ko canjin waye, Andan jima kadan sai ga Amira ta dawo tana konkwami tana fadin wai, maman su Hadiza tace takawo ta aje ko na baba ne amma taki bata ga kudin tana kokarin mikawa mahaifiyar ta kudin hannun ta, Amira mai yasa baki bata ba da kika dawo da kudin nan may zanyi maki dashi a nan , Maji cewa fa tayi wai zata ajewa Baba ni kuma nasan ba,bashi kudin zatayi ba shiyasa nace mata tabari na tambaya sauran shiya muji in ba nasu bane, Yadda maji take magana da yar ta acikin lumana ba daga harshe ya ba Bintu shawa sosai sai faman bin su da kallo take yi, na sha,awa. Yadda uwa takewa yar ta magana a cikin kwantar da hankali da fahinta, Inda Bintu take a zaune Maji ta,waiga tana fadin inaga canjin Alhajine idan ya dawo zan tambaya muji in har ba nashi bane zan sa su dawo mata da kudin. Bintu ta mike don fita daga dakin a daidai lokacin da Umar ya shigo dakin ke nan babu ko sallama. Sai cewa yake ni zan tafi ball kada kuma ace ban fada ba natafi , yana,wani cicin magani cikin dakewa, Haba babana kai wai yaushe ne zaka girma zaka shigowa mutane daki babu ko sallama kana wani shan kamshi da cin magani. Kamar wan da zai tafi gurin wani abin arziki wai ball, ball din mai zai tsinana maka a rayuwanka ne wai, Maimakon ya tsaya yaji karshen maganan ta,sai juyawa yayi kawai ya fita daga dakin, A hankali maji ta sauke ajiyan zuciya tana furta Allah ya shirye ka babana, Bintu dake tsaye ta amsa da Ameen Mama sosai har cikin ran maji taji dadin Ameen din da Bintu ta amsa mata dashi. Mama ni zan tafi sai anjima ke nan zan fada mata yadda akayi, to kin ji yar albarka ki gayar min da Hajiyar masa din kinji , Bintu takai kofa Maji tace may ye sunan ki ne bakuwar hajiya ? Cikin murmushi Bintu ta amsa da Bintu nake mama Allah sarki sunan mai kyau sunan mahaifiyar maigidan nan ke nan ai. A waje ta samu wanan mai bakin ran yana tare mashin zai hau ko kallin shi batayi ba don tsoro ma yake bata, ita,