Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 23

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 23

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 23: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 23. ****** ********* ****** Zaune take a f gaban mahaifin ta a…

2,858 words

****** ********* ****** Zaune take a f gaban mahaifin ta a cikin natsuwa take sauraren shi, yana mata zance akan zuwa birnin da zatayi gur8n kaunan shi dake can tana aure don ta matsa a kan Bintu tazo mata hutu ta dan kwana biyu a gurin ta, Sam Bintu bata,son wanan tafiyan don dai babu yadda zatayi ne da umurnin mahaifinta da gaskiya bataje ba, Don tafi son ta,zauna a kauyen su tare da mahaifinta don koda take mace ce itace kamar jagoran gidan nasu duk da kasancewar Bintu karamar yarinya , Haka take yawan aikin wahala a kan su samu dan abinda zasuci a gidan su kasancewar mahaifin nata ba,wani mai abin hannun shi bane, Itace zuwa icce itace suyan awara da rana da safe kuma tana koko da kosai kafin ta dawo zuwa makarantan bokon da yake a ranta, Yanzu gashi gwagonta ta birni ta matsa sai tazo gurin ta wai hutu wanda ita bata san dalilin da ya sa,duk tazo sai tai zancen zuwan Bintu gurin ta hutu ba, Yan kayan ta,already ta,shirya su a dan jakar ledan ghana most go karama duk jakar ta tsufa sosai don har ledan jikin jakar ta dan tashi ya,wani dan takure daga jikin shi, Kudi mahaifinta ya ciro daga aljihun shi dubu daya ya mika mata tayi kudin mota dashi, Kallon kudin take tana mamaki inda ya samo har dubu daya yabata wai tai kudin mota dashi, Hannu biyu Bintu ta mika ta karbi kudin cikin ladabi tare da fadin na gode Baba, Bayan ta karba ne yake cewa tau Bintu ki saurareni kiji abinda zan fada maki da kyau, Ki sani dai rayuwar birni daban yake da,tamu irin na kauye don haka kiyi taka tsatsan da duniya ki kama kanki , Ki kawar da idon ki ga duk abinda,bai shafeki ba a rayuwan ki ki tsaya inda gwagon ki ta tsayar dake duk da yake ke yarinyar ce nnatsatsiya amma nasan zakiga abin mamaki da zai iya canza maki rayuwan ki a can, Don haka kiyi taka tsatsan da duniya baki dayan ta a yanzu babu gaskiya ki tsaya a matsayin ki na yar talkawa kamar yadda kika samu rayuwar mu, aciki tun farko, A hankali Bintu tace insha Allahu baba zan tsare kamar yadda kace zaka kuma samayni da kiyayyewa insha Allahu, Yace Allah yai maki albarka Bintu Allah ya tsare min ke da tsarewar shi ta karba da amin Baba idanuwan ta sun kawo hawaye kamar zasu digo dag idanuwan ta, Shi da kan shi ya rakata har tasha inda zata samu motar da zai kaita, garin Sokoto, Tana zuwa motar ta cika suka kama hanya sai Sokoto zuciyar ta fam da kunci a cikin sa, Sai karfe biyu suka shigo gatin na sokoto a lokacin mutane suna ta haramar yin sallah azahar a garin, Mai yar mashin ta dauka kamar yadda akai mata kwatance tace a kaita Sama road, a bakin shagon dantani mai yar mashin ya tsaya da ita, Shi ta tambaya gidan Gwago Asmau mai masa ya nuna mata da kwatance tabiya mai mashin kudi ya tafi ta dauki yar jakar kayan ta zuwa gidan da akai mata kwatance, dashi, Da sallama a bakin Bintu ta shiga gidan ta samu gwago zaune a tsakar gida tana gyara kayan yin masan ta, Tana ganin Bintu ta fara fara,a tana cewa a,a,a wanake gani yau garin namu kamar Bintu, Maraba da yar gwago sannu da zuwa sannu da zuwa tana mata maraba cikin jin dadi da ganin ta, Daki ta nunawa Bintu ta,shiga da kayan ta daga cikin dakin tare da,samun guri ta dan zauna a takure daga gefe guda, Gwago ta,shigo, dakin dauke da kwanon abinci a hannun ta a rufe ta aje a gaban Bintu, tana fadin zauna ki ci abinci sai mu gaisa, Cikin yar muryan ta take cewa gwago sallah nake son nafara yi tace tau Bintu ga bayi can jeki ki kewaya, Sai bayan ta idar da,sallah ne ta fito inda gwagon ta take zaune tana gyaran alaihu tana kokarin karba daga hannun ta, A,a haba Bintu jeki ki ci abinci mana daga zuwanki zaki buge ga aiki haka jeki kawai ki ci abinci kinji Bintuna, Kamar yadda gwago tace haka din Bintu tayi ta koma daki ta zauna tare da lankwashe kafafuwanta a hankali ta bude kulan dake gaban ta shimkafane da,wake da mai da yaji a cikin kulan abincin da gwago ta aje mata,sai salad da tumatir da aka yanka daga saman shi, A hankali take ci a cikin natsuwa har ta kare cin abincin nata wanda ko rabi batayi ba ta mayar da kulan ta rufe wai ta koshi, Bata zauna ba a,tare sukai aikin masa da gwago ranan ba bata lokaci suka kammala komai da wuri, Nan suka samu guri suka zauna,suka,fara hiran mutanen gida gwadabawa,

****** ******** ****** Hasken ranan da ya haska dakin ne ya haska dakin abinda ya farkar dashi daga nauyayan barcin da yake ke nan, Zubur ya mike gami da salati a bakin shi, yana cewa subbahanallahi da sauri ya dan dago daga kwance sai dai jikin shi ya dake mai sai wani nauyi da ciwo yake mai kamar yai wani aiki, Wanka ya fara shiga yafito da,sauri yake shiri don zuwa makaranta saboda duk abinda yakeyi bai wasa da al,amarin karatun shi ko kadan, Yana cikin shiri yaji cikin shi yana wani irin kugi na yunwa duk yai waban shaye shayen nashi da dare haka zai wayi gari yana jin cikin shi kamar yai kwana goma bai saka komai a cikin shi, Don haka da sauri ya shirya ya nufi cikin gida don ya dan samu abinda zai ci a ran shi don yasan cewa yanzu Maji nacan ta aje mai abin karyawan shi ko, Yana fitowa don zuwa part din mahaifiyar nashi ne yai karo da,daya daga cikin kannen shi diyan dakin mama maimuna, A guje yaron yake tafe bai ankara da Umar dake fitowa ba daga part din samarin gidan ba,sai ji yayi sunyi karo da junan su, ba,shiri UMAR yakai mashi nashi yana,fadin wanan wani irin iskanci ne haka zaka bangajeni ko kai makahone wai, Yaron bai tsaya ba don sani zafin zuciya irin na UMAR don yasan idan ya tsaya zai iya shan dukan tsiya yanzu da farar safiyan nan a gurin shi, Da sallama ya shigo falon mahaifiyar nashi Maji tana tsaye a tsakiyan falon tana magana da kaunar shi Amira, Shigowan shi ya sa Amira,saurin cewa ina kwana yaya Umar,? Lafiya kawai ya,ansa mata dashi a takaice ba wani dogon magana Maji dake tsaye jin muryan shi ya,sa ta,waigowa da,sauri tana kallon shi fuska a matse babu walwala, sai wani kallon takaici take mashi, Maji ina kwana ya kara fadi cikin dan dukar da kan shi kasa cikin jin nauyin mahaifiyar nashi, A dadare ta,amsa gaisuwa sai cewa tayi Amira dauko mashi abincin shi a kitchen kinji, Amira ta juya zuwa dauko ma yayan nata abincin nashi kamar yadda mahaifiyar su ta umarce ta da yi, Kujeran dake falon ya nufa don ya zauna wa saman kujera sai dai muryan Maji ne ke cewa ina ka shiga haka jiya Baba na har dare yayi sosai baka dawo gida ba alhalin kasan mahaifin ku bai son wanan bakin yawon har tsawon dare haka, Kafin ya bata amsa sukaji muryan Mummy tana fada tanacewa ina Farukun yake ne wai wallahi bari kaji ba,zan daukan maka dukan min yara ba iskancin ka ya tsaya iya kannen ka da uwarka ta haifa amma baga yarana ba wallahi don bazan daukan maka hakan ba, Ke kuma Hauwa wallahi kiyiwa danki fada yafita harkan yara na a gidan nan tun mu na,sheda juna dake, Tajuya fuuu tafita daga kofan falo ran ta a,bace sai lokacin ta juya gurin dan nata tare da sauke ajiyan zuciya, Tace Baba na kafita harkan yaran matan nan a gidan nan don ban son fitina a,rayuwana daka ganni nan, Dukar da kai kawai UMAR yayi yana kallon kasan dakin ran shi yana kuna don wanan wulakancin da akewa mahaifiyar shi bazai iya dauka ba dole ne ya dauki mataki, Dama yasan don dan wanan rakwashin da yai mai har uwar shi zataji haushi tazo har dakin uwarshi kafa sheda da da yai mai dan banzan dukan tsiya wallahi, Har ya gama cin abincin shi Maji bata tanka,mashi ba saboda ran ta ya baci sosai, dashi saboda yawan maganan da yake jawo mata a gidan nan yaiyawa gaskiya, Jin sallaman shi tayi kawai yana ce mata yatafi sai yadawo zai shiga school don gap yake yanzu da yakare karatun shi, a jamia mataki na biyu da yakeyi, Yana fita takai kalkon ta ga kayan da yaci abinci tana matukar mamakin yadda wani lokaci yake cinye yawan abincin da take aje mashi duk safe sai dai da rana bai wanan cin abincin haka, mai yawa sosai sai da,safe, Nan dai ta kwashe kayan zuciyar ta a cunkushe da bakin cikin dan nata, mai yawan jawo mata fitina a gida da,waje, Jiya da dare mijin su yai mata masifa a kan shi yau kuma da safen fari kishiyarta har daki tazo tai mata still a kan shi dai din guda Haba haba haba dai babana Allah dai ya shirya min kai kawai zan iya cewa don matsalar ka tai min yawa wallahi kowa dai kai kowa dai kai ya Allah kai min dauki akan halin wanan yaron, Ya Allah ka,shirya min su baki dayan su ka,shiryawa sauran kullimin musulmin Allah a baki daya,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,, A LOKACIN MU KE,,,,,

MAJI ce kwance a,saman dogon kujeran dake cikin falon dakin ta, ziciyar ta a cacushe yake mata da bakin da bacin rai ga radadi da zugin da yake mata. Bakomai ke damun zuciyar Maji ba sai irin halin rayuwan da Allah ya jarabi dan ta dashi. Wanda a da can baya ba haka rayuwan shi take ba sai yanzu da girma ya fara shigan shi ne bakon al,amarin ya fara shigan shi haka. Hayaniyar da take ji yana tashi daga cikin gida yasa ta sauri mikewa zaune da sauri, don ta saurara idan dai ba saudakine ya ja mata wani sabin maganan ba kuma a gidan. Aikuwa jitayi mama tana fada tana cewa wanan yaro ya dai zama muna masifa a gidan nan yanzu. Yaro guda ya zama alkakai acikin yan uwa wai mai saudauki ke son mayar da mutane ne haka wai, duk yaro abu ba abu ba ya kai mai duka bugu haka har na tsiya. Sai muryan dayar kushiyarta da take biwa tana cewa ni wallahi karan shi zanyi akan takalman banza zakaiwa yaro mugun duka haka har ka fasa mai baki. Anty watau amaryan su tace a,a kada ki karan shi kijira har shi mahaifin nashi da ya bata shi ya dawo ki fada mai muji ko muga abinda zai yi, Basu suja batashi ba da so sun dauki son duniya sun dora akan shi yanzu ai ga abinda so ya jawo masu sun gani. Maji dake daga daki takai zaune a hankali saman kujeran da ta tashi a kanshi tana maijin zafin maganganun su a ranta don dai ita tasan a iya yinta ba wani gatan da ta gwadawa dan ta, a baya fiye da sauran yan uwan shi. Amma babu yadda zatayi don ance dan kuka mai jawa uwar shi jifa don da bai shiga harkan yaran su kamar yadda ta hore shi da zafin zuciyar shi akan ya rage da bai ja mata yawan magana na habaici ba ga kishiyoyin ta. Wasu irin hawaye ne masu dumi suka fito daga idanuwan ta a hankali, a daidai lokacin Amira dake cikin daki kwance tafito falon nasu. Ganin yanayin uwar,su yasata karasawa kusa da ita ta zauna tanavmai kura mata ido tace yaya sadauki ne ko maji. Don Allah maji ki fita zancen su ki daina zubar mashi da hawaye malamin mu fa na islamiya yace muna ba kyau uwa tai kuka akan dan ta musan ma ma da namiji don Aljannar shi yana ga hannun ki mama don Allah ki yi hakkuri ai ya kamata ace kin saba da halin shi yanzu ki daina bata ranki a kan zancen shi hakana. Suma ai daukan magana ne mai yakai su ga kayan shi tunda sun san bai son raini shi. Baki maji ta bude da nufin tai magana sai kuma bacin rai ya hana ta iya furta komai sai taja bakin ta tai shiru, amma duk AmiraA yarinyace karama zancen ta ya shiga ran ta sosai don haka tai shiru kawai amma a zucuyar ta ba dadi sam wani kunci take ji sosai. Har dare sadauki bai shigo gidan ba don yasan abinda yaiwa kanin shi yana can ana jiran shi dashi cikin gida. Shi ko yanzu daidai yake jin shi dakowa don ya fahinci daga mahaifiyar su har su duyan ta ba mai kaunan su a gidan gaba dayan su. Sai yamma kamar kullun malam Habu yadawo gida ko hutawa ba,a bari yayi ba aka tare shi da zancen sadauki akan yaiwa Abdul mugun duka wai don kawai yasa mashi takalman shi na kwallo yafita dashi gurin wasa. Kai kawai malam habu ya kada yace wanan yaron wanan yaron ya kai min ko ina a rayuwana wallahi. Daidai lokacin Maji ta shigo dakin saye da hijjab din ta mai ruwa light green. Tana mashi sannu da dawowa amma bai karba mata ba,sai cewan da yayi Maijidda wallahi danki ya zama min masifa a rayuwana . Kullun har zullumin dawo gida nake daga kasuwa don nasan da zaran nadawo da,wuya ba,a tareni da zancen shi wanda zai bata min rai ba. Shiru maji tayi tana,sauraren kalamin maigidan nasu a gaban sauran kishiyoyin ta yana cewa ki fada mashi wallahi zanyi maganin shi don na lura kamar ma ya fara shaye shaye ne a rayuwan shi. Niko bari kiji in har hasashe na ya zama gaskiya to wallahi ba zan barshi a gidana ba ya bata min sauran yara na na kirki. Allah ya tsare ya kare Maji ta furta a fili aidama haka kawai zaki iya cewa bayan shi baki da,wani abin fadi ai, Bata ce komai ba,sai hadiyan bacin ran da tayi tare da juyawa tana fadin Allah ya kyauta. Malam Habu yace ai zai zo ya samay ni zan mu hadu dashi don ba zan yarda ya,sabauta min yara ba ga banza. Maji dai fita tayi daga dakin don tasan ko ta,tsaya,babu abin da,zataji banda bacin rai kawai. Din haka taiwa kanta kiyamallaini tabar dakin don bazata iya jure sauraren kalaman mijin nasu ba akan ita da dan ta. Tafiya take zancen mijin nasu gareta yana ci mata rai don zancen sadauki shi ne zance mafi muni dake hada ta,da maigidan nasu. Duk irin kwaram din da,aka,sha a,baya baya akan kishiyoyinta da ita a baya, baya tayar mata da hankali kamar zancen sadauki da ya taso mata a yanzu, Yanzu saboda shi tana ji tana gani duk wanda ya kwaso zancen shi akan tane zai yaba mata don halin dan ta kawai, A kulun kalaman maigidan ta ga dan ta yanzu yana kona mata zuciyar ta da jikin ta ba ma zuciyar ta kadai ba, Ita a,zaton ta ai wanan abin abinda ya shafe su ne baki dayan su bawai ita kadai za,a dorawa laifin ba don itace mahaifiyar shi ne kawai kowa ke ganin laifin ta ita kadai. Abin da ya kamata su taru su nuna bacin ransu a kai su tayata bakin ciki amma sai gashi kowa ya,zamay yabarta da laifi ita daya. Amma babu komai ta furta a,ranta tare da hade yawun bakin ciki a cikin ta, tana mai sauke ajiyan, zuciya kawai. Bata ankara ba,sai hawaye kawai taji yana biyo mata a idon ta. Gaskiya zancen Sadauki yana tayar mata da hankali sosai ta rasa wanda zata kai kukan ta gare shi ya tayata bata shawara a cikin gidan. Don duk yanzu suna matukar nuna mata kyama akan zancen shi gabadayan su gidan har shi maigidan kan shi. Shin may nayiwa Allah da yai min wanan mumunan jerabawan haka akan dan tilon da daya da Allah yabani namiji a duniya ? Ni dai nasan harga Allah ban cuci dan kowa ba a rayuwana da wanan jerabawan yafado a kaina. Duk da ni marainiya ce na riki maraici na ban kai kaina inda Allah bai kaini ba, ina zama a matsayina na mara galihu har a gidan aure na. A hankali ta kara lumshe idanuwan ta tana tuno rayuwanta na baya da kuma irin kokatin ba yaran ta tarbiyan da takeyi. Ba komai take kara tunawa ba,sai irin dafin bakin da maigidan su yake mata a,baya, Da yakan ce maijidda duk da ba komai ke gare ki ba,a,duniya ni ina sonki a yadda kike. Don kina da komai da nake bukata sabida ke ta daban ce acikin matana, ba zan iya jure rashin mace irin kiba . Kallo daya in nai maki yana wanke duk kan wata matsalar rayuwana don haka nake kwadayin samun zuri,a dake don nai alfahari dasu koda bayan rayuwana ne. Murmushi gami da hawaye ne yazo mata a lokaci guda ta furta namiji kanin ajali.

Readers Also Read