A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 24
A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 24: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 24. ****** ********* ****** Akwana a tashi yau Bintu satin ta hudu…
1,999 words
****** ********* ****** Akwana a tashi yau Bintu satin ta hudu gurin gwago Asmau a garin sokoto. Kullun sauraren take raji gwago na mata zancen zuwa gida amma shiru kake ji ba zancen, har ranan ta gaji tai wa gwagonta zancen komawan ta gida amma sai gwago take ce mata. Haba Bintu yanzu ke har kina sha,awan komawa gida gurin wanan bakar matan uban naki mai mugun nufi a kanki ko yaushe. Nifa da mahaifinki mun yanke shawaran kiyi zaman ki a nan don yace hankalinshi yafi kwanciya idan kina a guri na ko kiyi ni sa dasu kadan. Don haka ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki a nan ba zancen komawa gida don hankalin mahaifinki ya kwanta. Badon Bintu taso ba dole ta yarda da zancen gwago din don tasan haka zancen yake. Kullun adduan mahaifinte ke nan akan Bintu Allah ya kawo lokacin da zaki bar gidan nan zuwa wani guri ke ma ki huta hakana wa rayuwan ki. Tunda mahaifiyarki ta barki bata damu da damuwar ki ba ko wani hali kike bata sani ba. Gaki yarinya natsatsiya duk halarcin da kikewa matar nan da diyan ta kina bauta masu dare da rana ba gani take ba. Amma kiyi hakkuri da irin rayuwan da kika tsinci kanki a ciki haka Allah ya kaddara maki taki rayuwan zai kasance a gidan uban ki. Hawayen da ya silalo mata ne ta dan sa gefen hannun ta ta share a hankali. Duk lokacin gwagon tana kallon ta a cikin muryan kuka ta dan dago kanta a hankali tace to gwago zancen karatuna fa ? Wanan ba matsala bane ai Bintu zan yi magana a,samo maki makaran tar jeka kadawo dake can kasan layin mu ta gwaunati sai kici gaba da zuwa ko? A hankali Bintu ta,daga kai alaman taji ta juya jiki ba karfi zuwa cikin dakin kwanan su don ta gyara masu saboda yamma yayi kuma,su basu sharan dare saboda ance baida kyau, yana kawo tsiya a gida. A kwana a tashi ba,wuya a,wurin Allah Bintu tafara zuwa makaranta kamar yadda gwago tai mata alkawari a baya. Da yake Bintu yarinya ce mai hazaka baiwanta daga Allah ne, sai bata sha wani wuya ba sosai a cikin karatun ta komai tana ganewa yadda ya dace. Yawan aiken da take mata gidan malam Habu yadan sa tasaba da Maji da yaran ta don a gurin su kawai take dan samun fuska a gidan ko su ba wani can sosai ba. Sai dai idan Maji ta aiko sayen masa in har Bintu ce a kan tandar suyan waina sai ta cika masu kula fam tace akaiwa maman ta. Haka yasa watarana Maji tasa su Amira su dan yi kwalemar kayan su su ba Bintu don taga tana da bukatan haka saboda rashin wadatan da basu dashi ita,da,gwagon nata. Gwago Asmau batai sanyi a kafa ba gurin shiga gidan don taiwa maji godiya ita da yaran ta, da suka ba yar ta kyautan kaya. Ta shiga gidan bayan sallah azahar lokacin Bintu ta dawo daga makaranta ke nan. Tare suka shiga ita da Bintu din, inda suka samu maji zaune a falon ta kasan tias din dakin nata tana gyara wani ganye da,alamar magani take hadawa dashi. Sallaman su yasa ta dan gyara tana mai ansa masu sallaman su da fara,a a fuskan ta. Sun gaisa da,gwago inda tafara zabga masu godiya tana mata fatan alheri akan alherin da sukai wa yarta, Bintu. Cikin murmushi Maji take cewa ai Bintu yarinyar kirki ce halin alherinta ne yasa sukai mata haka. Sun dan fara hira tsakanin gwago da Maji inda gwago ke cewa wallahi nakan so shigowa mu gaisa da ke, amma kuma yanayin gidan naku ne baida dadin shigowa don kowa idan ka,shigo sai ya,dinga ma kallon munafuki. Maji tace haba dai hajiyan masa ai ba yau muke dake ba koma sun zarge ki da hakan ai su ma mutanen arzikin su suna shigowa gidan nan amma ban damu dasu ba ni. Gwago tace ai babu komai insha Allahu zan dan dinga shigowa idan na,samu lokaci. Suka mike suna,wa junan su sallama nan gwago ke cewa ina Sadauki ya yashiga kwana biyu bana ganin shi dai. Murmushi Maji tayi tana cewa yana nan baidai zamane suna batun rubuta jerabawan su na karshe ne shi yasa ba,a ganin shi yanzu. Allah sarki inji gwago Allah ya taimaka Allah ya bada sa,a Allah ya tsare muna su daga duk wani abinki dana sheri a rayuwan su. Amin inji maji inda taji dadi sosai da addu,an mai masa da,taiwa sadauki wanda ta dade rabon da taji wani mahaluki yai mashi wanan adduan. Har,zasu fita Maji tace su dan tsaya tazo inda tashiga daki ta dauko masu dan sabulun wanki da clean cikin irin wanda mijin su yake kawo masu duk sati don wankin tufafin su. Gwago tana ta godiya da fatan alheri ga maji suka fito, a tsakar gidan nan suka hadu da amaryan su tana shigowa gwago na gaishe ta wani kallo ta,watsa mata na ke wacece ? Gap da zasu fita daga get din gidan suka hadu da sadauki yadawo ko kallon arziki basu ishe shi ba sai ma gwago ke ce mai Umar sanda mazan fama andawo daga bokon ke nan ? Ya wani sha toka fuska babu walwala ya ansa ciki ciki Maji dake tsaye daga bayan su data rako su take ce mai bakajin hajiyan masa tana gaida kai ne sadauki Yace cikin wani murya ai na amsa mata mana ya shigewan shi part din su na,samarin gidan. Allah ya shirya ka inji maji ta furta a fili sai gwago tai dan murmushi tace amin ke dai ai yaran yanzu sai addua kawai. Ke dai kibi abinki da,addu,a Allah yasa halin iya kurciya ne kawai . To Amin hajiyan masa halin wanan yaron sai shi wallahi haba bari fafin haka mana inji gwago ke zaki kara jan abinki ga jiki kina lurar dashi dasannu zai bari ai wanan kurciya ne Allah yasa takara fadi tai masu sallama ta tafi. Bayan sun tafi maji taga yadace tabishi dakin shi suyi magana tunda Allah yasa yashigo a gaban idon ta. Yana duke yana hada wayan tv tashigo dakin abinda yasa shi saurin dagowa ke nan daga inda yake duke. A hankali take bin dakin dake hargitse da kallo sai warin dakin irin na,samari ke tashi daga dakin. Cikin ya mutse fuska take ce mashi, yanzu kaiko inda kake kwana baka iya gyarawa babana ace dakin dan musulmi ne haka inda ake ibada? Wai may ke damun kane haka babana na zaci kaine mutim na,farko da za,ayi koyi da halin shi nagari a gidan nan sai dai kasshh ban samu hakan daga gareka ba sadauki. Naga alamar abinka ba mai yankewa bane, sai a lokacin yadago kai yadan kalli mahaifiyar tashi yana fadin may kuma nayi yanzu maji? Yanzu fa na dawo daga makaranta tun safe da nafita gidan nan . To babana shine baka iya,gyara muhalin ka haka dubi fa kagani ai wanan wani abin cutarwa ma yana iya shigo maka baka,sani ba. Zan gyara ya bata ansa a takaice don yasan duk lokacin da tai amfani da kalaman babana a,gars shi maganace ta kwantar da hankali da fahinta take nufi a gare shi. Don ba ko yaushe take amfani da kalman babana a gare shi ba tafi kiran shi da,Sadaukin da kowa a gidan yake kiran shi kamar yadda mahaifin shi yake kiran shi dashi tun yana karamin shi dashi. Ta,dan dade a,tsaye tana kallin shi a cikin tausayawa dan nata ga,irin rayuwan shi ta bahagon halin da ya,fada ciki. Hawaye ne ya,gangaro mata a,daidai lokacin da ya,dan dago kan shi ya kalleta don jin da yayi tayi shiru a,tsaye bata fita ba daga dakin. Shiru yayi yana kallon ta sai ya dan dukar da kan shi gareta, tace babana ban son ganin rayuwan ka haka . Wanan rayuwan da kake yi ba,shine irin rayuwan da na,soka dashi ba a,rayuwan ka. Don Allah babana ka canza rayuwanka a gidan nan ka koma kamar ko wani yaro na gidan nan. Ina son naga ka canza ka koma normal life din ka kamar kowa a gidan nan wanan halaiyar dakakeyi ba,rayuwan alheri bace a gare ka damu ma kan mu da muke naka. Katai maki rayuwanka saudauki ka canza halinka don Allah kazamo min abin alfahari a,duniya, gama kowa dake tare damu. Zan so ace na zamo uwa abin alfahiri ga duniya na nasamu da dan albarka a,rayuwana, kamar yadda sauran uwaye suke alfahari danasu diyan. Zan so ka,sasauta halaiyar ka akan wanda kake a yanzu don samun natsuwar hankalina dana mahaifin ka. A hankali maji ta fashe da kuka,wanda kuka ya sa ta kasa karasa maganan da take son ta fada mashi. Maji ya ce cikin sanyin murya nifa ban san wani hali da nake yi ba,wanda har zaisa ki zubar da hawayenki haka akaina. Kallon shi maji tayi a cikin mamaki don watau shi bai fahinci ma yana,da nakasu ba ke nan tare dashi. Tace kako san har mutanen gidan nan sun fara zargin wai kana shaye shaye ne, Ya,dago kai da,sauri ya,dan kalle ta sai kuma ya dukar da kan shi yace maji nifa wa yan nan mutanen sun fara isa ta,sun fara saka min ido har da bina da,sheri haka? Ni dai ka gyara halinka shine bukatana a,gare ka idan ka gyara babu wanda zai dora ma,sheri ai. Ta juya tana cewa Allah ya kyauta kaji bukatana gareka don naga yanzu guduna ma kakeyi baka son shigowa nasan lafiyan ka kamar yadda kasaba yi a baya. Bin bayan mahaifiyar shi yayi yana mamakin mutumin da,yafara gano likin shi a gidan don haka ya zama dole ya canza takon shi tun mahaifan shi basu tabbatar da,zargin su ba akan shi. Don yasan in hakan ya tabbata ba karamin tashin hankali mahaifiyar shi zata shiga ba har ma mahaufin shi din dake nuna yanzu babu ruwan shi da shi yanzu.
****** ******* ****** Zaune take ta tula kudi a gaban ta,sai faman kidayawa take a hankali don gudin tai kure. Sai da ta kirga su cif tajera a,faban ta tana kallo sannan ta,sauke ajiyan zuciyar ta. Yanzu abin da ya rage min na hada kudin fridge din nan saura dubu goma don haka bari na kara kaimi naga sun hadu na,samu kafin azumi na dauko babban fridge wanda zai isheni sana,a yadda nake so. Tashi tayi da sauri ta mayar da kudin inda ta ciro su ta boye, don gudun kada wani ya gani yasan inda ta,aje don tasan da,zaran maigidan ta ya kyala ido yaga kudin nan sunan ta sorry don yanzu zai mata dadin baki sai ya karbe su gaba daya su huta. Abinda bata sani ba shine shi maigidan nata sam hankalin shi bai ga,abin hannun ta ko kadan don asali ma,shi bai bukatan wanan sana,an wahalan da yaga tana saka rayuwan ta a ciki yanzu. Don da,ace yana,da,hali da iyalin shi sunji dadin rayuwa a gurin shi. Amma ina talauci kamar ya yanke saka ne a kan shi don kullun bida yake amma kamar ba,ayi yake sai dai Allah bai hanashi dan abinda zasuci ba agidan daidai gwargwadon hali. Mikewa tayi ta gyara dakin har zuwa tsakar gidan su don akwaita da,tsabta ko yaushe duk da,talaucin su zaka,samu gidan su tsab tsab dashi. Yaran tane suka fara dawowa daga islamiya inda tun a,waje tasan da zuwan su din saboda hayaniyar su da taji tun daga waje. Sannu da gida Umma suke cewa sai faman ce masu take kun dawo sannun ku da,dawowa , Yar karamar yar ta,take cewa mama yau a makaranta malam yai muna alwala mungani nima zan iya yadda yai muna nagani. Nanyaran suka shiga bata labarin yadda malamin su ya koya musu yadda ake alwala har lokacin da mahaifin su yadawo daga kasuwa suka juya gurin shi yana,alwala suna bashi labari n abinda yafaru a islamiyar su yau.
ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,,