Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 38

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 38

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 38: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 38. Da,dare ba karamin farin ciki sadauki ya tsinci kan shi a ciki…

2,531 words

Da,dare ba karamin farin ciki sadauki ya tsinci kan shi a ciki ba don duk wani abin da yake ji cikin zuciyar shi yanzu ya,kau mashi aran shi. Hakane ma ya bashi dama,daga kwance yake kasafin irin abinda yake son yaiwa mahaifan shi don su fara,alfahari dashi a,rayuwan su. Su dai mahaifan shi murnan su kawai suke da,farin ciki akan dan su yaje lafiya ya kuma,dawo masu lafiya yadda suke fata. Fatan kawai dama Allah yasa wanan wasan da Allah ya,nufe shi da,zaiyi ta nisanta,shi daga,akidar shi ta,shaye shayen da ya,fara nisa a cikin sa. Gashi kuma,da,alama Allah ya taimake su akan haka don dai ko bai bari ba ya dai rage kan don yanzu ya,dawo kamili salihi dashi ba kamar da can baya,ba da ko su sai sunyi da gaske akan shi zaiji. Wanan rashin nuna,damuwa da,abin duniyan da,ake tsanmani daga masu irin fita wanan wasan kwallin da mahaifan shi suka,nuna mai ya kara sa,shi sanin cewa shi din dan gatane na kwarai. Sabon halin da,ya,tsinci kanshi aciki ma shaye shaye shi ya kawar mai da gatan shi a gare su . Adinin mu da,al,adan mu duk sun kyamaci mai wanan irin halaiyar tashi ta shaye shaye. Wasu hawaye masu dumi ne suka dan zubu mashi daga idon shi yai saurin mayar dasu a inda suka fito. Nan dai ya yanke hukuncin duk wasu tdare tsaren da ya dade yana planning din su a ran shi yana ganin komai ya tafi mashi yadda ya dace. Kwanan shi biyar da,dawowa yafita daga gida tun safe bai ko shigo ya karya,ba. Haka yasa hankalin Maji ya dan tashi don tasan yanzu yana gida ko yaushe bai fita waje. Amma yau ga abin karyawan shi bai shigo yaci ba ga kuma na rana har ana batun kare girkin dare kuma again. Haka yasa ta kasa daurewa tana jin shigowan Imirah gida don shi ke fara dawowa daga kasuwa ko yaushe, da kayan cefane da dan abubuwan da,suka sayo na gida. Maji tafito inda yake tsaye yana,ba Umma sako tace a Imirana an dawo lafiya yaya kasuwan? Ya amsa da Alhamdullahi a takaice kawai, Maji tace don Allah Imirah ko dan uwan ka yana kasuwa ne tare da ku don bai shigo gida ba tun dazun da safe . Yace waye dan uwa na Maji? Duk da tambayan ya bata mata rai amma sai ta share ta,dake a ran ta tace mashi Sadauki. Kafin yaba da amsa Umma tace, dan uwan shi don Allah gyara hausan ki mana. Kada ki sa mashi bakin jini da zargi ga mutane, ace ko tare suke shaye shaye dashi. Imirah yace haba Maji, may kuma zai kai Sadauki gurin ni tunda harkan mu ba daya,ba dashi. Maji tace Allah sarki ai zatona yana tare da kune a can kasuwan, kasuwan kan ba gidan yan maye bane ai. Ba ta dai juyo ba ta koma part din ta inda dama daga itace sai Bintu su Maryam basu dawo ba tukun. Ba,a jima ba suka shigo dawowan su ke nan daga makarant alokacin, sai suka shiga neman abinci. Maryam da tafita waje ta samo ruwan sanyi don sai sun saye basu da fridge a part din su. Nan ta samu Umma nata fada dan may za,ace wai Sadauki dan uwan Imirah ne ganin maryam bai hana ta fadan da takeyi ba. Maryam na dawowa take cewa halan anyi wani abin ne wai naji Umma na tafada wai dan shaye shaye don rainin wayo za,ace dan uwan tane. Bintu ce tabata amsa tace kin san basu da tunane da mama take fada wai don ta tambayi yaya imiranah yaya sadauki da,bai shigo gida,ba tun da safe yau. Ikon Allah shine kuma abin fada inji Amirah cikin nuna mamaki karara a fuskan ta. Komai fadan su dai ai ba,a raba anta da jini ko? Don basu san cewa wata rana suma abin zai iya shafan su ba ko, Nan Amira take ta fada ran ta a bace basu san shigowan shi ba sai ji sukayi ana cewa wai kedawa ke fada haka ne Mira, Tace hmmm ashe ma ka dawo yaya nida su Umma mana da basu so a zauna lafiya. Nan take fada mai abinda ya faru shiru yayi baice komai ba suma dai din hakan ne. Maji tafito da alwala tana mashi kallin mamaki tace kai ina ka,shige yau haka ne. Yace maji wallahi ina cikin gari kayan mune ya iso shine naje nai clearing din su a gurin da ake saukewa. Kaya kuma wasu irin kaya ne haka yace cikin wasa yana wuce kayan yan kwallo mana maji. Kai kan da kwallo Allah ya inganta kawai, don ya zama maka jinin jiki ko? Fatima kawo mashi abinci kinji tun safe mutum bai karya ba yana gurin zancen kwallo kawai aranshi. No Maji gaskiya,abar abincin nan don sha dan drinks a can kada naji yunwa saidai anjima da dare zanci. Yaro ke fadin wai ana sallama da Umar UF a waje, inji wani mutum. Mikewa yayi yafita saida Maji tai mamaki take cewa a ranta yau kuma Sadauki akewa sallama a gidan nan. Allah dai yasa mutumin kirki ne ba abokan shashancin shi bane suka fara biyo shi su mayar dashi ruwa. Amira ce ta sako zancen abinda Umma takeyi na kokarin raba su da yan uwan su don ganin su basu da komai wanda yakai ace sun hada alaka dasu. To koma maye ai dai ai su yan uwanku ne kuma duniya ta sani to may ye abin damuwan kai a ciki uwar ta,basu amsa. Kafin tai magana sai ga sadauki ya shigo yana zama yake cewa Amirah gobe zaku shiga school ne da safe. Wani abin kake so ne yaya, ya na,gyara zama yake cewa bani amsa mana kafinki min halinku na yan Nigeria. Tace idan da abinda zanyi sai na bari sai jibi ko na shiga yace dana gode sai yai shiru daga haka bai kara magana ba suke tahiran su kan wata yar uguwar su. Dawowan Alhaji yasa Maji fita tabar su don zuwa gaidashi kamar yadda ta saba, Sai da ya mike, tsaye bayan fitar mahaifiyar su, yake cewa don Allah Amira gobe ku kwashe kayanan gaba daya kufita dashi kafin nine na safe. Amma kada ki fadawa maji yau sai goben kawai taga kuna kwasa please angama yaya tace mashi do ita kadaice a falon lokacin su maryam da Bintu suna ciki. Maji na,shigowa bata ga sadauki ba take cewa,a,a shi kuma wanan din ina,ya tafi ne wai,? Bai faci abinci ba yau gaba daya Amirah tace yako fita ina ganin saida safe ke nan, nan Maji tasawa maryam da Bintu kira tace su zo sukaiwa yayan su abincin shi a dakin shi. Tai hakane don tagani idan yana gidan ko yafita don in fita yayi to gaskiya zancen ya fara baci ke nan kuma. Zun dauki abincin zuwa part din samarin gidan tun daga,nesa,suka gane yana cikin dakin nashi don wutan dakin da yake kunne a lokacin. A hankali ta kwankwasa kofan don itace a gaba maryam hankalinta yana kan wayan ta. Sadauki wanda yake zaune dakin shi yana karatun wani littafi mai ban tausayi yaji nocking din kofan shi mamakine ya kama,shi don dama har ya rufe daki ko. Don haka ya taso ya bude don yaga wanda ke kwankwasa mai kofa a wanan lokacin haka. Daga shi sai yar singileti da gajeren wando irin da maza ke kwanci dashi da dare idan zasu shiga kwana. Bintu ce yagani da kayan abinci a hannun ta ya zuba mata ido baice mata komai ba. Ganin yadda yake yasata dukar da idon ta kasa tana cewa Mama ce tace mu kawo maka abincika nan. Dan guntun tsuki yaja yace banace na koshi ba shine sai an biyoni dashi har nan kuma. Bai sanda maryam suke ba,saida taimagana daga bayan Bintu tace kasan maji in bakaci ba hankalinta bai kwanci ai. Maryam na koshi wallahi yanzun na,rage yawan cin abincin nan sosai don gudun kada nai nauyi da yawa na,kasa yin wasa kuma. Yace shiga ki aje min daga ciki, yadan jaye mata a hanya Bintu ta shiga ta aje mai a bakin katifan shi da sauri tafito bata sab yana gap da ita ba sai ji tayi tayi karo dashi. Tsaki yaja yana fadin ke dai yar kauye ce wallahi ko baki ganine zaki tureni haka kamar baki da ido. Yi hannkuri ta fadi cikin dan muryanta kamar zatayi kuka shi dai ya kauce mata ta,wuce ta gaban shi yai tsaki yace yar kauye kawai da ita. Maryam dariya take take cewa kai Bintu ke dai matsoraciyace wallahi kamar wace za,a kama ko tai laifi. Har suka shigo gida Maryam tana mata dariya take basu Maji labarin abinda ya faru. Maji tace wallahi in yana kiramin yarinya da yar kauye sai na bata mashi rai Allah, duk wanan kokarin da yarinya ke mashi baya gani.

Washegari kamar yadda ya umurci Amirah dayi haka,tayi don ta,tayar da Bintu suka,fara aiki don ita a,zaton ta fenti zai sa ai ma,shiyan nasu. Matan gidan kowa tana fita daga gidan daya bayan daya zuw gurin aikin su inda suke gulma a ran su cewa, kullun sharan daki kamar wani tsiyane cikin shi. Mani dai a zaton ta gyara kawai yaran keson yiwa shiyan don karan kan su kawai. Tara da yan mintina sukaji muryan sadauki yana cewa wasu mutane ku shigo dashi nan. Set ne na kayan gado tare da masu hakawa aka,shigowa Maji din dasu nan masu aiki sukansuka fara aikin gyaran guri kamar yadda ya dace. Labule sabbi, kujeri set masu dan karen tsada, fridge sabo dal dashi a kwalin shi, TV plastama babban size din sai center carpet mai laushi duk a falon. Dakunan ta duka ukku an saka sabbin gadaje a ciki don shi ana shigo da kayan ya fita abin shi waje, bai shigo ba,balle maji da imani ya cika ta tambaye shi inda wanan abinda bata taba mafarki ba ya fito masu. Kafin karfe biyu masu wanan aikin da yake aikin su ne har sun gama komai ko nan su Amira suka karasa sauran gyaran da yarage masu. Sai uku ya shigo gidan da ghana most go manya manya har guda hudu niki niki dasu aka zube su a falon Maji. Maji tace Sadauki zonan cikin damuwa da rudani take tambayan shi ina ka,samo wanan kaya haka. Ya lura cewa ta,shiga tashin hankali yasa shi zama kasa gap da kujeran da take yace Maji ko kin manta kin gura danki tilo guda sadaukar da ranshi wa kasanshi ne. Yace abinda kika yarda shine alherin shi ya fara zuwa maki a yau din nan duk abinda zan samu ga,wasan da nakeyi Maji nakine ke da yan uwana gasu nan. Sai mahaifina da kuna kakannina da suka nuna min hanya madaidaiciya da ta dace dani. Don haka kwantar da hankalin ki Maji dankine ya,fara kawo karfi lokaci yayi da zamu fara shiga mutane muma ayi damu. Maji yau ina matan gidan nan suke? Duk sun fita gurin neman na kasu da rufin asirin diyan su, amma ke kina gida kina masu bautan da basu gani har abada. Idan na samu bakiji dadin ba Maji ai ban haihu ba gare ki. Wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata don abin kamar a mafarki take ganin shi a ranta. Ji yayi ta dafo kan shi abinda ta dade batayi mashi ba tun yana yaro in zasu tafi makaranta take mashi haka. Takance Sadauki Allah ya tsare min kai Allah yabada sa,a Allah ya daukaka min kai Allah ya albarkace ka da arziki ta hanyar alheri. Yau ma da yaji ta dafa mashi kai yasan maka manci haka za,ayi sai yaji tace. Allah nagode ma daka azurta min Sadauki ta hayan daka zaba mashi a rayuwan shi. Ya Allah ka tsare min shi ka kare min shi daga duk wani abincutarwa da kuntatawa a,rayuwan shi Allah ka albarka ta min wanan yaron fiye da tsamanin mai tsanmani, Ya Allah ,,,,,,, sai kawai kuka mai karfi ya subce mata ta kasa karasawa abinda tai niyar fadi daga karshe sai a cikin ranta tafadi Allah ka,azurta shi da zuria masu albarka. Bintu ce mai karfin halin amsawa don duk kuka suke adakin gaba dayan su har ita Bintu din dake kallon ikon Allah. Saida sukaci kukan shi ne ya,fara yin shiru cikin su yake cewa Amira dauko jakarcan na baya ki bude. Tajawoshi dakyat zuwa gaban su inda ta bude turamay zannuwane irin na kasar ghana ciki makil dasu. Yacd tajawo dayan kuma shima dogayen riguna ne na yan mata acikin sa su takalma da hand bags, nan suka,rude suka shiga fitarwa, Dai dayan shadda ne ciki masu tsada suma dayan kuma kayan kantine nashi da yan kanneshi kana yasayo masu. Nan ya,ware wa kowa naahi kason kamar yadda yasayo su tun can ghana din. Maji tai matukar jin dadin haka a,ranta don yafara da yaddaya dace duk da nagari yayi yasamu yan uwa su sheda. Tasan Allah ya hore mata da nagari wanda yasan zafinta da darahan ta a idon duniya ke nan. Yace ban sayo maki kayan kitchen ba don ban san kayan da kuke so ba sai a saya a nan kawai. Maji tace a,a dakata ko wanan ma sun isa haka wallahi. Saidai banji ka fadi may kaiwa mahaifin ku ba har yanzu don baiyuyuwa ace ni kai min haka amma shi banji nashiba. Yace Maji na Baba daban ne nasan ya dade yana son harkan noma don haka noma nake son yafara bana sosai akwai kudin da zan bashi wanda zai dan isheshi yafara dasu. Allah yai maka albarka sadauki takara fadi a fil kowa yace amin cikin jin dadi da farinciki. Gardama ya fara a tsakanin Amira da maryam gurin rabon kayan su nan ya fitarwa kowa da wanda ya sayo mata ya mika masu. Bintu dai tana gefe tana kallon ikon Allah da jin dadin uwayen dakin ta ganin farin ciki ya sauka masu yau. Maji tace ban fa gane ba sai duk suka joyo suna kallonta don jin may zatace dashi. Tace naga kayan su Amirah amma banga na diyana,ba mana ko ita ba yar uwarka,bace. Shiru sukayi gaba daya don su sai a lokacin kan su ya kawo wuta ga hakan. Shiru yayi bai bata amsa ba kamar badashi takeyi ba ma sai da takara tambayan shi ne yake cewa ban sayo da itaba Maji. Don may sadauki shiru yayi kawai yana dakilar wayan shi bai bata amsa ba. Ta juta gurin su Amira tana ffadin ku miko min kayan nan a,kasa uku kowa ya kwasa. La Mama don Allah kibar masu watarana idan ina da rabo za,a sayo dani ai. Ba zaiyuyu ba gaskiya ku miko min nan kawai kunji tafada cikin bacin rai yace Maji bar masu sai a sayo mata a nan. Amma maji bata saurare shi tai masu jan ido suka miko kayan inda ta raba daidai ta cirewa Bintu suna ta bata rai don may za ai masu haka. Waya ma dole bai basuba saida dare ya shigo da guda hudu sai dai na Bintu baikai nasu kudi ba.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,

A LOKACIN MU KE,,,,,

Readers Also Read