A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 39
A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 39: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 39. Yau kwana arbain da,wasu yan kwanaki da tafiyan Sadauki don…
2,621 words
Yau kwana arbain da,wasu yan kwanaki da tafiyan Sadauki don haka a wani yammaci Alhaji ya dawo kasu Maji ta tafi gaishe shi yake ce mata. Maijidda kunyi waya da Umar yau kuwa tace bai kira mu ba don kasan kiran shi nada wahala ta nan. Indai ba shine ya kiramu ba ni ban faye kiran shi ba gaskiya, ya dan juyo yana kallonta ciki kada kai yace haba maijidda ya wuce ki kashe dubu daya da dan kai gurin jin lafiyan shi kawai. To Alhaji kudin fa ai yazama cacan kudi kulun gaskiya ace dubu dubu haba dai idan dai ya kira muji lafiyan shi ai. Yace tau yace min insha Allahu gobe zai karaso gida don yau jirgin su ya,sauka Nigeria da safen nan. Wani irin murmushin jin dadi Maji ta sauke a lokaci guda afili kuma tace Allah ya kawo muna,shi gida lafiya. Alhaji ya amsa mata da Ameen yace da farko naji tsoron tafiyan yaron nan amma kinga da muka,bar ma Allah zabin shi gashi har sunje sun dawo lafiya. Maji tace a hankali Alhaji nafika jin tsoro don ina gudun yaje ya kara hinjire muna a can. Ai kawai al,amarin daga Allah ne maijidda don dai ni san ba wai rashin tarbiya bane ya jefa yaron nan cikin wanan yanayi. Jerabawa ne kawai daga Allah ya zo min ta hanyan shi wanda mafi yawan mutane yanzu kowa da kalar tashi jerabawan da,ake jarabtar shi dashi. Allah ya sauwaka Maji ta fadi a fili tareda mikewa don tabar dakin don tasan idan takai wani lokaci a ciki yana iya zama masu matsala da maigirkin ranan watau mama Asiya. Ta koma dakin ta ta samu yaran ta kowa da waya a hannun shi suna dakala. Sai Bintu ce da bata da waya ta ke zaune tana karatun littafin islamiyan ta da take bita. Shigowan ta yasa su dan dogo kai suna kallon ta don sun saba idan ta je gaida Baban su tadawo suna kallon yanayin ta idan bada bacin rai ta,shigo ba don gudun ace yayan su ya aikata wani abin asha kuma. Sai dai sunga tsatson farin ciki a fuskan ta inda kafin su tambaya take ce masu Amirah ance gobe insha Allahu yayan ku zai dawo garin nan yau sun sauka lagos gobe zai karaso gida da yardan Allah. Gaba dayan su dadin wannan labarin sukaji don sun san tun da har yakai warhaka kuma ance sun dawo komai ya tafi normal insha Allahu . Ba kamar yadda suke daridari ba da farko don gudin kada yaje yai shaye shayen shi a koro masu shi. Washe gari tun da safe suka fara dan gyaran wuri da kuma yi mashi abinci na musan man dan taron shi. Maryam ce da Bintu suka gyara mashi dakin shi tsab don komai sada suka fitar suka share suka goge mai sabon zanin gado maji tabayar suka shimfida mashi. Wanda karfin aikin ma duk Bintu ce tayi shi ita kadai maryam sai karatun ta take a cikin wayan ta kawai. Ganin suna aikin yasa yan sa idon fahintar kila mai dakin zai dawo ke nan. Mama Asiya ce ta fara samun Umma da zancen cewa yau naga mutanen ki sai wani jin dadi sukeyi harda gyaran wuri. Nafisa tace da zan shigo dazun naga suna,gyara dakin yaya sadauki ai. Muga atsiyar da ya tsinano masu a can ai sai rawan kafa suke wai yatafi ya dawo. Wanan dan shaye shaye may kike zaton zai ita tsinano masu a can, ai yadda yaje haka zai dawo tsula dashi dan ganye kawai. Ranan sai kawai aka kafa dandali a tsakar gida don gulma katuwar tabarma suka shimfida wa kan su nan aka baje ana ciye ciye ana hira wai. Maryam ce tashigo gidan tana cewa yau kan gulma yakai gulma a gidan nan bakiga har tabarma,aka baza ba manya da yaran su a tsakar gida don kawai aga may yaya zai dawo dashi. Ni dai Allah ya kawo min shi gida lafiya yasa wanan tafiyan ta zama mai silar shiryuwan shi. Suka amsa mata da Ameen maji. Sun zage sai faman goge gogen falon su da babu komai sukeyi don dai ya haske kawai. Sun gama dan har wanka sunyi lokacin suna zaune falo suna dan hira jefi jefi tsakanin su. Suka jiyo muryan shi ya shigo gida da sallama a bakin shi, kamar muryan yaya sadauki naji a,waje Amira take fadin haka. Hamdala Maji tayi a fili tana fadin shine ba kama ba ai taji dadi don ko ba komai ta tsinkayo canji ga yanayin shi sosai don gashi ya shigo gida har da sallama a bakin shi yau. ,Nan sukayo waje don taron shi da saurin su hae suna karo da junan su. Kamar yadda ya tafi daga shi sai yar jakar shi wanan karon ma haka yadawo masu sai yar karaman jakar daya goya a bayan shi. Daga inda matan gidan suke zaune da yaran su suna shan rake suka tsura mai ido kawai. Shine yake ce masu sannun ku da gida mama daga haka bai karasa ba ya juya zuwa part din mahaifiyar shi. May na fada maki Asiya na fada maki tsula ya tafi tsula zai dawo muna rabu da dan matsiyaciya kawai masu gadon tsiya ta ko ina. Dariya suka sa dasu da yaran su a lokaci guda wanda sai da ran sadauki ya dan sosu don yasan dariyar a kan shi ne. Sai dai ya dake ya rugumi kannen shi da suka sheko suka rugumay shi suna mashi sannu da zuwa. Banda Bintu wace take tsaye daga gefe sai dai da murna a fuskan tana cewa, Sannu da zuwa yaya cikin yar muryan ta ko bai jita bane yadai ja kannen shi suka shige kawai abin su ciki. Bayan su tabi suku suku da ita tana dan dariyar yake a fuskan ta. Inda MMaji take zaune ya isa cikin farin cikin shi ya zauna kasa tare da sa kan shi saman cinyarta yana cewa Maji yaya na samay ku? Murmushi maji tayi tace anya Baba na kwallo kaje kuwa kaga yadda duk ka canza min a lokaci guda. Murmushi yayi yace kai haba dai maji kwallo ko naje wallahi ban ramay bane? Sai tai dan murmushi wanda rabon haka a tsakanin su ya matan lokacin shi. Maji ta,waiga inda Bintu take rakube tana cewa, Fatima kawo wa yayanki ruwa ko yasha Amirah tace da abinci ko gaba daya. Nan suka shiga kitchen din tare wanda Bintu ta fara dauko abin shan da suka shirya mashi takawo mashi. Ta duka ta aje zata juya yake cewa ke wata irin bakauya ce kinga mutum ya dawo baki iya gaishe shi ne. Amira dake aje tire din abinci take cewa aiko ta gaida kai yaya sai dai in bakaji bane. Maji tace kadawo ke nan ko hutawa bakayi ba zaka fara takura min yarinya ko. Ya juya inda suka aje mai kayan abinci a gaban shi yana fadin kai kai kai Amira duk ni kadai wanan abinci haka mai yawa. Ga,wacce tayi su nan ai da yawa tana nuna mashi Bintu dake can gefe kujera a zaune kasan ties a dakin. Amira tace ta ba bako yake ba yau ai batai laifi ba ko don ance bakon ka annabin ka. Sosai yaji dadin wanan karamawan da kannen shi da mahaifiyar shi sukai mashi haka wai duk shi sadauki keda wanan taron. Shigowan hjy Kubura dakin shi ya katse hiran jin dadin ganin shi da suke yi a lokacin Tashigo da fara,a a fuskan ta tana cewa yanzu su Anwar ke fada min wai bakon ghana ya dawo ina shigowa. Murmushi yayi yana cewa mummy mun samay ku lafiya ko? Lafiya kalau sadauki yaya hanya yaya can kuma I hope komai normal.dai ko ? Inda dane Maji zatace tsakani da Allah tazo taron shi amma yanzu data rage ta, sai take kallon makirci ne ya kawo ta kawai. Nan ta kare kitihin ta ta fita daga dakin daga inda Bintu take zaune tabi da kallon makira kawai ita da maji da suka san komai. Maji bayan yaran sun kaure da hira tadan fito tsakar gida tun daga inda su mama suke zaune aka jefo ta da hausa. Tsula ke nan wai tafiyan sundundun madundun yadda aka tafi haka aka dawo zaban kunya. Dan nagada ai bai iya gado ba dama taya za,ace kagaji abu kuma ka ketare shi. Maryam dake bayan Maji bata san tafito waje zubar da bawan lemun da suka,sha ba, sai jin muryan ta maji tayi daga bayan ta tana cewa. Mu dai mun gode ma Allah ai yaje lafiya ya dawo lafiya yan bakin ciki da suka so kada ya dawo sai su mutu. Da sauri Maji ta juyo kanta tana cewa ke maryam ban son rashin kunya fa da suke zancen su sun ambaci sunan wani ne. Sadauki da suke daki suna jin amsar da maryam ta bayar sun san akwai magana a waje sai sukai shiru daga ita har sadauki din lokaci guda. Maryam ta shigo tana turo baki gaba tana cewa yan bakin ciki kawai dama nasan sheri da ganin kwam ya,zaunar da su ai a gurin kuma sun gani. Maji ta shigo dakin don haka maryam din tai shiru don tasan in taji tana mita,yanzu zata balballeta ne da fada. Sai da maji ta zauna ta dube su a nutse take cewa abinda nake so daku maryam shine. Duk wacce taji a na,sake magana a gidan nan inda ba sunan mu suka ambata ba kada wacce ta kara tankawa kowan su. Amirah tace Maji su wasu irin mutane ne da son fitina daga dawowan mutum zasu fara sakewa mutane magana kamar suna jirace da shi. Maji tace suna jirace mana ba hassada bane kawai rudin shedan ai komai mutum zai iya yi don jan fitina. Fitana,suke so don sunga yadda yaje haka ya dawo masu shine abin dariyar su ai tunda dan matsiyaciya ce shi. Murmushi kawai Sadauki yadan yi yace su suna nan da halin nasu har yanzu wai. May zasu fasa tunda kullun mugin nufi suke sakawa akan mutane inji Amirah tana mikewa take fadi hakan. Haka fa jiya naji Nafisa tana zagin Bintu wai yar ci rani ba bu ranan komawa gida anga wuri. Maji tace sai dai su mutu kuwa,don ko babu ranan komawan Fatima gida a gidan nan. Bintu tadan ji kunya ta,sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta. Maji tace gani sukayi yar ci rani tafi su mutunci da sanin ya kamata shine hassadan su, don babu wanda zaice tai mashi laifi a gidan nan tunda bata shiga harkan kowa. Ta juya inda Bintu take zaune tana cewa don haka Fatima ki saki jikin kawai ki dainawa kowa dari dari tunda ba wanda ya isa ya koreki cikin su. Wama ya isa inji Amirah bakin ciki ne kawai da hassada don ko ranan naji yaya Imirana yana cewa, wai ina aka samu yar kwara ne haka wai. Sai naji Umma tana mashi fada wai ina kwara din take yarinya haka da fari kamar zabaya. Duk kan su dariya suka sa Maji tace cikin dariya kai bakin ciki ho ina Fatima tai irin farin zabaya kuma in ba,sheri ba. A fakaice ya dan saci kallon farin Bintu da ake magana shi dai baice masu uffan ba a cikin zuciyar shi kawai yake magana shi kadai kan al,amarin kishiyoyin mahaifiyar su. Tun suna yara yake jin suna kirawa Maji kalman tsiya har su kan su din diyan ta. Mikewa yayi a lokaci guda yana fadin zan je dakina maji ina key dina yake ne wai ? Yana fita daga dakin daga gurin da Bintu take zaune bata san lokacin da ta sake ajiyan zuciya ba a fili. Duk suka juyo suna mata dariya Amira tace dodon ki ya fita ke nan ko , don naga idan yaya yana guri zakiga Bintu a,takure kamar wace za,a yanka. Ba dole ba yana son firgita min yarinya da mugun halin shi ki saki jikin ki Fatima haka halin shi yake baudade ne shi ko yaushe. Murmushi kawai Bintu tayi batare da tace masu uffan ba,sai mikewa tayi tafara kwashe kayan da suke a tsakar falin nasu.
****** ********* ****** Yaron yana tsaye tana loda mashi ruwa a,sabon roban da ta,sayo mashi wanda yafi na farko da yake fita dashi girma. Don yanzu ya dan fara sabawa da,tallan ya iya,ba kamar farko da yake dawo mata dashi ba idan ya fita. Tana gamawa ta juya inda yake tsaye tana fadin na jakka da hamsin ne na saka maka kai sauri ka,sayar kadawo kafin mafadacin ubanku ya dawo gidan. Ya dauki ruwan da,kyat yai mata,sallama ya fita, hat ya yi nufin zuwa inda ya saba kaiwa gurin masu wasan ball sai kuma ya fasa yace bari yakai wani guri da yaga ana aikin gina. Yana,tafe yana fadin a,saya,ruwa mai sanyi ruwa dai, mai sanyi, Sai yaji ance daga wani gefe pure water da sauri ya juya zuwa gurin har yana,dan tuntube. A bakin wani shago wasu matasa ne zaune su hudu suna hira sukackira shi. Yun bai karaso ba dayan yake cewa kai amma yaron ga gaskiya yana da kyau gashi dan tallakawa yana,talla amma tsab tsab dashi wallahi. Ai kasan wasu iyayye suna da kokarin gyara yaran su kafin su fito yafi kazo sayen abu gun yaro kazanta ya hanaka iya,saya. Ysron na karasowa gurin su dayan yace sauke mana dama tin da,zun nake nema ruwa masu sanyi wallahi don layin mu jiya babu wuta wallahi. Nan suka fara zukan ruwan sai da kowa yasha leda biyu biyu dan sanyin da,ruwan yayi sosai ga dama ana,dan karen zafi a garin. Ganin da Aliyu yayi yanzu yanzu yayi cinki yasa shi dan samun guri dan nisa kadan dasu ya zauna kafin su sallamay shi su bashi kudin shi ya tafi dama ya gaji nauyin ruwan yai mashi yawa. Da haka mutanen dake wucewa suka zo suna saye har ruwan ya,saura kadan a roban. Sai ga,wata mai abinci tazo ta zauna daga gefen shi take ruwan ya kare ya karbi kudin shi ya juya gida da sauri ya,karo wani. Wasa wasa,sai yagane gurin ana,samun ciniki fiye da inda yake zuwa da,farko don haka ya mayar da,wurin gurin kai tallan ruwan shi ko yaushe. Yana mayawa kusan biyar a rana kafin ya koma gida don zuwa makaran ta da,sukeyi da yamma. Watarana kuma in yan tsiyan sunackan maria sai tace mai idan sun tashi cin breakfast ya gudo yazo ya fita mata da ruwan ta. Da sannu yan gurin suka fara sabawa da yaron har suka yarda dashi suka,fara dan aiken shi sayen taba abinci da sauran su. Yakai yanzu inva ruwan shiba basu sayen ruwan kowa do shi ko yaushe ruwan shi zaka samay shi da sanyi sosai koda ba,wuta don freeze maria yana aiki sosai duk yadda aka kawo wuta zaiyi saurin daukan raba yai sanyi. Tun maigidan yana zargin tabarbarewan karatun dan shi yana fada har yagaji ya,saka,mai ido do uwar bata bari ya,fadi tinda tasan abinda take shukawa a bayan shi. Sosai maria take jin dadin yadda danta yake mata,talla haka tana cewa Allah ya,bashi kan ciniki sisai tayi sa,an haihuwa ita. Tan godewa Uwarta data,bata wanan shawaran da badon haka ba da yanzu tana,nan tana,wahalan neman dan talla bata samu ba. Kulun bankin ta,sai bunkasa yake don yana samun canji suna shiga mashi yadda ya dace. Yanzu ji take koma mijin ta yasani baida yadda zaiyi da ita don bazata iya hanawa dan ta wanan tallan ba. Shiko maigidan mutane da dama sun shatare shi suce sunga Aliyu yana tallan ruwa da yazo yai magana bai gand komai gareta. Don haka yaja,bakin shi yai shiru har ranan da zai kamasu da hannun shi ranan yai alkawarin zai dauki mataki a kanta, sai ta rena kanta ga hakan.