Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 51

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 51

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 51: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 51. Washe gari mukayi bakuwa a gidan mu kowa bai santa ba sai dai…

2,444 words

Washe gari mukayi bakuwa a gidan mu kowa bai santa ba sai dai tashigo gidan tana tako daidai da ita tana tambayan mahaifiyar U F. Mama Asiya tai mata nuni da dakin maji cikin binta da kallon ke kuma daga ina. Tana cewa o mun shiga uku U F kuma a gidan mu kamar gidan wasu arnaku can mukan wanan yaro yazama muna jaiba agidan nan wallahi. Daga kofa ta tsaya tana sallamu alaikum daga ciki muka amsa mata. Tashigo yar gaye ce ta karshe ga kyau ga ilimi yana nunackan shi a fili. Sai data zauna take cewa maji tare da dan zaudowa saman kujeran ina wuni mama. Lafiya kalau inji maji tace kunzo lafiya ta amsa da fara,anta lafiya kalau mama. Sai sukai shiru maji ce tai karfin halin fadin ban fahince ki ba don ban sheda ki ba yar uwa. Mama baki sanni ba, well na dai zo ne nan don daki Umar U F ni yar adamawa ce ina son na auri yaron ki ne shikuma ban samu kan shi ba shiya sa nace bari na zo na nuna kaina a gare ku. Don Allah ko daddy din shi yana gida shima mu gaisa dashi, don yasan ni na san shi. Ikon Allah inji maji tace mahaifin nashi yanzu baya nan ya tafita yana kasuwa. Tace ok ba matsala ai ina garin zamuga juna da dare idan ya dawo gida. Sai ta wani harde kafan ta daya saman daya tana taunan cingan a bakin ta kas kas kas. Mukan ido muka zuba mata wanan fitsara haka wai zamani ina zaki damu hakane? Kai A LOKACIN DAI MU KE KAN,,, Juyowa tayi inda muke a zaune tana cewa, sannun ku fa yan mata ya kuke cikin wani daga muna hannu? Ni dai na mike zuwa ciki na hado mata kayan drinks na kawo mata ta karba tana cewa yauwa na gode fine girl. Waya ta dauka ta kira layin shi mun dai ji tana ce mashi yazo gida gata nan dakin mama. Nasan tambayan ta yayi wata mama, sai cewa tayi mummcy mana ta sokoto. Dama na kusa karasa abinci na mike nafita, zuwa kitchen na duba girki na na samu ya dahu nan na tsaya na hado ma,bakuwar mu abinci mai kyau dashi . Daga kitchen ina jin muryanta tana,waya sai kiran abokan ta take tana fada masu tazo sokoto yanzun haka tana dakin mumm din U F a zaune. Sai gashi da saurin shi ya iso gidan tun a kofan gida ya sheda da gaske takeyi tazo garin don ganin motan ta da driver ta dayayi. Tun da sadauki ya diso falon yaji wani irin bacin rai ya kama shi a ran shi yake fadin wai may mata suka mayar da kan sune yanzu? Ya shigo da sallama a lokacin na fito daga kitchen dauke da abincin da zanbawa bakuwar mu. Tana ganin shi ta saki wani shu,umin murmushi tare da cewa my man you think iam joking ko ?. Ta wani shagwabe murya tana cewa I really miss you alot and i can't keep it, Dole na biyo ka don nazo na ganka nakuma ga su mama da little sisters din mu. Sadauki ya dan shafa sumar kan shi da hannun shi na hagu ya dan kalli inda Maji take zaune cikin kallon ikon Allah. Don yasan yau sunga fitsara a gurin Fatima ba kadan ba don ita bata da kunya ko kadan. Tace ya naga ka,wani bata rai ko you are not happy with me here ne? Yace cikin yanayin su na yan duniya No ba haka na bane ban dai yi expecting din ki a nan bane. Tace ai na fada maka zan baka surprise dama to gani yau a,sokoto kuma dakin mummcy. Yace saukan yaushe ? tace wallahi dazun nan na iso dama nasan bazan sha wahala ba gurin gane gidan ku don sha haranka. A kaduna na kwana shiya ka gan mu a wanan lokacin, amma fa gaskiya akwai nisa. Yace to ya hanya? Tai wani har da idanuwanta tare da langabe kan ta tace hanya lafiya kalai tunda na gan ka. Sadauki ya juya inda maji take zaune ta hade rai ba yabo ba fallasa a fuskan ta a lokacin. Ni dai na,aje abinci ina cewa, ga abinci nan tace yauwa sannu little sister wai ya sunanki ne tunda nazo kike wahala dani. Sai da na dago daga duken da nake nace Bintu tace wawwwo, sunan mu daya dake ashe. Amma ki daina cewa kanki Bintu kamar wata yar kauye akiraki da,Fatiman ki kawai ai nice, name ne sunan mu. Sadauki dai yakai zaune daga dayan kujeran nan bakuwar ta mayar da hankalin ta a kan shi suna dan hira jefi jefi. Wanka na,shiga na fito na saka wani dogon riga light gren mai kamar bubu daga sama kasa an mashi sharp yafito da sura na na,daura dan kwalin shi a kaina. Sam na ma manta cewa da bakuwa a falon nan nafito ina cewa Anty Amirah wai yaushe ne zamu tafi gaida baban su Amata. Wai wanan pretty din itace last born din mune gaskiya tana da kyau sosai wallahi. Kamar bazai bata amsa ba sai can yace No diyar sister din maman mu ne ita ga dai sisters dina Amirah ga maryam itace yanzu a,matsayin last born din mu. Yanzu ita wanan din ba blood sister dinka bace yace a dan hasale na fada maki yadda muke da ita ai ko. Take ta hade fuskan ta, tace there's problem here yace akan may fa tace No barshi ina dai magana ne kawai. Maji bata falon tashiga ciki don bata iya,karasa hadiyan takaicin da yazo mata har dakin ta yau. Wanan abin haka ba kimtsi ke kiran kanta da,suna wai sarakuwarta ta ina ? Kai duniya kowa da,tashi matsalar dai kenan yanzu ita haka duk rabin jiki kusan tsirara shine wai tazo nuna kanta a gurin sarakai a haka. Kai wanan tanbadewar da fitsara da may yai kamane haka wai tundaga wata uwar duniya yarinya ki taso kice wai kinzo gurin na miji. Ban kai ga zama ba naji muryan maji tana kirana daga ciki da sauri nake na nufi gurin ta. Zaune take saman gadon ta hannunta yana rike da caunter na zikkiri take ce min har yanzu wanan fitsararar bakuwar taku tana nan ke nan bata tafi ba ko? Nace ai zaci anan zata kwana ne don naga daga nesa ta fito. Tsaki taja tare da kawar da kanta a gefe tace yaro zai jamin wani sabon abin fade a gida yaya zanyi na fada mashi yai gagawan fita da ita gidan nan kafin mutanen gidan nan su ankara da ita. Nace mama bani wayan ki ta mike min gurin sunan shi nai mashi massage kamar haka. Ka gagauta fita da ita kafin mahaifinka ya dawo yasamay ta nan. Na tura mai ina turawa nafito daidai ya fara karantawa wani kallon ke ko yabini dashi. Nace sannu da zama ko wani kallo ta watso min kamar tasan nice na turo mai da sako yanzu tace yauwa. Amirah tace, yau zaki koma dai ko? Murmushi tayi tare da,gyara zama tace a,a har kun gaji da nine ke nan ko Amirah tace a,a ha mutum ai bai gajiya da bakon shi. Yana gama karata massage din ya dagi kan shi sai kai mukai tozali dashi ina kallon matar . Harara ya,kara watsa min niko nai mashi dariyar mugunta a fakaice. Muryan shi mukaji yana fadin Fatima muje na kaiki inda zaki sauka kafin dare yayi cikin diriricewa. May kake nufi da hakan ba a nan zan sauka bane gurin mummcy ? Yace baki da hankali ne a cikin gidan namu zaki sauka don baki da kunya to mu nan ba haka al,adan mu yake ba Yace so ki tashi na kaiki kafin dare yayi ban son daddy na ya dawo ya samay ki a gidan nan haka. Don mu ba haka al,adan mu yake ba ya mike don dale itama bashiri tamike tare da daukan hand bag din ta tana cewa ina mummcy muyi sallama yace ta shiga alwala ke nan. Yana gaba tana bayan shi suka fice daga gidan aiko basu dade da fita ba sai ga Baba ya dawo daga kasuwa a lokacin. Sai da suka bar uguwar ya sauke ajiyan zuciya tare da cewa look Fatima bai nai maki wullakanci bane da hakan amma idan har mahaifina yadawo ya samay ki a gidan akwai matsala babba wallahi. Kakanki kin sani wanan tsarin da kikazo dashi ba tsarin mune na hausa fulani ba. Tai wani wal da idanuwan ta tace nima nasan da hakan amma ban dauki wanan a wani abu can da zai iya kawo maka matsala kamar ka babban yoro haka. Yace wai ma ba wanan ba may yakawo ki garin nan ne wai Fatima ? Fatima tai wani marairaicewa tare da kallon shi cikin wani yanayi tace, Matsala aka samu danaji kace an maka mata agida ana batun auren ka shiyasa na kasa zama naga gara nazo ayita a kare a gaban iyayyen ka. Sadauki ya katseta da cewa dakikazo gaban iyayyena kice masu may ? Yace look Fatima da farko na so na karbi bukatanki gare ni amma yanzu hakan da kikai min duk kin jagula komai don haka idont think zan iyaci gaba da zama dake kuma again. Ran Fatuma ya,sosu da jin maganan da sadauki yai mata sai dai dole yasa ta daure don tana son guy din. Da sauri ta juyo gare shi tana cewa cikin hada hannayen ta biyu guri guda tare da marairaicewa tace don Allah U F kada kayi fushi dani. Yin fushin ka akaina zai iya jefani cikin mawuyacin hali a rayuwana sosai wallahi don na mutu da son ka sosai wallahi. Yayi wani guntun tsuki tare da kawar da kan shi gareta yana cewa don may zaki biyo ni har garin mu don baki da hankali. Tace kayi hakkuri wallahi duk na,rude ne da ka fada min zakayi aure na,rasa may zanyi akai shiyasa nabiyo ka har nan. Sadauki ya kara jan tsuki ya kalleta a wullakance yace na fada maki cewa anyi min mata a gida kuma bazan canza maganan iyayyena ba insha Allahu akaina. Yace kuma ki sani na kyaleki ne yanzu don garin mu kikazo don haka yasa na kyale ki idan badon haka ba da na dauki mataki a kanki sosai. Don bazan yarda ki hadani fada da iyayyena akan ki jamin wullakanci a gidan mu. Ya farka mota da karfi cikin five star hotel da suka shiga da alama ran shi yakai kololuwar baci a lokacin. Nan Fatima ta kifa kai tafara kukan tana rokon shi akan yayi hakkuri ya,aure ta zata zauna da wata su zama matan shi su biyu. Tace na gane wanan far yarinyar dana gani itace proposer taka don naga tafaye shegen kyau. Yanzu akan wanan karamar yarinyar kake min haka may zaka,gane a gurin yarinya karama haka ne please cikin kuka take magana. Yace look Fatima na fada maki tun farkon haduwan mu ni ba mazina ci bane kuma ban iya,neman mata ba ina under control din iyayyena . So kike akan ki na saba dasu ne for god sake don haka ki sauka na sama,maku masauki da safe ku kama hanya ku tafi. And kuma na roke ki tun magana bata kaimu ga bacin rai ba kada ki kara,shiga harkata is over hakana. Nan ya bude mota da zuman tafito su shiga ya kama mata masauki sai ma kunya da yake ji kada wasu su gan shi da mace azaci yazo yin wani masha,ane. Cikin kuka tace no kabarshi zamu koma kaduna mu kwana gobe na koma Abuja. Yace is better for you. Nan tafito tashiga motan ta driver yajata tana kuka suka kama hanyan kaduna da yamma lis sosai. Ya sauke numfashi duk da yaji tausayin ta yasan wanan shine kawai hanyan da zaibi yasamu kan shi daga shu,umancin ta akan shi.

A gida kuwa maji takai kololuwa da bacin rai sai jiran shi take ya dawo da yadawo yara yaba sokon maganin mama da kuma kaji da drinks da yasayo masu sanyi. Yace ace yana massalaci zaiyi sallah mamatace koma may zaiyi ai zai shigo ya samay ni gidan nan. Bai shigo ba sai da suka sallamay isha,i yashigo cikin gida kannen shi na gaida shi amma bai iya amsawa ba idon shi yana kan mahaifiyar su don jira yaji may tace mai yakeyi. Ya zauna Amira tana fadin yayana kadawo ya bakuwar ta mu take, nan ma shiru yai mata baice mata uffan ba sai take cewa, a can ka barta ne ?. Don Allah Amirah ki barni na huta haka na wanan tambayan ya isheni wallahi haba gaki kamar yar jarida. Zama yayi ba,wanda yace kallah a cikin su sai zuwa can Maji ke fadi a da can baya idan ance min kana hurda da mata bazan taba yarda ba koma waye ya fada min. Amma yanzu da yake ka fara rike kudin kanka gaskiya nai mamakin ganin wanan irin yarinyar ace wai da,su kake harka. Allah yaceceni in ba kuma wani sabon rayuwan ne ka bulle min dashi ba aji dadin yin min sabon zagi a gidan nan. Maryam na gaba ina bayan ta muka fito daga cikin daki mun samu mama tana mashi fada sosai kan wanan sabon halin da tagani a gare shi. Maryam tai tsagal tana cewa ni dai kwata kwata,batai min ba mace haka yar bariki gata nan da ita sai wani iskanci take wai wayewa ke nan. Maryam ba ga ku nan da irinta ba a gida ina yanzu Nafisa haka take shiga sai kaya ya matse ta sosai duk suran jikin ta a waje. Amirah ke fadin haka wa maryam tace idan zagine kuma ai akwai shi a gidan ku. Maji dai fada sosai take mashi akan mutum yayi hankali da duniya kafin ta kure mashi don duniya,ba matabbaci bace. Baiyi magana ba sai chartting da yake da,wayar shi a zaton mu da bakuwar shi yake fira kafin ya fita zuwa gurin ta. Amma har dare muna dakin zaune tare dashi sai hira yake da wayar shi kawai da amsa call. Maji tace daka bar yar mutane acan may zataci sai a lokacin yai magana yace sun tafi maji. Tace acikin daren nan suka tafi haka basu gudun dare yai masu a hanya. Bai ce uffan ba yana zaune har dare goma da wani abu yamike yana fadin zai tafi ya kwanta sukai mai sai da safe kaina na duke ina karatu tun zaman shi ban yi magana ba a falon.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,

A LOKACIN MU KE,,,,

Readers Also Read