Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 50

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 50

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 50: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 50. Wanan dalili fadan nasu yasa ya yanke shawara a ranshi zai…

3,539 words

Wanan dalili fadan nasu yasa ya yanke shawara a ranshi zai nisanta kan shi da gida, don gudun bacin ran mahaifiyar shi kada ciwon ta yazo yatashi mata a sanadin bacin ran shi. Sai da dare ne daya,shigo yake fadawa Maji cewa zaiyi tafiya zuwa kasashen waje kuma yana ganin zasu dan dade a can din. Maji tai shiru kamar bazatai magana ba sai zuwa can tace sadauki ba wai ban son tafiyan ka nisa bane a,a. Halin rayuwa irin naka nake tsoro anan ma da kake yaya aka,kwashe dakai balle kayi nisa da mu inda ba makwabi. Yace Allah nan ai Maji insha Allahu abinda kike zato bazai faruba don wasan mu ba,a yarda mutum yai wanan dabiar ma. Tace to shike nan sai ka samu mahaifinka ka fada mashi don yasan abinda ake ciki kada sai kashirya yaji zancen daga sama. Ya samu mahaifin shi ya fada mashi zasufita zuwa waje kuma zasu dan jima acan suna wasa da sauran kashe nan yaja mai kunne tare da fatan alheri a gare shi. Bayan kwana biyu ya shirya duk muna falo ya shigo sallaman su inda kowa ke mai Allah ya tsare da fatan alheri suna ta bashi sakon abinda zai sayo masu a can. Nidai ina gefe bance komai ba bayan Allah ya tsare da nai mashi ban kara tankawa ba saida zai tafine muka fita rakiyan shi wanan karon hardani da ban fita rakiyan shi saida na fita. Motar shi a gida ya barta yace wa Amira idan zamu school adinga zuwa dashi don dama sun iya mota su.

****** ********* ****** Yau Aliyu yana dauko talla direct dakin sisko ya nufa ya samay shi yafito daga wanka yana daure da towel a jikin shi. Sai yaron yadan tsaya daga waje don ganin shi haka da yayi ba,sutura a jikin shi. Yace shigo mana boy may zai sa ka tsaya daga waje sai yadan aje roban tallan shi daga waje kadan yace shigo dashi mana kada wani yagani kuma asan kana nan. Sisko baiji kunyan cire tawul din dake jikin shi ba wai yana shafa mai haka yasa Aliyu yadan kawar da idanun shi gefe. Dago kan da yaron zaiyi yagani ko yagama sai ganin Sisko a gaban shi gap dashi yayi tsirara haihuwan uwar shi. Ya na mika mashi mai wai ya shafa mashi daidai cinyar shi yaron yakarba ya fara shafa mai sai wani lumshe ido dan iskan keyi a lokacin , Nan wasa yafara canza launi ya shiga yiwa Aliyi wasu abubuwa da yaron ya kasa hana shi yi mashi yana cewa ba kaga yadda muka kalla ba a TV ranan dakai. Shine nake son karafa koyo kaga inka girma ka iya abinka ko nan yaron baiyi aune har yakai ga tube shi ya danne shi sai da ya biya bukatan shi ya sarara mashi sai faman ihu yaron yakeyi don yafi karfin shi sosai. Yaron duk da sisko ya sauka a kanshi bai fasa kukan neman taimakon da yakeyi ba. Yuka ya jawo ya nunawa yaron tare da,bashi tsoron yace idan ka fadawa wani abinda nai maka sai na yanka ka wallahi ka mutu gaba daya wawan banza mai shegen tsoron tsiya kawai. Dakyat ya samu har yaron yai shiru yabar kuka nan yadaga gadon shi ya dauko dubu biyu yaba yaron yace yaje yasai duk abinda yake son ya saya ci . Amma kada ya fadawa kowa abinda yai mashi inba haka ba har baban shi sai ya kashe. Ganin yaron bai iya tafiya yasashi tare mai mashi akaishi gida yana,tajawa yaron kunne. Yaron ya isa gida da kyat yake tafiya ya samu har maman shi ta gama abinci tana ganin shi take cewa a,a yau har ka dawo haka . Tace aje roban ga abincinka can ka dauka kafin babanku ya dawo kadan kara fita. Sai ya shiga daki yafito yakuma koma da sauri ya kasa tsaye ya kasa zaune. Amma sakaren duk bata kula ba sai cewa take wai may kake nemane haka ka zauna mana kaci abinci kafita. Sai yaje gurin frizer su ya dan dafa don ya zauna aiko sai ya saka ihu, da sauri ta aje kwanon da taje debo ruwa ta nufo shi tana fadin wai may nene haka tunda ka dawo nake cewa ka zauna amma kana min wani abu can dabo dabo dakai. Maza zauna kaci abinci kayi kafita sai hawaye shar shar yace mama, mama wallahi ban iya zama. Ikon Allah may yasamay ka da,baka iya zama kuma yaron yai shiru yana dan buga kafan shi tace maza zauna dan bura uba kawai ni zaka kawo wa diban albarka. Yaje zama sai kuma ya mike da karfi yana tsala ihu yace wallahi mama ban iya zama da sauri ta kamo shi lokacin yaron ya tsananta kukan shi sosai. Wandon shi tacire tagani ko kurjine ya samay shi aiko tafara cin karo da ajiyan maza ta hankada shi da sauri bata san lokacin da tace na shiga uku ni mariya wa yai maka wanan ta,asan haka. Ina sai ihu yaron yake wallahi mama na bari take ta saka kuka abuna farko dayazo mata a rai shine uwarta ta kwsheshi tare da rufe gida suka nufi waje nan ta tare mai mashi sai gidan su. Uwarta naganin yanayin su tasan babu lafiya may yafaru may ya samay shine wai? Tana kuka tana mayarwa uwarta abinda ya faru da yaron tambayan duniya sunyi mashi amma basu gane komai ba sai kuka yake yaki fadi. Uwarta ce kinga mariya wanan magana yafi karfina bari mu nemi mahaifin yaron nan tun abu bai lalace muna ba. Mariya tasa hannu akai tace ta shiga uku umma baifa san yana talla ba dama. Tace yau kan ai ba boyo don dole yasani don wanan magana,banamu bane mata. Nan takira samari kannen maria suka dauki yaron zuwa asibiti guda kuma yatafi kasuwa kiran mahaifin shi. A sukwane ya iso asibitin yana tambaya ana fada mashi cewa wani ne yai lalata dashi ta baya kuma asibiti sunce basu taba yaron sai an kira yan sanda. Karasawa yayi gurin yaron yace Aliyu wa yai maka wanan abi haka a ina ka hadu dashi, Bai basu amsa ba sai kukan da yakeyi dole suka nufi gurin yan sanda dashi nan aka tasa shi gaba da tambayin hikima irin na yansanda. Yaron yace yace ina fadi sai ya yankani kuma ya kashe babana da kyat dai aka samu yafara magana cewa. Ummh dama wani ne mai sayen ruwana kullun shine shine yace nazo dakin shi kullun na dinga kai ruwa yana saye shine yau yau danaje sai sai ya kamani ya danne yai min haka? Salati uban yasa yace Aliyu dama kana tallane ban sani? Cikintausayi da langabe kai yai maganan tare da kurawa yaron ido. Ya juya inda yan uwan maria suke tace shike nan maria taci amanata ta cuci yaronta ta tona min asiri a garin nan. Sai yakai zaune darsha ya sake wani irin kuka mai tsuma zuciya inspector yace yanzu ba wanan ba ku tashi muje asibiti a duba yaron nan a gani tukun don a san halin da yake ciki don da gani yana jin jiki. Nan suka dunguma sai asibiti da yaron saida yan sada suka sa hannu likita ya fara duba yaron. Nan yake sheda masu sai anyi mashi aiki an rage mashi abinda ya shiga cikin shi kuma aikin akwai tsada don sai sukanshe kudi dubu dari da hamsin cikin ragowa. Uban yaro yafara rusa kuka yana ya shiga uku ina zai shiga ya samo wanan kudin haka masu yawa. Dole aka fara neman inda za,a samu kudi don a taimakawa yaron dake cikin wahala.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,

A LOKACIN MU KE,,,,,,,

Tun bayan fitan yaya Sadauki a falon dakin shi ya nufa kai tsaye ya fada a kan katifan shi ya kwanta yai lamo tankar wanda yake barci, sai dai ba barcin yake ba. Damuwa ce tayi masa yawa a ran shi a hankali wasu yan siraran hawaye suka rika silalowa daga idanuwan shi. Ya dade a haka ya mirgina gefe daya yana fadi a fili, wayyo rayuwata may yasa nake yawan tsintar kaina a cikin mawuyacin halin komai na tashin hankali akaina yake faruwa ni kadai a gidan nan. Allah ya jarabci rayuwana da masifa saka uwata a tashin hankali ko da yaushe . A yadda ya lura maji ta dauki son duniya ta kwallafa mashi shi kuma gashi ya kasa bata farin cikin rayuwa. Ya kai zaune daga kwancen da yake yana cewa ya Allah kada kasa na zamo sanadin jefa uwata a masifan rayunwata. Gashi tunda ya tafi waje bai mai da hankali ga sha ba amma yana dawowa gida sai ji yake zuciyar shi tana azzalzalar shi sai da yaje yasha ya samu natsuwa a zuciyar shi. Ba don wanan yar kauyen yarinyar mai saka ido ba da ta taimake shi da bai san yadda zai yi ba idan maji tafito ranan ta fahinci a buge yake. Can kuma ya tuna zancen baffan shi wai ba zai ba mashayi yar shi ba shi dama Rahama bata gaban shi abudai ne in Allah ya nufe ka dashi ba yadda zakayi. Tuna siffan Rahama yayi bai san lokacin da ya sake wani tsuki ba akan wanan abin har za,ai masu wulakanci shi da uwar shi a cikin gidan su. Yana da,budurwa da ta lake mai yar adamawace amma saboda zancen Rahama da maji ta nace shiyasa ya,fita zancen ta kuma yarinyar irin masu son abin duniya din nan ne ko yaushe cikin bani bani take shiyasa bai son al,amarinta. Sai dai abinda ya daure mashi kai shine kishiyoyin mahaifiyan shi da bai san may tare masu ba haka a rayuwa. A,sanin shi dai komai yana masu wanda ya dace in ma ba yanzun da yaga tsana tayi yawa a tsakanin su dashi ba yake nisanta kan shi da al,amarin su. Kiran wayan shi akayi bai tsaya duban ko waye mai kiran nashi ba ya daga wayan tare da karata a kunnen sa yace hello. Muryan Fatiman adamawa ce tace sweety na baka kirana sai dai ni na kiraka ko? Dan guntun murmushi ya sake iya bakin shi, yace Fatima ya akayi ne, ? Tace my life nayi missing dinka sosai, tunda ka tafi gida baka kirani ba banji daga gare ka,ba. May yasa kake min hakane, baka damu dani ba sai nice ke yawan nuna damuwata a kan ka, Yai yar guntun murmushi yace Fatima bakiyi min komai ba wallahi nima rashin ki yana damuna abubuwane sukai min yawa a nan gida shiya sa baki jini ba. Tace karike min kanka kada kaci amanata don min ni taka ce, ka sani. Yayi murmushi tare da,cewa ban maki alkawarin ni naki bane don haka ban dauka ba. Dariya tayi daga bangaren ta tace kanace ina wasa ne ko gaskiya nake fada maka. Yace ni ban yi alkawari ba don ki sani aure ma zanyi very soon don har an kammala komai ko. Cikin wata irin murya mai karfi tace what are you joking? Yace bana wanan da ke ai gaskiya na fada maki tun farko ina da mata a gida da zan aura. Kalaman Sadauki sin tayarwa Fatima adamawa da hankali don haka sun gama waya bayan ta kashe ta kasa zaune ta kasa tsaye shawara daya ta yanke wa ranta shi kuma zatayi. Washe gari haka na muka tashi ba dadi a gidan kowa zuciyar shi a cushe take mai. Daga cikin matan gidan su mama ba wace ta damu da damuwan mu sai sha,anin su sukeyi da raha da yaran su. Hjy kubura ce kawai ta shigo dakin namu zuwa rana don Saturday ne bata fita ko ina. Ta samu na hada wa mama abin kari ina duke ina zuba mata sugar tai sallama falon. Muka karba mata take cewa, daidai lokacin maji nace nabar mata sugar hakana. A,a hjy maijidda ke ma bakin son sugar ashe da yawa ni gashi na rasa yadda zanyi na daina shan wanan sugar don ba lafiya yake ba mutane a jiki ba yanzu. Murmushi Maji tayi mata tace ni sugar dama bai damay ni ba wanan yar tawa ce ma take yawan son samin sugar ko yaushe. Ta zauna saman kujera a kusa da maji nan muka shiga gaishe ta mummy ina kwana tace lafiya yau ana gida ba,a fita ba ne. Maji tace sun samu hutu ne shiyasa kika gan su a gida tace ayya har hutu yazo ashe? Nan ta juya gurin Maji tace ashe kuma haka Alhaji sani yai muna akan zancen yaran nan ? Maji tai dan murmushi tace kila shine yafi zama alheri a rayuwan su damu ma gaba daya. Amma gaskiya Alhaji sani bai kyauta ba yaci kafa bai yada ganye ba yadda Alhaji ya rike shi har yakai haka kuma yanzu kan yar matsalan rayuwa zai kawo wanan dalili haka. Ai yana da gaskiyan shi don ba mai son ya dauki dan shi ya bayar inda babu tarbiya. Haba sadauki ne baida tarbiya hjy maijidda sai dai ace kawai wanan lalurar dake kan shi. Kuma wanan aiba wai wani abin da za,a ki mutum bane kan shi shidai kawai yana da wata manufa ga hakan ne kawai ya sha zugi daga cikin gidan nan. Tau koma dai maye sai ya,rike dan shi shima Allah ya bashi wata wace tafita ba shi ke nan ba. Hjy kubura tai matukar mamaki a ranta yadda maji tai saurin basar da zancen a lokaci guda. Don ita a zaton ta abin zai jawo mata matukar tashin hankali amma sai gashi tashi daya sunga ta basar da zancen ita ma. Shiru sukayi a lokaci guda falon babu wanda,yai magana a cikin su sai hjy Kubura ta mike, tana cewa dama cewa nayi bari nazo na jajanta maki kan al,amarin. Maji tace nagode Allah ya saka da alheri, ai zaki kai ga sarakuwa ba da dadewa ba insha Allahu. Lokacin Bintu ta shigo dauke da ruwan da maganin maji a hannun ta . Sai ta ce yar gidan maijidda ni dai da ma da Bintu kika hadasu da zaifi don kin san halinta tasan nashi. Gaba daya muka kalli hjy kubura wace ni ban ma fahinci maganan ta ba,sai da naji mama tace ai da hakan zai faru sai nafi kowa farin ciki . Da sauri hjy kubura tace mai zai hana hjy maijidda abu tuwona maina. Fatima tana da mijin ta da zata aura ai bada dadewa ba ma zasu kawo kayan auren ta. Allah sarki ashe har wani ya riga mu niko tun jiya nake anyana hakan a raina, wallahi ni dai da haka zai yiyo da yafi komai sauki wallahi. Gaskiya ba zai yuyo ba a haka ma ya suka kare kullun yana samin yarinyar gaba da hattara sai na jajirce mashi akanta. Wanan ai ba matsala bace don bari zasuyi dasunyi aure amma wanan cin fuskan da Alhaji sani yaiwa mutane ban son a wuce lokacin auren nan Sadauki bai samu wata ya aura ba. Komai na Allah ne inji maji tace an auri mahaukaci ma balle dan shaye shaye, Hjy kubura tace ai shine lokaci ne dai bai yi ba amma sadauki yanzun ai abin so ne ga ko wace mace. Zasu dawo suna da sun sani ai a baya don sun wa yarsu ai ba wani sukaiwa ba amma may ye abin kushe ga sadauki inba wanan harkan ba. Tana fita dakin su maryam suka ce munafuncin banza kawai kamar da gaske. Maji ta katse su tace ko na munafuncine tayi min don shine dama zaman kishin. Tafi sauran dake ta nuna farin cikin su akan al,amarin amma ita dai ko tana da manufa ta dai nuna halarci ai. Sai maryam ta,kwashe da,dariya tace kaji mummy da,wani zance wai Yaya Sadauki ya auri Bintu. Kirmitsi ke nan inji Amirah, tace cikin kwashewa da,dariya, sai kuma tace wallahi fa da sun dace, don itace kawai ta karanci rayuwan shi. Nace don Allah Anty bari zancen nan kina son ya kashe ni ke nan mama tazo ta kwashi gawata. Maji tace da shima na kashe shi ranan yadda ya kashe min "ya. Aka kwashe da dariya a falon nan sukai ta hira suna dariya wanda hiran tasu nake jin yana kona min zuciya daurewa kawai nayi ina dariyan yake. Kada nai magana mama tace nima na kyamaci dan ta duk halarcin da zatai min amma saura kiris nace wa zai auri wanan kazami. Don ni yanzu balain haushin da takaicin shi nake ji don wallahi duk yafita raina kwata kwata. Sannu sannu aka fara rage zancen don sunga wa yanda su keyi a kan su basuma damu da zancen ba don ko a jikin su ma. Min fita zuwa kasuwa don sayo yan abubuwan da ake bukata a gurin mu na girkin mu ni da Anty Amirah muka fita,mun bar maryam tana girki a gida. Komai mun sayo harda ma abinda muka manta bamu saka a list ba duk mun sayo da sauran canjin hannun mu. A gajiye muka dawo gida da kayan mu niki niki, nan muka zube a falo bamu dade da zama ba sai ga yaya yashigo wanda shigowan shi gidan ke nan tun safe da ya fita. Tv yana kunne ya zauna suna kallo da maji suna gaisawa tambayan inda ya shiga take tunda safe haka. Ya dan yamutsa fuskan shi yace wallahi ina cikin gari ina dan zagawa ne kawai. Maganan da ake a tv shi ya daukewa kowa hankali a falon don photos wani yaro aka nuno bai wuce shekara sha, goma ba zuwa sha daya. Wai wani yai mashi fyde ana neman gudun mawan gurin mutane don a,tallafawa iyayyen shi ai mashi aiki. Salati falon ya dauka lokaci guda ga mahaifin yaron annuna yana kuka yana bayani acikin tv. Hankalin kowan mu ya tashi nan maji tace oh wanan duniyar ina zaki damu haka yanzu wani daukan alhakine wanan karamin yaro haka ace wai kato yai mashi aika aika haka ba dadin gani. Maji bari na,dawo abinda ya fadi ke nan ya,mike yabar falon da sauri. Ashe yana fita asibiti ya nufa gurin da aka sanar akai taimakon kan yaron nan sadauki ya ba da kudin aikin dubu dari biyu dana sayen magani amma yace kada a fadawa mutane shine. Amma duk da haka abin yanzu bai boyuwa don saboda al,amarin media da yai yawa. Da dare muna zaune falo sai hira ake yana tare da uwarshi suna maganan da ta shafe su amma mu hankali mu baya a kan su. Maganan da ake a TV ya mayar da hankalin kowan mu akan tv din labari ne akan yaron da aka nuna dazu da yamma. Nan suke sanarwa cewa an samu wani matashi mai kishin kasa da addinin shi yazo yabiya kudin aikin yaron tare da daukan nauyin duk wani magani da za aiwa yaron har yaji sauki. Wanan kuma ba kowa bane sai matashin dake tashe muke alfahari dashi acikin garin nan watau UF. Shahararen dan wasan kwallon nan dake bugawa kasa kwallo yanzu ayaune kuma muka samu labarin yatafi wasu unguwanni na,tallakawa inda yaiwa mata da yara marayu kyautan kudi da kayan abinci da sutura. Waya ya dauka ya kira wani nomba zai fara magana yaga wani irin kallo da uwarshi ke mashi na mamaki. Yace yanzu danace kada a nuna wanan abin sai da kuka nuna amma sai mai labaran ke fadin duk da yace mu boye shi kada mu fadi wanan alheri nashi ga al,umma. Munga ya dace ace mun fadawa duniya don matasa masu hannu da,shuni irin shi suyi kishi da halin shi suma. For god sake banji dadin wanan nuna program din nan ba da kasa ayi cikin fushi ya kashe wayan nashi. Sadauki muryan maji ce take cewa dashi wanan alheri keyi a gari haka bamu da labari. Dukar da kanshi yayi kasa yana cewa maji Annabin rahama yace idan zakai alheri ko hannun hagun ka kada ya sani, Amma kinga mutanen nan sai da suka baiyana ni a fili haka. A dakin Umma kuma tana ganin abinda ake fadi ana yabon sadauki tace cikin wani tsawa don Allah ku kashe min wanan shegen karyan haka kafin na,bata maku rai. Dole yaran suka kashe TV suka kunna kaset suna kallo ba don ran su yaso ba don sun fi son suga labarai akan dan uwan su saboda yanzu akan shi har wani jiji dakai suke a gari. Baba kuma yana zaune a falon shi yaga wanan labarin sai cewa yayi Allah nagode maka da wanan baiwa da kaimin ta tsatsona. Gidan hjy saude kuma tana kallo taja tsuki tana cewa aikin banza adai karata can, sai ga yarta tashigo dakin tana cewa yanzu ake min waya wai anga yaya sadauki yana raba alheri a tv. Ke rufe min baki ki rabani da zancen wanan mashayi mai kyau dan maciji. Nafada maki ki fita zancen wanan mara mutuncin, yaron da baida tarbiya ko kadan. Rahama tace mama amma ni gaskiya na fada maki na ina son shi ko a hakan. Bazaki so shi ba nace yaron da akace idan yasha har fitsari yake a wanda da amai kacakaca shine zaki wani ce nabarki ki aure shi bata karasa maganan taba Rahama tasa kai tabar dakin cikin turo baki gaba.

Readers Also Read