A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 57
A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 57: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 57. Muna gidan maman Bashar matar bata da matsala itama tana da yan…
3,122 words
Muna gidan maman Bashar matar bata da matsala itama tana da yan mata guda biyu sai wata yar karamar yarinya jikan ta. Bamu da matsalar komai a gidan don tana bamu kulawa yadda ya dace uwa tabawa diyan ta. Gasu da addini duk da sun girma basubar zuwa isalamiya ba daukan hadda da sauran litattafai. Zazzabi nayi na kwana biyu da wahalan da nasha Bashar da maman shi suka kaini asibiti sai da nasha allurai na mike. Hankalin mu a kwance muke komai a gidan babu tsangwama kuma su kadaine a gidan. Zamu zauna da uwar muyi hira da ita cikin sake jiki babu ruwan ta. Sadauki ko ya samu jikin Baba yai sauki sosai don har yafita yai dawafi duk da da sauran jikin shi. Sai dai yasan cewa Umma tana hake dashi don irin yadda take mashi tunda ya iso kasan. Bai kula taba don maji taja shi a gefe tunnisowar shi take tambayan shi abinda ya faru. Hakalin ta ya kara tashi sai dai da taji cewa ai yaranta yanzu suna can uguwar arkilla gurin mahaifiyar Bashar hankalin ta ya kwanta. Kwana shi uku tare dasu ya tafi garin Riyahd ya barsu gurin wasu yan team din kwallo. Nan ma ya,bugawa wasa inda ya samo riyar masu yawan gaske don yan kan har taya shi sukayi akan yadawo kasan su da wasa amma yace masu kasan shi ma suna bukatan shi. Ya dawo suna shirin tafiya ya ba su kudi kowa tayi tsaraba wa yan uwa da yaran ta. Umma tai matukar rudewa da irin kudin daya basu a can hankalinta ya tashi tasan in bata zake damtse ba sai wanan yaron ya zarce tunanen ta. Maji ta samu kudi ta sayo muna kaya masu kyau da,tsada zannuwan gado masu kyau da sauran tarkacen daya dace a sayo. Sai kuma Umna abin ya tsone masu ido wai yabawa uwar shi kudi yafi nasu ya nuna masu banbancin cewa ita ce ta haife shi ke nan. Maji dai tana gyaran kayan ta sai murmushi tayi kawai batacewa mama Asiya uwa ka iya komai ba. Don umma ta zugata itace ta fito fili tana maganan cikin hasala da bacin rai. Sai dai duk iya shegen su basu yarda suyi a gaban Alhaji don yanzu zaici masu mutunci ne. Satin su biyu da kwana hudu suka iso sokoto zakace ba jinya sukatafi ba da bauta don duk suyi kyau abinsu. Ga zancen tafiyan su ya bi yan uwa da abokan arziki kowa ya san da cewa dan kishiyan su ne da suke kira mashayin gidan su yakai su saudiya umar da jiyan mijin su. Saidai kan kowa na ciki na ciki jira ake a dawo gida a zazzage balain da aka kullo. Kafin su dawo mun shigo mun gyara ko ina na part din mu muka koma gidan su Bashar muna jira su dawo gobe. Mahaifiyar su bashar tasa ai muna gyara jiki kitso har kumshi saida ta sa akai muna, siffa mai kyau mun koma kamar wasu amare da mu. Sai bayan sun dawo har sun huta yaya sadauki yaje ya,kwaso mu har mahaifiyan Bashar din ta rakomu gida. Mun samu gida ya rude da murnan dawowan iyayyen su ko wani daki sai hayaniya akeyi. Gaba dayan mu muka fada jikin mama cikin murna da farin cikin ganin ta a lokacin. Maman su Bashar sai kallon mutake cikin sha,awa nan mana ta fara mata godiya, kan karamcin da tayi mata na rike mu a gidan ta. Tace haba ai ba komai yaro ai duk na kowane dama absan haka tun farko da can suka zauna harku dawo. Yaya sadauki da Bashar na zaune sai kallon mu sukeyi duk nabi na takura da zaman su a gurin. Na mike tare da fara daukan jakkunan kayan mu da muja dawo dasu yanzu zuwa cikin daki. Maji tace Fatima bazaki bari har ki huta ba nai dan murmushi nace mama bari na shiga dasu kawai. Ina shiga maman Bashae tace ai Fatiman nan taki akwai kokari wallahi ko can haka nake fama da ita gurin aiki. Mama tace ta riga ta saba bata son zama da kazanta ko kadan . Ashe aure zatayi bada dadewa ba jiya nake jin suna mata sheri wai angon ta yazo yaga wanan kwalliyan nta sai nake tambya suke fada min an kusa bukin ta har an kawo kayan lefen ta. Hakane hjy nice ban aika maki ba. To Allah ya sanya alheri ai mijinta yai sa,a ya samu yatinyar kirki ta san ya kamata sosai. Kai wanan yarinyar dai shu,umace kowa sai kaji yana yabonta ko akan may oho. Bai zaci maganan zucin shi yafito fili ba sai jiyayi Bashar na fadin kaine kake ganin ta shu,uma amma ai Fatima mutunce wallahi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,
IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA, BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAN MUNA,,,,,
Bayan dawowan su maji daga saudiya da yan kwanaki jin ba wanda ya tayar da zancen abinda akai min agidan, Maji ta kawar da kaiwaici a idon ta inda ta samu Imirah ya dawo daga kasuwa ke nan zai shigo gida take ce mai, Imirana ji mana sai ya dan waigo yai tsaye kerere yana kallon ta cikin rashin mutunci. Yace ina jin ki, Ganin babu mutunci yanzu a tare dashi yasa maji cewa ,yanzu Imirah baka ji kunyan abinda kayiwa yarinyar nan ba da bamu nan? Amatsayinka na babba a gida anbar maka amanan yaran nan shi ne kuma kaida kanka kai kokarin keta mata haddinta? Fuska a daure yace dama don wanan maganan kika tsayar dani ? Saurayi nake ita kuma nudurwace zan iya shigar da kai na akanta ko hakan kuma illa ne. Murmushin takaici maji tayi tace amma tir da halinka na dan akuya, halin maha,inta. Idan zina abin yine jeka ka nemi yar uwar yin zinanka can kuyi tayi amma ba yar mutane da aka bani amana ba. Murmushi yayi yace Maji kada kiga laifina yar taki ce da shegen kyau wanan aiba komai bane, Allah ya shirye ka,Allah kuma ya tsare amma ni dai Hauwa,u ina maka kashedi akan diyan mutane a gidan na wallahi muddin ka kara yi mata wani abin tashin hankali again zan ba mutun mamaki don shiru ,shiru ba tsoro bane kuma in mutum bai jiba ya gwada ya gani. Sai muryan Umma daga bayan su akaji tace tau isassarsa masu gida wallahi duk sherin ki baki na kakan ki ba. A hir din ki akan diyana ina fada maki Hauwa,u ki sakan min maran diya don bani nasa danki yayi tambada ba abaya. Haka,kawai don yar kauyen diyarki zaku saka min yaro gaba dasheri don kawai a bata mai suna. To wallahi ta Allah ba taku ba kuma karya kukeyi nagaba yayi gaba nabaya sai labari. Kuma kijawa karuwan diyar ki kunne da take kokarin cusa kanta gare shi tayi kwantai a kauye ankawo ta gari ana neman mashinshini a cafke. Murmushin takaici maji tayi tace kaice yaya a matsayin ki na uwa kuma diya mace kin san zafi da munin irin abinda Imirana ya tashi aikatawa yarinyar nan amma idon ya rufe da kin gaskiya. Babu komai ai Allah ba azzalumin kowa bane yana sama yana gani duk bayin shi. Ta juya inda Imiran ya fara tafiya tace wallahi kaji na fada maka duk ka sake kokarin ketawa yarinyar na hadin ta sai kayi mamakina a gidan nan. Tashige cikin part din mu duk muna jin yadda suka kwashe da Umma da dan ta maji tace kai Allah dai yasa kin kusa aure ma kowa ya huta, ki bar wanan gidan namu mai tarin fitina cikin shi. Muryan Baba ne daga waje yake fada kamar haka amma dai ke kan anyi uwar banza wallahi. Yanzu ashe abinda yaron nan yaiwa yarinyar nan ke nan bansani ba shine har kike fada don kunya bai ishi idon ki ba ke, Ida da yarkice wani katon gardi haka yai niyar illantawa haka zaki fadi an mashi kazafi ne ba gaskiya bane hakan Dama ai nasan hakace zai kasance muddin kaji ba ka tsaya kai bincike irin yadda ya dace, Tunda da matar so dinka ake fitina to ku sani ni diyana basu da gadon iskanci masuyi dai kowa yasan su don haka sherin mutum yabishi can cikin kayan shi . Haka Umma ta tare ta hana Alhaji ya,tsaya yai fada akan wanan zancen don idan ya matsa zagine da tonon asiri zai dawo akan sadauki da,uwar shi . Wanda yanzu daga uwar har dan tausayi sukw bashi sosai don duk abinda zasu gujewa gudun magana agidan suna kokarin yin shi don kimar su ta riga ta zube , Su Umma da mama an samu gurin zagi da gori da habaici koda akan da tsinke ne. Shiyasa yakan kawo ido yasa,wa Umma inda ita ko tana ganin kamar tafi karfin kowane a gida sai yadda tayi da kowa agidan baki daya. Hjy kubura ce kawai bata samu ta mallake yadda ranta ke so ba amma ko ita din ba laifi don bata iya kifar mata da,gwaunati a gurin mijin su ba. Amma wanan munafukan Hauwa,u zamani amarcin ta Alkah daine yanufi takai wanan lokacin a gidan Alhaji don gaba daya hankalin shi ya koma ga majine kamar ita kadaice mace. A ganin su Umma ke nan a lokaci amma kuma a gurin Alhaji tausayin Maji yake jin don ya dakatar da ita ga karautun ta yadauko ta ya hada cikin matan da ke aikin gwaunati suna da abin kansu.
****** ********* ****** Yanzu abinda ya,rage bukina baifi wata bakwai ba don an dagar da zancen bukin da babana yai ciwo ne shi ya roka abari har guri ya sha iska sai ayi. Haka kawai kwatsan ranan muna zaune sai ga sadauki ya shigo ya fito daga cikkin garine fun safe safe ya fita sai da yamman nan ya shigo gida. Suna hira ne da maji yayin da mu muke harkan gaban mu can ya sa murya ya kira sunan Amirah ta amsa da sauri tana fadin na,am yayana. Yace zaku iya yin aiki hajji bana kuwa don tare nike son in tafi daga club din mu na samu kyautan kujera har har biyar. Kinga dani dake da maryan nake son mu tafi sai tsagal Maryan tace da Bintu ko? Tsit falon yayi don sun san maryam tayi tsaga da fadi gaskiya. Yace wanan bakauyan taje mijin ta ya kaita mana nidai ni dake da Amirah nace kina min gayyan wasu takarce can daban. Kai ban son rashin kunya Fatima ce takarce kuma yace ba tana da miji ba taje ya kaita. Ai dai kasan zai iya kaita tunda yana da halin shi shima maji ta fada mai hakana. Don Allah dai yaya ka hada,harda Bintu mu tafi ita ma ta sauke don Allah tana fadin cikin dan marairaicewa kamar karamar yarinya. Yace maryam ashe ke karamar yarinyar ce yaya zai kai ta saudiya bayan tana da miji idan yai karana fa na kai mai mata saudiya bada sanin shi ba. Don haka ki bar wanan zance don Allah nikan da naji ta matsa zance ina duke kaina akan littafi. Nace Anty maryam bar zancen nan nima ban faye saka kaina inda Allah baikaini ba. Nafi kowa murna yau dajin yan uwana zasu gabas su sauke farali at early age din su. Muryan maji ne tace ai yadda Allah ya bashi ikon , biya wa yan uwanki ko ke haka zai bashi ikon ya biya maki atafi dakw kafin kiyi aure. Maji na fada maki wanan kujeran kayautan su na,samu nima daga wa ni kungiyan mu dake can kasan Dubai. Jin nan babana ban son tsaya wani kace nace kawai ka bari yaran nan su tafi da yar uwar su . Kai kanka kasan da cewa, bamu taba tsan manin irin haka ba a rayuwan mu. Shiru yayi har maji ta gama fadan ta baice uffan ba nidai takaicin irin wanan halin da yakw min sun kai min ko ina amma indai har nai aure na bar gidan su na huta da komai ma. Can ya dan furzo iska yace yauwa Maji na dade ina son in tambaye ki naji sai abubuwa sukai min yawa ban samu lokacin tsayawa tambaya ba. Fadi ina jikin muma dai shiru mukayi muna saurarwn shi sai da dan garani ina kokarin yin abindake a gabana ne alokacin. Yace Maji wai akwai wa ni tsoho da naje gurin shi kwanaki bashar ne yakaini gurin mutumin To da zan dawo sai yake cewa idan nazo gida na fadawa mahaifiya na kada ta manta da alkawarin da tayi na cewa zata kaini da kanta gurin da aka bukaci ta kaini. Ni din nan inji maji ta fadi cikin dan murmushi da mamaki a fuskan ta a lokaci guda. Tace kai mutane akwai yaudara wallahi ko sai mutum yai karya ne zai samu abu daga gurin mutane ? Shiru nayi idona akan littafi amma kuma zuciya ta tana nazarin wani zance can a baya tun farko. Amma maji wanan mutumin wallahi tsoho ne sosai kuma ban tsan mani yaudara bane yadda yai min maganan Don zanfita cikin murmushi yace nacewa mahaifiya na tayi niya ta tafi inda tai alkawarin zata kaini da kanta in ba haka ba gaskiya akwai matsala,babba nan gaba. Don tana tunka ana walwale mata ne za,a mayar da hannun agogo baya sosai . Mai makon naji maji ta tuna alkawarin da tayi a baya sai naji sun buge da zagen tsohon mutane kawai. Suna kiran macuci ne ma yaudari don taci kudinw yake fadin haka Allah yasa dai ni ba mai zuwa gurin malamai bane da yan tsubbu neman taimakon su na dogara ga Allah. Amirah tace ba dai maman ba kan yaje can ya yaudari wasu gaba amma ba nan ba kan. Batare da na kalle su ba don shima mai maganan kanshi na duke ne kawai alaman surutun su yai mashi yawa. Sai muryana kowa yaji a falon ban juyo ba ban dago kai ba nace mama kece ba karya mutumini keyi ba. Da sauri sadauki ya dago kai yana kallona itama uwar hakane ixo ta tsura min don ban taba mata haka,ba duk zamana da ita. Tace Fatima kikace nine nace zan kai sadauki wani guri ban kai shi ba nace eh mama , Kai Bintu yau kuma maji zaki kullawa sheri haka maryam ke nan ke fadin haka cikin dariya. Na girgiza kai na nace bazan taba yiwa mama sheri ko wani nataba har abada. Dan tabe baki yayi daga inda yake zaune yana wani game da,wayan shi na,wasan driving. Don yakan dan taba wasan mota a America tare da,samari yan uwan shi don nishadi kawai haka har kudi suke sakawa ko kyautan wani abu ga wanda yaci. Mama tace dada,Fatima kikace nine nai alkawari na kara cewa eh mama sai dai bazan tuna maki ba sai wani lokaci in kuma kin tuna shike nan. Amira tace a to dama dai ba,a shiga tsakanin Bintu da maji don sun fi kusa, kila tare da ita akai zancen. Nace ai harda ke anty don gaba dayan mu musan da zancen sai dai mantuwa kawai . Dan dariya yayi yace wanna yarinyar Allah munafukace Maji baki dai son ana fadi ne kawai amma ji daurewa wai kowan ku yana gurin. Dakata Babana tunda Fatima ta kuke da haka akwai magana ke nan ya mike tsaye yana fadin ni kan na fita don bsn iya sauraren shirmayn yarinyar nan gaskiya. Yana ba da baya na,shake murya nace mama kin manta maigani yace kikai mashi sadauki inda gwago mai masa ta tafi. A,a,a anyi haka Fatima shiku jin ina kus,kus da maji yasa shi juyowa ta ce tabbas anyi haka Amirama,tace wallahi na manta muna zaune kuwa aikai maganan. Cikin wani fargaba Maji tace babana dawo ka,zauna don Allah da mamaki yake kallon mahaifiyar nashi don bai san may shu,umar yarinyar na tafada mata ba a lokaci guda yaga ta birkice. Tace don girman Allah ka fada min yadda aka fada maka ka fada min a take ya kara nanata mata, sakon da tsohon ya fada mai. Tace inko ba wani ikon Allah ba yaya akayi wani yasan wanan zancen don dai ba,a nan akayi shi ba. Mamakin yadda maji ta rude a lokaci guda haka ya bashi mamaki matuka yace Maji injin dai lafiya ko yace cikin kallon fuskan ta ido cikin ido. Take ya fahinci da akwai matsala ke nan yace please Maji may ke faruwa ne wai? Ko zancen mutumin gaskiyane dai yake fada don ni ban dauki zancen da wani muhinmanci ba kada haka ya tayar maki da hankali. Maji a sanyaye ta,ke ce mai gaskiya Babana akwai matsala saboda akwai wani mutum da haduwa kawai nayi dashi ranan ina asibiti ya shigo gaida mu yake cewa kana da matsala don Allah nayi kokari nazo dakai gurinshi ya ganka. Nai alkawarin zan kaika amma kuma kaga na manta shaf wallahi inba yanzu da Fatima ta tuna min ba. Ban san lokacin da na sauke ajiyan zuciya ba jin yadda Maji ta canza maganan a lokaci guda. Don dama ina gudun ace daga gwagona zancen yafito yace zata koya wa uwarsu bin bokaye nima yana iya sakani gaba da zagi don nasan halin shi. Yace amma Maji kin dauki zancen serious ke nan ko?. Tace idan ba serious matter bane yaya za,ayi zancen ya fito daga gurin wanan tsohon. Kaga ke nan maganan mutumin gaskiyane tunda ga zancen yafito a gurin ka. Jikin maji yai sanyi sosai a lokacin don sai ta shiga tunane watau ke nan masu sherin basu daina ba ake nufi ke nan. Tai mamaki da taji yace yanzun za,a tafi gurin mutumin ke nan tace ya kamata gaskiya . Zan samu lokaci sai mu tafi kafin na koma ke nan don na kusa tafiya ba kuma zan dawo ba sai nazo daukan yaran nan mutafi don ta inter national zamuyi tafiyan. Maji tace amma na fada maka da diyata za,a atafi baice komai ba har ya mike zuwa kofa sai lokacin ya ke cewa Maji sai ki shirya mu tafi dake kenan don bazan kwashi wa yan nan ba duka su zama min wahala a can. Don nima ina son nayi inganttacen ibada banda lokacin taulali dasu gaskiya don kin san yar ki bakauya ce matar bakauye kuma. Yana fadin haka Fita yayi daga dakin nima sai yau banji haushin shi ba don ya gama min komai a duniya. Mutumin da adalilin shi zai shiga kasa mai tsarki ai yagama min komai wallahi ko a duniya dole nayi hakkuri dashi don iyanzu na fahinci halin shine haka gwatsale mutum a take don bai son raini. Nikuma yar kauye ce baruwan mu da banbants babba da karami gurin fadin magana.