Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 58

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 58

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 58: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 58. ****** ********* ****** Maji ta tsara Baba hat ya yarda cewa…

3,315 words

****** ********* ****** Maji ta tsara Baba hat ya yarda cewa zadu duba jikin Baba na ne akauye don haka muka fara shirin zuwa gurin da akai magana. Don ta kira gwago ga waya sunyi magana akan tafiyan mu kuma gwago taiwa dan uwan nata magana yasan da zuwan mu gurin shi. Sadauki ne dai bai san cewa da mu za ai tafiyan ba sai lokacin da za,a tafi yaga duk mun shirya tafiya yake cewa Wa yan nan fa kuma Maji ? Tace dasu zamu tafi don suma ina son na kaisu gurin mutumin ya gan su. Kaman zai yi magana sai kuma yai shiru yana tsaye tsakar falon ya harde hannayen shi guri guda. Can yace sai dai da Bashar zamu tafi ban tsan mani motar zata dauke mu ba fa. Tace ai zamu iya matsawa mu hudu a bayan dukkan yace da yake ita wanan yar fillon ba jiki gareta ba ko? Yadda maji tace hakane mu hudu muka matse a bayan motan muka kama hanys sai garin. Tun shigan mu mota banyi magana ba don idan na shiga mota amai nakeyi ko yanzu shi ke damuna. A hankali na bude ledan da na riko na shige cikin hijjab dina naita kwarara amai tun ina yi a boye har Maji ta gane da sauri tace subbahanallahi. Fatima amai kikeyine ? Da sauri ya juyo yana fafin oh shit, Don Allah Bashar parke motan da sauri kada ta damay mu da wari a mota. Fada yake yana fadin kin san baki da lafiya don gulma shine sai kin biyo mutane kuma? Yaja tsaki aka fito da sauri na samu guri nai ta shara amai mama tana a kaina sai sannu take min. Da ya tsaya min muka shiga mukaci gaba da tafiya, an fara tafiya cikin jan tsuki yace i hate naga ana amai wallahi. Bashar tace kasan wasu mutane idan sun shiga mota sai su dinga amai don warin petror. Da kyat naga,mun kawo garin kaina yana,duke sai ciwon kai dake damuna a lokacin sosai. Gida ne irin ginan kauye na haki da itattuwan dake basu innuwa manya manya a kofan gidan. Suka tambaya kamar yadda aka fada masu wani yaro ya shiga yai masu iso akace a shigo daga zauren. Maji ce tafara shiga taiwa mutumin bayanin komai yace to a shigo babu komai dama irin matsalan nan sai anyi wa mashi dabara. Dattijone fari dogo dashi baida jiki sosai sai dai yana da fatin gemu mu bamu shiga ba muna zaune a bayan mota. Sai Bashar dake tagaba sosai bai shiga ba har sun shiga sadauki ya fito yai mashi hannu daya biyo su mana. Sun zauna aka gaisa yake tambayan shi yaya jama,a ya aiki ya amsa tare da bin zauren da kallon irin littafan dake tare a cikin zauren da ido. Malam ga yaron kamar yadda kai umurnin nakawo maka shi yace nagan shi hjy. Hannu ya mikawa sadauki inda shima ya mika mai azaton shi gaisawa zasuyi sai yaji ya rike hannun nashi idanuwan shi ya lunshe yana fadin ikon Allah. Can yace umm,umm Allah mai iko, aida sun barka da sun sha alheri fiye da tsanmanin su. Sai ya sake hannun sadaukin yana girgiza kai yace mutane basu da imani yanzu duniya tai nisa wallahi. Agida akwai matsala sosai hjy hakama a,waje akwaishi. Sai dai ita matsalar ta waje ba wani matsala bane akan harkan samun shi ne. Nan ya dago kai yacewa sadauki ka na iya gane wani bakin mutum daga cikin ku mai dan saje a fuska sai dai ma naga kaman ba musulmi bane. Yace akwai ranan da yaba wani abu a cikin leda fari kai kadai baiba kowa ba. Sai dai anyi sa,a kana zuwa gida ka manta bakaci ba sai bayan kwana biyu kaga ledan ka bude amma sai kaga abin ya zama baki. Shiru yayi yana son ya tuno wanan ranan sai zuwa can yanisa yace anyi haka malam, Amma Daniel ne abokin wasa na ne saida iyamurine shi ba musulmi bane. Yace nagani ai . Yace Allah ya kareka da kaci yadda wanan anin ya koma baki da haka jikin ka zai koma ayi maganin duniyan nan sai dai Allah gaskiya. Yace amma idan baka yarda ba abinda zan baka yanzu idan ka gwada zakaga insha Allahu ba yin mu ba da yardan ubangiji bazai yarda ko hannu ya kara hadawa dakai ba. Burin shi shine saboda kaine bai daga ba kakai mashi ko ina don yana ganin kaine ka,tare mashi wuri. Ikon Allah inji maji tace ko ina da matsalan dai, malam yace yanzu muna A LOKACIN NE, Ai yanzu duniya ba,ai mata hawan kawara sai dashiri ake shigan ta don mutum yana barci ana mashi nasari ne. Bashar yace kaji abinda nake fada maka kullun amma kai baka ganewa ne shiyasa. Shi dai nisawa kawai yayi. Hankalin shi na gurin tunanen Daneal kawai yasan bai kaunan shi tun farkon haduwan su suka fara samun matsala amma daga baya sai ya daina tsanar shi. Yace hjy sai zancen gidan ku gaskiya bazan boye maki ba akwai matsala sosai a gidan. Nan ya fara basu bayani tiryan tiryan amma bai fada masu sunayen masu wanan aikin ba kamar yadda yaiwa gwago bayani a baya dama kuma,shirin da suke a yanzu. Har kan yaranta mata da aka,asirce mata su akan suyi ta zama ko kare bai kaunan su balle mutum. Nan kan ran sadauki yai matukar baci cikin bacin rai yake fafin wai Maji may mukaiwa wa yan nan mutane ne haka a duniya. Kagin tai magana malamin yace hassadane kawai don sun san kokai waye shiya kawo haka kawai.. Maji tace yaran suna nan nazo dasu ai yace na sani don nagan su su uku ko? Sai dai dayar bataki bace Allah daine yakawo maki ita cikin hikima irin na ubangi wanda duk abinda kaga ya tsara ba,a banza yake tsara shi ba. Zaman ta gareki alheri ne sosai koda yake bama sai na fada maki ba ai kema kin sani. Sai dai zatai aure amma dai auren yanzu gaskiya sai Allah don banga yuyuwan shi a halin yanzu. Malam daga gurin mijin ne ko kuwa yace Allahu,a,a lamu sai gaibu sai lillahi gaskiya. Cikin ran sadauki yace aidama nasan wanan mutumin yaudaran tane zaiyi sai yaji malamin na fadin amma akwai abinda zanba kowan su insha Allahu komai zai walwale da yardan Allah. Sauran ma insha Allahu mazajen su zasu fito bada dadewa ba ai. Nan dai yaba yaya sadauki abubuwan da,suka dace tare da kara jaddada mai yadda zaiyi amfani dasu. Sai yace ace mu shigo idan mun fito sadauki ya shigo shi kadai sai uwarshi akwai maganan da zai yi dasu wanda siri ne. Nan dai yai muna duk abindaya dace da kowan mu muka fito da yan ledojin kulin maganin daya bamu daga zauren. Ni a lokaci duk a galabace ma nake don ni ban san wai ina da matsala ba,su dai ne na dauka masu matsala kawai. Muna fita sukai magana ta siri sosai da mana ta fada mashi damuwan ta yai kuma alkawarin taimaka mata. Sadauki ya shigo ya zauna mutumin ya kalle shi yace kai babban mutum ne watarana zaka tuna da magana na matsalan ka dayane shine wanan shaye shayen da kakeyi. Duk da naga abinda sauki yanzu sosai akan ka don abin yarage maka fiye da baya can. Yace sai kuma ka kara da hakkuri don ko yaushe biyayya na iyayye yana kai mutum ga alheri. Yai mashi nasiha sosai akan duniya tare da kara mai wasu yan abubuwa irin nasu. Inda yace ya tabbatar kagin ya tafi gurin neman shi yayi abinda ya bashi din. Kudi masu yawa ya ba mutumin sai yai dariya yace ba haka nake ba ni dari biyar kawai zaku bani ko shi kada kuce naki karba ne da ban karba ba wallahi. Sunyi mamaki sosai muka kama hanya sai sokoto koda zamu dawo naita kakarin amai saidai da yake cikina ba komai sai kumfa kawai nake zubowa. Bashar dasu mama suna ta faman yi min sannu amma,shi ko kallo ban ishe shi ba. Da la,asar muka iso gida tun lokacin kowa ya fara abinda aka bashi yayi daga gurin bawan Allah. Don har bashar saida ya anso nashi shima don mutimin shi da kan shi ya bashi taimakon. Tun dawiwan mu nikan ina dunkule saman dogon kujera harda barcin wahala saida nayi. Anty maryam ce ta dafo min liptop da lemun tsami na dan sha shine na dan ji dama sosai. Ya shigo falon yayi wanka ya,sauya kayan jikin shi a lokacin yasa wando da rigan na maza mai dogon hannu. Gani a kwance na dunkule yasa ya dan tsura min ido sai yaji na bashi tausayi sosai. Yace ke may ke damun kine yanzu kuma? A sanyaye nace cikin bata fuska kaina ke min ciwo. Bari in nafita sai a sayo maki magani kisha. Nace nagode. Wanan gidiyan da nakan yi mai idan yai min alheri yakan ji matukar dadi a,ran shi don shi mutum ne mai son yaji ana godiya gare shi. Sosai ya mayar da hankali shi ga maganin shi da mutumin ya bashi don yai matukar yarda da zancen mutumin ba din komai ba,rashin amsan kudin su da mutumin baiyi ba. Ya dawo ya,sayo min magani harda na amai da kuma drinks mai sanyi na kwali. Ina kwance na na dunkule a saman kujera su na kallo ni kuma gani kwance a dunkule sai dai ba barci nakeyi ba idona biyu. Muryan shi naji yana tambayan su ita wanan barcin takeyi har yanzun ne ko jikin ne ke damun ta? Maryam tace tace kanta kawai ke ciwo yanzu yace ke tashi ga magani ki sha ko zai lafa maki. A hankali na mike zaune daga kwancen da nake sai dai still ina dunkule ga hijjab ga kuna blanket dana yafa ajikina. Na karba tare da bare maganin na kai abakina saida na dago kai naga ya tsura min ido ashe ni yake kallo daga inda yake zaune. Da sauri na dukar da kaina kasa bban tsaya shan drinks din ba yake cewa bazaki sha juice din ba ne? Nace a,a ban iya sha yanzu sai nakai kwance daga inda na tashi yamike zai bar falon yana cewa idan bai bari ba sai akaiki asibiti ke nan. Ya fice daga dakin na lumshe idanuwana tare da komawa barci a lokaci guda.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,

IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA BAMU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAR MU NA AKAN KI,,,,

Tun kawo laife na yaya sadauki ya kara tsananta min a gidan su, dan abu kadan zanyi ya dinga min fada cikin hasala da bacin rai. Wanda shi kanshi bai san dalili yi min haka ba haka,kawai yake jin haushin yarinyar a ranshi. Duk da maji tana mashi fadan haka amma ya kasa rangwanta kiyayyan da yake ji nawa a ranshi. Idan yana gida ban fitowa falo sai naji ya fita daga gidan zan fito falo don nima haushin shi nake ji yanzu don a matsayin mugu macuci nake ganin shi. Nasan kuma don saka mai idon da nakeyi ne abaya shine yasa yake jin takaicina haka. Maji sai shirin bukina dake kara matsowa takeyi a hankali, irin su kayan kitchen da wasu uan abubuwa su take sai min. Kabir yace idan anyi aure a sokoto zan zauna a gidan shi na garin sai idan anyi hutu zan diga zuwa gurin su Abuja. Maji yakira ya fada mata tsarin da yayi akaina da ta tambaye shi kan al,amarin karatuna da nakeyi. Sadauki ya shigo ya samu mama tana wayan da Kabir yana jin duk abinda suke fadi a karshe Kabir din ke cewa mama ko tsarin bai maki ba haka? Maji tace gaskiya naji dadin hakan Allah ya albarkaci rayuwan auren ku, ya amsa cikin jin dadi da Amin mama. Mama tace Kabir don Allah ka rike min Fatima amana don Fatima yarinyace dake bukatan kulawa yace insha Allahu mama kada kiji komai nima nasan da hakan. Yana zaune ya fahinci da wa mama take waya ya lumshe idanuwan shi jin hiran nasu yake kamar a fili Kabir yake ya shake shi. Sai tsuki yayi lokacin suna sallama zata kashe wayan yace tsohon banza kawai. Kaidawa kuma kake tsuki anyi wani abin ne ko may? Yace cikin daure fuska kawai dai nayi ne don wanan shirmay danaji anayi. Shi waye da zai dinga yiwa mutane barazana kamar wani attajiri can. A,a ikon Allah waikai sadauki ina ruwanka da zancen nan ne? Ina da ka mayar da kanka abin kwarai agurin kane za,a zo neman auren yaran nan. Yace wani maji da ban bashi ba kawai mutum ya tsufa amma yana halin yara . Idan aure yake so bai zuwa ya samu bazawara su shirya sai yafake zai bata yar mutane. Ya juya inda nake zaune raina yabaci don abinda yake min yafara isata, yace jita don Allah daga kawai ance mutumi a abuja yake duk kin wani rude a kan shi don kawai kije abuja. Baki tsaya kin tsarawa rayuwan ki abinda zai fishekiba mutum da iyali haka ke karama dake may zaki gane a gurin shi inba wahala ba. Kai dakata ya isa haka na,rasa gane dalilin dayasa kake wanan abin haka Yadago ya kalli uwar yace may nakeyi maji iyaka dai ina fadin gaskiyane ni kawai. Duk abinda na hango mata kun kasa hangen shi sai faman rawan kai takeyi ita zatayi aure wawiya kawai doluwa. A,a wai sadauki kana da hankali kuwa da may wanan abin yai kama hakane wai? Mikewa nayi fuuu, nabar falon cikin fushi na shige ciki abina don ban iya tsayawa sauraren wanan shirmay na shi. Tun ranan idan yaya sadauki ya shigo falon duk hiran da ake haka zan mike tsam na shige daki abina. Ranan muna tahiran mu cikin dariya har maman tamu tana saka muna baki a hiran mu don hiran wasu samari da suka zo wai suna son maryam muke yi muna dariya. Ya shigowa suna mashi ina wuni da jan shi da hira yana batun zama namikw tsaye tsam daga inda nake zaune, ina cewa. Zan shiga na kwanta maryam tace wazai kwanta yanzu ke da baki barci koda rana shine yanzu da yamman nan zakice wai zaki kwanta. Ya dago lumsarsun idanuwan shi masu nuna a gajiye yake a lokacin don tun safe yafita daga gida . Ya dora su a kaina gaba daya yaga na canza mashi na koma wata fresh sosai dani don nima ban san may mama take yawan bamu ba muna ci muna,sha na gyara jiki kawai . Ko kiftawa bayayi don mamakin sauyawa na a lokaci guda da yaga nayi mashi a lokaci guda. Mama taga yadda yake kallona sai abin ya bata mamaki kwarai da gaske amma sai ta dauka wani sherin yake son fadi akaina kuma. Don haka tai shiru tana sauraren taji abinda zai fadi a lokacin tai mashi tsiya. Maryam dai tasan yar tsama muke duk kwanakin nan ta dai dubeni saboda ta san ba,kwanciyan zanyi ba ganin yaya ne kawai yasani barin falon nashige tana ce min atashi lafiya ko? Nashige batare da na,kara,waiga inda yake ba ballw yace ga abinda nai mashi kuma. A bangaren sadauki kuwa, fuska ya kara,daurewa batare da ya kara bi ta kaina ba don yasan mama tana jiran shi ne. Maryam daga inda take tai mashi kuri da ido tana dariya cikin kyata tace ban san wanan fadan na yaya da Bintu ba wallahi. Bai tanka mata ba sai tsukin da yaja ya dan dafe kan shi yana fadin rabu da,wawiyan banza kawai gaskiya ne bata so a fada mata. Daga gurin da maji take cikin takaici tace gaskiyan may kada tai auren ko may ? Yace ni fadan gaskiya nake mata saurin may take da,bazata iya tsayawa ta karasa makatantar taba ne wai, duk tsoho ya, hure mata kunne bata jin kiran yanzu sai When it's too late to her zata gane kuren ta ai. Allah dai ya tabbatar muna da abinda yafi zama alheri a gare ta. Ina shiga daki kamar jira kabir yakw na shiga dakin sai ga kiran wayan shi ya shigo min. Mama ta kwalla min kira wai nazo za ai program din da nake so wasan kwaikwayo a NTA sokoto wanda nake so ina kallo ina dariya don shirin irin namu ne na mutanen kauye. Hakan bai hanani yin wayana ba don can na manne gefe guda yadda,ba mai jin abida nake fadi. Kallo daya zakai min ka fahinci cewa ina cikin nishadi da wayan da nakeyi ga kuma kallon film din da nakeyi a tv duk a lokaci daya. Muryan kabir ce ta ratso dodon kunne na yana cewa Fatima nayi rashin ki kwana biyu aiki ya hana nazo na gane ki. Nayi murmushi tare da lunshe idanuwa na na gyara zama da kyau. Ban bashi amsa ba sai yar murmushin da nayi har yana jiyo ni a,wayan a lokacin . Ya naji kina murmushi ko baki yarda na damu da nazo na ganki bane wai? Na koma yin murmushi mai hade da sautin dariya wanda ya jawo hankalin kowa a kaina a lokacin. Nace may zai hana na yarda duk da dai nasan akwai wasu a,tare da kai ba,wai wani damuwa zakayi sosai hakana ba ai. Yace kowa daga cikin ku ina bashi hakkin shi ai nace ai nasan da hakan, yace da kyau da kika fahince ni. Yace wai kin san wani abu kuwa nace a,a cikin dan girgiza kaina kamar yana gani na a fili. Nace sai ka fada dai, Yace wai ko Fatima kin san yadda nake jinki a cikin raina kuwa, ? Wallahi da ina da iko ko kuda bazan yarda ya sauka a kanki ba. Don ina ji a jikina ke wani abune da,Allah ya jefo min a cikin rayuwana mai muhinmanci a gareni. Murmurshi nake irin mai kyalkyatawan nan nace kai amma kuwa nikan nayi sa,a,a,rayuwana wallahi. Insha Allahu zanci gaba da kullan maka da kaina a duk inda nake . Nace ni wallahi zancen kama har yasa na manta ban tabayeka lafiyan anty na ba da yara. Yace duk suna nan lafiya yanzu tare muke da uwargida ta dan shiga shago tayi sayayyane. A rude nace wai har na zaci ai a gaban ta kake waya dani haka wallahi. Yace aiko a gaban ta sai nayi don ba ta damuwa tama fini matsuwa kizo gidan ai yanzu. Na saki wata yar siririyar dariya nace kai ka taba ganin kishi har tafi ango damun akawo mata kishiya a duniya. Yace baki san halin ta bane shiyasa amma ni nasan zanji dadin zaman ku a tare sosai wallahi. Nace ni dai ka rufa min asiri kada dayar matarka tani tace zamu hade mata kai don muna shiya daya da ita. Yace ai itama tasan cewa Haulatu na waya dake tai fada harta gaji tunda babu yadda zatayi. Nace ni nasan dama idan ta sani sai anyi rikici don bata da dama,wallahi gurin kishi. Maryam tace kai kai wanan matar dai tun ba,a shiga ba na hango ita ce matsalar ku ke da Kabir . Dariya na kama tare da kashe ina cewa kai anty maryam watau kina jin hiran mu ashe? Tace duk abinda kuke fadi inajin ku ai in ya damu ba sai yazo ya zauna ba yai ta kore maki kudan da baison yasauka a kanki. Ya suke da hiran mu yakai geji yakawo iya wuya sai yaga fita dakin yafi mashi jin takaici kawai. Ya mike yanace maji zan fita sai na dawo tace mai a dawo lafiya tare da ci gaba da kallon ta. Yana fita Amira tace ke Bintu watarana sai yaya ya make bakin nan naki akan wanan wayan da baiso. Mutum da mijin shi zai make ta idan yaji takaici yaje ya samo tashi matar mana shima inji maji takeba Amirah amsa.

Readers Also Read