Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 67

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 67

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 67: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 67. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi…

2,046 words

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,

DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH YA SAKA MIN AKAN MAI SHI,,,,,

Fuskan ta a daure ta watso min harara tace shige ciki da wanan wasan banzan naku, simi simi nabi gefenta na shige cikin gida. Binshi tayi da kallon mamaki shiko ko a jikin shi saima gyara hannun rigan shi yakeyi kawai. Mama batai mashi magana ba sai kutawan da tayi ta shige ciki yace a fili i will dealing with you silly girl kawai. Duk nabi na takura kaina sai jira nake mama tai min maganan amma shiru babu zancen haka yasa na sake gaba daya. Rayuwa tana ci gaba yayin da takuran da sadauki ke min bai fasa ba don duk wani aikin shi nice zai saka komai wahalan aikin kuwa. Zancen Maryam da Bashar har ya kawo gida yanzu don iyayyen shi sunzo gurin Baba. Sadauki sai da ya dauki zafi sosai da Bashar har ya gaji ya sake don kan shi don Bashar din ya nuna mashi halin ko in kula ga yadda yake nuna mashi . Halin zaman kishi na gidan su mama yana nan daram bai gushe ba don sai da suka samu mahaifiyan Bashar da cewa don may zata yarda ta hada zuria da wa yan nan mutane masu jinin tsiya fakirai masu gadon tsiya. Inba yanzun ba da saudauki ya samu abakin may Hauwa,u take a gidan wace bata iya mayar da taro sisi zuciya ya mutu mata. Amma dai yanzu ai Alhamdullahi ko don dama azziki ai gida biyu ne ko kai kayi ko danka yi ? Mahaifiyar Bashar ce take tambayan su da hakan tace ai shi arzikin da yafi na iyayye dadi don zaka koma tankar basarake ne. Baku jin ance bayan wuya sai dadi ba, dama cewa kukayi yarinyar bata da halin mutunci ne kila da sai na duba. Amma Alhamdullahi, na zauna da yaran nasan halinsu don haka aure ne idan Allah yayi a tsakanin su nafi kowafarin cikin hada zuria da kamilan yara irin zurian maijidda a duniya. Sai kuma suka fara cacan baki wai sun gane dama,kwadai ne kawai ya kai Bashar ga maryam don dan abinda yake samu ga,sadauki din. Dama sun sani ai don haka ya raba shi da kowa nashi ya manne mashi kamar cingun. Da,Bashar ya dawo ake fada mashi bai nuna bacin ranshi ba don yasan zasu iya hiya da hakan ma. Amma yana barin gida direct kasuwa ya nufa gurin Baba ya fada mashi komai yace ai masu Umma iyaka dashi da uwanshi. Ran Baba yai matukar baci sosai haka yasa shi dawowa gida a lokacin yai sa,a basu jima da dawowa daga gantalin su ba ke nan. Ganin Baba gida ba lokacin dawowan shi ke nan ba yasa kowa mamakin ganin shi cikin wanan lokacin. Gaba dayan su ya kirasu basuyi tsanmanin zancen bane sai da Baba ya tambaye su da cewa Atika ke da Asiya ina kuka tafi ne yau ? Wana ta dubi waccan suka fara a tsakanin su sai umma ce yar gadara tace asibiti muka shi gaida Hanse yace abisa umurnin wa kuka tafi? Yace bama wanan ba don na riga na barku ga Allah kan fitan da kuke yi bada izini na ba a gidan nan. May ya kaiku gidan marigayi salisu mai engine ? Da mamaki mama ta dago tana kallon su sai hjy kubura ce tace gidan Alhaji salisu mai engine ai gidan su Bashar din da zai auri mayam ke nan mana. Yace eh can din? Shiru sukayi sai Umma tace da muka je ance maka munyi wani abin ne acan. Yace mai zaihana kuyi tunda shi ya kaiku yace da farko da Sani ya fada min kuka soke zancen auren sadauki da Rahama ban yarda ba sai yau din nan nayar da da hakan don kaidin ku ya wuce yadda nake tsamanin ku. Na dauka duk wani "da da ya fito daga tsatsona kamar kuma dan kune a gidan nan kuma. Ya girgiza kai yace ashe nayi kuskuren yin wanan tunanen a kanku don ku din nan ba abokan zaman alheri bane a gareni tun da har kuka, iya wanke kafan ku kuka tafi soke auren yar yaruwan ku. Salati suka saka suna fadin yaushe akai haka su sheri a ka kulla masu kawai daga sun tafi, gaida mahaifiyan shi kawai. Yace to yanzun dai Bashar ya samayni ya roke ni nai maku kashedi akan gidan su da uwarshi don haka duk wacce ta kara shiga harkan shi duk abinda yai mata ita tajawa kan ta tunda daini bada izzina na kuke fita ba gidan nan. Abin bakin ciki da rashin sanin ciwon kai ace kun fi son yaran nan suyi ta zama a gida suna shashanci kamar yadda diyan ku sakeyi suna bata min suna a gari. Abinda Nafisa keyi a garin nan waye zai aure ta a haka da ita watsatsa yau itace wancan party gobe itace gidan mashaya gata kuma gata wai a kungiyan yan madigo a gari. Da sauri Umma tace kan yar ka yar gwal kada ka kulkawa diyata sheri don da baifi daba a duniya. Yace sheri kan Atika aike kika kulawa kanki ke da baki kaunan dan wani da karuwa kina ganin Allah zaibar naki yadda kike so ne ke ? Ran Umma ya baci kan bankada asirin Nafisa da ya yi a gaban kishiyoyin ta nan ta hau sababi tana borin kunya. Yace magana daya ya rage gareku yanzu shine daga mazan har matan duk kowa ta fito da miji tai aure su bar min gida na hakana na huta da fitina haka. Ya girgiza kai cikin takaici jin borin kunyan da Umma ke tayi wai bai kaunan ta ita da diyan ta agidan dabakin shi yake kulla masu Sheri don ya gyara zuciyar masoyan shi. Shidai yafita bayan yai masu warning da gargadi mai karfi kan duk wace ta kara fita bada izinin shi ba har yaji sai tabar mashi gidan shi. Maji ta dawo dakin ta cike da mamakin wanan irin bakin jinin da mutanen nan suke gwada mata haka. Nan take fadawa yaran abinda su Umma sukajeyi gidan su Bashar daga inda nake nace ai sun kai karshen gulma indai gidan su Bashar ne Inna ce ko Bashar din ai suna daidai da su. Waya mama ta dauka takira Inna na ta kwashe duk yadda akayi ta fada mata mama tace Allah ya kyauta nabar su ga Allah. Buki za,ayi a family house din su Baba haka yasa yanzu su mama basu zama a gida sosai don suna zuwa can gidan gurin aikin bukin da za,ayi. Shima yaya sadauki baya zama a gida sosai don ina ga,akwai wani aiki da yasha mashi gaban shi don sai dare yake dawowa gida. Yauma da dare ya shigo har lokacin su mama basu dawo gidan ba suna can cikin gari. Daganin shi a gajiye yake sai dai kuma alama ya nuna min yana cikin halin shi don ya dan sha a lokacin. Maryam waya take da,wata kawarta Amira tana kallon wani season film a tv bayan an gaisa dashi kowa ya juya gur8n harkokin shi. Ni dake zaune da litrafi ina karantawa na mike sai gaban shi na ce mashi a hankali control yourself mr. Da sauri ya dago jajaye idanuwan shi ya watso su a kai na gyada kai nace ka natsu kokabar falon nan tun mama bata shigo ba. Mamaki takaici haushi ya kama shi a lokaci guda yace cikin tsawa ke kin raina ni ko dayawa ? Easy mr behavour self da sauri maryam ta dago ta kalle mu nace akawo maka abincib ne. Ban sani ba ya fadi a fusace sai ya mike cikin rangaji ya bar falon ran shi a bace wanan yarinyar kodai aljannace wai ita ? Maryam na kallona na gyada mata kai alaman ya sha yau tace oh Allah wanan masifa da may yai kama. Mikewa tayi tabi bayan shi, sai nima na biyo su yana tsaye ya dafa bangon dakin shi bai shiga ba yaji muryam maryam tana fadin haba yaya sadauki. Da sauri ya juyo takaraso tana fadin kada kaga laifin Bintu gaskiya take fada maka tsawa ya daga mata lokacin nakaraso gurin. Ya bini da wani mugun harara yace sai na karya ki a gidan nan wallahi yar iska mai balain sa idon tsiya kawai. Sai kuma yai shiru tare da kyatafa kawai ya dafa bango kan shi ya dukar a kasa. Nace yaya kayi hakkuri bani son mama ta fahince ka a hakane wata rana kaji may likita ya fadi a kanta. A guji bata mata rai don dazara akai mistake watara zuciyan ya buga a lokaci guda za,a iya rasata gaba daya. Yaya kana son sanadin ka ace mahaifiyan ka ta rasa ranta kan bacin ran ka ne ko yaya ? Maimakon yai cikin mu da masifan daya fara yadda nai tsanmani sai naga ya dukar dakan shi a kasa. Ikon Allah sai Allah yau gani mukayi yata sadauki yana kuka kuka kuma mai ban tausayi. Yace maryam bani sha a ko ina sai ina garin nan i don't know why nakejin irin haka kawai a garin nan ? Idan ina garin nan in basha ba bana jin dadi rayuwana sam wallahi sai na dinga jin kaman zan kama da,wutane. Amma kudai tayani addua kawai Allah ya kawo min agaji ga halin nan. Bana son ace sanadina uwata ta samu matsala a rayuwan ta ko kadan bani jin dadin hakan idan na tuna. Kuka ne ya dan fi karfin shi maimakon mu bashi hakkuri sai nima nafara kukan abinda yasa Maryann itama kuka ke nan lokaci guda. No no ku bar kuka please zanyi kokari naga cewa na daina hakan insha Allahu. Nace yaya idan ka fara jin haka don Allah ka dinga nafila kana kai kukan ka ga Allah don ka samu sa,idan jin hakan da kake yi. Ya dago ya kalle ni ina makure a bango kaman zaiyi magana sai kuma yai shiru, ya dade a haka yace ku shiga gida kada wani yazo ya samay ku anan. Har na juya nace abinci fa yaya yace No kibar shi kawai I am OK. Kuka sosai maryam tayi bayan shigan mu gida da kyat na samu na lalashe ta har tai shiru tana tausayawa halin da dan uwan ta yake ciki. Bintu fada min yaya kike gane yaya yasha ne wai ? Nai murmushi na ce da farko idan kinga ya shigo da glass a idon shi to yasha sosai ke nan. Idan kuma kin gashi ya shigo ya zauna yai shiru kaman akwai abi dake damun shi to abin yadan fara sake shine hakanan bai son yawan magana sai kasala kawai yake ji. Sai kuma da zaran kinga yana bukatan abinci a gagauce to abinda yasha ya fita kan shi ke nan sai kiga yana jin yunwa sosai. Zakiga yana shiru shiru sometimes to yana cikin dan maye ne zai dinga zama kaman wani salihi can dashi. Bintu baki ganin kaman asirin da akace su Umma sunyi mashi a cikin gidan nan yake kuma kilama a dakin shine ko makamancin haka ? Nace sanin gaibu sai lillahi anty amma hakan kuma fa magana ce sosai. Tace in hakane yabar gidan nan ya koma gidan shi mana da zama zai fi mashi sauki nake gani. Anty yaya zaibar gida baiyi aure ba? Ke kinga alaman aure a gaban shine yanzu Bintu ? Nace ai irin su mata basu gaban su anty duk matar da zai aura matsayin baibar wanan rayuwan ba sai tayi hakkuri wallahi. Don bata gaban shi idan yasha kuma sai dai yai ta tabara yana zubar da kiman shi a idon ta da jama,an da suke tare. Wai ke ina kika san wanan halaiyar tasu ne haka Bintu ? Murmushin takaici nayi nace a gurin mijin mahaifiyata mashayine shima amma shi irin shan nan na yan kauye yakeyi mara fasali. Nan nai ta bata labari na yadda mamana take hakkuri tana kuma nema mashi maganin hakan ? Nisawa tayi tace shiyasa lokacin da su Baba Sani suka hana yarsu daga baya banji haushin su ba wallahi. Don yau babu wanda zaiso ace nashi na cikin fitina ko tashin hankali haka ai ?

Readers Also Read