Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 68

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 68

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 68: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 68. ****** ********* ****** Washegari Mama ta tilsata mu kan sai…

3,370 words

****** ********* ****** Washegari Mama ta tilsata mu kan sai mun tafi gurin buki don ayi kamun amare damu tana fada take cewa, ban san may yasa baku son yin zumunci ba wallahi. Zumunci da kuke gani ba abin wasa bane wallahi don igiyace mai kai mutum aljanna idan Allah yaso. Amma rashi sanin darajan shi yasa kuke sakaci da shi alhalin gaku Allah ya baku yan uwa bila,adadin a gari babu gidan wanda kuke zuwa kullun kuna kulle a gida kaman kayan wanki. Ba don mun so ba muka fara shiri bayan sallah azuhar zuwa gurin sa lalain yan uwan su da za,ayi a family house din su na diyan kannen baban su. Ga ba dayan mu dogayen riguna muka saka muka daura dan kwalaiyan su akawunan mu. Shigar tai matukar karban mu sai dai matsala motar da zata kaimu ce babu a lokacin haka yasa yaya sadauki yace mu bari ya kaimu da Amirah tai mashi magana. Amirah ce agaba tare dashi mu muna baya a zaune sai dai ban san yaya akayi na zauna a setin mirror shi ba na gaba. Maryam ke fadi wai yau kan sai mun sha surutu a gurin mutane yaushe rabon da naje gidan nan ni. Amirah tace ni wallahi ba,son zuwa ne banyi ba yadda ake damun mutum yaushe zaiyi aure yake damuna. Daga inda nake zaune nace kai mutane akwaisu da daukan wa rai shifa aure kamar rayuwa yake idan ya tashi koba shiri sai anyi shi haka ma rabuwan shi idan yazo ko bashiri sai anyi shi. Dago kan da zanyi naci gaba da magana muka hada ido dashi ta glass din motan yadda naga idanuwan shi sai naji gaba na ya fadi daga haka naja bakina nai shiru ban kara magana ba don duk na dago kai dashi nake arba sai ma na daina daga kan nawa kawai. Tun a kwanan gidan muka fara ganin dandazon motacin mutane da sukazo gurin kamun. Wata mata tazo da motar ta shige gaban mu maryam tace shegiya mu akewa kurin mota mima watarana insha Allahu ki gan mu da namu. Nace kai anty kin rage mata kaya bata masan kinayi ba ita, Allah Bintu inason naganni da mota ina ja wallahi. Nace in Allah ya nufi ki ja sai ki gan ki dashi kuwa ai tace wai da su Umma sun mutu ranan. Nace su kuma ai zaman su ke nan hassada wallahi basu ko tsoron haduwan su da Allah. Allah suka sani aida basuje gidan su Bashar suke auren maryam ba inji Amirah. Da sauri ya juya gareta yace kamar yaya wai har muka isa inda zamu sauka tana mashi bayani haka yasa bamu fito daga motan ba sai da tagama mai bayanin komai yadda akayi. Mutanen dake tsatsaye daga waje sun matsu sugs ko suwaye a wanan haddadiyar motatar haka ga shi na cikin motan basu fito ba. Sai da suka gama magana ya bude muna tare da tambayan mu karfe nawa zai dawo ya dauke mu Amirah tace shidda daudai yaya. Nice na fara sako farin kafa na a waje daga gefen da nake zauna sai wata tace dama nasan wasu special ne daganin wanan uban motan haka sai gidan gwauna, muna fitowa ashe su Rahaman shi ce a tsatsaye nan shima ya hango su, Kiran mu yayi muka dawo gare shi daya bayan daya yake muna magana kowace tana juyowa da dariya ganin ya gama magana da kannen shi yasa nima na juya zan wuce nabisu sai yace Fatima nace naam yaya yace zo nan na karasa gaban shi. Yace don Allah kada kiyi masu kayanci agurin nan kiga dai duk ido akanku yake. Maganan shi ce tasani dariya a lokaci guda wanda mutanen dake gurin suna zaton ko wani maganan soyayyane yake fada min hakanan. Yana fadin haka yaja mota yana murmushi duk suka bishi da idanuwan su caaaa kowa na son ace itace ta mallaki aana haddaden guy din mai kyaun dan maci ji. Abokan Rahama da yan uwanta ke ce mata kai amma gaskiya kinyi hasaran miji ko dai wanan yarinyance zai aura ne? Tace a kufule kamar yaya zai aureta anfada maku anfasa zancen namu dashi ne halan . Nan suka shiga gaisawa da mutane yan uwa da abokan arziki ana ta masu sheri don yau bukin gidan su ne yasa su fitowa. Buki yayi buki duk guri ya kicimay da kida don an fito da amare su hudu ne gaba dayan su a filin. Muna tsaye gefe sai kallon amaren muke gwananin ban sha,awa nace anty Allah ya nuna muna naku muzo musha bidiri muma. Ameen ke dai Bintu inji maryam itako Amirah cewa tayi nifa duk wanan abubuwan basu damay ni ba fa. Nace nima nafison in zanyi aure aimin walima haddade wallahi duk yafi wana gwatsale gwatselen da mata da yara keyi. Ji mukayi wai ana kiran dagin amaryam su Amirah su fito suyi rawa a fili basu so fita ba kuma banyi tsanmanin zasu jani tare dasu ba sai ji nayi maryam ta jawo hannu mun shiga fili tare ban iya rawa ba don ban ma,taba yi ba don haka takawa kawai nake yi a hankali. Kaina a duke naga su maryam su falle jakkan suna min liki take guri ya hau ihu da sowa sai tambaya mutane keyi wacece ita da suke mata likin kudi haka? Komai namu a gurin a natse muke abin mu cikin nuna sanin ciwon kai da kuma tarbiya. Muna gefe mu kaji guri ya kaure da sowa maryam ke tambayan ko su waye wata tace wai ance wasu mashaya ne yan uwan su amaryan yan mata suka zowa kawarsu kara. Innalillahi wacece kuma maryam taja min hannu Anty Amirah na gaba muka leka Nafisa ce da kawayen ta suke wani irin rawa gasu sunyi shega zakace akwatawan ghana ne su guri ya rude da sowa masu tir da Allah waddai suka shiga bakin su. Daganin su a buge suke don rawan ba rawan kai sake bane har gaban samarin da suka shigo suke shigewa. Kiran wayan da sadauki yaiwa Amirah yasa mu saurin barin gurin muka fice a filin gada ma agan su ace yar uwar su ce. Mun shiga mota su Amira sai yankan fada sukeyi suna tir da Allah waddai da halin rayuwan Nafisa. Maryam tace yau maganan nan sai yakai kunnen Baba ai akwai magana agidan nan yau wallahi. Umma tagama jin kunya da nauyi ya agaban su fa su Nafisa ke wanan rawan tsiya waisu ga yan iska. Allah dai ya shirya su damu baki daya nace daga inda nake a zaune sai lokacin yai ajiyan zuciya bai dai yi magana ba. Maimakon mu tafi gida sai wani hanya ya dauka da mu can hanyan masarauta. Gurin kaman company sayar da motoci ne yana tsayawa naga mutane suna nufomu suna gaiyar dashi daya bayan daya. Amirace kawar shawaran shi da hira dama yace Amirah tace na,am yayana yace kin san gurin nan tace ,a,a yayana yace kallo signboard din can ki karan ta muna alokaci daya duk muka daga kan mu an rubuta da mayan haruffa kamar haka. MAJI ENTERPRISISE da sauri kowan mu ke kallon shi a cikin mamaki maji suna kuma kaman na majin mu? Natane yace cikin rashin ko in kula ya fadi hakan gurin muke zagawa muna duban motocin dake gurin latest masu kyau da tsada yakai mu wani layi yace ga layin na mata da ake yayi nan mukai ta kallon motocin cikin mamaki. Wanan tace ai wancan yafi kyau haka sukai tayi a tsakanin su naga wani assh color nace amma wanan sai naga duk tafisu kyau kai amma dai Bintu baki san mota ba wallahi nace ina kuwa zan san su anty daga jaki sai rakumi na sani dandamama doki. Wani irin dariya suka samin ganin yamma yayi daga inda yake tsaye yanufo yana fadin mujen ku magariba ya kusa yanzun. Muna hanya maryam tasakani gaba da,sheri wai nace jaki da rakumai na sani dan dama dama doki. Shima dariya yai min yace bana fada maku yar kauye bace kunki yarda dani, Amira tace ,a,a gaskiya yaya yanzun Bintu ta wuce irin bakauyan da kake nufi fa. Yau gasgi harda rawa tayi a gaban mutane ida dane waya usa yasa Bintu rawa a bainan jama,a haka. Yace ai bata da kunyane ki shiga rawa gaban mutane kamar wata chuss can dake, da sauri na dago kai muka hada ido a gaban motan da yake Amirah tace ai duk mune don mun fita rawa ita da take wani yauki kaman a gaban saurayin ta take. Kila yana gurinne tunda kukaga tayi hakan kin san yar tara samari ne ita bata da kunya ai. Ai duk rawan karya mukeyi da mukaga uwayen mu sun iso aikowa ya jaye gurin gabadaya aka basu fili. Ni dai har muka iso gida ban yi magana ba shiru nayi kada ya disgani yadda ya saba yi. Sallah muka fara gabatarwa tukun muka dawo falo muka zauna sai ga mama sun dawo daga gidan bukin. Sai faman yi mata sannu da zuwa mukeyi maryam tace maji yau munga abin mamaki gidan saida mota da sunan ki wallahi. Sunana kuma ? Maryam tace wallahi maji har gurin yaya yakaimu mu gani muna ta mamaki. Wayan Baba ne ke kiran mama a lokacin bayan ya tambaya dasun dawo tabashi amsa da eh sun dawo tana gida yanzun haka. Nanmuka ga ta mike ta fita daga dakin zuwa can mukaji hayaniya a tsakar gida maryam tace kuyi shiru mu ji don Allah, Kaman fada ake a tsakan gida muna ji muka kwasa zuwa waje da saurin mu Baba ne da Umma yake ta ja mata Allah ya isa akan Nafisa tana mayar mashi da amsa. Sabon tashin hankali sai ga Amirah tashigo gidan abuge ta ita tayi tatil kawayen ta sun kawo ta kofan gida sun zube ta haka. Ranan muga tashin hankali don Baba zubewa yayi kofan shi da sauri su mama suka tare shi suna mashi fitara. Yaya Sagir yana gida shi ya fara jibgan Nafisa baji bagani cikin bacin rai gida sai koke koke sukeyi . Itako sai tabara takeyi tana fadin magana irin nasu na yan maye bata fasa magana ba shi kuma bai fasa dukan ta ba. Abinka da yan uwan taka sai ganin su Amirah nayi suna rike shi suna bashi hakuri yayi hakkuri kada ya halakata. Yana barin dukanta utakuma Umma ta shiga jibbagan ta kamar an aiko ta tana kuka gwanin ban tausayi da ita. Maryam.takira yaya sadauki ina jin yana kusa shi yazo ya dakatar da Umma yana bata hakkuri ya dauki Baba suka nufi asibiti dashi. Haka muka zauna jigun jigun damu agidan babu dadi don harka ya lalace ranan baki gaba daya ya mutu wa Umma. Can mukaji tana kuka tana fadin wallahi bata yarda yiwa Nafisa akayi talalace kaman yadda dan maishi ya lalace ita wallahi bata barwa Allah sai ta dauki fan sa. Anyi daidai sun dawo da Baba lokacin hajiya kubura tace ji mahaukaciya kawai sai ki matsa ai kaikayi koma kan mashekiya ce akan ku zai kare yan banza. Nan kuma suka shiga sabon cacan baki a tsakanin su da mummy sai zage zage da tonon asiri sukeyi. Kai haba mummy ku tausayawa bawan Allah nan mana ku dubi halin da yake ciki da wani zaiji da fitanan ku ko da abinda ke damun shi. Sadaukine yake wa mummy magana tace ai na bari sadauki amma in Alhaji ya mutu gidan nan da hjy Atika da diyan ta zamuyi kuka wallahi. Yaran kawai gasu nan ba,a gama wani ba su jefa mutumi a wani yaya za aiyi mutum yai lafiya haka ? Muna shiga daki bamu jima ba mama ta shigo dakin ita ma ta zauna jiki ba karfi tare da ajiyan zuciya. Tace ni fitinan gidan nan wallahi ya fara isata abu tun ana da jajjayen sawu har girma yazi baza,a daina ba. Tun farko shiyasa ban so zama ba wallahi babane ta tauyeni wai na zauna na saman ma sadauki abokan shawara a gida shine kukaga har nakai war haka a gidan nan. Mani mukan ai gara da kika zauna da bamusan inda za,a haife mu ba kuma inji maryam cikin dariya. Mama ta harare tace wawiya kawai don baki san irin wahalan dana fito cikin shi ba ko ? Mama al,amarinki kaman na mamana,wallahi haka sukai ta,kwasa da mama ta bawa har mamana tagaji tabar mata gidan gashi ko yanzun dai sai hakali. Maji tace haka abin yake yanzun ai a hanaka zaman lafiya gidan mijin ka in bakakai zuciya nesa ba sai ka bar gurin gaban kuma da kake hange sai dace. Tambayam bazata mama ta jefo min daidai lokacin da na daga kaina sama ina tunanen halinda mahaifiyana take ciki a can kauye. Wanan tunanen bayau na farashi ba walau in naji dadi ko naga wani abinda ya danganta da rayuwan ta. Muryan mama tana ce min Fatima yayan ku ya shigo yaci abincin shi kuwa yau ? Da sauri na dago kai ina kallon ta don tambayan ani ya bani mamaki nace ina ganin baici ba don tunda muka dawo banga ya shigo ba. Tace dubo min shi a,waje ko yanan nai magana dashi naji may zai ba su baban ku gudun mawan buki? Namike tare da zura takalmina ganin a cikin gida zan tsaya sai ban saka hijjab dina na ba nafita haka nan. Na duba waje baya nan kaman nakoma na fada mata sai nace bari na leka dakin shi tunda naga wuta a bude. Na leka sai naga kamar bai ciki hakan yasa na dan kara takawa ciki zaune yake yana shakan wani abu a wabi farin takarda haka. Jin motsina yasa shi saurin dago kan shi da sauri mukai ido biyi da sauri na juya zanbar dakin. Abinka ga dan kwallo tako data ya cafko ni sai jikin shi ta baya zan saka ihu ya danne min bakina da hannun shi daya. Bakina yana matse nake ce mashi mamace tace nazo na dubaka wai tana magana da kai . Saboda hannun shi daya ya taushe min baki bai bari yaji abinda nake fadi ba. Birkito dani yayi daidai fuskan shi muna kallon junan mu face to face ni dashi a hankali yace may yakawo ki dakina muna fuka ? Ya dan sauke hannun shi daga bakina nace mama ce tace nazo na,,, sai ya kara matse bakin iya karfin shi. Mamaki da tonon asiri sai jin saukan hannin shi nayi zuwa kirjina yana fadin abinda kikazo nema ke nan bakar jarababiya kawai. Na girgiza kai idona a rustse nace da karfi wallahi mamace ta aiko ni gurin ka. Bai sake ni ba kuma bai fasa abinda yakeyi min ba a lokacin, wasu hawaye naji sun fara dan silalo min daga idanuwana. Bin jikina yake a hankali da shafa yayin da nake jin saukan numshin shi a kunnuwa na cikin wani bakon yanayi. Cizo nakai ma hannun shi nace da karfi wallahi Allah ba gulma nazo ba mama tace nazo na kiraka wai . Daidai kirjina ya tsaya ya dakata da abinda yake min nace don Allah yaya ka sake ni in tafi wallahi mama ta aiko ni na kiraka . A hankali yakai hanniwan shi saman kirjina yadan shafo su cikin hikima irin ta maza da sauri na dan sulale nai kasa don abinda naji a lokacin. Kara dago ni yayi daga dan dukawan da nayi ya dago fuska na tare da hada shi da nashi ban aune ba yakai bakin shi ga nawa ya dan fara tsotso a hakali. Nan na shiga ture shi daga jikina kaman dutse nake turawa don ko motsi baiyi ba kuma bai fasa abinda yake min ba. Can naji ya turani da baya da karfi tare da dafa bango yace yar iska gobe ki dawo min daki kadan kika gani yau. A hankali na dafa bango tare da dan bugewa cikin kuka nake fadin har nakai kofa wallahi ban yafe mugu mazinaci kawau aiko ta biyoni a guje ban tsata ba sai falon mu. Yaya haka kuma da sauri mama ke tambayana tare da son jin bayani daga gurina tana kallona. Nace cikin kuka ba yaya bane ya kai min nashi wai may yakawo ni dakin shi. Sai gashi ashe yana bayana a lokacin sai kamshi yakeyi kamar bashi ba. Tace kai kuma daga na aika yarinya ta kiraka sai ka kai mata nashi kai dai wallahi sadauki katon banza ne wai dadin may kake ji gurin zaluntar yarinyar nan? Yace haka tace maki nashin ta nayi ? Ai duk ni na ja mata hankan tana zaune zaman ta ta tashi na aike ta kiran ka na manta kai mugune gareta. Inda nake zaune ya dan kalla sai faman zubar da miyau nake ina tofarwa tare da goge bakina da dan kwalun dana cire akaina. Gashina daya sha gyara yana kwance hat gadon bayana yasha gyara sai walkiya yakeyi. Murmushin ke ta ya sakar min tare da dan kashe min idon shi guda daya. Mama tace mai dama zancen abinda zakaba iyayyen kane maza masu buki, don banji kace min komaiba har yanzu kan zancen. Yace ni maji may zan basu kuma ? Sadauki iyayyen naka kuma suna buki zakace may zaka basu bayan kowa yanzu yasan kana dashi. Murmushi yayi kamar wanda yake a cikin nishadi yace OK maji sai ki fadi abin da za,a basu din ai ina ganin is OK. Nasan aljihun kane Baba na balke na shatama ko nawa zaka iya ba iyayyen ka yace, maji ki fadi kawai ba matsala ai tace hamsim hamsin yayi ko yace kai haba haba mji adai basu koda dari biyu biyu ne ai ina ganin is ok for them, Kai yaya har dubu dari biyu biyu baiyi yawa ba yace baiyi yawa ba Amirah bari a basu kawai. Yana fadin haka yace maji abari har da safe sai na ciro masu na kawo maki kiba Baba ko ? Har lokacin ina zaune sai hawaye nake zubarwa ina bakin cikin abinda sadauki yai min yau ashe dan iska ne haka ban sani ba shi da yake ikirarin cewa bai taba zina ba ashe tsohon mazinacine haka ban sani ba. Nai zurfi a cikin tunane na nake jin muryam maryam da karfi tana fadi, da gaske yayan mu yace saka hannun shi ga aljihu yace kowa tazo ta karbi nata key din gashi sai lokacin na dan dago ina kallon su. Keys ne ya ciro daga aljihun shi yana mika masu nakai ido ina kallon keys din . Yace kowacen ku wanda ta zaba dazun shine nata juyawan da zasu gurina sai ganin ina kuka sukeyi. Lah Bintu badai har yanzu kukan dan nashin da yayayai maki ki ke tayi kamar wani nashi can. Ya dago tare da kallo yace au wai kuka takeyi bafa wani nashi sosai nai mata,ba dama nasan kukan shagwaba da jin dadi zaki tsaya yiwa mutane haka. Ya kare maganan shi cikin lashe bakin shi kamar wani maye can nace a fili mugu azzalumu kawai na mike na shige daki cikin kuka. Dan murmushi yayi tare da lumshe lumsarsu idanuwan shi da da tun shigowan shi falo suke mashi haka. Ko may ya tuna sai yai murmushi tare da bude idanuwan shi caraf acikin na maji tace Baba na wai wani irin keta kaiwa yarinyan nan yau haka har kasa ta kuka. Yace bata fada maki ba maji dan kai mata nashine fa nayi kuma ban ma samay ta sisai ba fa. Wallahi kadai ji tsoron Allah gashi don tsaban ket kasa yar mutane kuka haka idan bata ji zafin abinda kai mata bata bacin ka haka yau. Ai ba yau kafara mata kyeta ba amma bata taba fada haka ba ido da ido sai yau ? Wallahi maji bata jin magana ne tafaye shegen gulman tsiya kungan ta nan. Mi dai bata taba muna gulma ba don muke zama da ita sai dai ke da ka saka mata ido don kiyayya kake ganin haka gare ta. Kiyayya kuma maji aiko yayana bai ma Bintu haka kawai dai ke ke ganin hakan wallahi amma ita,ai Bintu ba baya ba itama kingan ta shegen tsokanane da ita. Anty Amirah Anty Amirah wallahi ki iya bakinki akan Bintu da yayan mu, inba haka ba watarana zakiji kunya sosai wallahi.

Readers Also Read