Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 69

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 69

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 69: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 69. ****** ********* ****** Kwance ya ke saman gadon dakin shi…

3,089 words

****** ********* ****** Kwance ya ke saman gadon dakin shi rigingine ya saka hannun shi yai crossing dashi idon shi biyu amma yanayin kwanciyan shi sai kace yana barci ne. Saboda idanuwan shi da suke a lumshe a lokacin a hankali yake tariyo abinda ya faru a tsakanin shi da Fatima. Hannun shi da ya sauke akan kirjin tane ya fado mashi a rai yana tunanen may ya hanashi ya cire hannun shi a jikinta a lokacin. Murmushi yayi da yadda ya samu sa,an bakin ta ya tsose su yadda yake so son ran shi. Wani murmushi yayi naketa yace gobe ki kara yar iskan yarinya kawai gaba abinda zan maki idan na kama ki sai yafi wanda nai maki yau. Dariya ya kwashe yadda maji ke fadan wai ya nashi yar mutane ba gaira ba dalili don cin amana. Yasan da yau maji tasan abinda yai wa yar nata da ya shiga uku a gurin maji da masifa sai yabar garin ba shiri. Yakwashe da wani irin dariyan keta shi kadai yadda ya ga na koma gefe ina kuka a falo dazun da ya shiga. Yace a fili may be this is her time to have romance with somebody ? Ina daki barci ya gagati indona nayi brush yafi a kirga kafin na kwanta don ina ganin ya zuba min abin mayen shi ga bakina kila ga kazantan da nake ji a raina. Har anty maryam tafara zargin may wainake ta wanke ma bakine tun daxu nace mata ina jin bakina badadi ne yau. Tace aike ne dan abu kadan idan yaya yai maki sai ki ta faman mashi kuka shiyasa yake jin dadin yi maki kyata ai. Kema ki zage kai ki dinga ramawa idan yai maki bawai ki zauna kina kuka ba tunda naku sallon takon ke nan a haka. Hararan ta nayi nace don Allah anty barni kada ki kara min bakin ciki naja bargo na rufe jikina don sanyin da akafara a lokacin. Washegari ban fito da wuri ba ina gudun in fito na hadu dashi a falon sai guraren shadayan rana nafito falon . Ban dade da zama ba sai gashi ya shigo falon da sallaman shi nan suka shiga gaidashi ban dani da nai kaman ban gan shi ba. Nan ya dora idon shi a kaina ko kyaftawa bai yi yace ke baki iya gaisuwa bane halan yar kauye? Da sauri na mike tsaye zanbar falon yace kina tako daya daga gurin nan yanzu sai nai maki abinda kike so. Cak naja na tsaya guri guda ban motsa ba daga inda nake yace look at her kamar wata takwarai can nan ko shedaniya ce ta karshe. Na juya nace ni wallahi ba shedaniya bace sai dai in kaine shedan,,,,,,,,aiko ina ganin ya taso na ruga ciki da guda na kargamay kofan daki ina mai da haki. Yace ashe ke karamar yar iskane ai daki bari na samay ki gurin yanzu na wujujugaki wallahi. Daga cikin daki nace anki a tsaya din mugu kawai macuci yace ai kama ki zanyi sai kin fada min waye mugu a gidan nan. Ban fito ba sai da na tabbatar da yafita daga gidan ina fitowa suka kwashe min da dariya Amira tace kai Bintu ga tsoro gajan magana ai shine maganin ki wallahi. A raina nace baku san komai ba da bakuce min haka ba kuma da kun raina shi wallahi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,

YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH KA SAKA MIN AKAN MAI SHI,,,,,

Zaune yake a falon fuskan shi a daure tun da ya shigo gidan yake hakanan mama ta fahince shi amna sai batai mashi magana ba. Yana nan zaune ya dafe kan shi yai shuru tare da lumshe idon shi Amirah tafito ta gan shi zaune a gurin tace ,a,a yayana ashe ka dawo ne yace eh a takaice kawai. Takara cewa yaya akawo abinci ko don mun san shi ke shigo dashi cikin gidan wani lokaci. No Amira barshi kawai wanan abinda nasha dazun is ok for me, ya mayar da idanuwan shi ya lumshe su. Can yace Amirah ta amsa da na,am yaya. Ina wanan yarinyar take ne? Tace wa ke nan yaya? Yace Fatima. Suna ciki ita da maryam ina ga kaman waya takeyi ma dana fito. Yace kiramin ita please ? Ta mike na fadin toh. A tare muka fito mu uku a lokaci guda tanagaba ina bayan su . Yadda muka samay shi yasa mu dan shan jinin jiki don babu fara,a tare dashi. Nace a yar murya gani yaya ya dago jajjayen idanuwan shi da suka sauya zuwa ja jajir sai da gabana ya fadi. Yace ke a ina ki san wanan guy din dana gan ku tare a waje dashi ? Shiru nayi na dukar da kaina kasa ya dago cikin hasala yace ba ke nake tambaya ba ne ? Nace a,anan garin yake. Kin san ko shi waye da kike tsayawa dashi ne ? Maryam tai tsagal tace yaya a banki yake aiki nan gari yake da zama ai kuma dan ga,,,, Ban tambayeki ba maryam ita nake son ta fada min abinda ta sani akan shi kawai. A hankali nace ban san komai ba akan shi yadai zo yace yana so na ne. To ki rabu dashi daga yau kada na kara ganin kazamin motar shi a kofan gidan nan in ba haka ba sai na sa an kulle shi wallahi. Kai wai yaya haka may yayi shi mutumin da zaka yanke masu wanan hukuncin haka ? Maji ban yarda da shi bane don bai da record mai kyau, shine dalilina kawai. Kallon shi mama tayi kamar zatai magana sai taji na ce nagode yaya na juya na bar falon jikina yai matukar sanyi sosai. Ina tunanen wani irin halin banza ne ga Usman da yaya ya yanke min wanan hukunci a kan shi. Sai kuma nace tau Allsh dai yai min zabi mafi alheri da kan shi. Amma maganan yana ci min zuciya sosai ga Usman yana kirana amma sai naki daga wayan har ya tsinke. Haka yai ta kirana yana min text amma ban bashi amsa ba sai daga karshe yace nagane wanan dan wullakancin yayan naki ne ya hanaki hurda ni. Don dama tunda naga yadda yai min na fahinci shima yana kaunan ki don irin kallon da yai mi tare da kin amsa gaisuwa na. Wanan massage din yasa na dauki waya na kira Usman din nake ce mai tir da maganan shi, don mai zai min wanan furcin ga dan uwana. Fatima kada ki boye min nasan komai wallahi nasan shi ya hana ki kulani kada kice zaki boye min ni ba yaro bane fa. Haushi ya kara bani nace ashe da gaske baka da mutunci usman ni ka sani kawai don matarka na lura tafi karfin ka shiyasa na daina kulla ka kawai amma kada ka kawo min wani magana can na daban. Sai na kashe wayan na fara tunanen zancen Usman may yasa wai duk masu sona suke zargin hakane ga yaya sadauki. Ni dai iya sani na babu wani abin soyayya daya taba hadani dashi banda hattara da tsangwama da kina da yakeyi.

****** ********* ****** Sai bayan kwana bakawai da zuwan shi muka wayi gari da abin arziki don tsaraban mota mama da Baba suka samu inda yai masu Umma kuma kyautan kudi masu yawa. Ni dai ko tsinke bai bani ba dama tun ranan da yai min wanan magan muke zaman yar tsama dashi bani yarda mu hadu dashi. Kaman nasan bani da tsaraba, sai Allah ya rufa min asiri ban ma fito falon ba a lokacin hayaniyan ihun su nake ji suna murna a falon. Maryam ce ta shigo dakin inda nake tana nuna min sabon wayan ta mai matukar tsada daya canza masu da sauran tarkacen daya kawo masu. Nace kai anty amma kun gode yaya yayi kokari sosai wallahi Allah ya saka mai da alheri. Tace mama ta samu mota har da Baba kai ina son irin wanan tafiyan na yaya wallahi don a jike yake dawo muna idan yayi nasara ga ball din shi. Tace a,a na fa manta sai yanzu na tuna banga yaya ya baki, naki tsaran ba ko dai abin yar sirice kuma? Nace don Allah anty maryam daina wanan zancen kin san yaya mugu ne kada yaji zamana a gidan nan yakare da mama. Taso muje ki ga tsaraban mu don Allah kada ta tsanmani wani abu na sauko daga gado muka fito tare da ita. A zatona baya falon amma ina fitowa yana zaune sai dai kwana biyun da banganshi na ya sake min sosai. Gabana ya fadi don sai zuciya ta ta fara zargin ko dai yaya koma ruwa ne wai don yanayi yau da na gani akwai magana gaskiya. Ganin shi zaune yana waya muryan shi kaman mai jin barci ko kasala haka ya kara tabbatar min da zargina akan shi. Na nufi inda mama take zaune, cikin murmushi nace mama ashe alheri ya samay mune haka yau ? Eh amma ai bai gama ba don banga ya nuna min naki ba duk cikin tsaraban. Nace kai haba mama kullun fa ana bani don yau kawai ai ba komai bane kila ya manta da nine kawai. Murmushin manya mama tayi tace ya manta dake Fatima, haba magana dai yana da dalilin yin hakan da yayi kawai. Ya dago still cikin irin muryan farko da yake waya ba ko darr a ran shi ya ce, wai wanan yarinyar ban mata ba ban dai sayo mata bane ai na fada mata tun a cikin waya ba zan sayo mata komai ba. O ko gadarare ya mike tsaye tare da gyara wandon shi da ya dan takure don zama yace eh maji. Sai ya fice ko mama sai da tai mamakin wanan irin tsauri da yai mata yau ido da ido haka don ba halin shi bane bata ansa a tsatsaye. Yana fita dakin shi ya shiga dakin duk a hargitse haka ya kwanta rubb da ciki don tun daren jiya yai mugun hadiye kwayoyi ko zai rags damuwan shi a ran shi. Duk abinda nake hankalina yana ga yaya sadauki don haka nace wa mama zan shiga gurin gwagona don tana gari tana fama da ciwon kafa. Tafe nake ina tunane abinyi sai wata zuciya tace min gwada dai ki gani ko zargin ki hakane ? Ina tura kofan ga mamakina dakin da yake a rufe ko yaushe, sai na samau shi a bude, kamar na koma don na hango shi a kwance rubb da ciki kamar yana barci. A hankali nake bin dakin da kallo har na hango wani farin roba saman dan stoll din dake dakin yana dagwara kaya akai, Na jima gurin ina kallon roba don zargina ya zama gaskiya ko naga evidence da idona. Zan juya naji yace Fatima, Jikina ya dauki rawa kamar na ruga a guje don tsoro, ya ce may ya kawo ki dakina ? Bance kallah ba nai shiru, Yakara cewa uban wa yakawo ki dakina nace maki? Ya dago daga kwancen dayake yana fuskan tana idon shi duk sunyi ja jajir dasu. Bance kala ba sai karasa shigan danayi na taka har zuwa inda roban drugs din yake na dauka nace ga abinda ya kawo ni dama kuma nagani. Komawa yayi ta,kwanta,lamo kamar ya koma,barci nikuma ina tsaye na kasa daga kafata nai bar mashi dakin shi. Lokaci mai dan tsawo na zaci barci ya koma duk a tsorace nake a lokacin, Nafara tafiya sai naji yai yar dariya da sauri naja na tsaya cikin tsoro da sauraren shi. Ga tsoro ya kamani ban san gulman da ya kawo dakin shi ba don gani kwam kuma a part din samarin gidan gaba daya. Hawaye ne na fara zubar wa daga idona a hankali ba tare da ya dago ba yace kuka kuma again cikin magana kamar rada ya fadi hakan? Don Allah yaya kayi hakkuri dama zargi nake tun dazun dana gan ka a haka ? Murmushi yayi tare da mikewa zaune yace, ashe bayan gulma har kin zama C I D ban sani ba ? Haka kawai na tsinci kaina cikin karfin halin fadin gulman da nakeyi a inda ya dace nayi nakeyin shi ba hakana kai tsaye bs ga abinda ba damuwa na ba. Fuska a daure yace, lalaima yarinyar nan ta raina ni wallahi sosai, zaki gane baki da wayo don gobe baki karawa wani bakin shishigin tsiya irin haka. Wani irin naji cikina ya ansa kululu nace a raina yau ko na shiga uku nakawo kaina da kaina. Amma afili nace duk abinda zakai min nasan akan kauna mama kai min don irin halarcin da take min a rayuwana komai zan iya yi akan farin cikin mama don bata nuna min banbanci ba a cikin ku. Shiru mukayi dagani har shi ba wanda yai magana don kukan da yaci karfina a lokacin. Ba tare da fargaba ba naci gaba da cewa why yaya why baka tausayin mahafiyan ka why please ? Kai kadaine da namiji da Allah ya bata a rayuwan ta kaine take tunanen samun farin ciki a gurin ta. Yan uwanka da ma mu dake a karkashin inuwan ku gare ka muke fatan samun budi a rayuwan mu, Amma kai yaya baka tausaya mata baka jin kan ta baka tuna irin gorin da ake mata tsawon lokaci a gidan nan a kan ka why baka tausayawa kan ka da mahaifiyan ka ne please? Kafi son ko da yaushe ka zama abin kyama ga al,umma da kuma abin kwatance a gari yaya kawai Allah kabar wanan harka ka dage da rokon Allah da bayar da sadaka akan Allah ya rabaka da wanan halin kodon goben ka. Ina kaiwa nan na fara tafiya zanbar dakin yace Fatima, naja na tsaya tsaye cak guri guda. Ido ya zuba min na dan lokaci yace wanan magana ta tsaya iya ni dake a nan. Na girgiza kaina nace har abada bazan taba tona asirin dan uwana ba ga wani kai dai kadai tsoron Allah idan wani baigani ba ko yaji ai Allah daya hanamu shan maye yana kallon ka. Murmushi yayi tare da mikewa tsaye daga zaunen daya ke ban tsan mani har ya kawo gareni ba sai ganin shi nayi a gaba na ido da ido muke kallon juna dashi. Banyi wata alaman ta razana ko kadan kada ya gane a razane nake lokacin dashi. Ya nuna ni da yar yatsan shi yace ban san koke wata irin shu,umar yarinya bace da baki da tsoro haka nima ina mamakin kaina da nake tausaya maki amma tafi babu komai zamu kara haduwa wata rana. Nace kadai tausayawa mahaifiyar ka da kan ka kafin har mukai ga kara haduwan. Kuma bani fatan haduwan ya kasance irin wanan zargin a kan ka sai da ya zama wani abin alheri can daban. Roban kwayan na hannu na fita daga dakin tabi bayana da kallon mamakin irin karfin halin dake gareni haka. Sam banda tsoro ko shayin wani a idona yadda ya hango cikin kwayan idona gaskiya ce sahihiyar ta na fada mashi kuma na fita. Ina tafe ina sharan hawaye har nakai gidan gwagona sai da na samu gidan yana rufe tafita ke nan . Na juyo na dawo gida tareda boye roban kwayan a jikina har sai da na kai part din mu ina shiga mama tace har kin dawo ne nace bata nan tafita. Amma kuma ya fuskanki kamar kinyi kuka na dan yi yake nace kuka kuma mama? Banyi kuka ba mama daga haka na shiga daga ciki sai kuma mama ta fara zargin ko dai tsaraban da sadauki bai kawo min bane ya bata min rai har nai kuka? Ina kwance daki saman gadon mu kaina sama kafana suna zufe daga kasan gadon, na dan jingina jikina da kan gado. Ban san shigowan ta dakin ba don nai zurfi ga tunanen da nakeyi a lokacin. Fatima naji ta ambata abinda yasani saurin dago kaina ke nan ina kallon ta da sauri ina kokari gyara zamana da kyau. Itama dai zama tayi daga gefe na kadan tare da kura min ido kamar mai nazarin wani abu a gare ni. Abinda yaron nan yai maki ne yasa ki kuka ko? Da sauri na girgiza kaina nace wallahi Allah ko daya mama ko kadan ban sa haka a raina ba. To may yasamay ki kai kuka da fitan ki yanzu, don ba haka kifita ba a gidan nan. Dukar da kaina nayi kasa nace a hankali ba komai mama,. Yanzu har takai lokacin da zaki iya boye min wani magana a cikin ranki. Da sauri na kara dago kai nace wallahi mama ban boye maki ba sai nai shiru. Bazaki fada min ba ke nan ko? Maimakon nai magana sai na sake kuka shiru tayi tare da kura min ido har tsawon lokaci can tace nace zancen tsaraban da ya rabane yai maki cin fuska kin ce a,a. Wallahi Allah mama bashi bane kuma ba komai, ikon Allah inji maji ba komai kike wa kuka ba to may yakawo kukan? Mama yaya ne sai kuma nai shiru don, na tuna da zancen alkawarin da nayi bazan fadawa kowa ba. Hakali a tashe tace yaya yai maki may hankali a tashe take tambaya may yai maki Fatima ? Fada min mana nace may sadauki yai maki ne wai,? Taba ki yayi ko may ? Nace da sauri a,a mama don nagane may take nufi da tambayana tabaki yayi. To may yai maki nai shiru nace mama ba komai bane cewa yayi wai na faye yau shiyasa maza ke ganina . Sai naji tai ajiyan zuciya tare da dafa ni tace kyaleshi ai munyi maga in don zancen Usman ne ya fada min yaron ba mai gaskiya bane. Nace cikin kuka tau mama ta ce ki kwantar da hankali Allah zai kawo maki wani wanda yafi Kabir insha Allahu. Tace karbi wanan kayan daga cikin kayan lefen da ya aje ne na debo maki kema a matsayin naki tsaraban. Da sauri cikin girgiza kai nace mama a barshi wallahi ko kadan raina bai baci da rashin kawo min ba don ai yasaba kawo min. Au kyautana ne kuma baki bukata ko may na girgiza kaina da sauri na sa hannu na karbi kayan dogayen riguna matsu kyau da masifan tsada har guda hudu. Nace amma mama kaman kayan su yi yawa fa tace nifa na baki Fatima nace na gode mama.

Readers Also Read