Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 70

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 70

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 70: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 70. ****** ********* ****** Da yamma daya daga cikin rigunan nai…

3,337 words

****** ********* ****** Da yamma daya daga cikin rigunan nai kwaliya dashi kaman yadda suma su maryam shi suka saka sai dai nawa yafi nasu tsada da haduwa, nisa ba kusa ba. Sam ban san yana cikin falon ba nafito cikin dogon rigan mai maroon clour sai tsakiya a bude yake an yi mai kwalliya da wani silk dark blue da duwatsu har kasa, hannun rigan manya manya ne shara shara dashi . Kwaliyan yai matukar karbana fa kamshi turare na na white musk da ko yaushe shi nake shafawa a jikina da tufafina. Haka kawai ganin shi zaune yasa kirjina bugawa a lokaci guda yana zaune cikin shiga ta kamilan mutane. Masangalin kujera kawai na dafa nace ina wuni yaya ? Kamar kullun wanan yaudararen idon nashi ya watso min ya na kallona a fakaice, da su. Kai Bintu wanan hadaden rigan fa kuma maryam ke tambayana don bata san dashi ba. Nace daga mai kauna na, a takaice. Kan shi kawai ya girgiza don jin amsan dana ba maryam din a lokaci guda, wayancewa yayi don yasan inda magana ta dosa. Na kalli maryam nace akwai wani tambaya ne kuma anty ? Ai ni dama nasan da,wata a kasa tunda naga ba,a baki taki a fili ba nasan zance ya canza ke nan. Nace wanan kuma zargin ki ne anty ni uwata mai kaunata tabani shi don tasan nina dace dasu. Da sauri suka juya gurin Maji da idanuwan su suna mamaki wanan riga mai bala,in kyau yaya akayi tabani shi gasu. Maji bata bada fuskan tambayan ba balle su san gaskiyan maganan don haka sai kowa ya share zancen. Ganin yanayin shi duk a tsarge ya ke lokacin saboda yana ganin sai na fadawa mama zancen kwayoyin dana kwaso daga gurin shi. Yana zaune ya rafka uban tagumi sai sauraren zancen, kanne shi yakeyi ba tare da yai magana da kowa ba sai kace wanda aka aiko ma wani sakon tashin hankali. Daga inda mama take a zaune muka ji muryan ta tana cewa ku tashi ku bamu guri zanyi magana da yayan ku. Hakan yasa muka mike daya bayan daya muka koma daga cikin dakin mu. Shiko jin abinda mama ta fadi yasa shi saurin dago kan shi da sauri yasan ta faru takare kenan yanzu sai da munafukan yarinyar nan ta tseguntawa maji zancen nan aiko sai ball da yar iska gidan nan algunguma kowa ya huta. Tace Baba na magana nake son yi da kai akan Fatima, yace shike nan yar iska tafadi ashe. Ba karamin kokari yayi ba gurin gyara natsuwan shi tare da dan dagowa daga kujeran yana fuskantar uwar. Mama tace ina son ka fada min gaskiya may ya hada ka da Fatima dazun da rana tashigo gidan nan tana kuka? Yace maji ita may ta fada maki nayi mata da ta shigo? Kai ma kasan halin Fatima da zurfin ciki da kyat na samu ta dan fada min wai kace tana kwaso samari kala kala a gidan nan. Yanzu har wasu samari Fatima ke dasu ina bayan wancen da Allah baiyi auren su dashi ba sai wanan da kace baka amin ta dashi ba kuma ta daina nagani. A jiyan zuciya ya sauke yace ta rufani ke nan ashe ai nazaci bata da,wayo ne ? Tace tunda kai mata fada kuma taji banga abinda zaisa kuma ka kara matsa mata ba akan zancen. Murmushi yayi yace maji ni fa duk abinda nake mata a saboda ke nake matashi don tana karkashinki ne. Idan da a, wani dakin take mai zai kaini saka mata ido da daukan mataki a kan ta amma tunda bata son fada ai shike nan. Maji tace dakata malam yarinyar nan fa amana take a gurina ka sani amma irin yadda naga ka dauko tsangwama mata bazan lamunci hakan ba gaskiya. Yanzu irin cin fuskan da kai mata ka bawa kowa tsaraba a gidan nan amma ita ka hana mata kayi daidai ke nan Baba ? Amatsayinta amma a guri na ina duk abinda kaga naiwa yan uwanka ita ma ya dace kai mata tunda ni bani banbanta tsakanin su. Waya san ta hanyan da zata taimaka muna itama watarana shi mutum fa rana garw shi ta inda ba,ai tsanmani ba. Yace maji yin haka bada wani manufa nai mata hakan ba kawai dai dama alkawari nai mata cewa idan bata gayar da mutum bazan mata tsaraba ba. Tace wanan matsalar kace don ni na bude akwatin kayan lefen dake aje na zaba mata wanda ta dace da ita. Ya dago kai kamar zaiyi magana sai kuma yai shiru can yace ai shike nan ko? Idan kuma akwai abinda ya dace akara mata daga ciki sai abata suma su Amirah abasu man shafin da turare da sauran abubuwa suyi amfani dashi. Tunda ba wani abin kuma za,ayi da kayan ba yanzu ai, ko ? Kamar yaya ba wani abin za,ayi da kayan ba ka manta da maganan mahaufin ku ne da yace nan da wata daya ku fitar da matan da zaku aura. Murmushi yayi yace maji ni ina zani na nemo mata nan da wata daya hakkuri dai Baba zai yi muna har lokacin yayi. Mama tace wanan kuma maganan ku ne da mahaifin ku idan baka fitar va ai shi ya maka mata da kan shi. Ya zaro ido yace haba maji kamana za,ace za aiwa mata kuma ai ni yanzu na wuce wanan ko. Wancan ma da kukayi da farko ba,aji dadin shi ba balle yanzun ace za,a sake wani kuma again idan lokacin yi yayi ai za,ayi din ne maji. Ina ruwana ina zaune ni a dakina matsalan ku ne da mahaifin ku ni banda na cewa ai. Duk hiran da suke da uwan hankalin shi yana akan zancsn abinda ya faru da rana tsakani na dashi. Mama ta kwala muna kira tace ku fito tun dan uwan ku bai fita ku kara mashi godiya ya baku kayan kwaliyan dake cikin akwatinan shi gaba daya wai ku raba ku uku. Godiya mukai mashi sai dai yana kokarin ganin idona danake boyewa a bayan Amirah. Mikewa yayi don wayan da akai mashi yafita lokacin naji dadin sakewa sosai a falon.

****** ********* ****** Sannu sannu na dan sake jikina na koma normal na bar zancen komai a raina sadai kallon mai bisa ruwa nakewa sadauki doni na tsinke da lamarin shi yanzu. Maryam tafito tana tambayana na bata wani handout din muna chemistry na 200 level nace ta duba a cikin jakad litattafaina yana ciki don ina kitchen ina aiki. Zaro takardan da zatayi sai ganin roban wanan drugs din dana dauko a dakin yaya tayi. Saman gado ta zauna tana kallon maganin tare da karanta shi a fili ta furta drugs kuma a jakkan Bintu. Hankalin ta ya tashi sosai a kitchen ta samay ni tace Bintu zo nan ganin hankalin ta a tashe yake yasa ni bin bayan ta zuwa dakin mu. Sai da muka kai zaune ta zaro roban daga inda ta boye fuska a daure take ce min Bintu may ne ne wanan nagani a kayan ki? Cikin kura min ido bata ko kiftawa don son jin bayani daga gare ni cikin damuwa. Nace ba nawa bane anty nima dauko shi nayi a wani guri na boye shi a nan da kika gan shi. Bintu fada min gaskiya a ina kika dauko wanan roban in ba naki bane ? Na nisa nace wallahi anty ba nawa bane nagi maki kama da mai wanan halin daidai da rana daya ne ? Tace shi ya bani mamaki ai nake son sanin nawaye ? Nace na dauki alkawarin boye zancen anty don Allah kiyi hakkuri amma,wallahi ba nawa bane Allah. Sai naji tace na yaya sadauki ne ko ? Da sauri na kalle ta nace ni ban ce ba anty. Amma kin san zaman su haka a gurin ki hatsari ne babba kuwa a gare ki ? Yanzu dabanice nagan su akayan ki ba kuma nasan halinki may kike ganin zai faru ? Nace nayi kuskuren barin su a tare dani amma na aje su don sheda kawai. Tashi kiyi flushing din su yadda kikayi a ranan tun wani bai gani ba hankalin maji ya tashi. Yadda tace din haka nayi na zubar dasu a cikin toilet suka bi ruwa suka wuce. Nan na barta zaune tayi shiru tana tunanen dalilin da yasa na boye mata tasan cewa na yayan sune duk yadda akayi. Da dare da Bashar yazo ta samay shi yadda ya fahinci bata cikin hayacin ta ya sa shi matsa mata da tambaya may yake damun ta hakane wai ? Tace matsalan yayan mune yayana ina ganin kamar bai daina shaye shaye ba har yanzu. Da sauri yace, kai may kika gani ban tsan mani yana sha ba kuma har yanzu gaskiya. Tace koma may nene Bintu ta san komai sai dai tana boyewa ne, nan ta bashi labarin yadda mukayi da ita da rana. Ya nisa bayan yaji maganan ta yace tabsa tunda kikaga taki fadi akwai magana gaskiya amma yaya akayi ta samu wanan abin a gurin ta in ma nashi ne. Tace nima shi nake ta tunane nasan tayi hakane don farin cikin maji don kada hankalin ta ya kara tashi kuma ? Tace nima abinda na fhinta ke nan hakan take boyewa don kada aji hankalin shi ya tashi amma ba matsala gobe da safe zanzo na kaiku makaranta anan zan fito mata da zancen muji. Yadda suka tsara haka din ne kuwa da safe sai ga Bashar mun gani a jenction din gidan mu yana jiran mu. Muna shiga muka gaida shi yafara hanya sai dai tuki yake a hankali, sai naji yace malama Binta ya garin dai nace lafiya kalau yaya Bashar. Ya ce ranan sai mutumina ke fada mai ta,asan da kikai mashi da kayan shi ? Da sauri na dago kai na kalli maryam sai na dukar da kaina nai shiru bance mashi uffan ba. Yace Binta yaya akayi kika kwaso abubuwanan a gurin shi shiru nayi babu amsa. Yace look Binta ba boyo ki fada min komai nai maki alkawarin bazan fada mashi komai ba akai don hanyan da zamu ceto rayuwan shi nake son mu bida a cikin sauki. Nace shi may ya fada maka don nasan na daukan mashi alkawari bazan fadawa kowa ba wanan magana. Sai Bashar ya nisa tare da buvun sitiyarin motar shi yace ina ganin baki fahince mu bane kawai. Nace yaya Bashar kadai gane cewa nashine ne ko to abar maganan don Allah, kyau alkawari cikawa. To shike nan na fahince ki yanzu, amma don Allah yadda Allah ya hore maki gane irin halin rayuwan da yake shiga ina son muyi amfani da wanan daman naki guri gano abinda ke saka shi a irin wanan halaiyar. Sai yai kaman ya bari sai kuma ya koma ciki tsunbul dashi al,amari gaskiya akwai daure kai a cikin sa sosai. Nace nima na fahinci haka amma gaskiya ban tsan mani zan iya ci gaba da wanan aikin ba saboda yai min warning sosai akan mashi shishigi ga al,amarin shi. Zaki ya mana inji Bashar abinda nake so dake shine kamae yadda baki tsoron fada mashi gaskiya haka zaki daure ki ci gaba da fada mai a kai tsaye. Murmushi nayi nace anya yaya zan iya hakan kuwa yace kwarai kuwa Binta ai zaki fitar da tsoro ne ga komai ki kama aikin ki,amma fa kuma kin san aikin nason jan mutum a jiki sosai. Nace da sauri yaya zanhi in ja yaya sadauki a jiki mutumin da kullun yake cikin hattarana da tsangwama. Yai murmushi kafin yace wanan kuma,wani haline nashi nan dai ya fara fada min ga yadda zanyi akai nace to ba matsala zan gwada nagani amma idan naga da,wahala gaskiya bazan yi ba. Yace zakima iya tunda kina da hakkuri kawai ki dan sake dashi shine farko. Muna kaiwa school ya sauke mu tare da min fatan alheri nace Allah yasa muyi nasara dai.

****** ********* ****** Yana tsaye ya bada baya waya yakeyi kuma a handfree yasaka wayan nashi a lokacin. Magana yake da wata mace sai dai magan tankar fada sukeyi yake cewa na fada maki ni mace bata a gaba na yanzu. Don haka ki daina yaudaran kaki don baxan aure ki ba koma zanyi aure yanzu akwai qualities din abubuwan da nake so ga matar da zan aura ke kuma baki da ko daya daga cikin su so kima daina yaudaran kanki a kaina. Ban san may yarinyar tace ba sai ji nayi tace wanan kuma matsalar kine ni da kika gannin ban taba zina ba a rayuwa ta kuma akanko ba zan fara ba. Da sauri na juya don nashige ciki sai nai karo da dutse ina batun faduwa naji ya riko ni bai bar wayan ba kuma bai sake ni ba. Nace a kakausan murya sake min hannuna kaji malam, wani kallo ta watso min na ki shiga taitayinki kinji ko. Sai da ya gama wayan ya juyo gare ni yace ashe kuma banda sa ido harkin fara lebe ne kuma ? Cikin tsiwa nace, akan may zanyi labe Allah ha rabani da annaminan ci ni fita zanyi nagan ka kuma zan koma. Murmushi yayi yace idan ma baki taba ba ai yau gashi kinyi ko? Amma anyway zan baki bashin na yau don kin min alkawari a baya don haka nima ya kamata nai maki uzurin na yau. Nace aini ba don ka nayi ba don mama nayi amma ba saboda kai ba sake min hannuna na wuce. Yai dan murmushi kadan abinda bai saba yi min ba yace ba abinda yakamata kice ke nan ba Fatima kice dai kin boyeni don baki son ace ni din mashayi ne ko ? Amma ko banza dai ni koma maye aikin min alheri ko Fatima don haka nima zanso ace nadan yi maki ko na rana guda nane kamae yadda kikai min din. Cikin wani shu,umin murmushi yace min tafi sai kin jini nan gaba, nima, Na dan kalli hannuna da yai ja saboda riko da yasha a hannun shi nace mugu kawai ashe yajini yace may kikace da gudu na zura zuwa cikin gida kada ya kamani sai ganin mama nayi a gaba na tsaye.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,

ALLAH DUK WACCE TA KARANTA BATA BIYA BA KAINE SHEDA INA BINTA BASHI,,,,,

Zaune take duk abin duniya ya damay ta a ranta ga shi yanzu daga ita har dan ta sun zama abin magana a gari. Ko a gaban ta zataji mutane suna bayar da labari yadda ma ba,ayi abin ba haka za,a zake ana labarata shi. Kowa da,kalar abinda yake fadi a bakin shi ba dama yaron ya fita sai yara abokan wasan sbi su fara gudun shi kaman sunga dodo. Haka zai dawo gida yana kuka yana fadin abinda yara yan uwan shi sukai mashi. Abin duniya ya ishi mariya a ranta tai kuka har tagaji ta hakkura don kan ta babu wanda zata kai kukan ta gare shi. Gashi zaman gidan kawai takeyi tun lokacin da aka dawo da ita daga gidan su daya tura ta manyan suka zo suka bashi hakkuri. Ba don yaso ba ya hakkura da ita haka na amma zama takeyi ba abinda ke shiga tsakanin su. Koma cefane ne idan ya shigo dashi sai dai ya aje mata a kofan daki ba tare da yai magana ba. Idan kuma tana son wani abu sai dai ta tura yara su fada mashi abin da ake bukata a gidan. Ranan dai taga yana ta gyaran wani kangon dakin shi a zaton maria shine zai koma ciki don ya bar masu dakin su sai bata kawo komai a ran ta ba. Don dai tasan ba aure zaiyi ba mutumin da ko kudin cefane sai ya fita ya nemo masu abinda zasu ci. Ranan wani laraba ta zaune tana wanke wanke taji wasu mata su biyar sunyi mata sallama. Suka gaisa da ita sai suke fadin wani ne dakin da aka gyara daya daga cikin su tace, tana ganin wancan ne da ke da sabon siminti. Basu bi takanta ba suka nufi dakin suka shiga ciki suna dan dubawa anan suka barta tsaye da mamaki. Bata iya masu magana ba suka fita sai gasu da kaya suna shigowa dashi. Kasa daurewa maria tayi tace wai bayin Allah daga ina haka bakuce min komai ba kun kama shigo da kaya cikin gidan mutane. Dayar matar tace a,a shi mai gidan bai fada maki yai aure bane yau matar zata tare ma. Ai mu amarya muka kawo yanzun haka munzo gyaran dakine ma kagin anjima mu kawo ta. Allah ne ya taimaka maria bata fasa ihu a gaban su ba amma sai ta fada dakin ta can ta fasa abinta ita kadai tana fadin na,shiga uku yanzu da wani zanji halin da nake ciki ko da zancen kishiya kuma? Bata fito ba sai da taji fitan matan daga gidan mayagin ta ta dauko sai gidan su ga girkin da ta dora a saman wuta nan tabarshi ta fita. Da kuka ta samu uwar ta tana fada mata abinda ya samay ta nan uwar tashiga zagi tana fadin amma Atiku ya cika tsohon macuci wallahi. Yanzu da yake nan yana yawo kaman almajiri ashe har yana da kudin da zaiyi aure, bamu sani . Nan sukai ta kullawa ita da uwarta a tsakanin su har dare ya soma ta fito zuwa gida. Koda ta koma ta samu har girki ta ya kone wuta ya mutu don kan shi nan dai ta kwashe shi haka na don bazata iya girka wani ba yadda take ji a lokacin. Atiku na shigowa gida ta tare shi da masifa da jidali nan ya dakatar da ita yace. Maria ki shiga hankalin ki wallahi kada na bata maki rai a gidan nan kin dai san ina da haushin ki dama to ki iya kan ki dani wallahi ko ayita a akare a gidan nan don dama kin kai min ko ina wallahi. Nan ta shiga zage zage tana kiran shi macuci azzalumi dama ashe yana da kudi yake ce masu baida shi yanzun ina ya samu kudin aure. Yace wanan aure kikace dole na samo shi don naji dadin rayuwa na kuma duk mata ta shigo gidan nan kikace zaki daga muna hankali wallahi sai dai ki koma gidan ku kinji na fada maki mara mutun ci da tausayi kawai. Ke abinda kikai min a duniyan nan har kina da bakin magana don zan kara aure. Kuma ai dole na kara aure na samu wace zata kwantar min da hankali na wadda zanji dadi da sanyin rai a gurin ta. Ba irinki da kikai shekaru da shekaru kina gwada muna boni ni da diyana ba a gidan nan. Don tsaban iya cutan ki harda dan ciki kika zalunta dakanki da kanki kin mayar damu abin zunde da kwantance a gari saboda tsaban kwadayin ki. Yana fadin haka yai alwala ya fita, daga gidan ran shi a bace yana kutawa shi kadai. Bayan sallan magariba kaman masu jiran a idar da sallah sai ga yan kawo amarya da gudan su sun shigo gidan. A zaton maria za,a kawo mata amarya dakin ta irin na al,ada sai taga sabanin haka. Sai ma jin da tayi lokacin yaran ta suna cin abinci a,waje matan na gardama a tsakanin su cewa. Ko wanan ne akaiwa fyaden cikin su dayan tace karamin ne fa akace sai dayan tace a,a fa ance babban ne mai sayar da pure water uban ma bai ko san tana aza mashi tallah sai ranan da abin ya faru ya sani. Kai amma wanan matar ta cika azzaluman mace ita tajawa dan ta wanan bakin sunan haka har ya mutu ana kwatance dashi a gari. Wani irin zafi da radadi maria taji a ranta take ji kaman ta fito ta basu amsa amma kuma ita kadaice a gidan kada su taru su yi mata tsinanen duka don taga a tsaye suke su ma.

Readers Also Read