A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 72
A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 72: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 72. Ganin shi kawai sukayi da yammacin jumma,a ya diro garin nan…
1,125 words
Ganin shi kawai sukayi da yammacin jumma,a ya diro garin nan suka gaisa mama take tambayan shi yaya akayi kuma ya dawo ba yace suna da wasa wani sati ba sai satin sama zai dawo gida. Yace eh maji nadawo ne nai wani abu a garin kuma da akwai wasu takardu dana manta ban tafi dasu ba da zan tafi. Yakai wani lokaci a zaune baiga giccina ba hakan yada shi sanin cewa har lokacin ban dawo ba ke nan garin. Ya mike ya fita kaman wani mai jin kasala a lokacin, Bashar ya kira yazo idan an fito sallah su fita. Ranan Monday maryam tafito a cikin shirin ta zata shiga makaran ta,a waye ta samay shi ya fito daga gurin exercise . Sun gaisa yake tambayan ta ita wana har yanzu taki dawowa ba kun koma makaranta ba tace eh munyi waya da ita tace bata san ranan da zata dawo ba kila ma, Fuska a daure yace ina ne garin su? Tace, a yaya baka san garin su Bintu ba kai, duk zaman ta a gidan nan? Yace don Allah malama fara bani amsan tambayana kafin kiyi min halin ku na yan kasa tukun na tambaya cikin tambaya. Tace can rabah take nan dai tai mashi kwatancen yadda ake zuwa garin yace inda muka tafi gaisuwan wancan mutumin da tatashi aure kenan ya rasu ko tace mashi eh can ne ya amsa mata da ok good. Zaka tafi garin ne yaya ta tambaye shi tare da kallon fuskan shi yace ban sani ba tambayan ki kawai nayi. Sai batan kamar kwana biyu da tambayan maryam ranan da safe yace wa Bashar ya shirya zasu tafi wani dan kauye su dawo. Sam Bashar bai kawo komai ba a ran shi nan yazi ya dauke shi shi yaja mota suka tafi. Ban zuwa gidan kowa amma ranan haka kawai nace zan je na gaida kakanin mu kafin na tafi don saura kwana biyu na tafi. Mun fita gida da kaman awa biyu suka shigo garin wani mai faci bakin titi suka tambaya gidan dan Amo shayi akai masu kwantacen gida. Da farko da suka isa gidan yaso yai gardama ko banan ne gidan ba saboda ganin yadda gidan kaman ma yafi ko wani gida na uguwar lalacewa a shiyan. Sallama suka ce ai masu da maigidan yaron da suka tura yace kai mai gidan kan yanzu ba,a samun shi gida yana can gurin moli. Basu gane may yaro ke nufi yace yashiga yace wai bakine daga sokoto sun zo ganin Bintu. Mamana tanajin haka tace, Bintu bata nan tafita amma ace su waye yace ace yaron hjy ne yazo tafiya da ita. Jin haka yasa mama tace ace su shigo daga ciki ai su yan gidane nan ta tura yaron ya kirani gidan kakan nina, basu so shiga gidan ba amma dole suka shiga. Shi dai bashar sai kallon ikon Allah yakeyi kawai don abin ba mamaki ba daure mai kai yayi. Bin gidan yake da kallo da mamakin yadda dan adam ke rayuwa cikin wanan rubaben ginan haka da akoda yaushe yana iya rushewa. Bai san cewa shigina in har akwai mahaluki a cikin shi ba Allah na karewa yadda yaso. Tabarma mana ta shimfida masu daga dakin ta nan ma yai matukar mamaki wai dakin da ake rayuwane, acikin shi haka. Ruwa ta debo masu acijin wani kufin silver ta sabo ta kawo masu bashar ya karbi ruwan ya dan kora a cikin shi. Shikan bai san yaya zai iya kai wanan cup din a bakin shi ba gaskiya don tun bashar baisha ba yaji kaman yai amai. Bayan mama ta dan fita dauko masu abin fitara ne Bashar yace wallahi kasha ruwan nan don ba haka ake neman aure ba. Cikin tsawa yace Bashar you are very stupid wallahi. Neman auren wa kuma can sai dai idan kaine kazo neman auren ban sani ba don kai baka raina mata naga alaman haka ? May ye abin rainawa ga abinda mutum ke so a ran shi ? Shiru yayi don mama ta dawo a lokacin tana mika masu abin fitaran tana fadin kuyi hakkuei akwai zafi wallahi. Sai ga wata akuya tashigo nan ta hau saman tsadaddun takalman su ta sake mai fitsari a na shi. A hankali yace oho shit da ido yaiwa bashar din signal ya kalli kofa abinda akuya take mashi. Murmushin keta bashar ya sake mashi, yace don't mind my friend duk ciki ne ai. Lokacin na shigo gidan da mamakin ko su waye aka ce sun zo nemana a lokacin daga sokoto. Sam ban kawo cewa shine ba don sai ina zaton mamace ta turo wani ya dauke ni kila. Ina bullo daga kofa mukai arba dashi zaune cikin fararen shaddan shi yaci starch. Nai matukar mamakin ganin su a gidan mu dakin uwata musa ne ya hango akuyan tai fitsari akan takalmin dayan su ya shiga koran akuyan ya debo ruwa ya zubawa takalman. A hankali na tsaya daga kofa ina masu sannu da zuwa, duk na shiga rudewa da ganin su. Bashar yace min humm Bintu kinzo kinga mama shike nan kin manta da zancen an koma makaranta ko ? Nai dan murmushi nace ban man taba yaya kawai dai ban tashi dawowa bane a lokacin nan. Da sauri yaya sadauki yace sai yau she baki da hankali ne wai ana karatu zaki zo ki samu guri ki zaman ko a kauye. Ganin zai sake layi yasa Bashar tare da fadin yanzu dai mama tace muzo mu dauke ki yau din nan don an koma school tun ranan Monday kin sani kuma. A hankali nace yau din nan yaya yace eh haka ta bamu umurni shiyasa muka zo ai daukaki din. Nace ni gaskiya ban shirya ba fa sai dai idan na shirya zan dawo anytime. Kafin wanin mu yai magana sai mamana ke fadin may zaki shirya kuma ina kin yi wanki jiya kitashi kawai ku tafi tunda har kikaga hajiya ta aiko a dauke ki. Ban so ba haka na shirya zan bisu su suka fara fita yakawo kudi masu yawa yabata yace tayi hakkuri babu kudi a jikin shine. Sai da zantafi nace mama ki boye kudin nan kafin mijin ki ya dawo ya kwashe su kiba musa yakai maki gidan su kakale a boye maki su ku dan samu abincin abincin rana dashi. Nakawo sauran kudin dake hannuna sunkai dubu goma nace tace ga abinda aka bata. Mukai sallama dasu muka fara hanya ina baya sai tunane nakeyi kawai a raina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN KARANTA KO KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDAN MUNA BINKI BASHI,,,,
ALOKACIN MU KE,,,,