Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 73

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 73

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 73: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 73. Mun kama hanya sai hiran su suke shi da Bashar niko ina bayan…

3,884 words

Mun kama hanya sai hiran su suke shi da Bashar niko ina bayan mota zaune a takure cikin damuwa. Bashar ne daga inda yake zaune ya dan juyo yace min Bintu gaki kinyi shiru mana. Nai dan murmushi yake kawai nace ba komai yace ko kina son a sai wani abune? Kai kawai na girgiza mai nace idan mun kai wani kauye zan sai dan tsaraban da zan kai wasu mama kada naje masu hannu sake. Sai faman gudu yake shararawa da mu har sai da naji tsoron gudun da yake da mu nace komai nashi dai na muggai ne ko kashe mu yake son yi ne wai ? Kafin wani lokaci sai gashi mun fara hangen garin sokoto daga nisa mun da kara gaba nani ya taka burkin motan da karfi sai dana nan dan firgita bani ba har Bashar dake gaban mota sai da ya kalleshi. Muna nan zaune shiru ya bude mota yafita zuwa gefen da nake zaune ya bude marfin mota fuska a daure yace nafito ina fitowa ya mayar da marfin motan ya rufe . Ina tsaye jikin mota ya daro hannau shi guda saman kan mota dayan kuma ya sashi daga gefen kunkuruna sai dai mota ya dafa. Take naji cikina ya kada min fuskan shi a daure tamau yace ke dakata kiji kada kikaga nazo na dauko ki naji wanan zancen a gida ran ki zai baci sosai wallahi duk kika bari maji taji cewa nine nazo na dauko ki sai na bata maki fiye da tsanmanin ki. Nace baka son asani may yasa kazo ka dauke da ka barni mana har lokacin da na tashi dawow,,, Bakina ya murde dakarfi yace ke baki da kunya ko ina magana kina magana who is the master? Jin zafi a bakina yasa na dan zille na duka sai ya komane sai saman kirjin shi na fada. Da sauri na kara dagowa hakan yasa muka tsaya muna facing din juna face to face. Ya dan dade yana kallona sai ya kuta ya juya ya shiga mota yana fadin kinji warning din da nai maki wallahi duk naji zancen nan sai ranki ya baci dani wallahi. Na shiga mota idona yai ja kaman zanyi kuka ina cewa ni wallahi wanan cin zalin ya isheni don anfika karfi sai a dinga cuta maka kawai. May kike fadi yace sai lokacin Bashar dake muna dariya yace haba ka barta hakana mana please? Ya tayar da mota muka ci gaba da tafiya, bai tsaya ba sai wani guri da ake sayar da kayan irin na kauye na ciye ciye. Nan suka fita sai gasu da sayayan kayan tsaraba mai yawa irin na kauye ana lodawa a buth din motan. Muka bar gurin nidai ban san may damay suka sayo ba a lokacin muna shiga gari a play over ya samu guri ya tsaya. Can ya tare wani mai Napep yake cewa, ya kaini gida tare da mai kwatancen inda zai kaini, yabiya shi kudin shi nan mutumin ya loda kayana a cikin motan shi. Su mama suna zaune sai ganina kawai sukayi a bazata kawai nan suka shiga cewa la Bintu ashe kina hanya ? Yaran da suka shigo min da kaya na diban masu rake gyada dafafa na basu suna ta jin dadi suka fita. Naje gurin mama na rusunna na gaida ita cikin jin dadi da gani tace Fatima shike nan kinje kin samu guri kin share ai har ina batun binki ne da banga kin dawo satin nan ba. Nai murmushi nace mama ai zan dawo tunda an koma makaranta, tace yayasu wajen mamaki suna lafiya ko nace duk lafiya kalau mama suna gaida ku. Ta kalli tsaraban da nazo dashi tace Fatima wanga tsaraba haka mai yawa fa dariya kawai nayi a raina nace aikin mahaukaci ne. Nan muka shiga hira dasu anty suna min sheri wai naje naga mama na kasa dawowa. Sadauki bai shigo ba sai da yamma lokacin ina cikin daki maryam ke fada mai Bintu fa ta dawo yaya. Yace taga daman dawowa ke nan ta samu kauye ta zauna kaman wani birni can. Tasa min kira na fito sai ganin shi nayi a zaune nace yaya ina wuni ? Ya amsa a kasalance da lafiya? Kinga daman dawowa ke nan ko ? Murmushi kawai nayi mashi na karasa gurin maryam nace gani anty tace dama yaya na kiraki ku gaisa ta fadi tana dariya. Na juya kawai na koma ciki, ina gyara kayana ban fito ba sai bayan magariba don nasan lokacin bai nan. Ina cin abinci kawai sai gashi ya fado falon saudaya na daga kai na kalle shi ban kara ba. Maryam ce take ce mai yaya adebo ma tsaran Bintu na kauye yace kai maryam kayan kauye ai sai yan kauye. Daga inda nake zaune nace, muko dashi mukafi wayau kayan kauyen don yafi bada lafiya ai. Yace ke yanzu lafiya kike ke nan a haka kamar a karya ki? Kafin nai magana maryam tace a,a yaya aiko yanzu Bintu ta yi kiba in kuma tafi haka ai bata kyau. Ni wallahi duk da mace ce amma nafi son mace haka silynder da ita sharp din mutum duk dress din da yayi sai yai ma mutum kyau. Ga Bintu kuma dagowa ce ga wanan uban farin nata kamar yar larabawa da ita. Kai maryam don Allah ya isa haka kada kisa kan Bintu ya fashe wanan dadin haka inji Amirah? Maryam tace wallahi anty da har haushi nake ji idan mun fita da Bintu yadda matane ke yabata amma yanzu nima nasan gaskiya suke fadi. Watarana fa muna alwala a makaranta wata na ganin gashin Bintu ta yanka salati wai ikon Allah yanzun ke kina da wanan gashin haka kike faman boyon shi ga hijjab kullun ? Sai lokacin yaya yai magana yace, shiyasa ta bude ai don su gani su yi magana. Nace kai haba yaya haka kawai zan bude kaina wa nake son ya gani kuma? Ke kika sani dai tunda an gani an yaba din ai yadda kike son agani din. Shiru nayi wani takaici ya kumay ni a raina nace ni wallahi wanan ai zargine kawai? Yace nakara jin kin bude wani part dinki a jikin ki sai na bata maki rai gidan nan. Dan Allah yaya ji yadda maryam ma take wani zuzuta fatima wallahi sai kace wata sarauniyar kyau can. Su dai suka sani shedanun yara ne wallahi kin gan su nan shiya sa duk suka fita sai maza sun biyo su don suke kiran su. Wanan sheri da may yai kama saboda Allah haba dai yaya kana biyewa Anty Amirah tana zuga ka kawai yaya. Ni dai wani haushi da takaici bai bari na ko iya dago kaina ba a lokacin don irin takaicin da nakeji. Amirah tace maza kan na zuwa har ana masu yanga da kuri kafin a dauki wayan su tafadi cikin dariya. Kai haba anty ai wanan sheri ne kawai kike kulla muna gar wasu maza muke kulawa mu don Allah, Baiyi magana sai shirun da yayi can ya dan bude abincin da aka aje mai agaban shi ya fara ci nikan na mike na shige dakin mu. Amirah tace kibar gudu ai don kada a ci gaba da zancen zaki shige ko? Shima bai bi ta kaina ba yaci abincin shi ya tafi abin shi kawai. Ban san yaya akayi Bashar ya fadawa Anty maryam su suka daukoni daga kauye ba ranan da na dawo. Amirah na falo ta dunkule saman kujera tana chatting maryam na zaune tana gyaran farcen ta. Maji na zaune tana gyaran wayan ta da ke hannun ta ruwa ya dan zubo mashi da take sha. Nafito da plate a hannu na da abinci zanci na zauna na fara ci ban dade ba sai ji nayi maryam tace. A humm wai ashe ke Bintu yaya sadauki ne yaje har kauye ya dauko ki da zaki dawo? Da sauri na dago kaina kalle ta cikin mamaki sai banyi magana ba don ina mamakin ina taji wanan zancen ita. Amirah tace ke kan Maryam wallahi uwar sheri ne wata Bintu ne can yaya zai je har kauye daukowa? Maryam tace au kina nufin karya nakeyi ke nan ko,ai ga Bintu nan shi in ba shi yaje tun daga nan ya daukota ba wallahi. Kin ma raina yaya Allah shine zai tafi har kauyen nan mai uban nisa akan Bintu. Don in nunawa Anty Amira na kai nace to anty maryam don ya dauko ni wani abune halan ni nace yazo ? Ni da ban ko shirya dawowa ba amma yasa ni tasowa ba shiri saboda zuwan shi. Bintu da gaske yaya ya dauko ki wai ko may? Nace su sukaje sukazo dani ban ko shirya ba amma ya matsa min wallahi saida mama tace na shirya su zo dani. O lalai ma yayana shine yai pretending kamar ma bai san komai ba a ranan da ta dawo. Bake ne ba idan ana magana akan yaya da Bintu sai ki wani kakarw ki hana a fadi ni dai ban kara magana ba ina mamakin yadda maryam taji zancen ga kunya mama duk ya kamani lokaci guda. Nace dama,na,sani kawai tun ranan in fada mata tare dasu nadawo da yafi min yanzu gashi anji ko. Amirah bata bar zancen ba sai da ya shigo gida har kowa ya manta ashe ita abin yana ranta. Yashigo cikin yar fara,an shi bayan ya zube saman kujera yake, cewa maji yau naga wanan kawar taki da tun muna tsohon gida kuke tare. Maji ta dago kai tace wata kawana kuma ke nan yace ko yar Rabin isha ake ce mata ba ? Au kace uwar goyon ka dai ai itace tai giyon ka lokacin tana amarya a unguwar na mu da anyi maka wanka sai gidan ta. A ina kagan ta yace can wani unguwa naje duba wani tsohon gida da akai min talla tun kwanaki ban samu zuwa ba sai yau din nan. Naji ance wai ba sadauki maji bane nan yace wallahi ban gane taba maji ta tsufa duk ta lalace sosai dagani tana cikin wahala. Tace Allah sarki, tun lokacin da mijin ta ya dauke ta suka koma kauye ban kara jin duriyan taba. Yace lalai na gan ta yau kan maji tace inji ka samu abinda ka bata ? Yace dubu goma kawai na samu na bata banda kudi ga aljihuna a lokacin amma nai mata kwatancen gidan nan ai tace zata zo. Yauwa yayana wai ashe kai ka dauko Bintu daga kauyen su ranan da ta dawo ? Da sauri ya daure fuskan shi kaman bashi ke fara,a ba yan dakikoki kadan da suka wuce. Yaba ta amsa da eh mu muka dauko ta wani abin ne akayi kuma ? Inda nake ya kalla fuska a daure nima na daure nawa tare da dukar da kaina kasa. Amirah tace da nace karyanr wallahi da maryam ke fadi dazun ban yarda ba wallahi. Yace naga bata da niyan dawowa school ne gashi ankoma shiyada naje nazo da ita ai. Daga haka yai shiru maji najin su batace kallaba ko wanan lokacin ban da cewa da tayi Allah yasa yar Rabi dai tazo gidan nan wallahi na dade ina tuna ta sosai wallahi. Mikewa yayi yana cewa zan shiga daki maji duk nagaji yau wallahi zan dan huta. Yana fita na sauke ajiyan zuciya a hankali don nasan nawa ya samay ni kuma tunda yai min gargadi kada na fadi. Ban taba sanin yaya yana da nombana ba sai yau ina daki ina shirin sallah naji wayana na ruri. Ina dauka naji yace ke ashe baki da hankali gulman ki hae yakai can ban sani ba dana ce kada ki fadi sai da gulman ki yakai kika fadawa maryam abinda na hana ki. Na marairaice nace wallahi Allah yaya bani na fada mata ba ban san inda tajiba wallahi ko. Sai naji ya kashe wayan dip nabi wayan da kallon mamaki tare da sauke ajiyan zuciya. Kwanana biyu da dawowa ya sa kai ya tafi zuwa kashen waje gurin wasan su don can yafi dawowa a jike idan ya tafi. Tafiyan shi, na dawo normal kullun ina cikin yan uwana muna mu,amulan mu yadda muka saba dasu. Bamu da matsalan komai a gidan yanzu don gaskiya Alhamdullahi, mota kowan su na dashi, haka ma sutura duk muna dasu matsu tsada, waya kowacen mu babba take riko a hannun ta duk shi ta saya muna, gurin abinci sai wanda ran mu yake so zamuci, ga uwa uba makka da muka tafi kowan mu da hakoran makka a bakinta irin na adon mata yana walkiya. Matsala guda yanzu shine matsalan gidan su maji na fitina a tsakani kullun ga Nafisa yanzun abinta yai kamari sosai gwanin ban tausayi da ita. Idan iskancin ta ya ishi Baba haka zaifito tsakar gida yai masu tas ita xa uwarta, sai in Umma ta gajine takan tanka itama tace. Ba kan diyana aka fara lalacewa ba ai a gidan kan suyi ai wasu sunyi kuma nasan hannu aka samin suka lalace. Don haka koma waye na sani kada maishi yaga kamar yaci bulus wallahi indai nice bashi akaci wallahi. Don sheri saboda mutum yaga nashi ya lalace sai ya mayar da dan kowa lalatace a gida. Badai na su kawai duniya zata fada ba sai an fadi na mutum tukun. Mummy tafito daga dakin ta tace kai amma dai hjy Atika tauhidi bai sheki ba wallahi. Ashe shi wanda kike nufi hannu aka saka mashi ke nan a lokacin yazama haka bamu sani ba ko sai yanzu da yakawo akanki ne kika san haka ne. Kada ki manta iskancin namiji ado ne a gare shi duk yadda ya iya lalacewa bai rasa macen aure a duniya itako diya mace fa ? Ke tsohuwar kilakiya kada ki manta mun san komai wallahi, nan kikagama tambadewan ki ba mashinshine in bashi alhajin dayazo yatara ba ya dauko muna masifa a gida. Kin ishe mu kin ishi diyan mu wai ke adole ga yar bariki to anriga ki indai barikine a gidan nan don gidan kikazo. A haka cure ake barikin don shifa bariki iyawa ne dama don kinga ashe nafiki iyawa ke nan tunda kika fadi. Dariya mummy tayi tace wai a haka ashe ke bariki kikeyi ke nan ba,a sani ba ko ? Nafisa dake daki tayi tatil da ita ta leko tana fadin Umma rabu da wanan gajar matan mai muna mazuru muna shaho. A,,,, mu,,mun,,san komai,,,wallahi, ikon Allah ai gara kija yar mayer yar ki daki kafin wani ya shigo yaga wanga tabaran nata a fita damu waje. Haushi da takaici ya kama umma da Nafisa ta bude bbaki zatai magana ta wani daka mata tsawa tace don Allah rufa muna baki kinji kin jawa mutum gori a gida kawai. Haka sukan ta faman jidalin su ita da mummy da bata iya hakkuri idan tana habaicin ta. Maji dai bata kan tanka mata sai dai tai shiru kawai tace tabar ma Allah kuma Allah ya tsare mata zurian ta. Irin wanan jidalin yakan tayar wa Baba da ciwon shi wani lokaci sai ya kwanta asibiti saboda bakin ciki dake damun shi gashi duk wanda ya sanshi sai yai mashi korafi akan Nafisa abinda takeyi baida kyau a gari. Ranan dai ya tara iyalin shi yai masu fada sosai yace da mazan da suka isa aure da matan kowa ya fiddo da miji da mata aure duk aurar dasu zaiyi gaba daya kowa ya huta a gidan dasu. Yace kai Imirah na fada maka ka kawo mace kafin na zaba ma da kaina wallahi kaji na fada maka. Ya juya gurin mama Asiya yace danki yace min muje gidan yarinyar da yake so aiyi zancen auren su. Mama tace ba dai wanan yar iskan ba da ta tsohe mashi ga shekaru da komai yace shi din maye inba halin su daya ba a ina suka hadu da ita? Tunda yace ita yake so kuma shi zai zauna da abin shi ke ina ruwan ki da zancen su ne wai? Zan tura iyayyen shi suje nema mashi auren ta nan dagobe insha Allahu. Mama ta tubure tana fada tana zagin Ahmad tace badai ya auri wanan karuwan yarinyar ba agidan nan. Baba yace ai sai mu zuba mu gani tunda kece zaki zauna mashi da ita ai kina bani mamaki wallahi. Ki fara tambayan danki yaya ya hadu da ita kafin ki fara zagin yar mutane haka nan. Ya juya gurin mamana yace idan danki ya dawo ina son ko fada mashi sakona yafito da mata na da karshen sabon wata duk aure zasuyi muddin ina raye a duniyan nan. Mama tace shi sadauki yana da mata kuma na yaba da tarbiyan ta kwarai yace mashs Allahu haka nake son ji dama. Duk gurin sun so sanin wacece matar don su sani ko yar gidan maikudine ko wani kusan gwaunati can. Don kada yazo yafi diyan su zaben yar gidan mai kudi azo ana mazu feleke a gida. Haka dai akabar falon kowa da abinda ke cikin ranshi manya da yaran su na gidan da aka kira. Ina daki a zaune suka shigo kowa sai gunaguni takeyi maji dai ta shige tabar mu nan zaune muna hira. Amirah ce takira yayan ta da waya take fada mashi hukuncin da Baba ya yanke akan su. Yai dariya yace Amirah kice mun kusa shan buki ke nan yan kanne na sun kusa zama amare. Tace bamu ba ai harku yaya don yace wa su Maji wallahi duk fito da matan aure a aura maku dariya yai mata kawai. Tace yaya kai kaga abin dariya ma ni wallahi duk na rude na rasa may nake ciki ma aallahi. Yace ina samarinki ba sai ki fitar da daya ba kawai a zarga maki dashi, tace yaya ni duk fa basuyi min bane na ma rasa wa zan tsayar a cikin su ni wallahi komai ma ya jagule min yayana. Yai dan murmushi yace kibari zandawo month end sai mu san abin yi tace ni dai da Baba zai min hakkuri ne har faba dayafi min. Yace No Amirah ki godewa Allah fa gaki har kin gama karatunki ma may kuma kioe so yanzu inba aure ba kuma. Tace yaya ke nan bazaka bashi hakkuri ba har zuwa gaba yace wa ni rufa min asiri please bari mu rabu lafiya da Baba don Alla dai. Tace yaya naji maji tace wa Baba wai kai kana da mata shine mu bamu san wanan lucky girl din ba da tai wanan sa,an haka? Yace No,No Amira maji ta dai fadawa Baba hakane kawai don ta kare ni gare shi ammani for nowa ban da kowa a kasa tukun na. A kwai da wata wadda nake son fada masu akan ta don yar kasar ghana ce sai dai akwai matsala gaskiya. Matsala kuma yaya ? Yace eh don ba musulma bace Christian ce ita sunan ta Linda. Yaya kafira kuma ? Yace eh amma ai idan munyi aure zata musulun ta ne insha Allahu. Tace ashe kuwa akwai case ke nan nasan maji da wuya ta yarda gaskiya don yadda bata kaunan kafirai ko kadan. Ni dai daka jaye zancen ko zaka samu wata nan gaba ku shirya yar asali yar gari. Yace ban ma san ni may yasa suke son mutum yai aure bane yanzu wallahi. Amirah tace kasan maji kance ita dai muyi aure don yanzu Life is to short knowadays. Hakane kuma fa Amirah gaskiyan maji ne rayuwan yanzu dan kalilan ne gaskiya. Yace ni nasan zamu kwasa da parents din mu dama both don ko ita parents din ta takw ji yanzu. Shiyasa tace zata zo Nigeria sai muyi auren mu kawai sai daga baya iyayyen ta su sani. Amma ban yarda da wanan ba ni don ban son ni ai min haka gaskiya. Tace yaya ai matsala shine yaran da zaku haifa zasu zama ruwa biyu ke nan fa? Yace kai Amirah akwaiki da shirmay wallahi ni fa ban ko tunanen yin aure yanzu balle wasu iyali can . Yaya kadai yi tunane kafin kazo da maganan nan gida don za,a samu matsala sosai wallahi. Ki bari kawai idan nazo sai mu san yadda zamu bullo wa zancen cikin sauki haka zaifi ai. Tace ni wallahi maji nakejiwa akan zancen nan don nasan halinta akan abinda bai mata ba. Yace ke dai kawai kiyi shiru ban son kowa ya ji wanan zancen a bakin ki sai nazo tace shike nan . Nan sukai sallama,dashi yace ta kwantar da hankalin ta yana nan zuwa month end insha Allahu. Suna gama waya gulma yaci Amirah ta kasa barin zancen a ranta tace wata sabuwa wai yaya kafira zai aura fa ashe? Muna hada baki da maryam gurin cewa kafirah fa kika ce antu ? Tace wallahi yanzu yake fada min wallahi wai yar kasar ghana ce ita Sunan wai ko Linda ? Nace wayaga Leather ke nan kuma ? Kai baima yuyuwa gaskiya kafira arniya mai fitsari a tsaye zai ce zai dauko muna. Muji da wani irin gori da habaici gidan nan kuma ba,a gama wani ba har yau a fada wani ke nan kuma. Ai da su Umma an samu abin dariya ke nan a gidan nan wallahi don shi za,a aza a faifai kuma ana talla lungu lungu inji maryam ke ta sababi haka. Tace ni wallahi har girman shi ya zube min wallahi arniya fa Allah tsare mu da ita a gidan nan. Diyan shi sai su girma suma su zama kafirai ke nan ko ? Nace to shine daidai daahi don shima ai zuben yare ne gare shi baka taba ganin yaya kace mai dan hausawa ne kullun yana cikin kananan kaya irin nasu. Ke Bintu inji Amirah yaya din ne mai zubin arna kuma? Nace rufa min asiri anty kada yajini nawa ya samay ni a gidan nan kuma . Maryann tace na rasa may yasa mafi yawan yan kwallo suke auren diyan kafirai wallahi. A ji anty marayam fa ba,a cikin su suke ba suna ganin su kullun may zai hanasu fadawa tarkon su. Shine ai tunda dasu suke mu,amula can suna ganin su fa ko yaushe inji Amirah. Sai da muka watse ne zancen ya tsaya min a rai na nace cikin zuciya na ai dama muguntan mutum ke cin shi. Yaya za,a kana dan musulmai kace arniya zaka aura a haka ma yaya aka iya dakai balai ka auro kafira mara sallah kuma. Wanan kan sai yadda Allah yayi dashi kan don ba ranan shiryuwa gare shi ke nan kuma. Ai su gasa junan su da mugun hali sune ma daidai da halin shi, ai tunda shi yace shi mugu ne su karata, can wallahi. Maji suna waya take ce mai ka sayo kayan da aka taba a cikin kayan lefen ka don a cika. Yace cikin murmushi maji ai yanzu angama yayin su kawai a rabawa yaran nan sai na hado wasu kawai amma kada a taba gold din don akwai wanda na sayo da tsada tun lokacin. Mani tace zan dai zabi na kwarai na aje idan ka kawo sai akara ciki kawai yace duk yadda akayi maji shike nan insha Allahu idan zan dawo zanzo dasu din. Sukai sallama tana mashi fatan alheri da saka mashi albarka tana rokon Allah ya tsare mata shi ya shirya su baki dayan su.

Readers Also Read