Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 77

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 77

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 77: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 77. ****** ********* ****** Tun ranan da akai zancen naji ban kara…

1,922 words

****** ********* ****** Tun ranan da akai zancen naji ban kara ganin shi bani haka nake ba walwala tare dani ko kadan yanzun ma idan na dawo daga school ban zama a falo ina dakin mu. Don ni idan da hali badon na gudu mama tace ban mata diyyauci ba da na gudu daga gidan gaba daya. Shima haka sadauki bai shigo ba gidan tun ranan da Baba yai mashi magana. Haka ya gaji da fushin shi ga kiran da Amirah ke damun shi dashi tana tambayan shi ko yai tafiyane bata ga ya shigo ba don ita batasan dawan garin ba. Maryam bata fada mata ba don ta fahinci Amirah bata kaunan hadi tsakanina da yayan ta don ita a ganin ta yayan ta yafi karfi wata Bintu can yar kauye can. Don idan maryam na magana tana min sheri kan yaya Anty Amirah bata iya boye kin da take wa hakan a zuciyar ta. Tashiga fada ke nan da maryam tana cewa kefa baki da wayyo don Allah may ye kuma na wanan magana ba dadi ina yaya zai kai wata Bintu can kuma haka. Ina gani maryam din tagane zuciyar yar uwar ta ne yasa ta ki fada mata komai akan halin da ake ciki. Mun tafito zamu school muka ganshi tsaye a kofan gida shi da wani mutum da gani dai mutumin ya girmay shi sosai. Ina ganin shi na dukar da kaina kasa ban yarda na kalli inda suke ba inajin maryam tana gaida shi ni kan ban tsaya ba na wuce abina. Sai dai shi muna fitowa idon shi akan mu don yana facing din hanyar fitowa daga cikin gida. Ya ramay ya dan fada kadan sai dai ba kowane zai gane hakan ba sai wanda ya sanshi sosai zai iya gane hakan. Ina tsaye tazo da motan ta ta dauke ni muka fara hanya, sai da muka dan yi nisa take cewa Bintu nace na,am anty. Mayasa baki gaida yaya ba ? Shiru nayi ba amsa tace indan kina haka maji bazata ji dadi ba gaskiya na fada maki ki nuna bakomai a zuciyar ki haka zai sa tafitar da zargin komai a kan ki. Nace anty ni wallahi ban son ganin shi ma yanzu bakiji yadda nake jiba a halin yanzu dana gan shi a zuciyata. Kada ki damu insha Allahu komai zai zama normal amma sai inkin bi shawara na fa. Don haka dakikeyi kin san yafi wayo zai iya hada ki da maji laifin ya koma akanki don haka ki gyara halinki tun wuri har inkina son kanki da lafiya. Ban tanka mata ba shiru nayi tare da kwantar da kaina ga glass din motan ta kawai. Can tace dama ina son indan mun tashi daga makaranta na fara koya maki mota. Da sauri na dago kai ina kallon ta nace, mota anty ni ina zan samu mota kuma? Dariya ta kyalkyale dashi tace kin san abin Allah ne yar uwa da zakice haka? Muna wucewa ya shiga gida bayan bakon shi ya wuce daga mamane sai Amirah zaune a falo suna karyawa a lokacin. Amirah tana ganin shi take cewa kai yayana har zan kai cigiya da sanarwa gidan redio da talabijin a kan ka. C U yace an fada maki ni raggone da zan bace ko ni bakauye ne da zanbace maku? Ya juya gurin mama yace ina kwana maji cikin dukar da kan shi yake gaishe ta. Ka gama fushin ne dakakeyi halan mara hankali kawai? Fushi kuma maji akan may zanyi fushi da abinda kike so akaina ? O nice ma mai so bakai ba ke nan ko mara tunane kawai, dariya yayi don zagin da maji ke mai bai san dalilin shi abugi mutum kuma a hanashi kuka ke nan yace a ran shi. Zama yayi tare da cewa bani breakfast dina Amirah ya fadi Amirah dake masu kallon mamaki bata fahinci komai ba a fadan tace. Yayana may kuma kaiwa maji hakane wai? Yace wallahi ban sani ba kaunata kawai dai maji na son min fada ne don taga ban shigo ba kwana biyu ni kuma aikine yai min yawa. Amirah tashige kitchen ta hado mashi abin karyawa tafito koda tafito ta samu maji na fadin. Kai akwai gatan da za,ai ma dayafi na daga kayi arziki ka samu yarinta gari yar arziki zata rufa maka asiri daga shi har Amirah kallon maji sukeyi don jin abinda ta fadi a lokacin tace eh ba rufa maka asiri zatayi ba may zatayi, kai may ya saura a jikin ban da ragowan maye sai ball. Yace maji nine yarinyar nan zata rufawa asiri ko zan rufa mata dai kece kike ganina haka maji amma ai duniya ta san ba abin banza nake ba yanzu. Wallahi maji inkina fadi haka a gaban ta dadi zataji ta raina ni don bata da kunya Allah. To ubana sai ka rufe min baki tunda kakawo karfi yanzu ka wuce fadana yace ni bance maji cikin dariya duk yana kokari yaga ta sauko daga fushin ta. Maji wai wata yarinya ta ki ka yiwa yayana sababi a kan tana haka? Cikin bacin rai ta dago tace mata Fatima mana ko da me ya fita oho? Itama Fatima in ba tauye tan danayi bata iya musa min ba mitakai dashi haka ba makari. Maji mi yayana zaiyi da Bintu kuma yar kauye da ita ba asali ga mata yan asali da yawa a cikin gari. Da may yahita da zakice haka, nice hwada min damay hita, ? Shi har wani asali yakaso yabar kyau ne tun wurin wanka ai yanzu ya makara da wanan ko? Da mamaki furcin mahaifiyan shi ya dago kai yana kallon ta sai abinci yake cusawa a cikin shi kaman dolle yake ci. Amma gaskiya maji kaman mara galihu zakice wai da Bintu zaki hada shi Bintu may can don Allah dai Amirah ta fadi haka cikin yanayin bacin rai. Walle Amira kihita min ga ido tun banci kaniyaki ba gidan ke ko kwatan Fatima kin kaine asali ne mi ake bukata ga asalin ba uwa da uba ba. Hwada min wane ta rasa daga ciki? Ko shi arzikin ga dakika gani Allah ya bashi kikawa katobara, haka. Ita ke san inda Allah zai aje tane halan ? Nikkara jin keyi wani magana mara dadi akan Fatima walle saina lahira yahiki jin dadi a gidan nan marasa ta ido kawai. Amirah tahau ta cika ranta ya baci ta kalli dan uwanta hadade guy ye haka son kowa kin wanda ya rasa amma ace ga Bintu yar tallakawa zai kare. Sai dai ba dama ta muda ko tak yadda uwarsu hau tasan yanzu nata na samun ta. Bai jima zaune ba yamike yana fadin shi zai fita, maji bata tanka mashi ba don haushi. Mun dawo gida a gajiye don an kusa fara kiran magariba a lokacin saboda huturu yayi. Amirah ce a falo, zaune ina shigowa naga wani ir8n kallon banza da wulakancin da tai min. Take nasha jinin jikina da zargin akwai wani abu bani ba har Maryam sai da ta tsargu . Mun shiga saida mukai sallah muka fito maryam ta fara fitowa bata dade ba nafito nima falon. Zama nayi tare da cewa anty Amira an fara film din end of love ne? Kamar batajini ba ta kyaleni maryam tace min yanzu za,a fara time yayi ai. Can taja tsaki tace dama kwadai ya kawo mutum ai don kwadayin tsiya abi an asarice muna uwa da tsafi sai yadda akayi muna da ita. Komai tsafun mutum dai wallahi sai ya bar mu kuma sai ya bar gidan nan don yawan kwadai ma har diyan mutum ba,a bari ba. Ke dawa ye kuma Anty inji maryam, ke tambayan ta cikin kallin fuskan ta. Ke dalla kyaleni da takaicin daka damuna yanzu don kwadai sai a asirce muna uwa tasa dan ta ya tillatawa kan shi wata gaja can mara asali. Kai amma anty Amirah na raina maki wallahi, wanga magana kuma ina ya fito maki haka da girman ki. Shi yaya din yace maki lakaka mashi ita akayi kan dole ko wa ya fada maki ? Maryam kifita idona wallahi kafin na bata maki rai a gidan nan don naga ke kina ganin kin girma wawiya kawai da batasan ciwon kan ta ba. Kasa hakkuri nayi nace Anty Amirah kamar yadda kike gani an lakakawa yaya sadauki ni haka nima aka lakaka min shi. Don ni yaya sadauki baiko cikin irin namijin da so na aura a,rayuwa na, don kwata kwata baya burgeni. Shi kuma asali da kike nufin bandashi uwane banda ko uba, bski fini uwa ba baki fini uba ba. Tsafi kuma ni bamu san shi ba a gidan mu a gidan ku nazo naga a na tsafi. Aiko tayo kaina wai zata mare ni maryam ta shiga tsakanin mu tace wallahi baki bugun ta don amsan maganan ki tabaki. Jin hayaniya yasa mama fitowa ta samay mu tana tambayan basin may yafaru kuma mayye haka wai ? Nan maryam ke dada mata abinda ya faru tsakanin mu da amsan da na bata. Tace Fatima shiyasa nake son ki don baki shayin kowa gurin fadin gaskiya. Wawiya kawai sakariya kinga har tabar ganin girma ki ta baki amsa ba yau ba nake ganin take taken ki kan Fatima gidan nan. Uba kika fita ko uwa ki fada min nace ? Gurin ubanki ko uwarki tazo maula kin taba jin Fatima ta roki wani abu a gidan nan duk zaman ta damu. Ku arziki yake rudi har ya rufe maki ido kika manta da Allah, da tazo gidan nan gurina may nake dashi. Shiru Amirah tayi karshe bata tsaya falon ba ta tashi fuuuu ta shige ciki can ta kira sadauki ta fada mai abinda ke faruwa a gidan yadda maji tai mata.

****** ********* ****** Ranan bamu zuwa school misalin sha biyu da rabi na rana maryam na baya tana wanki mama tana dakin ta tana barci. Sai ganin mutum nayi tsaye a kaina ban san shigowan shi falon ba sai da na gan shi tsaye a kaina. Ya nayi yana dan waige waige kamar mara gaskiya yace cikin daure fuskan shi ke jinan. Na dago na kalle shi saudaya na dukar da kaina yace wallahi duk kika sake kika yarda har maganan maji ya zama gaskiya a kan mu sai na halakaki garin nan. Mara mutunci kawai banza dake ina mai shawartan ki da kiyi maza maza ki sanarwa maji baki son wanan hadin kema. Jiki dan Allah ko na rasa mace a duniya may zanyi da kucakar mace mara fasali irin ki. Duk da zagin ya bata min rai sai nai murmushi a fili nace amma kaima kana da bakin fada mata ko don naga kaman yan maye basu da ta ido kaga kaine daidai ka fada mata idan kayo mayen ka. Ni kasan lafiyata kalau don haka ina da kunya da daraja ba zan iya kallon idon mama na fada mata ido da ido don ban da kuya ba wai ban son dan ta gudan jinin ta. Amma kaika nasan zaka iya tunda bata idone dakai ba inkai haka ka taimaki rayuwana da ga auren kaddara aure alkakai da zan tsinci kaina acikin shi gidan mashay,,,,, Kau ya kwashe ni da mari daidai maryam na shigowa falon daga waje, bata tsaya ba tai ciki gurin maji.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,

IDAN KIN KARANTA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDA HAKA MUNA BINKU BASHI,,,,

Readers Also Read