A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 80
A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 80: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 80. ****** ********* ****** Ina idar da sallah na fito na fara…
2,483 words
****** ********* ****** Ina idar da sallah na fito na fara gyaran gidan kafin wani lokaci gidan ya dauki kamshi gaba daya, nan na fada kitchen for the first time don na fara girka abinci da akaina. Kayan aikine na electronic gasu nan kala kala a kitchen din na fara tunanen wani simple abinci zan yi a lokacin. Ina bude store din kitchen din naga kayan abinci da na,shaye, shayen, kwali da sauran duk abinci da sha tap a store din. Na dan dade tsaye ina bin kayan da kallon mamaki don abin yayi yawa sosai a store din. Dankalin iris na debo tare da kayan miya nai tunanen yin dan fate mai ruwa na sa naman koda dake cikin fridge din na dan yi amfani da danyen attarudu. Sai ruwan shayin dana dafa yaji kanunfari kamshi na tashi daga cikin shi. Ina tsaye a dining ina gyara kayan abinci naji ya shigo gidan cikin kayan motsa jiki yake. Ban san baya gidan ba sai da naga dawowan shi daga inda nake tsaye nace mai ina kwana. Lafiya kawai ya amsa dashi ya shige part din shi kai tsaye inda ya shiga wanka. Nima wanka na shiga na gyara jikina ina tsaye bakin wardrobe dina da hijjab dina don sai da nai sallah walha, zan dauki kaya naji an shigo dakin. Na juyo a firgice ina ganin shine nace cikin daure fuska don may za,a shigo min daki haka ko sallama babu kuma. Kallon mamaki yai min tare da daure fuskan shi sai kuma naga ya dan dara yace dakin ki fa kikace yarinya? Nace au nan din dakinkane ko kaga ni nashiga naka dakin ne da zaka ce nan din ma nakane? Yace lalai yarinya kina da karfin hali wallahi ni da gidana kuma yau ake son kafa min doka akai. Yace to bari na tunatar dake in har kin fara shagala kin samu gidan zama. Ki sani duk wani abinda ke cikin gidan nan gaba daya har ke mallakana ne don baki san yadda na samay su ba. Saboda haka ina son ki shiga hankalin ki daga yau don kada ki wani mike kafa wai ke ga maigida tunda kinga banza ko ? Ashe shiyasa jiya nida gidana da kayana har kika sawa daki key wai ke ga mai daki ko? Nace saukin abin dai nima ba kasuwa aka dauko ni ba dai yace towa kuma yasani sai anbincika wanan. Raina yai balain baci nace kamar yadda kaima akwai alaman bincike akan ka dole. Sadauki yai murmushi saboda yaba ma karfin halina yace yarinya idan zamuci gaba da haka zanfi kowa farin ciki da hakan a gidan nan. Yace ai duk macen da zatayi abinda mijin ta ke so ana kyautata zaton samun sakamako mai kyau a gurin ta. Don haka mu zuba dake a haka a gidan nan aga wanda zai sha wahala. Ya fara tafiya yake cewa sai ki fito muci abinci don ban yarda dake ba kada ki kashe ma uwana ni. Nace bazanci ba idan kaci sai ka mutu don kai ke tsoron mutuwa yanzu kuma ma na kashe ka nakai tarin zunubin ka ina ? Yai murmushi yace ban dai yarda ba na fada maki ina jiranki a falo don nasan halin yan kauye da son banza don a gajewa uwata da yan uwana dan abinda aka gani. Ya sa kai ya fice daga dakin yana dariyan keta raina yai balain baci haka na karasa shiryawa ina mitan maganan shi a raina. Kaman bazan fita ba amma kuma sai tsoro ya kamani kada yazo wani abu ya samay shi ace nice nafito tare da dan saka takalmin na tare da daura dankwalin rigana ga kaina sai karamin hijjib na saka iya kafada na. Saye nake a cikin redmaid din dogon rigan abaya maroon color nafito nima sai kamshi ke tashi a jikina. Yana zaune yana waya yana jin motsin fitowana ya kura min ido da sauri naga ya kawar da kan shi gareni. Ashe gaban shi ne yai wani mugun faduwa ganin yadda na sake mai a lokaci guda. Naja kuran dake gefe zan zauna yace kaji min yar kauye yana kashe waya yake kallona yace wancan kujera zaki dinga zama mai fuskantar wanan don kada wani ya shigo ya samay ki cikin zaman kauyawa ace yar kauye na kwaso gida na. Ban zauna ba sai jawo plate din da nayi na fara zuba mashi abinci komai da ya dace na dan zuba mai yadda muka saba zuba mai a gida. Na koma na zauna a inda ya umurce ni yana daukan spoon yace one warning again daga yau idan ina gidan nan bana son ganin wanan takunkumin hijjabin naki kamar zaki cin kasuwan kauye dake. Nace ai ni ba don ka na saka ba don Allah nake saka abina dama. Yace kin makaro da wanan dakin zauna gidan ku sai kita faman saka abinki amma ba gidan Umar ba kan. Haushi ya kamani ganin ya kura min ido yana jiran na cire hijjab din dake wuyana. Dole na dan sa hannu na zare hijjab din daga wuya na gaba daya surana yafito a fili. Sai lokacin naga ya fara cin abinci nikan na kasa sai naji yace may kike nufi ko dai da gaske kinyi barbaden ne a ciki wai? Nace banda gadon wanan amma ban sani ko ku kunayi a gidan ku shiyasa kake ganin duk mata haka suke. Dago kai yayi ya kalleni yace dakata kada wautanki ya kaiki ga zagin gidan mu yanzu na koya maki wayyo a gurin nan. Shiru nayi don nasan zai iya idan na kara magana na fara shan dan faten da na zuba a plate a hankali. Banyi ko rabi ba naji na koshi sai na fara juya cibin kawai ina wasa dashi a plate din a hankali. Yana kallon abinda nakeyi bai min magana ba har yagama ci na mike zan fara kwashe kayan. Yace shiyasa baki kiba oya maza ki cinye abincin nan kafin nazo na sure ki dashi yanzun nan. Don bakin barna kinga banza yasa kika dafa da yawa kin san baki ci? Na turo baki gaba nace nifa gaskiya na koshi don ban jin yunwa saboda ba abinda na hade balle yunwa ya damay ni. Tsawa ya daka min yana fadin will you finish it my friend ? Dole na dan fara turawa kamar zanyi amai ga nauyi da kunya da suka cikani lokaci guda. Ganin saura kadan ya mike ya bar gurin na zaci fita zaiyi amma sai naga ya koma saman kujera three seater ya kwanta tare da dora kafan shi daya saman kan kujeran. Kitchen na shiga na wanke kayan da muka bata na kara gyara gurin da mukaci abinci na juya zan shiga daki naji yace. Waye dan gadin gidan ki kina daki ina falon ina maki gadin gida maza ki dawo nan ki zauna mara kunya kawai. Nace ikon Allah nifa ba boya bace don naga kana son mayar dani kamar wata wacce ka sayo. Yace amma ke yarinya ce karama ba,a fada maki cewa sadaki na biya bane lakadan ba bashi ba kikazo gidan nan ne ba wai. Don haka ina da right din da sai abinda nake son za,ai min a cikin gidana idan kuma kince ba haka ba sai na kira maman naki da taci kudin sadakin nawa tazo nan tabani abina yanzu. Don ba zan biya kudina ba don bukata na kuma a kun tata min a banza yadda nace dole shi za,ayi a gidan nan kinji na fada maki daga yau. Haka na dawo falin na zauna ina jiran wani sabon cin mutunci daga bakin shi kuma. Bai min magana ba sai wayan da yake ta bugawa ana kuma bugo mashi wanda akasari murna ake mashi kan auren da yayi. Sanyin A C da yai yawa a falon yasa na dan takure a guri guda har barci ya daukeni a zaune ban sani ba. Jin kaman nai barci a inda nake zaune yasa shi juyowa yaga ina barcin kuwa. Ido ya kura min har tsawon wani lokaci yana bin ko ina na jikina da kallo har tatsun hannu na da kafa sai da ya kare masu kallo lokaci mai tsawo. Nikan sai barcina nake hankali kwance jin kaman an tabani yasa ni farkawa furgigit idon shi a kaina. Na turo baki tare da gyara wuyana da yai min tsami nace ni dai in mutum yana maita ne ko shan jini wallahi kurwa na kur akan shi. Dariya yayi yace yar kauye kona kara maki karfin A C din ne don naga kinji dadin hakan har da sake min baki kina barci. Nace inda bamu dashi ne a dakin uwata sai kai min gori dafin abin kafin kayi kudin ka kaganta dashi. Yace ai nasan shi ya jawo ki yanzu tunda can kauye babu shi anzo an samu na banza ana sha nan. Nace dakata wallahi gida gidane haka uba ubane kada ka kara zagan min gidan iyayye na nima. Yace idan an zaga may zakiyi nace na rama aiko yayo kaina cikin tako daya duk yunkurin mikewan da nayi nagudu sai da ya cin min gurin. Nan ya matse ni saman kujeran muna shakan nunfashin juna yace ki rama din ina sauraren ki. Shiru nayi ina fadin ka sake ni kawai mugu sai kara matseni a kirjin shi da yayi bai sake ni ba. Wani irin bugawa naji kirjin na yi fal, fal gashi kuma bai sake ni daga jikin shi ba. Nace cikin karfin hali mugu kawai ka sake ni wallahi ko na fadawa mama cin amanan da kake min yanzun kuwa. Yace go ahead kirata yanzu tunda baki da kunya ki fada mata na matse ki ko ? Sai da ya gaji don kan shi ya sakeni daga jikin shi na tashi da sauri nai daki ina fadin mugu kawai ni bari ma na cire kayan nan don sun haramta gare ni daga yau. Yace wallahi duk kika cire kayan nan sai na tube ki zindir a gidan nan naga tsiya. Ke har wata mace ce can da kike ganin kamar kina da wani ajine wai? Daki na koma na zauna a bakin gado idanuwana suka ciko da hawaye don takaici. Nace a raina may kullun yake nufi da fafin wani har mace ce da za,a gani aji sha,awan ta ko may ? Muryan shi naji daga falo suna gaisawa da wasu haka yasa da sauri na saita kaina nasan baki mukayi a gidan. Ashe yan uwan mamane suka zo gaida mu da kuma yi muna sallama washe gari zasu koma gida. Shi ya shigo yana fada min zuwan su tare da jamin kunne na saita kaina in har na bari suka fahinci wani abu har naja sukai mashi fada sai na yabawa aya zaki. Nafito ina murmushin dole nace lah mama kune ashe sannun ku da zuwa. Maimakon na zauna saman kujera sai na zube kasa ina gaida su a cikin girmamawa. Masha Allahu Baba kaikan wallahi kayi dacen mata a rayuwan ka yarinya haka da ladabi, yaushe yaran yanzu masu rawan kai zasu tsaya yiwa sarakai wanan gurmamawan haka. Baba don girman Allah ka rike matar da daraja ku mutunta junan ku, ku rufawa kan ku asiri a tsakanin ku. Darajan miji shine na mata yadda ka mutunta matar ka haka duniya zasu mutunta maka ita. Ke kuma Fatima don Allah basai mun fada maki ba don yaran yanzu boko yasa kun san komai na rayuwa zaman takewan aure sai dai idan kun ki amfani dashi kawai. Don haka kin dai ga yadda uwar ku take rayuwan ta a gidan ku idan kinyi koyi da halin yayan mu da kika zauna da ita babu wani rayuwan da zai gagareki hakkuri a duniyan nan. Don haka yi nayi bari na bari abinda duk mijinki bai so kin sani, don kun zauna guri guda gwargwado kin san halin shi yasa naki. Gaba dayan ku idan kuka ba da kunya uwar ku kuka tozarta ita da taga dacewan hakan ta hada ku. Komai yaya bata boye muna ba na hadin da tai a tsakanin ku kuma ku yanzu bazaku taba fahintar manufan ta ba sai nan gaba. Don haka ku taru kuba mara da kunya ku kashe ku bisa a tsakanin ku ba komai ne ma ita yayan sai taji shi ba tsakanin ku duk abinda zakuyi ku boye sirin auren ku tsakanin ku don gujewa shigan ta wani hali. Kai kuma Baba don Allah duk wani abin kurciya da akayi sai abarshi a matsayin kurciya ne yanzo kakai ga tara iyali nan zuwa badi war haka in Allah ya kawo rabo sai kuga mun dawo taron suna gidan nan kuma. Nan dai sukai muna nasiha ma ratsa jiki suka zauna nan tare dani sai dare suka koma gidan mukai sallama cewa bazasu dawo ba kuma. Har kofa na raka su suka tafi suna muna fatan alheri da samun zuria ta gari. Suna wucewa na koma ciki wanka nayi tare da sallah ishai na zauna ina zikiri naji dawowan shi gida tare da rufe kofan gidan. Hakan yasani sani bazai fita ba ko ina ke nan again ganin shi nayi tsaye da farar leda a hannun shi, na dago kai na dube shi ban san yaya akayi ba naji bakina yana mashi sannu da zuwa a lokacin. Ledan ya miko min yace na dafa mashi liptop din dake cikin ledan naman kuma na kai mai falo saman dining zai fito yaci. Inda ya aje min saida na shafa namike zuwa yin abinda ya sani na fara dafa ruwan liptop din batare da na tsaya karan ta kona maye ba. Na fito na aje mai naman da zafin shi a table tare da ruwa da drinks mai sanyi. Ina kitchen naji fitowan shi, falon ya zauna ya fara cin naman da na aje mashi. Sai da na juye ruwan ga wani dan karamin flask na hado da cup na nufo falon yana zaune yana cin naman shi hankali kwance nace ga shayin na dafa. Ya dago kai yace injin baki zuba sugar ba a ciki nace mai a,a hakana na dafa don ban san ko na may ye ba. Da hannu ya nuna min na aje anan ina ajewa na juya zan shige yake cewa ke bazakici naman bane ? Na koshi na bashi amsa a taikace yace may kikace ban fa son shegen gardaman nan naki kinji na fada maki. Nace naci abinci a dasu mama na koshi dazun kafin su wuce don sai da nai masu girki sukaci da yamma. Baice min komai ba na juya na shige na zaci daya gama zai shigane amma sai naji ya kunna TV dake falon ko da ban fita ba wasan kwallo akeyi a tv nace bissimillahi Allah nazo gidan masu yi. Ni dai har barci ya kwashe ni ban san lokacin da ya shige ba sai tsakar dare na falka naji shiru na kara jan bargona na gyara rufe jikina da kyau.