A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 81
A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 81: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 81. ****** ********* ****** Haka mukaci gaba da rayuwa a gidan…
3,010 words
****** ********* ****** Haka mukaci gaba da rayuwa a gidan zaman doya da manja ba wani abinda ke shiga tsakanin mu sai in yana bukatan wani abu zai shigo daki ya fada min. Sai dai a nawa bangaren ina hankalina a tashe yake don ina ganin bazan iya cika alkawarin mama ba akan shi don a halin yanzu ban san wani rayuwa ma yake ciki ba agidan sunan muna gida daya ne kawai dashi. Satin mu uku da aure na gama komai gashi hutun mu ya kusa karewa zamu koma school wani sati. Sai ganin shi nayi dakin lokacin ina kwace na kifa cikina a saman gado ina sauraren kira,a a wayana kaina babu dan kwali na daure gashi na da ribon ta baya , Ganin ya shi ya shigo yasani saurin lalabo dan kwalina na daura akaina kallona kawai yayi ya basar kamar bai san may nakeyi ba. Yace ke nazo na fada makine yau da dare zan koma gurin aikina don haka sai ki fada min abinda kike bukata a sayo maki idan na fita. Nace ni ban bukatar komai sai dai Monday mai zuwa zamu fara school insha Allahu. Yace gashi ke baki iya mota ba balle na bar maki motana kiyi amfani dashi sai kuma idan wani driver zan samo ya dinga kaiki. Nace ai ko da kake daukata yar kauye ba wai doluwa nake ba yadda kake tunane don ni mota kuma yanzu sai dai na koyawa wani tuki. Fatan kawai yanzu Allah ya hore min yadda ya horewa kowa na samu nawa na kaina insha Allahu. Kallon mamaki take min kaman zaiyi magana sai kuma yai shiru kawai yafita daga dakin. Duk da nace komai akwai shi a gidan amma sai ga kaya niki niki maigadi ya shigo dashi wanda kusan yan kayan lashe lashe ne a cikin kwalayen. Sai da yai wanka yafito ina kitchen ina girka abincin dare ya zo bakin kitchen din ya tsaya yake ce min zancen motan da mukayi dazun na binciki maryam ta fada min ki gwane don kece ke jan ku zuwa school don haka ga motana nan zan bar maki ki fara amfani da ita kafin na duba wanda ya dace a sayo maki. Ni zan shiga gurin maji nai masu sallama kagin dare yayi min sai ji nayi nace ni dawa zan zauna cikin wanan katon gidan haka. Yace kedawa kikazo gidan nan dama baki san gidan yadda yake bane kika shigo kai tsaye. Shiru nayi nace to don Allah ko na roka kanina musa yazo ya zauna dani kafin ka dawo. Yace no kada ki fara min aanan tarkace inama laifin ki ce nace Amirah tazo ta zauna dake har na dawo. Nace amma kana gani ita anty zata yarda tazo gidan nan saboda ni kuwa ? Gidan ki ne ko gida na Amira fa yar uwatace kada ki man ta da hakan don haka ki barni da tsarina kawai. Ya juya yafita na ce o Allah takawo ni gidan gwauna kaida sai dai obey the rules kawai ba jin views din mutum. Ya samu mama zaune falo tana zaman kadaici na rashin mu tare da ita bayan mun gaisa take tambayan shi lafiya na yace ina lafiya kalau. Tace da fatan dai ba wani matsalan komai a tsakanin ku ko? Ya kai haba maji matsalan may kuma dai ni nama zo ne nai maku sallama yau zan tafi Spain ne muna da wasan da zamu buga har agentina zan tafi ina ganin kuma zan kwana biyu a can idan na tafi. Da sauri mama tace ita matarka da,wa zata zauna tsawon wanan lokacin haka dake fadi? Yace da cewa nayi ko Amirah zata koma can har na,dawo, amma ita kuma naji tana fadin wai ko za,a dauko mata kanin tane agida ? Sai dai na kashe wanan magana don ban yarda da yan kauyen na su zo su zauna min gida ba suyi min barna. Kana da hankali kuwa yan kauye kan tunda ka dauko diyan su ai kashiga ganin su ke nan a gidan ka. Ina yaron kanin tane uwarsu daya kuma ba wani babba bane can fa shi yaron. Kuma ma ita wanan malaciyar inba kwanciya ba may zata yi a gidan amma shi yaron ko wani aike ne ko aiki ai zata iya saka shi yayi mata ko ? Kada fa kace zaka hanata zumunci da yan uwanta, tun yanzu dan sune gatan ta. Ya ce maji ba wai zan hanata zumunci dasu bane kawai gani nayi dauko yaron kaman wani long process ne kuma yanzu. Mama tace aa ka aje da zai kaita makaranta kuma don dazun maryam ke fada min wani sati zasu fara school insha Allahu. Yace mun gama wanan magana ko zanbar mata motana tayi amfani dashi don ashw maryam ma ta koya mata mota ko. Tace madallah ubangiji Allah yai maka albarka Allah ya baka zuria masu albarka da zasu tausaya maka kaima. Yace amin maji nan ya ciro kudi masu yawa ya bata yace ta rike a hannun ta idan da bukatan wani abu a bayan shi sai ayi. Yadda ya saba tafiya a gida ba tare da daukan kaya ba yauma haka yayi sai yar bakar jakar tafiyan shi kawai ya rataya. Ina zaune falo don na kasa zama daki kamar mai tsoro yafito ganina zaune a falo tasa shi zama a falon shi ma yana waya ina ganin bashar ne don naji yana fadi ya biya ta gida yazo da Amira kafin ya wuce. Sai da ya gama waya ya miko min kudi yana fadin karbi na nan nakali kudin tare da karba sai baice min komai ba. Cikin karfin hali nace namay nene kuma yace ki rike a hannunki don amfani idan kuma ma da wani matsala bashar yana gari sai ki nemashi. Ni gaskiya kudin nan sunyi min yawa ban da abinda zanyi dasu haka dubu biyu ma sun isheni saboda naga komai akwai a gidan ai. Kallon mamaki yai min yace wanan kudin ne sukai maki yawa dubu darine fa kawai idan kuna son sayen wani abin fa bana gari. Nace ni dai sunyi min yawa don ban saba kashe kudi ba komai mamane take saya muna na fadin cikin sanyin murya. Ok sai ki aje a gurin ki idan na dawo sai na karba don ban saba alheri ba na karba ni. Bashar suka shigo da Amirah sai wani shan kamshi take kamar an sata zuwan dole ne nake gani. Amma tana ganin shi ta dan sake tana fadin yayana dazu shine kaje gida ina barci baka sa atayar dani ba sai dana tashi maji ke fada min kazo wai yau zaka koma. Yace Amira ai ina ce baki gidan ne ma a lokacin da dake zanyi magana yanzun dai ga wanan nan zaki zauna min da ita har na dawo ba zan dade ba nake gani sosai sai dai kuma yadda tafiyan ya kaya min dai idan naje. Kudi yabata itama madu yawa yace ina tsan mani akwai komai da zakuyi amfani dashi abinda babu dai ga Bashar sai ku tuntube shi kawai. Bashar ya shigo ina gaishe shi yake fadin kaunata ashe yau wanan mayen ball din zai koma ya bar min ke ai yayi arziki hutun ku ya kare da kafanshi kafan ki wallahi. Tsaki sadauki ya mashi yace dan Allah mu tafi ni ban iya shirmay ka da ka saba kaji. Sai naga na mike nima da suka mike kallo na yayi cikin yanayin da bazan fahinci na maynene ba, sai suka fara tafiya daga ni har Amirah muna bayan su tafe. Sheri bashar ke mashi wai ashe shine bakauye yana kira min kauyan ci murum zaiyi tafiya mai nisa shine zaiwa matar shi wanan sallaman haka. Yace kai dai kasani jarababen banza ni yanzu ma har ina tausayawa maryam da wanan shegen jaraban naka da ka samo. Yace ni matata ba irinka bane don chakwai muke abin mu ban kuntata mata bata kuntata min kaine aka bari da jan ajin banza kawai. Suna shiga mota muna masu Allah yakai lafiya ya bada sa,an tafiya. Sai da suka bace muka shigo ciki mai gafi ya rufe get inda suma naga ya tsaya ya basu wani abu. Muna shiga ciki batai min magana ba naga tafara jan dan troler din ta ta nufi dayan dakin dashi nace ,a a anty ba anan zamu zauna tarw bane. Ta wani juyo a wulakance ta dube ni tace ina ko kin mata ni bani zama da kowa daki dayane don ban son yawan takura. Sai kawai taci gaba da tafiyan ta can kuma taja ta tsaya ta juyo duk ina tsaye ina kallonta tace Bintu kada fa ki manta gidan dan uwana ne nan ina da right din shiga duk inda naga dama batare da wani shamaki ba. Kiyi hakkuri anty ni bada wani manufa nai magana ba gani nayi gidan nada girma mu zauna daki daya kawai shi yafi. Tace to ba zan zauna ba sai inda naga dama zan zauna kuma kada ki kara cewa zaki min katsalandan ga al,amarina kinji na fada maki ko. Ni dai nabita da kallon mamaki don ban san laifin da nai mata ba har muka koma haka da ita kaman wasu makiya can.
ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI DA ALLAH,,,
ALOKACIN MUKE,,,,,
Tunda nai wanan mafalkin na tashi jin kaina nake yana min wa ni irin ciwo gani banda sukuni a tare dani. Haka na daure nai muna abincin rana tare da na dare a lokaci guda sai dai ina sake sake a raina kan mafalkin kabir da nayi may hakan ke nufi ne wai? Kudi na fito dashi da abinci nace ma musa ya bayar min da sadaka a waje ya samu karamin yaro ya bashi. Na gama shirya dining table da kayan abincin dana girka nashege daki na kara wanka. Dogon rigan atamface a jiki dinkin shi mai hannu daya ya matse ni sosai rigan wanan dai kan sai zaman gida don da aka kawo dinki naita fada da anty maryam akan dinkin. Ina fitowa ban san da dawowan shi ba sai ganin shi nayi falo kwance saman dogon kujera ya sa hannun shi daya ya rufe fuskan shi dashi. Dagani tunane yakeyi ko may yake tunane oho sai da nakai daidai kan shi na tsaya daga bayan kujeran tare da dan rakwafowa saman kujeran nace. Sannu da dawowa yaya kamar daga sama yaji murya na sai naga yai sauri cire hannun shi firgigit da sauri yana bude ido mukai arba dashi. Cikin mamaki ya amsa min fuska a daure yana cewa yyawa nace akawo ma abin sha ne ? Eh kawai ya,bani amsa na juya zuwa inda fridge yake, na dauko lemon five alive mai sanyi da cup. A kasale ya mike zaune daidai ina isowa da drinks din a hannu na sai dana aje cup na bude lemon na fara tsiyayawa a cup din. Na dauka tare da mika mashi sai naji ya sauke ajiyan zuciya yana karba daga hannu na. Sai da na samu kujera na zauna ya kai cup din a bakin shi ya fara dan kurbawa a hanlali tare da lumshe idanuwan sh. Sai da ya kurba kusan sau biyu naji ya ce may ya hada ki da Amira ne wai ? Shiru nayi ina wasa da yatsun hannu na kaina a kasa sai ji nayi yace bake nake tambaya ba ne ? Nace wallahi yaya ni ban san wani abu ya taba hada ni da ita ba. Kwayar idona ya daga idon shi ya kalla don tabbatar da maganan da nayi yace kin tabbatar da hakan da gaske ba abin da ya hadaku bayan bana nan ? Kai kawai na daga mashi da eh haka ne din amsa na . Yace shi ke nan ai idan ma wani abu kikai mata ai zanji don zan dauki mataki akan hakan. Don ba zan yarda matar da nake aure ta wullakanta min yan uwan haihuwa na ba ko kadan. Dan murmushi nayi nace nima ai yan uwana ne don banda wanda sukafi a garin nan yanzu don may zan mata wani abinda ranta zai baci akaina. Wanan kuma ai matsalar ki ce ni dai kin ji may na fada maki ai sai ya mike tsaye zai fara tafiya nake cewa abin yana saman dining tun dazun. Sai nayi sallah zanci ya bani amsa ba tare da ya juyo gare ni ba nan nabi bayan shi da kallo kawai. Dogon mutum ne sai dai ba irin can din nan ba kuma karfafa ne mai fadin kirji ga shi da dan dogon fuska da hanci irin zubin fulananin kasan sokoto sak dashi. Musa ne ya dawo yana cewa anty na dawo dazun na samu bakya falo. Sai a lokacin na dawo daga tunanen wanan zaman da baudaden mijina da nakeyi. Don nidai yanzu ban san kuma wace irin kulawa ake so na bashi ba wanda yafi wanan da nake mai yana mai dani kamar wata shakatafi can. Na saki ajiyan zuciya a fili tare da dan murmusawa nace ga abinci can fa na zubo maka ne musa. Yace anty lokacin sallah yayi alwala na shigo nayi naje massalaci hakan yasani mikewa nima na shiga don nai sallah. Bayan na idar da sallah ban mike ba ina zaune a gurin da nai sallah na dan jingina jikina da gadon dakin sai tunane nakeyi. Shine ya shigo dakin daga kofa ya tsaya yana fadin abinci fa ? Sai da na shafa nace gani tafe har musa ma yana zaune falon nashigo. Direct dining na nufa na fara kokarin bude kulolin abinci lokacin suka karaso suka zauna. Sosai yake cin abincin hankali a kwance sai can ganin ban zuba nawa ba yake cewa ke bazaki ci bane nace na koshi. Da sauri ya kara dago kai hannun shi rike da spoon din da ya debo abinci zai kai a bakin shi yake cewa. Da kikaci may kika koshi nace breakfast din da mukayi dazun bana jin yunwa yanzu. Tsuki yayi yace will eat now my friend ban son wasa da yunwa kada ki jawo wa mutane matsala. Na dan turo baki tare da tabe fuskana nace ni wallahi ban jin cin abinci a koshe nake yace ko kici ko na dura maki shi yanzu kuwa. Dole na zuba kama spoon hudu na dan fara ci sai dai kuma na kasa ci sosai don banjin ci din. Daga inda yake zaune ya taso sai ganin shi nayi a gabana yana fadin oya open your mouth. Wani kallo na watso mashi nace ni wallahi na koshi musa na ganin yaya ya mike ya nufe ya mike dama yagama cin nashi yafice a falon bayan ya dauke plate din. Ganin da nayi da gaske yake zaiyi feeding dina da kanshi yasa na fara tura sauran abincin da sauri a bakina yana tsaye yana kallo na gani saura kaman spoon daya yasa shi jan tsaki yace kan cin abinci sai na saba maki a gidan nan. Tunda na gane so kike kija min fita gurin maji tace na barki da yunwa cuta ya kamaki don sheri. Ina gamawa na kora da ruwa tare da dan dafe kaina a hankali wanan ai cin zalin ne na fadi a hankali na dauka ya wuce ne ashe yajini. Sai kawai naji ya kamo min baki yana fadin wanan bakin mai bakar magana da tsiwan tsiya sai na yi maganin shi. Zan bude baki nai magana sai hannun shi naji a bakin nawa mikewa nayi don na gudu sai ji nayi ya rugumoni ta baya ya matse ni a jikin shi. Cikin wata yar kara nace don Allah yaya ka sake ni na daina wallahi kayi hakkuri please ka sake ni. Maimakon ya sake ni sai ji nayi ya kara rugomoni sosai ajikin nashi ya shiga bin jikina a hankali. Kafana naji ba zai dauke ni ba a loka in don irin abubuwan da yake min a lokacin. Sosai ya matse ni yadda ran shi ke so a lokacin kuma gashi na kasa hana shi. Sai ganin abin nashi yana son wuce gona da iri nace cikin wata kasalaliyar murya don Allah dai yaya ka kayi hakkuri na tuba na daina zan dinga ci. Hannun shi yakai a kirjina abinda yasani saurin zillewa da karfi nai kasa ke nan da sauri Allah yaban sa,a ya sake ni. Wani irin numfashi ya sauke tare da shafo kan shi ya juya zuwa dakin shi ya barni a gurin a tsugun ne. Cikin jin haushin abinda yai min naja kafana zuwa dakina saman gado na fada a rigingine idanuwa suka shiga kawo hawaye a lokaci guda. Na furta ya Allah ka bani ikon cinye wanan jerabawan da nake cikin sa a cikin sauki. Shima dakin shi ya shiga kwantawa yayi yana mamakin kan shi don bai san yadda akayi har kai ga taba wanan yarinyar ba haka yau. May yake bukata gurin wanan yar kaunan bayabayan shi haka ne wai ? Sai kuma yai murmushi zuciyar shi tace may tarasa acikin abubuwan matan da kake bukata ita . Ba gashi yanzu yanzu kashiga wani bakon yanayi ba a zuciyar ka ka kasa controlling din kan ka akanta sai da ka dan taba ta ka samu natsuwa a ranka. Ranan bai kara fitowa ko falo ba yana ciki a kumshe nima dai hakan ne ina dakina a kwance don yanzun haka kunya yadda zan hada ido da yaya yau nake ji. Yadda yau ya hagula min jikina haka son ranshi yanzu a haka yana mashayi zan dinga bashi jikina yana yadda yaga dama dashi son ran shi. Oho ni Fatima naga ta kaina zama da mashayi hada jiki dashi don raya sunnan ma,aiki don gujewa zunubi a kaina. A hankali na lumshe idanuwa na har tsawon wani lokaci sai tunanen makomar rayuwa na ke yi kawai. Bayan sallah la,asar naji fitan shi daga gidan haka yasani sauke ajiyan zuciya na fito falo na zauna da musa nan mukai ta hira akan matsalan mahaifin su.