Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 85

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 85

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 85: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 85. ****** ********* ****** Washe gari kafin kowa ya tashi na gama…

1,771 words

****** ********* ****** Washe gari kafin kowa ya tashi na gama hada komai na gyara ko ina na gidan sai kamshi ke tashi na koma ciki na gyara jikina tare da saka kaya wani dogon riga Afr abaya mai simple design. Ina zaune gaban mirror wayana yai kara na dauka ina mamakin mai kira na da safiya haka. Anty maryam ce ina dagawa tace amarya kina kamshi fa, yaya labari. Dan tsuki nayi nace kai anty maryam ni dan Allah ki rabani da wanan zancen kinji. Tace cikin daga murya may kike nufi wai wallahi Bintu kiji tsoron Allah duk wanan nasihan da nai maki kina nufin baki dauka ba ko may ? Nace haba Anty yaya kike son nayi da mutumin da baidamu dani ba zargina mafa yake wai bai yarda da sauyin da yagani gare ni ba. Dariya naji tayi tace bashi bane ya fara kamuwa ke nan kedai kawai yi yadda na fada maki shi da kan shi zai kawo kan shi gare ki sai dai in ba mace ta haife shi ba. Amirah ta koma ne nace tana nan what wani gulma ya tsayar da ita kuma a gidan ku amma dai Anty bata da kunya wallahi. Yanzu zan sa maji ta aiko a dauke ta tunda ita bata san ya kamata ba don may zata zauna maku gida ta haku walawa. Shi musa nasan namiji ne ba zai tsaya saka maku ido ba namaji yayana na fadin makarantan kwana yake so ya sama mashi nagari ya kai shi. Wani mugun dadi naji a raina nace da gaske Anty tace wallahi jiya naji yana magana cewa yana nan yana mai process don baya son ya koma kauyen nan kuma don yaron nada kirki. Nace wai ban ma san urin godiyan da zan ma yaya Bashar ba wallahi na dade ina tunanen mafita akan kannne na anty don haka suke zaune ba karatu wallahi. Tace a sannu duk sai ai masu mafita yanzun dai mu samu kan wanan baudaden mijin naki tukun shine mafitan komai. Nace nifa anty ba wai ya damay ni bane kawai ko hakan ma da muke is ok ai. Tace kina da hankali kuwa Bintu mace baliga kamar ki zaki zauna danamiji sai kallo ni na fada maki sa ido kiyi kallon yadda zamu kamashi wallahi. Mun dan kai wani lokaci muna waya da ita tana kara fada min abinda zanyi, mukai sallama da ita. Muna gama waya ta kira mama tana cewa bayan sun gaisa ko anty Amira na kusa na kira wayan ta bai shiga ba tace ba tana gidan yayan ku ba ko kin manta ne ? Tace bata dawo gida bane mai takeyi a gidan kuma bayan maigidan ya dawo ? Yaushe ya dawo inji mama tace jiya da yamma mana ya shigo gari haba dai ita ko gidan amare mijin mutum ya dawo may zata kuma zauna yi masu a gida? Maji tace ai yanzu zan tura Abdul ya dauko min ita bata da kunyane da bata zauna a tsakanin su ba ai. Bayan sun gama waya da Maryam mama ta kira wayan yaya tana cewa ashe ka dawo ne Baba na? Kunya yaji da ta fadi haka yace cikin dan kamay kamay wallahi yanzun nake shirin nai wanka nazo gida ai. Tace babu komai ka huta abinka har zuwa yamma ka shigo ai wanda ke da iyali kuma ina zaka da dawowanka. Sai dai ka fadawa kaunan ka ga Abdul nan zuwa yanzu ya dauke ta maza ta dawo gida. Ban san may ta tsaya yi maku gida ba kuma bayan tasan kana bukatan hutawa da iyalinka. Murmushi yayi kai haba maji jiyane fa na dawo ai ba komai takeyi ba zata dawo anjima idan zan zo . A,a maza yanzu ga Abdul nan zuwa zai dauko ta dawo gida haka na ladan ya isa kuma. Suna gama waya da mama ya shiga wanka sai da ya shirya tsab cikin kanan kaya kamar yadda ya saba shiryawa, ya fito daga dakin shi sai annuri da kamshi ketashi gare shi. Amira ce zaune a falo nan ya zube gurinta suna gaisawa da ita sai wani shan kamshi take wai tana fushi ya shiga guri na amma shi bai ma fahinci may take nufi ba da hakan. Yace maji tace ki shirya ga Abdul tafe yanzu zai tafi dake wai. Bata so batace tunda safen nan kamar abin kora kuma ? Yana zaune idon shi na akan kofana amma babu alaman fitowa na a lokacin. Mikewa yayi tsab ya nufi dakin nawa tsaye nake ina shirin fitowa ke nan Allah ya ingizo shi dakin. Ina ganin shi na zube kasa ina fadin ina kwana yaya? Yace ba tare da ya amsa ba Amira zata koma gashi kayana basu iso ba har yanzu. Nace ko zata tsaya har su iso ne juyawa yayi yana fadin umurni ne daga maji. Ki fito ki bamu abinci kafin Abdul ya iso daukan ta mun samu bata falon a lokacin haka yasa na bita dakin ta. Da sallama na shiga amma bata karba min ba nake cewa anty ashe yau zaki koma yanzu yaya yake fada min haka. Tace eh zan koma nabarki kiyi yadda ranki ke so ai nasan kece da aanan kullin don na tare maki guri jarababban yarinyar kawai. Haba anty may kika tare min aiko kina nan ba,a fasa abinda za,ayi kinga ashe zaman ki bai hana komai. Bintu kada fa ki kawo min rashin kunya wai ke adole ga wace ta san dadin namiji ko ? Dariya nayi nace anty aure ne fa kema idan kikayi zaki gane haka ba wai jaraba bane dadin aure ne kawai. Lalai yau Bintu har nikikewa gorin aure har wani aure ne kikayi har kika san dadin shi ke. Kai haba anty kema aikin gani gashi kuwa kamar har ya damay ki kullun kina magana a kan shi. Da ki baro idan kayan yaya yazo ki karbi tsaraban ki zaifi ki koma hakana don kada mutanen gida suga kin dawo empty. Dama sjine gurin ku ai ku mamaye komai nashi ya zama naki ke da yan uwanki kawai. Ba abinda zaki taba sai nazo gidan nan don nasan halin yayana dole nice mai raba mashi kayan shi. Nace da ke nan kuma anty yanzun kan ai akwai mairabo tsakanin ku ina fadin haka na fito daga dakin na barta tana yabo min magana. Mun karya duk da a takure nake amma ban yarda Amira ta fahinci komai ba akan zaman mu dashi a gida. Munan cikin karyawa Abdul ya shigo gidan nan suka shiga gaisawa da yayan shi ina gefe nace yaya Abdul ina kwana ya juyo gareni yace sarautan mata yaya kike? Nace mai na zubo ma, abinci ko yace kaman kin san bar karya ba nace nasani mana yaya tunda gauro kake. Bintu yaushe mijinki yai aure da zaki fara kira min gauro saurana fa kusan shekara bakwai ko takwas. Kai yaya wallahi kada kaiwa kanka baki nasan komai fa ina Nadiya take da zakace haka? Yana zaune yanajin hiran mu da yaya Abdul inda ya juya kan Amira yace kin shirya ne ku tafi ? Yaya ko kaima kora na kakeyi ne kaman wanan mara kunyan yar kauyen dake fanin ta samu guri. A,a Nafisa yaushe kuma kuka fara haka da Bintu ina Bintu tai kama da yar kauye ko ada can balle yanzu da ta zama wata princess can da ita. Nace yaya Abdul fada mata dai ko zata bude idon ta tagani ni dai nasan akwai wata a kasa tsakanina da Anty kawai amma ni nasan nawaye ai yanzu. Dariya magana ta tabashi yadda nai magana waina waye Amira tace kaiyya haka kike gani ashe ke don kinga yanzun kina rayuwa a cikin wanan gidan . Abar rayuwan kauye ko nace kai anty ho ke manta ni diyar mamace tun yaushe mama ta mayar dani yar gatan ta. Dama ai shine gurin ku ashigo a mamaye komai ai aleale sai yadda akayi da dangin miji ko? Kai Amira tashi ku tafi please bani son irin maganan nan for god sake kaunan kice fa kubar wanan irin maganan mana ? Yaya Bintu ce kaunata ko wa shiru yayi yadda na fahinci baiji dadin kalaman ta ba a gare ni. Kallon mamaki take mashi tamike tare da shiga dakin da ta mayar nata ganin tafito da jakar tasa namike zan karba. Tace kada ki soma taba min jakkana munafuka zamu zuba ni dake don babu gurin zama agidan nan gurin ki. Ido muka hada yai min wani shu,umin murshi na mugunta tafita batare da tace dashi uffan ba. Mikewa yayi yabi bayan su ina mata agaida mutanen gida. Gurin da mukaci abinci na gyara muna tare da kawar da duk wani abinda ya dace a gidan . Daki na koma ina zaune ban san barci ya dauke ni ba a gurin can yadawo suna falo da musa ya mike zai fita yace ina zaka tafi ustaz yace akwai inda nake fita gurin mai shago muna hira ko dasu maigadi. Yaron nafita yaji zaman falon ya ishe shi don haka ya mike zuwa waje jin dayayi shuri ban fito ba yashiga dakin. Dakina ya shiga ina kwance na dunkule saman gado kamar wata yar jaririya dani. Kallon yadda na dunkule kamar mai jin tsoro yayi ya dade a kaina saida na dan gyara kwanciya tare da kara dunkulewa yabar dakin. Ikon Allah sai gashi nai mafalki da Kabi yanace min Fatima yau ina iliminki da,wayon ki suka shiga. Kina kokari kasa cin jerabawan ki zaki halaka kanki kin kuwa san irin dumbin masifan da zaman dakika zaba da mijin ki yake haifa maki? Ubangiji babu ruwanshi da halin shi rayuwan biyayya da zaman takewan ku zai duba abinda yakeyi tsakanin shi da Allah shi ne. Muddin baki bi mijinki ba Allah zai kamaki da laifin haka, kuma makomar ki shine wuta. Fatima kibi mijin ki kinji sauda kafa don Aljananki yana karkashin kafan shi ki faranta mashi ko yaushe kinji kaunata kad ki halaka kanki. Sai nafara kuka murmushi naga yai min kawai yajuya yafara tafiya kaman cikin wasu duhun itatuwa ya bace abinshi. Zubur na mike tare da salati sai zufan da yafara karyo min a goshi na kawai duk da A C dake aiki a dakin. Kabir na furta a fili wasu irin hawaye naji suna zubi min nace Allah ya jikan ka bawan Allah kila sadaka yake so nai mashi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,

IDAN KUMA K8N BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA NA BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,,

A LOKAC8N MUKE,,,

Readers Also Read